na jira. Samira tace a'a gaskiyq ban
yarda ba. Dole suka koma da ita don tace
bazata sharada ba gidan Hajja.
A asibiti Amal na tsaye gaban gadon Ya Rayyan
tace kayi hakuri yaya bansan kafi son Ju a kaina
ba. Ni na hakura idan an ganta a kai maka ita
gidanka. Tana fadin haka ta juya zata fita Mami
tace Amal ko ciwon da kikayi ne ya taba miki
kai ace ko tausayin halin da yan uwanki ke ciki
baya damunki. Ya Sagir ne ya ja hannunta suka
fita waje.
Cikin mota suka shiga tana masa kuka yace
wallahi idan bakiyi shiru ba zan miki dukan tsiya
a wurin nan. Yanzu Amal ina iliminki da hankali
ya tafi? Na zata ko yau Ju ce ta wayi gari tace
tana son Rayyan ke me bashi shawarar aurenta
ce. Nan ya rinka yi mata fada da nasiha karshe
yace Amal ina ji miki tsoron zama daga cikin
mutane masu butulcewa rahmar Allah. Da Yaso
fa da kina nan kamar karamar yarinya ita kuma
a kaita gidan idan sun so su kula dake idan
sunki su cutar dake. Ni shawara kawai na baki
kiji tsoron Allah. Amal tace nima abin na damu
na Yaya kishi ne yake sani yin hakan.
******************
Washegai Fauza da Nafisa ne a gidansu Samira
bayan sun gaisa da Ummansu Fauza tace ni
kawar Samira ce tare muka yi secondary school
ta fada min zata yi aure amma bana gari shine
nazo a raka ni gidanta don wayata ta fadi bani
da number dinta. Umman Samira ta kira kaninta
tace ya rakasu. A waje Yasmin tace dana biku
zata ganeni. Allah Yasa tana gidan dai.
π JUWAIRIYYA π 20
Kamar muryar Fauza nake ji fa Ju ta ce da
Samira. Sallamar suka sake ji Samira ta je ta
bude kofa. Fauza ce tare da Yasmin da Nafisa.
Su hudun rungume juna suka yi suna kuka.
Bayan sun gama bata labarin duk abinda ya faru
bayan tafiyarta harda rashin lafiyar Ya Rayyan
,Ju ta share hawaye tace ni ya zanyi ne da
raina? Idan na aka bar auren nan zumunci sai
ya tabu haka ma idan aka raba. Nafisa tace kiyi
hakuri mu koma gidan Dada wallahi Mama ko
abinci bata iya ci. Yasmin tace amma dai zaki
zo duba Ya Rayyan ko. Murmushin yake tayi
wanda yafi kuka ciwo tace in sha Allah.
Yaya mun nemo Ju tana gidan Dada abinda
Fauza ta radawa Rayyan kenan a kunne. Yayi
kokarin tashi zaune amma jikinsa babu kwari
yace kin tabbata ta gyada masa kai.
Alhamdulillah yace da har Mami da Ya Sagir
suka ji Mami tace me ya faru? Bai iya bata
amsa ba sai Fauza ce tace Mami mun nemo Ju
dazu mun kaita gidan Dada.
Mama Allah lafiyata kalau abinda Ju ke ta
fadawa mamanta kenan wadda tun shigowarsu
gidan take ta juyata tana shafa mata jiki tare da
tambayar babu inda ke miki ciwo ko. Dada tana
daga gefe ta kalli Baba wanda sai murmushi
yake tace kaga rashin kunya ko? Da sai ka zata
bata son yarta she dai tana zuci.
*********************
Mami da Amal ne suka shigo gidan Dada kowa
ya bisu da kallo. Ju ce tayi kokarin gaishe da
Mami. Amal sai taje ta rike hannun kanwarta
tace Ju kiyi hakuri da abinda ya faru nasan ban
kyauta ba. Dama nasan bazan taba iya saka
miki ba wannan sai Allah amma yanzu a gaban
iyayenmu nayi miki alkawarin bazan taba zama
silar mutuwar aurenki ba. Idan har akayi kokarin
raba aurenki da Ya Rayyan to nima nayi
alkawarin bazan taba zaman aure dashi ba.
