Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
be kai ba?" Kafin Umman ta kamo Huda ta cakumi wuyan rigarta tana cewa "gayamin wa kika bawa abinci bai baki kuɗi ba?" Huda ta zazzaro idanu waje cike da tsoro tace "wlhi Umma babu wanda na bawa daga zubin abincin ne haka" "Dan ubanki ce miki akayi nima a shago irin zubin abincin da sukeyi min kenan?" Huda ta girgiza kai cike da tsoro, Umma tace "gobe in Allah ya kaimu wlhi tallahi kinji na rantse idan baki dawo min da kuɗina cass ba sai na illataki tunda kin fara nunamin rashin gaskiya" Jikin Huda na rawa tace "nayi miki alƙawari Umma ki sakeni wlhi zan kawo miki gobe" Sannan Umman ta saketa tana mayar da numfashi kamar wacce tayi gudu, Tsabar tsoro da ya kama Huda, tunda ta miƙawa Umma kuɗin ta ɗauki buta ta yi alwalah, ta dawo ɗan ɗakinta ta shimfiɗa wani ɗan ƙyalle ta kabbara sallah, tare da rama sallolin azhar da la'asar, kana ta zauna jiran magriba. Har akayi isha'i bata fito ba, Umman ma bata nemeta ba, IFFAT A hankali Hajiya ƙarama ta dinga bata tea tana sha cikin nutsuwa, sai dai har yanzu babu wanda yaji sautin muryarta, ko kallon da take yiwa mutane ma wani iri, marar kyau, duk wanda yaga ƙwayar idanuwanta inda suke juyawa yasan Iffat na cikin wani hali. Haka suka wuni jiki a sanyaye babu wani kuzari, zuwa yamma Dady ya ɗauki Hajiya babba suka koma gida, ya rage saura Hakeem da Iffat ɗin da kuma Hajiya ƙarama, Hakeem ne ya fara fita yin sallahar magriba, bayan ya dawo Hajiya ƙarama taje tayi alwalah itama ta kabbara sallah, Hakeem na zaune yaga Iffat nata jijiga, alamun jikin ya tashi, cikin hanzarin da gudu yai ofishin likitan, ko sallama babu bare neman izini yace "doctor kazo yarinta zata mutu" A inda Hakeem ɗin yayi magana, doctor ya bawa wanda yake sallama haƙuri kana ya fice da gudu, abin al'ajabi, likitoci uku ne suka haɗu a kanta, amma sam har yanzu Iffat bata numfashi, a zahiri dai an fara kyautata zaton ko mutuwa tayi?, hankalin Hakeem yayi mummunan tashi, zufa babu ta inda bata karyo masa, rai a ɓace yace "aikin banza aikin wofi, likitoci kunkai ku huɗu amma kun kasa ceto rayuwar yarinyata kun kasa dawo mata da numfashinta?" Ɗaya daga cikin likitocin yayi murmishi ya girgiza kai, Ana fita da Hakeem yana ci gaba da gaggaya musu maganar da duk ta fito daga bakinsa. GIDAN MALAM YUSUF Har akayi kiran sallahar magriba Hajara na zaune akan kujera ƴar tsugunno ta rafka uban tagumi, tashin hankalinta baya wuce idan malam Yusuf ya shigo gidan ya fara surfa mata ruwan masifa, shine babbar damuwarta, jin an shiga sallah ya sanyata miƙewa ta ɗauki buta ta nufi banɗaki, tsaki tayi, sakamakon ganin tiƙeƙen kashi a bakin masai, kana ta samu tsinke ta tura tana Allah wadai da hali irin na Juwairiyya, kama ruwa tayi ta fito, kana ta tsugunna ta ɗaura alwalah ta nufi ɗakinta, tana shiga tasa ƙafa ɗaya ta faɗi tiimm, sakamakon santsi da ya kwashe ta wanda batasan ta ina yazo ba, cikin ɗaga murya tace "Juwairiyya bakya jina ne ?inata ihu dan Allah kizo ki taimaka min in tashi ƙafata ta gurɗe" Juwairiyya na daga ɗaki tace "kinga bani da lokacinki, kuma wlhi girki ne dole kiyi, idan baba ya kawo" Hajara tace "wlhi banga wanda ya isa ya sanyani girki a gidan an ba, musamman ma a wannan halin da nake ciki" Juwairiyya na daga ɗaki tace "idan baba ya dawo zaki mai-maita masa" Hajara ta fashe da kuka, mai ban tausayi, cikin ƙarfin hali ta kama bango da ƙofa ta miƙe, kana ta nemi guri akan kujera ta zauna, cikin ikon Allah aka kawo wutar nepa, Hajara ta kalli gurin da ta faɗi, ga zahiri nan sosai mangyaɗa aka zubar domin ta, tasan aikin na Juwairiyya ne, ba sai an gaya mata ba, Hajara ta girgiza kai, ta fara tunanin itakam me ta tarewa Juwairiyya a gidannan ne? Tana tsaka da tunani sai jin mutum tayi ya faɗi timmm..., cikin firgici tace "malam lafiya?" Ashe tun daga ɗakin Juwairiyya yake surfa masifa, yazo yiwa Hajara ya faɗi a bakin ƙofa, santsin man gyaɗan ya yar dashi, hajara ta rufe bakinta sakamakon dariya dake zuwar mata, malam Yusuf ya tattaro dukkan ƙarfinsa, yana cewa "ƴar baba zo kiyi temako babanki ya faɗi" Juwairiyya ta fito da gudu, ta bankaɗo labulen ɗakin Hajara, tana cewa "wlhi baba ina kallonta ta zuba maka miyar yauƙi a gurin kawai zata kashe mana kai ne" Tana maganar tana kamo hannun mahaifin nata, cikin ikon Allah ya miƙe amma har yanzu yana riƙe da Juwairiyya, Hajara ko ta zuba musu ido ba Um, ba um-um. Har zasu fice "Hajara tace "baba kasan dai ni marainiya ce, mahaifiyata ta rasu dan Allah baba ka rabu da Hajara, domin inada yaƙinin zuwa gaba zata iya kashemin kai" Cikin bin umarnin Juwairiyya yace "Hajara kije gida har sai na nemeki" A hassale Hajara ta miƙe, tama mance da zugin da ƙafarta keyi, cikin masifa tace "wlhi tallahi idan har baka sakeni yau ba, baka cika lusari me jin maganar fitsararriyar ƴarsa mai gurɓatacciyar tarbiyya" Sosai maganar tayiwa malam Yusuf zafi, zuciyarsa na raɗaɗi jikinsa na ɓari yace "Hajara yaushe kikayi baki da har kike jifana da munanan kalamai?" Kafin Hajara tayi magana, Juwairiyya ta saki baba ya faɗi ragwab, ta taho da sauri tare da ɗaga hannu zata mari Hajara, cikin azama Hajara ta riƙe hannun ta yar da Juwairiyya a ƙasa ta dinga duka kamar an aikota, malam Yusuf dake ƙoƙarin miƙewa ya kasa, gashi yaji Juwairiyya tana nishin mutuwa, cikin ɗaga murya yace "Hajara ki tattara duk abinda kika sani naki ki barmin gida, na sakeki saki uku na sake ƙara uku, kai idan anayin goma sha biyu yau nayi miki fice, karki kashemin yarinya ita kaɗai Allah ya bani, dan kinga ke bakya aihuwa shine zaki kashe ta, munafuka muguwa, Hajara tayi tafi tare da cewa "ayirii- yirrii, wlhi tafi nono fari, dama zaman gidanka ya zamemin dabaibayi ne, babu inda zanyi, yanzu kam Alhmdulilah" Ta fara tattara kaya, Juwairiyya ta miƙe jiki babu ƙwari, ta kamo baba suka fice, ita kuma Hajara ta fara tattara kayanta, takai kusan azhar sannan ta