Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 10
inata wannan tunanin barci ya ɗaukeni har muka isa gidan sarki, bamu sha wahalar shuga gidan ba saboda ganinmu da sukayi da Baby Su'ad, sarkin mota yafara ganinmu ya washe baki yana dariya ya ce "Hajiya barka da zuwa, kunzo kuma gidan basa nan yanzu Umma ta futa asibitin da Turakin yake" da sauri na ɗago na kalleshi muryata tana rawa na ce "Baba maiya sami Fu'ad ɗin?" "E to nadaiji ance ciwon damuwa ne" sarkin mota shiya mana jagora zuwa hospital ɗin Fu'ad na zaune jingine da fulo Usman yana gefansa ransa a ɓace sai masifa yake "Akan wata banza can kake neman kashe kanka dan tace bazata aureka ba saime, ni ban taɓa ganin irin wannan mahaukacin son ba, basu baka ita ba tana budurwa yanzuma data zama bazawara sai sun tsaya suna ja maka rai kamar itace..."Ya isheka Uthman kasan abinda zaka rinka faɗawa Su'ad itace rayuwa ta ruhina, wallahi a wannan karan na rasata mutuwa zanyi na gaya maka damuwata ne danka taimaka min baka zauna kana gayamin maganganun dazasu karamin ciwo ba, so ba karya bane na tabbata kasan mainene so tunda auran soyayya kayi! Su'ad koda ace ta tsufa mijinta ya rasu wallahi zan iya auranta a ko wanne yanayi take ita nakeso ba wani abu na jikinta ba *itace burina* idan nasameta banida sauran wata damuwa, dan Allah na rokeka kaje ka lallaɓamin ita ta daure ta aureni dan Allah" Fu'ad yafaɗi haka yana saka hannunsa cikin na Usman🤝 Jikin Uthman yai sanyi yana bin ɗan uwan nasa kuma aboki da kallo yama kasa magana sai kafesa dayai da idanu yana kallon yanda hawaye ke zubowa daga idanun Fu'ad hannunsa yaruko zaiyi magana sallamar mu tasa yai shuru da sauri na isa gaban gadon cikeda damuwa ganin yanda Fu'ad yai wata iriyar rama ya kara fari kamar wanda ba jini a jikinsa, ganina dayayi tsaye a kansa yasa ya ce "Kagani ko Uthman kana kallo tafara min gizo ko Aboki gayamin kodai na haukace ne ita nake gani a gabana dan Allah Uthaman karka tashe ni daga wannam barcin danake ka barni na dawwama tare da ita a cikin mafarki na, hannu ya miko min alamar na matso kusa da shi, ban matsan ba saima komawa gefe danai nasoma kuka "Kaima mutuwa zakayi kabarni kamar yanda Uncle yatafi ya barni, nifa wasa nake maka ko yanzu ka shirya na amince zan aureka indai hakan zaisa ka farin ciki, kasani ina sonka! inason ganinka cikin farin ciki da walwala kwanciyar hankalinka shine nawa", lumshe idanu yayi tareda maida kansa saman fulo ya kwanta yana mikomin hannu, hannuna nasa cikin nasa ya janyoni na faɗa jikinsa yasa hannayansa ya rungumeni yana sauke numfashi, muna a wannan yanayin har bamusan sanda Uthman ya futa ba, da sauri na janye jikina daga nasa tuna cewa hakan haramunne, Allah yayi hani da haka da sauri na fara furta Astagafirillah na koma can gefansa na zauna ina kallon sa, ya rame sosai sai uban haske daya kara. "Zubamin abinci yunwa nakeji" Basket ɗin dake ajje saman fridge na ɗakko na buɗe warmars na zuba masa fatan dankali dayasha hanta da alayyahu sai tashin kamshi yake, na mika masa plate ɗin amma sai yaki karɓa sai hannu yasa ya ɗauki spoon ɗin yafara ɗiban abincin ahankali yana ci ni kuma ina rike da plate ɗin abincin, muna a haka ta shugo da sallama, kyakkyawar maca ce fara kakkaura, tana rikeda da Baby Su'ad sai dariya