Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 6
Amaimakon kayi sauri kasiyomin magani? Habeeb yayi mamakin yanda mommy takeson korashi amma be kawo komai aranshi ba!. Yace mata mommy kuɗi zan ɗauka sabida kuɗin hanuna yakare, Mommy tace kaje ɗakina kacire acikin jaka, yace tom Mommy. Saida Habeeb yabar gidan kafin Mommy tashiga ɗakin ta ajiye hoton yanda tagani ta gyara wajen kamar ba'a taɓa komai ba. Harda fesa turare. *_Ahmad_* Tin bayan tafiyan Habeeb yashiga damuwa kamar da dama acikin abokananshi daga Habeeb sai Abdul ne kaɗai suke kwantar mishi da hankali saɓanin Bash dayake bashi giya yasha kuma yakawo mishi mata. *_Bintu_* Bintu kuwa da Abdul soyayya tayi nisa idan Abdul beji muryan Bintu ba To ranan akwai tashin hankali. ****************** "Bayan wata ɗaya da sati uku, wanda yayi daidai da kawo kayan lefen Bintu Daza'ayi ayau juma'a, gidansu Bintu ne yau ake shirye shiryen karɓar kaya, inda Mommy tayi namijim ƙoƙari wajen ganinta ƙayata abun, Abinci musamman akayi daga gidan Abincin Mommy, yayinda aka dafa abubuwa masu daɗi da ban sha'awa aka zuba a take-away, drinks kuma ba'a magana mommy tayi ordernsu kamar ba gobe. (Azuciyana nace wannanma ba ranar Auren ba) An kawo kaya komai yayi daidai inda akayiwa Bintu kaya nagani nafaɗa, kowa yasa Albarka anyi mata fatan Alkhairi. Abdul ne yabijirowa Bintu da maganar pre-wedding pics, Bintu taje sama ta sakko kasa tace bazatayi ba! Hakan ya fusata Abdul har yayi fishi da ita kota kirashi baya ɗaukan kira. Abun yadami Bintu, tasamu Beebah tayi mata bayanin duk abinda yafaru, Beebah tace Abu me sauƙi basai kitura mishi text kice kin yadda zakiyi ba, Idan yazo saimu tafi tare inyaso sai ayi dani. Thats my sisterluv inji Bintu tabawa Beebah hannu suka tafa tace hakan kuwa za'ayi.. _✅ote, comment, and share pls_ ✍️🗒️ *_jiddah S Mapi_* [6/23, 12:50 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to my love_ *WATTPAD* Jiddahpretty *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* Page 41&42 " hakan kuwa akayi data turawa Abdul message aranan yazo suka ɗibi kaya sai wajen ɗaukan hoto, Dasukaje ɗaukan hoto akace Bintu tashirya, Bintu tace itafa bazatayi wani hoto ba sabida bidi'a ne, amma ayi da Beebah tinda su 'yan biyu ne, Da farko Abdul yaki amma dayaga Bintu ta nace kawai saiya amince suka ɗau hotunan" Beebah kamar itace Amaryan dagaske, tayi kyau bana wasa ba, Sunyi hotuna kala-kala ciki harda wanda Beebah tariƙe wuyan Abdul, da wanda yaɗan sunkuyo daidai wuyarta, sunyi kyau matuƙa fiye da tsammani. "Ahmad yana kwance akan gado yana ɗan chat da Abokinshi Habeeb, sai kawai yaji karan message. daya duba message ɗin saiyaga Abdul ne yatura mishi hotona, daya buɗe hotonan saiyaga Abdul da wata fine girl, sunyi kyau sosai, Yacewa Abdul gaskiya kunyi kyau Amaryar taka kyakkyawa Allah yabada zaman lafiya. "Ameen" cewar Abdul. _Bintu_ Ita kuwa Bintu dilki akeyi mata lagadan ba ajalan ba, Beebah ma tace sai tayi dilkin tare