An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Arewa hausa novels
Novels villa
Duniyan novels
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)
WHATSAPP NO:
+2347039625239
💕 JUWAIRIYYA💞
Zuciyarta cike da fushi tana ta sauri kamar ta
tashi sama. Duk wannan saurin tsoronta daya
kada Tasi ya shiga gida kafin ta cimmasa. Yau
sai ta masa dukan tsiya wallahi don ita bata
tsoron ta mutu bare tayi rai. Nafisa ce ta taba
ta tace Yaya kinga Tasi chan da abokansa.
Kafin ta gama magana yayar tata ta ruga da
gudu taci kwalar Tasi cikin fushi tace kai don
ubanka me ka fadawa malam dazu a islamiyya.
Ya make mata hannu tare da cewa gaskiya na
fada masa, ba wani abu yasa kuke makara ba
face rike sandar tsohonku da kuke aje bara.
Abokansa kuwa sai ihu da dariya suna fadin sai
'ya'yan Idi makaho.
Zuciyar mata fa tazo wuya nan ta rufe ido tana
kai musu dukan mahaukata. Da Allah Ya bata
sa'a ta kama kwalar Tasi sai kokawa ta
kachame. Nafisa da Bidaya suna ganin abin ya
baci sai gida da gudu.
Mama tana kwasar tuwo ta gansu a gigice ta
fara fadan yau ma tseren kuka yi ko kamar
maza. Bidaya tace Mama Yaya Ju ce suke fada
da Tasin Baba Ya'u. Nan take ta saki marar
dake hannunta tana kwalawa Ismail kira. Ya fito
yace mama naji abinda suka ce muje ki raka ni
Bidaya.
Akan Tasi ya hango ta tana tula masa kasa a
baki yara sun taro ana ta wakar ku casu
bamban ku casu. Ismail yayi sauri ya finciko
kanwarsa tare da bata kyawawan mari har biyu
sannan yaja hannunta gida.
A tsakar gida suka riski iyayenta wanda tun
kafin su iso ake jiwo kukanta daga soro don ta
maru. Mama cikin fushi itama ta damko ta ta
fara duka tana fada. Yanzu Juwairiyya bakya jin
dadi sai kin dauko min magana ko. Ta cigaba da
cewa shekarunki goma sha hudu fa amma
bazaki dena dambe da maza ba. Na fada miki
ke macece ba namiji ba yayyanki maza ma
wallahi basuyi abinda kike ba. Duk wannan abin
da ake Juwairiyya bata ce komai ba kukan ma
ta dena ganin yadda babanta yake lalube da
hannunsa yana kokarin hana mama dukanta.
Yace Mariya kiyi hakuri don Allah ki bar
dukanta. Juwairiyya ta kama hannun babanta ta
zaunar dashi akan tabarma. Yana zama ya lalubi
kunnenta yace wai meyasa bakya jin magana.
Ta share hawayen idonta tace Baba zaginmu
suke harda cewa bara muke raka ka. Wallahi
idan zasu zageka sau dubu zan rama sau dubu
ai ba tsoronsu nake ba. Ismail yayi saurin doke
mata baki wato ana miki fada ke ko gezau
bakiyi ba har kina dada maida martani. Baba
yace bari dukanta haka. Ya sake rike mata
hannu yace Juwairiyya kinsan dai dani da baban
Tasi wa da kani ne ko. Ta kada baki tace ai ba
babarku daya ba. Mama ta jefa mata harara
tace wai baza kiyi shiru ba. Baba ya cigaba da
cewa ki rinka hakuri akan duk abinda zasu fada
miki ko yan uwanki. Kinga Ismail da yayanku
Najib basa kula su, kuma ma ai duk garin nan
babu wanda zaice ya taba ganina da kwanon
bara. Nan duk 'ya'yansa dake wurin suka yi
murmushi saboda yanayin da ya fadi maganar
banda mama da ta ce Alhaji kaine kake sa
yaran nan basa daukar maganarka da girma
saboda kana musu wasa. Yace to kowa ya kallo
ni nan suna kallon shi kuwa ya sha kunu a dole
ya bata rai suka sake yin murmushi Ju kuwa har
sautin dariyarta ake ji. Yace don Allah ku dena
biye musu ko me zasu fada. Lalurar makanta
jarabawa ce daga Allah. Da ina da idona
rangadau farare kal kamar na Najib da Ismail.
