An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
*MU RAYU A TARE*
Zainab Habib (Mom Islam
Book1
Page 1-2
Zaune take gaban mahaifiyar tata wacce ta kasance mahaukaciya, Iffat yarinyar ƴar shekara huɗu, tunda ta fara wayo ta gano basu da gidan daya wuce bola, inda taga mahaifiyarta take zama koda yaushe.
Iffat yarinya ce mai wayon gaske, gata da surutu, tana gyarawa mahaifiyarta zani wanda ya buɗe ana ganin ilahirin cinyoyinta, taji ance "kee yarinyar mahaukaciya ungo"
Kafin ta juya taji saukar abu a gabanta, a hankali takai dubanta tare da kunce baƙar ledar dake ɗauke da abinda mutumin ya jefo mata, tana washe baki tace "Umma tuwo ne miyar kuka zakici?"
Umman ta karɓe ledar tare da ajiyewa a gabanta, ta fara ci hannu baka hannu ƙwarya, tunda Iffat taga Umma ta kusa cinye tuwon, ta janye ledar tare da rugawa da gudu, tana gudun tana cin tuwon.
Umma ta miƙe tana wasu irin yaruka wanda Iffat ɗin ta gane me take faɗa amma sam taƙi kula Umman,
UNGUWAR DALA, DAKE CIKIN GARIN KANO.
"Haba Wasila tun ɗazu na kawo cefane amma naga ko tukunya baki ɗora ba?"
Cikin yanayin rashin jin daɗin gane halin da take ciki na hura wutar tace "malam tun ɗazu nasa yara su kwasomin makamashi, wlhi har yanzu basu dawo ba gashi gawayin sam yaƙi kamawa, ko uffan bece ba ya juya yana tsaki, Juwairiyya ta fito riƙe da ƙugu tace "baba.."
Har ya kusa kaiwa bakin ƙofa ya juyo, cike da nuna kulawa yace "ƴar baba ya akayi?"
"Wlhi bacci tasha, har sai da naje na tashe ta , tasan yanzu ƙarfe ɗaya na rana ne, muna jin yunwa amma taƙi ɗora abinci saboda mugunta, baba ni dai na fasa cin abincin"
Malam Yusuf ya dawo da sauri tare da cewa "haba ƴar baba, idan kikace bazakici abinci ba, ki gayamin me zakici?"
Cikin shagwaɓa Juwairiyya tace "baba Fate nakeson sha"
Malam Yusuf yace "ke Hajara, sauke tukunyar shinkafar nan ki ɗora fate"
Cikin ɓacin rai Hajara tace "haba malam gashi nayi sanwa har da kayan miyar, amma zaka ce in sauke?"
Eh ki sauke ki auni masara mudu ɗaya akai ɓarji ga nera hamsin"
"Juwairiyya zoki miƙa niƙan"
"Taɓɓ wlhi nikam yunwa nakeji baba kai dai ka tafi kawai tunda ka faɗi abinda za'ayi"
Malam Yusuf ya wuce yana cewa "ƴar baba kenan"
Yana fita Hajara ta kalli Juwairiyya dake girgiza tana kallon Hajara, cikin tuhuma Hajara tace "idan alkairi kike ƙullawa zaki gani, idan sharri kike ƙullawa duk zaki gani"
Kafin Hajara ta ƙara magana, Juwairiyya taje tai saurin zubar da sanwar abincin da Hajara tayi...
Idan har naga ya samu karɓuwa posting kullum, idan naga akasin hakan to sai sati-sati,
Cikin gadara Juwairiyya take cewa "kin kashe mahaifiyata kina neman mallakemin mahaifi, to ta Allah ba taki ba,"
Cikin tsananin ɓacin rai, Hajara taje ta wanke Juwairiyya da mari, zuciyarta na ƙuna tace "karkiga ina biye miki ba tsoranki nakeji ba, muddin kikace zaki dinga jifana da munanan kalamai wlhi sai nayi maganinki"
Juwairiyya na tsaye riƙe da kumatu, tana bin Hajara da kallon raini,
Kamar inda malam Yusuf ya bata umarnin aunar masara hakan tayi, a gajiye take tafiya har ta isa bakin ƙofar gidan hannunta riƙe da ƙwarwar da ta auno masara, kafin ta ƙwalawa ɗaya daga cikin yaran da suke wasa a ƙofar gidansu ta hango an ɗauke wutar nepa, cikin baƙin cikin hakan, Hajara tace "nepa basu da tabbas ya zanyi nikam?"