gama, ta fita ƙofar gida neman mota, cikin sa'a kuwa ta hango motar wani saurayi, wanda suke mutunci dashi, wato akori kura, ta ƙarasa tayi masa magana, ya amince zai kwashe mata kayan, amma zata nemi kuɗin fetur ta bashi, kan kace me, har sun kusa kwashe kayan, hatta tukwananta duk ta kwashe, babu abinda ta bari wanda ya kasance mallakinta. Bayan sun gama ta shiga gaban mota suka wuce anguwar su dake Rugan Julli, bayan drivern yayi parking a ƙofar gidansu, kasancewar ta nuna masa tun suna nesa, ta buɗe motar ta fito, shima haka, ta shige ciki, shi kuma ya fara firfito mata da kaya, tana shiga ta fashe da kuka, Goggo Dije na ganinta ta taso da sauri tana cewa "Hajara lafiya?" Hajara ta share hawaye, kana tace "mama baba yana ciki ne?" Goggo tace "ai ya tafi Kaduna neman kuɗi, ki sanar dani meke faruwa?". Kafin Hajara tayi magana, samarin anguwar sun fara shigowa da kayan gado, Goggo tayi shiru, domin ta fara zargin aikin gama ya gama, "Hajara kaso auran naki kikayi?" Hajara tace "wlhi Goggo duk hakurin da nakeyi bai gani ba, ya sakeni saki uku, Goggo tace "me kikayi masa?" sai ga wani saurayi nan ya shigo da takarda a hannunsa ya miƙawa Hajara, Hajara tayi masa godiya kana ta kalli takardar, kasancewar taɗan taɓa hausar boko tace "Goggo takardar saki ce" Goggo kam ta kasa furta koda kalma ɗaya, tunanin ta bai wuce baban Hajara idan yazo ya surfa musu masifa itada Hajara ba, dama sau tari yakan ce itace take hana Hajara zaman aure, tunda auran Hajara na biyu kenan, duk da ƙarancin shekarunta. HUDA Yau ma kamar kullum, taci kwalliyarta ta sanya riga da zani na atamfa, ɗinkin yayi mata kyau, kayan ma sababbi ne, kasancewar ɗinkin ƙaramar sallah ne da Umma tayi mata, rataye da jaka da hijab ta fito tsakar gida, Umman ta miƙa mata abinci a kwano tare da cewa "lokaci dai ba tsayawa jiranki zeyi ba" Cikin sauri-sauri, Huda take cin abincin, bata kai ga cinyewa ba ta miƙe tana cewa "Umma na ƙoshi" "Ai ke haka kike, daga ance miki kiyi sauri sai ki ajiye kwanon abinci, to wlhi kanki kika yiwa ba niba" Umman ta faɗa tana shiga ɗaki ta ɗauko mata takalmin sallahar ta, Huda na gani, ta zaro ido, kafin tace "umma wannan ai takalmin sallah ta ne" "Eh sai me, inace ni na siya miki?" Huda bata sake magana ba, tasa tare da ɗaukar bokiti tayi waje, Umman kuma ta ɗouko babbar kula, sukayo waje, cikin sava sai ga mai mashin ɗin da Umma ta samar mata, wanda sukayi dashi zai dinga zuwa yana ɗaukarta kullum, Cikin ikon Allah suka iso gurin sana'arta, bayan ta sauka ya sauke mata kayan abincin, tayi masa Allah ya tsare ta wuce, Yau kam anfi koda wane lokaci cika a gurin, dan harda baƙin ido wanda bata sansu ba, lokacin zuba abinci nayi ta fara zuzzuba musu, suna bata kuɗi, wasu sai sun gama ci sannan zasu miƙa mata kuɗi, wanda yake tare mata faɗa, ya miƙe tare da cewa "Huda dama ke nake jira kizo inyi miki sallama, babana yace in koma gida saboda aurena ya kusa" Idanun Huda sun ciko