koma ya rufe gate d'in. Har ya wuce ya shiga ciki Baba na kallon sa yana k'ara neman tsari wajen Allah tsakanin y'ar sa da wannan yaron. Shi kansa yasan zamanta a gidan nan hatsari ne babba. To halin rayuwa da rashin mafita yasa yake zaune da ita a nan.
Main falo Isma'il ya same su H Balaraba da Suwaiba harda Asiya suna karyawa kan Family dinner. Haka ya kutsa kai cikin gidan babu sallama bare gaida na gaba dashi yaja kujera ya zauna yana zuba abinci. Dukkaninsu babu wanda ya damu da abunda ya yi hankali kwance suke cij abinci. Can Balaraba ta d'ago tana kallon Isma'il dake cin abincin kaman zai had'a da kwanan babu nutsuwa. Rai a b'ace tace
"Wane irin cin abinci ne wannan kaman wani k'aramin yaro?"
"Idan kina so na daina wannan dabi'u ki amince nayi aure. Kuma dole ki yarda da yarinyar da nake so"
Ya k'arasa maganan da wani mugun murmushi kan fuskar. Ido kawai ta zuba masa bata ce komai ba. Dariya Suwaiba ta fashe da ita daya k'ara tunzura Balaraba a zafafe tace
"Kinga halin nasu ba. Shi yasa nake so Moha yazo gari ya saitamin ku. Babu yarinya da zaka aura sai in har nice na baka ita. Kama ajiye batun ko wace yarinya ce a gefe babu kai babu ita. Zab'ina nake so kuma dole kabi umarni "
A fusace ya miƙe ya yi jifa da kwanan da yake cin abinci yana zuba uban huci yace
"Wlh baki isa ki hanani auren yarinya nan ba. Dole saina aure ta babu wanda ya isa ya hanani auren ta" ( da alama Isma'il yana manta cewa komai da ikon Allah ne yake faruwa). Fuu ya wuce yana jifa da dukkanin abunda yasha masa gaba.
"Kinga ni ba. Suwaiba yau zamuyi tafiyar nan kinsan halin Isma'il idan ya kafe kan abu, yana da mugun taurin kai. Haka kawai bazan yarda ya nemo wata yarinya da zata juyashi ba. Tun abun baiyi nisa ba ina buƙatar Moha don shine kad'ai zai tsawatar masa"
"Maganan da nake son yi miki kenan"
Suwaiba tace tana kurb'an tea. Asiya dai tunda ta zauna bata ce uffan ba. Hankalin ta gaba d'aya na kan wayarta tana chat da Jojo.
Tafe suke da k'awar ta Amina bayan sun taso daga makaranta. Amin y'ar makocin sune. Yarinya ce data fito daga Babban gida amma sam bata da girman kai. Tunda taga Jadwah take son ta saboda nutsuwar ta da hankalin ta. Amina ta jima tana son Moha. Tun tana k'arama take masifar son shi gashi shi kuma baima son tanayi ba. Sau d'aya ne suka tab'a had'uwa da ita lokacin tana shekara 13 a lokacin ne ya bar Nigeria ya koma Italy da zama saboda karatun sa.
Kallon Jadwah tayi tana murmushi a karo na ba adadi tana k'ara gaya mata irin son da take wa Moha. Da irin mafarke-mafarke da take a kansa na kasancewa matarsa. Baki Jadwah ta d'an tabe tana cewa
"Kin gamu da aiki wlh. In ba haka ba. Ina amfanin son wanda baisan kana yiba"
D'an murmushi Amina tayi mai d'an ciwo daidai suna tsayawa k'ofar gidan su ta juyo tana kallon Jadwah tace
"Baza ki gane abunda nake nufi ba sai ranan da ki ka ganshi. Ina nan ina Addu'a Allah ya dawomin dashi nan kusa"
"Hmm, to Allah ya kyauta bari na wuce ni kar Baba yaga na dad'e"
"Aikuwa kwana biyu ban samu na shigo mun gaisa da Baba ba. Ki gaidamin shi don Allah kafin na shigo"
Sallama suka yi ta wuce da sauri Amina ta shiga gida. Turus ta tsaya tana kallon yayan ta Junaid dake tsaye bakin k'ofar alamun ya dad'e a gurin. Yana ganin Amina ta shigo ya yi saurin riƙe ta yana cewa
"Ina ki ka san wannan yarinyar?"
