Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 10
faɗamin nasaka" taɓe baki nayi ina juyawa yaya baya na ce "Daman zai faɗi haka mana tunda yasan yariga yagama da rayuwata, yarabani da farin cikina"mirmushi Yaya tayi ta futa daga ɗakin, tana aikawa da Su'ad harara Wasa wasa sai gashi yau alhamis saura kwana biyu ɗaurin aurena da Fahad har sannan bansakejin ɗuriyar Fu'ad inata dai saka idanu zuwansa tunda yace zai zo ɗaurin auranmu nasan tabbas zaizo ɗin, ba wani taro za'ayi sosai ba kuma ma ɗaurin auran a karaye ne shiyasa tun ranar juma'a da yamma Mami dasu yaya fatima sai wasu matan yayun ummi suka wuce karaye. Da yamma ina zaune nida fadila yar wan ummice kawata ce sosai tun yarinta haka kawai nakejin faɗuwar gaba wacce narasa ta maice na ɗora kaina saman kujera ina jiyo Fadila tana waya dasu Mami kamar daga sama naji kamshin turaransa ban buɗe idona ba har sanda naji sallamar Ankul wanda ko tantama babu nasan tare suke da Fu'ad, ilaiko muryarshi najiyo yana gaisawa da Ummi data futo daga ɗakinta, muryarsa fes kamar bayada wata damuwa, banbuɗe idonaba har saida na tabbatar da sunbar falon zuwa sashin Ankul sannan na buɗe na ɗauki wayata na shuge ɗakina inajin yanda kirjina da kaina suke bugawa "Ameen maiyasa maiyasa zakazo ayanzu so kake ka hanani karasa biyayyar danake shirin yiwa mahaifina kanason tarwatsa zuciyata ne" kwanciya nayi lamo har sanda naji wayata tana kara koda bansan wake kiranba amma na tabbata Mami ce dan ring ɗinta daban yake a wayana "Dota kinci abinci kuwa" "E!" nabata amsa ina sauraron abinda zatace. "kaiwa Ankul wayanki zamuyi magana na kira tasa baya shuga ko baidawo ba?" Inama zan iya yiwa Mami karya danace mata bai dawo ba, amma bazan iya ba dole na mike nabi hanyar zuwa ɗakinsa, da sallama na shuga suna zaune su biyu da'alama magana suke mai mahimmanci ganin yanda hannunsu yake sakale cikin na juna, banko kalli inda Fu'ad yake ba namikawa Ankul waya nace "Mami ke kiranka, bansan maita gaya masa ba nidai ina tsaye naga ya fuce da sauri ko wayar tawa bai bani ba, na fara tafiya zanbar ɗakin naji Fu'ad ya ruko hannuna, na juya ina kallonsa hawaye na zarya a fuskata na tausayinsa ganin yanda ya zabge lokaci ɗaya kamar wanda yai jinya banyi aune ba kawai naji na fashe da kuka hannu yasa ya toshe bakina murya kasa kasa Yace "Princess rufa mana asiri so kike Ankul ɗinki ya jiyomu" da sauri yasa hannunsa a cikin jakarsa ya ciro karamin akwati mai ɗan karan kyau yasakamin a hannuna ya koma saman gado ya kwanta ni kuma na futa daga ɗakin da sauri, banga Ankul ba da'alama baya gidan. Ankul kai tsaye gidan Baban su Zainaba ya wuce, har ɗakin baban yashuga yazauna yana gaida Baban dake masa wani kallo kamar zai kai masa duka. Yace "Yanzu gobene ɗaurin auranka amma ka kasa zuwa ka gayamin sai yayarka ce take gayamin saboda bakuda zumunchi kun rainani ko saboda ni banida kuɗi, to bazan wakilceka ba kaje ka nemi wani bani ba" taɓe baki Fahad yayi tareda mikewa ya ajje masa ledar ɗinkin da Mami tace yakawowa Baban sannan yace "Badamuwa Baba inma bakaje ba bazan rasa wanda zai wakilceni ba barema da kaina zan iya karɓarwa kaina aure" yana gama faɗar haka yafuce daga ɗakin, dai dai sannan Zainaba tashugo ɗakin a ruɗe ita bata taɓa jin zancan auran ba sai yanzu innarta ke sanar mata, zubewa tayi