da hawaye, tace "Allah ya kiyaye hanya, shike nan bazaka sake dawowa ba?" Saurayin yace "gaskiya da kamar wuya, inayi miki fatan alkairi" Ya wuce shima zuciyarsa babu daɗi, An kammala cin abinci mutane biyu basu bata kuɗi ba, Huda ta miƙe tace "dan girman Allah ku bani kuɗi zan tafi gida", ɗayan ya ciro ɗari biyu ya miƙa mata, Huda tace "hamsin ɗin fa?" Saurayin yace "ki yafemin" Shiru tayi batace komai ba, shiko wanda bai bata kuɗin ba, ashe ya faki idonta ya gudu, gashi kowa ya tafi, Hankalin huda a tashe ta ɗora hannu a kai, kana ta fara hararo masu shagunan gurin, tare da shawarar "gurin wa zataje ya taimaka ya bata kuɗin abincin, gashi jiya tayiwa Umma alƙawarin yau zata ciko mata kuɗin daya ɓata" Ayi min afuwa kwana biyu banyi posting ba, Please a tayani share fisabilillah *💋MU RAYU A TARE💋*               Mom Islam Page 9-10 Jiki a sanyaye ta nufi shagon wani saurayi, yana siyarda manja da man gyaɗa da kuma kayan hatsi, cikin ladabin dole ta durƙusa a gabansa, kafin tace "ina wuni" "Lafiya lau ya kasuwa?" Me shagon yace mata, lokacin da yake fitowa daga cikin shagon sbda ya ganeta, yana yawan ganin an wuce da ita a mashin da kular abinci, "Malam dan Allah ka taimaka ka bani ɗari biyar, Ummana ce tace yau idan ban koma mata da kuɗi sun cika ba, sai tayimin duka" Mai shagon ya girgiza kai, tare da jin takaicin iyaye masu irin wannan halin, kafin ya ciro ɗari biyu, yace mata "nima ban daɗe da dawowa daga kasuwa ba, duk na kashe kuɗina" Da sauri ta karɓi kuɗin jikinta na karkarwa, ta miƙe tanayi masa godiya, A cikin zuciyarta kuwa bayan ta miƙe cewa takeyi "an kashe miciji ba'a sare kansa ba" Tana tafe tana kuka, ta ƙarasa shagon dake can bayan gidan mai, tana shiga shagon mai siyarda su drinks ɗin ta ƙarasa ciki, kasancewar bataga kowa ba, ido shaɓe-shaɓe da hawaye ta durƙusa a gaban mutumin da a ƙalla zeyi shekaru arba'in, kana tace "malam ka taimakeni ka bani ɗari uku, zan cikawa Ummana kuɗin abinci idan na koma gida duka zatayi min" Mutumin ya ce "meyasa zata dukeki?" Huda tayi shiru, sakamakon kukan da ya kuɓce mata, "Zan baki amma nima zaki bani wani abu" Jikin Huda na rawa tace "wlhi zan baka, saboda sam bata ma san abinda yake nufi ba, sbda kwata-kwata shekarunta basu wuce sha huɗu ba, amma Allah ya azurtata da cikar halitta, sbda ƙirjinta a cike yake, idan ka kalleta sai kace mai shekaru sha takwas ko ashirin. Mutumin ya ciro ɗari huɗu, kana ajiye su can kan dogon bencin dake shagonshi, kana yace "idan kika amince dani kinga harda nera ɗari na ƙara miki, yanzu Huda ta fara gano abinda mutumin yake nufi, Tunda ta tuna da dukan da Umman tace zatayi mata, sai taji zuciyarta ta tsinke, sbda idan Umman ta tashi yin duka bata raga mata, musamman ma akan dukiyarta, kamar wacce aka tsikara tace "na amince" Me shagon ya ce "bismillah" Yayi mata alamar ta shigo da hannunsa, ba musu tashigo, ya shiga da takalmanta ciki, kana ya rufe ƙofar shagon, kafin ya rufe