Kuyi hakuri yan mata bansan yaya naku suke
ba. Amma dai abinda nake so ku gane shine ni
bana bakin ciki da niimar da Allah Yayi min da
kuma cikin ikon Sa yanzu ma da lalurar tazo
bamu kasance cikin kaskanci ba. Zai cigaba da
magana yaji kiran sallah sai yace a tashi ayi
alwala Allah Yayi muku albarka. Ju ta debo wa
babanta ruwa ta zuba masa yayi alwala ismail
yayi masa jagora zuwa masallaci
**********************
Bayan kwana biyu da fadan Ju da Tasi tana
dawowa daga makarantar boko taci karo dashi a
kwanar gidan liman shima ya taso da yan
korarsa a baya Lado da Haladu. Suka fara binta
da sauri dama yaci alwashin rama abinda tayi
masa a rannan duk da rashin mutumcin da
babarsa taje tayiwa maman su Ju har gida da
wanda babansa yayiwa babanta a kofar gida. Ju
dai ko a jikinta data gansu duk da cewar ita
kadai ce yau abokiyar tafiyar tata Madina bata
je makaranta ba saboda ranar hutu ce garesu
yan aji biyar an gama jarabawar kwalifayin zasu
dan kwana biyu a gida kafin sakamako ya fito.
Tasi da abokansa suka samu suka tare mata
hanya yace ke ubanwa kika zubawa kasa a baki
shekaranjiya?Tace uhmm wai dani kake? Yace
hade girar sama da kasa ya sake maimata
tambayarsa. Tace to ubanka na zubawa mai
jajayen hakora.
Tasi yace yarinya yau kin gama yawo. Ya
cakume ta zasu fara kokawa ta aje jakarta a
gefe ta Allah Ya gani bani na takali fadan nan
ba.tana fadin haka ta kai masa duka a ciki nan
fa maxa uku suka far mata suna dukanta amma
bakinta yaki mutuwa sai masifa take tana
dukansu itama. Liman ne ya fito yaga abinda ke
faruwa yayi musu tsawa suka tsere. Ju kuwa
yau an mata taron dangi hijabinta ya yage har
kasa ga wuyan riga shima ya yage har kusan
cibiyarta. Gashi ita yarinya ce mai garin jiki
kirginta ya kusa gama cika. sai da liman yace
wuce ki tafi gida ta kula da yadda kayanta suka
yi budu budu ga yagewa. Yau tasan ta gama
yawo a wurin mama.
**********************
Ju ta bayan gidansu ta zaga ta taka wani
kututturen itace ta haura katanga. Tana dira
bidaya tana watsa shara nan take ta kwala ihu.
Mama ce tazo da gudu tana tambayar
lafiya.itama turus tayi yadda ba don jininta bace
itama bata gane ju ba. Bidaya kuwa runtse ido
tayi tana fadin mama aljani. Mama kam ko baa
fada ba tasan yau ma yar tata tayi sanaar da ta
saba. Batare da cewa komai ba ta koma da
baya taje ta tada Najib wanda bai dade da
dawowa daga makatanta ba yana level 3 a
jamiar garinsu wato wudil wadda aka fi kira da
KUST. Tace fito a hankali kada babanku yaji ina
jiranka a wurin shanya. Ai nan ya sameta da
wayar redio a hannu ta bashi ta nemi wuri ta
zauna a kasa tace zanemin 'yar iskar yarinyar
nan wadda bata jin magana. Najib dama haka
nan ma cin zali ne dashi bare an bashi license.
Nan ya fara dukanta ko tambayar baasi babu.
Kamar kullum yauma ba ihu sai hawaye da take
zubarwa a zuciyarta kuwa tana kara rayawa
wallahi duk wanda zai zagar mata uba Allah ne
zai raba ta dashi. Ju kenan ta baba idris.
Tun da ta fara wayo ta gane babanta makaho
ne take tausayinsa. Wani lokacin sai ta sami
loko tayi ta kuka saboda tausayinsa. Akan baba
Ju ta fara qiyamul layl tunda wata rana malamin
su yace duk mai yinta komai ya roka Allah zai
amsa. Mama da kanta ta fuskanci hankalin Ju
kamar baya tare da ita tace wa Najib ya kyale
ta. Suna juyawa suka ga baba a tsaye rike da
hannun bidaya. Yace idan kun gama dukan ku
bani 'yata. Ju wadda kanta yake a durkushe
tana jin muryar Baba sai kuka mai tsuma zuciya
taje ta kankame shi tace wallahi baba na tsane
su kuma bazan yafewa duk wanda ya zage ka
ba.
Wannan abu yasa Mama kuka itama. Suka koma
dakin Baba gaba dayansu sai yace a fita a
barshi da mama da ju. Kowa na fita yace
Juwairiyya kina so inyi fushi dake ne. Tayin
saurin cewa a'a. Yace to daga yau idan kika
sake fada a waje a kaina bani ba...bata bari ya
karasa ba tace WALLAHI WALLAHI WALLAHI
bazan kara ba.Sai yace tashi kije Allah Yayi miki
albarka. Tana fita yace mariya yarinyar nan ta
gado fushinki. Ita kanta mama yadda Baba ke
magana ya bata tausayi domin tunda ya kamu
da lalurar nan baya ko daga murya yace yana
gudun kada ladan hakurinsa ya ragu. Mama tace
Alhaji yau fa duk kayan jikinta a yage suke gashi
kamar an mata wanka da kasa. Yarinyar nan
mace ce amma abinda take ko namiji ne dole
ayi masa fada.Baba yace mu cigaba da yi mata
adduar shiriya da kuma sassautawar zuciya.
********************
Hajiya Asiya ta dubi yar uwarta tace ni tun ranar
da kika min waya akan fadan da Juwairiyya tayi
hankali na bai kwanta ba don babansu Amal
baya nan ne da washegari zaki ganni a garin
nan. Idan kin yarda mariya ki barni na tafi da ita
kano tunda ta gama jarabawa kafin result ya
fito. Mama tace anya yaya ayi haka da dai kin
bari sai nan da sati ukun muzo bikin Amal tare.
Yarinyar nan kawa zucin gida gareta gashi duk
safiya da dare sai tazo taga babanta. Haj Asiya
tace wai kin manta yadda kike likewa baba ne
da kamar kaska ta fada taba dariya. Kuma
yarinyar nan ina ga kawai tausayin babanta take
yi. Ga karayar arziki ga makanta lokaci guda
dole a tausaya masa. Ki bari mu tafi muyi shirye
shiryen bikin yayarta Amal da ita tunda su
nafisa basu yi hutu ba ga Alhaji bazaki iya zuwa
da wuri ba.
Baba ma ya amince bayan da mama tayi masa
bayanin shawarar da yayarta ta kawo. Ju kuwa
an gama hada kaya da murnar zuwa wurin yaya
amal sai dai kafin ta isha ta lallaba ta fita taje
gidan wan mahaifinta wanda shine silar karayar
arzikinsa da makantarsa ta sami Baaba mai
koko tana tatar gasara ta tsaya ta kama kugu
tana murguda baki tace mai koko zan tafi kano
gobe nasan duk kowa yana ciki suna sanaar
kallo to ki fada musu duk wanda ya zagar min
uba ko yan gidanmu Allah Ya isa. Tana fadin
haka ta ruga ta koma gida. Mai koko ta bata
sami mayar da magana ba ta rike baki tace bari
malam ya dawo idan bamuyi da gaske ba
yarinyar nan zata tona mana asiri wata rana.
Sai mun sake haduwa da jin rayuwar Juwairiyya
(Ju) a kano da asirin da su Mai koko suke
tsoron ta bayyana.
💕 JUWAIRIYYA💞 2
Jan motar su Haj Asiya ke da wuya mal Yau ya
fita shima bayan sun gama shawara da maikoko.
Bakin titi yaje ya tari mota sai wani kauye. Boka
Dillin yana ganinsa yace mugu dan masara yau
kuma bayan wa kake son gani. Mal Yau ya
zauna a inda ya saba idan tasa ta kawo shi
yace yarinyar kanina ke neman ballo min ruwa
kasan na fada maka tasan komai don ma kayi
kokarin rike bakinta ne. Amma fa bata tsorona
yanzu kada wata rana tayi magana. Sannan
akwai yayar babarta kusan ita ce gatsnsu
yanzu. Itama ina son a hada su duk a tada musu
hankali. Tazo ta dauki Zuwairan sun tafi kano
bikin yarta. Boka yayi dariyar mugunta yace
indai wannan ce matsalar to an gama fadi wata
idan akwai.
*************************
Ana bude gate din gidan Haj Asiya wani dadi ya
rufe Ju. Ita dai tana son gidan mami kamar
yadda yaranta da suma yan gidansu suke kiran
Hajiyan. Bari uku ne a cikin tankamemen gidan.
Daya na Alh Bashir mijin mamin sai na wansa
Dr Umar sai kuma na babarsu Hajja a tsakiya.
Mami tace Juwairiyya muje mu far gaida Hajja
ko. Tace to Mami ai ni ina sonta tunda tana
zuwa duba Baba. Mami tayi murmushi ita kam
ta rasa yadda akayi yarinyar nan take son
babanta haka.
Suna shiga Ju taga 'ya'yan wan babansu Amal
da take kusan saar su Fauza da Yasmin sun
takurawa Hajja wai sai sun daura mata
gwaggwaro da biki tunda bikin jikokinta biyu
zaayi. ita kuma Hajja ta dage tana turewa abin
ya ba Ju dariya tana kokarin karasawa gaban
Hajjan su gaisa taji ta taka wani abu, kafin ta
ankara ta juyu kuwa aka hankada ta ta fadi
kada kanta ya bugu da hannun kujera. Tan take
kowa hankalinsa ya dawo gare ta wanda ta taka
kuwa cikin fushi ya tashi yace are you stupid?
kina tafiya bakya kallon gabanki. Hajja tace
Asiya duba min goshin yarinyar nan. Kai Rayyan
tun dazu nace ka tashi daga kwanciyar nan kayi
hanya kaki. Ju kafin Mami ta taba ta ta shafa
goshinta taga jini ai nan taķe ta manta da
manya a gabanta tace kan uba ka fasa min
goshi. Allah Ya isa, kazo ka kwanta kan hanya
kuma ni ina jin na taka maka kafa niyata na juyu
na baka hakuri. Mami ta daka mata tsawa tace
ke Juwairiyya bana son rashin kunya. Ta juya ga
Rayyan tace yi hakuri babban yaya. Sai a
lokacin ya durkusa ya gaishe da mami sannan
kafin ya fita yace ni dai Mami indai wannan
ce mai aikin da zaa daukarwa Amal na mun
yafe. Hajja tace kuga yaro mara kunya babar
matar taka kake fadawa haka? To yarta ce
itama.Mami tace Hajja ya zaki korar min da.
Duk suka yi dariya sannan suka gaisa
******* ***************
Bayan anyi sallar azahar Ju da Amal sun cin
abinci tare suna hira Mami ta fito daga daki ta
zauna kan kujera tace Amal idan anyi laasar ki
dauki Juwairiyya kuje ku gaida Dada. Tace to
Mami amma motata tun safe Abdul zaije siyo
min mai giyar ta makale sai dai mal Garba ya
kaimu a taki. Mami tace na aike shi gidan mai
turaren wuta. Abdul yace dazu naji Ya Rayyan
yace zaije yau. Mami tace to ka fada masa
akwai yan rakiya. Amma jira su gama cin
abincin ka raka kanwarka ta gaida Umma.
Sunje sun gaida Umma matar Baba Umaru har
Ju ta zauna hira wajen su Fauza don ita Mami
duk yaranta shida maza ne sai Amal ita kadai.
Bayan laasar sun fito zuwa gwangwazo gidan
kakarsu babar su Mami wato Dada sai Ju ta
hango Ya Rayyan tsaye jikin mota ai kuwa ta
taba Amal tace yaya da wancan mutumin zamu
je. Tace eh Ju tace shine fa don wulakanci yace
min mai aiki. Amal ta kwashe da dariya tace kin
dai rama ko. Tace a'a amma zan rama. Abdul
autan mami wanda dashi zaa yace ke Ju shine
angon fa. Ta zare ido tace angon wa yace na
yaya Amal. Ju sai tayi tsit da baki har
sukavkarasa mota. Suna shiga Amal tace Ya
Rayyan shine ka kira kanwata mai aiki ko. Yana
kokarin ribas da mota yace yi hakuri amarya ai
ban sani ba.kanwar taki ce akwai baki kamar
reza. Ju dai da tasan angon yayarta ne da tayi
shiru da bakinta amma jin yace bakinta kamar
reza yasa ta bata rai. Shi kuwa sai ya cigaba da
cewa she talks alot, i could hear her voice from
my room. To Ju taga abin kamar da rainin
hankali wai ana magana da turanci a gabanta
tace a ranta wallahi sai na rama. Ko yaya
Rayyan kalli mudubin zai duba bayansa sai yayi
ido hudu da Ju ita kuma tana lura da hakan da
ya kallo sai ta murguda baki a haka har suka
isa gidan Dada.
*********************
Kwanan Ju uku a gidan Mami amma duk gidan
ya fara isarta. Sau biyu tun zuwants ta hadu da
Ya Rayyan amma yana ganinta yake bata rai.
Inda sabo ta saba da ganin mutanen da basa
sonta a gidan baba Yau amma abinda yasa
wannan ke damunta tausayin Yaya Amal take
ace mutum irin wannan zata aura mara fara
yadda take da son mutane.
Yau gidan Hajja a cike yake da baki 'ya'yanta
mata Hassana, Usaina da Habiba na duk sun zo
saboda taron gaggawa da Hajja ta kira sati biyu
kafin a fara biki. Babu kowa a falon sai yayanta
maza da matansu sai matan da kuma Amal da
Rayyan. Baba Umaru ne ya fara magana da
tambayar yaran shin a falon nan akwai wanda
ya taba baku shawarar auren juna? Suka ce a'a.
Yace madalla. Ku kuka hada kanku sannan kuka
sanar damu sai yanzu saura sati biyu auren ku
Amal kice kin fasa. Amal wadda kanta a kasa
yake tunda aka fara magana tace wallahi Baba
idan na aure shi wani mugun abu zai same ni
kila ma na mutu. Rayyan wanda ko daren jiya
bayan sun gama hira sun dade kuma a waya
abin sai ya zo masa wani iri don shi duk a
tunaninsa irin nasihar nan aka zo yi musu. A
firgice ya dago kai yace Amal what did you just
say?. Mami tace na shiga uku Amal lafiyarki
kuwa. Anti Usaina tace ni dai yau bayan asuba
ta kira ni ta fada min tana kuka shiyasa nazo na
sanar da yaya. Hajja tace zo nan Habiba dayake
shine sunan Amal na gaskiya. Me ya hadaki da
dan uwanki. Cikin kuka tace ba komai. Babanta
wanda ya rasa abin fada ya dafe kai yayi shiru,
Mami itama cikin kukan tace Alhaji kana jin
abinda yarinyar nan take baka ce komai ba. Nan
dai ya dago kai yace Rayyan kana son auren
nan? Yace eh Abba amma ..... bai karasa
magana ba Abba ya mike ya fita. Baa jima ba ya
dawo tare da Sagir dansa da kuma Aliyu wanda
yake bin Rayyan ya dubi yayansa yace ni dai
indan har kun amince a daura auren nan yanzu
naga iya gudun ruwanta. Ya dubi Amal yace
uwata yau ba don abin nan na gida bane so kike
ki mayar dani karamin mutum. Anti Hassana
tace yaya Bashir abi maganar nan a hankali. Ta
kalli Rayyan tace ka fada mana gaskiya me ya
hada ku. Shi da jin abin nan yake kamar wani
mummunan mafarki yace wallahi anti babu
komai, Amal tace na gaya muku babu komai
auren ne bana so. Nan babanta ya kwada mata
mari. Baba umaru yace meye haka Bashir ina
wuri kana zartar da hukunci. Hajja kam kuka
take sosai don tashin hankali ganin haka dai aka
yi shawara akan a daura auren idan ma hure
mata kunne ake sa yi maganin abin.
A gabansu Abba Bashir ya bada duba dari a
matsayin waliyin Rayyan shi kuma Baba Umaru
ya karba sauran yaransu maza suka yi sheda.
Sagir na gama addua Amal cikin wata irin murya
kamar ta maza mara dadin sauraro tace kun
daurawa kanku bala'i. Tana fadin haka ta fadi
timmm a kasa. Nan da nan kowa yayi kanta
cikin rudewa ana salati.
Wai meke shirin faruwa a gidan Hajja ne daga
zuwan Ju?
💕 JUWAIRIYYA 💞 3
Sagir da Rayyan ne akan Amal suna kokarin
dagata amma duk sun kasa. Baba Umaru yace
wai me kuke jira ne ku dago ta akai ta dakin
Hajja. Sagir yace Baba mun kasa fa. Nan dai
hankali ya sake tashi Abba ya fita ya kira liman
aka zo ana ta karatun Qur'ani da adduoi.
Ju da sauran yaran da baa barsu sun shiga
bangaren Hajja ba duk hankalinsu ya tashi don
ko baa fada ba sun san ba lafiya yadda suka ga
manya suna ta shige da fice.
Sai bayan magriba Amal ta farka daga yanayin
data shiga ta fara kuka. Anyi anyi tayi shiru abu
ya gagara karshe dai gidan Marigayi Tafida
Abubakar ranar baayi kwanan farinciki ba.
Duk wannan tashin hankali Mami ko kadan
batayi kuka ba don sai a yau ma ta kara yarda
kuka rahama ga bawa. Asubar fari ta kira
kanwarta Mariya a waya ta sanar da ita duk
abinda ya faru, sai a lokacin mami tayi kuka
tace mariya ban fadawa Dada ba.Mama tace
karki damu in shaa Allah yau zan zo. Bayan sun
gama waya tayiwa Baban su Ju bayani shima
hankalinsa ba karamin tashi yayi ba kuma yayi
mats izinin tafiya. Mama ta barwa su Nafisa da
babban yaya Najib sallahun yadda zasu kula da
gidan da babansu kafin ta dawo. Fitarta ke da
wuya wurin 7:30 na safe taci karo da Lawi dan
baba Yau ko kallo bata ishe shi ba ya juya ya
koma gida. Yana shiga yace da mahaifiyarsa
naga ta fita amma ita da Ismail ne inajin tasha
zasu. Har ya juya zai koma daki sai yaga yadda
innar tasa ta washe baki. Yace wai inna meyasa
tun jiya kika ce nasawa mutannen gidan can
ido. Tayi murmushi har wawolunta na hakoran
gaba ya bayyana tace kai dai jeka nagode. Da
sauri maikoko ta shiga daki ta tashi malam Yau
tace inajin fa abin ya tabbata don munafukar ta
fita kuma inajin kano ta nufa. Yace ai kinsan
aikinsa na kyau a hankali maji wane tashin
hankalin ya tura mu.
