Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 9
rike ta tace "karki damu za'a ganta" hameed wanda ya shigo cikin damuwa tareda su sultan fuskokinsu kaɗai ya isa ya nuna halin da suke ciki, ammi tace "an ganta?" duk sukace "A,a" itama ammi zuwa yanzu ta gama tsorata tace "na shiga uku Amrah ina kike?" kafin ta rufe baki sukaji faɗowan abu daga saman silin, a mugun tsorace sukayi baya ganin Amrah ce ta faɗo kasa kan tiles, jini ne ya fara bin tiles ɗin bakinta ɗaure da ɗankwalin kanta hanunta ma a ɗaure idonta a rufe alaman bata raye tun da jimawa. Ammi duhu take gani ta zama kamar makauniya sai tattaɓa hanya take, zubewa kasa tayi, da rarrafe ta isa wajen zata taɓata ya kaseem yace "dakata ammi kar kiyi saurin taɓata bari a kira police, a rufe gidan babu me fita sai an gwada hanun kowa" gaban aneeta yayi wani irin mummunan faɗuwa ji tayi kirjinta kamar zai fashe tsaban tsinkewan rai, ganin kowa ya tsaya babu wanda ya taɓa gawan an fara rufe kofofin gidan ta kalli Amrah dake kwance sannan ta rufe ido, faɗuwa tayi a kanta kamar ta suma, ganin haka kaseem ya dafa kai yace "wayyo Allah shikenan aneeta ta taɓa ta" Ammi ganin haka ta rungume Amrah kawai ta fara ihu, Amnah kam tana tsaye tana bin kowa da kallo, da masu ihu da masu kuka ita kam batasan ma me take yi ba, tasan dai kawai ta kasa ɗauke idonta daga kan ƴar uwarta abin alfaharinta wato Amrah. _Jiddah Ce....✍️_ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 7* ~Jikin kaseem yana rawa yace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un me yake faruwa?" hameed ma jikinshi rawa yake sai kallonsu yake ya kasa yin komai, minat kallon Amnah tayi yadda ta bushe a tsaye, da sauri taje ta riketa cikin tashin hankali tace "kija numfashi amnah" girgiza kai tayi alaman ba zata iya ba, tace "Amnah kija numfashi" girgiza kai kawai take ta kasa magana, meenat da karfi tace "ya kaseem Amnah fa bata numfashi" da sauri yazo ya riketa, wani irin rikeshi tayi ta kwala ihun daya amsa gidan gaba ɗaya, mai martaba wanda ya shigo yanzu ya zuba musu ido ya kasa cewa komai sai zufa da yake, Amnah da Ammi ihu kawai suke meenat tana tayasu, cikin kuka tace "Amrah meya kawomu? Amrah tarefa mukazo meyasa zaki tafi ki barni?" hameed ɗaga Aneeta dake kwance yayi ya ɗaurata akan sofa, ruwa ya ɗibo ya watsa mata, da sauri ta buɗe ido tana kallon shi, kallon Amrah dake kwance tayi sai kuma ta rungumeshi tana kuka tace "wa yayi haka? waye ya kashe ta ranan aurenmu ayi kisa hameed? hameed na fara tsorata da wannan gidan wallahi akwai wani abinda yake faruwa" mai martaba ne yayi karfin halin yin magana yace "ayi jana'iza kada a ɓata lokaci" kaseem yace "Abi a bari ayi bincike" Ammi dake kuka idonta ya jika da hawaye tace "kaseem a birneta babu wani bincike da za'ayi a bari sai an birneta komai ma za'ayi sai ayi daga baya" yace "sabida bakiso a gano wanda ya kasheta?" da mamaki ta kalleshi sai kuma ta share hawayen tace "banaso kuma? me kake nufi kaseem?" murmushin gefen baki yayi yace "ai kinfi kowa sanin me nake nufi..." a fusace ta mike tana kallonshi da tsananin ɓacin rai akan fuskanta tace "me kake nufi kaseem? kana zargin zan iya kashe ƴar kanwata? ko kana nufin zan bada goyon baya a