Iyayensu mata harma da Dada sai kuka. Mami
tace Mariya kiyi hakuri naso na biyewa sharrin
zuciya na watsa zumuncin mu. Itama Mama
tace nima ki yafe min Yaya. Dada cikin murna
tace Allah Yayi muku albarka. Baba Idris baki
har kunne don farinciki yace Alhamdulillah tunda
Allah Ya korar mana shedan Allah Ya kara hada
kawunan mu.
Mami dai ta kawo shawarar a hada su duka ayi
biki tare nan Baba yace a'a Haj Asiya ni tawa
shawarar shine a fara bikin da Amal bayan
shekara daya sai Juwairiyya ta tare hakan zaifi.
Mami tace dama abinda Baba likita yace zai
fada maka kenan idan ka yarda. Baba yace ni na
amince. Allah Ya basu zaman lafiya.
Ju da Amal da suke cikin daki suna jin hirar
iyayen nasu. Amal tace Ju kin amince da
hakan? Ju tace kai yaya ba dole ba Allah Yasa
kafin nan ma kin haihu. Nan Amal tayi mata
dundu a baya. Ju ta kwalla kara Mama tayi
saurin cewa lafiya? Suna shiga suka gansu suna
dariya. Har zuciyarta Mami taji dadi sosai yadda
suka hade kansu. Ita kuwa Mama murde musu
kunne tayi.
*******************
Yau dai falon Hajja alkhairi aka kulla aka tashi
cikin farin ciki da annashuwa. Kamar yadda
Baba ya fada Amal ce zata fara tarewa.
Gaban Ju har faduwa yake ta tsaya kofar dakin
da aka kwantar da Ya Rayyan. Amal ce ta fito
tace to ni zan tafi nayi kanwata na bashi hakuri
tare da tabbatar masa mun hada kanmu. Ju ta
tsaya kamar an kafe ta don wata irin kunya take
ji. Amal kuwa tura ta tayi tace anjima zan dawo
sai mu tafi gida yanzu wurin neman venue zamu
da Fauza da anti Habiba.
Ju tana shiga dakin taji an rufe kofar an
rungumeta ta baya. Tana kokarin gudu taji ya
rada mata a kunne keep still. Tsayawa tayi
kamar yadda ya umarceta. Sunyi kusan 5 mins a
haka sannan ya ja hannunta suka zauna a bakin
gado. Duk kunya ta rufe Ju yace ba gaisuwa?
Tayi saurin sauka tace ina yini ya jiki? Da sauki
tunda kinga damar zuwa dubani. Ju bata ce
komai ba ya cigaba da maganarsa da baki dawo
ba da aurena zaki mutu ko ina zaki a duniya
don bazan sake ki ba. Allah Ya sa na iya hakuri
har sai an shekara kafin a kawoki.
π JUWAIRIYYA π 21
Bata ce komai ba yana ta surutunsa shi kadai.
Wai dama haka Ya Rayyan yake ta fada a zuci.
Sai yayi ta wani shiru shiru kamar baya magana.
A nan ta yini abinci ma ranar a plate daya suka
ci don cewa yayi bazai ci ba idan bata sa hannu
ba. Amal ta dawo tare da Fauza suka dan taba
hira sannan suka tafi.
Yau saura kwana uku bikin su Amal gida ya cika
da 'yan uwa na nesa harda su Mama. Dinkunan
amare duk iri daya akayi ita kuma Ju da su
Yasmin da kannenta nasu dinkin iri daya. Mami
wani special kulawa take bawa Ju. Ya Rayyan
dai ba karamin farinciki yake ba domin yadda
yaga matan nasa sun cigaba da rayuwa kamar
yan uwa.
Anyi kamu a gidan Hajja ranar ba karamin kyau
amaren sukayi ba. Itama Ju tayi kyau sosai
tasha gwaggwaro ga kunshi mai kyau kafa da
hannu. Washegari yini akayi sannan aka kai
amare wadanda suka sha kukan rabuwa da gida.
