nawa kike da zaki dinga nunawa mutane isa?, badan Haseem yace yana sonki ba, wlhi baza'ayi miki aure yanzu ba"
Nidai ina jinta uffan ban ceba, taci gaba da cewa "karki sake neman wani abu a gurina, nima na cire hannu a lamuranki, kuma wlhi koda wasa kika sanarwa da yayanki maganar bakyason Haseem sai nayi maganinki"
Ashe Uncle yana laɓe a bakin ƙofa yana jinta,
Washe gari da ta fita anguwa ya kirani yacemin "in kwantar da hankalina anty Karima mutumce da inhar ta ƙwallafa rai a abu sai ta sameshi, shikuma bazai bari na auri Haseem ba, insha Allah gobe iyayen Zahradden zasu zo tambaya tare da dukiyar aure, in nuna bansan komai akai ba zeji da ita"
"Toh" nace masa idanuna na tsiyayar ƙwallah,
"Tasneem bawai kin isa aure bane, kawai ina son kuɓutar dake daga wannan gidanne nasan koda ina lura da wasu abubuwan bayan na dawo, idan na fita bansan abinda zatayi miki ba"
"Daga nan ya miƙe yabarni a parlo inata kuka"
Washe gari, ina ɗakina naji Uncle yana sanar mata da cewar "iyayen saurayina suna hanya tayi musu girki"
Cikin rashin fahimta tace "bata fahimci abinda yake nufi ba, dama zugani yakeyi akan kar inso Haseem, shi kenan ta zuba mana ido, abinci ne bazatayi ba yayi abinda zeyi"
Kasancewarsa mai haƙuri banji yace mata komai ba, sai ma ficewa da yayi,
Can anjima na fito ina wanke-wanke, naga ya shigo da babbar leda, ashe abinci ya siyo a restaurant ya nemi kula ya juye ya Kai ɗakinsa,
Dama yanada fridge ya ɗibo kayan sha ya ajiye musu.
Ina kallonsa ta labule, tunda ba mai duhu bane,
"Allah Sarki iyayena"
Na faɗa lokacin da hawaye ke bin fuskata.
Abinda zai baki mamaki, ta ƙofae baya suka shigo, har sukayi maganganu su suka gama babu wanda ya sani, ashe harda ƙanin kakarmu da abokin ƙanin kakarmu Uncle ya kirawo akayi maganar.
Fitowar Uncle ya tabbatar min da sun tafi,
Tun daga ranar na fara fuskantar matsaloli sosai, saboda wlhi ko abincin kirki bana samu, gashi kakannina duka sun rasu, sai dai ta wajen uwa, itace a raye, mahaifin Ummana ya rasu,
Ranar da Anty Karima ta tafi anguwa na samu Uncle nace "masa, ya mayar dani gurin Hajiya, kakata mahaifiyarsu kenan, yacemin inyi haƙuri lokaci kaɗan ya rage"
Kuka nasa masa, dole ya tausayamin washe gari, yasa na tattara komai nawa na koma can da zama, ranar nayi bacci sosai dan babu masifa, ita farinciki tadingayi da zuwana
Dama Uncle ya sanar mata da maganar saka ranar biki da akayi sati Uku, Hajiya ta dingayi masa masifa akan ya gaji dani ne da ake shirin aurar dani yanzu ba a bari nayi karatu ba?"
Haƙuri ya bata, daga nan bata sake cewa komai ba.
"Allah Sarki Tasneem kice kinga uqubar rayuwa, bari mu ɗora girki naga har ƙarfe ɗaya saura 12:45pm"
Back to story 🤞
Sosai tausayin Huda ya kama Amani, sosai taji zafin abinda Ummanta tayi Mata, amma ta fara tunanin Anya uwarta ce kuwa?
Suna isowa gida, Aseela ta riƙewa Huda hannu suka wuce part ɗinsu, Amani kuma ta ɗauki jakar kayan, Mahabob yaji daɗin kulawar da suke nuna mata.
