skin and I
don't like it. Abbas yace Ju ko. Cikin mamaki
yace what do you mean..Abbas Yace ni kaina I
cant remember when it started amma baka da
zance sai na yarinyar nan tayi kaza ko tayi kaza
kana fada kana wani lumshe ido. Rayyan ya kai
masa duka yace to tunda ban ambaci suna ba
ya akayi kasan da ita nake. Abbas yace sau biyu
muna tare da kai zata wuce gaba daya
hankalinka sai ya koma gareta. Ka siyo rigar
baccin don nasan zata yi rana very sooooon.
(fauza ta tsegunta masa auren da aka daura
amma tace yayi shiru kada ya fada). Rayyan dai
ya dauko irin rigar har biyu duk tsiyar da Abbas
ke yi masa sai ya share kawai.
Yau kwana biyu Ju tana aikin kuka ko abinci
bata ci tunda Baba ya fada mata zancen auren
da aka daura mata da Rayya.
π JUWAIRIYYA π 9
Mama tun tana bada hakuri har abin ya fara
bata haushi tana fada. Baba ma yayi nasihar har
ya fara fada shi da babu wanda yake jin kansa
da Ju. Gidan Baba Idris dai ya zama kamar ana
zaman makoki Ju data zo kwana biyu sai gashi
tayi kwana takwas. A kwana na taran Ya Najib
yasa Ju a gaba yana ta lallabata tayi hakuri don
duk fadansa yana son kanwarsa kuma yana
tausaya mata. Suna cikin magana sai kawai
suka ji sallamar Mami da Umma . Ju tana
kokarin tashi ta gudu daki sai taji an kira
sunanta. Amal ce fuskarta duk hawaye da gudu
Ju taje ta rungumo ta taja hannunta dakinsu
Nafisa. Umma tace lallai ana fushi damu yau ko
kallo bamu ishi Juwairiyya ba. A falo dai ta
barsu tare da Mama suka shiga daki tace da
Amal abinci tana mata nuni da baki Amal tace
gyada kai alamar tana so, Ju ta tashi zata debo
mata sai ta biyota har ta debo iyayensu dai
suna kallo. Sai a lokacin Ju ta gaishesu bayan
ta dan huce da fushin tace Mami ko kwalΔΊi baa
sawa Yaya ba kuma wannan siket din bata jin
dadin tafiya dashi ni bana sa mata. Umma tace
to Juwairiyya idan baki amince da auren nan ba
wace mace kike tunanin zata kula miki da
yayarki kamar yadda kike yi. Kuma kina jin
akwai mijin da zai yarda ki rinka zuwa kula da
ita kullum? Ta cigaba da cewa mu da muka
hada auren nan munyi ne bayan tunaninku duk
ku ukun kuma da yardar Allah alkhairi muka
kulla. Mami tace Ju kiyi hakuri da bamu baki
hakkinki na sanar dake ba nayi tunanin bazaki
amince bane. Ganin yadda suka taru suna
lallaba ta sai taji ba dadi tayi murmushi ta kama
hannun Amal suka koma dakin. Hakan ya
tabbatar wa da iyayen nata zaa sami nasara a
hankali.
************************
Al'amarin Ya Rayyan kuwa tun ranar da ya dawo
ya sami labari a wurin iyayensa. Bayan duk
iyayen sun taru a gaban Hajja sai Abba yace
Rayyan bayan tafiyarka fa an daurawa
Juwairiyya aure ai kafin ya kai karshe jikin
Rayyan ya fara gumi yace Abba aure kuma?
Dama tana da saurayi ne? Ko na dole akayi
mata? Baba yace kai wannan irin tambayoyi
haka da kai aka daura. Rayyan wani yanayi ya
tsinci kansa shi bai gane ba murna ce ko
kishiyata. Nan dai iyayen nasa suka yi masa
bayanin komai tare da nasiha.
A dakin Umma Rayyan yana nuna mata
sayyayyar da yayiwa kowa tana yabawa tace
banga ta amarya ba. Rayyan ya wani bata rai ai
bansan da maganar ba. Ni an rinka daura min
aure a haka kenan babu ko katin gayyata.