Ta wuce gida tana riƙe da ƙwarya a hannunta.
Ko sisi bata dashi bare ta ƙirƙiro dafa wani abun, ruwan sanwar da zata mayar dashi fate, Juwairiyya ta kifar, bata da zaɓin da ya wuce ta koma ta zauna ta zubawa sarautar Allah ido, kana kuma ta jira hukuncin da malam Yusuf zeyi mata.
HUDA
zaune take a ɗan madai-daicin ɗakinsu wanda ya kasance ɗaƙi ɗaya ne suke amfani dashi, kasancewar gidan nasu babu wasu yawaitar ɗakuna, a hankali Huda take bin kowanne sashe na fuskarta tana shafa jar hoda ƴar zazzage, Umma dake tsakar gida ta ƙwala mata kira tare da cewa "Huda yanzu fa muna ƙarfe goma ne na safiya, tun tuni kike kwalliya sai kace mai sauya fata, kin daɗe gurin wanka yanzu ma bakida niyar fitowa naga kamar?"
Da ɗan ƙaramin bakinta na tsiwa tace "Umma gani nan, na gama kaya zansa"
A gurguje Huda tasa doguwar riga ta material wanda yayi mata kyau, duk da ya tsufa,
Tana sanya mayafi ta fito tana cewa "umma nagama ke nake jira"
Umman ta gyara zaman kular data ajiye abincin da bokiti wanda yake ɗauke da robobi da cokula, kana da omo da soso, sai ɗan ƙaramin bokiti mai ɗauke da jar miya taji mangyaɗa, Huda tace "Umma wlhi kafin in ƙarasa bakin titi ina gajiya, kodai inje in taro me mashin ne?"
Kafin Umman tayi magana, daga can waje sukaji ƙarar mashina, Umma tayi waje da gudu tana gyara ɗaurin zani, tana leƙawa ta ƙwala wa me mashin ɗin kira, me mashin yace "yana jira"
Umma ta dawo cikin gida ta samu har Huda ta kwaso kayan, Umman ta tayata miƙo ragowar, kana ta kunto bakin zaninta ta miƙawa Huda nera ɗari tace "Allah ya kiyaye hanya, saura inji kin dawo kince wani yaci be baki kuɗi ba, wlhi sai na lahira yafiki jin daɗi, dan bazaki mai dani...
Mai mashin yai saurin figarsu da gudu, sbda ya gaji dajin kalaman Umman, ya girgiza kai.
Tana isowa gidan mai, kafin takai ga sauka daga kan mashin samarin gurin suka taso suna shewa suna sauke mata kayan abincin, Huda ta miƙawa me mashin kuɗinsa ya wuce, ta kalli samarin tana murmishi tace "kodai kunci kun ƙoshi ne shiyasa kuketa yimin dariya?"
Ɗaya daga cikinsu yace "mun isa ai bamu isa muci abincin wata yarinya anan ba, dole naki zamu jira,
Huda tasa dariya, ta gyara zaman kayan a cikin wata ƴar rumfa, kana ta nemi gefen dogon benci ta zauna, sha biyu na rana, mutane suka fara zuwa, tana zuba musu, harda samarin gurin, wani saurayi yaci abinci be bata kuɗi ba, ta miƙe tsaye sbda taga ze tafi tace "malam baka bani kuɗina ba?"