kasheta?" shima yana huci yace "to meyasa zaki hana?" cikin raɗaɗin mutuwan Amrah da haushin maganan da yakeyi tace "sabida nice na saba kisa? ko ka manta kaine...." mai martaba a tsawace yace "ya isa haka!!! nace ya isa haka!!! wai meyasa kullum ba zaku faɗi alkhairi bane? meyasa kullum cikin zargin juna kuke? maimakon ku maida hankali akan mutuwan da akayi ayi bincike me kyau domin a hukunta wanda yayi amma kuna wannan banzan maganan mara am....." rike kirjinshi yayi yana salati jin wani zafi da kirjinshi yake, idonshi ya rufe kasa ya faɗi da mugun gudu hameed yazo ya rikeshi, kallon kaseem dake tsaye yayi ya kalli jakadiya sannan ya nuna mata kofa alaman ta buɗe mutane su fita, da sauri tace "to yarima" zuwa tayi ta buɗe kofan mutane suka fara fita, saida ya tabbatar mai martaba ya farfaɗo kafin hankalinshi ya ɗan kwanta. har aka fita da Amrah kanwarta Amnah bata cikin hayyacinta, gidan ya zama shiru babu me magana, amnah tana zaune a gefen meenat da ammi tayi tagumi har hawayenta sun tsaya yanzu sai kukan zuci take, Aneeta kuma tunda ta faɗa zazzaɓi ya kamata tana ɗaki kwance, kaseem ne ya shigo sanye da jallabiya yayi shirin kwanciya amma yace bari ya dubasu, da sallama ya shiga sannan ya zauna a kusa dasu yace "sannu Amnah" a hankali tace "yawwa yaya" yayi shiru har na ɗan lokaci, cikin nutsuwanshi yace "dama akwai wanda suke gaba ne?" girgiza kai tayi sannan cikin muryanta daya dishe tace "ko ɗaya Amrah batada abokin gaba, maganan bakinta ma baida yawa kaima ka sani, bata fiye shiga harkan kowa ba..." kuka ta kara fashewa dashi, yace "kiyi hakuri na san zafin da kikeji Amnah kiyi hakuri kuma na miki alkwari saina samo wanda ya aikata wannan mummunan abin" yayi magana yana kallon ammi, itama kallonshi tayi, tun daga kasa suke jiyo karan buga kofa, sunan Amnah ake kira babu kakkautawa, Amnah dake zaune tashi tayi farat tace "Dady ne" tare suka fita yana tsaye sanye da babban riga da alama daga tafiya ya dawo hulanshi ya cire ya wurgar jijiyoyin kanshi sun tashi, hameed dake ɗakin Abi yana bashi malt yaji hayaniya da sauri ya kalli Abi sannan ya kalli kofa, tashi yayi ya fita Abi yabi bayanshi, Aneeta dake zaune akan stool tana kallon kanta a madubi taji hayaniya murmushi tayi ta shafa fuskanta da yayi jajur sabida kukan karya da tayi, rigan bacci ne a jikinta milk color ya bala'in karɓan jikinta, murmushi tayi tace "haka nakeson ji, ko kaɗan banason ganin gidannan babu tashin hankali, ko kaɗan banaso naga ana zaman lafiya a wannan gidan, idan ana hayaniya da tashin hankali ji nake kamar na zuba ruwa a kasa nash" tashi tayi tana kallon jikinta da kayan baccin ya matukar karɓanta, hijabi tasa dogo har kasa sannan tace "bara naje naga me yake faruwa" fita tayi ta maida fuskanta kalan tausayi, tana ciza baki kamar mara lafiyan gaske, dadyn Amnah cikin tsananin fushi yaje yaja hanunta yace "ko kwana ɗaya ba zaki kara a wannan gidan ba, saida na faɗa muku keda Amrah wannan ba gidan zuwa bane, na faɗa muku har mahaifiyarku ta mutu bata magana da wannan matar duk da uwa ɗaya uba ɗaya suke amma kunki jina, saida kuka zo Amnah gashi yanzu sun kashe ƴar uwarki" Ammi tace "amma salisu daka bari ta kwana idan yaso zuwa gobe...." cikin masifa da