Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 6
maganan daya ɓata mata rai irin ta yau ba, Ahmad ne farko yafara kiranta da shegiya. A hankali ta ɗago kanta tace "kayi hakuri zan gyara insha Allah " Ai kuwa yaja tsaki ya fita a ɗakin yanaji kamar ya shaketa ta mutu kawai. Wato yarinyannan duk abunda za'ayi mata bazatayi kuka ba, saide tayi tabada hakuri kamar marokiya, sai nayi maganinta ay. Ita kuma Fateemah yana fita tasa kuka me cin rai, Tana cikin kuka ne taji muryan Fareedah tana, Besty ina kike? Ta share hawayenta tace "gani nan" Fareedah ta rungumeta tace "meya sameki naga kamar kinyi kuka? tace "Aa babu komai kaina ke ciwo" Ayya sorry kinsha magani? Eh nasha, Ok muje ɗaki to ki kwanta. Da daren ranan Fateemah takasa bacci, data rufe ido sai tana tuna maganganun Ahmad na ɗazu. _ba laifinki bane_ _Laifin iyayenki ne_ _Dasuka haifeki a titi_ Wato ni shegiyace? A titi aka haifeni? To ina iyayena suke!? Meyasa suka yadda ni? Shine tambayoyin data kasa amsawa kanta, Data kara tunawa seta fashe da kuka, Jikinta yafara zafi, tana kokarin ta tsaida kukan amma ta kasa. Da haka har tafara tari, jikinta yafara rawa taja bargo ta lulluɓa jikinta amma har yanzu tana jin sanyi. Tana cikin wannan halinne Fareedah ta tashi zatayi fitsari, Taga Fateemah acikin bargo jikinta yana rawa gashi fuskanta yayi ja, A razane ta iso wajenta tana tambayanta meya faru Fateemah ba bakin magana se ido kawai, Ta fita da gudu taje ɗakin mommy ta kirata, A tare sukazo da mommy, Mommy tana ganin halin da Fateemah take ciki tace akira mata Alhaji, Ai kuwa Alh Kabeer yana zuwa yace aje akira Ahmad yazo su tafi Asibiti. Fareedah ce taje kiranshi tana zuwa tayi knocking yace "yes waye? " Tace Yaya Fareedah ce, Yace me kikeso? Tace "Daddy ne yace nakiraka" Daddy kuma? Meya faru? Nima ban sani ba! Ok ina zuwa, Ahmad yana zuwa Daddy yace "oya ɗauke ta da wuri mu tafi Asibiti kar dare yayi sosai. 😳Daddy wani Asibiti? Dama wani Asibiti muke zuwa? Inji Daddy Daddy Ai yanzu dare yayi abari sai gobe mana da safe.... Kai Ahmad baka da hankali ne? Ko baka ganin halin da take ciki? Ko da Fareedah ce zakace abari sai gobe? Yayi shiru dan besan me zecewa Daddy ba ganin yahau 90, A haka badan yaso ba ya ɗauketa yakaita mota, Ji yake kamar ya shaketa tamutu ko ze huta ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:45 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story/written by_ Jiddah S mapi _dedicated to my lovly sister_ @walidation Page 13&14 "Alh 'yarka tana cikin matsala" zai fi maka sauki ka kirata ka lallaɓata, ta faɗa maka meke damunta, sabida hakki ne a kanka. To fa nan Daddy yafara share zufa, yanason yace ba 'yarshi bace, amma yana tsoron kar likitan yace mishi makaryaci. "Yace toh doctor nagode" yanzu ya ake ciki? Doctor yace "a halin yanzu de an ɗaura mata ruwa, saura na rubuta muku magungunan da zaku saya" Ahmad kuwa abokanshi sunata kiranshi awaya, yana ta tsaki wannan wani irin abune? Bamu santa ba! Ba dangi ba! Ba 'yan uwa ba! Amma ahanani yin komai chewww.... Yasake jan wani dogon tsaki ganin ana sake kiranshi. "Dan Allah karka dame ni Bash, ka kyaleni na huta wannan wana irin Bala'i ne?" naji da matsalar Da Daddy yasani yau ne ko da naka? Ɗittt ya kashe wayar. Zo nan my son! "To" Yawwa dama zuwa zakayi ka siyo magunguna acikin asibitin, to Daddy ya karɓi papern yana tafiya yana tsaki. Fareedah kuwa takasa zama, da zarar taga likita yana wucewa sai tace doctor ya jikinnata? tin suna amsawa har sukayi shiru ***************** Da ahmad yakawo maganin suka ɗunguma gaba ɗaya suka shiga ɗakin, suna shiga suka tarar da Fateemah ta farfaɗo, Fareedah tayi gudu ta rungumeta. "Ita kuma Fateemah ta lumshe ido" Ahmad kuwa yau kamar ido ya faɗo tsabar harara *nace oho de* Ya jikin naki inji Daddy a hankali tace "da sauki" tom Allah yakara sauki tace "Ameen" Daddy Yace idan kika ɗan samu sauki bazaki je gidan marayu ba gida zamu wuce, tnx Daddy gaskiya nima nafison taje gidanmu zamufi kula da ita. A take Ahmad ya ɗago kanshi yana kallon Daddy, yace "Daddy wani gida zata wuce? " Wani gida kake ciki? Cewar Daddy, nan yai shiru yana kallonsu. ************* Washe gari bayan an sallamesu ne daddy yace "Ahmad ka kaisu gida ni zan wuce gidan marayu nafaɗawa mamansu nacan bazata koma ba sai ta samu sauki", to Daddy. Mommy tace "Alhj tunda ga Fareedah me ze hana su tafi tare mu kuma muje gidan marayun tare", ok ba matsala ay Ahmad kaisu gida, to Daddy Da kyar Fateemah take tafiya, sabida tanajin jiki. Fareedah ce ta riketa har suka shiga motan a hankali. Bayan sun ɗau hanya suna tafiya ne "Fateemah tafarajin Amai, A hankali tace inajin Amai! Fareedah tace yaya kayi hakuri ka tsaya tanajin Amai, yai shiru kamar bai jita ba, ta sake cewa "yaya Amai takeji", nanma shiru ba amsa sema kara gudu dayake. Nan Fateemah tafara sheka Amai kamar ba gobe, tofah nan yaja birki ya tsaya. Yace "fitah" sukayi shiru dan Fateemah ta galabaita, ya sake cewa "nace kufita" Fareedah tace "haba yaya baka ganin Amai take ne kabari mana tagama". Zaku fitane ko sai na Ɓata muku rai, ya daka musu tsawa!!. Fateemah tafara yunkurin tashi Amma ina ba dama, da kyar Fareedah ta riketa suka fita, suna fita a motar Fateemah ta faɗi dan bata da karfi ko kaɗan. Haka yana gani yaja motarsa yabar wajen _wattpad_ Jiddahpretty ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:46 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *jiddah S mapi* _Dedicated to my lovely sister walidation_ ✅ote me on wattpad *Jiddahpretty* Page 17&18 "Suna shiga cikin Asibiti Likitocin sukayi kansu da gudu suka karɓe ta sai Emergency Room", Daddy kuwa hankalinshi duk a tashe yanata zagaye Asibitin. Azuciyarshi yana tunanin to me ya tadawa Fateemah ciwon tane haka, Dahaka har likita yafito daga ɗakin yacewa Daddy yana buƙatar magana dashi, Daddy yace to. "Bayan yashiga ɗakinne likita yace mishi Alh idan har kanada daman dazaka Aurar da 'yarka to kayi mata Aure, kaga idan har agidan miji take bazata rinƙa yin wasu tinani barkatai dahar ciwonta zai tashi ba. Daddy yayi shiru yana tinani, se daga baya yace to nagode Doctor. Doctor yace "yau zamu sallameku sabida anyi mata Allura ansa mata drip idan ya kare zaku iya tafiya" Bayan an sallamesu ne suka koma gida, Daddy ya kira Hajiya Mariya yayi mata bayanin abinda Doctor yace, Yace "Mariya bakya ganin kawai mu haɗa Auren Fateemah da Ahmad? Tunda mun yadda da tarbiyanta, To Alhaji ne dai banƙi ta taka ba Amma baka tinanin karmu shiga haƙƙin yarinya marainiya, Kaga Ahmad shi bawani isashen hankali ne dashi ba kar muzo muyi abinda zai damemu, Haba Mariya shi Ahmad ɗin ba haifanshi akayi ba? Tunda haifanshi akayi ai munada iko dashi. To Alh Allah yasanya Alkhairi cewar Hajiya Mariya. Dahaka Daddy yasanya ranan Auren Fateemah da Ahmad, suma kansu basu sani ba! ******************** Akwana atashi ba wuya a wajen Allah yau ne Ranan juma'a wanda yayi daidai da yanda Alhaji Kabeer yasa ranan Auren Fateemah da Ahmad, Fareedah da Fateemah sai ganin mutane suke suna shiga gidan suna ta guɗa. Fareedah ta tambayi Mommy meyake faruwa mommy tace ba komai, Shi kuma Ahmad yana wajen Abokansa sunata shashancinsu, inda suketa shaye shayensu, Bayan juma'a aka ɗaura Auren Fateemah da Ahmad, akan sadaki dubu Hamsin wanda Alh Kabeer ne yabiya, Se dare Ahmad yadawo gida, Daddy ya kira wayanshi yace "kasameni a falo" Daddy yacewa Hajiya mariya takira mishi Fateemah da Fareedah, Bayan sun hallara a falonne, Alh Kabeer yayi gyaran murya yace "Da farko dai nasan yau zakuyi mamakin yanda mutane suketa zirga zirga agidannan, to yau Aure aka ɗaura, Auren Fateemah da Ahmad". A razane Ahmad yaɗago kanshi yana kallon Daddy, Ya buɗa baki zaiyi magana Daddy ya ɗaga hannu yace "Banason jin komai daga bakinka kuma babbar kuskuren da zaka aikatamin shine sakin Fateemah ko wulaƙanta ta" Sannan kuma daga gobe zata tare zuwa side naka, Idan naga yanayin zamanku ba matsala kuma idan kun fahimci junanku saiku koma gidanka na jambutu, Yace zaku iya tafiya. "Tofah dahaka suka wuce ɗaki kowa jikinshi a mace, Ita kuma Fareedah murna take kamar me, suna shiga ɗakin ta rungume Fateemah tana ta tsalle, ita kuma Fateemah shiru kawai tayi ta rasa me zatayi, Dahaka Fareedah tafara haɗa mata kayanta tana cewa gobe a ɗakin yaya zaki kwana kai ammafa i will miss you, Fateemah shiru tayi batayi magana ba tana ganin anya bazataje wajen Daddy tace a raba Aurennan ba? , Kai idan tayi haka kuma batayi daidai ba domin sunyi mata halacci" Azuciyar Ahmad kuwa yanata kulla salon muguntar daze yiwa yarinyan, Lalle zakici ubanki Ai nagodewa Allah ma dayasa babu Wanda yasani acikin abokai na dako nasha kunya, Ina yaro dani ace nayi Aure ay Akwai raini. "Haka Fateemah da Ahmad suka fara rayuwa, Inda Ahmad yake mugun takura Fateemah, idan dare yayi sai yayi ta sata tsallen kwaɗo kuma yace idan ta faɗa saiya kasheta, Haka Fateemah tayi ta hakuri dashi idan Fareedah tashigo saita saki fuska tayi ta dariya idan suna hira, Amma da zarar taji muryar Ahmad tofa zuciyarta tafara tsinkewa kenan" "Dahaka Fateemah tayi ta hakuri da Ahmad wulakancin yau daban na gobe daban haka zatayi ta hakuri dashi, babban abinda yafi daminta dashi shine shaye shaye dayakeyi, tanason tafaɗa ma Fareedah amma tana mugun tsoronshi dan yace mata idan ta kuskura tafaɗa wa iyayenshi yana shan abu saiya kasheta!" Me karatu Fateemah tasha wahala a wajen Ahmad fiye da misali. Yauma kamar kullum Ahmad ne yashigo gidan A buge yana tafiya yana tangaɗi, Fateemah kuwa tana kitchen tana itada Fareedah suna girki, Kawai se sukaji karan buga kofa Fareedah tayi sauri zata je taduba ko menene, Fateemah tayi saurin katseta. Tace ki bari zanje naduba dan ita tasan halin Ahmad may be yaje yasha abune yadawo, Tana leƙa ɗakinshi taga ya kwanta rub da ciki. Ai kuwa tarufeshi a, Dataje kitche tacewa Fareedah ay ba kowa. "Tofah har dare Fateemah kwata kwata ta manta da ta rufe Ahmad a ɗaki, haka Har tayi abincin dare ta ci tayi wanka ta kwanta har bacci yafara ɗaukanta, amma taji zuciyanta yanata tsinkewa tarinka cewa