Umma dai dariya ma take tace zaka iya bagarar
da kowa banda ni ba tun yau nake lura da yadda
ka damu da yarinyar nan ba sai ka rinka nuna
halin ko in kula. Rashin zancen da take ma
maigadi ya fada min kai kace duk wanda yazo
nemanta ace tana da miji. Shiru yayi don yasan
gaskiya ta fada. Can dai yace Umma ko ke kika
bada shawarar auren tace eh don nafi kowa
sanin meye a zuciyarka. Zai fita ya waigo to
nagode tace ba godiya ba itama kayi mata tata
tsarabar na gani.
*************************
Sai da su Umma sukayi sallar magrib sannan
sukayi shirin tafiya tare da Ju. Sai da ta dake
sabon kuka Baba ya dai bata hakuri yace banda
abinki ai ba yau zaa kaiki ba abinda ance sai
bikin Fauza yazo nan da wata hudu. Kije Allah
Yayi albarka. A soro sukayi kicibis da Ya Sagir
da Nafisa suna zance tana ganinsu ta gudu shi
kuma ya fita yana sosa keya. Umma tace almuri
shiyasa kullum Juwairiyya zata zo kake cewa
zaka kawota. Mami kuwa a ranta tace ashe
naso yin kuskure ba yar yake so ba.
***********************
Kan Amal ne a cinyar Ju tana yi mata tsifa
washegarin da suka dawo a dakin Hajja su
Yasmin suna ta tsokanar Ju wai tazama dauko
wando ita kuma sai kumbura baki take taki kula
su. Hajja tace zanci kaniyarku yaran nan. Suna
haka Ya Rayyan yayi sallama duk suka yi shiru
sai aka fara gaishe shi banda Ju data sunkuyar
da kai sai hawaye Hajja tace su Yasmin su fita.
Ta juya ga Juwairiyya tace baki gaishe da
yayanki ba Ju still bata dago ba tace ina yini bai
amsa ba ya dauko kitkat nan da nan Amal ta
tafi wurinsa ya bare mata. Hajja tace bazaka
amsa ba yace sai da kika rokar min fa Hajja to
lafiya tunda kin rokar mata itama.
Wannan zama akwai kallo
π JUWAIRIYYA π 10
Ju bata sake cewa komai ba ta gama tsefewa
Amal kai taja hannunta suka tafi daki. Rayyan
yana falon Hajja sai ya jiyo kukan Amal. Yana
kokarin tashi Hajja tace wankin kai akeyi indai
kaji kukan nan amma bata kukan kitso ai. Wata
kitkat din ya dauko ya shiga dakin sai ya ga Ju
daga ita sai daurin kirji tana gogewa Amal kai.
Ai tana ganinsa da yadda tsaya kallonta duk da
Amal na kokarin kwace chocolate din da ta gani
a hannunsa yasa Ju kwalla kara Hajja ta dogaro
sandarta tayi saurin shigowa tana tambayar
lafiya yace nima ban sani ba. Ju kuwa cikin
karamar murya tace Allah Ya isa.
Kwana hudu kenan da Ju tayiwa Rayyan Allah
Yasa tun daga ranar take wasan buya dashi don
tasan yaji ta saboda wani kallo da yayi mata.
Tana kitchen suna aikin abincin sadaka ita da
Mami na juma'a kamar yadda al'adar gidan take.
Yau turn din mami ne tayi abinci Umma kuma
tayi zobo. Wayar Ju ce take ta ringing taje ta
dauka wata classmate dinta ce ta kira take fada
mata Waec ta fito taje ta karbi scratch card a
makaranta ta duba. Da murnarta ta fadawa
Mami tace mata to tunda goma batayi ba taje
ta fadawa Yasmin suje driver ya kaisu su karbo.
Gaba dayansu suna da 9 credits don haka da
murna suka dawo aka nunawa kowa. Bayan
magrib Mami tace Juwairiyya ki dauki abinci ki
kaiwa Rayyan tun dazu ya dawo. Ju tace ni
kuma Mami tace tace kinga wani a nan ne. Ki
tafi da result dinki ma ki nuna masa don tun
zuwanki garin nan shi yake biyan kudin
makarantarki. Ju cike da mamaki tace ba Abba
bane. Mami tace a'a Rayyan ne kuma daga yau
kullum rana da dare rinka kai masa abinci daga
nan don na riga na fada masa ma.
*************************
Jikin Ju a sanyaye ta dauki abincin da copy din
result ta fita. Mami a ranta tana tausayin Ju sai
dai tasan dole idan zaayi zaman auren dole su
saki jiki da juna shiyasa ta fadawa Umma a
dena aje masa abinci.