take mata, take gabana ya faɗi daga gani ba tambayya na tabbata wannan ce matar Fu'ad mahaifiyar Baby Su'ad, zama tayi kusa dashi tareda taɓa jikinsa ta ce "Dear yaya jikin naka?" "Da sauki" yabata amsa a takaice yaci gaba da cin abincin nasa, ɗagowa nayi na sake kallonta itama ni take kallo tana aunamin harara. "Princess bani ruwa" Fu'ad da muryar maras lafiya, atare muka mike da ita na rigata isa gaban fridge saboda yafi kusa dani, ruwan gora na ɗakko masa na ɓalle masa murfin na basa a hannu ya kafa kai ya shanye ruwan tas, plate ɗin abincin na ɗauke wanda shima yaci dayawa na ajje sa saman fridge bayan nasa wani plate ɗin na rufe. Yanda ta shugo ɗakin cikin nutsuwa da kamala haɗe da cikakkiyar sallama yasa na maida hankali ga dattijuwan matar wacce nake zaton bazata wuce shekaru hamsin da biyar ba zuwa sittin, yanda naga fadawa na take mata baya ga yammata biyu atare da'ita ɗaya na rikeda hand bag ɗayan kuma na rikeda wayoyinta, hakan yasa na gane itace Umma matar mai martaba, hannuna ta ruko tana murmushi ta ce "Sannu da zuwa Su'ad ɗin Fu'ad yanzu sarkin mota yake gayamin kunzo kun kawo baby Su'ad" Kasa na zame ina gaidata cikeda girmamawa, hannu tasa ta ɗagoni ta maidani gefan gado na zauna. "One Boy yaya jikin, sai kuma ga Sweet heart tazo cuta ta warke" Murmushi kurum yayi sai sannan Umma taga Baraka dake zaune can gaban gadon kan kujera, "Ran uwargida ya daɗe yaushe kika zo, na baroki a gida kin rigani zuwa,kodan na tsaya duba marassa lafiya a genarel hospital" Baraka murmushi kurum tayi taci gaba da danna wayarta, Umma katuwar dadduma ta shimfiɗa ta zauna nima ta umarceni dana zauna ta zubomin abinci, kasa cin abincin nayi sai danna wayata da nake, shugowar Dr yasa na mike zan futa, dan tun ɗazu nake zuba idanu naga ta inda Yaya Shareef zai ɓullo amma shuru gashi har anfara kiran sallar la'asar, futa nayi ina lalubansa amma babu shi babu alamunsa ko matarsa ma bata inda ya ajjeta, cikeda damuwa nake danna lambarsa harta shuga bugun farko yaɗaga yanamin dariya. "Yah Shareef ina kaje ne?naga baka compound na hospital ɗin" "Waini kike tambayya toni kin ganni nan a abuja nafi minti talatin ma da sauka" Shar shar idanuna suka zubo da kwalla "Yaya zakamin haka ka barni a garin mutane katafi ka barni yanzu yaya zanyi na koma gida?" "Kinga kwantar da hankalinki motata ma tana nan garin jirgi nabi saboda kiran gaggawa na samu daga office, Umman mai martaba ita tace na barki gobe su Mami zasuzo duba Fu'ad saiku wuce tare" "Kwana kuma yaya anan garin kai haba bazan iya ba" "Bazaki iya kwanan gidan surukai ba" naji an faɗa daga bayana katse wayar nayi na juyo ina kallon Umma dake magana "Kiyi hakuri ni nayiwa Maminki waya ta turo mana ke Fu'ad yana cikin kunci da damuwa kamar yanda abokinsa Uthman yagayan kece damuwar Fu'ad, kiyi hakuri inma wani laifi yayi maki ku sasanta, yana sonki sosai Su'ad inya rasaki a wannan karon bazai iya jurewa ba, zuciyarsa tayi rauni sosai a kaunarki ki tausaya masa" Sunne kaina nayi kasa ina wasada zoben hannuna ganin bance komai ba yasa taja hannuna muka koma ɗakin, bakin mata da miji muka tarar jin danai Umma ta ce "Lale da Abiee munyi fushi sai yau kazo duba one boy ɗin nawa" hakan data faɗa yasa na gane mahaifin Fu'ad ne wannan "Ayi hakuri abubuwane