gaban baban tana rusar kuka "Wallahi baba ka cuceni kaine kayi silar rabani da Fahad gashi yanzu inaji ina gani zaiyi wani auran ka kasa taɓuka komai😰kilama tazo ta haifi namiji shi kenan dukiyar da muka sakawa rai tabar tamu" Dariya Baba yayi kamar wani sabon kamu ya zira hannunsa a aljihu yafuto da wani kullin magani yana nuna mata yace "Kalli wanan ɗazu na samosa a wajan wani malami badai gobene ɗaurin auran ba to yanda aka kaimasa amarya haka za'a ɗakkota kedai ki zubamin idanu kawai inada abinda nake kullawa" Sosai Zainaba take murna dajin maganar da Baban yafaɗa hakan yasa ta koma ɗakinta zuciyarta fes da farin ciki. *RANA BATA KARYA* Tun sassafe samarin gidanmu suketa shirin tafiya karaye dan shaida ɗaurin auran Aminatu da Fahad, sosai Fahad yake cikin farin ciki marar musaltuwa kallo ɗaya zakayi masa ka gano farin cikin dayake ciki, yana sanye cikin Fara kal ɗin shadda yasha malum malum shugarsa shida Jabeer iri ɗaya ce, ko'ina ka hangosa baki buɗe sai zuba murmushi yake duk sun shirya Fu'ad kawai suke jira yagama shiryawa su wuce, Tsab yagama shirinsa yafuto yana gyara zaman rawaninsa suka jero shida Fahad zuwa wajan da motocin dazasu shuga suke. Ina tsaye baki window ina leka compound burina kawai na saka sa a idona nai masa kallo na karshe, irin kallon danasan har abada bazan sake masa irin kallon ba. Da sarsarfa yake tahowa kasancewar su Fahad sunyi masa nisa dan harsun shuga mota shi ya tsaya amsa waya, binsa nake da kallo yanda yayi kyau cikin bakar shadda ya ɗora malum malum ta farar shadda wacce akayiwa aiki a gaban rigar da bakin zare, rawaninsa da takalminsa harma da agogon fatar dake hannunsa duk bakake ne, kamar wanda akace ya juyo muka haɗa ido cak ya tsaya yanamin murmishi tareda ɗagomin hannu yaci gaba da tafiya, murmushin da nakejin har abada bazan taɓa mantawa dashi ba kasancewarsa na karshe da yayimin ina kallo ya shuga motarsa wani yaja wanda nake zaton tare sukazo saboda kayan gidan sarauta dana hango a jikinsa da'alama dogari ne,komawa nayi na zauna gefan gado tareda jan tagumi, ina nan zaune har barci ya ɗaukeni ban sani ba saidai farkawa nayi naji gidan yakaraɗe da hayaniya na buɗa ido da sauri na sakko daga gado dai dai da shugowar Fadila tana murna da faɗin yarinya bani tukwaici nagaya maki wata magana...✍️ 07039793439 [6/4, 7:48 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹 Story and writtin by Mamie Yusuf Daboo🥰 ☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️ Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation MARUBUCIYAR HALIN RAYUWA SOYAYYA DA ZUMUNTA SANYIN IDANIYA AIMANAH YANAYIN RAYUWA AND NOW KUKAN ZUCIYA *Na gaisheku ƴan group ɗin KUKAN ZUCIYA comment ɗinku na sani nishaɗi wannan page ɗin gaba ɗaya nakune kuji daɗinku* "Wanne abu zaki gaya min da har saina baki tukwici nasan dai cewa zaki an ɗaura min aure da Fahad koba haka zaki faɗa ba" ban jira Fadila ta ce komai ba na faɗa bathroom na kunna famfo ruwa na zuba na fashe da matsanancin kuka "Shikenan shikenan yanzu na zama mallakin Uncle haba kaddara mai yasa zaki mana haka maiyasa zaki rabani da farin cikina wayyo Allah wayyo zuciyata wayyo Ameen" ta karasa faɗa da karfi tareda nemar waje na zauna na fashe da matsanancin kukan takaicin rashin Prince Ameen, Mami gaba ɗaya hankalinta na gida hakan