number danginta, dole ta haƙura tunda basu da wani isasshen lokaci, duk wata hanya da ya gani kutswa yakeyi ta cikin jejin har Allah ya kawosu wani babban titi,
Cikin azama ya sake sauya hanya, ga mamakinsu dukkansu a jirgi aka koma bibiyarsu.
Yau kwanan Hassan bakwai a gidan Ala-Uddin Samir tun tana rashin sabo har ta saba, duk wani damuwa da take ciki da matsasti yanzu kam tana cin abinci tunda, taga babu larabar komawarta mahaifarta,
Kamar kullum tayi sallahar azhar ta ɗaga hannayenta sama tana kaiwa Allah kukanta, kamar daga sama ya shigo hannunsa riƙe da babbar leda,
Sallama bata cikin huruminsa dan haka ya nemi guri ya zauna, tare da wurga mata ledar dake hannunsa, bayan ta shafa adu'a ta kaleshi ta kalli ledar kana ta ajiye a gefe.
"Haseeaina ki buɗe wannan ledar sannan ki fito da kayan cikinta, inaso yanzu kisa, zaki iya shiga toilet ko bedroom kokuma in baki guri duk wanda kika zaɓa"
Jiki a sanyaye ta ciro kayan riga ce mai ruwan ƙwai yellow mai hannu ɗaya, iya ka nonuwanta kawai koda tasa zasu rufe mata, sai skel ɗin shima mai ruwan yellow da ratsin baƙi, shikuma mazaunanta zai rufe mata, gashi ko kauri babu, sai hula baƙa wacce ta kasance kamar ta sojoji mai adon tuta a gaba, cikin jin kunya Hassana ta kalli kayan tare da ƙare musu kallo, kafin tace,
"Dan Allah shugabana kayi haƙuri bazan iya wannan shigar ba, a musulunce ma haramun ne, Allah ya haramta"
"Okay haka kikace, idan baki saka kayannan ba sai na cire miki wanda ke jikinki in sanya miki waɗannan sai ki zaɓa..."
Tofa ya kuke ganin lamarin zai kasance?
# Mona
# Shahazad
# Ala-Uddin
# Hassana
# Mahabob
Yawan comments yawan typing.
Mom Islam 08141799224
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
63-64
Book1
"Dan Allah kayi haƙuri, a musulunce haramun ne, ni kaina bazan iya shigar da zata fallasa tsaraicina ba"
Tana shirin sake yi masa magana, taji ya kamota ya haɗe ta da jikinsa, kafin ya rabata da komai ya sanya mata wannan,
Da sauri ta runtse idanunta hawaye na sauka, tare da ambaton "Innalilahi wa inna ilaihir raji'un, astagfirullah Allah kana gani bana da niyar zina ko saɓa maka Allah kayimin katanga daga sharrin wannan bawa naka"
Cikin hukuncin Allah wayarsa ta fara ruri, rungume da hajaran ya ƙarasa ya ɗauko wayar, tare da karawa a kunnensa, "da sauri taga ya miƙe tare da ficewa bai ce da ita komai ba,
Hakan ya bata damar cire kayan ta mayar da wanda ya cire mata tana hamdala.
Yana fita ya daddanna waya ya kira lambar Lulu,
Cikin tausayawa naji yana cewa "Lulu babu abinda ya sameki ko?"
Muryarta bata fita sosai tace "Please Hub ka zo"
Ya buɗe mota ya shiga, dole na kusa dashi ne yayi driving har suka isa hospital.
Ko rufe murfin motar beyi ba, ya shige,
Dokar asibitin ne sai ka tabbatar musu da wanda kake nema, sannan kuma sun yarda dakai ba cutarwa zakayi ba, sai da Ala-Uddin ya cika sharuɗan sannan ya samu damar shiga dubata,
Cikin murya irin ta nuna tausayawa yake cewa "Lulu ya ciwon cikin naki?"
