"to shikenan TAHEER hakan ma ya yi. To babu komai "
Kai Gwagwo da kwashe-kwashe take wlh. Waye kuma TAHEER?. Tunda nazo Jordan nasan Gwagwo ta jama'a ce. Kullum gidan cike yake da mutane. Samari ,manya da yara. Ko dan tana da barkwanci ne da faran faran. Gata Sam bata da rowa. Kusan samarin layin a nan suke cin abincin rana .ko duk lokacin da suka bushi iska zasu shigo neman abinci. Nima zama a gidan na fara sabawa da wasu. Mai na d'auko ina shafawa ina sauraran Gwagwo dake waya da wannan Taheee kafin ta kashe. Kallona tayi kaman zatace wani abu sai kuma ta girgiza kai ta juya ta fice na bita da d'an kallo. Baki na tab'e na cigaba da harkar gabana. Kafin zuwa azahar gidan ya fara cika da hayaniyar mutane dake ta safa da Marwah cikinsa.
Majina ta k'ara sharewa tana kallon kawarta Saudat. Tsaki Saudat tayi tana cewa da Amina
"Ai saida na gaya miki kiyi hankali da wannan yarinyar simi-simi kasauce. Kina ganin ta hakan wai ita saliha munafukace. Yanzu ba gashi nan taci amanarki ba. Tasan kina san Moha amma ta zagaye ta aure. Ke kuma da yake banza ce kin zauna kina ZUBDA HAWAYE kan wanda bai sani ba. Nace miki a kawai hanya da zaki same shi a saukake number nashi kawai zaki samo kiga aiki da cikawa. Idan ita bataji komai wajen butulci ba ke me yasa zakiji idan kin mayar mata da abunda ta aikata miki?. Wannan rayuwar fa kowa kanshi ya sani. Tun wuri ki newa kan ki mafita"
Majina Amina ta k'ara facewa idon nan sunyi jazur .har wani rama tayi saboda sawa kai damuwa. Tsana da k'iyayyar Jadwah sunyi mata katutu a rai. Sam bata damu da auren sa da Asiya ba tunda tuntuni tasan da wannan. Kuma a ganinta Asiya bata isa ta hana ya sota ba. Babban bak'in cikinta Jadwah. Ta san yanda take masifar son shi amma ta zagaya taci amanarta. Ashe tasan abunda take tsabar munafurci idan tayi mata zancen sa tayi ta kushewa. Kwafa tayi ta sharce hawayen dake fuskarta tace da Saudat
"Yanzu menene abun yi? ,in har number nashi ne ba abu ne mai wuya ba. Nasan Ya Junaid bazai rasa ba"
Murmushi Saudat tayi " abunda za'ayi ki shirya yanzu zan kai ki wajen Malami dake min aiki. Cikin d'an k'ank'anin lokaci kema zaki samu Moha. Taya ki ke tunanin nake juya wannan alhazawan cikin yatsun hannuna?"
Murmushi Amina tayi ta miƙe da sauri tayi b'angaren Junaid. Da sallama ta shiga shiru babu kowa. D'akin sa tayi kai tsaye nan ma bayanan sai k'arar ruwa da takeji daga banɗaki. Dad'i ne ya kamata hango wayarsa da tayi kan gado . Da sauri ta d'auko wayar ta buɗe tana bincika number Moha. Wajen number biyar suka bayyana ko wacce k'asar ta daban. Duka ta kwas.he numbobin don bata san da wacce yake amfani ba yanzu.
Karya sukayi wa Maman su suka fito da zummar zasuje dubi wata k'awar su da bata da lfy. Can kasan ran Amina abunda take shirin yi tana d'an shakkar sa amma inta tuna cin amanar da Jadwah tayi mata sai taji tsananin b'acin rai da tsanan ta.
Suna zuwan wajen Malami kaman yanda Saudat tace. Ya gama bincikensa ya d'ago yana kallon su yana wani lashe lebe yace.
