ina matukar ji da Khady kasancewar bata da kowa a kasar nan mahaifiyarmu yar kasar sudan ce ta haɗu da mahaifina Alhaji bello a jami'a lokacin yana malamin makaranta a jami'ar su sunyi soyayya sosai dashi kafin maganar aure ta shuga tsakani, kakana wanda ya haifi Abbunmu shine sarkin garinmu su biyu jal ya haifa shiyasa yake matuwar son ya'yansa da basu duk abinda suke so shiyasa a sanda yaji labarin soyayyar Abbi da Ummu takanas yatashi zuwa Sudan bai dawo ba saida ya tabbatar an ɗaura masu aure sannan yabaro su acan yadawo, shekara biyu da auran Allah yaiwa mai martaba rasuwa hakan yasa Abbi suka dawo nageria lokacin ina ɗan shekara ɗaya, ankai ruwa rana akan naɗin sarauta inda majalissar sarki suka zaɓi Abbi shi zai maye gurbin mahaifinsa sam shi dama can baya ra'ayi sarauta, cikin dare ya lallaɓa sukabar gida shida Ummu dani ba'a sake jin labarin suba saida aka naɗa kanin Abbu ɗinmu sannan suka dawo, shekarata goma sha biyar lokacin muna secaundry nida Fahad aka haifi Khadija nayi murna sosai lokacin da muka koma gida muka tarar Ummu ta haihu, nida Fahad mun shaku sosai shakuwarmu tasa ko hutu akai tare muke tafiya gidanmu muyi rabin hutunmu acan sannan muje gidansu mu karasa hutun a can shakuwarmu ta zarce Abota tazama aminta, a shekarar da muka gama Secaundry Allah yaiwa Ummuna rasuwa sakamakon haihuwa datazo yi Allah baisa zata haifi abinda ke cikinta ba suka koma tare! munyi kuka kamar bazamu daina ba nida Khadija da Fahad, awannan yanayi Abbansu Fahad ya ɗaukemu yakaimu Rasha karatau acan mukayi karantu likita, bamu taɓa komowa gida ba har saida muka kammala karatu watanmu biyu da dawowa nan ma Allah yaiwa Abban su Fahad rasuwa, nadawo na samu Abbunmu yayi aure kawar Ummu wacce tunda tazo nageria batada aminiya sama da'ita, sosai take azabtar da Khadija ni kuwa daman ba zaman gidanmu nake ba ko yaushe ina tareda mai martaba kanin mahaifina acewarsu nine yarima mai jiran gado saboda mai martaba bayada ɗa ko ɗaya ya'yansa duka matane, shiyasa ko yaushe muna tare, awannan lokacin Fahad yayi aure ni kuma na wuce Canada inda naci gaba da karatu bayan na kammala na sami aiki acan shekaruna goma acan ban sake waiwayar gida ba inadai bincikar rayuwar Khadija wacce nasa matar mai martaba Umma ta ɗauketa ta maidata wajanta, Umma nada kirki ita kullum mukewa kallon uwa mahaifiya wacce bata ɗauki lamarin mu da sauki ba, ko kafin rasuwar Ummu akwai aminta mai karfi tsakaninta da Umma idan bakasani ba ka ganmu tareda Umma bazaka taɓa zaton ba ita ta kawomu duniya ba duk da wasu na mata kallon da wata munufa take nuna mana so". Sosai Fu'ad yabani tausayi ganin yanda yake goge kwalla tabbas rashin uwa babban rashine daba kowane ke ganewa ba sai wanda yarasa tashi Cikeda tausayawa nake kallonsa nama kasa cewa komai, kiran sallar damukaji yasa muka mike atare zuwa cikin gida, da yaya shareef naci karo abakin kofa ya harɗe hannu yana kallona fuskarsa babu walwala yace "Ke meke tsakaninki da AMEEN Fu'ad" ɗan ɗagowa nayi na kallesa yasake haɗe rai yana kallona nace "Ba komai kawai naje garden ne nagansa shine fa mukayi hira" wucewa yayi da'alama daman masallaci zashi ganinmu dayai tareda Fu'ad yasa ya tsaya tambayata, kai tsaye ɗakina na wuce wanda ke manne dana mami na, kasancewar ina priod yasa banyi alwalaba na kwanta saman gado.