Cikin masifa da tsageranci saurayin yace "na ƙarfi ne naci kuma bazan bayarba"
Huda tace "kaje kaci nacan wlhi sai Allah ya sakamin"
Saurayin ya ɗaga hannu ze mareta, wani daga cikin wanda suke siyan abincinta ya taso yana cewa "amma baka da imani, kaci abincinta ka hanata kuɗi, har Kanada ikon dukanta?"
"Eh ance baza'a bada ba ko Kanada abinda zakayi ne?"
Mai kare Huda yace "eh yanzu ma kuwa"
Kafin wanda ya shigarwa Huda ya zaro bel, saurayin ya gudu,
Huda ta fashe da kuka gashi abinci ya ƙare, tsabar tunanin kuɗin hannun wannan saurayin ta cikawa mutane abinci,
"Kiyi haƙuri Huda, nawa ne kuɗin wancan ɗan iskan gayen?"
Huda tace "ɗari uku"
Saurayin yace "ga ɗari biyar ki ajiye a gurinki, gobe zanci abinci"
Huda tayi godiya, sai a lokacin taji mugun sanyi a ranta, ta tattara kayan abincin, harda robobin da bata wanke ba ta tari mashin ta wuce gida.
IFFAT
Yamma tayi sosai, ga wani gagarumin hadari ya haɗa, Iffat ta kamo hannun Umman ta tana cewa "Umma zomu samu gida, ruwa ze jiƙaki"
Mahaukaciyar sai wasu irin abubuwa take, tana ta fizge-fizge, da soshe-soshe, Iffat ta tattaro ƙarfinta ta turo Umman nata, kafin ta kamo hannunta sunata tafiya, a barandar wani gida suka zauna, Iffat ta kalli sama, tace "Umma ruwan ya fara zubowa"
Kasancewar ba magana mahaukaciyar takeyi ba, yasa ta ƙurawa Iffat ɗin ido kamar me shirin yin magana, me gidan ya fito yana ganinsu, ya haska fitila, kana yace "ke riƙe hannun mahaukaciya kuyi wani gurin, tsabar iskanci ku rasa inda zaku zauna se nan gurin?"
Iffat tace "malam ka bawa Ummana abinci dan Allah yunwa takeji"
Cike da masifa yaci gaba da cewa "dalla tashi anan yunwo"
Iffat ta kamo hannun Umman ta suka bar gurin, suna cikin tafiya, wani mutumi ya kira Iffat, a tare suke tafiya da Umman nata har suka iso gurin Mutumin, ya miƙawa Iffat dubu ɗaya, kana yace "jeki cikin kasuwa ki siyo muku kayan shayi"
Yasan suna cikin tsananin jin yunwa, sbda yana gani aka koresu.
Iffat ta karɓi kuɗin kana ta ruga a guje tana fara'a, duk da ana shirin kiran sallahar magriba,
A hankali wannan mutumin ya fara tunkaro mahaukaciyar yana wani irin murmishi, daga karshe ya cafke ta ya sanyata a motarsa wacce ya parkata can nesa dasu, motar babba ce irin Sharon ɗinnan, ya tura mahaukaciya a ciki yabar anguwar da ita,
Tana ta buge- bugen gilashin motar da surutai, hakan besa yaji tsusayinta ya ajiyeta a kusa ba, sai da ya iso can bayan gari, gurin babu mutane sai gonaki, hanyar ma, ba kasafai mutane suke Bin ta ba, sai uzirinsu ya kawosu, bayan yayi parking ya kwantar da kujerar gaba tare da kallon baƙin tinted baƙi na gilashin motar, kana ya cire rigarsa ya kuma cire wandonsa, ya rage saura gajere.
ALHAJI AUWAL
Babban ɗan kasuwa a Bauchi, birni da ƙauye babu wanda be san sunansa ko labarinsa ba, ya shahara sosai yana uku daga cikin masu kuɗaɗen NIGERIA.