"Mafita guda d'aya ce. Wannan yaran da ki ke so yana da burin ganin ya hayayyafa da yawa. Yana da son yara. Zan iya juya mahaifar matars da yake zaune da ita yanzu ta hanyar da bazata tab'a iya haihuwa ba. Ke kuma zaki shiga gidansa ki hayyafa ta yanda zaki kasance ke kaɗai ce cikin zuciyar sa. Amma fa da sharad'i guda d'aya "
Ido Amina ta zuba masa tana jiran taji menene sharad'in. Lashe harshe ya k'arayi
"In har kina son hakan ya tabbata dole ki shiga wannan d'akin yanzu"
Ya nuna mata wani k'ofar d'aki mai duhu. Ido Amina ta zaro matsanancin tsoro ya rufeta ta shiga uku. Anya kuwa zata iya wannan abu?. Tayi alkwarin ajiyewa Moha budurcinta na har abada. Ganin damuwa dake kwance kan fuskar Amina kaman tana son janye kudurin nata Saudat tayi maza tace
"In har kina son Moha wannan ba komai bane. Ki sawa ranki kin same shi kin gama sai yanda ki ka yi dashi kuma bazai tab'a rabuwa dake ba. Abunda ki ke damuwa dashi bazai tab'a ganewa ba .akwai hanyoyi da dama da zaisa bazai gane ba. Kedai karki damu ina tare dake"
Numfashi taja mai k'arfi ta fesar. Tabbas maganan Saudat gaskiya ne. Akwai hanyoyi da yawa. In har burinta zai cika zata mallaki Moha za tayi komai a kansa. Kai ta d'aga ta kalli d'akin kafij ta miƙe tayi ciki. Murmushi Saudat tayi Malam ya miƙe da sauri yabi bayan Amina. Malam an samu y'an shila bai damu wai Amina budurwa bace ya zage yana juyata sai sumbatu yake yayinda Amina keta ihin azaba ga uban wari da hamami da Malam yake.
Saida ya gurji Amina san ranshi sannan ya fito zuciyar sa fes sai washe jajayen hak'oran sa yake. Da kyar Amina ta iya fitowa sai sharce hawaye take . A hankali ta zauna kusa da Saudat daketa jera mata sannu. Zama Malam ya yi gaban k'asar sa ya yi wani rubuce-rubuce kafin ya d'ago yana kallon Amina dake share hawaye.
"Kina da number nashi?"
Da kyar ta iya d'aga kai. "To maza a kirashi yanzun nan. Duk inda yake zaizo gareki"
Amina najin wannan batu ta wartsake jiki na rawa ta fara neman number Moha. Saida taki wajen uku a kashe ta hud'un ne number shi ta US ta shiga. Wayar na fara ringing Amina ta dafe k'irjinta dake tsananin bugawa kaman zai tarwatse. Har ta fidda rai zai d'auka sai taji wannan muryar mai tsananin taushi da gardi ta ratso speaker wayar
"Hello"
Wani iron d'auke numfashi tayi ta kasa cewa komai saida Saudat ta zungureta. Muryar a hankali tace
"Ya Moha"
Shiru ya ratso wayar na y'an mintina kafin taji yace
"Who is this?"
"Amina ce"
"Amina" Ya maimaita sunan da wata irin murya data kaaa fuskartsa. Da ido Malam yace yi mata nuni ta kashe wayar. Bata musa ba ta kashe do gaba d'aya ta rud'u bata Sam abunda zatace ba.
"Wannan kiran nashi da ki ka yi. Baza ki k'ara ba daga yau. Shi zai dinga kiran ki a ko da yaushe. Ki tsaya ki gani. Aikina yankan wuk'a ne a take yake ci"
Ya k'arasa maganan da wani irin murmushin mara kyau kam fuskarsa. Yana rufe baki kuwa wayar Amina ta fara ringing. Wayyo Allah ran Amina kaman wacce aka yiwa albishir da Aljanna.
SOME WEEK'S LATER.
US.