zafin mutuwar ƴarshi yace "gobe? gobe fa kikace, to nasan me zai faru da ita da darennan idan ta kwana? wannan gidan naku da yake ɗauke da mummunan tarihi an gaya miki ban san komai bane? kuma wallahi ku sani ƴata ba zata mutu a banza ba, na rantse da Allah saina ɗau fansa, ke kuma....." ya nuna ammi jikinshi har yana rawa, Abi wanda ya gama cika yace "an gaya mata itace tayi kisan da zaka zo kana gaya mata bakaken maganganu?" ya kalli Abi da idanunsa da sukayi jajur yace "a cikin gidannan waye baya kisa?" kaseem wanda shima ranshi ya gama ɓaci yace "ka daina yi mana kuɗin goro ai laifin wani ba zai shafi wani ba" jan hanun Amnah dake kuka yayi yace "muje babu ke babu su daga yau ba zasu sake ganinki ba kema kin rabu dasu" meenat tana kuka tace "dady dan Allah kada kayi haka dan Allah ka barta mu zauna tare, ka barta mu ɗibe mata kewan ƴar uwarta data mutu, dady yanzu haka Allah ne kaɗai yasan zafin da Amnah take ji dady kada kayi haka" yace "meenat na gommace Amnah ta mutu yau a gidana sabida zafin mutuwan Amrah data kwana a wannan ƙazamin gidan naku" fita yayi da ita tana tirjewa tana cewa "dady ka bari na kwana anan" suna fita kaseem ya kalli ammi dake rusa kuka yana huci yace "mutum ɗaya ba zai ɓata mana suna ba nasan wanda yayi wannan kisan" Aneeta saida jinta da ganinta suka ɗauke na lokaci, yana kallon Ammi yace "kema kin sani hakeem ne zai iya wannan mummunan kisan..." tace "ya isheka kaseem ya isheka nace" jikinshi yana rawa yace "meyasa zaki danne gaskiya? meyasa zaki ɓoye abinda yake a bayyane? hakeem shine ya kashe Amrah" marin data ɗaukeshi dashi yasa yayi shiru yana kallonta hanunshi dafe da kuncinshi, ta nunashi da yatsa tace "inaso ka san nice na haifeka kaseem ba kai ka haifeni ba, kaseem zan iya yin komai idan ka kara sa sunan hakeem a cikin abinda yake faruwa a gidannan" murmushin da yafi kuka ciwo yayi sannan yace "okay kina nufin hakeem baida laifi?" tace "hakeem baida laifi kuma ko za'a kasheni ba zan taɓa yadda cewar yanada laifi ba" yace "to waye me laifi?" hameed dake tsaye ta nuna tace "hameed shine babban me laifi, yarima hameed shine da laifi ba yarima hakeem ba" hameed dake tsaye ya kalleta da manyan idanunshi a hankali ya fara yin baya jin abinda ta faɗa, Aneeta dake tsaye ta kasa karasowa ta zuba mishi ido tana gani jikinshi yana rawa, showglass dake cike da turare ya buɗe, kwalban turare ya ɗauka sannan ya fasa, aneeta tana tsaye tana kallonshi murmushi take a ranta tana kallo yadda kwalban yayi tsini, ganin hankalinsu baya kanshi sunata faɗa tsakaninsu yasa itama bata ankarar dasu ba domin so take taga gawanshi kwance baya motsi hakan zaisa taji ranta yayi sanyi hakan zaisa ta yafewa kanta, daɓa kwalban yayi a cikinshi, tana kallonshi har ya faɗi kasa jini ya fara bin tiles, sai a lokacin tayi wani irin ihu tareda kiran sunanshi ammi da kaseem waɗanda suka kai karshe wajen fushi suka juyo a tare suna kallon hameed dake kwance hanunshi akan cikinshi jini ya ɓata inda yake kwance idonshi a rufe da alama ya mutu. Meenat hanu ta ɗora a kanta tana ihu, kaseem da sultan da kuma fadeel tare sukaje suka ɗaukashi jikin kaseem yana rawa yama rasa wani taimako zai iya mishi kawai yace "mu tafi hospital" tare suka