Ju a gayyar Fauza ta tafi daga nan suka shirya
zuwa wurin dinner wadda Ya Rayyan da Abbas
suka shirya. Kaya Bidaya tazo dasu a leda ta
bawa Ju inji Rayyan. Wani lace ne white and
purple anyi masa dinkin skirt da riga sai
dankwalinsa, mayafi fari mai kyau da takalmi da
jaka purple. Ju tana juya kayan tace ya akayi
Yaya yasan size dina? Fauza wadda akeyi wa
kwalliya tace ni na kai dinkin i hope yayi kyau.
Shoe and bag kuwa zabinsa ne. Ju tace to
ankon mu dasu Yasmin fa. Fauza tayi dariya
zaki fara sabawa miji akan anko ko? To dai an
daura miki aure don haka dole abi Yaya da
kannen yaya ma ta fada tana kanne mata ido.
Taro ya kayatar sosai musamman shigowar
angwayen da amaren su. Ju dake tsaye bayan
amaren yau itama taji kishi a ranta amma tayi
saurin kawar da abin ta hanyar neman tsari
daga sharrin shedan. anyi taro an gama lafiya
sunfito duk zasu tafi Abdul ne zai ja motar su
Ju. Amal ce ta kula Ya Rayyan duk bashi da
sukuni tace Yayana kaje kayi sallama da Ju
mana zan jira ka. Harararta yayi kyaleta kawai
mu tafi. Kaga dai ka fita nasan kana son zuwa
am not that selfish fa. Waya yayi mata tana
dauka yace karaso wurin mota ina jiranki. Tana
zuwa tace Ya Amal kinyi kyau sosai Amal tace
nagode bari na karbi sako wurin Yasmin. Tana
fita ta share kwalla gaskiya kishi sai an daure.
Ya Rayyan kallon Ju yayi yace sweet Ju Allah
Ya kaimu ranar da zaki tare duk da bana jin
zanyi hakurin shekara daya. A zuci tace amin
amma ya kamata ku tafi haka sai da safe.
Korata kike ko? Nagode kada ki kashe waya dai.
Tana juya baya taji yace I love you tace me too
a hankali sannan ta tafi.
Ju ta fara karatunta a saa tana degree a
Nursing sabon department din da aka bude a
buk. Ya Rayyan kuwa kullum zai zo gida ya
ganta. Ko kadan ta dena bari su hadu inda ba
mutane don yana ganinta sai ya taba ko da
hannunta ne. Duk dare kuma zai mata waya ko
suyi chatting
a whatsapp.
Ju an gama exams tun safe yau ta hada kaya
zata tafi Wudil. Ya Rayyan yace zai kaita ya
gaisa dasu Mama. Supermarket ya fara kaita
yayi wa iyayenta siyayya sannan suka dau
hanya. karatu ya kunna musu Ju ta fara rufe ido
yace sweet Ju a hankali ta amsa da kyar don
bacci ya fara daukarta. Parking yayi a gaba
kadan da wani kauye yana kallonta. Jin alamar
sun dena tafiya yasa ta farka yaya lafiya kuwa.
Yace ina fa lafiya sweet Ju zata haukata ni. Ta
zare idanu me nayi maka yace sace min zuciya
mana cikin karamar murya. Tace Allah yaya ka
fiye shagwaba haka ka koma magana kuma.
Yace yarinya ban fara komai ba ma amma bari
kiga kadan. Matso da fuskarsa yayi daf da tata
tayi saurin rufe ido ya kama hannunta ya dora
kan kirjinsa bude idonki tace a'a, musu da miji
ko sai ta bude a hankali yace sweet Ju kinji
yadda zuciyata ke bugawa akanki? Don Allah
kice kina sona ko sau daya ne duk ya marairaice
mata. Tausayi ya bata duk da tanajin kunya tace
I love you Ya RΓ yyan. Kissing din hannunta yayi
yace kinga yadda ake shagwaba kasa mutum
yayi abu ko baiyi niyya ba. Lallai yaya kayi min
1-0 amma zan rama. Ya ce eyye ramuwa akan
miji tace eh. Dariya yayi suka tafi cikin nishadi.