Zaune take a katafaren parlonsu, wanda yake fidda ni'im taccen sanyi da sanyayyayen ƙamshi mai kwantar da hankalin wanda ya shaƙar, yarinyar ƴar shekara goma sha biyar ta fito hannunta riƙe da tsadaddiyar waya I phone 13pro, a yanayin inda tayi da fuskarta dole abin zai bawa mai karatu dariya, a hakan wai fushi takeyi, cikin girmamawa taɗan risina, sakamakon ganin fitowar Abban nata, "good morning Abba"
"Morning how are you?"
Cikin shagoɓa Amani tace "Abba ina lafiya sai dai akwai wata ƴar matsala"
Cike da nuna kulawa Abban yake kallon ta kana yace "my lovely daughter meke faruwa?"
"Abba inason kayi aure, tun bayan rasuwar Ummi ko maganar aure bakayi, ko jiya ma sai da mukayi shawara da bro Mahaboob da aunty Aseela da Inaya, sukace ya dace"
Abba ya nemi guri ya zauna tare da zuba mata idanu, kafin yace "zanyi shawara amma kafin nan meyasa kikeson inyi aure?"
Amani ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta, kafin ta buɗe tace "Abbana kodan ta dinga yi maka abinda kakeso, kaga duka abokanka sunada mata kaine kawai baka da ita"
Abba yace "shi kenan naji, amman nikam dalilin da yasa naƙi aure, banason in auri matar da zata dinga takura muku"
Amani tace "Abba karka damu"
IFFAT
Da gudu ta dawo tana cewa "Umma ga kayan shayin, kinga me shayin ma har a kofinsa ya zuba miki"
Shirun da taji ne yasata sake leƙa inda suke kwana, wato gefen bola taga wayam babu Umman, cikin ɗaga murya, tana shirin yin kuka tace "Ummaaaa naaa mahaukaciyataaaa"
Duk da haka babu wanda ya fito bare yasan ga halin da take ciki, hankali a tashe Iffat ta fara zagaye unguwa tana ƙwalawa Ummanta kira, sam ta gagara zama tasha shayin sai yawo takeyi dashi a hannu...!
Page 3-4
Tana cikin tafiya tayi karo da ƙaton dutse wanda yai sanadiyar kai ta ƙasa, cikin kuka Iffat ta taɓi bakinta wanda yakeyi mata zugi, hannun nata ta kalla, ganin jini ya sanyata fashewa da kuka tana yarfe hannaye, daga can gefe shayin da bredin ya zube, bredin ne dai beyi komai ba, dan haka ta miƙe tana karkaɗe jikinta ta, kasancewar garin yayi duhu, yasa bata hango kofin ba, ta riƙe bradin taci gaba da tafiya tana kuka.
A hankali mutumin ya raba mahaukaciya da zanin jikinta, idan mai karatu yaga mahaukaciyar nan, wlhi bazai fara tunkararta ba, duba da inda jikinta yake fitar da tiririn wari, marar daɗi,
A haka ya faɗa mata ya dinga sukuwa a kanta, daga ƙarshe ya wani shigeta da ƙarfin bala'i har ƙafafuwansa na rawa, kafin ya ɗaura mata zaninta kamar inda ya ganta, shima ya mayar da kayansa, yasa tissue paper ya goge gurin ya fesa turare, kana ya bar gurin da motarsa,
Suna tafe yana waya, sai cewa yake "ai nasamu na kwashi gara duk da mahaukaciyar ba wata babba bace amma wlhi tayi daɗi".
Kafin mutumin yayi parking a inda ya ɗaukota, ya waiga ko ina baiga kowa ba, kana ya ajiyeta tana dukansa, harda cafke masa riga, yai saurin ƙwacewa ya ƙara da gudu, tare da shigewa mota.