Tunda ta nufi shashen su Ya Rayyan gabanta ke
faduwa. Tana isa kofar dakin ta rasa me ya
kamata tayi. Karshe dai ta yanke shawarar ta
kwankwasa kofa kafin ya bude ta ajiye ta gudu.
Sai dai tana kwankwasawa sau daya taji ance
mata come in. Wani dum taji gabanta ya fadi
sai tayi saurin dokawa ta ajiye ta gudu sai dai
kafin ta dago kofar ta bude ya koma ciki. Turus
tayi a gaban tray din har sai da yace ke me kika
jira ne.
Yau ce ranar farko da Ju ta fara shiga dakin
Rayyan. Kwance ta sameshi yana waya ta ajiye
tray din zata fita ya daga mata hannu alamar ta
tsaya. Haka ya cigaba da waya kusan 15
minutes tana tsaye. Can dai sai ta fara tsaki ya
wani harareta kawai sai ta juya zata fita. Bata
ankara ba taga Rayyan a bakin kofa ya rufe ya
cigaba da wayarsa. Ai daga nan Ju sai kuka ba
shiri ya ajiye wayar ya kalleta ke lafiya me nayi
miki tace cikin kuka na gaji. Kin gaji fa kika ce
to ai baki ma fara tsayuwa ba punishment dinki
kenan. Tace Allah Yaya naci jarabawar ka gani
fa. Ya karba very good amma am not punishing
you for that. Ju har gumi ta fara ba komai ke
damunta ba irin fitsarin daya matseta kamar tayi
a tsaye. Ta daure tace me nayi. Allah Ya isa
kika yi min ko kin dauka banji ba. Zo ki zuba
min abincin ya fada yana canja tasha a tv. Ko
da Ju tayi yunkurin motsawa sai ji tayi fitsari ya
digo a ranta kawai cewa tayi komai ya fanjama
fanjam ta ruga da gudu toilet din dakin tayi
fitsarin. Ya Rayyan binta yayi da ido kawai sai
yaji shiru kusan 10 minutes da shigarta taki
fitowa. Kunya ta gama kamata ta yaya ma zata
fito wannan abin kunya da yawa yake.
Nima na tayaki jin kunya Ju
π JUWAIRIYYA π 11
Ke me kike yi ne shiru yaji ya sake maimaita
tambayar ba amsa. Kawai sai ya kama kofar zai
bude, ba shiri Ju tayi sauri ta danne kofar don
ta manta bata sa key ba. Ya Rayyan yace mata
kinsan baki fini karfi ba idan baki fito ba zan
balle kofar nan. Tace to ka dan fita daga dakin
zan fito, lallai yarinyar nan ta raina ni abinda
yace kenan a zuci. Tura kofar yayi iya karfinsa
ya zare mata ido zo ki fice. Ai da gudu ta fita
har tana bugewa da kofa. Sai da ya tabbatar ta
fita ya kwashe da dariya Allah Sarki ashe fitsari
take ji.
Allah Ya taimake ta a bangaren Hajja take
kwana da Amal da bata san me zata gayawa
Mami ba matsayin dalilin da yasa ta dade daga
kai abinci ba. Daren nan Ju har mafarki tayi
Rayyan ya bude ta a toilet tana fitsari.
Washegari tun safe Ju tace kanta yana ciwo
don kada taje kaiwa Ya Rayyan abinci da taga
bai dawo da rana ba ta ware tana harkokinta
magariba nayi ta kwanta harda shan panadol
extra ita a dole ga mai ciwon kai kowa yana
mata sannu. Kwana uku a jere ana ciwon karya
Mami dai har ta gane na rashin son zuwa ne
don haka tace zata yi maganin abin. Kamar
yadda ta saba Ju ana idar da sallar isha ta nemi
magani zata sha bata ganshi ba. Data tambayi
mami sai tace ita ta gaji da home remedy asibiti
zasu tafi ta kira ance akwai likita. Karya ba
kyau Ju dai ta sako hijab tana zuwa falo taci
karo da Ya Rayyan. Mami tace jeki mijinki ya
kaiki dama tun safe na gaya masa zai kaiki sai
kiyi musu bayani sai magriba ciwon yake tashi.