Alhaji Usman karaye shine mahaifina haifaffan garin karaye ne, makarantar allo yakawo sa cikin garin kano inda bayan yasauke kur'ani ya shuga makarantar boko, wanki da guga yake shiya rikesa harya kammala pramary da sceundry, anan karatun nasa ya tsaya saboda awancan lokacin ba abune mai sauki ba shiga jami'a kusan sai kanada hanya sannan zaka samu shuga, Alhaji Usman ya haɗu da wani tsohon soja dayake kawo masa wanki sun saba sosai ta yanda har gidansa yakanje anan ne yake gayawa Genaral Aliyu cewa yana son shima yazama soja amma bayada hanya, haka Genaral ya shuge masa gaba harya sami damar tafiya makarantar horar da sojoji dake kaduna, bayan kammalawar sa aka tura sa aiki can jos, Genaral yaɗauki babbar yarsa ya aurawa Usman, Allah ya jarabci Alhaji usman dason matarsa Amina wacce keda tsananin biyayya gatada kirki, Alhaji Usman yataka mukamai na soji da dama ya zauna a garuruwa sosai, shekarunsu goma da aure da matarsa Amina amma bata taɓa haihuwa ba, ko kaɗan hakan bai damesa ba saboda son dayakewa Amina bayajin zai iya haɗata zama da wata ɗiya mace, gwaggo mahaifiyar Kanol Usman ita ta takura masa lalle saiya kara aure inba hakaba wlh saiya saki Amina, cikin haka Allah yahaɗa kanol da Dr Baseera Wali wacce ke aiki a babban asibitin kasa dake JOS, ya nuna sha'awar auranta saboda ya lura itama tanada saukin hali, watan Baseera goma a gidan Kanol ta haifi yarta mace kyakkyawa mai matukar kama da'ita ranar suna yarinya taci sunan Gwaggo waton Fateema, shekara biyu tsakani Baseera tasake haihuwar ɗa namiji Jabeer sannan Shareef daga nan haihuwar ta tsaya mata har sannan hajiya Amina bata haihu ba, ko kaɗan rashin haihuwar bai dameta ba ta dogara ga Allah tasani shike bada haihuwa, iyayanta ma saida suka jima kafin suka haifeta tana scoundry sannan aka haifi FAHAD
Yaran gidan Kanol sun taso kansu a haɗe bazaka taɓa gane cewar Baseera ce ta haifesu ba, Baseera suna kiranta da Ummi yayinda Hajiya Amina sukr kiranta da Mami, shekarun Shareef goma Ummi tasake haihuwar ya mace ranar suna yarinya taci sunan Hajiya Amina suke kiranta da Su'ad ba karamin gata Su'ad ke samuba awajan Mami itace komai nata kusanma awajanta take sai shan nono ke kaita wajan Ummi koda aka yaye Su'ad gaba ɗaya Ummi ta barwa Mami Su'ad, Fahad kanin Mami ba karamin so yakewa Su'ad ba ko yaushe yana tareda ita, shekarun Su'ad goma sha biyu Fahad ya auri yar wan babansa bayan rasuwar mahaifinsu Genaral Aliyu, Kanol Usman da Ummi yanzu haka suna zaune a kaduna inda Ummi ke aiki shima Kanol acan yake aiki, Mami da yara suna zaune a kano saboda Su'ad dake makaranta da kuma su yaya Jabeer dake aiki, tuni anyi bikin Yaya Fateema tana auran babban ɗan sanda suna zaune anan kano.
