Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 9
kafin ya koma ɗakin hameed ɗin, har yanzu yana kwance yana kuka, yace "tashi kasha" tashi yayi da sauri sabida so yake yayi bacci kuma ciwon ya hanashi, karɓa yayi ya shanye duka, runtse ido yayi jin bala'in tsami, ji yayi babu sauki marairaicewa yayi ya fashe da wani irin kuka, kaseem ji yayi kamar ya kai mishi duka, cikin lallashi yace "ka daina kuka zaka samu sauki" rage kukan yayi a hankali ya gyara mishi blanket ɗin hanunshi yasa a cikinshi daidai inda yake ciwon ya fara shafa mishi, rufe ido yayi yana jin ciwon yana sauki, gyara kwanciyan yayi zai cire hanun yayi saurin rikewa yana kara rufe ido, murmushi yayi ganin yanaso yayi baccin ɗayan hanun yasa a kanshi yana shafa mishi kanshi a hankali lokaci ɗaya yana shafa mishi maranshi dake ciwo, babu jimawa bacci ya ɗaukeshi, a ranshi yace "ya zama dole hameed yayi aure, zan yiwa ammi magana a nema mishi mata tunda duk tarin ƴammatan da suke aika mishi sakon soyayya yaki kula kowa" a hankali ya zame ya kashe mishi wutan sannan ya fita daga ɗakin ya rufe mishi. ɗakinshi ya koma ya kwanta take bacci ya ɗaukeshi, washe gari ya tashi da wuri domin zai tafi asibiti da wuri, shiri yayi cikin farin yadi me kyau ya ɗaura labcoat a sama sannan ya rike briefcase ɗinshi, farin glasses nashi a idonshi, yayi bala'in kyau kuma da manyance yake yin komai nashi a nitse, ganin an shirya abinci amma babu kowa kawai ya wuce part na mai martaba, sallama yayi ya tarar da hameed a fada ya kwanta kamar me bacci, murmushi yayi yace "hameed dama ka tashi?" a hankali ya tashi ya zuba mishi kyawawan idanunshi alaman eh na tashi, mai martaba ya kalli kaseem yace "har ka fito? yau da wuri zaka tafi kenan?" cikin girmamawa yace "Allah ya taimakeka yau zan tafi da wuri, ina kwana" yace "lafiya ƙalau Allah ya maka albarka kaseem" a hankali yace "ameen" tashi yayi ya kalli hameed daya bishi da ido, yace "zamu je ne?" da sauri ya gyaɗa kai, yace "tashi muje" tashi yayi ya yiwa mai martaba bye kafin suka nufi dinning fadeel ne da sultan zaune sun zuba abinci amma suna hira suna ganinsu sukayi shiru, gaishe da kaseem sukayi ya amsa sannan suka gaisa hameed, hanu ya ɗaga musu alaman lafiya, abinci suka sa suma suka fara ci, Ammi da meenat tare suka fito meenat ta rike hanun ammi, tayi kyau cikin uniform black and white rataye da jakan school, cikin girmamawa ta gaishesu duk suka amsa shi kuma hameed ya mata alaman ya amsa kawai ya sunkuyar da kai yana cigaba da ci abinci, sam bai fiye shiga harkan kowa ba koda a gida yake saide shi da ya jabeer amma baya sakewa da kowa, kallonshi kaseem yayi ganin ya ajiye spoon yace "tunda ka koshi jeka shirya kazo mu tafi" tashi yayi ya wuce ɗaki, bathroom ya shiga ya haɗa ruwan wanka, ya jima yana wankan kafin ya fito yana ɗaure da towel a kwankwaso, a gaban mirror ya tsaya yana kallon gashin kanshi dake a jiƙe, faffaɗan kirjinshi ɗauke da gashi kwantacce, kiran jikinshi kamar me yin gym a kullum, yanada cikakken sura me kwarjini sosai, dryer dake gefe ya jona ya fara busar da gashinshi, saida ya bushe sannan ya aje a gefe, tsadadden man gashin da yake amfani dashi ya shafa sannan ya taje kanshi, fuskanshi babu