Sweet Ju ta Ya Rayyan
π JUWAIRIYYA π 22
Yau watan Amal takwas da tarewa amma an
hana Ju zuwa gidan sai ranar tarewarta. Sai dai
kullum suna waya balle da Amal din ta sami ciki.
A gajiye take tana cin abinci bayan ta dawo
daga makaranta Mami ta shigo dakin ta zauna
bakin gado tace Juwairiyya wane kalar curtain
kike so a falo. Ju ta sunkuyar da kai kai Mami
ni kowanne ma. Bikin ma ai akwai lokaci Mami
tace mai kwarmin ido da wuri yake fara kuka
Juwairiyya ko kin manta ranar asabar zaa kai
kayan yayanki Sagir gara ma hada bikin ke da
Nafisan kawai.
Ranar asabar ana ta shirye shiryen tafiya Wudil
kai kaya Amal ma ta dage zata je Ya Rayyan ya
hanata da kuka ta shigo gidan Umma na bata
hakuri karshe dai dole aka tafi da ita. Zata shiga
mota harda yi ma Ya Rayyan gwalo. Sunje Wudil
lafiya sai a hanyar dawowa ne Ya Aliyu ya fada
wani rami. Nan fa cikin Amal ya fara murdawa
kafin su iso kano jini ya balle mata.
*********************
A asibiti Rayyan ya same su an samu jinin ya
tsaya sai dai kuma Amal ta fara nakuda gashi
cikin watansa bakwai. Hankalin kowa a tashe
yake musamman Rayyan fita akayi aka barsu a
gaban gadon ya durkusa ya rike mata hannu
tana cizon lebe. Tace Sweet Yaya yana dago kai
yaga ta rike kunnuwanta biyu. Nan hawayen da
yake rikewa suka zubo tace kayi hakuri banbi
umarnin ka ba daga yau dan ba kara. Da
hawayen yayi murmushi yace sweet Amal ai ba
fushi nayi ba. Allah Ya saukeki lafiya kuma Ya
baki lafiya. Tace amin ka fita kuyi ta min addua
yanzu zaa kaini dakin gashi,wani murmushin
yayi ya ja mata hanci I want a beautiful baby
like you Habiba.
Jikin Ju har rawa yake da taga yadda Amal ke
gumi ta taba Mami tace haka ake haihuwar to ni
na yafe. Mami tayi karfin halin murmushi eh
mana Juwairiyya ke da zaki haifo mana dozen.
Nurses biyu ne da wata doctor akan Amal ana
ta kokarin ceton ranta dana abinda ke cikin. Da
gudu nurse ta fito daga dakin Rayyan yana
tambayar lafiya bata kula shi ba ta wuce. Jinin
da Ju ta gani a jikin hand gloves din nurse din
yasa ta fadi kasa a sume nan Rayyan ya
kwasheta ya kaita wani dakin abin duniya yayi
mada yawa. Tare da Baba nurse din ta dawo
shima baiyi musu magana ba ya shige. Sunyi
kusan minti talatin da shiga sai ga nurses sun
fito kowacce da baby daya a hannunta. Umma
da sauri tazo karba tace dama biyu ne nurse
tace eh duk mata ne daya ce bata kwanta daidai
ba shiyasa muka kira Baba. Baba shima ya fito
yace a wuce da yara SCBU inda ake ajiye jarirai
bakwaini ko marasa lafiya.
Sai da Amal tayi kamar awa daya da haihuwa
aka turo ta waje dakin hutu. Jikinta duk a mace
ba kwari ana ta yi mata sannu. Ya Rayyan ta
kalla harda harara tace daga wannan bazan kara
ba. Hajja wadda bata zo asibitin ba sai da aka
haihu tace haka kowa take fada sai kuma badi a
ganta da wani.