yasa ana gama ɗaurin aure itada Momy matar wan Ummi suka juyo gida, Ba wani shagalin biki akai ba sabida yanda bikin yazo ba shiri ga kuma rasuwar Daddy dako wata biyu bai yi ba, da mangariba Mami da sauran tsirarun ƴan uwa suka mika ni gidan Fahad, gidan da nasa a raina zan tabbata ina Kukan Zuciya a cikinsa, basu wani jima ba aka tafi aka barni daga ni sai halina tunda muka shiga gidan nake kuka ta cikin mayafin daya lulluɓe min duka jikina basu jima da tafiya ba uncle ya shigo, sallamar dayai tayi dai dai da bugawar zuciyata wanda yai sanadin dana kuma fashewa da kuka ya zauna kusa dani ya buɗe mayafin daya lulluɓe ni yana murmushi saidai annurin fuskarsa lokaci ɗaya ya kau, ya saki mayafin jiki sanyaye, bai cemin uffan ba haka nima bance masa, nadai lura jikin Uncle yai matukat sanyi ganin ya fita yasa na kwanta kan gadon ina kuka sosai, Fahad mai saukin hali kullum kalaman lallashi yake bina dashi musamman ganin naki sakin jiki da shi, kyautatawar Uncle a gareni yasa nabar kukan fili na rashin masoyi na koma kukan zuciya, Uncle na matukar kokari sosai ganin ya kwantar min da hankali komai na gida shi yake yi tun bana sakin jiki da shi harna ware na saki jiki muka koma kamar da sanda muna gida, har sannan mikin son Ameen Fu'ad na nan ɓoye cikin zuciyata nakan tina dashi a kullum nakan kuma so nasan a wanne hali yake yanzu ina yawan ɗaukar wayar Uncle a ɓoye nayita kallon hoton Fu'ad ina kukan zuciya wani bin sai nayi kamar zan kira lambar sa sai kuma na tina haramcin hakan na ajje wayar na ɓuya a ɗaki nai kuka sosai tareda addu'a Allah ya cire min sonsa a zuciyata, sanda hutun da aka bawa Uncle a wajan aiki ya kare ya koma aiki randa yatafi sai naji gidan shuru kewar gida ta kamani gashi muna hutun school, Zaune suke gaban malam na gangare wanda yasha uban rawani da malum malum kamar malamin gaske, Zainaba tana kuka take cewa "Dan Allah malam ka taimakamin inason mijina, gashi ya sakeni har saki uku, ya auri wata, sonake yasaketa yazo yamaidani acusa masa tsanarta sosai yaji nan duniya ba warda ya tsana sama da ita ya korata gidansu da takardar saki uku" malam ya zana wata kasa dake gabansa ya girgiza kai ya ce "Auran nan babu rabuwa aciki duk wanda yace zaija to komai zai iya faruwa dashi sannan kema babu sauran zama ke dashi sai dai kizaɓi abinda kike so bayan wannan" "Malam ka taimakeni!" Ungo wannan yamika mata wani kullin magani yace "Ki zuba sa a inda kika tabbatar zai taka koya tsallaka, inhar kikayi haka to ba abunda zai iya yiwa matar tasa zai zama fanko awajanta ita kuma zata kasa jurewa harta kai ga ta nemi saki, bayan yasaketan kizo ki gayamin zansan yanda za'ayi sai'a maida auran naku" cikeda murna tabasa kuɗin daya butaka ita kuma ta dawo gida ta tisa baba agaba akan ya kira Fahad yace yana son ganinsa yanzu, lokacin Uncle na shirin barin office dan haka ya shaida ma Baba da gashi nan zuwa yanzu insha Allah, Da gudu Zainaba tashugo cikin gidan tun ɗazu tana tsaye kofar gida tana jiran zuwan Fahad tun daga nesa data hango motarsa ta dawo gidan ta kunce kullin maganin daga gefan zaninta ta zuba sa a kofar ɗakin Baba, mahaifiyarta data futo daga ɗakinta tabita da kallon tuhuma "Zainaba mai kikeyi haka a kofar ɗaki ba sallamar Fahad nakeji ba, waima maine wannan a hannunku" Baba daya leko daga