fita dashi a hanunsu Aneeta da meenat suka bisu a baya, ammi itama binsu tayi, a mota ɗaya babba suka tafi asibiti a cikin daren da yayi nisa basu sani ba, babu mutane dayawa akan titin sabida dare yayi sosai ba kaɗan ba, banda kuka babu abinda aneeta take yi, tana cewa "dan Allah kada ka mutu ka barni hameed dan Allah ka buɗe idonka kada ka mutu ka bar marainiyar matarka" a hankali meenat ta rungumeta tana bubbuga bayanta tareda kwantar mata da hankali, shiru tayi a ranta tace "inama ace ya mutu, inama ace da gawanshi muke tafiya" suna shiga asibiti kaseem ya fito babu takalmi a ƙafarshi ya ɗaukeshi, shiga ciki yayi dashi duk masu aikin night sukayo kanshi suna bashi taimakon gaggawa, jikin kaseem banda rawa babu abinda yake yi, gani yake hameed ya riga ya mutu tun kafin suzo asibitin, zama yayi akan dakali ya rike kanshi da hanunshi, kukan da bai shirya ba ya fashe dashi, sultan dake safa da marwa ya kasa zaune ya kasa tsaye yazo ya durkusa a gabanshi, rungumeshi yayi yana bashi hakuri yayi shiru. Aneeta a bakin kofan ta tsaya kamar zata shiga kofan da aka rufe tana kuka tana addu'a, Ammi kam tsaban tashin hankali bin kowa kawai take da kallo kamar kanta ya taɓu. Aneeta cikin ranta tana addu'a tace "Allah kasa ya mutu ya rabbi kasa baya raye" a fili kuma cewa tace "Allah kada kasa hameed ya mutu ya barni dana sani da banyi wannan auren ba matukar zai kawo tashin hankali" Ammi da jikinta ya gana sanyi tace "saida nace kada ayi wannan auren nasan babu mu babu kwanciyan hankali matukar hameed ya samu yarima kuma yayi aure amma sunki jina, kowa baya jin maganata" kuka take yi sosai, bayan lokaci dayawa suka buɗe kofan, har rige rige suke wajen tambaya ammi tace "ya mutu?" da mamaki dr ya kalleta yace "kinaso ya mutu ne?" shiru tayi, ya kallesu su duka sannan yace "yana raye bai mutu ba amma yaji mummunan rauni" hamdala kaseem yayi sannan ya ɗago kai ya share hawayen, farin ciki ya bayyana a fuskanshi yace "Alhmdllh hameed bai mutu ba" shiga dakin yayi hameed yana kwance akan gadon hanunshi ɗauke da jini sun san jininshi kuma ya zubar da jini sosai, fuskanshi yayi fayau sosai, a hankali ya zauna a gefenshi ya rike hanunshi dake free, murza yatsunshi yake hawaye suna wanke mishi fuska yace "hameed kayi hakuri ka yafemin ban zama yaya na gari ba na zama yaya mara amfani a wajenka, kullum cikin ciwo kake baka taɓa samun kwanciyar hankali koda na kwana ɗaya bane" shafa kanshi yayi yace "ka yafeni hameed" shigowa sukayi aneeta ta tsaya a bakin kofan tayi shiru, kallonta kaseem yayi sai yaji ta bashi tausayi, yace "aneeta zoki zauna kusa da mijinki" cikin jin kunya ta sunkuyar da kanta, tashi yayi yace "kizo" a hankali tazo ta zauna kusa dashi, shiru tayi, kaseem yace "zaku iya tafiya gida idan yaso gobe saiku dawo zamu kwana da aneeta anan tare dashi" duk sukayi shiru basason tafiya, yayi kamar bai taɓa dariya ba yace "kuje mana" tashi sukayi ba dan sun so ba harda Ammi suka fita, kallon Aneeta yayi yace "kiyi hakuri da duk abinda yake faruwa sannan ki kula da mijinki ko sau ɗaya banaso ki tambayeshi abinda yake faruwa a wannan gidan, ko su meenat dasu sultan banso ki tambayi kowa, kici gaba da zama mutuniyar kirki kamar yadda kike" a hankali