A gajiye ya faka mota harabar motoci. A hankali ya fito sanye yake da k'ananan kaya farar riga mai botira da bakin jeans. Kayan sunyi masa kyau sosai duk da rashin barci dake tattare dashi. Kai tsaye cikin gidan sa ya nufa tun daga k'afar bene ya fara balle botiran rigar sa ya cireta ya wurgar. Yana buɗe k'ofar d'akin sa ya tsaya turus ya k'ara wara ido yana kallon Asiya dake kwance kan gadonsa da wasu y'an iskan kaya a jikinsa. Yaushe tazo nan har tasan inda yake zaune.? Wani irin mayen kallo Asiya ke masa tana bin murdadadden k'irjin sa da kallo zuwa fatar cikinsa dake shak'e da Abs. Lebe ta lashe ta taso tana wata y'ar iskar tafiya sai tana juya Mazaunai ta nufo shi. Ido kawai ya zuba mata fuskarnan babu expression harta k'araso gabansa ta tsaya. Hannu ta kawo a hankali zata d'ura kan k'irjin sa ya wani riƙe hannun kaman wanda ya riƙe kashi.
"Are you mad? What are you doing in my house?"
"Gidan ka? Gidan ka kai kad'ai? Nima ai gidana ne. Ai ba laifi bane idan mata tazo wajen mijin ta"
Taune harshe ya yi yana kallonta da wnai irin tsana. Kina matsayin mace amma kece ke nuna maitar ki kan namiji. Yana kallon yanda take wani kashe ido tana cije lebe ya wurgar da hannun nata kafin ya juya da sauri zai bar mata d'akin. Da azama tasha gaban sa
"Gaskiya abunda ka ke kana d'aukan hakkina. Yau watanmu nawa da aure? Tunda ka bar Azare baka k'ara waiwayata ba bare ka duba Mummy dake kwance gadon asibiti. Kasan ni dai ba dutse bace dole na buk'aci mijina tunda an daura shi yasa nayi tattaki nazo har inda ka ke"
Haushi takaici yasa ya zuba mata manyan ocean Blue eye's nashi ya kasa cewa komai. K'ara matsowa tayi sosai k'irjin ta kad'an ya rage bai had'u da nashi ba. Da wata y'ar iskar murya tace
"Kaima nasan kana buƙatar haka. Ba waliyi bane ba kai. Ka bari muji dad'in juna. You will enjoy this yanda baka tunani"
Wani irin shafo k'irjin sa tayi zuwa nipples nashi wani irin shock ya ratsashi .yana jin sautin numfashin ta daidai wuyansa tana k'ok'arin kai masa sumba. Kaman rad'a yaji wannan murya mai tsananin taushi da dad'i cikin kunnan sa kaman iska
"MOHA"
firgigit ya wartsake daga trans daya shiga daidai Asiya na neman had'e bakin salu . Wani irin ja ya yi da baya labbanta ya sauka kan iska. Idonta dake rufe ta buɗe tana kallon Moha daya juya da sauri yana sauka daga kan benen. Bata san sanda ta saki ihu na frustration ba tana kallon sa har ya fice daga gidan gaba d'aya. Da ihu ta shige d'aki tana jifa da dukkanin abunda taci karo dashi. A mugun buk'ace take ga Jojo bata nan. Rashin sanin abunyi ya haye gadon da hoton Moha tana saukewa kanta ishin dake damunta. Ihunta da sunan sa kawai ka ke ji yana tashi cikin d'akin.
A guje ya fice daga gidan shi kansa bai san inda ya nufa ba. Abubuwa ne sai kara jagule masa suke. Gefen titi ya faka motar ya koma ya kwanta jikin sitiyarin motar yaba sauke numfashi. Can ya d'auko wayarsa yana k'ok'arin kira kiran ya shigo masa waya. Ido ya zubawa number Amina dake yawo kan screen nashi. Wai what is happening to him ne?. Sam baya jin yarinya cikin ransa but ya rasa dalilin da yasa ya kasa cireta cikin ransa haka ya kasa daina kiran wayarta a kullum. Ya kasa hana kanshi neman aurenta duk da cewa can k'asan zuciyar sa bashi da wannan burin. Numfashi yaja mai k'arfi ya k'ara wayar a kunne.
A shagwaɓe ta kirasa kaman za tayi kuka
"Big Brother ko nayi maka laifi ne yau?"