sukayi yawa musamman wannan guguwar zaɓan data tunkaro mu bamuda lokacin kanmu kullum muna yawon kamfen, kuma nasan zuwan nawa ma baida amfani tunda gaku keda mai martaba,sannan ga Antynsa itama tana kusa tunda taki zaman abuja" Dariya Umma tayi batace komai ba, kallo ɗaya Anty Jameela tamin ta ɗauke kanta taci gaba da danna wayarta, nima shareta nayi nagaida Abiee kawai wanda ya amsa fuska sake yana tambayar Umma "Asiyya ina kika samu ya" "Au ashefa baka santa ba ita ta zaunar da Fu'ad anan" Umma tana faɗar haka yadafe baki🤭cikeda mamaki ya ce "Au anyi abun kunya nakasa gane Su'ad ɗin Fu'ad, haba shiyasa naga bakin ɗan naki yaki rufuwa" wani kallo da Anty Jameela tayi masa yasa yai shuru badan yagama magana ba, ɗakin yai shuru har sukai shirin tafiya, Baraka tabi bayan su tanawa Anty Jameela magana "Anty wai wannan yarinyar wacece ɗin su Abban Su'ad naga sai wani shisshige mata yake gani a waje amma bazai ce inmasa wani abu ba saidai ita" Anty Jameela saida tayi dariya kana tace "Hmmm wannan itace Su'ad budurwar Fu'ad wacce yaiwa mahaukacin so mijinta ya rasu shine yanzu yake so ta auresa, sorrynki yarinya idan har kikayi saken da wannan yarinyar ta shugo maki gida, kiga abata nan ma daya haifi ya sunanta yasa saboda ya raina maki hankali, lokaci yayi da zakizo mu haɗe kai muyaki yarinyar nan dan inkika sake ta shugo kin kaɗe ke matar shige (Anty mai zafafa) ita kuma matar so kinga babu haɗi, dole kiyita ganin takaici" Hannu Baraka ta ɗora aka🙆‍♀️"Wayyo na shuga uku daman Su'ad sunan budurwarsa yasa nifa na zaci na mahaifiyar sa ne, wayyo Allah na Fu'ad yakashe ni"😰gaba Anty Jameela tayi tabar Baraka anan tsaye tana goge hawaye. Nifa duk zaman garin ya'ishe ni, musamman yanda Fu'ad yake wani kallona duk na kasa sakewa hakan da Umma ta lura yasa gabda mangariba tace natashi mutafi gida, Fu'ad ya marairaice fuska "Umma tun yanzu zaku tafi yau bazaki bari ayi sallar insha ba" "E tafiya zanyi bakaga bakuwa ba, gida zamuje tai wanka ta kwanta ta huta gajiyar hanya" bayan Umma nabi data futa naji ya ce "Su'ad jimana" najiyo na kallesa "Wayan waye a hannunki" "Ta Mami ce" nabasa amsa ina kokarin futa,baicemin komai ba harna fuce, a wani babban super market muka tsaya Umma ta zaɓamin dogayan riguna masu kyau nayi amfani dasu tunda banzo da shirin kwana ba sai kayan ciki data sakani na zaɓi size ɗina, koda mukaje gida ɗakinta ta kaini ta haɗamin ruwan wanka nayi na shirya cikin daya daga cikin rigunan data saimin, nai sallar mangariba ina nan zaune ina cin abinci, aka shugo da sallama. ɗago kaina nai na kalli wacce tai sallamar itama kallona tayi ta ɗauke kai batare da tacemin komai ba, Umma ce ta shugo hannunta rikeda plate da aka shakosa da kayan fruit ta ajje agabana tana kallon yarinyar dake zaune gefan gado, "Juhaina bakiga bakuwa ba?Su'ad ce fa budurwa Turaki" Dan taɓe baki tayi tana kauda kai gefe ta ce "Naganta sannu fa" tana gama faɗar haka tai fucewarta daga ɗakin, murmushi Umma tayi tana rakata da kallo harta fuce. Sosai Umma take bani kulawa kamar yarta haka ta maidani, yanda kowa yasanni agidan abin har mamaki yake bani, kwana na biyu a garin aka sallami Turaki daga asibiti saboda yaji sauki sosai, wata irin kula yake bani duk da ni zaman gidan dik ya isheni hakan yasa na kira