Su'ad dake shirin yin barci taga shugowar Fahad ɗakinta, saida ya zauna saman stool kana
Yace "Naga abincinki baki ciba, Ummi tace yau gaba ɗaya bata ganki ba ina kikaje" turo baki gaba tayi dan in tana gaban Uncle ɗin nata gaba ɗaya narkewa take ta koma karamar yarinya, shi kuma yayita biye mata tana zuba masa shagwaɓa da shiririta "Nifa Uncle yau ba kalar abinda nakeso ba akayi, kuma ai Ummi tasan bansan kunun gyaɗa da doya shine tayi ni bazanci komaiba yau" tafaɗi haka tana gyara kwanciyarta, "Wacce irin maganace haka Besty amma dai kinsan banson ki zauna da yunwa ko yanzu fa har karfe biyu bakici komai ba, kinga tashi gayamin mai kike son ci saina saka a siyo maki" da sauri na mike na zauna saman gadon ina murmushi kafin nace "Nifa Uncle kawai ka kaini nayo take away chips nakeson ci da shawarma sai meat pie da Peach mai sanyi" dafe kansa yayi yana kallonta kafin yace "Oh Su'ad nagaji dayawa yau mutum biyu naiwa cs yanzu haka gudowa nayi nazo na huta kuma ki sani na sake futa, bari kawai nabawa Seteven yasiyo maki" komawa tayi ta kwanta tana ɓata rai ahankali take mita "Shikenan kaje ka kwanta ɗin aidaman nasan basona kuke ba yan gidan nan ace na wuni banci abinci ba amma ba wanda ya damu dani, dan anga Mami da Daddy basa nan ne aida ko shi nasan zai kaini naci abinda raina keso" Fahad zama yayi gefan gadon yana cewa "Kinga bafa wani abun damuwa bane wane yace maki bamu damu dake ba, yanzu dai bari naje nayi wanka nazo na kaiki kici abinda ranki keso, kema ai kinsan bama haka dake farin cikinki ai shine nawa koba hakaba yar Uncle" yafaɗi haka yana kashe mata ido ɗaya, gabanta ne yai wata irin faɗuwa saboda ganin kallon dayake mata wanda baida maraba da irin wanda Fu'ad ke mata ako da yaushe, Bayan yayi wanka yazo suka fita tare basu wani jimaba suka dawo gida
Su'ad tare suka shugo gida da Uncle Fahad, shike rike da ledojin da tayo siyayya, tsakiyar falon ta baje taci wancan taci Ummi da yaya shareef na kallonta ba wanda ya kulata harta gama ta wuce ɗakinta.
AMEEN sosai yakejin daɗin zaman Kano tun washe garin randa yazo yacewa Yunus ya koma gida inzai komo zai biyo jirgi ko fita zaiyi shi kaɗai ke fita a motar FAHAD sau biyu yana kaiwa HIDAYA ziyara suyi hira sosai yai wasa da yaranta sannan yadawo gidansu Fahad kusan baida matsala da kowa a zamansa na gidan, sosai Ameen keson rayuwa irin haka ta ba ruwan kowa da kowa ba kamar suba a masarauta ko ina zaka kana tareda rakiyar fadawa shi yasa ya kwashe sati biyu a garin kano kafin ya saka ranar tafiya,
karfe goma na safiyar Ranar Lahdi Fu'ad yagama shirinsa na komawa garinsu, har sannan baiga futowar Su'ad ba, har sun gama sallama da Ummi sun futa compound yanata waige waigen inda zaiga Su'ad ta fito harya shiga mota yahangi futowarta lokacin Fahad na kokarin tasar mota, da sarsarfa ta karaso wajan tareda buɗe back seat ta zauna, Fu'ad ya sauke wata nauyayyar ajjiyar zuciya wacce har Fahad ya kallesa batare dayace komai ba ya juya yana kallon Su'ad
"Daman kinada lacture amma baki shirya da wuri ba sai yanzu, bayan nagaya maki karfe goma zankai Fu'ad airport" cuno baki tayi gaba kana ta ce "Aini dai rakaka zanyi banason zaman gidan nan gaba ɗaya su Ummi basa son gani na dan anga Mami bata nan kowa baya kulani kaima duka ka canza min yanzu ba ruwanka dani ko kaɗan baku rike amanar da Mami ta baku ba Allah ma yasa yau Mami da Daddy zasu dawo" Fahad tasar motar yayi batare dayace komai ba ya girgiza kai kawai yana yaba rigima irinta Su'ad yafara tafiya gate man ya buɗe mana kofa muka futa, saida Fahad ya fara tafiya saman kwalta sannan na futo da wayana na kunna data sakon Fu'ad shiya fara shugowa na buɗe da sauri ganin yana online
_"Princess kinyi kyau! bakiji yanda naji zuciyata ba dana ganni cikin mota zan bar gari batare dana ganki ba"_
_Tayaya zan bari farin cikina yatafi batare dana sake ganin saba zanyi kewarka_ ɗagowa yayi yana kallona ta madubin motar yakashe min ido tareda murmushi mai narkar da zuciyar masoya, haka mukaita musayar zafafan kalamai nida Fu'ad har muka karasa airport ɗin, zama mukayi muna jira sai nan da minti goma sha biyar jirgin da zaije garinsu zai tashi, Uncle Fahad ya zuba mana ido yana murmushi yace "Duk kun ɗauki waya kunata chat kun manta dani awajan, Su'ad dawa kike chat ne?" FAHAD ya aika mata da tambaya yana kokarin leka screen na wayar tai saurin kifa wayar a kan cinyarta kana ta basa amsa
"Da Ameerah" Fu'ad ma wayar ya ajje suna ɗan taɓa hira har jirginsu yatashi raina duk ba daɗi haka muka koma gida.
