babanta ne ya fadu mata a rai ita
kuma Amal sai ta zata kwaikwayonta take ta
tashi ta dawo kusa da ita, umma ce tayi mata
signal da ta ja ta toilet ai kuwa akayi saa ta
bita. Ju dai taga ikon Allah don Amal ki tayi
kowa ya taba ta karshe dai ita ta gyara mata
jiki. Tun daga ranar wankin kashi da fitsarin
Amal ya dawo gareta harda wanka domin duk
wanda ya taba ta ba Ju ba to zata yini ta kwana
kuka.
A hankali Amal ta zama kamar yarinya karama
Rayyan kam ra rabu da faraa tun ranar da ta
fara ciwon don gani yake laifinsa ne. Malamai
kam suna ta aikin magani da addua amma dama
ciwo ke shiga farat daya sauki sai a hankali
gashi aljanun da ake tunani sune a kanta sunki
magana ma. Ranar da Ju zata tafi da sassafe
umma ta buga kofar gidan mami don kwana tayi
tunani. Lanti mai aiki ce ta bude mata sannan
ta kira Mami. Bayan sun gaisa tace Asiya ina
Abban yara shawara na kawo mana baki daya.
Abba ya zauna shima sun gaisa da Umma tace
to ni jiya hankalina ya tashi kan maganar
komawar Juwairiyya gida. Ni dai indai da hali ku
barni na roki Mariya ta barta a nan kafin Amal
ta sami sauki. Kuna ganin irin artabun da ake da
ita idan wani ya taba ta ba yar uwar ba. Na
fadawa Baba yace muyi shawara tsakaninmu.
Abba ya kalli Mami yace ya kika gani? Nasan
yarinyar nan kawaici kawai tayi mana akan
babanta.
Shin Ju zata yarda ta zauna a kano kuwa???
💕 JUWAIRIYYA 💞 4
Ju tayi mamaki da taje yiwa umma sallama tace
mata jiki mota ai tare zamu tafi. Taje ta yiwa
Hajja ma sallama harda kukanta, anyi sa'a Amal
na bacci bata ga fitarsu ba. Da yake tafiyar ba
mai nisa bace basu dade ba suka isa ita dai Ju
sai tunani take kala kala game da dalilin biyota
da Umma tayi.
Motar na tsayawa Ju ta ruga da gudu ta shiga
gida ba ko sallama dakin babanta ta nufa ta
fada masa a jiki sai kuka. Mama ta fito ta tari
Umma duk suka tsaya kallon ikon Allah yadda
Ju ta shige jikin babanta tana ta watso masa
tambayoyi. Mama tace Zuwaira ba gaisuwa ai
kuwa ta bata fuska Allah ni mama ba sunana
zuwaira ba, Umma tayi murmushi tace yo tunda
ita kin share ta ai dole tace miki zuwaira.
Baba, Mama da Umma ne zaune a falo sai Ju a
kasan kujerar da Baba yake zaune umma tace
nasan dai Asiya tayi muku bayani tun kafin mu
taho a waya amma duk da haka ina son jin ta
bakinku. Mama tace Juwairiyya kalli can tana
juyawa sai taga akwatinta ne sai wata ghana
must go da ledar viva tace Mama kayan meye
wannan. Mama tace mata munyi shawara da su
Yaya akan zaki koma kano kafin Allah Yasa
Amal taji sauki. Duk munsan yadda tafi yarda
dake kuma ko dazu kafin ku iso da muka yi
waya ina jin ihunta sun kasa bata abinci. Baba
ya mika hannu yana laluben Ju sai ta rike
hannun yace baki taba yi mun gardama ba idan
ba akan dambe ba don Allah kada ki tashi
hankali akan tafiyar nan. Umma tace ni muna
komawa zan bayar da kudi a siyo miki waya ki
rinka gaisawa da Baba kullum.
*************************
A haka dai aka lallaba Ju suka dawo kano tare
da alkawarin zaa saka ta makaranta ranar litinin
don ta cigaba da karatun ta. Mami ba karamin
farin ciki tayi ba da yadda Ju ta kwantar da
hankalinta bayan sun dawo ita ma Umma ta
cika alkawari ta bata sabuwar waya karama
tace idan aka koma makaranta tayi kokari zata
canja mata da mai kyau.