Idonta tsilli tsilli tace Mami ai yau baya ma
ciwon sosai idan nayi bacci zanji sauki. Dama
abinda Mamin tayi tunani kenan ciwon karya ne
sai tace gara dai kuje nima zamu dubiya nan
makota da umma. Ba yadda zata yi dole ta fita
gashi su Fauza sunje gidan kanwar Umma a
abuja zasu kwana biyu.
Bayan mota Ju ta nufa zata shiga Ya Rayyan
ya ce ke nayi kama da driver dinki ne. Sumsum
ta koma gaba ta rabe da jikin kofa. AC ya kunna
sanyi ya fara kada ta ga karatun Qur'ani yana
tashi tana bi a hankali. Sai da suka kusa isa
asibitin ya tsaya a gefen titi yace ke taki
amsawa ya maimaita still bata amsa ba sai yace
idan baki amsa ba zansa a kwantar dake idan
muka je asibitin naga kamar baki tsoron allura.
Tace naam cikin karamar murya. Ciwon kan nan
ki fada min gaskiya na gaske ne ko na gudu na
ne. A hankali tace na gaske ne. Kin tabbata
tsakani da Allah. A'a shine kawai abinda tace.
Uhmm to bari mu koma gida zan fadawa Baba
sun aura min mai shan kwaya. Wallahi bana
shan komai ni tana fada sai hawaye. Ke hawaye
baya miki wahala ne da anyi magana sai kuka.
Akan me kike shan magani kullum. Shiru dai Ju
tayi zai sake magana wayarta ta fara ringing sai
taga kiran Mami ne. Shi ya dauka yace gamu
nan dawowa Mami jikin nata da sauki. Bayan ya
ajiye wayar yace daga yau kullum kika kawo min
abinci zaki gyara min daki. Tace eyye yace eh
ai kinji me nace. Ya juya kan mota suka koma
gida.
**********************
Sati uku da faruwar haka kullum Ju zata kai
masa abinci kafin ya dawo taje ta gyara dakin
duk da kullum taje gado kawai take gyarawa sai
ta goge center table da,saman fridge da kan tv.
Kullum dakin babu datti. Ya Rayyan akwai tsafta
ga kamshi dake tashi a dakin kamar dakin mata.
Baba ne ya kira Rayyan yace tunda ya fara
annual leave dinsa ya kamata yaje Wudil ya
gaishe da iyayen Ju. Siyayya yayi ta kayan
abinci da sauran kayan masarufi ya nemi Sagir
su tafi tare sai Hajja tace wai ku yaran zamani
yadda ake jan hankalin mace ma sai an koya
muku. To ka dauki Juwairiyya ku tafi tare.
Ju ta gama shiryawa Mami tace na fada masa
gidan Dada zaku fara zuwa daga nan sai ku
wuce. Ki kula da kanki kuma don Allah banda
tsiwa. Murmushi tayi ta fice da gudu don taga
alama yau Mami kakar take da ita yau.
Bayan sun gaisa da Dada suka danyi hira ya
kawo dubu goma ya bata tana ta godiya dayi
musu fatan alkhairi sannan suka tafi. A hanya
babu wanda ya kula dan uwansa har suka isa
tayi mamaki daya gane gidansu. Baba yayi
murna sosai tare suka je masallaci da Rayyan.
Mama da Baba suka sake musu nasiha tare
sannan Baba yace don Allah idan Amal ta sami
lafiya ka kwatanta adalci tsakaninsu. Rayyan
yace da yardar Allah bazamu sami matsala ba.
Sai da suka yi sallar magriba suka kamo hanyar
kano. Kafin su iso Ju har tayi bacci. Ko da yayi
parking sai ya rasa yadda zaiyi ya tasheta daga
bacci. Kallonta kawai yake tayi masa kyau sai
da ya hango Abdul ya nufo motarsa sai ya shafi
gefen fuskarta ke tashi ki shiga gida. Wani yarrr
taji a jikinta ta tashi ta fita.