suke dilkin sunyi kyau bana wasa ba, idan kagansu kamar larabawa. *************** "Lokaci yaja kwanaki sun wuce, kamar yadda akasa date na Auren Bintu Da Abdul hakan kuwa akayi yau Alhamis, za'ayi kamu, a wetline dake cikin garin Adamawa" Bintu da Beebah anko sukayi sunsa doguwar rigan material jaa ne yalƙi sunyi makeup idan kaga Bintu zakace ba 'yar nan kasan bace kamar balarabiya Ƙawayensu kuwa sunsa Pink na dogayen riga plane material sun ɗaura kansu da baƙaken ɗan kwali, Abun ba'a magana. Hall ɗin da aka kama musu an ƙayatashi da kayan kyale kyale, Wajen yayi kyau, Abokan Ango sunsa baƙin shadda dayaji zubi Abun saidai kawai ayi shiru. Can nahango Beebah da Bintu suna musu, Bintu ce tace ita bazata iya zama acikin mutane ba! Beebah kuwa tace ay bata isaba! suna cikin musune Bintu dataga sun dameta sai kawai tajuya tafita a hall ɗin, daidai lokacin da MC. Yafara cewa ana neman amarya afili. Gashi Bintu tafita, ƙawaye sai juye juye suke sun rasa ya zasuyi,gashi MC. Yanata kiran Amarya, da Beebah taga haka sai kawai tafara tafiya Zuwa wajen Ango tana shiga tsakiya zata wuce taji MC. Yana cewa atafawa Amarya. "kawai sai taji wajen ya ƙaure da tafi, Abdul yana zaune yana kallon ikon Allah yarasa meyake faruwa, MC. Yace ana neman Ango afili" Abdul ne yatashi jiki amace yana Zuwa wajen MC. Yanaso yace ai ba ita bace Amaryar Amma yana zuwa daidai tsakiyan fili yaji ance atafawa Ango da Amaryarsa waje ya kaure da tafi ana ihu. MC. Yace Anaso ango yayi rawa da Amaryarsa rawa irinna nuna farin ciki da farko dai ango yakama hanun Amaryar tashi su shigo tsakiyar fili yanda baƙi zasugansu da kyau... _Ahmad_ Ahmad kuwa sauri yake ya isa garin Adamawa sabida Abdul yadameshi da kira, gudu yake akan kwalta kamar zai tashi sama, yana duba agogonshi yana kara spirit. _Bintu_ Bintu kuwa tana fita a hall ɗin napep takama ta tafi gida dan tafara jin kanta yana ciwo. Tana zuwa gida tawuce zata shiga ɗakin mommy taga mutane dayawa, kawai saita juya tawuce ɗakin Habeeb. Amma me? Tana shiga ɗakin Habeeb taganshi yarungume hoto yana kuka kamar ƙaramin yaro. Tayi sauri ta karata cikin ɗakin tana me kiran yaya Habeeb yaya Habeeb meya sameka kake kuka? Habeeb ne yayi saurin ɓoye hoton yana share hawayrnshe. Yace Bintu na meya dawo dake gida ana tsaka dayin kamunki? Yaya ni wallahi banason wannan hayaniyar ne tana sani ciwon kai. yaya meya sameka kake kuka? Kuma hoton waye ka ɓoye abayanka? Habeeb yayi shiru can yace Babu komai Bintu na, wannan wani sirri ne nawa dana ɓoye bana so kowa yasani harsai ranan da Allah yakarɓi rayuwata, Bintu tace yaya meyasa kake irin waɗannan maganganun yau fa ranar murna ce sanin kanka ne nice farkon da mommy tafara Aurarwa agidannan. be kamata ka zauna acikin baƙin ciki ranar Aurena ba! Kamata Ai farin ciki zakayi, Habeeb yace to Bintu insha Allah zan daina damuwa". yanzu ina kika bar su Beebah da Abdul? Bintu ta shagwaɓe fuska tace "suna wajen kamu". _Hall_ "Abdul da Beebah ba