Mami ina mata korafi "Nifa Mami wallahi tahowa zanyi gida, kawai daga zuwana sun wani rikeni ba dangin iya bana baba inata zama masu a gida" "A'a karki taho ki bari jibi zanzo duba Fu'ad ɗin saimu taho tare" nidai badan son raina nake zaman gidan nan ba wallahi. Da yamma ina zaune nayi wanka nasha kwalliya cikin doguwar rigar Atamfa Umma ta bani washe garin randa naje kusan kala shida da'alama bayarwa tayi aka ɗinkomin su, wayar Mami ce a hannuna ina chat, kiran Nurein daya shugo yasani kwantawa saman doguwar kujera tareda kara wayar a kunnena, ko sallamar danayi bai amsaba ya ce "Wai zaman me kike a garin mutane yau kusan kwananki huɗu kullum nazo bakya nan an shaida min kina bare, garinsu Fu'ad ne fa mai kikeyi?" "Nima zaman yana damuna Hubby nafison nadawo gida amma sunki bani dama jinake kamar na gudu" "Kinga karki rainamin hankali nafasan maike tsakaninki da gayan nan inma ba iskanci ba maiya kaiki zama a garinsu" "Nurein mai kake nufi?" "Kinga dan Allah kitaimakeni ki dawo nifa tsoron gayan nan nake karya kwacemin ke, Su'ad ina matuwar sonki banson abinda zai rabani dake, kinga Abbana harya fara maganar turowa gidanku wata yar matsala aka samu da tuni sunzo ma please dan Allah kidawo" Ajjiyar zuciya nasauke kana nace "Ok naji Hubby zan dawo jibi" Wayar naji an zare daga kunnena a tsorace na mike dan nidai nasan ni kaɗaice a falon, Fu'ad na gani tsaye akaina yana kallona yana juya wayar a hannunsa, kallo ɗaya nayi masa na kauda kaina daga kallon nasa saboda masifar dana hango cikin kwayar idanunsa, cije leɓe yayi ya zauna kan kuja ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yana girgiza kafar saman, na lura yana son yin magana amma tsabar fushi yasa yakasa cewa komai, nima zama nayi a kujerar dana tashi kaina a kasa ina jiran inji abinda zaice, karar wayar tasa na ɗago ina kallonsa, yanda yake huci yaso tsorata ni kallona yayi ido cikin ido. "Narasa maine maki kika daina sona Princess,na lura so kike ki kasheni da raina, kinsan irin son danake maki kuwa? Kinsan tsawon shekarun nan dai dai da dakika ɗaya sonki bai taɓa raguwa a zuciyata ba, kinssan mainene so kuwa Su'ad kinaso ki kaina lahira kwana na bai kare ba? sa'arki ɗaya wayar nan vataki bace wallahi da yau saina kwankwatsata naga ta inda wannan mayan zai sake kiranki, akaro na biyu karki yadda ayi na uku dan wallahi rai zaiyi matukar ɓaci, akanki zan iya yin komai, wallahi kinji na rantse idan na kara jin kina wayada gayan nan ko kika sake tsautsayi yasa na ganshi to wallahi saina ɗaure sa ko ɗan gidan waye a kasar nan saidai nima a ɗaurenin" yana gama faɗar haka yasa wayar a aljihu yasoma tafiya. "Kabani wayata to, waccan ma ka kwacemin wannan ai ta Mami ce kuma ni gidanmu zan tafi" ganin bai kulani yasa na mike nabi bayansa. "Nifa kabani wayata haka kurum zaka rabani da shi naga tare ka ganmu ko aurata kayi dazaka rinka kafamin sharuɗa" afusace ya juyo kamar zai dake ni yake faɗin "Haka kikace ko? wayar yamiko saida yabuɗe kofa zai futa ya juyo yanamin wani kallo dana kasa fassara sa ya ce "Ki shirya zansa a maidaki gida, kuci gaba da soyayya da Nurein Allah yabarku tare...