Su kuma su Abba da Batool suka wuce nasu part ɗin, Inaya tana murnar ganin Huda tace "yau kam bazata kwana a gurinsu Abba ba"
Lokacin da suka dawo ƙarfe 5:30pm tayi, Abba na zaune a parlo ya danna waya ya kira Amani, cikin bada umarni yace "Please ku dafa indomie ko kusha tea, na aiko Mahabob da bredi"
Dayake suna zumuɗi babu wanda yace komai.
Sosai Batool taji daɗin hutar da ita da Abba yayi, ta taho kusa dashi tare da zame ɗankwalin kanta, ƙananun kitsonta suka baiyyana,
A hankali yakai hannu yana shafa su, cikin kasalalliyar murya yace "yau inaso in kasance da matata"
Abinka da mai zumuɗi ko ince yarinta, sai cewa "tayi bakada matsala" ko wayewa ce oho.
Rungume da juna suka wuce bedroom, kafin sai da ta tabbatar da ta kulle ko ina sannan, da sauri-sauri ya rabata da kayan jikinta, shima haka, tare da rage hasken glob ɗin ɗakin, sosai yake murza mata bre hankalinsa kwance, har wani mammatsasu yakeyi tana nishi ita Kuma, a kunne ta raɗa masa magana,
"Inason yin magana dakai"
"Haba hajiyata kome kikeso ƙofa a buɗe take"
Cikin kissa da shagoɓa Batool tace "uhm dama inason in roƙi alfarma ne, naga Mahabob yarone mai biyayya, wlhi nayi masa sha'awar auren ƙanwata da ta gama karatu a Dubai, satinan har ta dawo gida"
Cikin gamsuwa da maganar tata, Abba yace "haba ai kema momynsa ce, baki da matsala indai akan wannan ne an gama, nima ai samunki da nayi Mai tarbiya ga biyayya, wlhi ba k'aramin daɗi naji ba"
Sosai Batool tayi murna saboda koba komai, kamar inda mamynta ta faɗa zasuci gado mai tsoka, inhar suka zamo su biyu a familyn Alhji Auwal.
Naso yi muku sau biyu, wlhi hakan bata samu ba, masu comments Nagode wlhi kuna raina Kunyi yawa bare in lissafoku ɗaya-bayan ɗaya, wannan saƙo ne ga duk wani masoyina meyin comments.
Mom Islam
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
43-44
Kwanansu biyar da zuwa Algeria, anyi aiki cikin sa'a,
A Koda yaushe Hajiya ƙarama takan keɓe kanta ta dinga gayawa Allah halin da Iffat ɗin take ciki, duk da har yanzu bata fara magana ba, amma alamomin sauƙi sunata samuwa, su da kansu likitocin suka gayawa dady ya haɗa mata dana islamic.
Kamar inda saurayin Juwairiyya Abdul-Alee yayi mata alƙawarin zuwa, sai gashi da daddare, zama yayi ƙofar gidansu kan dakali kafin ya kirata yace "ya iso gashi a ƙofar gidansu"
Juwairiyya jiki na rawa ta fito, harda wani karairaya, kallon gefenta dataga mutum tayi kafin tace "malam lafiya kazo ka zauna mana anan kalan ka shafa mana talauci?"
Abdul-Alee ya miƙe tare da cewa "haba Juwairiyya nine da muka haɗu dake ɗazu, dama motar abokina ne, na aro dan Allah karkice nayi miki ƙaryar arziki"
Tunda ya fara magana Juwairiyya ta ke kallonsa cike da raini tace "mtsw asara ance maka ni ajinka ce?, ka tambayi kaf samarin anguwarnan sunana matar manya, kul karka sake zuwa gidannan dama kaso ka yaudareni ne?"
Jiki a sanyaye ya miƙe har tana tofa masa miyau,
Ta shige gida fuuu kamar zata tashi sama.