Da mamaki tace "wai Jadwah?, kawata ce ai sosai. Suna zaune ne gidan su Big Brother "
Sata ya yi a gaba saida ta gaya masa dukkanin abunda ta sani game da Jadwah da Mahaifin ta.
𝐏𝐆 3.
Tun daga nesa ta hango Baba dake k'ok'arin buɗe gate alamun za'a fita da mota. Da azama ta k'arasa bakin k'ofar ta taimaka masa suka buɗe. Daga cikin motar da H Balaraba da Suwaiba ke zaune . Suwaiba ta d'an d'aga murya tana kiran ta. Matsawa tayi jikin motar cikin girmawawa tace
"Ina wuni Hajiya"
Murmushi Suwaiba tayi tana kallon Mummy Balaraba data mugun had'e fuska.
"Lfy lau Y'an mata ya. Ya sunan ki"
Babu tunanin komai tace "Jadwah, Hajiya "
"MashaAllah , sunana mai dad'i "
Kafin ta k'ara cewa wani abu Mummy Balaraba ta bawa direba umarni yaja mota. Da sauri Jadwah ta matsa gefe tana kallon motar data fice ta mayar da gate d'in ta rufe. A d'an fusace Suwaiba tace
"Ya haka ina magana da yarinyar zakice aja mota?"
"Suwaiba, ina k'ara gaya miki ki fita harkar yarinyar nan karmu samu matsala dake"
Ran Suwaiba a matuƙar b'ace ta yi kwafa bata ce komai. Tace duk abunda zatace amma bata isa ta hanata kauda kwad'ayin ta kan yarinyar.
Saida ta fara ajiye jakarta ta makaranta sannan ta fito riƙe da foam a hannun ta ta durkusa inda Baba ke zaune fuska d'auke da murmushi tace
"Baba ga katin mu na saukar Qur'ani nan da wata biyu masu zuwa inshaAllahu "
Da matsanancin fara'a da farinci ya karb'a ransa na kissimamasa hanyoyi da zaibi wajen ganin ya ajiye y'an kudade masu yawa da zai tara idan lokacin saukar yazo. InshaAllahu zaiyi bakin k'ok'ari wajen ganin ya yi mata abubuwa da iyaye ke yiwa ya'yan su a irin wannan rana mai Albarka da kuma farin ciki. Don haka tafiya ta kamashi zuwa Kano inshaAllahu wajen y'an uwa ko Allah zaisa a dace.
Albarka ya yi ta shi mata yana yi mata Addu'o'i na samun nasara. Farin ciki wajen Jadwah abun sai wanda ya gani. Haka ta koma d'aki ta chanza kaya zuwa doguwar riga da d'an k'aramin hijabi. Tana gyara wake don d'ura musu abincin rana Isma'il ya fito yasha manyan kaya. Blue d'in shadda d'inkin tazarce da bak'in takarmi mai yatsa sai bak'ar hula. Babu laifi ya yi kyau tunda abune da bai saba sawa ba. Har k'ofar d'akin nasu ya k'araso riƙe da mukulli ya durkusa kusa da Baba dake kallon sa ,Jadwah tayi mugun b'ata rai tana gyara wake bata kalli inda yake ba.
"Barka da hutawa Baba"
"Yauwa Alhaji Isma'il. Har an fito ne za'a fita?"
Kai ya d'an sosa yana cewa " eh wlh Baba zanje d'aurin auren wani aboki na ne da za'ayi k'arfe d'aya "
"To MashaAllah. Allah ya sanya alheri. A dawo lafiya "
Har cikin ransa zaka san yaji dad'in Addu'ar, saboda wani murmushi daya kufce masa ya miƙe yana kallon Jadwah da ko kurar sa bata kalla ba har ya wuce ya buɗe gate ya shiga mota ya fitar waje, kafin ya dawo ya mayar da gate d'in ya rufe ya fice ta k'aramar k'ofa. Daga Baba har Jadwah babu wanda yace komai dukkanin su ,suka bar maganan su cikin zuci. Tana gama gyara waken ta d'ora musu kafin ta dawo ta daka musu yaji mai shegen dad'i dayaji gyad'ar kamshi da tafarnuwa. Sosai suke hira da Baba aka sarin hirar su kan kakar ta ne Goggo dake zaune can rugarsu a Niger.