✍🏻 07039793439 🌹 *KUKAN ZUCIYA* 🌹 Story and Writting by Mamie Yusuf Daboo🥰 ☀️ *First Class Writer Assosciasion* ☀️ Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation MARUBUCIYAR HALIN RAYUWA SOYAYYA DA ZUMUNTA SANYIN IDANIYYA AIMANAH YANAYIN RAYUWA AND NOW KUKAN ZUCIYA 29&30 Gaba ɗaya kuma sai jikina yayi sanyi na koma na zauna, ashe Umma tana kallonmu ta saman mai martaba. "Kibi Turaki a hankali kwanan nan nakasa gane kansa gaba ɗaya ya canza nema yake ya birkice mana, ki shirya nasan yanzu zakiga ya turo ki futo amma banso tafiyarki yau ba, ba komai ai kin kusa zama tamu gaba ɗaya" Nidai bance komai ba na shuga ɗaki na haɗa kayana, ina futowa ko saiga dogari yace nazo, Umma ta kaini wajan mai martaba nai masa sallama, kyautar kuɗi yabani wanda naso kin karɓa Umma tace na karɓa in yayi kyauta ba'a kin amsa haka na karɓa ina godiya, Umma turaruka tabani masu kamshi da materi'al guda huɗu, ita ta rakoni a wajan motar dake parke a compound na gidan, glass ɗin motar mai duhu ne hakan yasa banga wanda ke ciki ba, nadai gane motar ta Fu'ad ce ganin danai ansa Turaki 3 baya Umma ta buɗemin na shuga kamshin turarensa danaji yasa na kalli gefena bayan Umma ta rufe murfin motar,yana zaune cikin motar ya haɗe cikin bakaken suit idanunsa na saye cikin bakin glass mai duhu ya maida hankalinsa kam laptop ɗinsa dake ajje saman kafafunsa ko kallon inda nake baiyi ba yaci gaba da abinda yake, jefi jefi nake ɗan satar kallonsa, ganin ba abinda ya shafesa da irin gudun da sarkin mota keyi. "Nifa kallon nan ya isheni haka" Turaki yafaɗi haka batare daya ɗago ya kalleni ba. Taɓe baki nayi bance komai ba inajinsa yana yan wakokinsa, bance mass kala ba har mukayi nisa, ɗan matsowa da yayi kusa dani yasa nai saurin kallonsa, hannuna ya ɗago yana kallon zoban hannuna, murmushi kwance saman fuskarsa ya ce "Haryanzu dai ina nan da matsayi na tunda ba'a cire zobena ba" zobena dana saka masa a ranar da mukayi ban kwana kafin bikina da Uncle, ya ciro yasaka min a kusa da wancan "Ga wannan nasan zai rinka tuna maki da Uncle duk da nasan shi ba sai lalle da zobe zakina tunasa ba akwai abubuwa da dama" yai kasa da murya cikin sigar lallashi idanunsa cikin nawa ya ce "Kice kikafi kowace mace mahimmanci acikin rayuwata, na rayu tsawon shekaru da soyayyarki, zan iya bada duk kan abinda na mallaka inhar zan same ki, yake masoyiyata ki sani kece mace ɗaya tak danakewa wani irin so da bazan iya misalta sa ba, dan Allah ki daure ki bani dama na futo nan da sati biyu ayi bikinmu nai maki alkawarin baki farin ciki aduk cikin rayuwarki, kibar batun matata ita ɗin kaddarata ce rabon Su'ad yasa aka auramin ita, Su'ad wallahi zuciyata babu soyayyar ko wacce mace inba taki ba" hannuna ya haɗe da nasa ya sumbata sannan ya saki hannun ya matsa can gefe ya ɗora kansa saman kujerar motar yai shuru "Zuciyata kaine kaɗai wanda takeson na riga na faɗa maka tun tuni na amince dakai ko yanzu ka shirya nima na shirya a ɗaura kawai, Nurein yanada zafin zuciya sonake mu rabu lafiya dashi shiyasa kaga ina biye masa amma tuni babu sauran soyayyar sa acikin zuciyata, mai waje yazo kaga mai tabarma dole yatashi, kaddarar auran Uncle tarabamu a baya amma a yanzu ba mai rabamu nidakai mutu ka raba" Wani kallo yake aunamin wanda na kasa tantance na maine shinna farin cikin maganata ne kona sone baice komai ba motar tayi shuru kowa yatafi tunani, karar wayarsa ta dawo damu daga