Cikin takunsa na nutsuwa ya ƙarasa jikin mota tare da kallon Mubashir, suna haɗa ido, Mubashir ya galla masa harara tare da cewa "wlhi kai wawa ne, ina ganin wulaƙancin da yarinyar tayi maka amma bazaka fasa zuwa gurin ta ba?"
Prince Abdul yace "wlhi tallahi Allah ya jarabceni da soyayyar wannan yarinyar, amma daga yau na haƙura insha Allah bazan sake zuwa ba"
"Oho wlhi kaci gaba da zuwa"
Daga nan suka shiga mota suka wuce.
Niko nace Allah sarki kwalli da turare ya kamo miki Prince kin koreshi.
Cikin ɓacin rai taje ta ɗibi gaushi tasa magani tayi hayaƙi, kana ta ɗauki turaren malam tasa tare da tozali, ta sauya kaya ta fice, a cewarta yau za'ayita ta ƙare.
Kai tsaye wata anguwar ta masu kuɗi ta nufa, tana tafiya tana sauya salon tafiya, cikin sa'a wata danƙareriyar mota tayi parking a gefenta, Juwairiyya taci gaba da tafiya, bata saurari taga waye a ciki ba,
Cikin ɗaga murya mutumin yace "ƴan mata dan Allah ki tsaya"
Cike da jan aji ta juyo tare da kallon motar, sbda bata hango mamallakin motar Ba, tunda a gaba take shikuma yana baya.
A hankali ta dawo gurin motar, da sauri ta sake kallonsa, a shekaru zeyi 40yrs amma sai kace ba wani babba ba, fuskarsa ce zata nuna maka yawan shekarunsa, "da farko dai sunana Alhji Al'amin, ina zaune a garin Abuja, bana zama a Nigeria nafi zama a Chad, bayan munyi aure zaki iya zaɓar ƙasar da kikeson ki zauna a cikinta Ni bamai takura bane"
Mamallakin motar ya faɗa yana kashe mata ido,
"Masha Allah ni kuma sunana Juwairiyya"
"Am ina fatan zaki amshi soyayyata dan bada wasa nakeyi miki ba, inhar kin amince nanda sati biyu zamuyi aure"
Cikin jin kunya Juwairiyya tace "babu damuwa Allah ya shige mana gaba"
Tana shirin wucewa, ya ciro waya ƙirar I phone 13pro max ya miƙa mata a kwalinta, mamaki ya kamata hannunta har rawa yake, tace "duk wannan nawane?"
Alhji Al'amin yayi murmishi yace "inhar kika zamo matata sai kin riƙe wacce tafi wannan, wlhi har cikin zuciyata nake sonki"
Har ƙasa ta durƙusa tayi masa godiya,
Yace "akwai sim card a ciki idan kika kunna zakiga kirana"
Tace "toh"
Zuciyarta nata rayo mata abubuwa da dama.
"Yanzu ina sauri zanje airport ne wlhi, ga wannan babu yawa, kuɗi ya miƙo mata bandir na dubu ɗaya guda biyu,
Hankalin Juwairiyya ya tashi, ta dinga yi masa godiya,
Har ya yi mata sallama ya wuce bata dena leƙen motar tasa ba, cikin sauri ta nannaɗe kuɗin a mayafi tare da wayar, ta dinga gudu har ta kawo gida.
Tana shigowa taga takalmin babanta, cikin ɗaga murya take cewa "baba ka fito wlhi abin arziƙi ya samu"
Baba ya fito da sauri, sbda a tsakar gida ta zube ta kasa ƙarasawa gurinsa, yana fitowa yayi ido biyu da kuɗaɗe, sbda waya kam besan kuɗinta ba, sai ita da ta sani, bakinsa har yana rawa yace "ƴar baba waye ya baki?"
"Wlhi baba ina fita na haɗu dashi, yace baya zama a Nigeria a ƙasar waje yake zama, kuma yace idan na amince nanda sati biyu zamuyi aure"
Jikin baba na rawa ya tattaro kuɗin yana rungume wa, tare da cewa "kice kin amince harda waya ya baki?"