Har ta kwanta sai taga text ya shigo wayarta
( ina fata kinyi sallah)
tayi reply ( who are you and why do you care)
( hmm i guess your English has improved
alot)
( what ever)
( baki ansa min tambayata ba fa)
( malam ina da aure fa ka dena damuna ko in
maka Allah Ya isa)
Rayyan dariya ce ta kamashi sosai ( to sarkin
Allah Ya isa baki gaji da punishment din
tsayawa bane)
Subhanallahi shine abinda Ju tace daga nan
bata sake reply ba. Da yaji shiru sai ya kirata
kamar ta share sai dai ta dauka tayi sallama. Ya
amsa yace wannan number ta ce kiyi
saving...goodnight
π JUWAIRIYYA π 12
Tun daga ranar kullum dare Ya Rayyan zai kira
Ju yace mata sai da safe. Su Yasmin an dawo
daga abuja ana ta bawa Ju labarin wuraren
shakatawa tace nima in Allah Yarda zani
wataran Fauza tace ki bari ayi biki kice da Ya
Rayyan nan zaku je honeymoon ke na tuna ma
ai yanzu ma zaku iya zuwa tunda an daura aure.
Nan dai hirar ta koma tsokana da abin ya isheta
Yasmin na cewa wai kina ma son yayan kuwa?
he is very good looking nasan by now kin fara
sonsa. Ju har ranta tasan ta fara son Ya
Rayyan don kuwa yanzu duk dare bata bacci sai
ta jira wayarsa wadda babu abinda yake cewa
sai kinci abinci, yaya Amal babu matsala ko
daga nan sai yace sai da safe. Kallon Yasmin
tayi ta wani kashe ido tace so kai. motsin da
taji a bayanta ne yasa ta waiga ashe Ya Rayyan
na bayanta a tsaye su Fauza suka yi ta tunzura
ta. Bata kara magana ba ta tashi ta koma dakin
mami suna mata dariya. Ya Rayyan yace ina
wasa daku ne kowacce ta tashi suna masa
dariyar shakiyanci.
An fara bikin aminiyar Ju a makaranta Samira
dama Mami ta riga tasan da maganar har anko
tayiwa musu ita da Yasmin tunda duk ajinsu
daya. Ranar kamu tasa ankonta wanda suka
dinka fitted gown tayi musu kyau sosai an sha
dauri suka kawo mayafi iri daya suka yafa har
ka. Sun shiga dakin Hajja yi mata sallama Ju
harda sanda kada Amal ta ganta sai Hajja tace
wai ni Juwairiyya yayanki yasan da maganar
bikin nan ta ce a'a amma duk su Umma sun
sani. Hajja tace buga masa waya maza baki san
fita ba izinin miji duk taku a wuta mace take yi
ba. Ju ta dauka Hajja da wasa take sai taga
abin ya wuce wasa dole ta dauki waya ta kira
sai aka yi rashin saa yana meeting wayar tana
office ta kira ya fi sau goma don bikin Samira
ne ko rokonsa ne zata yi. Tace da Hajja bai
dauka ba ina ta kira Hajjan tace sai ki hakura
Yasmin taje don bazan yarda da fita irin wannan
ba. Kafin kace meye wannan Ju sai kuka tana
rokon Hajja abu ya hada dasu Umma amma
kememe Hajja tace ita bata san wannan
tarbiyarba. Umma har text tayi masa shiru.
Yasmin dole ta tafi ita kadai Abdul ya kaita Ju
kuwa yini tayi kuka dakin Hajjan ma tayi masa
kaura. Ya Rayyan ya fito daga meeting ya tarar
da missed calls da tawa. Umma ya fara kira tayi
masa bayanin kiran sai ya kira Ju ta kalli waya
tayi tsaki karshe ma kashewa tayi gaba daya.
Ya kira wayar Mami amma sai ya kasa cewa ta
bawa Ju.
Bayan ya dawo ya tarar yau bata kai masa
abinci ba ya sake kira still wayarta a kashe sai
ya tafi wurin Umma tace ita bata aje masa ba
tana dariya yau ka taba amarya zaka yi kwanan
yunwa. Girgiza kai yayi anya Umma baki fi son
yarinyar nan ba a kaina har dariya kike tace ai
ko yadda take kular min da Amal dole na so ta.
Fita yayi ya kira Yasmin a waya wadda tana
wurin Ju tana bata labarin biki da yadda amarya
bata ji dadin rashin zuwanta ba. Tace amma na
fada mata baki da lafiya ne. Ya Rayyan cewa
yayi tace wa Ju umma na kiranta. Suka fito tare
sai suka hadu dashi yace wa Yasmin wuce gida
ke kuma biyoni ta wani gatsina fuska umma ke
kirana Umma ta kwanta ni nake kiranki.