A falon Hajja su Ju suna zaune da Yasmin sai
ga Yaya Sagir da Yaya Rayyan sun shigo da
ledoji masu dauke da note books,text books da
sauran kayan makaranta na kannensu. Rayyan
ya kalli Ju da take fama da Amal akan ledar
pure water yace ke aji nawa zaki shiga ne. Tace
SS 3 ya sake cewa science class ko arts? Tace
science. Hajja tace wace makarantar za a kaita.
Rayyan yace ta su Fauza, ya dubi yan matan
yace kuzo ku ware books dinku ku bar bata
sauran notebooks din gobe ku shirya da wuri
don ni zan kaiku saboda zan biya kudin nata
books din. Abdul autan su Amal yace wai ke Ju
nufinki aji daya zamu shiga tace kaima ka kusa
candy yaya Abdul? Yace ke fa yar kauye ce
meye wani candy ana zaune kalau, graduation
ake cewa. Ta murguda baki tace to kawai ka
gyara min mana sai kace min yar kauye, ai
wudil ba kauye bane. kowa yayi dariya banda
Rayyan wanda a halin yanzu damuwarsa tafi
farincikin sa yawa saboda ciwon Amal. Magani
kullum nema ake kuma Alhamdulillah ta rage
yawan kukan nan sai dai behaviours din yara.
Mami ta kawo kudin da Abba ya bata dubu dari
ta bawa Rayyan lokacin da suke shirin tafiya
makaranta tace gashi babban yaya ku tafi da
wannan idan ana bukatar kari sai ka fada min.
Yace haba Mami ai tunda dalilin Amal aka dawo
da ita kano ni zan biya kudin. A mota kannen
nasa suka same shi Fauza mayyar zaman gaba
tayi sauri ta shiga sai su Yasmin su uku a baya
Ju a tsakiyarsu ita da Abdul. Ya Rayyan yace
meye haka zama kusa da namiji tace to ba wa
na bane. Yace da Abdul get out ko kunya baka
ji zama cikin mata. Ke fauza fita ki koma baya
kuma daga yau ko driver ne zai kaiku kada na
sake ganinka a baya.
Suna fara tafiya Fauza tace Ju wallahi ki dena
magana idan Ya Rayyan nayi don baya so. Tace
to Allah Ya bani iko.
An zaunar da Ju a wani empty class da papers
biyar da ake son yi mata gwaji ko ta cancanci
class din da zaa sa ta na maths, english,
biology, physics da chemistry. To fa nan ake
yinta Ju dai ba turanci sosai saboda yanayin
lalacewar govt schools kafin kace meye wannan
dai ta gama maths da physics don tana son
lissafi sauran papers din kuma abinda ta
fahimta tayi wanda bata gane ba tayi kwabarta.
Ko da ta gama wata malama ce tazo ta mayar
da ita office din principal inda Ya Rayyan yake
jiranta. Principal din Mr Ayodele yace da Rayyan
ya tafi da ita gida gobe su dawo bayan anyi
marking. Rayyan yayi godiya yace ta taso su
tafi.
Washegari Ya Rayyan ya koma school din shi
kadai don principal din yayi masa waya yace ya
barta a gida yazo shi kadai. Result din Ju ya
gani taci maths da physics ba laifin amma
sauran dai ba bayani tun ba English ba. Ko da
rashin cin jarabawar bai masa dadi ba wani
sentence daya karanta ya mugun bashi dariya ta
rubuta ( My ankle is the bery wickedest man in
wudil). A zuciyarsa yace lallai yarinyar nan ta
tsani wannan kawun nata. Ya ce da Mr Ayodele
wane class yake jin zaa sata don ta sami ilimi
mai kyau. Mr Ayodele yace idan zai yarda zaa
mayar da ita SS1. Ya Rayyan yace shi yafi son
JS 3 don yana son a gyara mata turanci yadda
zata fahimci karatu sosai.
Sai da ya karbo duk books din da zata bukata
da uniform ya biya school fees sannan ya tafi
wurin aiki. Bayan magrib Rayyan ya sami Mami
yayi mata bayani tace JS 3 Rayyan to wallahi
kai da kanwarka ni ba ruwana ta fada tana
dariya. Ju da ta shiga daki da tulin littafai zata
rubuta suna a jiki sai taga duk ansa JS 3 a jiki
ta fito tace Yaya ai duk na JS3 ne Allah Yasa
ban riga nasa suna ba sai ka mayar musu. Yayi
wani dan murmushi yace ai a nan za a saka ki
sunce baki iya turanci ba.