Saida ya fursar da numfashi yace " No. Sorry nayi busy ne yau. "
Murmushi tayi " OK dama nace bari na sanan da kai abubuwan dana shirya na bikin da event da zamuyi"
"Hmm"
Kawai yace harta gama b'ab'atun ta baice komai ba sai OK. Suna gamawa ya kashe. Tunda ya tura mahaifin sa neman Auren ta bayan neman shawarar Gwagwo ta bashi had'in kai d'ari bisa d'ari. Shi yasa yake son matar duk da sanin matsayin sa gurin Jadwah . Sam bata da son kai. Numfashi yaja mai k'arfi ya fesar yana maimaita sunan JADWAH kan leben sa. Lokaci ya yi da ya kamata yaje ya ganta. A hankali ya d'auko wayar ya lalubo number Gwagwo ya danna mata kira.
Miƙewa nayi ina mik'a bayan na idar da sallan isha. Gwagwo dake kwance kan gado har ta fara munshari na kalla nayi y'ar dariya na gyara mata bargo. Garin yau sanyi ake sosai sabida ruwa da aka wuni anayi. Kan tawa katifar na nufa ina k'ok'arin cire hijabin dake jikina. Rigar barci nasa mara nauyi na samu guri na kwanta ina Addu'a tunanin Baba fal cikin raina. K'arar wayar Gwagwo yasa na d'ago da sauri ina kallon gefen Gwagwo da wayar ke ajiye. Da azama na tashi na d'auko wayar ina kallon suna TAHEER JIKA NA da Gwagwo tasa. Baki na tab'e na d'aga wayar da y'ar sallama
"Hello, Slma"
Wani irin shiru ne ya ratsa wayar sai numfashi da naji an sauke a hankali. Shirun nima nayi ina sauraran ko zaice wani abu.
"Gwagwo tayi barci"
Nace ina cigaba da sauraran yace wani abu. Haushi ya kamani na cire wayar daga kunnena ina d'an tsaki . Da wata irin rad'a naji ance "JADWAH " sai kuma diff wayar ta katse. Baki na hangame ina kallon wayar da tunanin waye ne kuma wannan? Ina kuwa nasan wannan muryar?.
𝗦𝗔𝗨𝗬𝗜𝗡
𝑳𝑨𝑴𝑨𝑹𝑰.
𝔸𝘚Η𝔸𝑵𝚃Ⲩ 𐐛૦𝚅𝞔.♡︎
𝐏𝐆 10.
Washegari ban gayawa Gwagwo kiran da akayi mata na cigaba da sabgogin gaba. Bayan kwana biyu da faruwar hakan yau muna zaune tsakar gida ina yiwa Gwagwo kalba. Duk da cewa shekaru sunja amma gashin Gwagwo har yanzu da tsayin sa da santsin sa, da kyar yake kamuwa .gashi ne har gadon baya. Baba da Ammi na basu da gashi sosai, amma ni kuwa gashina har hip's d'ina yake nayi gado wajen Gwagwo. Gashi baki mai tsantsi. Numfashi naja mai k'arfi na fesar Gwagwo ta d'an juyo tana kallo na.
"Lafiya ki ke sauke ajiyar zuciya? "
Murmushi nayi da baikai zuci ba nace
"Wlh Gwagwo ina son cigaba da karatu na. Yanzu lokacin saukar mu ya gabato za'ayi babu ni. Bansan ya ake ciki game da saukar ba. Zaman gidan ne ya isheni. Ina son na cigaba da karatun boko ma"
Kai Gwagwo ta jinjina kaman mai tunanin wani abu tace
"Kina da gaskiya. Bari za muyi magana da TAHEER naji yanda za'ayi "
"Waini Gwagwo waye wannan Taheer d'in ne da komai zakiyi sai kin nemi shawarar sa?"
Nayi magana da jin haushi. Y'ar dariya kawai tayi batace komai. Washegari na tashi da kiran Gwagwo. Miƙa nayi na miƙe zaune ina kallon agogo dake kafe jikin bango. Numfashi naja a hankali na miƙe ina salati. Hijabi na d'ura kan rigar barcin dake jikina na fito nayi falo inda nake jin muryar Gwagwo na kira. Baki na turo da d'an shagwaɓa na d'aga labulen d'akin ima cewa
"Waini Gwagwo kiran na menene haka kaman zaki fasamin dodon k..."