sai da ya duba yaga babu kowa sannan ya rufe, kana ya ƙarasa ciki, ya samu huda tana tsaye a raɓe tana kuka, a hankali me shagon ya ƙarasa ya rungumota, tare da miƙa mata ragowar taliya wacce yaci, ya rage, Tana karɓa ta fara ci, kamar wacce ta kwana da yunwa, tana gamawa, ta ajiye robar, ya miƙa mata ruwan wanke hannu ta wanke, kana ya fara matsota tana matsawa baya, har ya ƙureta a jikin bango, Cikin ƙaramar murya yace "idan baki yarda na taɓa nonuwanki ba wlhi bazan baki kuɗin ba" Da sauri Huda ta yaye hijabinta, mai shago ya ɗorata akan cinyarsa ya dinga lugui guice mata nonuwa, yana sauke wani fitinannen nishi, jin bugun ƙofar da akeyi ne ya sanya shi sakinta da sauri, yana cewa "gaskiya idan ina taɓawa  kamar kar in dena, idan kuɗinki ya sake ɓata kullum ki dawo wlhi zan dinga baki, Huda tace "to" jikinta na ci gaba da rawa, Tana kuka ta sanya hijabi tare da riƙe takalmanta a hannu... Shin me zakucewa Huda itada mahaifiyarta??? Nace ba?  idan akayi shar'hi read more 6 zan dinga yi kuma kullum insha Allah Mom Islam *💋MU RAYU A TARE💋*               Mom Islam 11-12 Sai da ya leƙa ta window  yaga me buga ƙofar, kana ya dawo ya zauna, wanda idan ya buɗe masa komai zai iya faruwa, Gurin Huda ya dawo, ya miƙa mata kuɗin kana yace "bari wancan munafikin ya wuce sai ki fita" Huda tace "to" jikinta na ci gaba da rawa. Can anjima da ya tabbatar wanda yazo ya wuce, ya buɗe mata ƙofa ta fita, tare da ƙara jaddada mata idan tana neman cikon kuɗi ta dinga zuwa. Kayan abincin nata ta kwashe ta haɗasu a cikin kular, kasancewarta babba, kana ta tsare me mashin ta gaya masa anguwarsu ta hau, suka tafi. Suna isowa ta nuna masa ƙofar gidansu, ya ajiye, ta sauka ta miƙa masa kudin ya wuce, ita kuma ta shige gida, kanta ɗauke da kular abincin, Da sallama ta shiga, ta samu Umman nata tana kwashe shanya, sakamakon hadari daya haɗo, "sannu da gida Umma" Huda tace, lokacin da ta ƙarasa ciki, cikin dakin fuska Umman tace "yauwa Huda ƴar albarka sannu, da fatan dai anyi ciniki?" "Eh Umma, na dawo miki da bashin da kikebi" Umman na murmishi tace "jeki ɗauki abincinki kici ƴar albarka" Huda zuciyarta a sake ta ƙarasa bakin murhu ta buɗe kwanon abincin nata, ta washe baki, kafin tace "Umma kice mutumina kikayi Umma na washe baki, tace "ai kuwa idan ma zaki ƙara akwai" Huda ta ɗauka ta wuce ɗaki, Tunda ta shiga ta ajiye ɗan waken a gefe, ta fara tuno abubuwan da wannan mai shagon ya dinga yi mata, a zahiri tace "inhar zai dinga bani kuɗi in dawo in samu Ummana cikin farinciki zan dinga zuwa" Kafin ta ɗauki abincin ta fara ci hankali kwance. IFFAT Yau kwananta Uku a asibiti, Hajiya babba ce ta koma kula da ita, Hakeem kuwa ya jingine zuwa aiki, saboda koda wane lokaci ka gansa baya cikin nutsuwa, yau ake saka ran sallamarsu, tunda jikin Iffat ɗin ya sauka, an samu ƙwararrun likitoci wanda sukazo daga waje, duk da taimakon Dady da shugaban asibitin, kasancewarsu abokan juna tun suna