duniyar tunanin da muka lula lokacin har mun shugo kano, kallona yayi kafin ya ɗaga kiran tana kuka take faɗin "Yanzu Abban Su'ad abinda kayimin ka kyautamin kenan, gaba ɗaya ka banzatar dani ka manta dani ka ɗauki wata can banza kun futa yawo wannan adalci ne maine maka haka daka tsaneni" lumshe ido yayi yanajin wani tausayinta na taso masa daga kasan zuciyarsa a hankali ya ce "Kinga ba yawo na futa ba kano naje zan maida Su'ad" yana gama faɗar haka ya kashe wayar sa gaba ɗaya bayason abinda zai katse masa wannan mode ɗin na farin ciki dayake ciki, satar kallon Su'ad yayi wacce ta wani haɗe rai, murmushi yayi a zuciyarsa yana faɗin mata sha'aninsu sai su, sam baitaɓa zaton zaiyi mata biyu ba amma ga yanda kaddara tayi dashi tabbas zaisha fama Baraka kishi Su'ad zuciya. Gabanane yafaɗi sanda muka shuga compound na gidanmu Nurein na hanga tsaye jikin motarsa yanda ya harde hannu a kirjinsa kawai ya nunamin a fusace yake Wani kallo Fu'ad ya watsamin tareda nuna wajan da Nurein yake "Wancan shine Hubbin naki ko hmm" yayi kwafa tareda futa bayan sarkin mota ya buɗe masa murfin motar, ɓangaran danake ya buɗe gabana yana faɗuwa na futo saboda bansan yanda za'a kwashe ba tsakanin Fu'ad da Nurein nikam banso wannan haduwar ba, ina futowa gaba ɗaya Fu'ad ya janyoni jikinsa ya rungumeni ta gefansa na soma kokarin kwacewa saboda ganin mutane awajan amma shi ko'a jikinsa a haka muka fara tafiya inata son cire jikina daga nasa. "Ai basai kayi haka ba, kowa daman yasan abinda kuke aikatawa kenan gashi nan yanzu ka futo ka shaidawa duniya" Nurein ke faɗar haka ransa a matukar ɓace, yacigaba da faɗin "Mai zanyi da ragowar wani kaje na bar maka ita" yana gama faɗar haka ya shuge motarsa yajata a fusace yafuce daga gidan, sakina Fu'ad yayi yana dariya harda rike ciki, ni kuwa gaba ɗaya haushinsa ya kamani da irin abunda yayimin ya wani rirrikeni gaban mutane yabani kunya "Daman saboda shi nayi haka Alhamdulillah kwalliya ta biya kuɗin sabulu ni daman haka nakeso"yana gama faɗar haka ya wuce ciki ya barni raina ɓace. Fu'ad bai wani jima a gidanmu ba ya wuce ashe karaye yatafi sukayi magana da Baban karaye a washe gari kuwa tawagar mai martaba sukaje nemarwa Fu'ad aure atake anan Baban karaye ya tsaida ranar ɗaurin aure sukuma suka bada komai ciki harda sadaki lefene sukace nan da sati ɗaya za'a kawo, ni duk abinda ake ban sani ba saboda rabona da Fu'ad tun da yakawoni ban sake jin ɗuriyar saba, ina zaune a ɗakina Mami ta shugo tanata faman murmushi kusada ni ta zauna ta kamo hannuna tana faɗin "Kinga ikon Allah ko ashe kunada rabon aure da Fu'ad yanzu baban karaye yazo wai an tsaida biki nan da sati biyu har sun biya sadaki" Kafafu na fara bugawa kamar wata karamar yarinya na soma kuka "Ni wallahi ban amince ba shine kawai zaije ya sami baba batareda ya nemi amincewata ba, ni bama yanzu zanyi aure ba sonake naci gaba da karatu na"murmushi Mami tayi tamike ta futa. Nurein tunda yabar gidanmu yake a fusace zuciyarsa yakejin ba daɗi, daman zargin dayake kenan gashi kuma idanunsa ya gane masa wayasan ma irin abinda sukai a can garin shi kuwa Su'ad ko daga ita sai shi suka rage a duniya yabarta bari nahar abada, zaije yaiwa mahaifiyarsa biyayya ta zaɓa masa koma wace ashirye yake daya aure ta. Yana tsaye