Wajen k'arfe biyu ta fito shirye cikin kayan su na islamiya. Tana k'ok'arin yiwa Baba sallama, Amina ta rangada sallama ta shigo gidan. Saida suka gaisa da Baba sannan sukayi sallama suka fito. Suna tafe suna y'ar hira Amina nata son ta kawo maganan yayan ta Junaid ,amma ta bar maganan zuwa wani d'an lokacin.
Mummy Balaraba da Suwaiba kai tsaye wajen Bauchi suka nufa wajen Jalli na kan dutse. Da yake suna zaune ne a AZARE/KATAGUM dake jihar Bauchi. Tafiya sukayi kaman zasu bar gari kafin su yanke hanya subi dokar daji. Daga Suwaiba har Mummy Balaraba babu tsoro ko d'ar a ransu don hanyace da suka saba bi. Saida suka d'auki wajen awa guda suna shiga cikin kwazazzabai da ciyaye kafin su fito wani katon dutse dake zaune tsakiyar dokan dajin babu gida gaba babu gida baya. Daga d'an nesa da dutsen kad'an direba ya faka motar shi kad'ai zaka kalla kaga tsoro tattare dashi.
Fitowa suka yi daga cikin motar suka cire takarmi kafin su durfafi dutsen duk taku d'aya idan suka yi suna wani irin kira kaman musu yaran Chinese. Wannan inkiya ce don su sanar wa da JALLI zuwan su. Wata irin iska ta kad'a a gurin mai tsananin k'arfi, kafin wata irin dariya mai ban tsoro ta k'arade dajin mai tsananin amo da amsa kuwwa. Kaman walkiya wata irin rub'ab'iyar bukka da, da babu ita kan dutsen ta bayya daga can koluwar saman saman ta.
Baiyanar Bukar Mummy Balaraba da Suwaiba suka k'ara gyara zannuwa su karsu fad'i. Saida suka d'auki wajen minti talatin sannan suka kai bukar sai had'a wata uwar zufa suke suna uban nishi. Kaman yanda suka saba shiga da baya-baya suna kirari, haka ma yau. Da farko babu kowa cikin buk'ar har suka samu guri suka zauna. Saida suka zauna ne wani irin hayak'i ya turnke ta bak'ikkirin dashi kafin siffan wani shegegen mutum ya fara bayyana a cikin da daga can k'uryar bukar. Fad'ar irin sananin muninsa abun bata baki ne wani irin bakin mutum ne mai kwala-kwala idon da katan kai. Daga Mummy Balaraba har Suwaiba, babu wanda ya firgita ko tsorota da ganin sa saima murmushi da suka yi suka k'ara gyara zama. Wani irin dariya ya saki mai amo mara dad'i yana cewa
"Nasan abunda ke tafe daku. Hahahahha"
Kwarya ya fito da ita cike da ruwa ya ajiye gabansa .ya k'ara fito da wani d'an kwalba karama da wani irin bak'in abu a ciki ya miƙewa Mummy.