Maganan tawa ta mak'ale sakamakon tsarkewa da idona ya yi dana Big Brother. Wannan manyan Blue eye's nashi sun kafeni da ido. Dum k'irjina ya buga nayi saurin d'auke nawa ido na k'arasa shiga falon na samu guri kusa da Gwagwo na zauna.
"Yauwa kin taso. Maza ki gaidar da Muhammadu. "
A hankali na d'ago inda yake zaune sanye da k'ananan kaya. Farar riga mai botira da bak'in wando sai bak'ar jacket d'aya d'ura kan rigar tashi. K'asa k'asa nace
"Ina kwana?"
Bai amsa ba sai ido kawai daya zubamin ko kunyar Gwagwo dake zaune gurin baiji. Rai na k'ara b'atawa Gwagwo tace
"Maza jeki deb'o masa Kiddirmun nan da ki ka hada akwai ragowar sa da gashin naman nan"
Ban musa ba na miƙe da sauri na fice daga falon ina jin idansa na bina. D'aki na koma na fara chanza kayan dake jikiba zuwa doguwar riga bak'a da d'an hijabin ta, sannan na fito nayi kitchen. Kiddirmun da na had'a mana jiya da daddare daya sha kwakwa da inubi na d'auko na zuye cikin glass jug da cup nashi na d'ura kan tire kafin na k'ara gasa masa gashin tsiri da nayi mana na tunkuya na juye cikin d'an flasks mai kyau. D'auka nayi na koma falon. K'asa-k'asa nake jin maganan Gwagwo tana cewa
"Bikin ya gabato kenan. Jibi-jibi nan. Ita Aminan ce dai?"
Banji mai yace ba na d'aga labulen na shiga ina k'ara kiran sunan Amina a raina. Bikinsa da Amina ne yazo?. Amma Amina shine babu labari?. Wai anya wani abu bai shiga tsakanina da Amina ba? Amma ace bikinta guda da Moha na kasa sani?. Wannan abun farin ciki ne a gareni don burinta ya cika ta samu wanda ta jima tana dakon soyayyar sa. Gabansa na ajiye kayan ina jin idon sa a kaina. Juyawa nayi zan fice Gwagwo tace
"Yauwa tunda kazo Muhammadu. Ka kaimun Jadwah kasuwa zata yimin cefane."
Da sauri na kalli Gwagwo dake k'ok'arin ficewa daga d'akin. Wai me Gwagwo ke nufi ne?. A hankali na mayar da ido na kansa har yanzu ni yake kallo. Kasa jurar kallon nasa nayi na juya da sauri na fice daga falon. D'aki nayi kai tsaye ina kumburi na samu Gwagwo zaune a hankali kwance.
"Waini Gwagwo menene sai faman had'ani ki ke dashi?. Mutum sai shegen kallo kaman maye ko kunyar ki bayaji, to kurwata kur"
Baki Gwagwo ta d'an hangame sai kuma tamin dakuwa
"Ungu nan. In bai kalle kiba ni zai kalla?. Kajimun wani shashancin banza. "
Haushi ya k'ara kamani na "kasuwar me kuma zamuje bayan akwai komai a gidan?"
"Aa babu Muhammadu na son cin tuwon masara niyar k'ub'ewa. Kije ki siyo mun k'ub'ewar da nama a dura masa. Da ai da kaina zanje amma tunda gaki ga mota kinga ai yafi sauki"
Wayyo yanda kuka san na rufe Gwagwo da duka wlh haka naji tsabar haushi.
"Wuce maza kije kiyi wanka ki chanza wannan kayan"
Ido kawai na zuba mata. Wai ba ita naji tana maganan auren sa da Amina ba?. Tasan kuwa abunda take tana neman had'ani dashi ta k'arfi da yaji don na gane inda ta dosa. Numfashi kawai naja na cire kayana fice zuwa banɗaki na watsa ruwa na fito. Sanda na dawo bata d'akin naji maganan ta falon suna hira. Shiryawa nayi cikin atamfa riga da sket na dura abaya a kansu. Gashina na nad'eshi kaman gammo nayi rolling mayafin abayar. Y'ar huda na shafa da man leb'e na fito riƙe da yar pose da flat takarmi da suka shiga da atamfar dake jikina light blue. Guri na samu a tsakir gidan nayi zamana saida naji Gwagwo ta kwad'amin kira na miƙe ina k'unk'uni na shiga falon
"Baki gama shiryawa bane tun d'azu ke yake jira?"