ɗakinsa yace. "Kefa mairo kin fiya saka ido ina ruwanki da maine a hannunta ke Zainabu cewa Fahad yashugo ina ciki" Fahad yashugo da sallama yana gaida Innah mairo fuskarta cikeda fara'a take amsa masa gaisuwar, yana shuga ɗakin Baba Zainaba tayi wani tsalle tana murna harda taka rawa, a kasa ya zauna yana gaida Baba, ta inda yake shuga bata nan yake futa ba faɗa yake sosai "Yanzu saboda rashin zumunchi irin naku ace kayan abinci ma bazaku iya saimin ba saina roka kuna kallon halin danake ciki aikima ya gagareni amma bazaku rinka tausayamin ba wannan ba halin ubanku bane, ubanku mutumin kirki amma kaida yar uwarka mahaifiyarku tashuga tsakani na da ku" Fahad dariya ma abin yabasa daya tuna ko karshan wata saida Mami tagaya masa ta turawa Baba kayan abinci, shine yanzu zai zo yana masa mita "Ayi hakuri baba ban zaci wanda Mami takawo harya kare ba yanzu bari naje zan aiko maka dasu" "Basai ka aiko ba kabani kuɗin kawai nasiya da kaina" mikewa Fahad yayi yana murmushi yafuta, mota yaje ya ɗebo kuɗi ya kawo wa Baban sannan yafuta, har sannan Zainaba tana zaune kofar ɗakin daɗi ya kume ta ganin har sau biyu yana taka maganin. Yau sosai nakejin nishaɗi hakan yasa da wuri na kammala abinda zanyi nai wanka ina zaune gaban madubi na gama tsantsara kwanliya wacce najima banyi irinta ba tun kafin rasuwar Daddyn mu, doguwar rigar material nasa wacce takama jikina tamin kyau sosai na feshe jikina da turere mai kamshi, na gyara gashina dayasha kalolin mayuka sai kamshi yake da kyalli, ban ɗaura ɗan kwalinba na ajjesa saman kujera ina kallon agogo karfe huɗu saura kwata, mamaki nake maiya hana Ankul dawowa bayan yacemin karfe biyu zai dawo zama nayi na ɗakko wayata na kunna data nahau online hira muke da Yaya Fatima kiran Fahad yashugo wayan nawa da sauri na ɗaga cikeda shagwaɓa Nace "Shine kayi zamanka har yanzu baka dawo ba bayan kace karfe biyu zaka dawo" ina jiyo sanda yai murmushi mai sauti "Kina son nadawo ne, inna dawo maizan samu mai kika tanadarmin?" "Na tanadar maka da komai,kuma ni tsoro nakeji nafison innayi motsi na ganka kusa dani hakan yana faranta min rai" "Da gaske to gani nan a hanya" kashe wayan yayi saida yayi sallar La'asar a masallaci dake ɗan nesa da gidansa kaɗan sanna ya karasa gida. Horn ɗin motarsa dana jiyo yasa na futa da sauri na buɗe masa get,yashugo da motar na maida gate ɗin na rufe na karaso wajan motar na buɗe masa murfin motar, yafuto yana dariya tareda sakani cikin jikinsa ya sumbatar bakina yace "Kinyi kyau sosai besty bakiga yanda doguwan rigan nan tai maki kyau ba" sosai naji daɗin yabon da yai min hakan yasa na kuma shugewa jikinsa ahaka muka jera zuwa ciki, saida nakaisa har ɗakinsa na haɗa masa ruwan wanka ya shuga yana tsokanata inzo na tayasa wanka, na futo daga ɗakin da gudu ina dariya, Allah yasani kunyarsa nakeji banajin akwai wata rana da zatazo wacce zan iya tayasa wanka, ina nan falo zaune ya futa sanye da wando 3 kwata da farar t shart mara nauyi, kusa dani ya zauna ya jawoni jikinsa yana shafa gashin kaina "Waini yaushe za'a daina jin kunyata saboda Allah ace wankama har yanzu da kaina nake baza'arinka yimin ba" rufe idona nayi alamar jin kunya ina dariya kasa kasa nace "Nifa bazan iya ganinka ba kaya ba ajikinka ai kunya zanji" dafe baki yayi yana dariya kasa kasa "Ok yanzu