"Matso nan ki riƙe wannan kwalban ki"
Babu musu ta matso da rawar jiki ta k'arba kaman yanda yace. Wani irin sumbatu ya fara yana tura d'an yatsan sa guda d'aya cikin ruwa sai ga wani hayak'i ya fito daga cikin sa. Kallon Mummy ya yi yace
"Ki buɗe wannan abun ki zuba cikin ruwan ,ki kira sunan yaron sau uku"
Buɗe kwalban tayi kaman yanda ya umarta wani irin wari ya daki hancinta kaman za tayi amai tayi saurin juye shi cikin kwarya tana kiran Moha. Tana gamawa kwaryar ta fara wani jijjiga sai tush ta bafe kaman an saka mata batir. Wani irin mahaukacin dariya ya saki yana cewa
"An gama aiki. Zuwa gobe duk inda yake zaizo gare ki. Haka kuma Auren sa da Y'ar ki babu fashi sai yanda ki ka yi dashi, amma idan har kina son aikin ya tafi yanda ya kamata dole sai kinbi sharad'i. "
Jikin Mummy na rawa tace " duk abunda kace mai Girma Jalli zanyi shi babu kuskure"
"Hahahaha, ina son daga nan idan kun fita ki samu budurwar karya a binne min ita da ranta. Zulkumu zaije ya d'auko ta da zarar kin binne ta"
Suwaiba da tunda suka shigo batace komai ba tayi saurin k'arbewa da sauri.
"An gama Jalli. "
"Hahahah , sharad'i na biyu . A yau d'innan dole ki sadu da mutum biyar. Kuma kar ki kuskura kiyi wanka har sai bayan sati gudu"
Babu jin komai Mummy tayi murmushi tana cewa " Wannan ma an gama shi"
Muguwar dariya ya fashe da ita mai ban haushi kafin ya b'ace bat. Suwaiba ta ciro bandir na dubu guda biyi ta miƙewa Mummy data k'arba ta ajiye bakin kwarya. Sai ga iska ta k'arade bukkar kuɗin nan bat shima ya b'ace. Miƙewa sukayi suka fito kaman yanda suka shigo ran Mummy tas kaman takarda . Burin ta yana gab da cika . Zata mallake Big Brother kaman yanda tayiwa Mahaifin sa, kafin Alhaji Balarabe ya dawo daga gurin Balarabiyar matar sa dake Dubai ta mallake Big Brother sai yanda ta juya su. Dukiya, gidaje, kamfanoni komai zai kasance sai yanda tayi.
Murmushi take bakin yak'i rufuwa har suka sauko daga kan dutsen suka shiga mota. Tun a mora Suwaiba ta kira yaron su da suke sawa yana musu irin wannan aikim ta umarce shi ya samo musu budurwar kare ya binna ,kar kuma ya kuskura ya wani ya ganshi idan gana aikawata.
Lokacin da suka dawo. Jadwah na zaune kan barandar sanye da riga da wando kaman Pakistan. Wandon nada d'an fad'i, rigar kuma ta kawo mata har gwiwa. Kanta kuma ta yane shi da mayafi mai d'an kauri daya shiga da kayan da suke Pitch color. Tayi irin nad'in nan na larabawa. Duk da fuskarta babu kwalliya tayi wani mugin kyau kaman ka sace ta. Manyan black eyes nata da suke d'auke da gashin gira yala-yala . Idonta tafe yake da dogon hanci kaman biro, sai d'an mitsitsin bakin ta da suke jazur dasu koda yaushe zaka gansu kaman ta shafa masu mai. Kullum zakaga suna shak'i.
Qur'ani ne a hannun ta tana bita da zazzakar Muryar ta mai tsananin dad'i. In kaji yanda take kira'ar kace Sudai ne na mace. Baba dake zaune gefen ta yana sauroro, hankali sa da nutsuwar sa gaba d'aya na kanta. Gefen sa shayi ne data d'ora masa irin na buzaye cikin y'ar buta sai zuba uban kamshi yaki na kayan had'i. Horn da akayi k'ofar gate yasa ta ajiye Qur'anin a hankali ta miƙe ta nufi k'ofar da d'an sauri ta buɗe. Suwaiba ta bita da wani mayan kallo har suka wuce ciki suka faka mota.