Tabdi wannan ai yafi karfin repeating Ju mai
shirin candy bana an maka mata demotion.
💕 JUWAIRIYYA 💞 5
Kan uban can shine abinda ya fara fitowa daga
bakin Ju sannan tace wallahi bazan yarda ba
Mami ce dai ta doke bakin tace haba Juwairiyya
kullum sai an miki fadan ki dena magana idan
babba nayi . Tace Mami kiyi hakuri kinji wai JS
3 zai kaini. Ajin da Yasmin take fa kenan.
Rayyan dai yau dariyar mugunta yake ji ya juya
zai fita sai ya dawo yace Allah idan kika sake
zagi a gidan nan ranki sai ya baci.
Abin takaici baya karewa don Abdul tsokanar Ju
ya rinka yi yana kiranta candy. Ranar da kuka
tayi bacci. Da gari ya waye taje ta gaishe da
Hajja da Umma sannan ta bawa Amal abinci
suka tafi makaranta. Abin mamaki Abdul bai
kara tsokanarta ba su Fauza da take tsammanin
zasu yi suma kowa bakinsa kanin kafarsa. Ashe
Rayyan yayi musu warning duk wanda yayi mata
dariya zai gamu dashi.
A makaranta Ju taji dadi sosai da taga ajinsu
akwai matan da suka fita tsaho banda maza
ma. Dama ita ba wani tsaho gareta ba jikinta
madaidaici ba rama ba kiba. Tana da kyau
daidai ga dan dimple a kumatunta na dama. A
ranar farko yan ajinsu sun fahimci Ju ta iya
mmaths don ba su da yawa a ajin kuma
malaman suna involving dinsu a ayyukan da
suke. A fannin magana dai tunda akayi mata
dariya bata sake ba. Su kuma da malami ya
shigo ana tambaya sai suce Ju ta amsa yadda
suka ji Yasmin na kiranta.
Satin ta daya da fara zuwa duk ta zama a
takure saboda yadda yan ajinsu ke damunta har
wasu students dinma. Yasmin da abin ya isheta
ta fadawa Ya Rayyan wanda kullum yake nuna
halin ko in kula a gabanta. Har school din yaje
ya sami principal yace idan bazai tsawatar da
students akan kanwarsa ba zai canja mata
school. Ju bata san me yake faruwa ba taga
canji sosai don a assembly Mr Ayodele yace zai
dau mataki akan masu takurawa new students.
***********************
Abu kamar wasa term ya kusa karewa kuma su
Mami suna kokari every two weeks ana kaita
wudil taga iyayenta.
Batun ciwon Amal kam ta rage kuka amma har
yanzu bata iya yiwa kanta komai. Ta dai iya
kiran Ju kamar ita ta rada mata. Kowa a gidan
yana yaba yadda Ju take kokari wurin kula da
Amal. Yaya Sagir kuma ya zama mai koya mata
assignment don Ju ta dage sai ta iya turanci.
Wata rana tana zaune suna lesson da Yaya Sagir
ita da Yasmin sai ga Rayyan ya shigo falon ya
zauna yana shan tea. Tana ganinsa ta dena
karatun da take Ya sagir yace mata cigaba
mana ta dan bata rai ta cigaba da cewa
( wicked, wickeder , wickedest) nan take Rayyan
saboda kokarin gintse dariya ya kware da tea.
Sagir yace wallahi zamu baku mamaki idan
muka fara tsara ku da grammer.
Karshen term Ju tayi ta 23 cikin mutum 25.
Tana zuwa gida ta tarar da Rayyan sun dawo
daga asibiti da Amal Fauza cikin murna tace
Yaya kaga result dina ta 4 nayi yace kinyi kokari
akwai kyauta ya kalli sauran ku fa. Kowa yayi
kokari dai banda Ju wadda yace zai sa a maida
ta JS 1 idan ta dauki sama da ta 20 next term.
**********************
Alhamdulillah Ju ta gama JS 3 lafiya don result
dinta na karshe ta 19 tayi. Rayyan yayi farin ciki
da hakan duk da bai nuna mata ba. Sai dai
yadda ya fuskanta tafi kokari a fannin lissafi
gashi bata yi kokori sosai ba ance bazaa bata
science ba. Ya dai roki alfarma idan an dawo
hutu s sake mata exam a eng don yanzu da
kanshi zai koya mata.