makarantar sakandare, idan mutum yaga Iffat komai rashin tausayinka dole ka tausaya mata, duk da uwarta mahaukaciya ce, bai hana jikinta yin kyau ba, ga yalwar gashi, amma yanzu ta koma kamar tsinke tsabar sirantaka, gashin kanta kuwa yayi wani iri, duk da dama ba gyara yake samu ba tun asali. Iffat ɗin na zaune akan cinyar Hakeem wani baturen likita ya shigo, cikin nutsuwa ya kalli Iffat kana yace "insha Allah akwai alamar nasara, a binciken da mukayi mun gano ciwon beyi mata yawa sosai ba" Niko sai kallonsa nake, saboda inda yake magana kai kace wanda yayi rayuwa cikin hausawa. Kafin yaci gaba da cewa, akwai buƙatar ta dinga samun walwalah koda wane lokaci, a guji ɓata mata rai, sauran bayanan zamu rubutasu" Ya nuna Hakeem yace, ya biyoshi office, Kafin ya miƙe ya kamo hannun Iffat yace "tare dake zamu tafi" Iffat kawai kallonsa takeyi amma sam ta kasa magana, sosai takejin bakinta yana yi mata nauyi sosai, haka suka tafi tana ɗan ɗingishi, suka ƙarasa office, aka basu magunguna da sauran abubuwan da ya kamata a kiyaye kana ya miƙawa Iffat hannu, har yanzu kallonsa takeyi, Hakeem ya kamo hannunta yasa ana doctor, kana yace "Kyakkyawar yarinya inayi miki fatan samun lafiya" Hakeem yace "insha Allah" Lokacin da suka dawo ɗakin da aka kwantar da Iffat, dady yazo suka tattara kayan su suka wuce gida. ALHJ AUWAL Bayan ya gama binciken cigaban da aka samu da naƙasun da ya shigo, ya dawo gida da wuri kafin sallamar magriba, sbda lokacin ma ƙarfe biyar ne, tun da su Mahabob da Amani sukaji ƙarar tsayuwar motarsa suka fito da sauri, Amani ta buɗewa Alhaji murfin mota, bayan ya fito Mahabob ya ƙarɓi takardun hannunsa sukayi masa sannu da dawowa, Cike da farinciki Alhaji Auwal yake kallonsu, kafin yace "Aseela da  Inaya ?" Amani tace "Abba suna ciki" Suna tafe suna hira suka ƙarasa cikin gidan, a parlo dukkansu suka yada zango, su Aseela suka fito, ko wanne yana ƙoƙarin tambayar Abban "ya gajiyar aiki" Cike da nuna kulawa yace "Alhmdulilah albishirinku" Dukkansu suka amsa da "goro" suna son a gaya,   musu. "To yau dai burinku ya cika nayi budurwa, yanzu ma zan kirata, amma me kuke ganin zance mata?" Amani tace "Abba Gaskiya ayi bikin da wuri, Mahabob yace "Abba nidai inason kafin bikin dukkanmu har da antyn muje Makkah" Inaya tace "kai bro iyayen ita antyn basu da hankali ne, ba'a ɗaura aure ba zasu bayar da ita?" Aseela tace "nidai Abba kayi mana kaya iri ɗaya da antyn harda kai" Inaya tace "eyeeee Abba zai kawo mana anty" Abban ya ƙyalƙyale da dariya kana yace "Mahabob sai anyi aure, wannan alƙawari ne, harda sabuwar mota zan siya muku kai da Amani da Aseela, ita kuma Inaya zan siya mata kayan wasa" Dukkansu suka fara yi masa godiya, kana gurin yayi shiru, Abba yace "yau anje makaranta kuwa?" Dukkansu sukayi shiru, sbda basu da gaskiya. Mahabob yace "Abba ka kirata mu gaisa" Dukkansu suka matso kusa da Abban, Alh Auwal ya danna number Batool, ring ɗaya zuwa biyu ta