tace "to ya kaseem insha Allah" shiru yayi yana kallon hameed dake bacci, ya tashi yace "zanje office ina zuwa" tace "to" fita yayi, ta kalli hameed a ranta tace "meyasa baka mutu ba? nace me yasa baka mutu ba hameed?" ta kalli jinin dake tafiya a jikinshi, fizge canulla ɗin hanunshi tayi ta bar jinin baya tafiya, murmushi tayi tace "ko kaɗan banso naga kana rayuwan farin ciki, so nake naga kullum kana kuka hameed, na tsaneka na tsani ƴan gudanku hameed na tsaneku" rashin jinin dake jikinshi yasa jikinshi ya fara zafi, fizgewa ya fara yana neman karya gadon, tana ganin yadda yake jin zafin ciwon a jikinshi da yadda yake fizge jikinshi sabida rashin jini, tace "ka mutu hameed ka mutu mana hameed" knocking akayi da sauri ta fara rike hanunshi tace "shigo" ya kaseem ne ya shigo da juice a hanu, ya kalleta ya kalli hameed wurgar da juice ɗin yayi yazo yana rikeshi, yace "ya akayi jinin ya fita?" tace "wallahi fizge fizge ya fara kuma na rasa yadda zan yi" ganin tana kuka yace "karki damu babu abinda zai sameshi" gyara mishi jinin yayi yana jin jini a jikinshi ya koma luf ya kwanta akan cinyarta. shiru tayi tana kallonshi, juice ɗin kaseem ya mika mata yace "gashi kisha nasan rabonki da abinci tun safe" girgiza kai tayi tace "bana jin yunwa, ba zan iya cin komai ba" yace "ki daure kisha dan Allah" shiru tayi tana girgiza kai hawaye yana wanke mata fuska, da kyar ya lallaɓata tasha kaɗan, a wajen tana zaune bacci ya ɗauketa. _jiddah ce...✍️_ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 8* ~Sunyi kwana biyar a asibiti kafin aka sallamesu, da kyar yake takawa sabida ciwon da yake cikinshi, wajen jeep ɗin dake fake suka nufa tareda ya kaseem da yayi kyau cikin yadi maroon, Aneeta kuma sunye take da hijab peach color tayi kyau sosai tasa mayafin a kanta bayan tasa hula me kyau baƙi, tana rike dashi yana takawa a hankali har ya shiga motan, itama shiga tayi sannan ya kaseem ya shiga, driver ne yaja suka tafi, koda suka isa gida a hankali yake tafiyan har aka kaishi ɗaki, kwanciya yayi akan gadon yayi shiru yana kallon Aneeta dake kallonshi, gira ya ɗaga mata alaman ya akayi? murmushi tayi ta kauda kai, zata tafi yaja hanunta ta faɗo kanshi, rungumeta yayi sosai yana sauke ajiyan zuciya, shiru tayi a jikinshi har zuwa lokacin daya fara shafa duk jikinta, duk wani taɓata da yayi ji take kamar wuta ne yake taɓa mata jiki, bakinshi zai haɗa da nata tayi saurin tashi ta bar wajen, binta yayi da kallo, sultan ne ya shigo yace "yaya yarima a kawo maka abinci?" gyaɗa kai yayi, yace "to" fita yayi jim kaɗan yazo da abinci yace "tashi na baka" tashi yayi ya zauna, jallof rice ɗin ya fara bashi yana ci cikin nutsuwa, fitowa tayi daga toilet ta karɓi plate ɗin tace "karka damu zan bashi" kallonta yayi shifa gabanshi yana faɗuwa idan yana kallonta ya rasa dalili, tace "tashi mana sultan zan bashi da kaina" a hankali ya tashi ba dan yaso ba, bashi ta fara, sultan ya fita daga ɗakin, fadeel yaga yanayin sanyin jikinshi yace "ya akayi sultan?" yayi tsaki kaɗan yace "wallahi haka kawai hankalina yaki kwanciya da Anti Aneeta musamman idan tana tare da ya hameed sai naji gabana yana faɗuwa" caraf a kunnen Ammi wacce ta fito daga ɗaki, kallon sultan