Mami ba karamin jin dadin yadda ake Ju ke kula
da Amal take ba. Idan tana period ma da kanta
take canja pad. Allah kadai zai saka ma yarinyar
nan abinda take yawan fada kenan.
Wani malami aka samu irin masu aiki tsakani da
Allah Ya tsaya sosai da addua cikin ikon Allah
aljanin dake kan Amal yayi magana yace turo shi
akayi amma yaki fadan ko waye. idan akayi
ruqiya sai ya fita malam na tafiya ya dawo yace
shi kawai a kwance auren. Haka dai ake fama
da adduar Allah Ya kawo sauki.
Rayyan ya aika yafi sau uku Ju tazo lesson taki
don ita tsoronsa ma take yanzu sai da ya hada
ta da Abba ta fara zuwa. Idan yana yi mata
magana ba amsa idan yayi fada tayi kuka. Daya
ga itama akwai taurin kai sai ya rabu da ita da
sharadin idan akayi mata exam bata ci ba zaisa
a mayar da ita js1. Ju da murna tace ta yarda.
Tun daga lokacin kullum Ju tana karatu da duba
dictionary bata tashi idan ba sallah ko kula da
wani abin da Amal ke so ba. a dakin Hajja dama
take karatun tare da Amal tana yan wasaninta.
Sati biyu da fara karatun nan na Ju suna daki da
Amal cikinta ya wani murda saboda bata wani
cin abinci kamar wasa da farko ta share sai
gashi ya kara da ciwo sosai tana ta yiwa Amal
alama da ta kira wani don ta kasa tashi amma
ita bata gane ba sai ma ta kwanta a kasa yadda
Ju tayi tana kwaikwayonta.
Hajja ce taji shirun nasu yayi yawa ta tashi ta
bude kofar dakin abinda ta gani ne ya sata
salati da karfi har Umma dake falon ta yi saurin
tasowa. Ju ce kwance a kasa sumammiya
kamar babu rai tare da ita
Yau kuma me ya sami Ju din Baba Idris.
💕 JUWAIRIYYA 💞 7
A falo Ju ta hadu da Mami da Ya Sagir suna
hira. Mami tace wa ya taba min ke naga kina
ta kumbura bakin nan na tsiwa. Ju tace Ya
Rayyan ne ya koro ni, Mami a gabansa fa ya
hauni da fada. Ya Sagir da bai gane me akeyi ba
yace gaban wa am confused. Ya Rayyan daya
shigo a lokacin yace gaban Lawal mai shago
mana. Cikin fushi ya cigaba da kallon Ju yace
wai ni waye ma ya baki izinin fita. Ya Sagir yace
Mami Ju zance take yi ban sani ba. Mami taga
yara zasu mata taron dangi tace kwana hudu
kenan yana turowa kiranta ina hanawa dazu
Hajja tace kada na sake hanata fita don dole
tayi aure wata rana. Ya Sagir yace to ni zan
mata magana ai su bata gama secondary ba.
Ya Rayyan kwance akan gado yana kallon
hotunan Amal cikin zuciyarsa yana dada
tausayin halin data shiga dalilin auren su amma
abinda yafi damunsa yadda Ju ke neman zama
centre of his thoughts. Wai shine har yake
fadawa wani shine mijin yarinyar nan mai tsiwa.
Ya tashi ya dauko papers din jarabawar da aka
yi mata farkon shigarta makaranta ya sha
dariya. Karshe dai alwala yayi ya sallah tare
dadewa yana addua musamman ga matarsa
Amal.
Lokacin WAEC ya matso su Ju an maida hankali
ga karatu don ita bata da burin da ya wuce ta
zama likitan ido ta taimakawa babanta. Ita da
Yasmin sun dage da karatu cikin ikon Allah
sunyi sun gama lafiya. Result din Jamb ne ya
fara fitowa ita tana da 214 Yasmin kuma 221.
Kowa ya tayasu murna. Kanwar Ju ma Nafisa
wadda saboda demotion din da akayi mata tare
suka gama itama ta sami 187.
