Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 6
yaɗau waya yakira Habeeb, yace mishi dan Allah ka nemamin jirgi yanzunnan, Habeeb ne yace ok kasameni a Airport, Ahmad yajuya motarshi yakoma Adamawa zuwa Airport, Yana zuwa yatarar da Habeeb harya karɓa mishi pass, Yamika mishi hannu suka gaisa, Yace yau ba surutu sauri nake, Habeeb abun yabashi mamaki taya za'ayi Ahmad yayi sauri haka? Duk yanda akayi akwai matsala. Mangariba cif yashiga garin KD, Yana sauka a Airport yafita da sauri yatari Napep, Yawuce sai gidan Mommynshi, Yana zuwa me gadi yahanashi shiga, Yarokeshi, megadin yace bazan yadda na rasa aikina ba Ahmad! Hajiya tace duk ranan dakazo nabuɗe maka kofa abakin Aikina, Amma Alfarma ɗaya zanyi maka Shine kazauna anan yanzu Fareedah zatazo dan hajiya ta aiketa, Idan tadawo saika faɗa mata sakonka.. Be gama magana ba, saiga motar Fareedah ta kunno kai, Tana ganin Ahmad ta ɗauke kanta tana kokarin shiga gida, Ahmad ne yayi mata Alama da hannu, yahaɗa hannunshi waje ɗaya Alaman yana neman Alfarma, Hakika Fareedah taji tausayin Ahmad yau, ganin duk yanda yabi ya rame yayi baƙi kamar bashi ba! Saita buɗe mishi ɗayar kofar tayi mishi Alama dayazo, Ahmad ne yasauke ajiyar zuciya, Yatashi yaje yashiga motar, Yana shiga megadi yabuɗe mata get tawuce ciki, Acikin gida ta tarar da mommy tana zaune tayi tagumi kamar kullum. Tana fita amotar tabuɗewa Ahmad shima yafito. Mommy kamar daga sama taga Ahmad acikin gidanta kuma amotar Fareedah, Tashi tayi ta iso inda suke, Tana zuwa ta fesawa Fareedah mari har guda uku, kana tace "Fareedah bakida hankaline? Kokin manta me nace miki? Ko kin fini son Ahmad ɗinne? " Fareedah tayi shiru. Ahmad ne duk jikinshi yayi sanyi, Har yayi dana sanin zuwa, Yatsuguna kasa zai fara magana mommy tace idan kasake kace uffan Allah ya isa! Fita kabarmin gida, Ahmad ne yafara kuka yace "Mommy nayadda zan fita nabar miki gidanki, Amma ina neman wata Alfarma? " Mommy tace "Banason jin komai daga Bakinka Ahmad kaficemin agida" Wannan karon Fareedah ma tasa baki a rokon mommy, Fareedah kuka Ahmad kuka, Kuma dukansu a tsunkuye suke, Mommy ce taga sun mugun bata tausayi, sai kawai itama tafashe da kuka ta tsunkuya tarike hanunsu ta ɗagasu ta rungume, Ahmad yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya, Rabonshi dayaji ɗumin jikin mommy tin lokacin da Daddy yarasu, Sun kai minti talatin ahaka kafin mommy tace kafaɗamin abinda yake daminka Ahmad? Ahmad ne yace "Mommy naga Bintu a Adamawa" Mommy ce tayi saurin rufe bakinshi da hannunta, Tace shiiii banason karya, karkayimin karya don kanason in soka, Ahmad yace mommy na rantse da Allah Bintu nagani, harda goshin sallahn ta Mommy tayi shiru, taya za'ace wanda yamutu ya dawo? Kodai Ahmad yasamu taɓin Hankali ne sanadin shaye shaye? Can tace idan har da gaske kake gobe zamuje Adamawan in tabbatar, Idan naje kuma naga karya kakemin, tofa bani bakai Ahmad, Yace mommy nayadda idan ba ita bace Karki kara yimin magana Kuma nima bazan sake zuwa inda kike ba! Fareedah tazama shaida. Mommy tayadda da sharuɗanshi sukasa niyyan gobe da safe zasu tafi Adamawa. ****** Mommy sunje wajen dasu Beebah sukabar Ahmad Amma basu ganshi ba! Mommy taruɗe tafita a hayyacinta, Da kyar suka kama hanya