"Eh wlhi baba bakasan tsadar wayar bane shiyasa baka ɗagata ba"
Baba yayi tsaki yana cewa "yanzu dai tunda hidima yanzu ya fara, mu tafi hotal (Hotel) muci abinci, wlhi ƴan dirama (Drama) suna birgeni idan naga sunacin abinci acan"
"Tabbas baya ka kawo shawara amma dole kasa kayanka na sallah saboda karsu rainamu"
LIBYA
Kamar inda babban likitan ya faɗa yau za'a sallami Mona, yau ɗin aka sallameta, kowa danginsa na zuwa, banda ita da maƙiyinta take gani koda wane lokaci, taji sauƙi sosai sbda tana tafiya amma tana ɗan ɗingishi, shima a hankali zata dena, cewar likitan.
Maƙudan kuɗaɗe Shahazad ya cika sbda ayi masa aiki Urgent.
Da yamma suka dawo gida, lokacin Hajara tana barci a ɗakinta, dan batayi zaton yau zasu dawo ba.
Sai da yaje ɗakin Mona ya kwantar da ita, kafin ya dawo parlo ya nufi ɗakin Hajara "Hajarrr!!!"
Ya faɗa da kakkausar murya, wacce ko a mafarki ta jita sai ta firgita.
Da sauri ta miƙe zaune, tare da ware idanuwanta tana cewa "ya jikin Madam?"
Kallon banza ya watsa mata kafin yace "ki ɗora abinci yanzu, Zarbiyan nake da buƙata akwai time table a sama ki duba da inda ake dafawa"
Zata kuma magana ya fice.
A hankali ta dafe kanta, tare da cewa "gobe insha Allah zan nemi alfarmar dena aiki a wannan gidan, wlhi bazan iya ba, gara in koma gurin Inna ko dusa zamu dingaci muci"
Kafin ta share hawayen da suka kwaranyo mata ta miƙe zuwa kitchen.
Allah ma ya taimaketa ta iya turanci duk da ba sosai bane, amma idan ta karanta tana gane wasu abubuwan.
Yau da wuri, Lulu ta tafi, dan ko ƙarfe 8:am batayi ba, sam taƙi yin brakfast a gida, sbda tace "sauri takeyi,
Gidan ya rage daga jami'an tsaro da ma'aikata sai Ala-Uddin da Hassana, tunda ta gaishe shi ya sanar mata da Black tea zatayi bata sake ganinsa ba,
Bayan ta tafasa shayin ta juye a cup guda biyu, da nasa da nata, already yasan cup ɗinsa, tunda yafi nata kyau, sai da ya tabbatar da ta shiga ɗakinta sannan ya fito cikin sanɗa yaje kitchen tana kallonsa ta window, magani ya jefa a nata kana ya dawo ɗakinsa da gudu,
Yanayin action ɗin da yayi yasa ta zargi akwai abinda yayi, tafito kamar batasan ya shiga ba...!
Insha Allah zanyi muku wani 9:30 insha Allah
Yau ansha hira naji daɗi sosai
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
45-46
Tana ganin ya koma ɗaki taje ta juye nata a gurin wanke-wanke, ta kunna pampo kana ta ɗauraye cup ɗin ta juyo ragowar na Kettle ɗin kana ta fito da cup biyu nata da nashi, shima ta window yake leƙenta har yana taka rawa, burinsa tasha shikuma ya iso gareta, a kan table na parlo ta ajiye coffe ɗin, kafin ta wuce da nashi ɗakinsa.
Da sallama ta shiga, ta sameshi yana sanye da ƙananun kaya, ba kamar inda Lulu ta barshi ba, tare da hannunta ya haɗo cup ɗin da take miƙa masa, kana yace "Haseeaina"
Cikin sanyin murya ta amsa da "na'am"
Makirin murmishi yayi, kafin yace "kin amince da buƙata ta?"
Jikinta na karkarwa tace "nidai kayi haƙuri ka barni in koma garinmu dan Allah na yafe maka duk abinda kayimin"
"Never!!!"