walwala kamar kullum, da wuya kaga yana murmushi bale yayi dariya, lotion me tsada da kamshi ya shafawa fatar jikinshi da ake kira da gold skin, wardrobe ya buɗe jerarrun tsadaddun kayanshi ya ɗau ɗaya kananan kaya yau yake da ra'ayin sawa, wandon ya fara sawa black ya ɗau pink ɗin polo zaisa, ta cikin madubi idonshi ya hango mishi wutan da yakeci kusa da dryer ɗin daya manta kashewa, grey eyes nashi ya waro a mugun firgice ya fara motsa bakinshi, kasa sa rigan yayi, wurgi yayi dashi ya fara yin baya ganin wutan yana nema ya fara cin ɗakin, jikinshi ne ya fara rawa, take idanunshi suka kaɗa suka koma jajur, banda motsa lips ɗinshi babu abinda yake yi, faɗuwa kasa yayi ya fara jan jikinshi zuwa waje, tsoron daya shiga ya nuna akwai mummunan alaka tsakaninshi da wuta, da kyar ya isa bakin kofa rasa abinyi yayi, hanu yasa da karfi ya fara bugun kofan, Ammi wacce take rike da cup na shayi jin bugun kofan da hameed yake yasa cup ɗin silalewa daga hanunta tarwatsewa yayi a kasa, tare duk suka juyo suna kallonta cikin tsoro ta tashi tana kallon stair, kaseem yace "menene Ammi?" tace "hameed shikenan ciwonshi ya tashi, hameed ne yake bubbuga kofa ku saurara kuji" shiru sukayi kaseem ne ya fara jiyo mugun bugun da hameed yake yiwa kofan, har rige rige suke dasu fadeel wajen haura stair, kofan ɗakin da yake a rufe suka fara bubbugawa kaseem yace "hameed are you okay? hameed ka buɗe kofan" shesheƙanshi sukeji, hankalin kaseem ya kara tashi, bubbuga kofan yake kamar zai ɓalla, yana cewa "hameed relax and open the door" zuwa yanzu ya fara rufe ido alaman zai iya suma a kowane lokaci, kaseem da gudu ya sauka kasa kitchen ya shiga ya ɗauko katon karfe zuwa yayi yace "duk kuyi baya" baya sukayi ya fara ɓalla kofan, da kyar kofan ya ɓallu, gani sukayi yana kwance luf a kasa ya suma, da sauri kaseem ya kalli wutan da yakeci kaɗan kaɗan, yace "sultan kashe wutan" zuwa yayi ya cire socket ɗin dryer ɗin take wutan ya tsaya, kaseem ya ɗaukeshi cak ya wuce dashi ɗakinshi, akan gado ya kwantar dashi Ammi wacce take kuka tace "wuta ya gani shiyasa ya fita hayyacinshi" kaseem yace "kawo ruwa meenat" da sauri taje ta kawo ruwan, karɓa yayi ya shafa mishi, ajiyan zuciya ya sauke me nauyi, ya kara shafa mishi buɗe ido yayi a firgice ya kalli kaseem sannan ya kalli gefenshi, da sauri ya rungumeshi yana hawaye, ammi juya baya tayi tana kuka, cikin muryan kuka tace "shikenan hameed rayuwarka ta lalace ba kamar hameed ɗina dana sani ba wanda bashi da tsoro, ba kamar hameed ɗina da baya tsoron komai ba a rayuwarshi, ba zan taɓa..." kaseem yace "ammi ya isa" juyowa tayi ta zuba mishi idanunta da suka jiƙe da hawaye tace "ya isa? ya isa fa kace kaseem kenan kada nayi magana akan ɗan dana haifa?" sakin hameed yayi yace "maganan bashi da amfani da magana me amfani zakiyi saina kyaleki" murmushin gefen baki tayi wanda yafi kuka ciwo, tace "kana nufin maganana bashi da amfani? kafi kowa sanin zafin da nakeji a kullum idan na kalli hameed, zuciyata kamar zata buga sabida abinda ya faru dashi...." a gabanta ya tsaya yace "ya isa haka ammi maganan ya isheki haka" kallonshi tayi da mamaki tace "kaseem ni kake yiwa tsawa?" ya dunƙule hanu yace "idan kikace zaki tuno