suka tafi Asibiti, Suna zuwa daidai Lokacin Bintu ta farfaɗo. Amma wani ikon Allah sai kallonsu take kamar bata sansu ba! Idan sunyi mata magana saita fara kuka, Likita ne yace sun duba sunga ba wani matsala zasu iya tafiya gida. Suna zuwa gida mommy takira Habeeb ɗakinta, Tacewa Habeeb "gobe zamubar garinnan" Kakiramin Abdul yazo muyi magana. Habeeb ya ruɗe yace, Mommy meyasa zamubar garinnan? bayan nanne mahaifarmu? Mommy tace banason dogon surutu Habeeb kayi Abinda na umarceka. Habeeb yayi shiru, can yace kuma Mommy kikace gobe? Mommy tace da Asuba ma kuwa... _✅ote, comment and share pls_ ✍️🗒️ *Jiddah S Mapi* [6/23, 12:51 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to all my fans_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _Jiddah S Mapi_ Page 51&52 "Washe gari" Mommy ce tacewa su Beebah sushiga mota zasu koma Gombe, Beebah tace "yanzu mommy kina ganin idan muka bar garinnan ba damuwa? Kituna fa mun saba da mutane anan, Bakya tunanin muje can mushiga wata rayuwa? " Mommy ce ta dakatar da ita da hannu tace "Beebah bakisan damuwan dazamu shiga anan idan har muka Zauna yafi nacan bakoh? " Beebah ce tace "Mommy wace irin damuwa zamu shiga? Kodan Bintu bata buɗi baki tayi magana bane haryanzu? Mommy kika sani ko iskokai ne suka shafeta?" Mommy ce tacewa Beebah wannan maganar taki ɓatamin lokaci kawai kike, Kishiga mota kawai mutafi. Beebah ce tashiga motar badan taso ba! Bwyan sun shiga mota gaba ɗayansu, Driver yaɗauki hanyar barin garin Adamawa, Beebah kuka takeyi sabida ko sallama basuyi da kawayenta ba, Mommy ce take bata hakuri tana lallashinta har tayi shiru. _Ahmad_ Suna idar da sallahn Asuba suka kama hanyan Adamawa, Amma mommy tace subi flight na safe, Suna zuwa Airport, daidai lokacin da aka fara sanarwa ashirya jirgi zai tashi, Daidai lokacin Ahmad ya tuna cewar ya manta wayarshi agida. Kuma bai kashe ba! Yacewa Mommy "mom inason in koma gida na manta wayana" Mommy tace haba Ahmad baka ganin jirgi zai tashi yanzu ne? Yace mommy matsalar ay wayar ba'a kashe ba! Za'ayi ta kirana aji switch off, Mommy tace kodai karya kayimin ne Ahmad? Yace haba mommy taya za'ayi nayi miki karya, Mutafi ma kawai, Haka suka shiga jirgi sukayi tafiyarsu. _Adamawa_ Sauri suke suga sun bar gari yola, daidai zasu fita a fire away from yola, Habeeb yacewa mommy, "Mom munyi babban mantuwa" Mommy tace me muka manta? Yace mommy mun manta da Abdul, baizo yabamu takaddan sakin Bintu ba! Mommy kar mubar garinnan da Aure akanta, Mommy tace hakane fa kuma, yanzu kiramin shi awaya ka tambayeshi ina yake, Habeeb yaciro waya yakira Abdul, Yacewa Abdul ina kake? Abdul yace ina Airport, Habeeb yace me kakeyi a Airport? Ina jiransu Ahmad ne yau zasuzo, ok gashima sun karaso. Ok idan kaɗaukesu kasamemu a fire away mana akwai wata muhimmiyar magana dazamuyi, Abdul yace to bari sai nazo. Ba'a daɗe dayin wayar Abdul da Habeeb ba, saiga su Ahmad sun karaso, Abdul ne yaɗaukesu amotershi, yace musu suyi hakuri zasu biya ta Fire away kafin su dawo Su Ahmad sukace ba komai, Ahmad ne yacewa Abdul idan mun dawo gidansu Bintu zaka kaimu, Abdul yayi mamaki sosai, ganin Ahmad dasu mom nashi sunzo wai yakaisu gidansu Bintu, Gashi abunda yafaru jiya. Sai kawai ya kawar da zancen. _Bintu_ Ita tarasa waɗannan wasu mutane ne? Tin jiya a asibiti sukeyi mata magana, Ita bata sansu ba! Hasali ma tanason ta tambayesu meya kawota nan? Wannan wani gari ne? Amma takasa Tambaya, Dataga sun shiga mota zasu tafi wani gari, azuciyarta tace Alhmdllh zasu kaini garina, may be ma satoni sukayi, Da Wannan tinani taji karan tsaiwar mota. Tana juya baya taga wani mutum yafito daga wajen zaman driver, Daga baya taga an buɗewa wata Mezata gani? Sai taga mommy tafito a motar, daga baya saiga Fareedah. Bubbuga motar datake ciki tafara Alamun tanason tafita. _Not Edited_ _✅ote & comment pls_ ✍️🗒️ *Jiddah S Mapi* [6/23, 12:52 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to my fans_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *WATTPAD* _Jiddah S Mapi_ Page 53&54 "Habeeb ne yaga alamunta, dasauri yabuɗe mata marfin motar tafita. Sai gani sukai Bintu ta tashi dagudu taje tarungume wata kyakkyawar mata da 'yarta, Bintu kuma acikin zuciyarta daɗi takeji tunda gasu mommy da Fareedah, tana ganin mommy tana hawaye tafara tambayanta mommy meya faru kike kuka? Ko Daddy ne ba lafiya? Alamun mamaki ne yabayyana afuskar su Mommy da Fareedah, Har Ahmad ba'a barshi abaya ba! Wajen mamakin tambayoyin da Bintu take. Basu tashi jin mamaki ba, saida Bintu tace "Mommy waɗancan mutanen satoni sukayi ko? Allah yataimakeni dannaji yana waya da wani wai a filin jirgi, dabaku zo dawuri ba, dasunana gawa!!! " Wannan maganar ya girgiza mommy [6/23, 12:52 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to my Eeshart much love habibty❤️_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *WATTPAD* Jiddah S Mapi Page 55&56 "Bintu kuka tafara kamar ba gobe, ita gaskiya batason Ahmad bata kaunarshi, idan ta tuna zagin dayai tamata lokacin datake gidansu sai taji ta tsaneshi, Hasalima tsoron shi takeji, wanda yayi niyan kasheka Amma kayadda kaci gaba da zama dashi? Wata zuciyar tace mata karkiyi haka, ta sanadin ki babansu yarasu idan kikace bakya sonshi ai kinyi butulci. Kiduba irin son da kanwarshi take miki" Mommy tace ke muke sauraro, Duk ɗakin sunyi shiru bakajin komai sai kukan Bintu, Ta ɓangaren Ahmad kuma ji yake kamar yaje ya rungumeta! Ya tsani yaga tana hawaye zafi yakeji acikin ranshi. Bintu tace "bazan iyaba!!!" wlh Mommy bazan iyaba!!!! Ahmad ne yafara ɗaga hanunshi sama alaman zaiyi roko, Mommy ta dakatar dashi. Mommynsu Habeeb ne tace "menene bazaki iyaba Bintu?" Bintu tace "bazan iya musu daku ba!" Alhamdulillah inji duk mutanen ɗakin, Ahmad ne yace mommy inada magana, Mommy tace muna jinka. Yace mommy inason kuzama shaida Kamfanina na takalma da jakunkuna nabarwa Fateemah halak malak yazama nata! Sannan akwai gidajena dake G.R.A a Kd guda biyu wanda nayi niyan zamu zauna da Fateemah aciki, sannan idan Fareedah tayi Aure zasu zauna da mijinta a ɗayan Yanzu ma haka Za'ayi, shikuma Abdul zan siya mishi gida agefen namu duk muzauna tare! Mommy tayi murna sosai sannan Habeeb da Abdul sunyi godiya sosai Su Ahmad kuma sunce gobe zasu koma, yayinda akasa ranan Aurensu Abdul da Beebah, Habeeb da Fareedah, sannan Ahmad da Bintu sati mai zuwa idan Allah yakaimu ****** yau akeyin ta! yaune ranan ɗaurin Auran su Abdul da Beebah, Habeeb da Fareedah! Amare sunyi