Yana saurin ajiye coffe ɗin,
"Wlhi bazaki koma ƙasarku ba har sai kin amince da ƙudurina, nima inaso burina ya cika akan masarautar mu"
Sam ta gaza fahimtar abinda yake nufi, dole ta zube a gurin tana roƙonsa, ganin yaƙi saurararta yasata cewa "shugabata tanada zafin kishi zata iya kasheni idan ta ganmu tare"
"Sai me? ƙarya ne, ni bazan bari ta gano komai ba, sosai nake samun nutsuwa dake, tun kafin a bani umarnin kusantarki, dan haka ko kinaso ko bakyaso sai na dinga sex dake koda wane lokaci"
A firgice Hassana ta miƙe tare da juyawa zata fice, da sauri ya fincikota ta faɗo jikinsa, cikin sauri ta kauce tare da sunkuyar dakai, hawaye na ambaliya a fuskarta, sam ta gaza haɗa ido dashi, sbda iya idanuwansa faɗar mata da gaba yakeyi,
Yayi kisa a gaya mata zai sauya mata gida wanda yafi wannan, sai ga Lulu nan, ashe tanata sallama basuji ba, ganin Hassana a durƙushe gaban Ala-Uddin Samir yasata wurga jakar kan gado, tana gyara sumar kanta da ta rufe mata ido, tare da riƙe ƙugu tace "Hub lafiya?"
"Mu Lulu wai dole sai ta tafi gida, naga kina buƙatar zamanta yasa nace "babu inda zata shine taketa kuka"
"Kai Haseeaina, wannan karon bakizo da niyar yin aiki ba, wancan karon ai kinkai shekara ɗaya da rabi, meyafaru kikeson zuwa gida, idan kuɗi ne baki dashi ki bani number account zansa miki"
Har Lulu tayi maganganunta ta gama Hassana ta kasa magana,
Sai ma miƙewa da tayi ta fice da gudu, tayi kuka sosai da ta koma ɗakinta, sbda ta kasa ɗaukar coffe ɗinma ta sha.
Hajara na kammala abincin tasa a faranti mai faɗi fari na tangaras, tare da saka cokula biyu, sbda haka Shahazad ya umarceta tun farkon zuwanta,
Tana haurawa steps gabanta na tsananta faɗuwa,
Batasan takamaiman ɗakin da suke ba, dole ta fara nocking na Mona, cikin sa'a, yace "Yes"
"Na kawo abinci ne"
Hajara ta faɗa tana jiran abinda zece mata,
"Okay"
Ta shigo bakinta ɗauke da sallama, karfa idanunsu ya sarƙe ana juna,
Hajara tai saurin sauke idanuwanta ƙasa, ashe Shahazad yana kallonsu,
Bata jira an bata umarni ba, ta fice.
Shahazad yayi wani irin makirin murmishi,
Jikin Hajara na karkarwa ta ƙarasa ɗakinta, itakam gida take buƙatar zuwa, amma bataga fuskar magana ba, "gashi sai ya dinga yi mata mugun kallo ko meye dalili oho?"
Mona na kwance, duk irin kallon da Shahazad yake yiwa Hajara tana kallonsa, murya wata iri tace "shin Hajar tayi maka wani abunne?"
"Ehhh, tana shiga gonar da ba Tata ba"
Shahazad ya faɗa cikin kakkausar murya.
"Dan Allah ka sassauta mata, tabani labarin batada iyaye, shiyasa ta zaɓi tayi aiki anan"
Shahazad ya shafi gashin kanta, kafin yace "ki kwantar da hankalinki ki ci abinci zamuyi magana zuwa anjima"
Mona ta fashe da kuka tana shure-shure tace "nidai kayi min alƙawari zaka riƙeta cikin aminci?"