**********************
Rayyan ba karamin damuwa ya shiga ba da gari
ya waye ya shiga bangaren Abba suka gaisa da
Mami da Mama wadda take ta sharar hawaye
bayan ta ga yadda Amal ta ke ance tunda ta
farfado haka ta kwana kuka ba sauti sai
hawaye. Rayyan ya zauna a kasa yace Mami
Abba ya tashi kuwa kafin yayi shiru Abban ya ce
gani Rayyan sannan ya zauna suka gaisa da
mama. Rayyan yace Abba ni dai idan babu
damuwa ko warware auren nan zaayi don ta
sami lafiya. Bazan taba samun kwanciyar
hankali ba nasan nine silar ciwon nan. Abba yayi
murmushi yace yaro kenan ai rayuwa ba haka
take ba. Ni bamu san Amal da lalurar aljanu ba
amma wallahi bazan taba yi musu yadda suke
so ba indai aure ne basa so tayi to sai dai suyi
hakuri don Allah Yafi su. Zamu nema mata
magani har Allah Ya bata lafiya. ka bar auren
idan har sauki bai samu ba da kaina zan shige
maka gaba kayi wani auren. Rayyan sai ya fara
kuka kamar yaro wanda hakan yayi daidai da
shigowar Ju falon tana ganin
yana kuka tace yi hakuri zata sami lafiya in
Allah Yarda. Takaici ne ya kama Rayyan ace sai
a weakest moment dinsa yarinyar nan zata shigo
harda wani bashi hakuri.
Wasawasa yau sati biyu da fara ciwon Amal
kullum zata fadi kamar sumammiya kuma tayi
mugun nauyi idan ta farfado kuma sai kuka har
cikin bacci tana hawaye. Da farko asibiti aka
kaita tayi sati daya tasha allurai da drip amma
duk a banza don ma asibitin na Baba Umaru ne
so baa biyan kudin treatment. Hajja da Dada ne
suka yanke shawarar a dawo da ita gida
malamai suyi aikinsu.
Mama dai kwananta goma a kano mami tace ta
koma wudil kada abin ya zama rashin hankali ta
bar yara da babansu shima kuma da tasa
lalurar. A dole ta tafi don tasan hakan ne yafi
dacewa amma kafin ta tafi mami ta roki
alfarmar a bar mata Ju domin bata da waata
mace ita take taimaka mata da ayyukan gida
kafin su koma makaranta.
Haka Ju ta zauna sai gashi cikin ikon Allah ita
kadai Amal ke yarda ta taba ta ko malami ne
yazo ita ke riko hannunta su fito falo don tuni
aka barta a dakin Hajja.
kullum safiya zata yi wa Mami shara da yan
sauran ayyuka duk da akwai mai aiki. Idan ta
gama zata je ta gaishe da Hajja ta bawa Amal
abinci.
**********************
Kwana biyu ya rage Ju ta koma Wudil sai amal
ta dena magana. Ana zaune zata yi fitsari ko
kashi sai dai aji wari dole tasa dena fito da ita.
Wannan kukan ya ragu amma ta dena magana
sai nuni idan ta ga dama. Ranar da ta fara
fitsari a zaune Mami tasha kuka don taga alama
yarta ta zama nakashashshiya akayi akayi ta
tashi a gyarata taki. Ju tana ganin haka itama
sai kuka don