***********************
Hajja tasa 'ya'yanta maza a gaba tace shawara
na ke son kawo muku wadda kuma zancen
gaskiya da Umma muka fara yi don ita tazo da
maganar. Abba yace Hajja mu ai umarni zaki
bamu ba shawara ba. Tace hmm kaji shi bayan
ku akan 'ya'yanku sai anbi a hankali. Baba yayi
dariya yace to muna sauraronki. Hajja ta gyara
zama tace to ba wani abu bane akan yarinyar
nan Juwairiyya ne, idan banyi kuskure ba ta
kusa cika shekara hudu a gidan nan kuma duk
tsahon lokacin nan a kula da yarmu tayi. Baba
yace hakane nima kaina ina tunanin me zamuyi
mu saka mata da alkhairi. Hajja maida kallonta
ga Abba tace Bashir kana ganin zaka yarda
Rayyan ya auri juwairiyya? Gaba dayansu basuyi
tunanin jin wannan maganar ba. Hajja bata kula
da yadda suka razana ba ta cigaba da cewa
yarinyar nan taci kashi da fitsarin yayarta ba
tare da ta taba bata rai ba. Allah Ya sani ina
tausayin Habiba amma kuma har yanzu bata
sami lafiya ba. Idan Juwairiyya tayi aure a wani
gidan wa zata yarda ya taba ta. Duk kunsan
yadda take kuka idan Juwairiyyan ta tafi
makaranta. Abba yayi shiru sai kawai hawaye ya
digo daga fuskarsa ya kalli dan uwansa yace
Yaya abinda Hajja ta fada gaskiya ne. Shi kanshi
Rayyan har kunyarsa nake ji ya gina gida ya
kasa tarewa kullum sai dai yaje aiki ya dawo ga
shekaru na karuwa. Yaya indai ka aminci to ni
bani da matsala akan hadin nan.
**************************
Kowa ya tashi da tunani a ransa amma Abba
tsoronsa daya yadda Mami zata karbi maganar.
Kwana biyu yana ta juya zancen a ransa karshe
dai ya sami dama da ta kawo masa zancen taga
alamun Sagir fa yana son Ju. Abba yace ya fada
mata ne tace a'a naga alamu ne dai sai ya fada
mata shawarar da Hajja ta kawo. Mami sai kuka
wiwi kamar yarinya tace yanzu Abban Sagir haka
Amal zata kare rayuwarta? Ni bana kin ya auri
Ju domin yata ce amma misali Amal ta warke
fa. Ni Asiya na shiga uku Abba yace haba
yaushe zaki rinka maganar kin shiga uku bayan
kinsan babu tsumi ko dabara idan ba abinda
Allah Ya tsara ba. Kada muso kanmu mu cutar
da wasu. Ki duba yadda yaron nan hatta da
abincin da Amal take ci shi yake siya kuma baya
tunanin wani aure ya hakura ya zauna da ita a
haka. Kada muyi zalunci saboda son yarmu idan
hakan alkhairi ne to muyi fatan Allah Ya
tabbatar da faruwar sa. Daren ranar dai Abba da
Mami kusan kwana suka yi sallah Allah maji
rokon bawa sai Ya sassauta musu al amarin a
zukatan su..
*************************
Yau Ju an tashi da farin ciki domin kuwa wudil
zata ta kwana biyu. Sai da tazo tafiya da kyar
aka rabata da Amal duk suna kuka Ju har waje
tana jin muryar Amal tana kiranta.
Ya Sagir ne zai kaita dasu Yasmin yan rakiya.
Fauza ana exams a buk tana karanta Economics
bata sami zuwa ba.
Koda ta isa gida murna take taga Yaya Najib
sarkin cin zali don ta kwana biyu basu hadu ba
saboda yana aiki a kaduna. Ya yi musu gyara a
gida harda fenti Ya Ismail kuma yana bautar
kasa a Kwara state. Gida dai sai murna ake da
zuwan Ju. Washegari abin mamaki sai ga Abba
da Baba da wani Kawun su kanin babansu.