Idanunta a buɗe ta ɗora su ana Ala-Uddin kana tace "naji sauƙi"
Ya kamo hannunta yana mammatsawa a hankali tare da shafa gashin kanta,
Shigowar likita yasa Ala-Uddin cewa " yadai jikin nata babu wata matsala ko?"
"Eh juna biyu ta samu shine ya fita, befi na sati Uku ba"
Ran Ala-Uddin fess ya ce "okay"
Sbda a halin da ake ciki yanzu bayason Lulu ta samu ciki har ta aihu, hakan yana iya zamowa matsala a gareshi.
Sai gab magriba sannan aka sallemeta suka dawo gida.
Sosai yake riritata saboda ya samu abinda yakeso, har wani lallaɓata yakeyi,
Suna kawance yana rungume da ita, ya raɗa mata "my Lulu ya akayi kikayi mana ajiyar baby bani da labari"
Lulu tayi murmishi kafin tace "naso nayi maka surprise ne sai kuma komai ya baiyyana"
Ala-Uddin ya sake rungumota kana yace "I love You so much my Lulu"
Ta lumshe ido tare da manna masa kiss a kumatu.
SHAHAZAD FOREST.
Yau SaLha ta kammala shirye-shiryen zuwa ɗaukar fansar mutuwar ƴar uwarta,
Ba ƙaramin goyon baya Shugaba ta basu ba,
Har ta fara tafiya, Raza ya ƙwala mata kira, cikin ɗaga murya yace "Salha karki kuskura ki ragawa mugu, zai iya dawowa ya kashemu gabaki ɗaya"
Salha ta shafi kansa kana tace "bazan taɓa bari yayi nasara a kaina ba, har sai na aiwatar da duk abinda ya kaini, zan zamo masa ƴar leƙen asiri a lokacin da yake buƙatar taimako"
Duka mutanen garin suka goya mata baya, bayan wasu daga cikinsu suka bata ma'adanansu wanda idan ta siyar zata samu maƙudan kuɗaɗe.
Rataye da jaka a wuyanta ta tafi, ƙafarta babu takalmi, har ta kuma yin nisa a karo na biyu, shugabarsu tace "Salha al'adar mutanen Libya sanya takalmi da kaya a jiki, kinga ke bakiyi kama dasu ba, zaiyi wuya idan ba'a ganeki ba, amma nasan Ubangiji bazai bari ki cutu ba, Yakamata ki fara da neman aiki ko a gurin makusantansa, sannan ki kame kanki da furta kalmomin da muke yawan furtawa bayan haka, karki yarda kici abinci da hannu yin hakan zai sa a gano daga inda kika fito"
Slha tace "bazan bari su gane ba"
Jiki a sanyaye tabar yankin nasu.
Tunda su Kharan sukayi nasarar faɗawa ɗayan titin, suka dinga tafiya a hankali, duk da jirgin dake bibiyarsu, hakan besa ya dakata ba,
Abin mamaki wanda baya ƙare wa bai wuce saukar jirgin a filin jejin da yayi ba, cikin tsoro Kharan ya yiwa motar key suka arce da gudu, hakan ya bawa mutanen da suke cikin jirgi damar fitowa tare da kutsawa inda suke, sai waya da waya sukeyi, tare da harbe-harbe da bindiga.
Sai da ya tabbatar da su ɓace musu sannan ya bar motar a gurin ya kamo hannun Hajara da Mona suka bar gurin, sbda gudu ƙafafunsu har ciwo sukayi, ga tsananin sanyi daya addabi Hajara, sai karkarwa takeyi.