Da yamma ina zauna inda nasaba zama na cikin gidanmu wata yar rumfa ce da'aka kawatata da shuke shuke kala kala wajan yanada daɗin zama ga iska dake kaɗawa, kamshin wajan kawai ya'isa yaja hankalin mutum ya zauna, Uncle Fahad ne yakaraso wajan cikeda damuwa yaja kujera ya zauna kusa dani yajima yana kallona batare da yace komaiba na kula yana cikin damuwa hakan yasa nace "Uncle lafiya kake kuwa" ajjiyar zuciya yasauke a fili tareda saka hannunsa ya shafi sumar kansa kana ya ce "Besty ina cikin damuwa sosai, wata yarinya nakeso amma narasa ta hanyar da zanbi na faɗa mata ina sonta, tsoro nakeji gani nake kamar bazata soni ba, besty bani shawara bakiji yanda zuciyata take kaunar yarinyar ba" saida nayi dariya sosai sannan nace "Wacce mai sa'ace wannan da har Uncle ɗina yake shayin gaya mata yana sonta! kasan me kafuto kawai ka faɗa mata na tabbata zata soka, kai kasan yanda ka haɗu kuwa ko wacce mace zatayi farin ciki ace namiji kamar kai mai tarin ilimi hankali da nutsuwa babban likita yace yana sonta na tabbata komai takeji dashi kafita, bama haka ba mazai hana kasami mahaifinta ka gaya masa kanason yarsa yabaka dama ka gana da'ita kaga shikenan in yayi na'am dakai itama dole tabi" kai kurum ya girgiza batare dayace komaiba yabar wajan.
Prince AMEEN Fu'ad lafiya yasauka airport na garinsu manyan motocin masarauta daya gani cikeda airport yasa ya dafe kansa cikeda damuwa yake takawa, Allah yasani baiso mai martaba yasan da dawowarsa ba shifa sam bayason rayuwar nan ko yaushe yana kusada sarki Allah ya sani baya ra'ayin sarautar nan, yana kokarin guje masu yaji muryar Chiroma yana dariya yace "Barka da zuwa magajin sarki" Fu'ad dafe kansa yayi🤦♂️ cikeda damuwa yake kallon Chiroma yace "Kaine ka gayawa Mai martaba yau zan dawo ko?" hmm yayi kwafa tareda cikin jibgegiyar motar da Sarkin mota ya buɗe masa, tafiyar yan mintuna takaisu gidan sarki, sosai ake murna da zuwansa musamman Deejah da Juhaina nan ya baje cikinsu sai surutu suke masa da kyar yasamu ya zille zuwa sashinsa na gidan mai martaban.