Bayan sun gaisa da Baba suka gabatar da
abinda ya kawo su na son nemarwa Rayyan
auren Ju. Baba yace Alhaji Bashir ban tari
numfashinka ba amma yaron nan ba shine mijin
Amal ba. Abba ya amsa da shine...sai baba
yace to don Allah ku bani mintuna kadan ina
zuwa. Sandarsa yasa ya shiga cikin gida ya nufi
daki tunda yau da gobe tasa yana iya yawoba
gidansa. A daki sautin kukan mama yaji yace
Mariya me ya faru? Tace yanzu muka gama
magana da yaya da kuma Dada akan abinda ya
kawo su Alh. Baba yace to me kuka yanke tace
ka amince don duk shawarar da suka bani kenan
saboda tunda aka fara maganar auren nan idan
ma munki to zasu nema masa wata karshenta
ya rabu da Amal din. Kuka yaci karfinta tace ko
kadan ba irin rayuwar danake wa Juwairiyya fata
ba kenan amma wai mahaifiyarsa ce ta kawo
shawarar kada mu aurar da ita a rabasu. Ta
share hawaye tace kuna kasan ina tausayawa
Yaya kafin najib ya kawo karfi duk dawainiyarsu
ta karatu ta dauke mana. Fatana Allah Yasa
abin nan ya kara mana zumunci. Yace amin
nagode Mariya da dukkan abinda kuke yi min ke
da yar uwarki.
Baba ya fita ya koma falon waje yace da
bakinsa yaushe kuke son a daura auren kunga ni
banyi wani shiri ba ko zaku bani lokaci. Abba
yace haba Alhaji Idris juwairiyya ai yata ce don
nafi ka morarta idan ka amince a yau zas daura
auren. Bidaya Baba ya kira yace ta kira masa
Najib da yazo ya tura shi kiran mal Yau da
Liman da wasu yan uwansu da abokan arziki.
Bayan sallar laasar aka daura auren Rayyan
Umar Tafida wanda wurin aikinsu aka tura shi
Germany na sati biyu da Juwairiyya Idris
Muhammad wadda ke daki suna hira da su
Nafisa bata san me yake faruwa ba.
Akwai rigima a gaba daga dukkan alamu
💕 JUWAIRIYYA 💞 6
Umma waya ta dauka ta kira Baba ta gaya
masa yanayin data tarar da Ju yace to ta sami
daya daga cikin samarin gida ya daga ta a sata
a mota su taho yana asibiti. Kafin ta gama
wayar Hajja ta kira Mami sun shigo tare da Ya
Aliyu kowa a rude. Aliyu na kokarin daga Ju sai
ga Rayyan ya shigo yace masa ya matsa shi ya
dauko ta kamar wata jaririya ya sata a bayan
mota Umma na gaba ita kuma Mami sa Ya Aliyu
suka biyo bayansu.
A asibitin ma Ya Rayyan bai jira nurses ba ya
sake daukan Ju ya shige ciki babansa ya fito
daga office tare da Aliyu daya fada masa sun
iso ya shiga zai dubata sai wata dr din tace
yallabai ka bari naje idan ba kasa zan kira ka
don iyaye basa iya duba yaransu sosai. Ba musu
ya koma office don ya yarda da ita yace su jira
shi a nan reception. Ya Rayyan duk ya kasa
zaune ya kasa tsaya ashe duk abinda yake
Umma na lura dashi amma bata ce komai ba.
Bayan anyiwa Ju allurai ansa mata drip likitan
data duba ta ta wuce office din Dr Umar Tafida
tace yallabai yarinyar nan fa yunwa ke damunta
don idan ta tashi zansa ayi mata test inajin
ulcer ma ta kamata. Ya mike da hanzari what
did you just say Dr Rufaida? Yarinyar nan fa
'yace a wurina kuma a gida na ma take. Tare
suka fito Baba ya hau fada ko suna maltreating
din yar mutane don tana kula da tasu.
**********************
Sai washegari bayan Ju ta dan dawo hayyacinta
Mami ta tambayeta meyasa bata cin abinci
tace karatu take kuma ita mntawa take da
abincin don kada yaya Rayyan ya mayar da ita
js1. Mami dai tayi mata fada sannan ta hada ta
da mama da baba a waya suka gaisa.
Rayyan ko kadan baiji dadin dalilin da Ju ta
bayar ba abin duk ya dame shi harda bawa
mami hakuri ya ce bai san zata dauki maganar
da gaske ba. Kayan fruits, snacks da sauran
kayan kwalama haka ya rinka siyowa kullum
yana kawowa Ju bayan kwana uku aka
sallameta. Tun daga lokacin kullum ya dawo sai
ya tambayi su Yasmin ko taci abinci. Wannan
abin ma da yake Umma na kallo tana sake sake
a zuci.
Ju dai kwalliya ta biya kudin sabulu don kuwa
taci jarabawar eng din saboda haka an bata
science class. Rayyan ya daukarwa kansa siyo
maltina, hollandia da su viju don kannensa su
sha ko su tafi dashi makaranta amma Umma da
yanzu bata da aiki sai lura da dan nata tasan
saboda Ju ya siya.