Iffat kuwa tayi nisa da anguwar sosai, saboda tsakaninta da inda aka dawo da mahaukaciya yakai nera ɗari, babu wanda ya ganta ya taimaka mata, haka ta dinga tafiya har, takai bakin titin anguwar da suke, wato ɗorayi, tana kuka ta nufi bakin titi ko waigawa batayi ba, sai ji kake ƙuuuuu...ƙiiii..., kafin kace me, wanda basu ga tsayuwar yarinyar ba duk suka hallara a gurin, sakamakon ƙugin motar da suka ji,
Kowa sai ambatar "innalilahi wa inna ilaihir raji'un" yakeyi, a gigice mamallakin motar ya fito, hankalinsa a tashe yana cewa "ku taimaka ku samin ita a mota wani ya biyoni mu kaita asibiti"
Wanda ya taya mai motar sa Iffat a mota, shine yabi mai motar suka wuce asibitin Murtala.
Suna isa aka karɓesu cikin kulawa, sakamakon jinin da yake kokawar kwaranyowa jikinta, aka wuce da ita ɗakin gaggawa,
Sosai suka fara bata kulawa ta musamman, kafin suka sanar musu da cewar "dole zata iya kaiwa gobe, bazai yiwu a sallameta a yau ba"
Hakeem ya danna number Hajiya babba, cikin wani irin yanayi na damuwa yace "Hajiya babba nayi hatsari a hanyar ɗorayi, nidai banji ciwo ba, amma yarinyar taci ciwo, bazan dawo gida yau ba sai zuwa gobe, dan Allah ki sanarwa da Hajiya ƙarama da Dady"
Cike da nuna kulawa Hajiyar tace "Allah ya cigaba da karamin kai yarona"
Hakeem ya amsa da "Amin"
Kafin tace "muma goben zamu taho da izinin Ubangiji"
Yace "Allah ya kawoku"
Bayan an gama gyara Iffat, barci mai nauyi ya ɗauke ta, doctor ya kira Hakeem zuwa office, cikin azama Hakeem ɗin ya bishi, anan ne doctor yake tambayarsa "ina iyayen Iffat?"
Hakeem ya sunkuyar da kansa ƙasa, kana yace, "sir a bakin titi na ganta, banma lura tana gurin ba, kawai ƙarar motata ne ya fargar dani, na tambayi wani mutumi wanda suka taimaka min gurin kawota da sanyata a mota, sunce basu santa ba"
Likitan ya girgiza kai kana yace "gaskiya bazan ɓoye maka ba, yarinyar ta samu ciwon taɓuwar ƙwa-ƙwalwa, ba komai zata iya fahimta a yanzu ba, sai dai nan gaba insha Allah idan kuka kiyaye maganin da zamu ɗoraku akai, abubuwan zasu dinga warwarewa a hankali, sannan a kiyaye ɓata mata rai..
*💋MU RAYU A TARE💋*
True life story
Mom Islam
Page 5-6
Hakeem yace "insha Allah doctor"
Kafin doctor ɗin yace "zaka iya tafiya"
Jikin Hakeem a sanyaye ya dawo harabar asibitin, ya samu jerin kujerun da suke ajiye a gurin ya zauna akai, hankali a tashe ya fara tunowa da illata rayuwar ƙaramar yarinya da yayi, besan iyayenta ba, bai ma san ta inda zai fara nemansu ba, a hankali wasu siraran hawaye suka zubo masa, yasa lallausan hannunsa ya share tare da ambaton "innalilahi wa inna ilaihir raji'un" kafin ya kalli mutumin da suka zo tare wanda, tunda Hakeem ɗin ya shigo yake kallonsa, a hankali mutumin ya ƙaraso jikinsa a sanyaye ya dafa kafaɗar Hakeem, kana yace "bawan Allah ni zan koma gida, iyalina zasu shiga tunani da fargaba tunda ba waya ne dani ba, ka kwantar da hankalinka, ko ban dawo ba idan an sallameku ka tafi da ita gidanku, duk da ban sanka ba, kuma ban taɓa ganinka ba, nasan kai mutumin ƙwarai ne ba mai cutarwa ba, zaka kula da ita inda ya kamata".
Hakeem ya sake share hawayen da suka ƙara samun nasarar zubo masa, murya a disashe yace "Nagode Nagode Allah ya tashemu lafiya, ga numberta ko zaka buƙaci magana dani"
Mutumin ya karɓa yana yiwa Hakeem godiya kana ya wuce.