Tsayawa tayi taki tafiya sai kawai yaja hannunta
ya koma dakinsa da ita
***********************
Yaya ka sakar min hannu bacci zanyi ko kula ta
baiyi ba sai da suka shiga dakin ya rufe kofar
harda sa key. Ya bude fridge ya dauko youghurt
yana sha ta tsaya tana share hawaye. Ke zauna
tace ba sunana ke ba bai kula ta ba ya kuma
cewa nace ki zauna da yaga taki yace ashe kina
son kwana a dakin nan. da sauri tace Allah Ya
kiyaye, ajiye robar yayi yace what did you
say...shiru tayi ya biyota tana ja da baya sai da
taji bango a bayanta. Maimaita abinda kika ce
nan ta fara kokarin gudu yasa hannuwansa biyu
ya kafe a jikin bangon ba hanyar gudu. Tuni
cikinta ya duri ruwa don ta fara tsorata ya
matso da fuskarsa kusa da tata yace me yasa
baki fada min kina da biki ba idanunta a rufe
saboda yadda take jin numfashinsa dab da
fuskarta tace babu komai a hankali. To kinga ba
laifina don an hanaki fita ni kuma bana son short
notice so ragowar events din ma bazaki ba.
Bude ido tayi a hankali ga wasu hawayen na
shirin sauka tace don Allah itace babbar kawata
idan banje ba zata yi fushi. Tausayi ta bashi to
idan na sake ganin hawaye bazaki ba hannu
biyu tasa ta goge idonta yace gobe me zaayi
tace dinner to ku shirya Abdul sai ya kaiku
amma da sharadi daya ina jin yunwa. Ju
murmushi tayi har dimple dinta ya fito yace ke
kin ci tace a'a amma zanci idan na shiga....wato
hunger strike kike saboda kina fushi dani.
Har ta kwanta sai tayi sauri ta dauki wayarta ta
tura masa text.
( yaya please ka fadawa Hajja kada ta sake
hanani fita)
( idan naki fa)
( don Allah kada ka ki)
( ki taya ni addua gobe ina da case. goodnyt)
Ju bata yi reply ba sai tayi alwala tayi sallah
tare da roka masa saa. Sai bayan magrib suka
shirya zasu tafi Mami tace kada ku wuce 9:30
amarya tazo ko bata zo ba. Ju tace in sha Allah
Mami. Sunyi wa Hajja sallama tace wa Ju yau
babu kuka ko tun safe ya fada min. Zuwaira
kenan wai an iya fushi jiya kika barni da Amal ta
hanani bacci. Abdul yayi ta dariya mu dai mun
ganku a rana.
Tara da yan mintuna Ya Rayyan yayi wa Ju text
( ki fito mu tafi) ta nunawa Yasmin ba don
sunso ba suka yi sallama da amarya don ma
sunyi saa ba ayi african time ba an fara da
wuri. A waje suka tarar da Abdul da Ya Rayyan
yace ka dauki Yasmin ku tafi na manta bance
kada ka dawo daukarsu ba. Ju bata ji dadi ba
don yayan nata ya fara bata tsoro.
Ju da Rayyan nice couple ko.
π JUWAIRIYYA π 13
A hankali yake tuki kamar bazasu gida ba kowa
yayi shiru da abinda ke ransa. Ju ta kwantar da
kai jikin kofa tana hamma Ya Rayyan yace ke
kada kiyi min bacci fa ba dama kiji sanyi ac sai
ki fara hamma. Mayafin ta taja ta rufe fuska. Au
ni bazan ga kwalliyar ba? Sai a gidan biki kike
nunawa. shiru tayi har suka iso gida tana
kokarin fita taji motar a rufe. Ina zaki yau zance
zamuyi na ma fadawa Hajja don kada taji shiru
ta rufe kofa. Yaya ni bacci zanyi ta fada tana
hammar karya. Bata ankara ba tayi ya janyo ta
kusan rabin jikinta duk akan cinyarsa take
fuskarta a kirjinsa. Tun tana kokarin kwacewa
har ta hakura don ba karfinsu daya ba. Zame
mayafinta yayi daga kanta yana shafa mata
gashi wanda yasha gyara a salon. Wani irin
yanayi suka sami kansu mai dadi can taji yace
wa Juwairiyya gabanta har faduwa yayi don
bata taba jin ya kirata ba....are you happy with
this marriage? Kasa amsawa Ju tayi. Idan baki
amsa ba sai mu koma dakina kila zaki fi sakewa
a can.A'a yaji tace to give me an answer. Da
yaji ta sake shiru ya cigaba I just want you to
know ban amince da auren nan ba don kawai
kina kular min da Amal. I love my wife kuma
kullum ina mata adduar samun lafiya amma you
are also special kada ki taba zaton ina tare dake
don kina taimaka min kamar yadda aka fada
miki a gida. I care about you. Dadi mara
misaltuwa Ju taji a ranta gyara mata zama yayi
ta koma seat dinta sai ya dauke ta a hoto.