Daga nan sukaci gaba da shiga jeji wanda ya kasance ba mai ban tsoro sosai ba, dole suka yada zango a gindin wata bishiya, Kharan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, kafin yace "Shahazad mutum ne mai hatsarin gaske, zai iya bibiyarmu har a wannan jejin ma,
da muke ciki, a shawarce ya kamata mu bar gurin an idan muka sake shiga ciki sai mu huta"
Kamar inda ya umarcesu haka akayi suka dinga tafiya basusan inda suke shiga ba, suna cikin tafiya wani mutumi ya daka musu tsawa, wanda yasa Mona da Hajara shiga cikin firgici,
Mutumin yace "Ɗan saurayi barkanku da shigowa jejin sarki Raja"
Cikin salo na jin asalin labarinsu yace "meke tafe daku, dan naga kamar baku da gaskiya"
Kharan yace "munason mu ga hanya zamuje
Garin AL-KUFRA"
Mutumin yace "nawa zaku biyani"
Kharan yayi murmishi kafin yace "a halin yanzu babu kuɗi a gurina amma nayi maka alƙawarin idan muka sake haɗuwa zanyi maka alheri"
"Ina bazan iya aikin wahala ba"
Karan ya shaƙo wuyan rigarsa tare da cewa "zaka nuna mana ne ko sai na sheƙeka?"
Jikinsa na rawa yace "kuzo muje"
Sukaci gaba da tafiya har suka ɓullo titin da zai sadasu da garin AL-KUFRA, sannan mutumin yace "amma kana kama da Kharan Khan wannan baban ɗan ta'addan"
Kharan yace "tabbas muna kama amma komai namu bai kasance ɗaya ba, sannan mungode"
Suna hawa titi, Kharan ya ciro waya ya danna number abokinsa Majid, ring ɗaya ya ɗaga tare da cewa abokina ina ka shiga su mama sunata tambayarka, nifa har na fara tsorata amma dai kana lafiya ko?"
"Eh ina lafiya, Majid ka taho da mota zuwa titin sabon titin tafiya AL-KUFRA"
"Mekuma ya kaika can, kai da ko yawo bakayi?"
"Haba Majid tambayoyin sunyi yawa a halin yanzu ina cikin hatsari"
Jikin Majid na rawa yai saurin ɗaukar key ya fito tare da yiwa motar key zuwa gurinda su Kharan suke,
Yayi nisa sosai, yaga sojoji a hanya, bai kawo komai ba ya ci gaba da tafiyarsa har Allah ya kawo shi gurin sojojin, abin mamaki wanda bazai taɓa wuce masa ba shine, hoton Kharan Khan mugun ɗan dabannan wanda suke kama da Kharan suka nuna masa, tare da ɗora masa bindiga a kai, sukace yanayi mana basaja da sunan su biyu ne, a safiyar yau ya saci matar babban ɗan kasuwa Shahazad Khan munason ka gaya mana ka sanshi kokuma Kanada inda zakayi mu haɗu?"...
More comments more typing
Mom Islam
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
65-66
Jikin Majid na cigaba da karkarwa yace "ban sanshi ba gaskiya"
Sai da suka ɗauki number motar kafin suka barshi ya wuce.
Duk da A C dake bada iska mai sanyi, amma gumi yake yi, sai da ya bari yayi nesa dasu kafin ya danna number Kharan,
Dama jiran kiran Majid yake yi, ya ɗaga cikin yanayin damuwa kana yace "Majid kayi sauri"
Daga can nesa Majid ya hango Kharan, hankali a tashe yake kallon matan dake tare dashi, kafin ya buɗe musu mota suka shiga,
Allah ya taimake su a hanya babu jam'i hakan ya basu damar wucewa anguwarsu,
Suna isa gida Majid yayi parking suka fito dukkansu, Kharan yayi musu umarni da su ƙarasa ciki, jikin mona da Hajara a matukar sanyaya suka shiga, Majid dake ƙare musu kallo yaje ya kulle get tare da rufe ƙofar da suka shigo ya dawo ya zauna kusa da Kharan dake mayarda numfashi.
"Kharan waɗannan suwaye a ina ka samo su?"
"Majid banason doguwar tambaya shi yasa ma na kawo su gidanka, tunda matarsa bata nan, idan na kuskura na kaisu gidanmu, tambayar Papa ma ta isheni"
"Oky karka damu zan tayaka kula dasu"
"Zanyi sallah Please "
Hajara ta faɗa da siririyar Murya,
"Bismillah"
Kharan ya nuna mata toilet.