Sai da kowa ya fita Ya Rayyan yace Sweet Amal
sannu da aiki. Allah Ya baki lafiya Yayi miki
albarka. Tace amin amma dai daga wannan sai
an kwana biyu na barwa Ju. Dariya yayi sosai
su Amal an horu fa wai anyi dinkin nan da kike
tsoro yana fada yana cewa bari na gani ta doke
masa hanne wallahi anyi baka ji ina ta kiranka
ba? Yau Baba yaji zance kala kala don ni daga
yau ya zama siriki na.
*******************
Sai bayan sati biyu aka sallami Amal da twins
wadanda suka ci sunan Mami da Umma wato
Asiya da Aisha. Mama ce tayi jinyarta a asibitin
bayan anyi sallama ta koma wudil. Sai da sukayi
wata daya sannan akayi taron suna Abba yana
ta fada wai son bidiarsu yayi yawa ace suna
bayan wata daya.
Ju tana zaune bakin gado dauke da Minal
( Aisha) ita kuma Manal (Asiya) ta bacci sai Ya
Rayyan ya shigo yace sweet Ju da babies dinta
ina Sweet maijego? Ju tayi dariya tace wanka
takeyi. Yauwa to dan matso kiji wata magana
tace anya Yaya nifa tuni na dena trusting dinka.
Ya kashe ido daya ke bakya cin ribar zance baki
ma tsaya kinji me zan fada ba.
Daga bayansu suka ji Amal tana cewa gulmata
zaku yi ko? Ju tace Allah ban saurare shi ba
Yaya. Dariya suka yi mata Ya Rayyan yace wai
dama cewa zanyi itama ta haifi biyu next year
ke kuma ki haifi gambo. Amal tace Sweet Yaya
yace naam ta dauki takalmi tace sweetly go out
tana fada ta bishi da takalmi ya fita Ju tana
dariya.
π JUWAIRIYYA π 23
Ance rana bata karya sai dai uwar 'ya taji
kunya. Yau ne ake bikin Juwairyya da angonta
Rayyan sai kuma Nafisa da angonta Sagir. Taro
kam yayi kyau Mami tayi rawar gani sosai don a
daki Mama ta sameta bayan an gama jeren Ju
taga irin abinda sukayi mata cikin hawaye tace
Yaya Allah Ya kara mana zumunci Ya basu
zaman lafiya da juna. Babu abinda bakiyi wa
Juwairiyya ba mu da muka haifeta ma
gudunmawar mu a auren nan kadan ce. Mami
tace Mariya kinsan dai kullum nasihar Baba gare
mu kenan kafin ya rasu saboda haka muyi
kokarin bawa yaranmu shawara mai kyau ta
zaman lafiya.
Mami ce ta bada shawarar ayi delaying
komawar Amal da sati biyu saboda amarya Ju.
Amal din bata musa ba don tasan kazantar da
baka gani ba tsafta ce kuma ita ai Ju ta yarda
ta bata watanni ma duk da cewa da aure a
kanta.
An kai amare dakunan su gidan Rayyan babba
ne ba laifi domin kuwa banda falon tsakiya
kowace mace harda shi tana da ciki da falo,
harda kitchen da toilet. Sai dinning area a falon
da wani toilet din guda daya da dakin baki. Gida
dai yayi kyau sai fatan zaman lafiya.
*******************
Tunda Ya Rayyan ya fita raka baki da kawayen
Ju cikinta ya fara kadawa. Samira tace mata
ana shan wahala gashi Anti Hassana ta sata
zama cikin bagaruwa wadda samiran tace kara
matse mace takeyi. Yana taba kofar dakin ta
sake jin cikinta na kuka ai nan da nan ta fada
toilet na shiga uku tace a ranta. Ni kuma da
gudawa na tare a gidan miji. Sai da ta gama
fitowa ta gagara kawai tonu ranar data shigar
masa toilet tayi a gida. Yana ta knocking taki
magana can da ya gaji yace zan bude fa. Tana
jin haka ta fara tube kaya tace ina zuwa wanka
nake. Ba yadda zata yi haka watsawa kanta
ruwan sanyi tana da rawar dari tayi alwala...da
muguwar rawa gwamma kin tashi.