A gurinsa Alƙawari ba ƙaramin abu bane mai muhimmanci, idan yayi zaiyi wuya ya saɓa,
Sam yaƙi cewa komai,
Taci gaba da kuka tana ihu,
Tunowa da dokokin asibiti da suka sanya masa, ya sashi saurin kamota ya ɗorata jikinsa kana yace "nayi miki alƙawari inhar kema kikayi min alƙawari"
Batasan Alƙawarin meye yakeda buƙata ba, cikin sauri tace "nayi maka"
Yana shafa gashin jikinta tare da mammatsa mata hannaye yace "Yakamata kisan ni masoyinki ne, inada burin baki farinciki sama da Ni kaina Amma kin kasa fahimtata"
Sosai tayiwa Allah godiyar wannan tambayar da yayi mata, dan ta samu damar tuhumarta iyayenta.
"Ka kawomin iyayena in gansu, nayi maka alƙawarin zan zauna dakai"
Shahazad yai saurin ture ƙafafunta, kana yace "me kikeso ince miki?"
"Dama kinsan zaki jawomin tashin hankali, su suka bani auranki, mahaifinki ne ya damƙamin ke a matsayin mata, nikuma na karɓa"
Da sauri ta tare bakinta, a fili tace "ka kashesu"
A nitse kamar ba kuka takeyi ba, yace "suna raye"
"Yaushe zaka haɗani dasu"
"Ranar Litinin saura kwana uku tunda yau muna Asabar"
Sosai farinciki ya kamata, shiko a halin yanzu yana jin babu daɗi a zuciyarsa.
Da sauri ya miƙe ya koma wani ɗaki can nesa da nata ya ɗaga wayar tafi da gidanka, wanda ya kira yana ɗagawa yace "kasan iyayen Mona?"
"Eh na sansu sun jima da mutuwa"
"Eh nasan da haka, inaso a samomin mutane biyu wanda suke da murya irin tasu, ka gaya musu ko nawa sukeda buƙata zan biya"
Wanda ya kira yace "to angama me gida"
Mona kuwa tanata farincikin zatayi magana da iyayenta.
NIGERIA
Yau kwanan Huda ɗaya a gidan Abba, bayan sun kammala cin abincin safe ta tattara kwanuka takai kitchen ta wanke, tana zama Inaya ta taho da gudu tana cewa "anty Huda wai kizo ki yiwa momy wanke-wanke"
Amani ta taɓe baki, kana tace "zauna ki huta, ai ba ke aka kawowa ita ba"
Huda tace "ai ba hutu nazoyi ba aiki aka ɗaukeni"
Karaf a kunnen Mahabob, ya kamo hannunta ya zauna akan kujera ita ta zauna a ƙasa kan carpet kafin yace "ke ba ƴar aiki bace, dole a tausaya miki, shima Abban ba a ƴar aiki ya ɗaukoki ba, dan haka ki kwantar da hankalinki"
Sam ta kasa kwantar da hankalin kamar inda suka faɗa, dan gani take kamar zata iya fuskantar hukunci a gurin momyn nasu,
Yana fita Amani itama ta shige ciki, Huda ta fice da sauri.
Lokacin Abba ya fita,
Batool na ganinta tace "wato har kin fara samun gurin da zaki miƙe ƙafa a kirawoki kiyi burus kamar ba ke aka kirawo ba"
Cikin tausasa murya, Huda tace "kiyi haƙuri Hajiya, na tsaya wanke nasu anty Amani ne"
"Aikinsu yafi nawa kike nufi?"
Kan Huda a ƙasa sam ta kasa ɗagowa, saboda cikowa da hawaye da sukayi,
Kicin ta wuce, kasancewar Batool ɗin ta nuna mata tana ci gaba da masifa.
Cikin sauri ta wanke kwanukan tunda ba yawa ne dasu ba, ta fito tasa hijabi ta koma part ɗinsu Amani, Batool ta bita da mugun kallo,
Tana zuwa ta samu Aseela a zaune ta share hawaye, kana tace "ina anty Amani?"
Aseela ta ƙwalawa Amani kira,
Sai gata ta fito tana gyara dogon wandonta.