KHARAN KHAN
Tunda yaji labarin Kharan ya tsere dasu Mona, kuma yawancin mutane sun raja'a shine, hakan ya bashi damar farautar Kharan sbda wata manufa tasa, yasan idan har ya mallaki matar shahazad a sashin sa, babu shakka zai samu maƙudan kuɗaɗe,
System ɗinsa ya ɗauko tare da searching sunan Kharan, tare da zooming na photonsa, Kharan Khan ya kalli fuskarsa a mirror kana ya kalli fuskar Kharan yayi makirin murmishi sbda kamar su ɗaya, abinda ya bambanta su idanun Kharan ruwan gold ne, shi kuma Kharan Khan idanunsa brown ne, boll's ɗin ciki,
Murmishi ya sake yi a karo na biyu, kana ya cigaba da bibiyar sunan mahaifinsa da inda yake zama da inda yafi zama,
Cikin Sa'a kuwa ya samu harda address na gidan Majid, hankali kwance ya ɗauki kwalbar giya dake gefensa ya kora, kafin yace "a shawarce, zanyi musu basaja, sannan nunar musu nine Kharan shi kuma idan ya shiga hannun jam'i nan ne zan samu damar buga wasa da shahazad, yana gama faɗar haka ya kashe system ɗin, tare da yin tafi.
Bayan Hajara ta idar da sallah, ta ɗaga hannu sama tana roƙon Allah yayi musu kariya, Allah ya rufa musu asiri, daga zuwa aikatau ƙasar larabawa ta shiga rayuwar d bazata iya fassarawa ba, rayuwar da take gani a Film yau itace a ciki.
Majid da Kharan, duka sun fice ya rage saura Mona da Hajara, Mona tace "Hajar kiyi haƙuri nasan zamu sha wahala amma wannan itace hanyar da zamu tserewa mugu"
"Babu komai, kowane bawa da tasa ƙaddarar"
Hajara ta faɗa tana miƙewa.
Can anjima, Majid ya shigo hannunsa riƙe da leda, ya ajiye a gabansu, kana yace su buɗe suci" Mona ta kwaɓe fuska, tare da riƙe ƙirjinta alamar tashin zuciya tace "nikam bazanci ba, basmati nake nema"
Majid ya zaro ido, sbda koda ya fita ana nan ana cigiyar inda Mona tayi, gabansa na tsananta faɗuwa yace "garin ya rikice ko ina babu daɗi"
Kharan na bayansa yace "kai rago me yasa zaka bada maza, ya bigi kafaɗarsa kana yace "jeka siyo mata abinda take so"
Majid ya fita jiki a sanyaye kana ya rufo ƙofar.
Yana driving ya kusa zuwa gidan Abinci, Kharan Khan kuma na tsaye a bakin hanya,
Sam Majid ya mance su biyu ne, sbda gigicewa da yayi, ganin Kharan Khan yasa yayi parking kana yace "Kharan har ka sauya kaya ne?"
Murmishi kawai yayi, kana ya buɗe motar ya shiga, yanata danne-danne a waya, har Majid yayi parking ya siyo Basmati ya dawo cikin motar, sunyi nisa sosai yace "ɗazu nan fa ka gama zolayata amma yanzu naga kayi min shiru, iska cin naka ya motsa ne ko?"
Kharan Khan yayi murmishi tare da cewa "uwum" ta cikin bakinsa,
Suna isa gidan motoci biyu wanda suke binsu suka shigo tare da parking, Kharan Khan yasa aka kama Majid, kana ya ƙarasa ciki, cikin Sa'a yaci karo da Kharan yana shan coffee, hankali kwance ya toshe masa baki ya fita dashi ta baya, shima aka sanya shi a mota suka wuce dasu.
Hannunsa riƙe da Basmati ya shigo tare da cewa "wacece a cikinku takeson Basmati?"
Mona tace "nice" tare dayi masa godiya,
Hajara tace "kanata ɗawainiya damu mungode" Kharan Khan yayi murmishi kafin yace "ai yiwa kaine, taimakawa mutane ya zamomin abokin rayuwa....
Kuyi hakuri wayata babu chaji, dan karkuyita zuba ido ne yasa nayi muku kaɗan anjima zamu ɗora
Mom Islam
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
Book1
67-68
Inda Mona take cin Basmati ɗin sai yayi matuƙar burgeshi har wani murmishi yayi, kafin ya miƙe tsaye yace "amma ke ƴar Nigeria ce ko?"
Ya kalli Hajara.
"Eh amma ina fatan komawa nan bada jimawa ba"
Murmishi ya sake yi a karo na biyu kafin yace "Mona matar shahazad Junaid Khan, ki ayyana a ranki kin tsere masa, abinda nakeso dake shine, ki rage tunani ni nan zan zamo muku gata ko wacce zata koma inda takeso"
Ya faɗi maganar yana shafa sajen da yayi luff a gefen kumatunsa.
"Bamu da isasshen lokaci, yanzu zamu bar nan zamu tafi India, sbda tserewa Shahazad, ya baza jam'i ta ko ina, mafitarmu shine mubar garin an, nariga na gama komai zamubi jirgin ƙasa"
Inda yake maganar sai ka rantse da Allah har cikin zuciyarsa yakeyi, hankalin Mona a kwance tace "nifa ƙauyenmu nakeso ka mayar dani, ita kuma taimako take nema zuwa Nigeria"
Kharan Khan yace "na fahimceku, Abinda nake nufi, duk wata hanya da zamubi za'a iya gano inda muke matsawar ba India muka tafi ba"
Gabaki ɗaya kan Mona ya kulle a fili tace "idan har sai mun koma India a bar mu anan ai lokacin dana nemi taimakon ka bakace min haka ba"
"Keee!!"
Kharan Khan ya daka mata tsawa, tare da cewa "bawai sai abinda kikace zanyi ba, ko kubini India kokuma in barku anan"
Tashi ɗaya suka fara kuka, Hajara kam sai ambaton sunayen Allah takeyi, gabanta na cigaba da faɗuwa.
Kharan Khan zeyi magana kenan, sukaji jiniyar motar sojoji.
Nigeria
Abubuwa sun faru, haɗuwar Juwairiyya da Alhaji Al'amin, sati guda da haɗuwarsu Amma ya sauya musu gida, ya siyawa Malam Yusuf Mashin ita kuma ya mayar da ita ƴar gayu, a take malam Yusuf ya tara shedu aka sanya ranar auren Juwairiyya akan sadaki dubu ɗari bakwai, kuɗin gaisuwa dubu ɗari.
Yanzu kam Alhaji Al'amin ya zamo ɗan gida, saboda daga yazo da mota zeyi sallama ya shigo,
Kamar koda yaushe idan yana gari baya rabuwa da gidan nasu, yauma hakan take hannunsa riƙe da babbar leda ya shigo da sallama, kasancewar malam Yusuf ya fita sai Juwairiyya yasa taje ta karɓi ledar tana gaishe shi, amsa wa yayi kana yace "nama ne na kaji ki juye, jiki na rawa taje ta juye, ta dawo tsakar gida inda ta shimfiɗa masa tabarma,
"Uhm kin kusa zamo wa mallakina ina jiran wannan ranar har mafarkinta nakeyi"
Juwairiyya ta rufe ido tare da cewa "me kakeci na baka na zuba?"
Yace "dambu"
Ta kwashe da dariya, tare da cewa "uhm saura kwana shida ai"
Murmishi yayi, kana ya miƙe tare da ajiye mata maƙudan kuɗaɗe ya fice ta miƙe ta rakashi, a hanya yake nuna mata photon gidan daya siya mata, kana yace kar su malam su siyi komai har kayan sawa.
Kamar zata rungume shi tsabar Godiya.
Malam Yusuf na dawowa ta sanar masa, yayi farin ciki harda ma ganin naman daya kawo musu.
Abinda kowa bai sani ba, Alhaji Al'amin bai sanarwa da danginsa auren da zeyi ba, ko meye dalili oho.
Acan ɓangarensu Dady yau suka sauka a garin su Bauchi, cikin kwanciyar hankali, tare da Iffat da Hajiya ƙarama, bayan sun gaisa a parlo, suka zube, Hakeem kam bakinsa yaƙi rufuwa, Hajiya babba kuwa ta shirya musu abincin tarba mai rai da lafiya, bata nuna musu komai ba, saboda cikar ƙudurinta,
Har ɗaukar Iffat tayi ta ɗora a cinya, kana tace mata "ya jiki"
"Da sauƙi" Iffat tace tana kallon Hakeem,
Hakeem yace "wato kowa kinje gurinsa amma ni kinƙi kulani ko?"
Iffat tayi dariya kana tace "yi haƙuri yaya gani nazo"
Ta taho tanayi masa dariya,
Washe gari, Dady ya koma ɗakin Hajiya babba, Iffat ta saba dashi, abinka da yaro ta bishi can, bayan sun gama breakfast ta hanyare cinyarsa tana cewa "Dady jiya da dare yaya yace zai sani a school idan ka yarda"
Hajiya babba ta galla mata harara tare da kawar da kanta gefe,
Dady yayi murmishi kafin yace "eh ni da kaina zan kaiki amma sai first an dawo hutu"
Iffat ta hau tsalle tana murna, Dady ya miƙe tare da cewa "nikam barin je in duba abubuwan da suka wakana bayan tafiyarmu kuyi hira ga Eshat nan"
"Toh Alhaji a dawo lafiya"
Yana fita ta kamo kunnen Iffat tace "wlhi idan kina shigo min sashe na sai na yankaki, kuma idan naji kin gayawa wani sai na ƙona bakinki"
Iffat ta toshe baki, tare da miƙewa zata fice, Hajiya babba ta fincikota ta faɗi ƙasa, kana tace "munafuka ƴar zina"
Iffat ta sunkiyar da kai, tare da fakar idon Hajiya babba ta ruga part ɗin Hajiya ƙarama da gudu.
Cikin tuhuma Hajiya ƙarama tace "my Eshat lafiya?"
"Babu kowa"
Iffat ta faɗa tana zaro idanu.
Har rana tayi Dady bai fita aiki ba, da yazo cin abinci yace "a kira masa Iffat"
Sai da Hajiya babba tayi jimm kana ta miƙe taje sashen Hajiya ƙarama ta tsaya a bakin ƙofa kafin ta dawo,
"Alhaji tayi barci"
Dady yace "ikon Allah barcinta babu wuya, nazo wucewa naji firarsu ita da hajiya"
Aran Hajiya babba kuwa, baƙinciki ne yayi kwance sam bata son taji Dady ya ambaci sunan iffat ko kaɗan.
Hakeem ya mayar da hankalinsa ga jarabawar ƙarshe da suke yi na s.s.c.e, shi yasa bai cika zama a gida ba, sai dai idan ya dawo, yana cin abinci zai wuce gurin aiki, hakan yayiwa Hajiya babba daɗi, sbda batason taraiyyarsa da Iffat.
Horn driver yayi a bakin get ɗin gidansu Amani, mai gadi ya taso da gudu ya buɗe get ɗin tare da yi musu sannu da zuwa, cike da isa da iko ta zuro ƙafafunta waje, kana ta fito da jikinta duka tana gyara mazaunin gilashinta, gyara zaman mayafinta tayi tare da fara takawa i zuwa cikin gidan, kamar mai tsoron taka ƙasa, cikin rashin sanin inda ta dosa ta murɗa handle ɗin ƙofar part ɗinsu Mona, Mahbob dake tsaye yana gyara zaman hular kansa suna magana da Amani, ta Kunno kai, a hankali ta jawo gilashinta tare da ƙaremusu kallo tace "Please nan ne gidan Alhaji Auwal?"
Amani ta ture Mahbob ta ƙarasa fitowa gurinta kana tace "dallah banziya marar tarbiyya ki koma idan aka koya miki sallama da tarbiyya sai ki zo ki tambaya, nan gidan ya samu ingantaccen yabo kinji"
Shikam Mahbob har ya riga ya fice, sbda baya son hayaniya,
Naeema ta zaro ido kana tace "kee!!!, kinsan dawa kike magana kuwa?"
"Ahh to dawa nake magana idan banda marar tarbiyya?"
Naeema ta danna number Batool tana ɗauka, Naeema ta fashe da kukan ƙarya kana tace "tayi mistake ɗin shigowa yaran mijinta sunyi mata duka"....!
Uhm nace kuyi haƙuri har yanzu banyi muku mai yawa ba.
More comments more eheem
Mom Islam
*💋MURAYU A TARE 💋*
Mom islam
Book1
page 69-70
Tuntsirewa da dariya Amani tayi, kana tace "shagali, sharri ga mai yinka"
Ta shige ciki tare da bugo ƙofa.
Naeema tayi ƙwafa tare da gyara zaman gilashinta, taci gaba da tafiya zuwa part ɗin su Batool, cikin zafin rai, take bubuga ƙofar, Batool ta buɗe mata tare da rungumeta,
Suna shiga ciki, kai tsaye suka wuce bedroom ɗin Batool, Naeema tace "wlhi anty Batool yaran mijinki basu da kunya harni zasu gaggayawa magana?"
Batool ta tashe bakin Naeema da tafin hannunta, cikin rage murya tace "haba Naeema so kike yi mahaifinsu yaji kinsan fa yana gida?"
"Mtsew ai yaran ne basu da tarbiyya wlhi"
Naeema ta faɗa tana cire mayafin jikinta,
"Yauwa ƙanwata, abinda nakeso dake, ki yi iya yinki gurin farauto zuciyar Mahbob, wlhi ba ƙaramin ji dake zai yi ba, kinga inda kika sake fresh ne ga kumatu kin ajiye"
"Highe anty Batool duk ma ba wannan ba, shine kika zuga su Dady da mama dole sai na auri wannan yaron?, Bayan kinsan a tsarina babu batun aure har sai na cika muradi na?"
Batool ta taɓo kafaɗar Naeema kafin tace "nasani amma dole ki kawar da ƙudirinki, tunda ga aljannar duniya zaki samu, ki wataya inda kike so ki taka wanda kikaga dama, duk da ke ba matar gwamna bace, amma dole da yawan mutane zasu biki, girkifa sai kinga damar yi har wanki wanke-wanke da guga, kinga kuwa rayuwar jin daɗi zakiyi"
Duk da haka dai Naeema batace komai ba,
Wayar Batool ta fara ruri, kallon screen ɗin wayar tayi, kana ta miƙe da sauri, tace "ki shirya zuwa gaishe da sirikinki"
Naeema ta waro ido kafin tace "uhm nifa banason takura"
Batool tace "nidai karki bani kunya"
Batool na fita Naeema ta cire rigar ta ya rage daga ita sai bra da dogon wando,
A hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin Abba, tare kutsa kai ciki, ga mamakinta taga har ya shirya cikin shadda fara, tasha aikin wuta,
Zama tayi a gefensa tare da kamo hannunsa tace "wlhi na ɗauka kana barci har yanzu shi yasa ban shigo ba"
Cike da so da ƙauna ya janyota jikinsa, yana cewa "inason fita da wuri shi yasa"
"Naeema tazo"
Batool ta faɗa, tana rungume a jikinsa.
"Masha Allah tazo lafiya?"