Kanol Usman na zaune cikin falonsa Fahad yai sallama cikeda ladabi yazauna saman carfet yana gaida Daddy sannan ya sunkuyar da kansa yana wasada yan yatsun kafarsa yafara magana muryarsa na rawa "Daddy daman ina son na ce" yanda yake magana a rarraɓe yasa Daddy yadakatar dashi da faɗin "Nutsu Fahad gayamin damuwarka kai tsaye yanda zakai magana da Amina kullum ina gaya maka karinkamin kallon nine yayanka ba Amina ba ina jinka" kasa Fahad ya kumayi da kansa kana yace "Daddy daman sonake kamin izini inason Su'ad sona gaskiyya inhar ka amince auranta zanyi! nafara zuwa kamin izini na nemi amincewarta" Daddy farin ciki ya lulluɓe zuciyarsa shi daman yadaɗe yana wannan hasashan cikeda farin ciki yace "Nabaka Su'ad Fahad na tabbata kai mai kaunarta ne, fatana ka rikemin ita amana kabata kulawa ko bayan raina! basai kayi mata magana ba kabarni da'ita kawai gobe insha Allah zanje karaye muyi magana da Baba Sunusi zan tsaida ranar auranku banason aja lokaci burina daman ako da yaushe naga na aurar da Su'ad kafin Allah ya karɓi raina kasan yanayin cutar danake fama da'ita ba lalle nasake shekara nan gaba a raye ba" Kanol yakarasa faɗa cikin damuwa "Insha Allah Daddy zama ka wuce hakan ai kanabin ka'idoji kuma kana kan magani" murmushi Kanol yayi tareda maida kansa saman kujera yana lumshe ido shi kaɗai yasan maiyakeji ajikinsa a jiya zuwa yau daya dawo Kano shi kaɗai yake jin matsanancin ciwon da cikinsa keyi.......✍🏻
07039793439
[6/4, 7:46 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA* 🌹
Story and Writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First Class Writer Assosciasion* ☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA
5&6
Kanol yashuga ɗakin Ummi da murmushi a fuskarsa, Ummi dake tsaye jikin madubi tana shafa humra tajuyo cikeda mamaki tana kallonsa, ba kasafai ya cika shugowa ɗakin matansa ba kusan saidai su samesa a samansa, ajje humran tayi tazo kusa dashi gefan gado ta zauna, jawota yayi jikinsa suka kwanta saman gado yana dariya "Kanol da'alama yau kana cikin nishaɗi gayamin maiya saka farin ciki haka" sake rukota yayi jikinsa yana murmushi "Abin farin ciki yasamemu Dr yanzu Fahad yake gayamin yanason auran Su'ad harma nayi wayada Baba sunusi mun tsaida rana nan da sati huɗu masu zuwa gobe ma zanje karaye mu sake tattaunawa, ni uban ango shi uban amarya" Ummi da itama daɗi ya kumeta tasake kankame mijin nata tana faɗin "Kai naji daɗin zancan nan sosai Allah yasanya albarka amma Mami bata sani ba", "E sai gobe zan gaya mata na shuga ɗakinta naga sunyi barci itada ɗiyar tata" anan Kanol yai shirin kwanciyar barci Ummi tana mitar yatashi su koma samansa yace "Dan Allah Dr kibarni na kwana anan daga yau fa shi kenan bazan sake kwana anan ba" shuru tayi kawai taja masu bargo suka koma suka kwanta.
*MUTUWA YANKAN KAUNA*
Lafiya kalau Kanol ya kwanta bayan yasha magungunan sa, amma cikin dare wani azababban ciwon ciki ya turnike sa sai murkusu yake tun yana iya daurewa harya tashi Ummi dake barci, ganin halin dayake ciki gaba ɗaya hankalinta yatashi ta gigice tama kasa basa taimako, Fahad taiwa waya sukazo shida Jabir suka garzaya asibiti, Su'ad da Mami basusan Kanol ba lafiya ba saida safe sukaje asibitin, lokacin yaɗanji sauki ba kamar sanda aka kawo saba, Su'ad na rikeda hannun Daddynta tunda suka shugo take hawaye shidai Kanol kallonta kawai yake yana girgiza mata kai alamar tai shuru, "Yi shuru Autata daina kukan haka nafa ji sauki Fahad yana shugowa zance ya sallamemu mu koma gida ko haka kike so" kai kurum Su'ad ta girgiza masa, shafa kanta yayi yana faɗin Allah yai maku albarka ya albarkace ku gaba ɗaya" shugowar Fahad yasa Kanol cewa "Yauwa maida Auta gida zamuyi magana da su Mami kici abinci ki wanka anjima saiki dawo ki tahomin da fatan dankali" kai Su'ad tasake gyaɗawa haka kurum takejin jikinta duk ba daɗi, jiki a sanyaye tamike zata futa, ta juyo tana kallon Kanol daya rike hannun Fahad duk da bata jiyo abinda Daddyn yake faɗa haka kurum take zaton maganarta yakewa Uncle ɗin"Ga amanar Su'ad nan na damka a hannunka itace karama kabata kulawa kabata duk wani farin ciki na rayuwa kada kabari ta koka ko bayan raina" Fahad yace "Insha Allah Daddy zanyi abinda kake so Allah yabaka lafiya" Ameen ya furta saman laɓɓansa kana muka fita daga ɗakin,
Kanol ya kalli Mami yana murmushi "Kuyi hakuri banjin wannan ciwon nawa na tashi ne! kuyafemin ga amanar yarana nan na damka a hannunku kuci gaba da basu ingartacciyar tarbiya kamar wacce muke basu ina raye, dan Allah kada kubari wani ruɗe na duniya yasa ku raba kanku kuci gaba da haɗe kanku kamar yanda kuke ayanzu, sannan Su'ad na bawa Fahad ya aureta ko bayan raina kuka canza ban yafe ba! da sauri Mami ta kalli Kanol "Abban Su'ad yazakace haka su yaran sukace maka suna son junansu shakuwa ce kawai fa a tsakaninsu ba soyayya, inma shi Fahad sonta yake to ita Su'ad tanada wanda ta..."Umarni na bayar lallene acikan burina ko bayan raina! "Kanol dan Allah kayi shuru cuta fa ba mutuwa bace, kabari inkaji sauki saimu tattauna" murmushi kawai yayi yana kallon Ummi data kasa magana hawaye kawai take, Kanol ya lumshe idanu yana faɗin "La'ilaha illallah muhammadan rasulillah" azabure Ummi ta ɗago tana kallonsa ganin yanda hannunsa dake cikin nata yasaki, wata kara tasaki haɗeda salati itama nan ta zube, dai dai shugowar Fahad daya dawo daga gida dan ganin yaya jikin Daddyn turus yayi ya tsaya bakin kofar ɗakin yama kasa shugowa, Mami ke salati tana girgiza Ummi datake zaton itama mutuwar tayi, "Fahad ka tsaya anan karaso ciki ka bata taimakon gaggawa Daddy yau Allah ya amshi abinsa, hasbinallahu wani'imal wakil" azabure fahad yashugo ɗakin yasoma tattaɓa Daddyn saida ya tabbata rai yayi halinsa kana yasa Mami ta ɗora Ummi saman gadon dake kusa dana Daddy yasoma bata taimakon gaggawa, a firgice ta farka dai dai shugowar Fatima da sai sannan taji Daddy bayada lafiya, ganin mutum lulluɓe da farin yadi yasa Fatiman ta buɗe yanayin dataga Daddy yatabbatar mata baya lumfashi luuu tayi baya zata faɗi mijinta ya rukota ta faɗa jikinsa tana fashewa da kuka, Fahad da kwamishina su suka jajirce kan gawar Kanol aka gama haɗasa suka ɗaukesa zuwa gida dan masa sallah akaisa makwancinmu na gaskiyya😰
*Su'ad*
Sauri sauri nake na kammala fatan dankalin da Daddy yace nayi masa ko wanka banyi ba haka kurum duk nakejin jikina yai wani irin sanyi, na zuba dankalin kenan naji wata faɗuwar gaba tareda kara haɗida salati kamar muryar Yaya Shareef nakeji shiyasa na futo daga kicin ɗin da sauri kamar zan faɗi na nufi compound na gidan inda nake jiyo hayaniya, nima salati na saki ina kamewa awaje ɗaya saboda abinda idanuna suka ganemin, wata irin girgiza nayi sai gani gaban motar na rirrike Uncle Fahad ina kuka kamar raina zai futa, Rukoni yayi sosai yana goge hawayan fuskarsa yama kasa cewa komai, hannuna yaja muka shuge cikin gidan ɗakinsa yakaini ya zaunar dani gefan gado shima ya zauna har sannan hawaye ke zuba daga