Jadwah ta maida k'ofa ta rufe ta koma inda take zaune ta d'auki Qur'anin ta ta cigaba da karatu. Da zalama Suwaiba ta fito tana kallon Jadwah dake karatu suka wuce ciki. Addu'ar Mummy Allah yasa Asiya bata nan. Allah ya taimaka kuwa bata nan dan Isma'il na fita itama Jojo tayi mata waya ta fice daga gidan. Kai tsaye ta kira masu tsaron ta mutum biyar suka haura sama suka bar Suwaiba falo da nata tunanin kan yanda za'ayi ta samu kan Jadwah. Babu jimawa da shigar su ihun Mummy ya fara dukan Suwaiba ta wage baki sai ihu take na dad'i maza biyar na kanta. Kai Suwaiba ta girgiza ta miƙe ta fice daga gidan bayan ta k'arewa Jadwah kallo. Ta gama yanke hukunci yanda za'ayi ta sameta a sauk'ek'e. Murmushi tayi har direba ya fice da ita daga gidan.
ITALY.
Dankareriyar Sport ferrari ce ta faka harabar wani k'aton gida mai shegen kyau da akayi rabin sa da glass. Duk da cewa dare ya tsala sosai, hasken fitilu dake gidan da waje sa, za kayi tunanin rana ce. Motar da aka faka cikin shegun motocin gidan wanda ke ciki saida ya d'auki sama da minti biyar kafin ya buɗe motar ya fito da wani irin slow motion. Wani Ingarman namiji ne dogon gaske ya fito daga cikin motar. Kallo d'aya za kayi masa ka san kakkarfa ne ko daga faffaɗan k'irjin sa da bai balle rigar ba, hannun ta kuma ya tattare shi zuwa gwiwar hannu kana hango jijiyoyin sa dake motsi koya ya motsa hannun.
Short hair nashi daya tsaya perfect kansa. Wanda yafi yawa daga gaba. Bak'in wando ne a jikinsa mai kaman leather. Hannu sa dake d'auke da agogo da zubuna ya kai ya tura cikin gashin nasa mai shegen laushi ,kafin ya juyo gaba d'aya zaiyi ciki. Ya hayyu ya Kayyumu. Matsanancin kyau da yake dashi abun bazai misiltuba. Manyan ocean Blue eye's ne dashi dake dauke da dogon hanci da gashin gira yala-yala kaman na mace. Full lips nashi da suke pink colour kaman mai shafa janbaki ya tura leben sa na k'asa ciki ya fara tafiya sak yanda yara suke idan suna koyon tafiya.
Yanda yake tafiya yana had'a hanya zai tabbatar maka a buge yake. Yana shiga ya zube cikin kujeru sai sumbatu yake shi kad'ai. Bai jima ba kuwa mugun barci ya yi awon gaba da shi.
𝐏𝐆 4.
Kiran sunan sa da yaji anayi da wata irin murya mai amo yasa shi buɗe ido cikin matsanancin mamaki. Maimakon ya ganshi kwance kan sofa kaman yanda yake sai ya ganshi cikin wani kungurumin daci mai shegen duhun tsiya da kukan halittu mai ban tsoro ya cika shi. A mugun firgice ya fara waige-waige yana neman tsira amma kaman wanda aka kafar a gurin ya kasa motsa ko yatsan sa sai kawayar idon sa dake waige-waige cikin matsanancin tsoro da firgice. Daga gefen hagun sa yaji wannan murya ta tunkaro shi tana kira da wani irin k'araji. Matsanancin tsoro da firgici Moha ki ciki abun sai wanda ya gani. Runtse ido ya yi ko Allah zaisa ya farka daga wannan mummunan mafarki da yake mai tsananin ban tsoro gashi kaman reality. Mutsu-mutsu ya fara neman k'ubutar da kanshi saboda muryar yanzu da take gab dashi. Moha sam ya manta da kiran mai duka ,hankalin sa da tsoron sa baisa ya nemi taimakon ubangiji ba sai numfashi da yake a guje kaman mai shirin samun heart attack. Ance Allah gafurur rahamin. Daga gefen daman sa iya inda yake gani ta gefen ido, wani irin haske ya bayyana da ya yi sanadin tsayuwar koma mene ne yake tunkaro shi daya kusa cimma.