da abinda ya faru a baya ba tsawa ba har..." sai kuma yayi shiru, hanunshi ta kalla daya dunƙule ta riko hanun tace "har duka ba? har duka na zaka yi ba kaseem? to dakeni ka dakeni kaseem, idan har da gaske nice na haifeka kaseem ka dakeni" huci yake yi, sultan jikinshi yana rawa yace "ya kaseem ammi dan Allah" fadeel jingina yayi da jikin kofa yayi shiru, meenat juya baya tayi sam batason abinda ya faru ya kara faruwa, fizge hanunshi yayi yazo wajen hameed ya shafa kanshi yace "kar kaji tsoro babu abinda zai sameka ina tare da kai, bari na ɗauko maka riganka saimu tafi ko?" gyaɗa kai yayi, ta gefen ammi ya wuce ko kallonta bai kara yi ba, zama tayi a kasa ta ɗaura kanta a bakin gadon, wasu zafafan hawaye ne suke wanke mata fuska, bata damu data share ba, kallonta hameed yake ya kasa yin komai sai binta yake da kallo, a hankali yazo yana share mata hawayen, a time ɗin ya kaseem ya shigo rige da rigan hameed ɗin bashi yayi yasa sannan yace "muje" sauka yayi a gadon suka fita ammi tabi bayansu da kallo hawayen yana kin tsayawa. "ɗan sarki jikan sarki yarima hameed barka da fitowa" ko kallonsu baiyi ba suka shiga motan ya kaseem yaja suka tafi, har suka hau titi kafin ya kaseem yace "sai can dare zamu dawo" gyaɗa kai yayi. _jiddah ce...✍️_ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 3* ~Asibitin sukaje, ya saba zuwa dama a office ɗin kaseem ɗin yake zama, akan royal sofan ya zauna ya kaseem kuma ya zauna a kujeran da yake zama kullum, yana duba laptop nashi, ɗago kai yayi ya kalli hameed ɗin yaga ya zuba mishi ido, gira ya ɗaga mishi alaman ya akayi? murmushi kawai yayi, wayanshi ya ciro daga aljihu ya fara typing ya kaseem ya ɗau wayanshi dan yasan sako zai tura mishi, gani yayi ya rubuta mishi "ya kaseem ka daina yiwa Ammi tsawa please" kallonshi yayi sai kuma yace "okay zan daina" wayanshi aka kira da sauri ya ɗaga ganin numbern asibiti ne, amsawa yace "dr na'eem ya akayi?" yace "emergency ne yanzu sir kazo dan Allah abin yafi karfinmu" da sauri ya tashi yace "ina zuwa" fita yayi hameed yabi bayanshi da kallo, ɗakin emergency ya nufa, gani yayi rabin ma'aikatan lafiyan asibitin suna tsaye a kanta sun rirriketa amma duk da haka tana kokarin watsar dasu, jujjuya kanta take idonta a rufe, masha Allah kyakkyawa ce ajin karshe fara ce sal gashinta me tarin yawa ya barbazu a bayanta amma yayi datti sosai kuma da alama birgiman da takeyi yasa bakin kayan jikinta da gashinta sukayi datti, suna ganinshi sukace "ga babban dr yazo" matsa mishi sukayi tana ganin sun saketa ta dira daga gadon zata fita ya rike hanunta cikin sanyin muryanshi yace "ina zakije?" tunda aka kawota asibitin sai yanzu taji anyi mata magana cikin nutsuwa jikinta ne yayi sanyi ta tsaya amma bata juyo ba, bai saki hanunta ba yace "fita zakiyi? me zakije yi a waje?" muryanta yana crack tace "zanje wajen mama na" ya kalli dr na'eem yace "tare dawa suka zo?" na'eem yace "mamanta ce kuma tun kafin a karaso dasu maman ta mutu itace tayi rai a motar da sukayi accident harda karamin yaro shima ya mutu" jikinshi a sanyaye yace "zakije kiga gawanta ne? meyasa kike fizge fizge sabida zakiyi faɗa da ƙaddara?" girgiza kai tayi, a hankali yazo gabanta ya tsaya