Bance komai ba naja na tsaya. Na fara gajiya da wannan kallon nasa. Miƙewa naji ya yi kafin naji wannan muryar tashi mai tsananin kaushi tace
"Bari muje Gwagwo sai mun dawo"
"To a dawo lfy Allah ya kiyaye. Kar ku manta da abinda nace"
"InshaAllahu Gwagwo "
Zuwa ya yi ya wuceni ya fice daga falon na ja doguwar ajiyae zuciya saboda kamshin sa mai sanyi da ratsa juya daya bugeni. Ban yiwa Gwagwo magana na fice daga falon don haushin ta nake ji. Ina fitowa k'ofar gida saida nayi dana sanin fitowa saboda jama'a da suka kewaye dankareriyar motar da yana nufa . Murfin motar ya d'aga sama sannan ya juyo inda nake tsaye. Jiki na rawa na nufi motar kaina a k'asa saboda idon mutane. Na tsani kallo wlh koya yake Jikina ta dinga rawa kenan. Da sauri na shige motar ya mayar da murfin ya rufe kafin ya zagaya ya shiga ya tada ida muka bar layin. Muna hawa kan titin sai ya rage gudun motar ya fara tafiya a hankali kaman mai sand'a. Numfashi na k'araja k'irjina na bugawa. Tunda na shiga motar naki kallon inda yake zaune. Kamshin motar da had'uwar ta ya sanya na jingina kaina jikin glass nata na rufe ido na. Chak naji motar ta tsaya da tafiya na buɗe idona a hankali ina kallan waje. Gefen titin ya faka motar motoci sai wucewa suke suna kallon motar dake fake gefeb titi. Idonsa da naji a kaina na had'iye wani irin yawu kafin na juyo a hankali muka had'a ido dashi. Kaifin idonsa yasa nayi saurin d'auke nawa na mayar windo. Wai menene ke damun mutumin nan ne?. Da deep voice nashi naji ya kirani
"Jadwah "
Yanda ya kira sunan kace don shi kad'ai aka rad'amin. Maganan nashi kana ji kasan hausa bata isheshi ba. Wani iri Ascent ne dashi mai dad'in gaske. Tsigar jikina ta tashi yamma, amma duk da haka ban juya na kalleshi ba.
"You have to tell me where we are going. "
Numfashi na fesar a hankali na juyo muka had'a ido nayi saurin kawar da kai. Dan dole nayi masa kwatancen inda zamu. Ina jin ya yi wani d'an k'aramin murmushi kafin ya tada motar ya hau titi yana bin kwatancen da nake masa. Kaman yanda Gwagwo tace na siyi k'ub'ewa da Nama. A hanya ya tsaya wani katon Mall ya shiga ban bishi ba don na kagu mu koma gida. Ya jima cikin Mall d'in can sai gashi da kaya niki-niki da yaran shagun biye dashi da wasu kayan. Saida suka gama saka komai cikin mota sannan ya shiga muka koma gida. Yana fakin na fice da sauri ina jin wannan mayuj idon nasa a kaina.
Tsakar gida na samu Gwagwo da wasu y'an maƙota suna hira
"A'a har kun dawo?"
"Eh" kawai nace na shige d'aki. Ina jin yanda ake ta shigo da kaya kafij naji muryar sa yana cewa da Gwagwo zaije ya dawo. Matan dake gidan sai hauka suke. Baki na tab'e ban fito ba saida naji tafiyar sa. Na fito nayi kitchen dan d'ura mana abinci. Kai na girgiza ganin yanda Gwagwo da matannan suks dukufa suna cin gashin kaza da lemo ga kayan makuleshe baje a gaban su. Tana cin nama Gwagwo ta kalleni ta d'auko katuwar leda ta miƙo min
"Ungu wannan taki ce kafin muga sauran kayan kuma"
Kabar kawai nayi na koma d'aki na ajiye na fito na d'ura mana abinci ban k'arabi ta kan kayanba. Wajen la'asar ya turo yaron sa aka karb'an masa abinci.