A zaune kan gado ta sameshi yace ana kawo
amare sunyi wanka ke daga zuwa zaki karar
mana da ruwa. Gabanta ya fadi ba dai yaji tana
flushing ba. Ya cigaba to kazamar amarya by
the way akwai ruwan zafi ma kuwa? Ga sanyi
ya fara zuwa. Sai ta basar ni zafi nake ji
shiyasa nayi. Yace to zo na shafa miki mai tace
ai zafin dai nake ji amma yanzu da gaske take
tunda ya shigo wani gumi ya karyo mata. To dai
duk wayon amarya...........
******************
Amal ta fito daga kitchen ta tarar da Ju tayi
tagumi a falo tana goye da Manal. Amal tace Ju
lafiya kuwa ko result ya fito ne nasanki da
zulumi kije ki duba kawai. Ju ta share kwallar
data fito mata Amal hankalinta ya kara tashi sai
taje ta yiwa Ya Rayyan waya. Bai dade ba ya
iso ya dauki Minal dake hannun Amal. Yace
lafiya sweet Amal tace tambayi Ju sai sharar
kwalla take. Yace sweet Ju ya akayi bata
kulashi ba ta tashi ta tafi daki. Amal ta ce Yaya
bita i think something is wrong.
Sweet Ju dina wa ya taba ki cikin kuka tace
tunda nazo gidan nan wata uku banyi period ba
kullum jiransa nake. Yanzu idan ciki ne dani
haka zanyi irin na Ya Amal? Da kyar fa ta rinka
tafiya gashi harda dinki.
Fita yayi ya kira Amal suka rinka mata dariya
Amal tace kin fiye tsoro Ju to sauke goyon nan
daga yau an yafe miki kada ki matse musu
kanne.
Ju ce a labor room tana ta kiraye kirayen neman
taimako. Idan tayi adduar sai ta fara kiran Mami
da Mama. Amal har kuka tayi don tace ita
bazata taba manta ciwon ba. Kusan awarta biyu
a ciki ta haifo katon jaririnta ana kokarin yanke
cibiya tace wa nurse din anyi min kari ne nurse
tace eh amma ba yawa uku ne Ju tace a garinku
uky ba yawa ko. ta ce na ma dena kiranka
sweet Yaya tana fada tana kuka. Sister Rabi
wato nurse din tace maigidan ne ko? Ai daga
yau ki kira sunansa kawai. A haka aka gama aka
fito da ita.
Rayyan dai ba karamin dadi yaji ba. Yaro kamar
shi yayi yakinsa. Amal tace Ju yaya kika ji
akwai zafi... hmmm Yaya ke dai bari sai godiyar
Allah gashi nasha dinki.
Ranar suna yaro yaci suna Idris abinda Ju bata
zata ba. Ba karamin farinciki tayi ba tace Sweet
Yaya ka fadi duk abinda kake so tukwici banda
haihuwa next year. Ya rungume ta sannan ya
rada mata a kunne ni ke nake so da dan bakin
tsiwar nan ya fada yana shafa mata lips.
*****************
Minal da Manal ke rike hannun Baba karami wai
yayi tata-ta Amal tace kaji iyayin yaran nan ko
yaushe tasu kafar ta gama mikewa Ya Rayyan
yace ai gara duk su mike tunda akwai wasu a
hanya yana kallon cikinsu ita da Ju. Duk dariya
suke Amal tace ni dai daga wannan na dena
itama Ju tace ai nima haka. Ya Rayyan yace to
sweet matana ai kunsan akwai fili a gidan nan
sai na karo biyu. Tare suka rufe masa baki Amal
tace Sweet yaya sai sweet Ju ita kuma Ju tace
da Sweet Yaya Amal. Ya juya hagu da dama ya
kare musu kallo ga yaransa suna wasa yace
Allah Ya bamu zaman lafiya da zuria dayyiba.
Tare suka amsa da amin.
I realy hope you enjoyed reading Juwairiyya my
Sweet friends.
Ku saurari next littafi na.
Taku Batul Mamman
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO:
+2347039625239
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels