kamar
yadda na binne zakaran nan Idris haka na binne
arzikinka da ganinka. Yadda gadon mahaifinmu
bai amfaneni ba kaima bazaka zauna cikin
jindadi ba. Ta cigaba da cewa tun daga ranar
duk sanda nayi niyyar fada sai inji tsoro kamar
idan na fada din Baba mutuwa zai yi. kowa ya
tausayawa Ju sannan malam yace gobe zan
dawo da safe muje wurin sa.
Anyi kwanan farin ciki gidan ranar sai dai Juvda
zullumi ta kwana don tsoron kada idon Baba
yaki budewa. Wurin 11 na safe suka shirya da
Abba, ya sagir da Ju sai malam suka wuce
wudil. Abin mamaki Ju a tsakar gida taga Baba
yana tafiya ba sanda. Mama ce tayi musu
bayani ai yau tun asuba idonsa ya bude. Nan dai
Malam ya sake basu wasu addu'o'in yace kuma
su kiyaye da yawan azkar. Mama ta tayasu
murnar samun lafiyar Amal tace zata zo kanon
idan an kwana biyu Baba ya kara jin sauki.
Maikoko tazo gulma ta kuma ganewa idonta
Baba ya sami lafiya. Taje ta fadawa Baba Yau
yace ke banda munafunci babu abinda kika iya.
Ina ce zaituna da Lami duk ciki garesu ga Tasi
baya da aiki sai shan kayan maye. Ki bari muji
da masifar gidanmu yanzu. Tace malam daga
kawo labari sai fada. Cikin fushi ya maka mata
carbin dake hannunsa ba ke kika rabani da dan
uwana ba. Matsa ki ban guri.
********************
Yau kwanan Ju hudu a wudil amma ko sau daya
Ya Rayyan bai kirata ba tunda ta taho. Da farko
tayi masa uzuri don Amal ta sami lafiya bayan
shekara hudu da ciwo. Sai dai a ranta tana sa
rai ko sau daya ya kira yaji jikin babanta. Wasa
wasa sai da tayi sati biyu a wudil amma kullum
suna waya da mutanen kano su mami da Amal.
Suna waya da Mami tace zuwan Sagir biyu na
dauka zaki biyu shi tace Mami zan tawo da Ya
Najib. Washegari Ju ta tashi da matsanancin
ciwon mara wato period pain ga zafin gari ya
isheta ta shimfida tabarma a tsakar gida ta
kwanta daga ita sai wata vest da dogon skirt.
Tana kwsnce bayan tayi amai Nafisa ta nayi
mata fifita sai suka ji sallamar su Amal. Tare
suke da Ya Rayyan suka shigo aka gaisa Mama
rungume da Amal tace mungodewa Allah da
samun lafiyarki. Amal ta kalli Ju da jikinta
kwatakwata babu kwari ta tambayi me ya
sameta. Bidaya tayi saurin cewa period pain ne.
Da kyar ta tashi suka gaisa da Amal tana yi
mata sannu. Ya Rayyan shima sannun yayi mata
ta wani harare shi duk da tana jin jiki. Tana
kokarin mikewa sai kawai ta fadi a sume.
π JUWAIRIYYA π 15
Da gudu Ya Rayyan ya tare ta ana ta sallallami
yace a bashi ruwa. Shafa mata ya rinka yi a
fuska Mama na fifita har ta dawo hayyacinta.
Kanta a cinyar Amal ta ganshi sai kawai wasu
hawaye masu zafi taji suna fitowa daga idonta.
Baba yace azo a tafi asibiti kwana biyu dama ya
lura bata cin abinci. Ya Rayyan yace indai ta
danji sauki gara su wuce kano kawai. Babu
wanda ya musa masa ita Amal da tazo wudil da
niyyar sati tare suka juya. Kafin su iso tayi amai
sau uku Ya Rayyan tuki yake kamar zai tashi
sama. Tafida Clinic suka wuce direct kafin su
karasa su Mami wadanda Amal ta kira a waya
sun riga su zuwa.
Bude ido tayi ta ganta kan gadon asibiti ga drip
a hannunta. Yasmin ce ta fara ganin ta tashi ta
taba Amal wadda take rike da hannun Ju har ta
fara gyangyadi. Wani hawayen taji suna hada ido
da Ya Rayyan ita kanta ta rasa dalilin wannan
kuka Mami tace dena kukan mana Ju kefa
dadina dake shagwaba. Ina yake miki ciwo
yanzu tace ciki ne. Baba likita da kansa yazo
yace kowa ya fita daga shi sai su Umma da Ya
Rayyan. 'Yata me yake hanaki cin abinci ulcer
tayi miki kamu irin wannan ya dubi umma kuma
abin ya hade mata biyu harda MP. Ana murna
yar uwarki da Alh Idris sun sami lafiya sai ki
tada mana hankali. Bata ce komai ba ya bada
umarnin a bata abu mai dumi tasha kuma bazai
bari ta koma gida ba sai yaga tayi biyun kibarta.
Mami murmushi tayi to ke taki ta same ki
kullum tuwo zan baki.
Amal tayi nacin a barta ta rinka kwana da Ju
Umma taki amincewa tace kema lallaba ki muke
yi. Muje gida Rayyan sai ka taho da Fauza.
Suna zuwa da Fauza Ya Rayyan yace ta zubawa
Ju kunun da suka taho dashi sannan yace ta
bashi wuri zasu yi magana. Kunun ya mika mata
karbi ki shanye ta karba tana sha kadan kadan.
ki bude baki kisha don kara miki zanyi.
Sai da yaga ta shanye yace Juwairiyya what
were you trying to do zaki dena cin abinci. Ni ba
dena ci nayi ba ta fada bata ko kallonsa. Baba
yayi miki karya kenan. Tayi saurin dago kanta
a'a. To meyasa kika tafi wudil bada izinina ba
nasa miki ido ina jiran ko zaki bugu kice ga
dalilinki amma ko sau daya banji wayarki ba.
Wani sabon kukan ta fara kinga idan bakiyi shiru
ba Allah a dakin nan zan kwana kowa yazo gobe
ya ganni. cijin kuka tace Yaya ko sau daya baka
kira kaji ya jikin Babana ba kuma ni saboda
naga Ya Amal ta samu lafiya shiyasa na tafin.
Kusa da ita ya koma ya zauna kice fushi kike yi
dani ko ya fada yana murmushi. Saboda haka
kika dena cin abinci I believe to kullum sai nayi
waya da Mama da Baba ki tambayesu ki ji.Ya
goge mata hawaye da hannunsa. Lallai ina da
aiki tunda na hadu da sarauniyar shagwaba. Ju
tausayin kanta take ji a ranta domin ta san
babban abinda ke damunta baya wuce son Ya
Rayyan da kuma tsoron rabuwa dashi tunda Ya
Amal ta warke don ita kam bazata yarda ta
hada miji da yayarta ba.
Satin Ju daya a asibitin su Mama harda Baba
sunzo dubata sau biyu daga wudil. Kebewa
Mami tayi da Mama tace idan Ju ta sami lafiya
sai mu fara shirin biki ko. Mama tace Yaya ban
tare ki ba amma inaga a ware auren nan da
Juwairiyya kada a sami matsala. Mami tace ko
kadan baza ayi haka ba tunda haka Allah Ya
kaddara musu auren miji daya dole su hakura.
*******************
Bayan an sallami Ju tana gida Mami bata sata
aikin komai wai gara ta huta. Kullum Amal zata
kaiwa Ya Rayyan abinci idan taje suyi hirar su.
Ko ya kirata suji bangaren Hajja. Wani lokacin a
gaban Ju ake hirar ma. Ko idan Amal ta dawo
tayi ta bata labarin yadda hirar ta kasance. A
wannan lokacin Ju ta tsani zaman gidan Mami
domin wani irin kishi take ji a ranta. Ni kam
bazan yarda muyi wannan zaman da Ya Amal ba
abinda take fada a ranta kenan kullum kuma
taga a gidan babu mai zancen auren nasu
saboda haka Amal bata sani ba. Ju ta yanke
shawarar yiwa Ya Rayyan magana.
Text ta tura masa na tana son magana dashi
yayi mata reply idan ya dawo zai nemeta. Ta
sake yin wani ita bata son kowa ya gansu. Yace
akan meye kike son maganar kawai sai ta tura
masa da reply din da ya tada masa hankali
( Yaya ina ganin ya kamata ka sanar dasu Baba
a warware auren nan dama anyi shi ne saboda
Ya Amal kuma ta warke. Nasan dukkanmu dole
aka yi mana gara kace ka fasa ku zauna lafiya
da Ya Amal nima sai na auri wani ).
Aikin da bai karasa ba kenan ya baro office.
Yana zuwa gida Umma ya nunawa text din tace
Rayyan tunda Amal ta warke kake neglecting
dinta duk irin halaccin da tayi mana. Nasan
ance a bari Amal ta yi wata daya da warkewa
kafin ayi mata zancen aurenku amma dole taji
ba dadi tunda tasan dama auren hadi ne.
Wallahi ina sonta Umma tun kafin ku hada kema
kin sani kawai ina kokarin samawa Amal
farinciki ne don ta wahala. Umma tace amma
kana yi ne at the expense of happiness din
Juwairiyya. Ka samu ka lallaba ta har a fadawa
Amal din.
Allah Ya taimake shi yau asabar Mami sun fita
da Amal sunje gidan Dada lokacin da zasu fita
kuma Ju da Yasmin sun tafi yin post UME
saboda haka ya sami chance din ganinta bayan
sun dawo. Abinci yace ta kawo masa taki zuwa
daga karshe da kansa ya bita falon Mami ya
sameta tana cin abinci sai ya karbi spoon dinta
ya zauna a hannun kujerar da take zaune yana
ci. Ju ta ajiye ta bar masa abincin sai ya tashi
shima ki biyoni ina jiranki tace bazan zo ba. My
Ju nima bakya raga min wannan tsiwar. To akan
text dinki zamuyi magana.
Tana zaune a kan kujera shi kuma gefen gado
yace naga text dinki kuma kiyi hakuri i got
carried away na share ki. Hajja ce ta bada
shawarar a bari Amal tayi one month da
warkewa sai a fada mata zancen auren ni kuma
ina tsoron kada taga ina yawan kula ki ban san
yadda zata ji ba shiyasa na hakura gaba daya.
Ya mike ita ma ya tayar da ita sai taji ya
rungume ta. My Ju dana fada miki you are
special i meant it from the bottom of my heart.
Ta suma yi masa kuka ni bazan iya kishi da
Yayata ba yace nima bana so kuyi amma haka
Allah Ya kaddara mana. Bazan taba sakin kowa
a cikinku ba you just have to learn to live
together. Ni.....sai tayi shiru. Ke me? Kishi
gareki haka Juwairiyya ya fada yana shafa mata
baya....gaba daya jikinta ya kama rawa Yaya ka
barni na tafi yace ba kina kishi bΓ ne ko haka
nake wa Amal idan tazo tayi saurin cewa a'a
ganin yadda ta tsorata ya bashi dariya. Bata
ankara ba taji yayi kissing dinta tun tana kokarin
gudu har ta hakura. Sai da ya sake ta yace this
is how much you mean to me. Tana kokarin fita
don gaba daya a rude take yace Ju ta tsaya cak
amma bata juyu ba I LOVE YOU kuma bazan
taba sakinki wani ya aura ba.
π JUWAIRIYYA π 16
Yau Ju ji take kamar an mata albishir da kujerar
makkah. Ita tasan ba auren soyayya suka yi da
Ya Rayyan ba amma indai Allah Ya kaddara
musu zama tare tana son ko dan yaya ne ya so
ta domin babu abinda take tsoro kamar auren
wanda baya sonta. Wai I love you, kai anya
kunenta ya jiyo mata da kyau kuwa. Haka ta yini
tana sake sake da ta tuna abinda Ya faru a
dakinsa kuma sai wani murmushi ya bayyana a
fuskarta.
Suna shirin bacci ita da Ya Amal, fauza da
Yasmin kowa tana bawa Amal labarin
saurayinta. Amal tace Ju wa kika samu mana
nan gabanta ya fadi sai kallon kallo tsakanin
yan matan Fauza tace Yaya kyale wannan ta
fiye boye boye. Ba yadda zaayi su fadi gaskiya
don an kwabe su sun san ba huruminsu bane.
Ya Amal tace ku barta idan tayi tsami zamu ji
ne. Ni dai kowa yasan nawa ta fada tana fari da
ido suna ta dariya tace yadda muka tashi gidan
nan iyayenmu ba kishiya muma Allah Ya tsare
mu da ita. Ju kam kamar an watsa mata ruwan
zafi. Sai da kowa ya kwanta ta tashi tayi alwala
tana nafila domin ita yanzu a tsorace take.
Tana addua tana kuka sai taji an taba ta. A
firgice ta juya taga fauza itama hawayen take.
Ju tun ranar da Ya Amal ta warke nake ji miki
tsoron makomar auren Yaya. Ju tace amma duk
baku yi min zancen cikin kuka gani nake kamar
yanzu i am intruding into your lives za ku fi
samun farin ciki idan na tafi. Fauza tace ko
kadan Ju nasan yadda Yaya ke sonki ko bai fada
miki ba kuma kema yanzu na yarda kina son
shi. Ki cigaba da addua nasan Allah bazai bari
ki tabe ba kuma suma iyayenmu baza suyi miki
sakayya mara kyau ba. fadawa jikin Fauza Ju
tayi tana kuka sosai i am confused fauza. Kada
abin nan ya bata zumunci. Hakuri Fauza ta rinka
bata har suka yi bacci.
*********************
Da safe wayar Ya Rayyan ce ta tashi Ju sai tayi
mamakin yadda bata farka da wuri babu kowa a
dakin koda yake kusan kwana tayi kuka. Me kike
har yanzu baki fito ba karfe goma da rabi fa ya
tambayeta. Tace Yaya ina kwana. Ban ganshi ba
ya bata amsa, haka aka koya miki ana gaishe da
miji. Zan koya miki at the right time yanzu dai ki
tashi kiyi breakfast kada kizo kina rike ciki
anjima.
Ta gama shiryawa zata fito fauza ta shigo dakin
tace Ju kinga yadda idanunki suka kumbura
kuwa. Ki dan yi kwalliya yadda zata boye idan
ba haka ba zaa gane kinyi kuka. Tayi murmushi
ta kara gyara fuska Fauza tace Yaya ya dace
wallahi.
Sun fito suna dariya suka hadu da Amal tana ta
danne danne a computer suka gaisa da Ju tace
mata Umma da Mami sun fita da wuri saboda
shirye shiryen biki zasu je zabar curtains dina
dana Fauza. Ju tace shine baku tashe ni ba ina
ta bacci ko gaisawa banyi dasu ba. Ta shiga
dakin Hajja ta gaisheta zata fita Ya Rayyan da
Ya Aliyu suka shigo ta gaishe su tana daga
labule zata fita taji wani abu yayi kara kamar ya
fashe tayi saurin fitowa suma su Ya Rayyan din
fitowa suka yi a tsatstaye suka tarar da Amal,
fauza da yasmin sai laptop a kasa ta rabe gida
biyu. Ya Rayyan yace Amal garin yaya kika fasa
min laptop. Bata bashi amsa ba sai ji suka yi
tas tas ta bawa Ju mari har biyu nan take
hancinta ya fara zubar da jini. Tana shirin kara
mata Ya Rayyan ya rike hannunta yace wallahi
kada ki kara. Ita Ju ta rike fuska tana hawaye
Hajja tace Habiba wane irin rashin hankali ne
wannan Amal na huce itama hawayen take ta
dubi Ya Rayyan amana ta zaka ci ta juya ga Ju
ke kuma munafuka shine kika dauki hotuna kika
tura masa ko ina kwance ba lafiya dalilin wan
ubanki shine zaki min kwacen miji. Wallahi baki
isa ba idan ma abinda ya kawoki gidan nan
kenan to da kafarki zaki fita. Dama talaka bai
san alkhairi ba. Hajja tace rufa min baki a
gabana kike wannan diban albarkar. Amal dai rai
ya gama baci bata yi shirun ba ta cigaba da
cewa Ya Rayyan da kanwata zaka ci amanata
shima ya gama kulewa amma ya daure yace
Amal ki zauna muyi magana a tsanake sai kawai
ta rarumi part din laptop din da ta fasa tana
kokarin kwadawa Ju a ka Hajja tace ke Habiba
yadda kike matarsa haka itama Juwairiyya
matar sa ce.
Amal sakin abin laptop din tayi a kasa tace ME
KIKA CE HAJJA
Gidan Alh Tafida akwai kallo
π JUWAIRIYYA π 17
Hajja ta sake cewa Rayyanu mijin Juwairiyya ne
kamar yadda yake mijin ki. Amal wata irin kara
ta saki ta fita daga falon da gudu ta koma
bangarensu. Dakin Mami ra shiga ta rufe kanta
ta zauna tana kuka mai tsuma zuciya. Wai ita
ce da kishiya? Kishiyar ma Ju.
Rayyan kokarin duba fuskar Ju yayi wadda ke
zubar jini ta hanci ta doke masa hΓ nnu. Itama
dakin Hajja ta shiga tana nata kukan. Hajja tace
wallahi bazaku tada min hawan jini ba ke
Fauziyya kira iyayenku su dawo gida. Rayyan
haka ya zauna a falon Hajja zuciyarsa na masa
suya. Har iyayen su suka dawo.
Amal bata fito daga dakin Mami ba sai da taji
Abbanta yace idan bata fito ba ta bari ya shigo
jikinta zai gaya mata. A falon Hajja wurin hada
ko warware ko wani al'amari aka zauna ga iyaye
ga ma auratan guda uku. Baba ne ya fara
magana yayi wa Amal fadan abinda tayi wa Ju.
Sannan yayi mata bayanin dalilin hada wannan
aure. Ya cigaba da cewa Amal duk abinda akayi
domin well being dinki ne. Saboda son kanmu ko
tunanin meye a zuciyar Juwairiyya bamuyi ba
aka daura auren nan. Iyayenta karshen halacci
sunyi mana tunda sunsan dalilin zamanta a kano
da irin dawainiyar da take dake amma ba musu
suka bada auren da muka nema. Yanzu don kin
sami lafiya kuma sai tashin hankali? Dama shiru
akayi wai ki kara samun lafiya. Sannan muka
sake yin shawarar sai kin shekara gidan miji
zata tare. Wannan magana gobe nake shirin
zuwa sanar da iyayenta sai wannan abu ya faru.
Baba, Umma da Mami suma duk bayanin da
suka yi mata kenan. Amal ta gama jinsu cikin
kuka tace yanzu da kanwata zanyi kishi Baba?
Abba yace ke ki fita idona wallahi duk abinda
akayi domin ki idan baki gode mata ba ai bazaki
saka mata da tsiya ba. Komawa tayi kusa da
Mami tana kuka don Allah Mami ki taimake ni
wallahi bana son kishiya. Bazan zauna da Ju ba.
Ju wadda tun zamansu banda sharar hawaye
babu abinda take sai share hawaye tace Abba
sai kowa ya juyu gareta ta cigaba don Allah ku
raba auren nan tunda Allah Yasa ta warke.
Kowa yaji tausayinta Rayyan kam ya kasa
magana amma Ju na ambaton saki yace ni
bazan saki kowa ba. Yana fadan haka ya fita.
Tashin hankali dai aka yini anayi a gidan. Mami
ta tsare Ju a daki tace kada ta sake ta fadawa
iyayenta abinda ke faruwa har ayi resolving
issue din. Ju tace to zata fita sai Mami tace
garin yaya Rayyan ya sami hotunanki har Amal
ta gani. Ju tace cewa yayi na tura masa kuma
lokacin ma bata warke ba. Kiyi hakuri Mami
shine kawai abinda tace ta fita.
*******************
Dare yayi ana shirin kwanciya yau Amal dakin
Mami ta tafi su Ju suna dakin Hajja. Amal dai
kukan ta cigaba da yiwa Mami tace ko sau daya
Ya Rayyan bai yi tunanin bani hakuri ba. Mami
duk tausayin 'yarta ya kamata tace kiyi hakuri
Amal nima ko kadan banso hadin nan ba amma
da naga it is to your own benefit na hakura.
Kuma kinsan Abbanki bazai taba yarda a raba
auren kowa a cikin ku ba.
Ju tana dakin Hajja tana aikin kuka don ita
wannan abin ita aka fi cuta. Gata cikin tashin
hankali kuma an hanata fadawa nata iyayen
balle su rarrashe ta. Hajja ta biyo su daki su
Fauza suna ta bata hakuri itama hakurin ta bata
game da irin abinda take fuskata a gidansu.
Tana shirin tada sallah Ya Rayyan ya kirata a
waya taki dauka. Yayi ta kira tana kallon wayar
daga karshe sai ta tura masa da text.
( yaya don Allah ka sauwake min auren nan
hankalin kowa ya huta )
Tana tura text din tayi saurin kashe wayarta.
π JUWAIRIYYA π 18
Sai bayan asuba bacci ya dauke Rayyan. Da gari
ya waye kowa a gidan bashi da cikakkiyar
walwala. Ju ta shiga bangaren Mami su gaisa
sai taci karo da Amal a falo. Ya Amal ina kwana
ko kallon Ju bata yi ba ballantana ta amsa. Ju
ta wuce dakin Mami anan ne Mamin ke
tambayarta ko zata aminci a raba nata auren da
Rayyan. Ju tace Mami ai tun jiya hakan na fada
yau ma kuma hakan zan fada musu. Tayi saurin
tashi saboda kukan dake kokarin kwace mata.
Mami ta tsayar da ita ko kina son sa ne? A'a
mami ai dama saboda Ya Amal ne na aminci. Da
sauri ta fita har tana karo da Ya Sagir tana
kokarin bashi hakuri hawaye wani na bin wani.
Yaji tausayin ta sosai bai ce mata komai ba har
ta fita ya wuce daki ya dauki key din motarsa.
Gidan Dada ya wuce.
Kamar jiya yau ma an sake taruwa falin Hajja da
niyyar kawo karshen wannan matsalar sai dai
yau kannen su Baba mata suna zaune. Kafin
kowa yayi magana Amal tace ni dai na hakura
da auren nan Hajja ya sake ni kawai na koma
makaranta. Baba yace bana son na sake jin
zancen saki a tsakaninku. Anti Usaina tace
yanzu ke Amal banda butulci irin na dan Adam
har zaki ce ba zaki zauna da Juwairiyya ba?
Amal ta suma hawaye Mami tace haba Usaina
me ya kawo maganar butulci kuma. Ta koma
kan Ju ke kina son zama dashi ne Ju ta girgiza
kai alamar a'a. Abba yace ku zaku yanke
maganar ne ko kuwa. Nan dai Ju ta tabbatar
Mami tafi goyon bayan yarta amma bata ga
laifinta ba.
Kowa da irin tasa shawarar karshe dai aka
yanke shawarar ya sake duk su biyun indai ba
zaayi sulhu ba. Amal sai kuka take ita zaa raba
ta da Ya Rayyan a dalilin Ju. Mami itama cewa
tayi bata yarda ba ai Ju din ba auren soyayya
tayi ba. Rayyan sai ya tashi ya dubi iyayensa
Baba ina son Juwairiyya bazan sake ta ba. Nan
fa wuri ya kaure da surutun mata kowa tana
fadin nata itama umma ta goyi bayan danta ya
zauna da wadda yake so.
Ana haka sai suka ji sallamar Dada da Ya Sagir
kafin ta zauna Ju ta rungume ta tana ta kuka.
Ya Rayyan kuΔ·Γ n nan har zuciyarsa yake ji.
Bayan ta gaisa da su Hajja ,Dada tace yanzu
Asiya yau kece akan yarki kike neman bata
zumunci? Mami ta harari Sagir wanda yace ni
naga yarinyar nan babu kowa nata a wurin nan
shiyasa na dauko Dada. Dada ta cigaba da cewa
Haj Habiba indai ba kwa bukatar wani taimako
daga yarinyar nan ni zan tafi da ita. Tazo
gidanku ta taimaka muku da abinda ko ke Asiya
da kika haifi Amal sai kin kai zuciya nesa zaki
jure masa amma ji yadda kuka taru a kanta
saboda Amal bata son kishiya. Yanzu ba don
yarinyar mai hankali bace kuna tsammanin da
tuni bata kira nata iyayen ba.
Hajja dasu Abba suna bawa Dada hakuri Sagir
ya lura Ju bata falon. Ina Ju tayi abinda ya
tambaya kenan hankalin kowa ya dawo inda ta
zauna.
******************
Ju ganin ana ta cece kuce a falon sai ta sulale
tayi waje tana tunanin ina zata je ba tare da an
gano inda take ba. A daidata sahu ta tara tace
masa ya kaita shagari qtrs. Daidai kofar gidan
Samira ta tsaya tace ya jira tana zuwa. Tana
sallama samira ta tashi da murna ta tare ta. Sai
Ju tace Samira bani 200 zan sallami mai
adaidaita. Sai data dawo Samira ta kamo
hannunta suka zauna lafiya yar uwa? Me ya
same ki haka? Ai kamar jira take nan Ju ta
fashe da kuka tana yi harda shessheka. Mijin
Samira yayi saurin fitowa sai tayi masa signal
da hannu alamun ya koma ciki saboda kan Ju a
sunkuye yake. Sai da tayi mai isarta sannan
Samira tace mu shiga daki muyi sallah sai muyi
magana.
Duk suna kan abin sallah basu tashi ba Ju ta
fadawa Samira abinda ke faruwa da ita. Tace
ina son Ya Rayyan Samira amma abinda yafi
damuna yadda zumuncin mu ke neman baci.
Wai ni Mami ke goyon bayan a saki. Wallahi da
Mama zata zo abin sai yafi baci don tafi Mami
zuciya da fada. Ni yanzu so nake idan basu
ganni ba asa ya sake ni na koma gaban iyayena.
******************
Wasa farin girki har magriba tayi babu Ju ba
labarinta gashi ta kashe waya. Su Mama anki
fada musu ana kokarin a gano inda take. Ya
Rayyan yafi kowa shiga tashin hankali, bai taba
sanin haka yake son Ju ba sai yanzu da yake
tunanin rasa ta.
π JUWAIRIYYA π 19
A bangaren Ju kuwa bayan ta gama bawa
Samira labari tashi tayi ta hado mata tea mai
zafi ta kawo mata. Ki daure ki sha Ju duk kin
fada tashin hankalin kwana daya kawai. Allah
Yasa lahirar mu tayi kyau. Ju tace ni bana jin
Yunwa. Samira ta harare ta so kike ulcer dinki
ta tashi ko to ba a gidana ba. Muna tsaka da
amarci Ya Rayyan yasa a kama mu. Dan
murnushi Ju tayi, Samira tace idan ma baki sha
ba kulle ki zanyi a daki na kira yan gidanku.
Ju na zaune a falo tare da Samira da mijinta
yace gaskiya na tausaya miki sai dai ya kamata
ko mutum daya ne a sanar inda kike saboda
halin rayuwa. Yanzu Allah kadai yasan halin da
suke ciki.
Hankalin Baba a tashe tun jiya yake kiran Ju
baya samu. Itama ma Mama tace tun tana kira
wayar na shiga har ta dena shiga. Daga karshe
dai Mami ta kira wadda a wannan lokacin sun
gama rudewa da rashin sanin inda Ju take.
Tana ganin wayar kanwar tata Abba ta mikawa
shima yace me zan fada musu, sun bamu
amana mun ci? Da suka ji shiru baa dauka ba
Mama ta kira Dada tana kuka tace tun jiya na
kasa samun Juwairiyya ita ma kuma Yaya bata
daukar wayar. Dada dama bata bar gidan Hajja
ba tace Mariya gobe ku taho kano. Mama na jin
haka sai kuka ta ajiye wayar ta fadawa Baba ya
fita ya kira Ismail da Najib. Gaba dayansu a
motar Najib din suka gwamutsa harda su
Bidaya. 9:47 suka isa gidan Hajja.
*********************
Lallai kudi da 'ya'ya suna iya haddasa fitina a
doron kasa domin yau Mama ta fadawa yayarta
kalaman da bata taba tsammani ba akan
Juwairiyya. Mami shiru tayi domin tasan rabon
da suyi fada irin haka da Mariya tun irin fadan
sakonni ta tabbatar bata kyauta mata ba. Gaba
daya gidan ya hargitse Baban Ju yace ni dai
Alhaji Bashir ku taimake ni a raba auren nan
kowa ya huta. Hajja dai ranar har kuka tayi
yadda al'amarin ya lalace lokaci guda. Tace
Mariya kiyi hakuri in Allah Ya yarda zamu ganta
domin tana da hankali nasan bazata inda bai
kamata ba. Kowa yaje ya kwanta dare yayi gobe
sai mu san abinyi.
Su Mama dai gidan Dada suka wuce don tace
bazata kwana a gidan ba.
Ya Rayyan kuwa tunda aka fara neman Ju ya
fita daga gidan. Ya rasa inda zaije dubata domin
kuwa kawayenta kadan ne a kano. Karshe
gidansu Abbas ya tafi sai dai cikin dare zazzabi
ya rufe shi baya ko iya magana. Wurin karfe uku
na dare Abbas ya kaishi asibiti aka kwantar
dashi.
********************
Yadda iyayenta basu yi bacci ba itama Ju haka
ta kwana kuka, sallah da adduar neman mafita
daga Allah. Amal kuwa duk sai ta tsani kanta.
Me yasa tabi son zuciya ta cutar da kanwarta?
Gashi yau a dalilin ta iyayensu sunyi fada gida
ya rasa kwanciyar hankali.
Da safe mijin Samira yace da Ju wa ta yanke
shawarar a sanar da inda take. Sai tace zata
tafi gidan kakarta. Samira tace kaga gara mu
kaita da kanmu don kada tayi wani wurin. Sha
daya na safe suka shiga gidan Dada sai dai
sunyi rashin saa bata nan. Ju tace nasan ta
koma gidan Hajja ku barni a nan zan shiga
makotan ta