Duniya tayiwa Hakeem zafi, duk da zamu kirashi mai ƙarancin shekaru, dan tunda ya taso ko a tv bai taɓa ganin inda akayi hatsari ƙwa-ƙwalwa ta bugu tashi ɗaya ba, har ya fara zargin kodai likitan ƙarya yayi masa,
Kamar wanda aka tsikara ya matsa jikin tagar asibitin, ya kafa idanunsa a gilashin tagar yana hango Iffat an naɗe mata kanta, sai wani irin numfashi take,
A razane ya sake kai kallonsa gareta ya kuma fashewa da kuka, kafin daga baya ya fara tunanin ya za'ayi taci abinci?,
Yanke shawarar komawa gurin likita yayi, cikin azama ya nufi ofishin likitan, yana zuwa kai tsaye ba tare da neman izinin shiga ba, ya shige,
"Likita nace marar lafiyar zata iya cin abinci kuwa?"
Hakeem ya faɗa yana tsaye a bakin ƙofa,
"Babu buƙatar cin abinci sai zuwa gobe insha Allah"
Jikin Hakeem a sanyaye ya koma ya zauna, a haka har gari ya waye ko runtsawa beyi ba, kafin a shiga sallar asuba yaje yayi alwala ya fara nafila har aka shiga sallah, bayan an idar ya ɗaga hannuwansa sama yana roƙawa Iffat lafiya a gurin Allah, har kowa ya fice aka barshi shi kaɗai, daga ƙarshe ya fito, tare da kallon harabar asibitin, duk da bawai gari yayi haske sosai bane.
Sai yanzu ya tuna tun dare da ya kashe wayarsa be kunna ba, ya cirota kana ya kunna, kafin ya cire a security kiran dady ya shigo, Dady yace "suna mota Hakeem ya gaya musu sunan asibitin, bayan Hakeem ɗin ya sanar dasu suka kamo hanya,
Shikuma Hakeem ɗin ya ƙarasa cikin asibitin, yana shiga ya doshi ɗakin Iffat, wani likita ya dakatar da Hakeem yana cewa "kaine ka kawo wata yarinya?"
Jikin Hakeem na rawa yace "eh nine lafiya?"
Likitan yace "akwai buƙatar a samo mata ruwan kunu ko shayi tasha"
Hakeem yace "insha Allah"
Jin Muryar su Hajiya babba yasa Hakeem juyawa yana yi musu sannu da zuwa, kafin ya nuna musu ɗakin da Iffat ke kwance har yanzu da oxygen a hancinta, jikin Hajiya ƙarama yayi sanyi matuƙa, sai kallon Iffat takeyi, wacce take ta rarraba idanu tana kallonsu kamar yau tazo duniya,
"Dady yace "iyayenta fa?"
Hakeem yace "dady kowa na tambaya cewa yakeyi be taɓa ganinta ba"
Dadyn yace "amma ya yanayin jikin nata?"
Hakeem yace "dady har yanzu dai banji tayi magana ba, duk da akwai abun numfashi a tare da ita, amma ance ƙwa-ƙwalwarta ta taɓu"
Dukkansu suka kama salati Hajiya babba tace "yanzu aiki kenan zasuyi mata ?"
Hakeem yace "wlhi nidai ban sani ba, gadai shi nan mun zuba musu ido"
Dady yayi shiru, tausayin yarinyar ya kamashi, yana son gano inda yasan yarinyar amma ya kasa ganowa, haka dai ya haƙura, ya kawar da tunanin ta, suna zaune likita ya shigo da kayan aiki, ya cire mata abin numfashin kana ya sake yi mata wasu gwaje-gwaje, kana yace "sannunku, zaku iya bata abinci amma marar tauri, suka amsa da "to"
BAUCHI
Cikin shirin tafiya aiki Alhaji Auwal ya fito, hannunsa riƙe da ja ka irin wacce ma'aikata suke riƙewa,
Amani ta fito riƙe da hular Alhaji Auwal a hannunta, ita kuma Aseela hannunta na riƙe da turare, Amani ta sanya wa Abba hula, Aseela ta fesa masa turare, Mahabob kuma yana riƙe da mukulin motar Abban, Inaya ta fito a shagwaɓe, kasancewar itace autarsu, Abba na ganinta yace "ƴar albarka lafiya?"