nagane laifin nawa ne, aiko yazama wajibi yau saina cire wannan kunyar dake tsakaninmu Allah yakaimu dare" murmushi kurum nayi tareda mikewa na kawo masa abinci na ajje bisa carfet dan nasan Ankul tun tuni bai fiyason cin abinci a dannig ba, sosai yaci abincin yana tsokanata inata dariya muna nan zaune muna hira har aka kira mangariba yafuta masallaci ni kuma na wuce ɗakina nai alwala. Ankul bai shugo gidan sai wajan karfe takwas da rabi lokacin har nayi shirin kwanciya bayan nayi wanka na saka night wear na zuba humra sai tashin kamshi nake banji shugowar sa ba kasancewar harna fara barci sai mutum naji cikin bargo ya haɗe jikina da nasa, na buɗe baki ina shirin yin ihu ya saurin haɗe bakina da nasa, yanda yake kissing ɗina yasa jikina yaɗauki rawa Sosai yake min wasu kalar abubuwa wanda sam bansan dasu ba, gaba ɗaya yafuta hayyacinsa niko har sannan jikina rawa yake musamma sanda naji yana kokarin shuga jikina sosai nake kuka da rokonsa amma baimasan inayi ba saidai cak ya tsaya yana maida numfashi lokacin dayai kokarin shuga jikina J ɗinsa yaga tai wani irin kankancewa da sauri ya janye jikinsa daga jikina ya kwanta gefena yana maida numfashi, ban fuskanci komai saima zato danai ko rokonsa danake ne yasa ya tausayamin yafasa abinda yai niyya amma yanda naga yana numfashi yasa na kunna light da sauri tausayinsa ya kamani ganin yanda ya haɗa gumi aruɗe nace "Ankul lafiya maiya sameka" janyoni yayi jikinsa tsawon lokaci yana cikin wani yanayi yanda idanunsa sukayi ja yasa na ruɗe na soma kuka, "Ankul na amince gani kayi abinda kai niyya dani inda zaka dawo dai dai amma ni tsoro...hannunsa yasa saman laɓɓana alamar nayi shuru, hawaye naga sun zuba daga idanunsa yace "Bazan iya maki komai ba Su'ad bansan iya tsawon lokacin dana ɗaukaba batare dana gano cewar bani da cikakkiyar lafiya ba nidai nasan har sanda muka rabu da Zainaba lafiya ta kalau" sam ban gane inda zancan nasa ya dosa ba hakan yasa gaba ɗaya hankalina ya kuma tashi aruɗe nace "Bakada lafiya Ankul tashi to muje hospital kona kira Dr Hafis yazo ya duba ka" "Ba rashin lafiyar jiki nake nufi ba kalli nan" yafaɗi haka yana nunamin J ɗinsa, kallon inda ya nunamin ɗin nayi da sauri na runtse idona saboda gamon danayi, Fahad yana murmushi yace "Buɗe idonki ki kalleni ki gane rashin lafiyar danake nufi ya zamuyi" yanzu kam nagano abinda yake nufi "mu gayawa Mami nasan zata samo maka magani" "A'a karmu gayawa kowa mubar wannan sirrinmu ne, zan nemi magani bansan da matsalar bama da tuni nasamo magani, wannan yazama sirri nidake karki gayawa kowa dan Allah" "Haba Ankul tayaya zan iya gayawa wani wannan matsalar ai tamuce dagani sai kai" rungumoni yayi jikinsa har barci ya ɗaukeni baiyi barci. Fahad dayaga Su'ad tayi barci tashi yayi yai wanka ya gyara jikinsa ya ɗakko system ɗinsa ya soma binciken magani daya dace ya sha. Tun sanyin safiyar lahdi yaketa shirya kayansa cikin trabiling bag fuskarshi fal da damuwa ga kansa dake masifar sara masa saboda damuwa idanunsa sunyi jawur sosai kamar wanda yai kuka,kofa yabi da kallo ganin tayi motsi cak ya tsaya yana bin Khadija data shigo ta zaune kan sofa ta fashe da kuka "Yaya Prince yanzuma tafiya zaka kuma yi ka barni ni ɗaya?" Khady ta faɗa cikin kuka sosai, rigar hannunsa ya jefa saman bed da sauri ya tsugunna gaban