sunkuyar da kanta dake fitar da jini tayi yace "koda kinyi kuka wanda ya mutu ba zai dawo ba" faɗawa tayi jikinshi ta kanƙameshi, sai yanzu ta samu wani kuka me cin rai ya kubce mata, shiru yayi yana kallon bayanta, cikin kuka tace "na kasa taimakon mama da Aliyu duk sun mutu ina kallo na kasa yin komai yanzu banada kowa banada kowa" cikin tausayinta da yaji ya ɗaura hanu a bayanta a hankali ya shafa bayanta yace "kiyi hakuri ki rinƙa addu'a insha Allah komai zai zamo miki da sauki" tace "to na gode" sakinshi tayi tace "zanje naga gawan mama" yace "muje" tafiya ta fara wani irin jiri da yunwa suka zo mata a lokaci ɗaya baya baya ta fara tana rike da kanta da har yanzu bai daina jini ba, zubewa kasa tayi, kaseem yayi saurin ɗagata, ta suma ya fita da ita, hameed daya gaji da zaman office ɗin ya fito domin yasha iska ganin ya kaseem rike da mace ga jikinta duk jini kuma a sume take yayi saurin bin bayanshi, akan gadon marasa lafiya ya kwantar da ita kallon hameed ɗin yayi wanda ya zuba musu ido da alaman tambaya akan fuskanshi, kaseem yace "accident tayi kuma da alama akwai damuwan da take ciki ka zauna kusa da ita bari naje na kawo abinda za'a bukata na kulawa da ita" a hankali yaje kusa da ita ya tsaya, ido ya zuba mata yana kallon kyakkyawan fuskanta, babu jimawa kaseem ya shigo ɗauke da abubuwan buƙata, fara dubata yayi ya tabbatar bataji ciwo ta ciki ba, sannan ya wanke mata jinin goshinta yayi dressing ciwon, ɗaura mata farin bandage ya fara, gashinta da yake da tsawo ya rufe mata fuskan, baya kaseem ya fara maida gashin amma idan wuyanta ya ɗan faɗa sai gashin ya kara zubowa ya rufe fuskan, hameed dake tsaye yana kallonsu kaseem ya kalla, yace "taimaka min na ɗaura mata bandage" zama yayi kusa da ita, zai rike hanunta yaga kaseem ɗin ya saketa ta faɗa jikinshi, ji yayi kirjinshi ya bada wani sautin da baisan na mene ne ba, ji yayi ya rasa duk wani tunaninshi na lokaci ɗaya, kaseem yace "gyara mata gashin" a hankali ya dawo hayyacinshi kame gashin yayi ya mayar baya, ɗaura bandage ɗin yayi saida ya gama yace "yawwa kwantar da ita" kwantar da ita yayi akan gadon kaseem yasa mata drip ɗin da zai kara mata karfin jiki, tashi hameed yayi zai tafi kaseem yace "ka zauna kusa da ita mamanta ta rasu tareda kaninta kuma inada tabbacin harda mahaifinta domin gawa huɗu ne a motan duk da driver, tana fizge fizge dole a samu me zama kusa da ita zanje ayi shirya gawan kafin ta tashi" shiru yayi ya zubawa kaseem ɗin ido har ya gama maganan, bai jira reaction nashi ba ya fita ya rufe kofan, shiru yayi yana kallonta ji yayi tana bashi tausayi tunda mamanta da babanta sun rasu bayaso yaga mutum maraya sai zuciyanshi ya karaya. Kaseem yasa aka shiryasu suna jiran tashinta kawai domin ta faɗi inda ƴan uwansu suke, yayi tagumi ya gaji gashi har yanzu ya kaseem bai shigo ba so yake yaje yayi bacci har kanshi yana ciwo sabida ɗan zaman da yayi, a hankali ya fara motsa hanunta kallonta yake tana buɗe ido har ta gama buɗewa ta kalleshi, kallon drip ɗin tayi sai kuma ta kara kallon ɗakin da take ciki, fizge drip ɗin tayi da ihu tace "mama, baba, Aliyu" toshe kunne yayi sabida baison ihu, grey eyes nashi ya zuba mata yana kallonta, dira tayi daga