sun rasa yanda zasuyi haka suka daure suka shiga fili sunata caskalewa, Abdul yariƙe hanun Beebah suna rawa kamar 'yan india, Abokansa kuma suna watsa kuɗi kamar ba gobe. _Ahmad_ 3:30pm cif yashigo garin Adamawa, bai tsaya ko inaba Sai a babban hotel na garin, yana zuwa yabiya kuɗin ɗaki aka bashi key yawuce, yana shiga cikin ɗakin ya ajiye kayanshi akan gadon yabuɗe toilet yashiga yayi wanka, yana fitowa daga wanka yashafa lotion da turaren jiki me kamshi, yataje suman kanshi, ya ɗauko wata baƙar shadda me kyau wanda tasha adon jaa ajiki, yasa jan hula, yaɗauko jan Agogo da takalmi jaa yasa, idan kaga Ahmad zakace balarabe ne, kamar asace a gudu yayi kyau har yafi kyau kyau awannan rana. "yayi sauri yaɗau makullin mota yabuɗe ɗakin yafita, Yana fita harabar hotel ɗin kallo yakoma sama, kowa idonshi akan Ahmad, wani dagacan gefe yace inama ace nine wannan. Jin hakaAhmad yajuya yace mishi bawan Allah ka godewa Allah aduk inda ya ajiyeka, ni nan dakasan matsalata da bazakaso ace kasanni bama balle ace kaine ni". Yana gama faɗan haka yajuya yayi tafiyarshi, wajen parking na motoci yanufa, yana zuwa yashiga baƙar motarshi kirar land-rover. ya tada motarshi yanufi hanyan wetline wajen kamu. Yana zuwa yayi parking yashiga cikin hall. Dashigarshi hall ɗin kallo yakoma sama, kowa yana kallonshi maza da mata. "MC ne yace ga babban abokin ango atafa mishi, waje ya kaure da tafi, ana ihu MC. yace muna neman amarya da ango dakuma babban abokin ango afili" Beebah tinda ta ɗaura idonta akan Ahmad taji zuciyanta ya buga, gayen ya birgeta infact wankanshi ne yafi tafiya da imaninta, MC. Ne yasake cewa muna jirnku, Ahmad ne yafara fitowa kowa sai kallonshi yake, nan Beebah da Abdul suka shigo, Beebah tana shiga fili tawuce wajen Ahmad tana rawa da jikinta kamar wata 'yar india, Ganin haka Ahmad yafara rawa shima yana watsa mata kuɗi, mutane sai tafi sukeyi musu. "Abdul kuma yatsaya afili kamar gunki yana kallon ikon Allah, yama rasa me zeyi? Sai juye juye yake yana dariyan dole" Beebah kuwa tazage afili kamar ibada sai juya jikinta take kamar hawainiya, Da Ahmad yaga yanda take rawa. Azuciyarshi yace wannan wace irin Amarya ce?... _✅ote, comment and share pls🙏🏻_ ✍️🗒️ *_Jiddah S Mapi_* [6/23, 12:50 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to all my fans_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _Jiddah S mapi_ Page 43&44 "A zuciyar Ahmad yace ay Amarya ko bata da kunya, ranar Aurenta tana ɗan jin kunyar mutane Amma ita ta zage sai tiƙa rawa taje agaban Abokan Ango? Kai wannan abu da alamar tambay" Beebah kuwa acikin zuciyarta tance kai wannan gayen ya haɗu ana gama kamu zan tambayi numban wayarshi, duk nan yafisu wanka, duk maganar dasuke acikin zuciyarsu be hanasu taka rawa a filin ba, har MC yace to mun gode Allah yasakawa amarya da ango dakuma babban abokin ango. Haka suka juya suka tafi, an gama kamu dab mangariba kowa ya watse. Ahmad ne yacewa ango yanason yabishi hotel ɗin daya sauka sabida sunada magana me muhimmanci, Abdul yashiga motarshi suka wuce Hotel. _Bintu_ Bintu tace ita wallahi daga kamu ba abinda za'a karayi a Aurenta na bidi'a. Washe gari ranar jumma'a ranar da za'a ɗaura Auren Abdul Muhammad da Bintu Umar, shirye shirye ake na musamman, kawayen mommy sunzo daga wani gari 'yan wanka ne kuma hajiyoyi ne. Bintu kuwa tasa leshi jaa me kyau tayi makeup kamar asace agudu, Beebah ma ba'a barta ba wajen kyau, kawayensu ma sunyi kyau sosai. Kawayen mommy suma leshi suka ɗinka garin mata dashi, idan kashiga gidan saika raina kanka. 2:30pm cif aka ɗaura auren Bintu da Abdul akan sadaki dubu ɗari lagadan ba ajalan ba, Anyi Aure an kammala komai da mangariba abokan ango sukazo su ɗauki amaryarsu. Tofa nan akeyinta Habeeb dayaga za'a tafi da Bintu yadinga suma kamar me farfaɗiya, har mutanen wajen suka fara mamaki, mommy ce tacewa Bintu takoma gida, Beebah ce tazama amaryan karya taje tashiga mota aka tafi da ita, bayan mutane sun watse ne mommy takira Habeeb cikin ɗakinta da Bintu ta ajiyesu, mommy ce tace Habeeb? Yace na'am tasake cewa Habeeb? Habeeb yace na'am Mommy tasake cewa Habeeb? Yace na'am, Mommy tace sau nawa nakira sunanka? Yace sau uku, mommy tace tom nataɓa kiran sunanka sau uku? Yace Aa tace inason kafaɗamin gaskiya. Meye a tsakaninka da Bintu?.. Habeeb yayi shiru sai kawai yafara kuka, mommy tace ba kuka natambayeka kayi ba, idan har nina haifeka kafaɗamin Abinda yake ranka? Habeeb yace Mommy inasonta ne!!! Kuma Aurenta nakeso nayi!!! Tass tass tass kakeji Bintu ce taɗago ta dallawa Habeeb mari tana huci... Bakada hankali ne yaya? Ko kafara shaye shaye ne? Ko ka sami taɓin hankaline? Ko bakasan ciki ɗaya muka fito dakai bane? Duk waɗannan tambayoyin tana yinsu ne cikin hawaye.. Yaya kai mahaukaci ne bakada hankali, sai yau na tabbatar da haka kanka ya taɓu. Ke Bintu kece me taɓin hankali bani ba! Kece kanki yasami matsala bani ba! Ina matsayin yayanki zaki kirani mahaukaci? Kece mahaukaciya! Yana magana yana hawaye, Kinsan iron son danake miki? Kinsan baƙin cikin danake ji idan naganki da saurayi? Kinsan yaya nake kwana acikin kwanakinnan da Auranki ya iso? Kinsan yanda nakeji kamar na kashe Abdul idan naganku tare? Duk nasan baki sani ba. "Mommy ce ta tsaya awajen ba bakin Magana sai zazzare ido datakeyi kamar wata taɓaɓɓiya, idan wannan yana magana tajuya ta kalleshi idan wannan yanayi ta juya ta kalleshi tarasa ya zatayi da duniyarta tarasa ina zatasa kanta ayau, jitake kamar ta tara kayanta tabar gidan kafin su fara mata tambayoyi, juyawa tayi zata bar musu ɗakin taga mutum akwance kasa ba alamar numfashi! Beebah ce kwance kasa, wanda ta daɗe da dawowa ta dalilin faɗa dasukayi da Abdul bayan ankaita gidanshi ta tsigeleshi tayi gaba abinta, tana dawowa shine ta tarar da abinda yafi karfin kunnenta. Jin kalaman Habeeb yasa tafaɗi ta suma! Mommy ta tsala ihu ta iso wajen da Beebah take kwance ƙasa!... _✅ote comment and share pls_ ✍️ *Jiddah S Mapi* [6/23, 12:50 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to all my fans_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *WATTPAD* _Jiddah S Mapi_ Page 45&46 "Mommy ce tayi kan Beebah dagudu tana ihu, ganin haka yasa Bintu tayi sauri ta ɗauko goran swan a frij tazo aka shafawa Beebah afuska, a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana buɗe idonta tafara tambayan Habeeb, yaya me naji kana cewa? Kamar naji kace kanason Hassana kuma da Aure? Kamanta mu 'yan biyu ne da ita? Ko ka manta ciki ɗaya muka fito da ita? Allah yasa dai wasa kake, duk tabayoyin datake mishi tanayine cikin hawaye sannan ta Zubawa Habeeb ido, Mommy tayi shiru tanayi wa Habeeb kallon tuhuma. Da Habeeb yaga duk shi suke kallo, ciki kuwa hadda Bintu, sai kawai yafara kame kame, yajuya yafita a ɗakin. _Ango_ Abokansa ne suke ta zagin Abu wai an raina musu hankali, yaza'ayi ranar Aure a nemi Amarya arasa, Abdul yatsaya yakasa yin komai sai gyara gari yake tin ɗazu da goge zufa, Yakira numban Bintu yafi sau 20 ba'a ɗaga ba! Azuciyarshi yace kodai yaudarana dama takeda niyan yi? Ahmad ne yadafa kafaɗan Habeeb yace "kadaina tunani dude" insha Allah gobe Zamuje gidansu Amaryar tafaɗa mana meyake faruwa, domin kasan lamarin Aure yanzu, kowa yana kokarin yaga an ɓata, Abdul ne yace "Haba Ahmad kana gani fa yarinyannan tadinga wulaƙanta ni a idon duniya, Aure wasane? Hakafa ranan kamu ta tafi tabar wajen saida ɗayar 'yan biyunta tazauna awajen, yanzu kowa yazata Beebah ce Matata!... Wani irin magana ne kake faɗa dude? Kana nufin wannan ba itace kake Aura ba? Kuma ai naga pre-wedding pics ɗin da ita akai. Abdul ne yayi mishi bayanin duk abinda akayi, Ahmad yayi shiru yana tunani can yace "Amma Abdul ka tabka kuskure Babbah! Meya kaika ɗaukan hoto da 'yan biyun wacce kake Aura kuma kace Ba itace matarka ba! Kana ganin mutane baza suyi maka mumunan fahimta ba? agaskiya ka aikata Babban kuskure! Abdul yace "hakika Ahmad na aikata kuskure to amma tayaya zan wanke wannan kuskuren danayi"? Ahmad yace mafita ɗayane garemu shine kaje gobe ka ɗauko matarka koma muje tare, kacewa kanwarta ta ɗauko duk kayan da kukayi hotunan dashi saimu tafi tare dukanmu huɗu, Ita matarka saitasa kayan da wancan tasa ranar dazakuyi hoton koda shike ai su 'yan biyu ne, bazasu rasa kaya kala ɗaya ba, Idan munje wajen ɗaukan hoton, ni saina ɗauka da Beebah kai kuma ka ɗauka da matarka, sannan muɗauka dukanmu huɗu, kaga zamu juya kan mutane, ba kowa ne zai gano bakin zaren ba, idan aka tambayeka saikace ai Bintu itace matarka! Abdul wani sanyi yaji azuciyarshi, yacewa Ahmad to insha Allah haka za'ayi, nagode da wannan shawarar. Suka sallami abokanansu suka basu hakuri, kowa yawatse. _washe gari_ Ahmad ne da Habeeb suka buga wanka, sunsa anko gaba ɗayansu shadda ne fari da zubin baƙi, sukasa hula baƙi da takalmi baƙi sai agogo baƙi, bakaramin kyau sukayi ba, suka shiga motar Ahmad baƙi, suka ɗau hanya sai gidansu