Khady yasaka hannunsa cikin nata yanaji inama shine yake wannan kukan inama shima zai iya kukan nan ko zuciyarsa zata masa daɗi "Khady yi shuru dan Allah ba laifina bane laifin Abie ne na gaya masa bana son tafiyar nan amma ya kafe dole wai saina fara aiki a asibitin legus nima zanso ace an barni nan na rinka ganinki ko yaushe amma insha Allah na maki alkawari zan rinka zuwa duk karshan mako please Khady ki daina kukan nan" cikin kuka Khady ta gyaɗa kanta tana bin ɗan uwan nata da kallon tausayin rasa masoyiya da yai, Khady da Juhaina daketa rawar kai tare suka raka Prince har filin jirgin sama saida yatafi sannnan suka dawo gida, a legos gida da motar hawa asibitin dazai fara aiki dasu suka basa kai tsaye yafara aikinsa ba ruwansa da sabgar kowa indai ba hospital zai je ba to bazaka taɓa ganinsa a waje ba kullum yana gida kamar mace, Sauri sauri yake shirin futa bayason makara saboda karfe tara yanada feshen ɗin dazaiwa c s, takwas saura ya shuga hospital ɗin tun daga resepsion yake amsa gaisuwar ma'aikata yanda suke basa girma kai kace shine mai asibitin a mutumche yake amsa gaisuwar saidai fuskar nan tasa tamke ba ko ɗigon fara'a haka yake haka suka saba ganinnsa shiyasa basu wani damu ba. Bai tsaya a ko'ina ba sai kofar katon office ɗinsa tamkar falon wani gidan saida ya zauna saman kujera ya sauke ajjiyar zuciya tareda cusa hannuwansa duka biyun cikin gashin kansa yana fuzzar da iska mai zafi daga bakinsa, shirye shiryan shuga tiyata yafara yi ta hanyar canza kayan jikinsa ya shuga ɗakin tiyatan. Anty Jameela na murmushi ta damkawa Suwaiba rafas ɗi nyan dubu dubu guda uku "Ga somin taɓin kuɗin aikinki nan bazan baki sauran ba sai aiki ya kammala" Murmushi Suwaiba tayi daɗi takeji sosai a ranta da ganin wannan uban kuɗin wai duk nata ne hakan yasa tace "Bakida damuwa Hajiya aiki kamar angama sane gobe insha Allah tun safe zanwa garin legas tsinke na ruga naga inda yake da gidan dayake zaune abu ɗaya zaki bani makullin gidan" "Au kinga na manta wallahi gashi" tamika mata makullin bayan ta ɗakkosa daga jakarta, mikewa Suwaiba tayi tana wani juyi kamar tana gaban mijinta🤭dariya Anty Jameela tayi bayan taga futar Suwaiba daga ɗakin, harda tsallanta na murna gobe iwar haka burinta ya cika an ɓatawa Fu'ad suna shida sarautar saidai yagani anayi💃 Fu'ad tunda yashuga asibiti bai futo ba sai tara na dare gaba ɗaya agajiye yake jin kansa, ta restaurent ya biya yayi take away sannan ya wuce gida wanka yafara yi saboda gajiyar daya kwaso, jiyake inama yanada mata tabbas yau da saidai su raba gajiyar nan, abincin yaci yaɗan hau online bai jima ba yafara jin barci haka yasa ya kashe datan ya wuce bedroom. Dare yayi sosai ahankali take juya kanta cikin barci kafin ta farka a firgice tana salati, salatin datayi shiya tashi mai martaba dake kusa da'ita yana barci, a kiɗime ya farka yana tambayar "Asiya lafiya naganki haka maiya sameki wani abune ya faru?" "Lafiya kalau ranka ya daɗe amma wani mafarki nayi, hankalina yatashi anya ko One boy yana lafiya" Mai martaba maida kansa yayi ya kwanta tareda lumshe ido kana yabuɗesu akan matar tasa "Lafiya kalau ɗanki yake ɗazuma saida mukayi waya dashi lokacin yana hospital yace bai koma gida ba" Umma sakkowa tayi daga kan gadon ta shuge toleit mai martaba yabita da kallo yana sakejin