astaghfurullah! Shi kuma Ahmad lokacin da ya dawo hankalinshi yayi wanka yanason yaje club amma me yana buɗe kofan yaji gumm! Ya rasa yanda zeyi gashi yanajin yunwa kuma ana ta kiranshi awaya club yacika saura shi kawai ake jira, Yadinga buga kofan yana kiran sunanta amma shiru. Haka ya zauna yana tuna abinda zeyi mata yau idan ta buɗe kofan, Wato raini yafara shiga takaninsu kenan! tana zaune kawai ta tuna yau Ahmad be zageta ba anya lafiya kawai seta tashi tafita tace bara na lekashi nagani, Tana zuwa taga kofanshi a rufe, taɗan buga ƙofan kaɗan. Kamar jira yake yace waye tayi shiru, yace oya open the door Sai alokacin ta tuna abundance yafaru da rana😳ta zaro manya manyan idanunta tace kayi hakuri zan buɗe na mantaka ne wallahi, Cabɗi ni ta manta? ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:47 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *jiddah S mapi* _Dedicated to my lovely daughter AFRAH_ _✅ote me on wattpad Jiddahpretty_ Page 19&20 "Yace taɓɗi ni ta manta lalle zataci ubanta, ai kuwa da gudu Fateemah taje taɗau malullin ɗakin tazo ta baɗeshi" Tana buɗewa taji mari tass, dan ubanki ni kika manta! Gidan ubanki ne? Dazaki rufeni kice kin manta yau sena nuna miki kuskurenki! Ya rike hanunta da karfi yana janta Yabi ta kofan baya da ita ya buɗe motarshi yasata aciki, yafita da gudu acikin gidan, "Yana gudu tanata bashi hakuri shi kuma hakurin datake bashi yana kara bashi haushi" Dahaka har ya iso wani gida, Tangameme me Ƙaton get yayi parking, Yafita agidan da kanshi ya buɗe get ɗin yashiga cikin gidan yace mata fita! Tafara cewa dan Allah kayi hakuri wallahi mantawa nayi. Yau zakisan kin manta ni! Haka ya ɗauke ta a motan Ya fita da ita Yana ɗaukan ta be ajeta ako ina ba se a wani bedroom wanda ya kayatu da abubuwan kyale kyale, Haka tana gani yafara yayyaga kayan jikinta tana bashi hakuri amma ina. Haka Ahmad yayiwa Fateemah fyaɗe (eh mana ai wannan fyaɗe ne), Haka Ahmad ya ɗauki Fateemah A sume yasata a mota ya kama hanya, Saida yayi tafiya me nisa kadin ya tsaya ya buɗe motar yana daga ciki ya cillar da ita waje yaja motarsa ya tafi. **************** "Bayan Ahmad yakoma gidane ya fara wani tinani me ze faɗawa Daddy idan ya tambiyeshi ina Fateemah, kai anya bazan koma in ɗaukota ba! Kodai nabarta ne! *(Nace duk kai kaɗai)*" Haka yayi wanka ya kwanta yayi baccinshi, Washe gari da safe Fareedah tazo ɗakin dan takirawa Mommy Fateemah, Tana zuwa tayi knocking, yace waye? tace Fareedah ce yace mene ne? Tace mommy ce take kiran Fateemah! Dumm yaji zuciyarshi ta buga, Kije ina zuwa tace toh, Yana zuwa ɗakin mommy yace "inakwana mommy" Tace lafiya ina Fateemahn? Yace Fareedah fita ki bamu waje, Fareedah tafita yasamu bakin gado ya zauna, Yace Mommy wato yarinyannan ta rainani ne jiy ta kulleni a ɗaki har dare wai ta manta ni, Shine me? Inji mommy, Yace shine itama nakaita inda za'a manta da ita! kana hauka ne ko ka fara shaye shaye ne? Yayi shiru, Ina ka kaita? Yace bayan gari, Ji kake tass tass tass Mommy ta wanke shi da mari har sau uku, kayi hauka ko? Yayi shiru ba magana nake maka ba? Shiru har yanzu, Tashi ya tashi Tace muje, Yashiga gaba suka fita! Suna fita yaga Fareedah a kwance lub abakin kofa kamar ba Rai, Da gudu Mommy taje wajenta tana kiran sunanta amma shiru, mommy ta kwala ihu tana kiran sunanta, shi kuma Ahmad ya rikece yarasa me