Bintu. Suna zuwa Abdul ne yashiga daga ciki dan Ahmad yace shi baze shiga ba! Yana jiransu awaje, Abdul yana shiga ya gaida mommy afalo, mommy take bashi hakuri tace kayi hakuri Abdul wata 'yar matsala aka samu, shiyasa kaga ba'a kai maka Bintu ba! Abdul yace ba komai, mommy ce ta tashi afalon taje takira Bintu aɗakinsu, Bintu ce ta tashi tasa dogon riga, gaba ɗaya ta rame tin jiya take cikin kuka da tinani tarasa meyake mata daɗi. Goga powder tayiwa fuskarta tasa baƙin kwalli acikin Idonta tayafa baƙin gyale, ta fesa turare ajikinta masu kamshi, tasa flat shoe, duk abinda takeyi Beebah na kallonta tace ko zamuje ku gaisa ne? Beebah tace no, tace dan Allah muje, Beebah data tuna dukan rannan saita diro akan gadon tace bari nasa hijab sai naje mu gaisa. "Suna zuwa falon Beebah tafara tsayawa abaya baya dan tasan rashin kunyan datai tamishi jiya, shi kuma saiya basar yace ya kike kanwar Habeeb? Beebah tace lafiya ya gajiya? Yace babu, Abdul ne yayi gyaran murya yace amm Hassana da Hussaina? Sukace na'am yace wata alfarma nazo nema awajenku, duk da Bintu yanzu ita matatace amma dole na nemi alfarma, Sukace ba matsala kafaɗa muji in Zamu iya, Yace dama inason ku ɗibo kaya waɗanda kukayi anko, da wanda mukayi pre-wedding pics dashi, yanzu zamuje ayi sabon hoton sabida wancan akwai matsala" "Bintu ce tace ita bazatayi hoto ba! Abdul yadinga haɗata da Allah taki, da Abdul yafusata yace look Bintu karkiga dan inasonki kice zaki wulaƙanta ni, yanzu miji nake awajenki umarni nake baki kitashi ki ɗebo kayanki zamuje ayi sabon hoto! Yafaɗa cikin fushi. Bintu ce tahaɗa rai ta tashi tashiga ɗaki ta ɗebo kayan dana Beebah, Beebah ce takarɓi kayan ta tafi sawa a mota, ita kuma Bintu tashiga cikin ɗakin mommy domin sanar da ita. _Ahmad_ Shikuma ya zauna yanata jiransu amma har yanzu basu fito ba! Ganin haka yasa yajuya kanshi yadaina kallon kofar gidansu Bintun, dayaji karar buɗe kofar saiya juya yaga Beebah ce takesa kayansu aciki, tace ina wuni? Yace lafiya, daga cewa lafiya be kara komai akaiba kuma be sake juya bayanshi ba, yayi readyn jan mota idan sun fito. Beebah ce tashiga cikin motar tazauna tana kallon side view na Ahmad. Abdul da Bintu Kuwa sunata rigiman fitowa. Bintu tace sai Abdul ne zai fara fitowa shikuma Abdul yana tsoron kada yashiga gaba ta gudu, shima yace sai ita zata fara fita. Da kyar Bintu tayadda tafara fitowa rai aɓace taje ta buɗe motar tashiga wajen da Beebah take. Shikuma Ahmad ko juyawa ya kallesu baiyi ba, yana ganin Abdul yashiga, ko gama rufe marfin motan baiyi ba! Yaja motar cikin fishi yafara watsa gudu akan titi.... _✅ote, comment and share pls🙏🏻_ ✍️🗒 *Jiddah S Mapi* [6/23, 12:51 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* _Dedicated to my Facebook fans_ *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _Jiddah S Mapi_ Page 47&48 "Ahmad gudu yake akan titi kamar zai tashi sama, Abdul ne yayi mishi magana yace, haba Dude wannan wani irin gudu kakeyi? Baka