"Ehee fita kikayi, sannan naga kamar kuka ma kikayi keda waye?"
Sam huda bataso sanar musu da komai ba, amma ta kasa daurewa sai da ta gaya musu abinda Batool ta faɗa mata,
Aseela tace "Anty Amani kira Abba kice matarsa tayiwa Huda duka"....!
Kunsanni da barci da wuri😫 wato yau comments ɗin da nagani, wlhi naji daɗi sosai sbda kuna ƙaramin ƙarin guwaiwa sosai.
Mom Islam
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
47-48
Sa'arsu ɗaya wayar Abban yaƙi shiga, dole suka haƙura.
Bayan Tasneem da Ummi sun gama haɗa girki, tasa taliyar bayan ruwan ya tafasa, kana ta kalli agogo 1:pm, sukayi sallah sbda gudun katsewar labarin, lokacin da suka idar abincin ya dahu, babu maganar ci, aka juyeshi a kula, kana Ummi tace "Tasneem nikam ina jiran ci gaban labari"
Murmishi Tasneem tayi, kafin taci gaba..
"Duk da na koma gidan Hajiya, Haseem bai dena bibiyata ba"
Zuwansa biyu, Hajiya ta tareni tana tambayata meyasa nake kulashi tunda ba shi zan aura ba, sam na kasa gaya mata komai, sbda bata sanshi ba, bata ma san yanada dangantaka da Uncle ba, da ta matsamin nace, Hajiya sbda nace bana sonsa shine anty Karima ta fara tsangwamata shine Uncle ya dawo dani gidanki"
"Ana auran dole ne yanzu?, har guda nawa kike da zasu aurar dake, nifa har yanzu hankalina bai kwanta da auranan da za'ayi miki ba, shiɗin yaron waye?"
Hajiya ta tambayeni cikin fushi.
"Yaron ƙanwar anty Karima ne, ya daɗe a gurinta dan haka take kiranshi yaronta kuma ɗan uwanta, dalilin da Uncle yace in dena kulashi, yana shaye-shaye"
"Innalilahi wa inna ilaihir raji'un, wato ke kuma taƙi ƙaddarar kenan, shi wanda ya turo iyayensa me sunansa?"
Kaina a ƙasa nace "Zahradden"
"To Allah yasa idan anyi auran ya riƙeki tsakani da Allah"
Nidai bance komai ba, na tashi na tattara kwanukan da nazo na samu, wanda hajiyar bata wanke ba, tass na wankesu na kife, na dawo ɗaki,
Zuwa yamma, wayar Hajiya tayi ring, ina daga tsakar gida, naji Hajiya ta ƙwalamin kira, da sauri na shigo ɗakin na sameta ina cewa "Hajiya gani"
Ta miƙo min wayar, tana cemin "Uncle ɗinki ne ya kira"
Ƙara wayar nayi a kunne kana nace "Uncle ina yini"
"Lafiya Tasneem ki shirya Zahradden zai zo yau Please ki nutsu karkiyi masa shirme"
"To" nace cikin jin kunya.
Sai da akayi sallahar magriba nayi, sannan na shiga wanka, ina fitowa na goge jikina da towel, na ɗauki mai na shafa, dama kwalliya bawai ta dameni bane, sai dai powder da na shafa, kana na buɗe akwatin kayana na ciro doguwar riga ta material, sai da na fesheta da turare, sannan nasa, kana na kalli kaina a mudubi, na ɗauki hijabi nayi sallahar isha'i kasancewar ana kiran sallahar, na zauna adu'a dama tunda nayi wanka nayi alwalar sallar isha'i.
Inajin ring ɗin wayar Hajiya gabana ya bada rass, sbda nikam ban taɓa hira da saurayi ba, wannan shine karon farko,
"Tasneem zoki karɓi waya"
Na fito da sauri,
"Yazo ki fito"
Bakina yayi nauyi, a zuciyata kuwa cewa nake "lallai ma ya raina Uncle shine ɗan aikensa"
Cikin sauri na dawo ɗaki na ɗauki hijab wanda ya tsaya min iya guwaiwa fari nasa, kana na fita jikina na kyarma sbda fargabar inda zan sameshi.