"Moha"
Yaji wata irin murya mai tsananin dad'i da sanyi ta kira sunan sa da saida gaba d'aya tsigar jikinsa ta motsa. Wani irin hannu mai tsananin taushi da laushi ya sauka kan kafad'ar sa da yasa shi d'an firgita. A hankali yaji muryar ta sakko daidai saitin kunnen sa tana cewa
"Allahumma ajirni fi musibati, wa aklif ni khairan min ha"
Bai san ya akayi ba yaji bakin sa ya fara motsawa ya fara maimaita Addu'ar kaman yanda yaji muryar nayi. Cikin ikon Allah kuwa gaba d'aya jikinsa da ya yi paralysis kaman wanda akayi snap abu jikin nasa ya saki. Da wani irin azama ya yi k'ok'arin juyowa bayansa don ganin wacece. Yanzu tana can nesa dashi ta bashi baya. A guje ya miƙe ya nufi yarinyar dake tsaye cikin wasu fararen kaya masu matuƙar shek'i . Duk taku d'aya idan ya yi don cimma ta sai ta k'ara yi masa nisa. Haka ya yi ta binta tana k'ara yi masa nisa. Ganin babu mafita ya fara kira kaman zai tsaga mokogaro.
"Wait, please. Who are you?"
D'an murmushi yaji muryar tayi kafin ta k'ara kiransa da muryar nan tata mai tsananin dad'i tace
"MUHAMMAD MOHA"
Daga haka sai bat ta b'ace daidai ya farka cikin matsanancin firgici. Ya had'a wata irin zufa kaman wanda aka deb'o ruwa aka watsawa a jiki. A yanzu ma dai big brother ya mance kiran sunan Allah sai hannu daya kai ya dafe k'irjin sa dake harbawa kaman zuciyarsa zata fito fili. Wane irin mafarki ne wannan kaman gaske?. Wacece wannan yarinyar mai murya da take da matsanancin dad'i?. Tazo kuma ta taimake shi?. Wai shin mafarki ne ya yi ko kuwa hallucinations ne?. Yanda heart nashi ke racing kace zata tarwatse. Duk da ya farka bai hana aikin Jalli tab'a shi ba don ji ya yi duniya a yanzu babu inda yake da burin ya ganshi daya wuce NIGERIA. Ko kwana d'aya baya son k'arayi a nan.
Jiki na rawa ya miƙe ya yi d'akin sa muryar nan nata yi masa amsa kuwwa cikin kunne. Hakanan yaji yana son sanin wacece mai muryar nan. Akwai ta a zahiri?, ko kuma mafarki ne kawai?. Yana had'a kaya ya kira mahaifin sa Alhaji Balarabe. Bugu d'aya ya d'aga da y'ar sallama yace
"Muhammadu ya akayi cikin daren nan?"
"Dad. Ina so na koma Nigeria"
Wani irin shiru Balarabe ya yi jikinsa ya yi sanyi matuƙa. Ba wai baison Moha yaje Nigeria bane A'a. Shi kansa ya rasa dalilin da yasa baison Moha ya kasance da Balaraba da ya'yan ta. Tun yana k'arami ta raini Moha. Kuma ya taso kan tarbiya data ginashi da ya'yan ta. Yasan irin mugun rawar data taka wajen lalacewarsa. Musamman ma kan Shaye-shaye. Babu abunda baiyi ba ya raba shi da shan giya amma abu ya faskara. Shi yasa ma ya dawo Italy nan da zama ,don da yana tare da matarsa SUHANA Balarabiyar Dubai daya aura saboda Moha.
Ya samu uwa da zata bashi tarbiya ta duroshi kan tafarki kai kyau. Amma Moha yak'i. Ko kad'an shi kansa baisn zuwa Nigeria saboda Balaraba data zame masa k'arfen k'afa. Babu yanda zaiyi da ita idan yana tare da ita sai yanda tayi dash. Sautari wani lokacin idan yana neman rufeta da tujara idan ta kaishi bango duk irin yanda zuciyar sa take zafi haka zai kasace mata komai saidai ya yi ta bata hak'uri. Numfashi yaja mai zafi yace
"Moha. Bana son komawar ka Nigeria. Idan ka gaji da zaman Italy d'in ne kazo nan Dubai wajen Mom naka mana. Kazo nima ka tayani neman wannan election da nake. Mutanen gari sun zabe ni ina running zabe na zama President. Come home to me my boy. I needed you here"
Stubbornly Moha yace
"No. I'm going to NIGERIA and that's final."