son matar tasa uwar gidansa yana sake shuga ransa musamman ganin yanda ta damu da lamarin Fu'ad ko yaushe batada magana saita Ameen yayi kaza ko yaranta data haifa bayajin tana yiwa so kamar yanda takewa Fu'ad, da Khadija duk da sauran matansa suna zargin son datakewa Fu'ad badan Allah bane dan tana ganin nan gaba shine sarki shiyasa take sonsa, shidai yasani ba haka bane son datakewa Fu'ad tun yana yarone sau tari Ummu kafin ta rasu tasha bata Fu'ad ya jima awajanta shiyasa suka shaku sosai, Umma tafuto ta shimfiɗa dadduma ta tayar da sallah tana rokon Allah yakare mata ɗanta ya nesantashi daga abinda tayi mafarkin yasamesa yanzu, sanda ta gama addu'o'inta ta shafa ta koma ta kwanta sannan ta lalubi wayarta taga karfe 03:44 am lambar Fu'ad ta buga tajima tana ring sannan yaɗaga aɗan tsorace yake tambayar Umman lafiya "Lafiya kalau One boy kawai cewa nayi bari na tashi ɗana ya ribaci daren nan da koda raka'a biyu ce ta nafila" dirowa yayi daga kan gadon yana murmushi yace "Na gode Ummana na mike kuwa alwala ma zanyi nayita sallah daga nan har safiya ina rokon Allah yakarawa Ummana lafiya da nisan kwana tayita bani kulawa har zuwa taga jikokina" dariya Umma tayi ta kashe wayar ta shige jikin mijinta tana murmushi, Fu'ad bai koma barci ba sai bayan sallar asuba daya dawo daga masallaci ya koma barci bayan yayi karatun kur'ani izifi uku yai azkhar sannan yakoma ya kwanta,dan yau bazai shuga hospital ba sai huɗu na yamma. Karfe shida dai dai jirginsu Suwaiba ya sauka a garin legos ikko ikon Allah cunkus ɗakin tsumma😹itada kawarta ne hotal suka kama suka ɗan huta bayan sallar mangariba Suwaiba ta wuce gidan Fu'ad, ta tarar baya nan hakan yasa tasa makulli ta buɗe karamar kofar shuga gidan ta shuge ciki ba kunya, ɗakuna biyu ta gani cikin falon ta murɗa handling na kofa ɗayar tajita a rufe hakan yasa ta nufi ɗayar tana murɗawa ta buɗe ta shuga, wanka tayi ta shirya cikin wasu shegun kaya kanana masu masifar kyau da fusgar hankali, ta feshe jikinta da kalolin turarukanta da wanda Anty Jameela tabata wanda ta karɓo daga wajan boka🤭 Takwas dai dai Fu'ad yashugo gidan bakinsa ɗaukeda addu'ar shuga gida harda sallamarsa kamar wanda yabar mutum a gidan, ajje ledan abincinsa yayi saman kujera yana shirin shuga ɗakinsa yaji an rungumosa ta baya ba karamin tsorata yayi ba saboda shidai yasan shi kaɗaine agidan, bai ankare ba yaji an soma shafa jikinsa ana kokarin ɗora hannu kan J ɗinsa, afusace ya jiyo yana karanta ayatul kursiyyu domin azatonsa gamo yayi saidai wazai gani inba gizo idanunsa sukai masa ba Suwaibace wannan a fusacen dayake ya danki wuyanta yana faɗin "Malama maiya kawoki gidana maiya sake dawo dake rayuwata bayan yaudarar da kikamin saboda kin maidani sha sha sha shine yanzuma kika dawo ki yaudare ni?", Suwaiba da idanunta suka furfuto tafara hango mutuwa saboda yanda ya rike mata makogwaro tace "Ka sakeni zangaya maka wanda ya turoni" bai saketanba saima kara rike mata makogwaro dayai idanunta dayaga ya firfito tana kakarin mutuwa yasa ya wurgata ta bugu da kujera tasaki ihu bai tausaya mata ba yasa kafa yatake hannunta "Zaki gayamin ko saina haɗaki da hukuma" kanta take girgizawa tama kasa magana sabida azabar da hannunta da kanta keyi,wayansa ya ɗakko ganin yana shirin kiran yan sanda yasa

Chapter 5 of 10