gadon zata fita a guje, riketa yayi sabida tuna maganan ya kaseem kada ya bari ta fita, tana kwace kanta tace "ka sakeni nikam ka sakeni mama!!! baba!!!" danneta yayi da karfi ta kasa ko motsi sai ihu take, akan gadon ya komar da ita ya kwantar da ita sannan ya zuba mata ido, tana kallonshi tace "waye kai? meyasa bakayi magana ba?" ɗauke kai yayi daga kallonta amma har yanzu bai saketa ba, ta fara tsorata dashi tace "kai ba doctor bane kuma ban sanka ba, meyasa ka rikeni? ka sakeni naje nayi wajen mama" bai saketa ba, shiru tayi ganin baida niyan cutar da ita, numfashi ta fara maidawa a hankali ta jingina kanta da bangon gadon tana kallonshi yadda ya kauda kai daga kallonta, a haka ya kaseem ya shigo, da sauri ya karaso yana cewa "am sorry na barka tun ɗazu wani aiki ne ya taso" sakinta yayi ganin ya kaseem ɗin ya shigo, karkaɗe hanunshi ya fara wai sabida datti, sai kuma ya juya zai fita ya kaseem yace "hameed" tsayawa yayi yace "dawo" dawowa yayi, ya kaseem yace "ki faɗi gidanku da ƴan uwanku sai hameed ya kaiki ki kirasu suzo su karɓi gawan" wani sabon kuka ne ya kwace mata, har tayi me isanta kafin ta share hawaye tace "banada kowa sai mama da baba da kanina Aliyu, baba yace baida dangi itama mama haka yauma barin garin zamuyi sabida baba baida lafiya kuma mai gidanmu yace idan bamu biya kuɗin haya yau ba zaisa a watsar mana da kayanmu waje hakan yasa baba yace mu koma kauye da zama shine a hanyan zuwa mukayi hatsari" shiru sukayi suna kallonta su duka, tausayinta ya cika musu zuciya, kaseem ne yayi karfin halin cewa "kenan babu wanda za'a kira?" jijjiga kai tayi, cikin tausayi yace "to bari mu tara mutane aje ayi jana'iza" kanta kasa tana kuka me cin rai, tun kukan yana fita har muryanta ya dishe, kallon hameed yayi wanda ya kasa ɗauke idonshi a kanta, yace "muje hameed" a hankali yabi bayanshi koda zasu fita juyowa yayi ya kara kallonta, fita sukayi aka kaseem yasa aka fito da gawan, kwantar dasu akayi a kasa kafin mutane su taru ya koma ya fito da ita domin tayi musu addu'a, babu takalmi a kafarta ga kanta dake ɗaure da bandage ga kuma idonta da suka koma kamar jan gauta, a hankali ta zauna a gabansu ta haɗa hanu biyu ta ɗaga sama, addu'a ta fara da larabci kamar ba zata tsaya ba, kowa saida ya tausaya mata, da haka har ta gama ta tashi ta juya baya, hameed ne yaji zuciyanshi yayi nauyi, ɗaukansu akayi aka fita dasu, a hankali yazo inda take ya rike hanunta, bata kalleshi ba amma tana ji yana murza yatsunta cikin nashi, kaseem ɗauke kai yayi daga kallonsu, har akaje aka birne suka dawo, cikin sanyin jiki ta janye hanunta daga nashi, ɗan durkusawa tayi cikin girmamawa ta cewa kaseem "na gode sosai da taimakon da kukamin Allah ya saka da Alkhairi Allah ya biyaka da aljanna, ni zan tafi" tashi tayi zata tafi hameed ya kalli kaseem girgiza mishi kai yayi alaman kada ya bari ta tafi, kaseem yace "tsaya" taki tsayawa tace "babu abinda zan tsaya yi taimakon da kukamin na gode" kaseem yace "kinada inda zakije ne? ko a titi zaki rinƙa yawo ba tareda sanin inda zakije ba?" kasa tafiya tayi, sai kuma tace "koda banida inda zanje asibiti ba wajen zamana bane" yace "idan kin yadda muje gidanmu na tabbata amminmu zata rikeki