"Lafiya lau"
"Am na mance ban gaya miki ba, jiya yayana yakai dukiyar auren Mahbob gidanku"
Batool tayi kamar zata shige jikinsa, a fili tace "Masha Allah, Ubangiji ya sanya alkairi"
Abba ya amsa "da Amin".
Ta ɗauko agogon hannu ta ɗaura masa,
Kana ya miƙe tsaye, itama miƙewar tayi hannunta riƙe da hula, suka fito parlo.
"Barin yiwa Naeema magana"
Tana tura ƙofar ta ganta daga ita sai bra da dogon wando, murya ƙasa-ƙasa tace "dan Allah ki sanya kaya da hijabi ki fito ku gaisa"
Naeema ta turo baki, tare da cewa "uhm ni wlhi kina takuramin da yawa"
Hijabi ta saka kafin ta wuce parlo, zubewa tayi ta gaishe shi, ya tambaye ta yasu mama, tace masa "lafiya lau"
Kana ta koma ɗaki,
Batool tazo ta zauna kusa dashi, dama ta riga da tasa masa hular, Abba yace "gaskiya Naeema akwai hankali ga tarbiyya"
Batool tace "kai Alhaji"
Yace "da gaske gidanku ai babu wanda zai samu mata yayi buruss iri mai albarka"
Batool ta kalli agogon dake manne a jikin bango, ƙarfe 12:30pm, Batool tace "Alhaji breakfast fa?"
"Zanyi yanzu"
Taje kitchen ta ɗauko flaks na ruwan zafi da gwangwanin madara da bonbita ta kawo, da cup kana da bredi, bayan ta haɗa masa shayin ta miƙa masa, ta kunce ledar bredi ta miƙa masa,
Suna hada ido sukayi murmishi a tare.
Yana kammala breakfast ɗin ya miƙe tare da cewa "sai na dawo"
"Allah ya kiyaye hanya Allah ya tsare"
Batool tayi masa kana ya fice.
Kai tsaye part ɗinsu ya wuce, dukkansu suna zaune a parlo yai sallama ya shiga, "walaikumusalam" suka amsa, kowanensu ya gaishe shi, lokacin suma suke karyawa,
Bayan ya amsa yace "ankai kuɗin auren Mahbob"
Inaya ta taho da gudu ta rungumeshi,
Cikin tsokana yace "auta maiyasa kwana biyu bakya zuwa part ɗin momynki?"
"Babu komai"
Inaya tace.
Daga Batool har Aseela babu wanda yace komai, bare Huda, da bakowa ba.
Da kallon mamaki yabi Amani, sbda ya santa farin sani, baya taɓa magana tayi masa banza, sannan duk abinda yake so shi takeso "
"Amani lafiyarki kuwa?"
Amani ta ƙirƙiro murmishin yaƙe kana tace "lafiya Abba"
Abba yace "ba haka kike ba maiyasa kika sauya"
Cikin ƙosawa da tambayoyin Abban tace "Allah ya sanya alkairi "
Amin yace, jiki a sanyaye ya miƙe, tabbas gabaki ɗaya yaran sun sauya masa, har Inaya da batasan komai ba,
"Ku shiga ku gaishe da budurwar Mahbob tazo ɗazu"
"Toh" sukace cikin haɗin baki.
Yana fita sukace babu inda zasu,
Amani ta kalli Huda tace "wlhi idan kika sake zuwa sashen Batool sai na ɓata miki rai"
Huda tace "Anty Amani, wlhi itace takeyi min masifa"
"Ai ƙarewar masifa ta dukeki shine zata tabbatar da ita ba kowa bace fashe muguwa"
Aseela tace "Abin mamaki aure daɗi, Abba baya shigowa ya duba tafiyarmu, ko yaga mun ci abinci ko bamuci ba, sannan ko fira ya dena yi damu"
Amani tace "mtsew ke kika damu dasu ma"
Huda tace "za'ayi bikin Ummana yau nakeson tafiya"
Aseela tace "bari bro Mahbob yazo sai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 16