kyau sabida sunyi dilki Idan kagansu kamar daga kasashen larabawa! Musamman Bintu data zama kamar 'yar india. Yau za'ayi lunching Amare dukka uku sunsa Dogayen riguna pink color me yalki da bakin roses suka ɗaura kansu, Me yi musu makeup na musamman aka ɗauko inda ta fesa musu kwalliya kamar ba gobe! Idan kaga waɗannnan Amaren zakace babu Amaren dasuka kaisu kyau. "Babban hall aka kama musu, inda akayi decoration na wajen da kayan ƙyaleƙyale na zamani, Kujeru uku me zaman mutum bibbiyu akayiwa kwalliya irinna gidan sarauta! _Ahmad, Habeeb da Abdul_ Suma ba'a barsu abaya ba wajen kyau, Sunsa Fararen shadda me ɗauke da zibin baƙi ajiki, Takalmi baƙi sukasa, sai agogo ma baƙi da bakaken hula. Subhanallah!!! Idan kaje kaga yanda aka tsara wajen da ƙawayen Amare da Abokanan ango da Amaren da angwayen, Sai ka raina kanka! Abinci kuma kamar ba dafawa akai ba! Drinks kuma babu kalan wanda babu, Amare sun zauna akan kujerun da aka kayata dominsu, Da angwayensu. Kuyi imagine yanda Amaren da angwayennan zasu bada light Awajen. An jera kawaye kamar cinnaka sunyi layi dukkansu da anko, dogayen rigane marun color sukayi anko sun ɗaura kai da peach na roses. Sumafa ba'a barsu abaya ba! Wajen kyau. Beebah ce taga ba'a kira Amare ba har yanzu gashi kawaye sai caskalewa suke afili, Sai kawai tamike Abdul yasan hali,, yasan mezatayi Yarike hanunta ta janye hanunta tafara tafiya tan rawa. Daidai lokacin aka sake wakan "Ahmad shanawa" Me taken agirgiza baya baya a karkaɗa ayi kamas Beebah ce tafara girgiza jikinta tana rawa kamar ba Amarya ba! Kowa ya juya yana kallonta rawa take tana juya jiki kamar hawainiya. Da Abdul yaga yanda take girgiza jikinta sai ya tashi shima yabi bayanta, Suka fara rawa atare dama Abdul ma ba daganan ba! MC. Yakira Amaren dukkansu da angwayen suka shiga fili. Ahmad yarike hannun Bintu. Sune agaba! Suna shiga tsakiya Bintu ta wapce hanunta tafita! Ahmad yatsaya yana kallon ikon Allah. Bintu kuwa acikin Zuciyarta idan ta tuna abinda Ahmad yayi mata sai taji ta tsaneshi, Batason Ahmad!!! Ta tsaneshi Amma bazata iya musu da mutanen dasuka taimaketa ba! Da yanzu tana gidan marayu, batasan ya rayuwarta zai kasance ba! Tana cikin tinani taga Ahmad ya iso wajenta, A hankali ya tsunkuya ya rike hannayenta duka biyu. Ya sassauta murya Yanda ba wanda zaiji daga ita sai shi Yace "Wifey meyasa kikemin haka? Kodai baki yafe min bane? Kisani fa Allah ma muna mishi laifi ya yafe bale mutum ɗan Adam, Dan Allah na roke ki, ki taimakawa rayuwata Kece farin cikina Rabona danaji farin ciki acikin rayuwata tin ranan da wancan abun yafaru, Daga ranan Na daina ganin haske a rayuwata, ki tausayamin my Teemah. Inasonki!!! Inasonki!!! Inasonki!!! I love you with all my heart, Zan iya rasa rayuwata idan kika gujeni. My teema inason ki manta komai mu gina sabon rayuwa, Wallahi idan kika gujeni bazan taɓa gane hankalina ba! Yafaɗa cikin hawaye. Bintu dataga yana mata kuka gashi mutane sunata kallonsu, saita fara kokarin tayar dashi. Shi kuma yazauna akasa yaki tashi sai hawaye dayake kamar Amarya, Ganin haka yasa Bintu tace "na yafe maka duk abinda kamin, kuma bazan taɓa manta halaccin da iyayenka suka min ba! Ahmad na yafe maka duniya da lahira" Ahmad ne yafara dariya kuma yana hawayen farin ciki. MC. Ne yafara magana yace "ana neman duk Amaren da ango a fili, suzo su nuna mana farin cikin Dasuke ciki ayau. Ahmad ne yarike hanun Bintu, Habeeb yarike Hanun Fareedah, Abdul kuma yarike hanun Beebah, Tafiya suke suna ɗan rawa, yayinda mutane suka sa tafi suna ihu. Wakar biki yayi biki akasa musu, inda suka fara rawa Amma banda Bintu data tsaya tana dariya. Ahmad dayaga zata badashi afili, sai ya rike kwankwason ta yafara rawa, Bintu kamar kasa ya tsage tashige tsabar kunya. Tafara kokarin cire hanunshi ajikinta Amma ina yaki saima kara janyota jikinshi dayake. Dataga haka saita fara kuka tana tureshi. Ahmad ne ya rungumeta afilin yasa bakinshi daidai kunnenta yace "Haba wifey mutane fa suna kallonmu ki daina kukannan kinji wifey" Tafi sukaji anayi musu, Ahmad yasaketa! Taga ba kowa afili daga ita sai shi su Beebah sun tafi! Dj ne yasake musu wakan Romantic, Bintu kamar gunki sai juye juye tafara, Ahmad ne yarike kwankwasonta yana rawa da ita. Dj yace atafa musu Akasa tafi Awajen. Dahaka har aka gama lunching kowa yashiga motan mijinshi aka wuce dasu gidansu Beebah. Suna zuwa Bintu ko cire takalmi batayi ba! Ta kwanta akan gado tana nishin gajiya, Beebah ce tace "dama ya lafiyar kura bale takama zawo" Bintu tace yanzu nice kuran Beebah? Nafa lura kin fara rainani a 'yan kwanakinnan, dan kinga zakiyi Aure ko? To bara nafaɗa miki har yanzu ke yarinyace awajena ehen. Fareedah tace "wayaga Babba kema ai ba Auran kikayi ba! Tare dai zamusan komai" Bintu tace wannan magana taki tafi karfina! Kinga namayi bacci, Dukka suka kwashe da dariya. _Ahmad_ Jinshi yake kamar wani sabon halitta, suna zuwa gida yakwanta akan gado yafara tunanin wai yau Fateemarshi ce tazama mallakinshi? Yanzu gobe war haka suna tare da ita amatsayin mata da miji, Can't wait to see yafaɗa da murya. Habeeb dake gefe yace "Wai me kake faɗa ne Ahmad?" Wallahi ina ganin kamar karya ne wai gobe nida my Teemah a ɗaki ɗaya kan gado ɗaya? Can't wait to see wallahi cewar Ahmad, Habeeb ne yaji zuciyarshi tabuga!!! Yanzu gobe Bintu a ɗakin Ahmad zata kwana? Kuma kan gado ɗaya? Dasauri yafara faɗin Astaghfurullah Ashe yanzu ita matar wani ne. Ahmad ne yaga yanayin shi yace "lafiya Habeeb?" Habeeb yace lafiya lau ba komai Kai dai kafiye zumuɗi, Ahmad yace ba dole nayi zumuɗi ba! Rabona fa da mace tun muna tare da Bash. Habeeb ne yayi dariya yatashi yashiga toilet da niyan Alwala. Beebah ce tacewa su Bintu ku baza kuyi sallah bane? Bintu tace nifa bana sallah tin jiya! Fareedah ma tace ita sai jibi zata fara. Ita kuma Beebah yau period nata yazo! (Tofa kunga Amare da period ranan biki) *Washe gari* Mommyn Habeeb da Mommynsu Ahmad ne suka tarasu babvan falo, Sukayi musu nasiha me tsima zuciya. Daga karshe Mommyn Beebah takira dukka Amaren a ɗakinta, tayi musu nasiha irin na zaman Aure Sannan ta basu wasu sirrikan yanda zasubi da mazajensu. Ta ɗauko wasu turare acikin jakanta, tace "ga wannan ku tabbatar sai idan zaku kwanta kafin ku shafa kada ku kuskura kushafa idan zaku fita anguwa" Turaren matan Aure ne! Sukace "to" Suna fita bayan kofa Beebah ta makale ta buɗe turaren tashafa kafin ta rufe tafita. Taje tasamu kowa yahaɗa kayanshi, musu suke, wai mommynsu Ahmad tace a motar haya zata tafi bazata bi motar mijin kowa ba! Sunyi sunyi tabisu amotar Ahmad taki, Haka suka hakura, kowacce tashiga motar mijinta Suka ɗau hanyar Kaduna garin gomna. Bintu ce take kukan rabuwa da mommy acikin motar, Ahmad juyawa yake yana kallon yanda tarufe ido tana zuba kuka kamar karamar yarinya. A hankali yarike hanunta me laushi da tsantsi yafara wasa dashi, Ta sauke ajiyar zuciya jin hanunshi cikin nata yana murzawa! "Beebah kuwa uwar kauɗi, tana shiga Abdul yazuba mata ido Yana kallonta, jin kamshin turaren data shafa yasashi lumshe ido. Tazauna agefenshi kamar mutuniyar kirki, Yace matso! Tayi shiru tana kallonshi, gashi Idonshi arufe amna yana mata magana. Yasake cewa matso mana A hankali ta matso wajenshi Yarike hanunta yace "wani irin turare kika shafa?" Tace "turare nane" Yace ban yadda ba! Kifaɗamin gaskiya, Tace gaskiya nafaɗa maka, Yace "ok". "Fareedah kuma tana shiga motar Ta sunkutar da kanta tana wasa da yatsun hannunta, Habeeb yace "kisaki jikinki ni mijinki ne" ✍️🗒️ *Jidda S Mapi* [6/23, 12:52 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to all my fans_ *WATTPAD* Jiddah S Mapi *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Godiya dubu ga masoyana masu bibiyar littafin Agidanmu Take!!! Banso labarin tazo muku a short story ba! Amma ya na iya Haka Allah yatsara, nagode da nuna soyayyarku gareni, banyi tsammanin first Novel ɗina zan samu masoya har haka ba! Sai gashi Allah yasa nasamu, alhmdllh ina godiya gareshi sannan ina godiya gareku* *Special thanks to mrs sardauna bazan manta dake ba!* *godiya ga Eeshart tnx for your comment i really appreciate* *Bazan manta dakai ba! Aliyu Ibrahim* *Much love to my Sister walidation S Mapi* *Ina miƙa gaisuwata da kuma godiyata ga ɗaukakin jama'ar kungiyar KAINUWA dashen Allah* *kuna raina kanne na! Walidation S Mapi da Hafsat Ibrahim Khalil* *Godiya ga ɗaukakin jama'ar group na Agidanmu Take!!! Bazan manta da kuba!* Page 57&58 🔚🔚🔚🔚 "Fareedah taɗan saki jiki kaɗan da Habeeb, ahanyansu nazuwa kaduna ansha love amota musamman Beebah data rikita ɗan mutane da turare, Bayan sun iso ne kowa yafito amotar a gajiye kamar an dakesu. Ahmad ne yanunawa Habeeb wasu gidaje tsararru kerarru haɗaɗɗu, guda uku yace "Habeeb kazaɓi gida ɗaya acikin waɗannnan" Habeeb yace "kowannema nagode basai nazaɓa ba! Allah yasaka da alkhairi sannan yabar zumunci" Ahmad yace "Ameen" To tinda gidan uku be kuma ajere komai naciki kala ɗaya ne nizan zauna a tsakiya tinda nine karami Dukka suka kwashe da dariya Habeeb ne yarike hanun matarshi yace sai kun karaso. Ahmad yace daɗin Abin dai baza'aci fuskarmu ba! Kowama yanada tashi. Duka suka wuce gidansu, Bayan sun idar da sallan mangariba da isha ne Ahmad yaɗauki wayarshi yakira su Habeeb da Abdul yace idan ba matsala yanason zasuyi magana agidanshi dukkansu da matansu, Sukace ba komai. Jim kaɗan saigasu sunzo suka zauna a babban falon da yake mallakin Bintu ne da Ahmad, Bayan sun zauna Habeeb yabuɗe musu da Addu'a. Ahmad ne yayi gyaran murya yace "da farko ina godiya ga Allah me kowa me komai wanda shine yayi sanadin taruwanmu anan, Sannan ina mika godiya ga Abokaina Kuma Aminaina Wato Habeeb da Abdul, hakika kunmin inuwa wanda ba kowa bane zai iya yiwa