Kunya duk ta rufe ta yace idan kin shiga gida ki
turo min wasu ina jira. Tana jin alamun ya bude
lock din taja dauki dankwalinta ta gyara mayafi
zata fita ya sake rike mata hannu gobe ma zaki
bikin ta eh,to ki fada min idan kun shirya tunda
saturday ne bana son ana kalle min
mata....murmushi tayi ta fita. God i love this girl
abinda ya fada kenan a fili.
**********************
Ju ta tsinci kanta cikin nishadi bayan ta kwanta
taji wayarsa tana dauka ina jira kawai taji yace
ya kashe wayar. Nan ta duba wasu hotunanta
masu kyau ta tura masa ta whatapp duk da bata
taba chatting dashi ba. Kiranta ya sake yi kinyi
kyau nagode. Mu kwana lafiya.
Wani malami anti Hassana tazo dashi gidan
washegari tace a islamiyyar yaranta yake
koyarwa amma taji ance yana ruqiya shiyasa
tazo dashi gidan. Ya Rayyan aka taso daga
bacci tare da sauran mazan gidan malam yace
duk suyi alwala nan ya fara karatu Amal sai ta
fara ihu sosai. Su Ju suna side din Mami su
duka harda su Mamin suna ta addua. Tuni ma
ta manta da yau zaa kai samira. Malam yana ta
karatu Amal ta fara fizgar gashinta nan Rayyan
da Abba suka danneta ta fara cewa cikin muryar
maza zan fita wallahi zan fita dama turo ni
akayi. Ku kira uwarta tasan wanda ya turo ni.
Malam yasa aka kira su mami Ju ta shigo taga
yadda Amal ta fita hayyacinta sai kuka. Malam
yace muna sauraronka makiyin Allah azzalumi.
Aljani wanda yace sunansa Zazzaq boka ne ya
turo ni bisa umarnin mal Yau yace in hana
babarta sukuni don ta dena taimakon kaninsa.
Ju najin haka kukanta ya tsananta. Shima kanin
mu muka rufe masa ido ya dena gani kuma
muka ruguza kasuwancinsa amma wallahi zan
bude don duk ka kona ni. Wannan yarinyar ma
tasan sanda aka binne asirin a kofar gidansu.
Duk ranar da tayi niyar fada sai na saka mata
wani mummunan tsoro a zuciyarta amma na
tuba na bika. Malam yace ni karka bini ina son
ka fita daga jikin yarinyar nan kuma makahon
nan ma ka bude masa ido idan ba haka ba duk
inda ka shiga a duniyar nan zan maka addua
kuma kasan baa boyewa Allah. Addua Malam ya
cigaba dayi dai Amal tayi atishawa mai
karfi....ta dan jima a kwance sai can ta bude ido
taga wanda ya rike mata hannu tace Ya Rayyan
kai ne?.
To ga Rayyan, Amal da Ju me zai faru da auren
su?
.
π JUWAIRIYYA π 14
Farinciki ne ya cika zuciyar kowa da jin yau
Amal ta gane wani bayan Ju. Nan 'yan uwanta
sai suka rinka cewa nima kin gane ni tana
murmushi tana basu amsa. Tana zuwa kan Ju ta
tashi ta rungumeta iyakar karfinta tana kuka. Su
duka kukan suke har suka bawa mutane tausayi.
Amal tace duk duniya babu mai saka miki Ju sai
Allah. Wani lokacin ina dawowa hayyacina
amma sai na kasa yi muku magana amma duk
irin kulawar da kike min nasani.
Malam na shirin fita Ju tace malam mahaifina
ne makahon, Abba yace hakane itace yarinyar
da ya nuna ai. Malam yace me kika sani game
da ciwon mahaifin naki. Ju cikin kuka ta fadi
yadda taga baba Yau ya binne zakara mai rai da
wasu layoyi a kofar gidansu sannan yace