cikin idanunsa yabuɗe baki zaiyi magana kawai yafashe da kuka, sosai yake kuka yanda yake kukan zakasan mutuwar ta taɓa masa zuciya, cikin kuka yake lallashina "Muyi hakuri! bamuda yanda zamuyi inama wani yana fansar wani dana mutu Daddy ya rayu, tabbas munyi babban rashi Su'ad dabazamu samu madadinsa ba" mikewa yayi ganin yanda na haɗe jikina waje ɗaya ina kuka dukkan ilahirin jikina karkarwa yake allura yake shirin yimin na ɗago ina kallonsa "Uncle mai zakamin allurar barci please dan Allah karkamin kabarni naga Daddy na nai masa kallon karshe nai masa addu'a", ajje alluran yayi muka futa falo tuni mutane sun fara taruwa, kasancewar juma'a ce ana idar da sallah a masallacin unguwarmu aka sallaci gawar Daddy munaji muna gani badan ranmu naso ba aka kai Daddy makoncinsa, mutuwar Daddy gaba ɗaya ta canzar rayuwata nazama wata slent sam ba rigimar nan dana saba bana komai sai karatun kur'ani dan tuni Mami ta takamin burki da yawan kukan danake, tace ba abinda zai amfanarwa Daddy saima azaba da zanja masa, Fu'ad yazo tun randa akayi matuwar dashi aka sallaci Daddy, yan uwansa ma sunzo sosai harda Umma da mai martaba, Abbi ɗinsa ne baya nan a waya yamin ta'aziya nai mamaki sosai yanda yan uwansa suka san dani, hatta babbar y'ar mai martaba Hidaya wacce ke auran sarkin garinmu saida tazo mana gaisuwa.
Rasuwar Daddy ta canza rayuwar jama'ar gidanmu baki ɗaya kowa yazama ustaz sai ahankali muka saba da rashin Daddy tuni kowa ya koma bakin aikinsa, yaya sharif ya koma kaduna inda yake aiki domin shima soja ne sai yaya Jabeer dake aikin banki nida Yazeed mun koma makaranta ni ina shekara ta biyu shi kuma yana shekarar karshe, duk fanni ɗaya muke karanta low.
Watan Daddy ɗaya da wani yammaci ina zaune falo na biyu wata mata tayi sallama ta shugo duka shekarunta bazasu wuce ashirin da biyar ba yanda take wani kalle kalle yasa nima nake kallonta kamar na santa amma na manta inda na santa, ta zauna saman kujera kamar bataso tacemin "Hajiya Amina tana nan kuwa?" kamar nace mata bata nan ganin tambayar rainin hankalin dataimin mutanan dake takaba ina zasu futa wata unguwa, bance mata komaiba na mike na shuga ciki danna kira Mami, tare muka futo da Mami da Ummi jin danai Mami tace "A lale da zuwa Zainaba daman kece?" ɗan shuru tayi kana ta gaida su mamin, jin danai ance Zainaba yasa na gane inda nasanta matar Uncle Fahad ce wacce suka rabu dashi shekaru biyar kenan, Ummi ke tambayar ina "Ameera yammata yanzu nasan ai ta girma" bata bawa Ummi amsaba sai dariya da tayi kawai tana nan har Uncle Fahad da yaya Jabeer suka dawo, ko zama Uncle baiyi ba bayan sun gaisa tai masa gaisuwa ya wuce ɗakinsa, bin bayan sa nayi yana tsaye cikin ɗaki harya fara rage kayan jikinsa yarage daga shi sai dogon wandon shadda sai farar singileti yana kokarin cire dogon wandon ni kuma nayi sallama na shuga kai tsaye, jin sallamata yasa ya juyo yana kallona yaɗan ɓata rai yana cewa "Banace ki daina shugomin ɗaki kai tsaye haka ba, kina fara neman izini tukunna" nidai bance masa komaiba na zauna gefan gado ina cewa "Uncle wai maiyasa bazaka maida Zainaba ɗakintaba kodan Ameera ma dake tsakaninku" ɓata rai yayi yana kallona ya ce "Kintaɓa ganin inda mutum yazauna da makiyinsa" turo baki gaba nayi ina cewa "Tayaya masoyi zai koma makiyi baka sonta daman ka aureta harda yara" zama yayi nesa dani kaɗan yadafe kansa yana magana.
"Bantaɓa son Zainaba ba, Mahaifinta wan mahaifi nane shiya ɗauramin aure da ita nazauna da'ita zaman