sabida tanason rike marainiya" shiru tayi tana tsoron binsu kuma aki karɓanta a gidansu, yace "idan kin amince to" a hankali ta juyo ta share hawaye idanunta sunyi mata nauyi so take ta huta koda na ɗan lokaci ne, tace "na amince kuma na gode" murmushi hameed yayi, kaseem ya kalleshi rabon da yayi irin murmushin ya jima, yace "ina zuwa" office ya nufa ya ɗau makulli da laptop nashi da sauran kayan bukata ya rufe sannan yazo yace "muje" cikin ladabi tace "to" tafiya sukayi, gani tayi sun buɗe mata wani lafiyayyen mota, a hankali ta ɗago ta kalleshi cikin nutsuwanshi yace "shiga mana" shiga tayi ta zauna a baya, shi da hameed suka zauna a gaba, jan motan yayi suka tafi, kallon titi take tana wasa da yatsunta, ta kasa sakin jiki domin bata saba da shiga mutane ba, bacci takeji a hankali ta fara rufe ido, baccin da bata shirya mishi ba ya ɗauketa, hameed ta cikin madubin ya saci kallonta, ganin tana bacci ya zuba mata ido yana kare mata kallo, murmushi ne akan face nashi, kaseem ya kalleshi sai kuma ya ɗauke kai yaci gaba da driving yana kula dashi har suka isa gida yana kallonta ta madubi, makeken gate ɗin aka buɗe musu ya shiga, a compound yayi parking sannan yace "ke? ke? tashi mun iso" a firgice ta buɗe ido tace "mama!!!" shiru yayi ganin yadda ta firgita, cikin tausayi yace "mun iso fito" bin gidan ta fara da kallo, ganin gidan sarki ne yasa jikinta yayi sanyi ko dai sun kawota gidan sarki ne sabida ba zasu iya kaita gidansu ba? hameed ne ya fita, kaseem ya buɗe mata marfin a hankali cikin tsoro ta fito tana kallon dogalin da yazo da bulala a hanu yana russunawa yana yiwa su hameed ɗin kirari, hameed yayi mata alaman muje, kin tafiya tayi, dogarin ya ɗaga bulala ya nunata dashi yace "hattara ƴar talakawa yarima hameed ke miki magana" a tsorace taje bayanshi ta ɓuya domin ta tsani ko ganin bulala ne bale ace za'a watsa mata, murmushi yayi suka nufi ciki, a ranta tace "ashe yaran sarki ne" sunyi knocking ammi ce ta buɗe kofan turus ta tsaya tana kallonsu, kaseem yace "zamu iya shiga?" matsa musu tayi suka shiga, da ido yarinyar yake bin ko ina da kallo, a ranta tace "koda ta amince ba zan iya zama ba a wannan gidan ban saba da irin wannan gidan ba nafi sabawa da gidanmu wanda ɗakina dana Aliyu kanina katifa kawai muke dashi da kujeranmu guda ɗaya, sannan na saba da lalataccen gidanmu wanda muke zaman rufin asiri a cikinta, na saba da talauci ba zan iya zama a wannan kuɗin ba" ji tayi kaseem yana bawa ammi amsan tambayan da tayi na wacece ita? shiru ammi tayi jin abinda suka faɗa, sai kuma tace "amma kaseem...." hanu ya ɗaga mata yace "na san me martaba ba zai taɓa yadda a kyaleta ta tafi ba domin koda yaushe shi yake faɗa mana kada mu kyamaci kowa musamman talaka" tayi shiru tana kallon yarinyar data sunkuyar da kai kamar ma a tsorace take, tace "ya sunanki?" shiru tayi ta kara cewa "ya sunanki?" ganin batama san ana mata magana ba ta taɓata, firgigit tayi tace "wayyo" hameed kallonta yake yadda take tsorata yafi komai tsaya mishi a rai, tace "ki nutsu babu me cutar dake a cikinmu ya sunanki?" a hankali tace "ANEETA" murmushi tayi tace "sannunki Allah yaji kan iyayenki" tace "ameen" meenat data shigo ta aje jakanta tana