"Abba aunty Aseela ce ta hanani wayarta, inyi Game"
Abba yayi dariya, shi yama ɗauka wani babban abu ne, cikin sigar lallashi yace "karki damu zan siya miki sabuwa, Aseela ayi haƙuri a bata kafin in siyo mata nata"
Aseela ta shagwaɓe fuska tace "Abba wlhi ta fiye shige-shige ne"
Kana Aseela ta miƙa mata wayar, ta koma ciki da gudu su kuma suka fita raka Abba parking space,
Suna tsaye ya shiga mota, Mahabob ya miƙawa driver key, suka yiwa Abba adu'ar Allah ya tsare, kana suka koma ciki.
Tunda suka dawo, suka kafa meeting, akan auran da suke son Abban nasu yayi, sunata adu'ar Allah ya haɗashi da mata ta gari mai tausayinsa,
A hankali drivern yayi tuƙi har suka iso ma'aikatar Alhaji Auwal ɗin ta ƙera kayayyaki, musamman atamfofi da rigunan sanyi, bayan drivern yayi parking an buɗewa Alhaji Auwal ya fito, idanunsa yai tozali da wata budurwa ta fito daga wani office, cikin nutsu yake kallonta har ta ƙaraso ta wucesu, ya ɗan tafi da sasarfa, kana ya tsaya ƙyam, yace "Ahmadu driver kiramin waccar yarinyar, cikin mamaki Ahmadu yace "to" har ta kusa fita daga get ɗin ya isar da saƙon Alhajin, jin ance mata Alhaji Auwal ne yake kiranta, sai ta fara rawar kai da rawar jiki, tunda ta sanshi tasan labarinsa, labarin gidansa ne bata sani ba, cikin nutsuwa ta iso gareshi, driver ya wuce, kana ta durƙusa ta gaishe shi, cikin farinciki da yabawa da hankalinta da yayi ya gyara tsayuwa, kana yace "sunana Alhaji Auwal"
A hankali budurwar tace "masha Allah" kana yace ko zan iya sanin sunanki?"
A kunyace budurwar tace "sunana Batool"
Allhji Auwal yace "masha Allah, idan bazaki damu ba ina sonki, so bana wasa ba so na aure, kinsan dai ni ba yaro bane"
Batool tace "to Alhaji yanzu zanje gida babana yanata kirana"
Alhajin ya karɓi number wayarta tare da ciro kuɗi har kimanin 20k ya bata kana sukayi sallama,
Tana tafe gabanta na ci gaba da faɗuwa, a zahiri bawai kiran nata akeyi ba, ƙafafuwan ta ne suka gaza ɗaukarta dan haka ta samo mafitar faɗan haka, Alhaji Auwal yayi murmishi, bai bar gurin ba har sai da Batool ta ɓace, kana ya shiga ciki,
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
7-8
Da sallama Huda ta shigo ita da wasu yara guda biyu, ɗaya yana riƙe da kular abincin siyarwarta, ɗaya yana riƙe da bokitin miya, ita kuma tana riƙe da robar soso da omo,
Daga inda Umma take zaune ta amsa tare da cewa "oyoyo Huda ƴar albarka, an siyar da abincin duka ko?"
Huda na murmishi tana kallon yaran da suka ajiye mata kaya tace "na gode" suka wuce.
Kafin tace "Umma an siyar amma naga kuɗin bekai kamar na jiya ba"
Cike da ruwan bala'i Umma tace "ni zaki mayar ƴar iska wacce batasan abinda takeyi ba, in tashi tun asuba in hana idona runtsawa kuma in hana jikina hutu, amma kicemin kuɗin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 16