zeyi. "Suna cikin haka Daddy ya sauko da sauri yana tambayan meyake faruwa? Mommy tace mishi Fareedah ce ta suma! Yace wa Ahmad kawo ruwa. Ahmad yatashi da gudu ya ɗebo ruwa aka Zuba mata a hankali tafara buɗe idonta tace ina Fateemah? Da alama taji duk maganganunsu, Ahmad yayi shiru Daddy yace wace Fateemah? Mommy tace Fateemah ce Ahmad yaje ya yadda ita!" Daddy yace what are you saying Mariya? Mom tace katambiyeshi kaji mana wai ta kulleshi a ɗaki shine yarama, Daddy ya ɗago idonshi yana kallon Ahmad Yace me nakeji, Yayi shiru, Daddy yace tashi muje suka ɗunguma duka suka shiga mota. Ahmad yajasu suka tafi sunata tafiya sukaga wajen yayi nisa mommy tana ta Addu'a a ranta, Har suka iso bayan gari kafin yatsaya, Daddy yace ananne? Ahmad yace eh ok ina take yayi shiru, Mommy kuwa tazuba ma wani dutse ido Taga kamar jini ne akai, tacewa Alhj kalli can, Daddy yana kallo yaga jini ne awajen! Suna zuwa sukaga jini dayawa akan dutsen harya fara bushewa, Daddy yace Wannan jininfa? Ahmad yayi shiru Daddy have ba tambayanka Nake ba? Daddy Nina ban Sani ba! Tass Daddy ya wankeshi da Mari. Ina kakai 'yar mutane? Inji Mommy yayi shiru... Ba tambayanka ake ba? "Shikamma yarasa ya zeyi idan yayi magana su mareshi yayi shiru suyi ta tambayanshi ya rasa ya zaiyi" "Suna cikin dubawa sukaga wani mutum yana zaune dagacan gefe, Daddy yaƙarasa wajen mutumin yace mishi, bawan Allah bakaga wata yarinya Acan Akwance ba? Tsohon yacewa Daddy, eh ai ɗazu wasu mutane sunzo sun ɗauki wani gawa acan kuma a yadda nagani gawan kamar mace ne........." Ai kafin yaƙarasa Daddy yafaɗi awajen, da gudu suka ƙaraso wajen suna tambayan tsohon meya faru? Yayi musu bayanin komai, kafin yakarasa zancanshi ai Fareedah ma tayi ƙasa, mutumin yarasa meyake faruwa. Mommy tadinga zabga ihu shikuma Ahmad atake jikinshi yafara rawa da ƙyar suka ɗaukesu zuwa Asibiti ************** Tun daga wannan rana Alh Kabeer yazama bashi da lafiya harya kasance jikin yayi tsanani hawan jini yake daminshi, Ɓangaren Fareedah ma bawani lafiyane da ita ba tazama shiru bata da yawan magana. Shikuma Ahmad yarasa meyake mishi daɗi Abu kamar wasa gashi yazama gaske, shima yazama shiru shiru dama gashi miskili. Alh Kabeer jiki yayi tsanani yana jinya sosai, yau kam jikinma yafi na kullum an kaishi Asibiti rai yayi halinshi saide muce Allah yagafarta mishi da duk musulman da suka mutu "Ameen" ✍️🗒️ *jiddah S Mapi* [6/23, 12:47 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _Story/written by_ Jiddah S MAPI _dedicated to my daughter Afrah_ _✅ote me on wattpad Jiddahpretty_ Page 21&22 "Tun daga Wannan ranan Hajiya Mariya tadaina yiwa Ahmad magana, Fareedah ma ba magana take mishi ba ko yayi musu magana ɗauke kai kawai suke Abun duniya yayi mishi yawa ya rasa ina zesa kanshi shi fa a Azuciyarshi yanaji bata mutu ba! Haka yazama kamar wani mahaukaci duk inda yaji ance Fateemah saiya juya yaga meshi, abokansa sun kasa gane kanshi baya zuwa club yadaina bin mata ko ankirashi awaya baya ɗauka sai shaye shaye yake kamar mahaukaci" Akwai wata rana daya kira Fareedah yace tazo tasaya mishi magani Fareedah batayi magana ba sai yaga kamar ta rainashi ne haka yarike Fareedah yayi ta dukan ta. Mommy tana dawowa taga Fareedah jiki a fashe tace meya sameki? Fareedah tace Ahmad ne ya daketa! Mommy tafita a ɗakin taje ta sameshi a kwance kan gado, mommy