gaban madubi yana ɗaura agogon rulex a hannunsa na dama, shugowarta ɗakin kenan ta tsaya daga bakin kofa tana kare masa kallo yayi mata kyau sosai ba karamin kyau kayan sarauta ke masa ba amma shi sam bai sani ba shiyasa bai fiya shugar ba, ahankali take takowa har zuwa inda yake tsaye yana kallonta ta madubi amma sai yayi kamar bai ganta ba ya kauda kai yana murmushi, tana zuwa kusa dashi ta rungumesa tareda ɗora kanta saman kafaɗarsa tana kallonsa ta cikin madubin ta ce "Abban Baby kayi kyau sosai sai ina kuma?ko unguwa zaku futa da takawa?" Murmushi yayi "Da gaske nayi kyau?" Kai ta ɗaga masa alamar e kan tace "Kyau sosai ma bakaga yanda kayan nan ke maka kyau ba, amma kai bakason sawa kafi kaunar kayita shugar kananun kaya kamar wani bature" "Naji to sakeni karki ɓatan lokaci kano zani" Wani kunci taji a ranta ashe daman duk wankan nan dayayi kano zashi wajan wannan shegiyar yarinyar tabbas duk yanda zatayi saita ɓata masa wannan kwalliyar sai taja abinda zai saka dole ya canza kaya dan bazata taɓa bari yaje kano da wannan shugar ba hannunta tai saurin ɗorawa kan j ɗinsa da sauri ya juyo zaiyi magana kafin yace komai tai saurin haɗe bakinta da nasa nan take ta fara aika masa da sakonni wanda yakasa jurewa dole ya maida martani, janyo shi tayi suka faɗa saman gado tana wasa da wasu sassa na jikinsa, ganin gaba ɗaya ya gama bada kai yasa tafara cire masa kayan tana jifa dasu kasa bayan ta gama yamutsa su ta yanda tasan dole dai ya canza wasu, sosai ta rikesa da salonta har sukaja lokaci kafin suka sami nutsuwa, shiya fara mikewa ya shuga bathroom bayansa tabi bayan ta kalli agogo tasan yana shiryawa ba'abinda zai hanasa tafiyar nan itaa kuma taci alwashin a yaudai bazaije kanon ba, a cikima bata kyalesa ba shima ya biye mata karar wayansa daya jiyo daga ɗaki yasa yai saurin yin wanka ya futo, itama wanka tayi tabiyo bayansa tana gunguni, kallonta yayi ya ce "Mai kike cewa?" "Nifa bai isheni ba kai kuma naga sai wani sauri kake?" "Hmm sodai kike ki hanani futa yau ki haɗani da kanwarki tayi fushi na shuga uku" Daure fuska tayi kamar bata taɓa dariya ba ta zauna gefan gado taja tagumi tana kallo yana sake wani shirin wanda yafi nada amsar sa. Ina zaune cikin shagonmu ina kallon yanda Mami kewa wata amarya kwalliya tai matukar kyau hotuna nake mata a wayar Mami danni har yau banda waya gobe dai nake saran zanje na siya nabawa Mami wayanta data dawo kamar tawa kiran Fu'ad ya shugo ina kallo ya katse ban ɗaga ba harsaida yasake kira nan ma saida ta kusa tsinkewa na ɗauka sallama yai na amsa masa ina wani cin magani "Amarya fatan kina gida gani na shugo kano nida Abokina Uthman" "Ok saikun karaso bana gida amma yanzu zan koma" Mami na gayawa Fu'ad ne zaizo na tafi gida, rasama mai zan masu nayi tunawa nayi yana matukar son gurasa na taɓa jin hakan a wajan Uncle hakan yasa na shirya masa gurasa wacce tajiku tai laushi tasha kayan haɗi irinsu cocumber kabeji tumatir green peper harda carrot dana gogasa sai lemun aya danai masa nasa a freezer, jin ana kiran sallar la'asar yasa na futo daga kicin ɗin na shuga ɗakina wanka nayi nai sallah kana na zauna gaban madubi na soma tsara kwalliya karo na farko kenan da zanyi kwalliya tun bayan rasuwar Uncle "Allah sarki Mijina I miss

Chapter 9 of 10