Ana yin sallan Magriba hadari ya had'u sosai muka shige d'aki nida Gwagwo. Allah yasa ma akwai wuta. Kwanciya muka yi bayan munyi sallah Gwagwo najin radio ba d'ago na kalle ta
"Gwagwo "
"Na'am "
Ta juyo tana kallo na " d'azu naji kina maganan Auren Amina? Amina dai tawa dana sani?"
Saida ta kashe radio ta juyo tana kallona sosai taja numfashi " eh ita. Me yasa ki ka tambaya?"
Jikina ya k'ara sanyi nace " Babu komai. Bansan me nayiwa Amina ba auren ta guda ta kasa aikowa a gayamin "
Gwagwo batace komai ba ta zubamin ido kawai. Numfashi na k'ara saukewa nace
"Yaushe ne bikin nasu Gwagwo ?"
"Jibi inshaAllahu za'a fara .haka Muhammadu yacemin "
Kai na jinjina " tafiya ta kamani gobe Gwagwo. Duk da bata gayamin ba ni zanje bikin nata nasan akwai dalilin da yasa bata gayamin ba. Amina ta wuce haka a gurina. Dole naje Gwagwo "
Zama Gwagwo ta gyara tana kallona "anya kuwa Jadwah. Me zakije kiyi?"
"Kinsan bani da kawa sama da ita. Zanje nayi mata bazata"
Gwagwo batace komai ba na juya na gyara kwanciya ban jima ba barci ya kwashe ni. Ido Gwagwo ta zubawa Jadwah dake sauke numfashi a hankali kafin ta yunƙura ta d'auko wayarta ta danna kira. Bugu d'aya ya d'auka
"Gwagwo "
Ya kira a hankali da muryar barci. " Taheer na tashe ka kana barci?"
"A'a Gwagwo "
"To kanaji yarinyar tasan zancen auren ka da Amina don ta ce gobe zata je. Nasan halin Jadwah da kafiya tunda tace zataje dole sai taje . Yanzu ya za'ayi kenan?"
Numfashi ya sauke mai zafi ya mayar da manyan idonsa ya lumshe. Sam bashi da burin zuwa bikin nan Kwata-kwata. Burin sa ya zauna a nan yana kallon wannan kyakkyawar fuskar tata dake so fierce kaman tiger.
"Babu komai Gwagwo nima goben zanje azaren sai mu tafi tare "
" to shikenan zance mata ta shirya ku tafi tare da tabi motar haya."
"Gwagwo bata buɗe wayar dana bata bane?"
Da d'an mamaki Gwagwo tace " au ka siyo mata waya? Yoo ai ita kanta bata sani ba. Bari da safe zansa ta fiddo da. An gode kaji Allah ya k'ara buɗi da arziƙi "
Da wannan sukayi sallama yana jin Gwagwo tamkar uwa daya rasa.
Washegari ya kaman alhamis. Ban koma barci ba bayan sallan asuba nayi tilawa da zikiri da gari ya fara haske na fito gyara gidan na d'ura mana abinci. Dana gama ba shiga wanka sai bayan na fito ne Gwagwo ta tashi daga barci. Kayana da zan tafi dasu na fara shiryawa cikin jaka sannan na shirya cikin atamfa maroon d'inki riga da sket. Duk abunda nake Gwagwo na kallona batace komai ba saida na gama shiryawa ta d'auko ledar dana ajiye ta buɗe tana lalube. Saiga kwalin waya ta fito da ita mai shegen tsada.
Ina kallo ta buɗe had'addiyar iPhone ta miƙo min. Da mamaki sosai kan fuskata na k'arba ina juya wayar tafin hannuna.
"Kunna mu gani"
Ban musa ba na kunna wayar .anyi set d'inta gaba d'aya don harda sim a ciki .cike take kuma da chaji. Karb'an wayar tayi ta saka number ta kira sannan ta miƙo min tana cewa
"Yauwa kinga na samu hanyar da