tace Ahmad bazaka kashe 'yar mutane ka kashe mahaifinka sannan kazo ka kashe Ƙanwarka ba, baka isa ba kayi kaɗan Katashi kabar gidannan cikin minti goma idan kasake dawowa saina tsine maka Albarka!!!Ahmad yabuɗe baki zaiyi magana amma Mommy tace idan ya kuskura yayi magana Allah ya isanta haka ya tattara kayanshi yabar gidan. Ahmad ya rame bashi da tinani saina Fateemah a halin yanzu yafara tuninin yana son Fateemah ne idan ya tuna da hakurinta da juriya, Sai yayi ta kuka kamar me, haka Habeeb yazo ya tarar dashi haka, Yace meya sameka Ahmad yayi mishi bayanin duk abinda yafaru. ********** *cigaban labari* "Yaune ranar zagayowar haihuwan Bintu da Beebah an haɗa party wanda kawayensu na makaranta dayawa suka hallara, inda Bintu da Beebah suka sa anko na skirt pink da top black suka ɗaura kai da black na ɗankwali, Faɗin yanda sukayi kyau ɓata lokaci ne domin yau 'yan biyun Mommy sunyi mugun kyau kamar asace a gudu, kawayensu kuma sunsa dogon riga baki sunyi kyau suma sosai an yanka cake ansa waƙa a speaker Inda Beebah tayi ta dansewa ita da ƙawayensu Bintu sai video kawai take yi musu tana dariya." Habeeb kuwa ya kira Beebah yace mata sweet sis ki hau watsapp kituramin hotonan da kukayi yau zansa a status ɗina tom broh bari na buɗe Data.... ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:47 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written By *jiddah S MAPI* _dedicated to my daughter AFRAH_ _follow ne on wattpad Jiddahpretty_ Page 23&24 "Beebah ta buɗe data ta turawa Habeeb hotonan su da videos ɗin dasukayi, habeeb yana ganin videon yace mata wow sweet sis kunyi kyau gaskiya tace thank you broh, Se mangariba dab suka gama partynsu suka raka duk ƙawayensu kowacce tashiga motarta suka tafi, Bintu ce ta kwashe musu gift dasuka samu daga wajen ƙawayensu tashiga musu falon mommy dashi". Ahmad yau ya tashi da tsananin ciqon kai inda yayi ta birgima yana riƙe da kanshi, dakyar yasamu yasha magani yaɗan samu sauƙi, ya zauna a gefen gado yana tinani azuciyarshi yace "da ace my teemah tana nan data bani magani da kanta nasha, komai nayi mata zatayi hakuri dani wayyo my teemah ina kike dan Allah ki bayyana min kanki nasan kina raye baki mutu ba! Ki fito dan Allah naganki zan nuna miki soyayyar dabaki taɓa jin labarinshi ba ko a Novel. Haka ya karashe tunanin shi ya tashi ya shiga wanka, bayan yafito daga wankane yashafa mayukanshi masu kamshi ya taje gashin kanshi me laushi kamar na indiyawa, ya buɗe wardrobe nashi yaɗauko wani riga pink colour da bakin wando ya ɗauko picap baki yasa ya dubi kanshi a madubi yaga ya rame sai de yayi fari sosai, a hankali ya rufe idonshi yace oh god help me out. "Habeeb bashi da damuwan daya wuce damuwar abokinshi Ahmad, kullum idan ya zauna sai yayi tagumi yana tinanin ta ina zai fara taimakawa Ahmad, har Mommy tagano yanayin shi da daddare suna zaune a falo suna kallo, Bintu tana ɗan danne danne awaya ita kuma Bebbah ta kwantar da kanta akan cinyar Habeeb tana mishi rigima wai sai yayi mata tsifa, Mommy tace Habeeb inason in tambayeka wani Abu mana? Yace to Mom ina jinki Mommy tace meya sameka ne naga tin ranan daka dawo daga Kaduna kashiga damuwa ko wani Abunne yasamu Ahmad? " Habeeb yace gaskiya mom Ahmad yana cikin matsala nan yafara faɗa mata duk abunda ya faru Amma ya ɓoye mata yanda Ahmad ya yar da Fateemah, Ba