*************************
Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah Ju yau sun
rubuta exam dinsu ta karshe a SS2. Amma ita
farin cikinta biyu ne don kuwa yau zaayi musu
walimar sauka a gida Baba da sauran yan
gidansu duk zasu zo.
Gidan Marigaya Tafida yau a cike yake yayyen
Rayyan mata su biyu Yaya Kubra da Ummi
suma sunzo da yaransu. Ju dai hankalinta bai
kwanta ba sai da taga shigowar yan gidansu.
Baba taje ta rungume ta suma kuka. Hajja tace
maimakon kiyi murna sai kuka kuma Zuwaira. Ju
ta bata rai Hajja nifa ba sunana Zuwaira ba. Nan
dai akaje kowa ya zauna ga kawayensu da suka
gayyata da malamin da yake musu karatu a
gida. Taro yayi albarka su Ju sun sha wani lace
mai kyau da Abba ya dinka musu shi kuma
Abdul shadda yasa kalar lace din. Kowa da
kyautar da ya basu Ya Rayyan kuwa waya duk
ya basu mai kyau.
Ana cikin taro Amal ta fara tari wanda karshe
sai da tayi amai a jikin Ju. Bata ko nuna
damuwa ba taja hannunta suka koma cikin gida
ta gyara mata jiki. Mami ta kalli yadda yarta ta
zama babbar mace lokaci guda har tana kula da
wata tayi hamdala domin Juwairiyya ta sa ta
fita kunyar yayarta.
************************
Yana shigo da motarsa ya haske musu ido. Ba
wasu bane Ju ce da wani dan makotansu daya
dage yana sonta. Yauma Mami ce ta takura
mata sai ta fita. Rayyan ba karamin bacin rai
yaji ba wanda shima baisan dalili ba. Yana
fitowa saurayin mai suna Lawal yayi saurin miko
masa hannu su gaisa. Rayyan ya wani gintse
fuska da kyar ya mika hannu. Lawal yace Alh
Rayyan yanzu ni ka zama yayana. Ina fata zaka
min kamfen wurin kanwwar taka. Ju kuma irin
kunyar nan wa ya kamaka kana zance ta
sunkuyar da fuska tace Ya Rayyan sannu da
zuwa. Yace daka mata tsawa ke da izinin wa
kika fito. Come on get inside. Ta zumbura baki
ta shige wannan ai dizgawa ne a gaban saurayi
Allah Yasa ma bata fara sonsa ba. Tana tafiya
ya juya ga Lawal yace Mal kayi hakuri yarinyar
nan tana da miji kada ka sake zuwa nemanta.
Lawal cikin mamaki yace yallabai na tambaya
tace babu kusan minti 30 da fitowarta babu
wanda yace ta koma. Rayyan yace to ni nace
don ni ne mijin.
Ikon Allah wai dama Rayyan yana son Ju ne???
💕 JUWAIRIYYA 💞 8
Rayyan tsaye a reception yana ta kallon agogo
ya gaji da jiran abokinsa Abbas wanda suka yi
alkawarin haduwa a reception din hotel din da
akayi musu masauki zasu je shopping domin sun
gama abinda ya kawo a germany saura kwana
biyu su koma gida nigeria. Da gudu Abbas ya
fito daga elevator yana bashi hakuri. Rayyan
sanye yake da wani ash din wando da riga light
blue kayan sun masa kyau. Fuskar nan tasha
gyara don shi baya aske gemu duka yana barin
kadan wanda ya hade da gashin bakinsa. Da
yake shi fari ne sai gashin yake masa kyau.
Suna tafiya Abbas wanda tuni ya kawo kudin
auren Fauza yace mu shiga kantin kayan matan
can kasan mai hada lefe idonsa idon kayan
mata. Rayyan yayi dariya to bana son rashin
kunya dai kanwata ce. Dukkansu sunyi siyayya
shi Rayyan banda Amal harda kannensa ya
hada. Zai je wurin biyan kudi ya hangi wata
farar night gown sleeveless wadda bazata wuce
gwiwa ba kawai sai yayi imagining Ju a cikinta
nan da nan yayi tsaki Abbas yace mutumina lfy.
Rayyan wanda hannunsa har ya kai kan rigar
yace yarinyar nan is getting under my