kallonta tace "Ammi wacece wannan?" tace "sunanta aneeta kaita ɗakinki tare zaku zauna tayi wanka taci abinci ta huta" tace "to" hanunta ta rike tace "muje" tashi tayi a yanayinta na tsoro take binta, stair da zasu hau tayi saurin yin baya taki tafiya, minat tace "muje mana" tana kallon stair idonta cike da tsoro tace "ba zan iya ba" dariya minat tayi sosai Ammi tace "ba dariyanta zakiyi ba riketa zakiyi sabida ba lafiyane da ita ba" riketa tayi tace "to muje" damke hanunta tayi suka fara hawa, ihu tayi kafanta yana rawa tace "zan faɗi" minat tace "ba zaki faɗi ba" da kyar ta haye da ita, kallon kasa tayi sai kuma taji jiri yana ɗibanta tace "ina jin jiri" minat tace "ki daina kallon kasa" tace "to" hanunta ta rike suka tafi ɗakinta, a bakin gado ta zauna tayi shiru, minat ce ta shiga ta haɗa mata ruwan wanka tazo tace "muje kiyi wanka" tace "to" tashi tayi cikin tsoro ta bita, nuna mata yadda zatayi wankan tayi sannan ta fita, cikin rashin iyawa ta fara wankan bata taɓa ganin wannan abin ba ko a tv bata kallo bale tasan yadda ake amfani dashi, saida ta gama kafin ta fito ɗaure da towel kanta yana yoyon ruwa, minat wacce ta cire mata kayan da zata sa tace "kin fito?" cikin sanyin muryanta tace "eh" dryer ta ɗauka tace "bari na busar miki da gashin" kallon abin take babu ko kyafta ido da alama fa yau ta fara gani, jonawa tayi zata kai kanta da sauri tayi baya, minat tace "busar miki da kai zaiyi" tace "amma ba zaiyi zafi ba?" tace "babu zafi" dawowa tayi tana kallonta ta fara busar mata da kan, tace "yawwa ya bushe saura kisa kaya" kayan ta karɓa tasa yayi mata kyau dogon riga ne na kanti ta bata hula tasa a kanta da tayi mata parking na gashin, tace "bari na kawo miki abinci" fita tayi jim kaɗan ta dawo da katon plate, aje mata tayi tace "sauko kici" girgiza kai tayi tana hawaye tace "ba zan iya cin komai ba" minat ta lallaɓata da kyar ta yadda taci abincin kaɗan sannan tace "zanyi bacci" tace "ki kwanta" kwanciya tayi a kasa, da sauri tace "tashi ki hau gado" tace "a,a anan ya isa" tace "dan Allah ki tashi" a hankali ta tashi ta hau gadon ta takura kanta ta kwanta ta rufe ido, wahallallen bacci ya ɗauketa. Ammi ta kalli kaseem da zai tafi tace "baka tunanin zaka iya kuskuren kawo wata gidannan?" yace "babu kuskuren da za'a kara yi a gidannan wanda ya kai naki" tace "kaseem kasan fa..." hanu ya ɗaga mata yace "dan Allah, dan Allah ammi ki kyaleni banaso ina faɗa miki magana mara daɗi" ta goya hannaye a bayanta tace "shikenan kaseem komai kayi daidai ne" tafiya yayi, hameed ya jima da komawa ɗaki, magani kaseem ya bawa minat yace idan ta tashi a bata tasha. _Jiddah Ce..._ 08144818849 [20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸 *ƘADDARA TA* 🌸🌸🌸🌸🌸 Na *Jiddah S Mapi* *Chapter 4* ~Har dare tana bacci babu wanda ya tasheta, sultan dake zaune a dinning suna cikin abinci tare yace "minat ya akayi bata tashi ba har yanzu? ko dai ta mutu ne itama?" hameed wanda yasa abinci a baki kwarewa yayi jin abinda sultan ya faɗa, ruwa kaseem ya mika mishi, karɓa yayi yasha sannan yace "sultan ka rinƙa faɗan alkhairi ko kuma kayi shiru" yace "to yaya" a hankali take takowa tana rike karfen gam gam da iya karfinta,

Chapter 2 of 9