ɗaga, cikin zazzaƙar muryarta, kafin tace "Aslamu alaikum Barka da yamma Alhji" Mahabob da Amani da Aseela da Inaya suka zaro ido. Alhji Auwal yace "Barka da fatan kin koma gida lafiya?" Batool tace "lafiya lau" Alhji Auwal yace "ga yarana zaku gaisa", Bata damu ba, tace "to" Cikin nuna ko ɗarr ya bawa Mahabob, ga mamakinta sai taji Muryar ƙato, bayan sun gaisa, aka bawa Amani itama bayan sun gaisa aka miƙawa Aseela, Aseela ta miƙawa Inaya, cikin shagwaɓa Inaya tace "anty ai zaki zamo Mamyn mu ko?" Batool tayi murmishi kafin tace "eh insha Allah, ya sunanki?" Inaya tace "sunana Inaya" Batool tace "masha Allah suna mai daɗi" Kafin Inaya ta miƙawa Abba, Yana dariya yace "kinji Inaya da rigima ko?" Batool tace "uhm" Kana ya sake cewa "ki sanarwa da iyayenki zan aiko magabata na" Nan da nan cikinta ya bada Ƙuuuuu, Sai kuma tace "toh" Sukayi sallama ya ajiye wayar. Acan ɓangaren Batool, suna gama waya da Alhji Auwal, ta fashe da matsanancin kuka, cike da nuna kulawa mahaifiyarta dake zaune akan carpet ta kalleta kafin tace "Batool lafiya naga kina kuka?" Cikin kuka Batool tace "Ummy wlhi wani Alhaji Auwal wanda yake da ma'aikatar sarrafa kayayyaki ne yace yana sona, dalilin haɗuwata dashi, naje Company ɗinsu gurin Sadeƙa, anan ya ganni, yanzu fa muka gaisa da yaransa, harda wani mai babbar murya, duk inda akayi ɗansa ma ya haifeni" Ummy tayi murmishi kafin tace "lallai Batool sai yanzu na tabbatar da ƙuruciya na damunki, kin dangwalo mana arziƙi kina neman yi mana haramiyarsa? kin kuwa san alkairin dake cikin auran wannan mutumin?" Batool tace "Ummy wataran zasu iya dukana fa" Ummy tace "wlhi basu isa ba, jefa baki da wayo, bakisan irinsu masu shekarunan sunfi nunawa yara kulawa ba, bazai taɓa bari a rainaki ba, duk da mahaifinki yanada ɗumbin dukiya amma ai kema kinsan be kamo ƙafar Auwalu ba, inhar na isa dake ki sanarwa da Alhaji kokuma ni in sanar masa" Cikin gamsuwa da maganar Ummynta tace "to Ummy ki sanar masa, nadena tsoro" Kiraye-kirayen sallahar magriba yasa suka bar parlo Ummy ta wuce ɗaki domin tayi alwalah, Batool ma ta wuce ɗakinta. Bayan anyi magriba, har lokacin sallah isha'i yayi, sannan Baban Batool ya dawo, Da sallama ya shigo, Ummy tayi masa sannu da dawowa, haka ma Batool ɗin kafin suka hallara a dining, tuwon shinkafa Ummyn tayi miyar kuɓewa ɗanya wace taji  soyayyen kifi, kana suka fara ci, sam Batool ta kasa zagewa taci abincin sakamakon tunani da yayiwa zuciyarta ƙawanya, Baba yace "Mamana lafiya kuwa?" Kamar wacce ta razana tace "baba babu komai" "A'a ban yarda ba" Ummy ta ajiye cokali kafin tace "Alhji wai dan Alhaji Auwal yace yana sonta shine tabi ta damu mutane" Baba yace "wane Alhji Auwal?" Ummy tace "wanda dai ka sani to shi, ɗan kasuwa" Baba yace "Mamana ke kinyi arziƙi ai ke abin alfaharinki ne ma, ace sunanki ya kewaye duniya" Sunata ƙarfafa mata guwaiwa, har Ummy take gayawa baba cewar gobe zai turo da magabatansa, Baba yayi murna