Bai jira abunda Mahaifin nashi zai cebe ya kashe wayar sa. A daren yabi jirgin sa zuwa Nigeria kaman yanda yaci buri.
AZARE.
Tsintsiya ce riƙe a hannun Jadwah dake share compound d'in gidan. Duk da cewa akwai masu aiki wani lokacin saboda yawon shige da fice da ake kafa duk an tako k'asa. A rayuwar Jadwah koya datti yake yana masifar ci mata rai. Duk lokacin da zata share k'ofar d'akin su zata had'a da compound d'in gidan ta share duk irin girman sa. Asiya dake zaune baranda su ta main kofa da ake shiga gidan tana waya taci uban riga da wando sai murmushi take zubawa kayi tunanin da wani saurayin take waya. Cire wayar tayi daga kunnen ta ta kalli Jadwah dake matsowa kusa da inda take tana shara. Wani irin tsawa ta daka mata ke
"Ke baki da hankali baki ga waya nake ba?"
A hankali Jadwah ta d'aga ta watsa mata manyan idon ta, bata ce komai ba ta juya ta koma k'ofar d'akin su. Ran Asiya ya yi matuƙar b'aci. Haka kawai ta tsani yarinyar saboda kyau da Allah ya bata. Kwafa tayi ta cigaba da wayar tana gayawa JJ abunda y'ar iskar yarinyar ke mata. D'akin su ta shiga ta lek'a wajen Baba dake barci saboda ciwon kai daya kwana dashi da kafa ,da kyar suka samu ya yi barci gabanin asuba. Dan yau ko Sallah Asuba da bata wuce shi a masallaci a d'aki ya yi. Duk Abunda Jadwah take tana dauriya ne. Ciwon Mahaifin ta ya dame ta matuƙa tana tsoron shima ya tafi ya barta kaman Mahaifiyar ta. Numfashi taja mai zafi idon ta cike da kwalla ta fito ta kwashi kwanuka tayi waje dasu don ta wanke.
Tana fitowa aka yi horn k'ofar gida don haka jiki a sanyaye tayi wajen gate d'in ta buɗe. Motar Hajiya Suwaiba ta shigo ciki , maimakon ta wuve sai ta tsaya kusa da d'akin su ta fito daga motar taci uwar ado kaman mai zuwa gasa. Murmushi ne kwance kan fuskarta tana kallon Jadwah harta k'arasa rufe gate ta juyo inda take tsaye. Gaban Jadwah ya yanke ya fad'i haka nan kawai taji matar bata kwanta mata a rai ba. D'an murmushi ta kirki da baikai zuciba ta d'an durkusa tana cewa
"Hajiya ina kwana ,an tashi lfy?"
Fuskar Suwaiba ta k'ara cika da fara tace
"Lafiya lau Jadwah. Ya kwanan ki dana Mahaifin ki?"
A hankali tace lafiya tana kallon k'asa. Murmushi Suwaiba tayi ta buɗe motar ta fito da leda ta miƙo mata
"Ga wannan babu yawa y'ar alawa ce ta yara dana gani naga ta dace dake."
A d'an razane da mamaki Jadwah ke kallonta tana girgiza kai. Yaushe ne sukayi sabon da zata karb'i abu gurinta. Ita koda ta sanka ma baka mata kyauta haka kawai ta k'arba.
" A'a wlh Hajiya. Nagode Allah ya saka da alheri "
Murmushi dake kan fuskar Suwaiba ya kai ta zuba mata tace
"Baza ki karb'i abun hannuna ba saboda me?, ko dan baki sanni ba?"
"Aa wlh Hajiya ba haka bane"
"To kina kyamata ne ko kuwa kin raina abunda na baki?"
Wace irin magana ce wannan?. Jadwah ta ce cikin ranta. Numfashi kawai taja ta fesar bazata iya cigaba dayi mata musu ba. Idan bata karb'a ba ,zata fuskance ta da wata manufar don bazata tab'a fuskantar ta ba.