Mommy ba har 'yan biyu saida sukayi hawayen tausayin Ahmad, Mommy tace yanzu shi Ahmad ɗin yana ina? Habeeb yace yanzu de yana gidanshi acikin kadunan Amna yace min bazai iya zama a Kaduna ba gaskiya ze tafi Dubai yayi zamanshi acan, Mommy tace to yayi Aure mana wata kila idan ita Hajiya Mariyan taji zata yafe mishi, Habeeb yace gaskiya mom Ahmad A halin yanzu ko yayi Aure to matar daya Auran agaskiya GANGAR JIKINSA TA AURA dan zuciyar Ahmad tana wajen Fateemah mommy tayi shiru tana tunani...... ✍️🗒️ *jiddah S mapi* [6/23, 12:47 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by *Jiddah S mapi* _dedicated to Eeshart💕_ *🌈KAINUWA WRITTERS ASSOCIATION* _{united We stand and succed; our ambition is to Entertain & motivate the mind of readers}_ *WATTPAD* @Jiddahpretty Page 25&26 "Bayan wasu lokutane Mommy ta ɗago kanta tace da yayi Aure dayafi dai Habeeb wata kila ta yafe mishi idan taga yayi Auren, musamman idan yaje mata da jika, (toh fa kunji mommy da zance) Habeeb yace ok mommy baradai nagwada yi mishi maganan ko zai yadda, to Amma mommy idan ya yadda wa zai Aura sabida kinsan bashi da budurwa! Mom tayi shiru daga baya ta nisa tace ga Habeeba saina bashi ita ya Aura! Habeeba tayi shiru atake zuciyarta ta tsinke!!! To Shikenan mom bara zanyi mishi maganan anjima inji Habeeb " Ahmad yana kwance ciwon ciki ya dameshi yasha magani ma ba sauki da kyar ya ɗau wayarshi yakira abokinshi Bash, Hello Bash dan Allah kana inane? Bash yace kanada matsala ne? Ahmad yace eh akwai matsala ok kana wani club ne? Bash bana club Ina gidana na anguwar sarki kazo ka sameni ok, Bayan wasu mintuna saiga Bash. "Bash yana shiga ɗakin yaga Ahmad a kwance yanata murkususu, ya ƙarata ɗakin da gudu yana tambayan Ahmad meya faru? Ahmad baya iya ko magana sai rike maranshi dayake, Meya sameka A hankali yace cikina! Bash yayi shiru yana tinani can yace "Haba gaye meyasa zaka cutar da kanka ga 'yammata a club kala kala ya zaka zauna da ciwon ciki kamar mace? Haba mana gaye karka bada ni mana" Aa Bash nadaina bazan sake kusantar wata mace ba a duniya, na riga nayi Alkawari idan ba my Teemah ba saide ciwon cikin yakasheni, to Amma ai saika ɗan sha ko kwalba ɗayane inji Bash, Ahmad yace nasha nasha banga anfaninshi ba sai ma ƙaramin cuta dayake, to Shikenan saika kashe kanka. Yanzu me kake so Nayi maka? Ahmad yace mommy zaka kiramin awayarka inason naji muryarta dana Fareedah, Bash yayi shiru dan ya tuna Mommy tahanashi tafiya da Ahmad idan tagansu tarema hararanshi takeyi Mommy taki jininshi, amma bari dai ya gwada. Yacewa Ahmad bani numbanta Ahmad yamishi nuni da wayarshi Bash ya ɗauko wayar yaɗau numban Mommy yakira ta, da farko kamar baza'a ɗaga kiranba sai daga baya aka ɗaga. mommy tace hello, ba'ayi magana ba! Tanata hello hello anyi shiru, Bash yakasa magana, sai can yace hello momsy ya gida? Mommy tayi shiru tsabar taƙaici tarasa me zatace mishi, dan tagane muryanshi, azuciyarta tace wannan Bash ɗin da kanshi kamar sandan mopping sainayi maganinshi, Tace meke tafe dakai? Yace am dama momsy Ahmad ne..... Mommy tace dakata banason shashanci komai Ahmad yayi a duniyarnan dasa hannunku aciki sabida ku abokanshi ne, ku kuke bashi shawara mara kyau, mom tafashe da kuka tace Allah ya isa tsakanina daku Bashir, kun ɓatawa ɗana rayuwa nabarku dashi nikam na yafe Ahmad duniya

Chapter 2 of 6