abokinshi Awannan zamanin" Ahmad yatsunkuyar da kanshi yafara hawaye yace "Habeeb kasan irin wahalar danayi a neman Fateemah kuma kaima ka tayani nemanta alokacin danake cikin taahin hankali, Sai wani ikpn Allah ashe Fateema A gidanku take!!! Bamu sani ba! Matar da Allah yarubuta zata zama matarka ashe A GIDANMU TAKE!!! nasan kanason Fateema Habeeb Amma Allah bai rubuta kai zaka Aureta ba! Matar da Allah ya rubuta zaka Aureta A GIDANMU TAKE!!! Habeeb ne yace "kayi hakuri Ahmad kadaina kuka komai yawuce kamar yanda matar dakake nema A GIDANMU TAKE!!! haka zalika matar danakeso yanzu A gidanku take!!! Ikon Allah kenan". Abdul ne yace "godiya yakamata muyiwa Allah daya nuna mana wannan rana ba kuka ba!" Ahmad ne yace "ku yafeni dukkanku nasan nashiga hakkin ku" Habeeb yace kadaina irin wannan maganar Ahmad komai yawuce. Muyi addu'a dai kawai Allah yajikan Daddy yasa mutuwarshi shiyafi Alkhairi mukuma idan namu yazo Allah yasa mucika da imani "Ameen" cewar duk mutanen falon. Kasancewar Amaren duk suna off hakan yasa mazajen duk suka hakura dasu, Banda Ahmad da saida ya yayi wasa da Fateemah Bintu. Bayan sati ɗaya, Ahmad ne naji yana yiwa matarshi sannu duk ya rikice, Dana leka ɗakin sai naga Fateemah Bintu kwance akan gado ba alamar motsi gashin kanta abarbaje, Naga Ahmad yashiga toilet nabishi naga ruwan zafi yahaɗa Bahon wanka, Naga yadawo Dali yaɗau 'yar mutane yayi hanyan toilet da ita, nikuma kasancewar ban kai age ɗin dazan san me sukayi ba! Yasa na ɗauki biro na da takadda na naɗaukan rohoto nayi waje sai gidan Habeeb. Ina zuwa naga Fareedah kwance akan cinyarshi tana zuba shagwaɓa kamar wata baby shikuma yazage sai biye mata yake, nace to abun nakun na yarane, nayi gaba sai gidan Abdul da Beebah uwar kauɗi. Ina zuwa naji abunda yafi karfina! Beebah ce take cewa Abdul "Baby anya ba ciki ne dani ba? Kaduba kaga yanda nake Amai fa" Abdul dayake rungume da ita yace "Allah yasa cikine, da bawanda zai kaini Farin ciki" Nayi gaba nace bada niba. *********** _Bayan wasu shekaru_ Gidan Ahmad ne naga wasu kyawawan yara suna wasa su biyu mace ce dakuma namiji farare kamar Auduga. Ahmad ne kwance atsakiyarsu yana cakulinsu sunata dariya, Sai naga wata kyakkyawar mata tashigo tace "Hubbie wai ina su mommyy karama sukaje ne? Tin ɗazufa suka fita wai wasa" Daga baya naji wata mace tace "Ai mommy karama A GIDANMU TAKE!!! Tin dazu suna wasa dasu Daddy karami" Juyawar dazanyi sai naga Polina da hijabi. Ashe wai Bash ya shiryu dayaga Ahmad ya gyara halinshi, Polina ma ta musulunta tayi Istibra'i sannan Bash wanda yanzu ake kira da Bashir ya Aureta! Suna zaman lafiya harta haifa mishi yara 'yan biyu Haneef da Haneefah. Suma suna zaune ne agefen gidansu Ahmad wanda shi Ahmad dakanshi ne yasaya musu. Ahmad ne yace to Alhamdulillah yanzu dai kinji inda suke, Tinda itama ga 'yarta tin ɗazu A GIDANMU TAKE!!! Alhamdulillah!!! Alhamdulillah!!! Alhamdulillah!!! Nan nakawo karshen littafina me suna A gidanmu take!!! Kuskuren danayi ko tuntuɓen harshe Allah yagafarta mani. Saimun haɗu a littafina na gaba me taken MAKAUNIYA CE!!! *special thanks to WALIDATION S MAPI sisi forever* ✍️🗒️ *Jiddah S Mapi* Taku ce 👍🏻 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani

Chapter 5 of 6