tayi, ashe ba ita kaɗai bace takejin haka akan aneetan shima yana ji, idan taga aneeta gabanta yana faɗuwa, idan tana tare da hameed sai taji bugun zuciyarta yana karuwa, tana kallonsu har fadeel ya dafa wuyanshi suka tafi yana cewa "ka kwantar da hankalinka babu wani abu mara kyau da zatayi mishi kasan tana masifan sonshi" fitowa Aneeta tayi da plate ɗin a hanunta ido huɗu sukayi da Ammi, murmushi tayi mata tace "sannu ammi" bata amsa mata ba kuma bata daina kallonta ba, taɓe baki tayi ta wuce taje ta aje plate ɗin ta dawo ta shiga ɗakin ta rufe. meenat wacce taga duk abinda ya faru tazo wajen ammi ta riketa, tace "ammi me yake faruwa ne?" girgiza kai tayi tace "ba komai meenat" tace "ammi amma kamar naga kina yiwa anty Aneeta wani irin kallo kuma naga ya sultan ma kamar jikinshi a mace da ita" ammi taja numfashi sannan tace "meenat wallahi na kasa nutsuwa da wannan yarinyar haka kawai banason ganinta kusa da hameed" tace "comon ammi babu komai fa kawai dai kinsa abu ne a ranki" tace "to amma meenat" tace "amma me ammi muje please ki huta kin gaji sosai" shiru tayi suka tafi, meenat kallon kofan ɗakin tayi itama haka kawai taji kamar akwai abu a kasa, itama ta kasa nutsuwa da aneeta tunda Amrah ta mutu, sannan tunda akayi aurensu da hameed sai taga kamar ta canja duk da tana ɓoyewa amma ta lura da hakan. sharewa kawai tayi. zaune suke a dinning daka anan ne suke haɗuwa su duka harda Abi, abinci sukeci da hameed wanda yake cin abincin a hankali yake kallon matarshi, murmushi yake idan sun haɗa ido, meenat tace "Abi zanso naje nima naga wani kasan saudiya kawai na taɓa zuwa gaskiya zanso naje wata kasar kuma" murmushi yayi yace "shikenan meenat zaɓi kasar da kikeson zuwa hutunki" tace "turkey" aneeta ta sauke cup na tea da take sha tace "me zakiyi a turkey? akwai sanyi sosai acan gara kije cairo yafi daɗi sabida babu sanyi sosai kuma babu za..." saurin yin shiru tayi ganin yadda duk suke kallonta bata sani ba ashe tayi ɓarin zanje, meenat da mamaki take kallonta sai kuma tace "ya akayi kika sani? keda kikace baki taɓa fita ko wani gari ba bale wata ƙasa?" gabanta ya fara faɗuwa da sauri ta kalli ammi wacce ta aje spoon tana kallonta tana jiran amsa, tace "a tv na gani ai, film na kalla ranan naga an faɗa" sultan yace "wani film?" ruɗewa tayi domin ta rasa amsan da zata bayar, tace "to ai ba zan iya rike sunan film ɗin ba sabida da turanci ne kuma bana jin turanci" meenat tace "kuma kikaji me suke cewa a film ɗin har kikaji sunce kasar turkey da sanyi?" tace "to ai naga suna saka rigan sanyi su kuma..." kaseem ne yace "ya isa haka" shiru tayi meenat kuma ta fara binta da kallo haka Ammi, hameed yana gamawa ya tashi ya tafi ɗaki. itama Aneeta bata jira yau ta gama duka ba ta tashi ta tafi, da kallo meenat ta bita. tun daga ranan bata kara yadda tayi suɓul da baka ba, yau weekend ne suna zaune a falo su duka banda hameed dake bacci a ɗaki, meenat ce kwance akan sofa tana chatting, tace "yanzu zasusa favorite film ɗina bara na kashe data nayi kallo" sunan jarumai aka fara nunata tana rike da wayan taji Aneeta tace "michael marrone, ashe kina kallon film ɗinshi wannan film ɗin After marriage ne ko?" kallon da meenat take mata yasa tayi saurin