A hankali nake tafiya kamar wacce ƙwai ya fashewa, har na iso gurin da Hajiya tasa a ajiye fararen kujeru banga kowa ba, cikin sanyin murya naji ance "ji inda kike zaro ido kamar matsoraciya"
Da sauri na waiga idanuwanmu suka sarƙe dana juna,
Kunyarsa ta lulluɓeni, bansan lokacin dana durƙusa har ƙasa nace "ina wuni ba"
"Lafiya" ya amsa yana dariya,
"Wow na samu yarinya har da durƙusamin"
Da sauri na ɗago, tare da sanya tafin hannuna na rufe fuskata,
Kafin ya sake wata magana nace "dan Allah kayi haƙuri zan koma gida cikina na ciwo"
Lura da yayi na riƙe cikin ina yamutsa fuska yasashi, cewa "tom sai gobe, ga wannan zamudinga waya"
Da sauri nace "a'a"
Harna fara tafiya, naji yace "sai na gayawa Uncle"
A zuciyata nace "yasan sunan da nake gayawa Uncle ɗin kenan?"
Dole na karbi wayar, yacemin "harda sim card a ciki" nayi masa godiya na wuce.
Ina shiga na miƙawa Hajiya wayar, na wuce toilet na dinga kashi, ƙarshe gudawa ne ya biyo baya, duk na tsure saboda tsoro, banyi zaton haka hirar take ba,
Ina fitowa, na zube a gaban Hajiya.
Kafin nayi magana, tacemin "masha Allah wayar tayi kyau"
Wlhi na ɗauka zata yimin faɗa ne,
Hajiya tayi-tayi dani inci abinci na kasa, na shige ɗakin da nake da wayar, na buɗe kwalin, infinix ce hot 10, ina kunnata kira na shigowa,
Ikon Allah har yayi saving sunansa wai My life,
Haka rayuwa ta dinga tafiya, koda yaushe muna waya, amma bana son inji yace zezo, shima da ya gane nafi sakewa a waya bai cika zuwa ba,
Kwanci tashi asarar mai rai har bikinmu ya rage saura kwana biyar, zuwansa huɗu, duka bana wani sakewa dashi, an sanarwa dangi na kusa dana nesa, tunda bikin ya rage kwana uku, mutane suka fara zuwa, irin gyaranan na fata da ake yiwa amare nikam babu wanda yayi min, ko meye dalili oho, amma fa naga gata sosai, ta fannin dangin mahaifina da mahaifiyata kuɗi da kaya har sai da aka nemi wani ɗakin,
Uncle yayi ƙoƙari shima, ta fannin furnitures daga ƙasar waje aka kawosu,
Ana biki saura kwana biyu, yayan Abbana yasa aka yankamin zabi manya aka soyesu akayi min miya, ranar da aka samin lalle nayi kuka sosai, sbda tunowa da mahaifiyata da nayi, duk da an nunamin gata amma wlh nayi kukan rashinta, ana gobe biki, Uncle ya kawomin ɗinkuna kala goma sha biyar, duk ciki babu na ƙaramin kuɗi, dama Ni ba ƙawaye ne dani ba, haka akayi taro ina ɗaki, anyita soya cincin da nakiya da dubulan, ranar da aka ɗaura aure, sabuwar gudawa ta dawo min, gani nakeyi kamar a mafarki, ban gama tabbatarwa gaske bane sai da naji ance wai motocin tafiya da amarya sunzo"
Lokacin anata yimin nasiha inata kuka, Hajiya ta riƙe hannuna muka shiga mota nida ita,
Motarmu ce ta fara tafiya kafin ta sauran iyaye ta biyo baya.
Gaskiya dangane da kyan gidan babu abinda zance, sbda ko gidan Abbana da ake labarin haɗuwarsa bekai na Zahradden ba, an narka nera, anan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 16