sosai, Acan ɓan garen Alhji Auwal bayan sunyi salloli harda isha'i, kafin suci abinci, Mahabob da Amani, sukace "Abba mu zamu siyo kayan lefe" Alhji Auwal yace "kamar nawa kuke ganin zai isa?" Sukace "sai dai munje gobe amma harda kai ko Abba?" Yana dariya yace "a'a kune zakuje, ai kunsan duk abinda ya dace" MALAM YUSUF. Da ƙyar Juwairiyya ta taimaka masa ya miƙe tsaye, ta ɗauko tabarma wacce take ɗakinta ta shimfiɗa masa,  tasa masa pillow kana ta kwantar dashi, sai wash-wash yakeyi, tanayi masa sannu. A wahalce yace "na rabu da Hajara na huta da ƙaya, Juwairiyya tace "ai kuwa wlhi Baba idan ka samu lafiya ka auro budurwa" Malam Yusuf yace "ina ni ina auran budurwa, ƴan mata yanzu idanuwansu sun buɗe kowacce budurwa zakaji tana cewa sai mai mota. Juwairiyya tace "nima baba ina fatan Allah ya bani mai mota" Tana cikin magana wani yaro ya shigo tare da sallama, Bayan ta amsa, akace wani mutumi yazo yace ayi masa sallama da Juwairiyya, Juwairiyya tace "kace ina zuwa" Ta miƙe tana cewa Allah yasa me mota ne. Ɗakinta ta koma ta feshe jikinta da turare, kana ta lulluɓa mayafi ta fito, A hankali ta kalli saurayin dake tsaye, kyakkyawa dashi son kowa ƙin wanda ya rasa, sai dai jikinsa wata koɗaɗɗiyar rigace wacce ta gaji da duniya, ƙafarsa kuwa tsohon silifas ne shima ba'a magana, a tsanake ta ƙare masa kallo kafin tace "a'uzubillahi wlhi nafi ƙarfin talaucinka, insha Allah sai me mota, ni zaka shafawa farar ƙafa, ma za wuce ka bani guri da jikinka kamar tsohon almajiri" Saurayin yayi murmishi kafin yace "haba ƴan mata, baki tsaya kinji abinda zan..." Kafin yakai ga idda maganar Juwairiyya ta shige ciki, Abokinsa Mubashir ya ƙaraso yana dariya ya taɓa kafaɗarsa kana yace "Prince Abdul ya kamata ka dena wannan basajar da ka ɗauko wa kanka, ka fitowa ƴan mata a kamanninka, nan ne zakaga rububi, mahaifinka sananne ne, kai kuwa kwanan nan ka dawo daga, Bangkok" Prince Abdul yayi murmishi, kana yace "nayi alƙawarin bazan taɓa auran matar da burinta ajiyemin yara da kuma burin mutuwata domin taci gado na, nafison matar da zataji tausayina kana ta soni tsakani da Allah, sannan kuma ta kula dani sannan ta haifamin yara masu tarbiyya, kasan kuwa zansha wahala, kuma yanzu na fara wannan shigar...! Waye shi ? Ya Rayuwar Iffat zata kasance? Ina mahaukaciya Juwairiyya fa? Hajara? Matar tsoho Batool? Idan akayi comments na gobe sai yafi nayau *💋MU RAYU A TARE💋*               Mom Islam 13-14 Kai tsaye su Prince Abdul suka wuce mota. Mubashir ne a mazaunin driver, shikuma Prince Abdul yana kusa dashi, Mubashir ya harari Prince Abdul lokacin da yake tuƙi sun kusa fita a anguwar, dariya kawai Prince Abdul ɗin keyi, sbda haɗe fuska da Mubashir yayi, yasan faɗa zasuyi dole. IFFAT Yau kwanansu biyu da komowa gida, hankulan mutanen gidan duk ya tattara ga Iffat, saboda ta shiga ransu sosai, abin mamaki ko ruwa Iffat batasan ta inda zatasha ba, sai dai Allah bai mantar da

Chapter 2 of 16