tsoron muyi hatsari? Ko kuma mu bugu da bishiya? Shiru Ahmad yayi mishi, ganin haka yasa Abdul yaja bakinshi yayi shiru, sabida yasan halin abokinnashi" Bintu kuwa acikin zuciyarta haushin wanda yake tuka motar takeji, mutuminnan wani irin mugu ne? Yana gani muna cikin motar amma yake irin wannan gudun? Duk yanda akayi wannan baisan darajar mutum ba, mugu azzalimi, duk acikin zuciyarta take wannan maganar. Beebah kuwa duk gudun da akeyi batama saniba sabida hankalinta duk ta tattarashi akan Ahmad, gayen yamatuƙar tafiya da imaninta, Haka har sukayi parking awani waje me kyau, saman wajen an rubuta "Adamawa special photos" Ahmad yanayin parking ya buɗe motar yafita ko juya bayanshi baiyi ba, yana fita su Bintu ma suka fito, dukansu suka shiga cikin ɗakin da ake ɗaukan hoto, suna zuwa sukayiwa me hoton bayanin yanda akayi, yace musu ba matsala za'asan yanda za'ayi. Duk maganar dasukeyi Ahmad ya sunkuyar da kanshi baya kallon kowa, har suka shirya dukansu, Bintu da Beebah sunsa anko na riga da skirt atamfa suka ɗaura kansu, sunyi kyau bana wasa ba, Me hotone yafara ɗaukansu hoto, dukansu, idan An ɗauka ɗaya saisu janza kaya. An ɗauki Beebah da Ahmad tarike wuyanshi, sai kuma akace za'a ɗauki Bintu da Ahmad. Ahmad yana zaune akan kujera tunda aka fara ɗaukan hoton bai ɗaga kanshi yakallesu ba, saidai yakalli me ɗaukan hoton, Bintu ce zasu ɗau hoto da Ahmad sai me hoton yace saikin rike wuyanshi idan har kunaso kar mutane sugane, Bintu ce taɗan sunkuyo kaɗan tarike wuyan Ahmad, jikinsu ne yayi shocking atake! Bintu tasake shi da sauri tayi baya, shima Ahmad yaji wani shocking ajikinshi harya kusa faɗowa kasa. "Me hoton ne yace ku muke jirafa". Bintu ta iso wajen jiki amace tarike wuyan Ahmad aka ɗaukesu hoto, ana gama ɗauka suka tara kayansu aka tura musu hotunan awaya. A hanyansu ne nakomawa gida motarsu tasamu matsala, Ahmad ne yace duk su fito, Beebah uwar kauɗi itace tafara fitowa daga motar, sai Abdul yabi bayanta, sai Bintu ce karshe, Ahmad ne yace wata tabamu ɗankwalinta mana zamusa awani waje. Beebah ce tahaɗa face alamun koza'a kasheta bazata bada ba! Bintu ce tacire ɗan kwalin kanta ta mika mishi tace gashi. Ahmad Azuciyarshi yace ashe tanada hakuri bara kawai mu gaisa da ita, ɗago kanshi yayi dan su gaisa saiyaga ta sunkuyar da kanta tana gyara gyellen ta, sai kawai yaɗauke kai, ita kuma tana Gama gyaran gyalle tajuya zata kalleshi taga ya ɗauke, saita basar, Ahmad kuma tin ɗazu addu'a yake acikin zuciyarshi domin tin jiya yakejin tsinkewar zuciya. Bintu ce ta ɗago kanta tanason yiwa Beebah magana daidai lokacin Ahmad ma yaɗago kanshi. Suna haɗa ido, Bintu tafara jujjuya ido alamun akwai matsala, Ahmad ne yafara ja da baya yana nuna Bintu, ita kuma Bintu ta tsala ihu tace "ku taimakeni zai kashe ni" Abdul ne yariketa da karfi yana tambayanta meya faru? Ta juya da karfi tafara gudu akan titi tana ihun ataimaketa, Abdul da Beebah ma suka rufa mata baya suna binta da gudu, Ahmad