rufe baki, meenat zuwa yanzu ta gane karya take yi akan abubuwa da dama domin yadda take kiran sunan abu kamar tanada masaniya sosai a kai, shakku ta fara a kanta, batayi magana ba kawai ta kawar da kai tana kallon tv, a zahiri kallo take amma a zuciyarta tana kara kallon Aneeta ne, a hankali tace "ya zama dole nasa ido sosai a kanta" saida aka gama film ɗin ta musu saida safe ta tafi ɗaki, ta rufe kofan ta jingina da jikin kofan tayi shiru, a hankali ta lumshe ido ta buɗe tace "wacece wannan?" zata wuce ciki taga sim a gefen gado, da sauri tace "sim ɗin waye?" ɗauka tayi tana kallo, sai kuma tace "ba nawa bane, ko dai na Amnah ne?" shiru tayi tana tunani sai kuma tace "no Amnah batada sim biyu saide Amrah itace take canja sim" da sauri tace "wannan na Amrah ne" da sauri ta buɗe wayarta tasa sim ɗin a ciki, dubawa ta fara taga sunayen duk yawanci a bakin Amrah takejin sunan, numbern Amnah taga tayi saving da blood sis, tace "tabbas wannan sim ɗin Amrah ne" barin sim ɗin tayi a wayarta ta kwanta ta fara bacci. Aneeta kwance take itada hameed ya rungumeta sosai yana bacci cikin kwanciyan hankali, so take ta samu waje tayi waya amma tana tsoron kada a kamata, a hankali ta cire hanunshi daga jikinta kunna wuta tayi taga karfe biyu na dare cikin sanɗa ta buɗe drower ta ɗau waya karami data ɓoye fita tayi daga ɗakin cikin sanɗa take tafiya, tsayawa tayi a jikin bango ta fara kunna wayan saida ya kunnu zata kira taji karan tafiyan mutum, da sauri ta rufe baki tana waro ido, sanye yake da bakin kaya ya rufe fuska kofan jabeer taga ya buɗe, fasa kiran wayan tayi a hankali ta fara bin bayanshi, tsayawa tayi a baya taga ya ɗaga hulan, alluran da ake yiwa hameed kullum taga ya ɗauka ya juyo dashi, zaro manyan idanunta tayi ganin sultan ne ya canja alluran ya ɗau original ɗin ya kalli kaseem dake bacci cikin kwanciyan hankali sannan ya juya zai tafi, da sauri ta ɓuya a bayan kofa, fita yayi ya rufe kofan, yana fita itama ta fita cikin sanɗa tana mugun mamakin me zaisa sultan ya canja allura? kiran wayan da batayi ba kenan ta koma ɗaki taga hameed ya buɗe ido yana kallonta, tasan da tambaya sosai a ranshi amma ba zai iya furtawa ba, a hankali ta kwanta ta rungumeshi tace "na fita shan ruwa ne kasan na saba da shan ruwan dare" shafa kanta yayi sannan ya mata kiss a forehead ya kara rungumeta ya lumshe ido, a ranta har yanzu ta kasa gane me yasa sultan zaiyi haka? tana ganinshi ta cikin dim light yana bacci like innocent baby boy, yadda yake turo baki kamar karamin yaro da ake shayarwa, shafa kanshi tayi a hankali ta fara shafa sajenshi, da sauri ta ɗauke hanunta daga jikinshi ta rufe ido tana cewa "bai kamata ba, bai kamata ba sam Aneeta" matsawa tayi daga jikinshi tace "ba wannan ya kawoki ba aneeta abinda ya kawoki daban kada kiyi kuskuren da ba zaki yafewa kanki ba aneeta" pillow ta ɗauka ta rungume, zuciyanta yana tafasa tana jin zafi a ranta. washe gari breakfast sukeyi Aneeta tayi kyau cikin baƙin kaya, akan ferfesun da take sha idonta yake bata yadda ta kalli kowa ba domin bata bacci idonta kamar na ƴar kwaya ya zama tsaban baccin da takeji, kaseem yana sanye da uniform cikin sauri yake cin abincin saida ya ɗan koshi yace

Chapter 5 of 9