kuma ya bushe awajen sai nuna waje ɗaya yake da yatsa! Gudu take Akan titi bata lura da yanda motoci suke wucewa. Abdul da Beebah sai binta suke suna kiran sunanta Bintu!!! Bintu!!! Bintuu!!! daidai wani dutse bintu tafaɗi kasa sabida ta gaji, tana faɗuwa kanta ya bugu da dutse atake kan yafara jini, Daidai lokacin Abdul da Beebah suka iso wajen, suna zuwa Abdul ya ɗauketa yatare Napep yace Asibitin specialist, suka shiga me Napep yakaisu. Suna zuwa aka karɓi Bintu akayi Emergency Room da ita. _Ahmad_ Shikuma Ahmad yakai minti talatin hanunshi asama yana nuna waje ɗaya, bakinshi kuma yana rawa kamar mejin sanyi, saida yaɗan fara dawowa natsuwarshi kafin ya buɗe mota yakama hanyan Kaduna, ko waiwayar Adamawa be karayi ba! "Abdul ne yaje gidansu Bintu yafaɗawa mommy abinda yake faruwa, aruɗe mommy tafito tashiga motar suka nufi Asibitin". _Bintu_ Bata dawo hankalinta ba har yanzu likitocine akanta, Beebah kuwa sai kuka take kamar ranta zai fita, Azuciyarta kuma tana Addu'an Allah yasa ba Aljanu bane suka shafi Bintu, Domin ita tana matsifar tsoron me Aljanu. _Ahmad_ Allah Allah yake yakarasa garin Kaduna, yama rasa me zai fara tinani a halin yanzu? Fateemahn shi yagani ko kuma idonshi ne yake mishi gizo? To Amma idan Fateemah ce ai zatayi mishi magana, to amma ita wannan tagudu, anya itace Fateemahn shi? Kodai kamane kawai? Komadai menene idan naɗauko Mommy da Fareedah zasu san komai, Yanata magana shi kaɗai kamar taɓaɓɓe, idan yatuna yanda tarike wuyanshi sai yayi murmushi.... ✍️🗒 *Jiddah S Mapi* [6/23, 12:51 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S Mapi* *Dedicated to my love* *بسم الله الرحمن الرحيم* *____________________________________* *🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼* *🇦SSOCIATION🤝🏻* ```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}``` https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation *____________________________________* *Wattpad* _Jiddah S Mapi_ Page 49&50 "Mommy suna zuwa Asibiti Beebah ta taso tazo wajenta, mom ce ta tambayeta meya sami Bintu? Beebah tace wallahi mom nima ban sani ba, Amma inada tabbacin Aljanu ne suka shafeta! Mom tace ke Beebah banason iskanci, kifaɗamin meya sameta ko kodai wani Abun Abdul yayi mata? Beebah tace wallahi mommy ba abinda aka mata kawai tana ganin Abokin Abdul damukaje ɗaukan hoto dashi tafara ihu wai ataimaketa zai kasheta" Mommy tace ina yake Abokinnashi? Mom tun lokacin data fara ihu yatsaya awajen yana nunata ko magana beyi ba To mukuma munbita, mun barshi awajen, Zuciyar mommy ce tayi matsifar tsinkewa!!! Atake ta tsunkuya dan wani hajijiya takeji, Tacewa Beebah kiramin Abdul yakaini inda kukabar mutumin, Beebah ce tace tom mommy lafiya? Mommy tadaka mata tsawa! Kiramin Abdul nace, Beebah ce tabar wajen da sauri dan ganin yanayin mommy. _Ahmad_ Gudu yake akan hanya, burinshi kawai ya iso KD dan jiyake kamar ba mai amotar, dayaga motar bata mishi gudu sai kawai

Chapter 4 of 6