Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 6
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [6/23, 12:43 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story/written by_ _jiddah S mapi_ _Follow me on wattpad_ jiddahpretty Hi guys this is my first story hope I will have your maximum co-op ration ❤️ *NOTE:* Banyi wannan littafin sabida wani ko wata ba, labarin kirkirrarre ne sabida haka akula sosai. _dedicated to fateemahsardauna_ Page 1&2 "Haba Ahmad meyasa bazaka dauki kaddara ba, kasani fa kowani dan Adam da irin tasa kaddarar, na wani yafi na wani amma Sam kai baka dauki kaddaraba. Nan naga Wanda aka kirada suna Ahmad ya dago kanshi, yana hawaye fuskarshi tayi ja, buɗe baki yayi yanason yin magana amma ya kas, sai kuka yake kamar wata mace, hadda shesheka dakyar ya iya cewa "Haba Habeeb ya bazanyi kuka ba, bacin kai kasan abinda yake damuna, idan Banyi kukaba me zanyi?" Yaƙare maganar cikin sanyin murya. Gyara zama Habeeb yayi haɗe da cewa. "Addu'a ya kamata kayi Ahmad, domin itace abinda yakamata kowani musulmi yayi, a lokacin daya samu kanshi cikin yanayi na kunci." "Ya isa haka Habeeb, ka ƙyaleni naji da abinda yake damuna, bawai ka cikani da surutunka ba, sanin kanka ne nayi babban rashi a rayuwata, rashin daba zan taɓa mantawa ba, tunda narasa FATEEMAH narasa komai, na wulaƙantata, na ƙuntata mata, nayi mata abinda bazata taɓa mantawa daniba, Ina zanga Fateemah? Ina zanji labarinta? tana raye ko Tana mace?" Ɗan jinkirtawa da maganan yayi, kana ya cigaba da cewa. "Idan Tana raye Ya Allah Ka bayyana min ita, idan kuma tamutu Allah Ka kai haske kabarinta!!" Ya ƙarashe maganan yana wani irin gunjin kuka. Awannan lokacin har Habeeb ba'a barshi abaya ba, duk dauriyanshi shima seda yayi hawaye, yana me tausayawa abokinnashi. *** *** "Wai Ina kike ne BINTU? kiyi sauri dan Allah kinsanfa mommy Tana jiranmu a mota." "Ina zuwa Sis HABEEBA, gyalena nake dubawa ban gani ba." Naji wata siririyar murya Tana fada. "Kiɗauki nawa a wardrobe mana bintu." Habeeba tafaɗi haka cikin yanayi na ƙosawa. "Okay nama dauka ae ganinan." Beentu tafaɗi haka tana mai ƙoƙarin yafa gyalen ajikinta. "Okay dama koban ce kidauka ba zaki dauka kenan?" Habeeba tafaɗa tana ɗan kallon gefen da Beentun take. Nan naga Beentu na sauƙowa daga kan step, cikin takunta mai ɗauke da nutsuwa. Farace sol doguwa siririya, tana da manya manyan idanu, bakinta dan karami, ƙoƙarin gyara gyallen take, tayadda zai zauna akanta. Cewa tayi "Haba My Hussaina, Kinsan fa bama haka dake, kuma naga kema ay kinasa abuna ko my sis?" "Da ma ay haka zakice, kullum se kinwa mutum laifi kizo kina mishi sanyin murya, to yanzu de muje kinga Mom nata kirana, kusan 6 missed calls tayi min" Habeeba tafaɗi haka tana mai duban wayarta dake riƙe a hanunta. "Okay to muje" Cewar Beentu. A tare suka fito daga falon suna sauri. _see me next page_ ✍️🏻 *Jidderh S Mapi* [6/23, 12:43 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story written by_ Jiddah S mapi _dedicated to fateemahsardauna_ _wattpad jiddahpretty_ Page 3&4 Suna fita daga falon habeeba ta kwalawa driver Kira yace gani hajiya tace Ina mommy yace ay hajiya ta dade da tafiya tace bazata iya jiranku ba idan kun gama ku sameta agidan abinci ok to kaimu driver yace to nan suka shiga motar suka tafi bayan driver yayi parking naga sun shiga wani waje me kyau Wanda naga ma'aikata da uniform suna rabawa mutane abinci wasu kuma suna dafawa Wasu na wanke plates daga gani de wannan gidan abinci ne Wanda yayi suna agarin ADAMAWA Ina daga kaina naga an rubuta HASSY and HUSSY'S KITCHEN suna fita a motar idanun mutane suka dawo kansu Ana tacewa kaga 'yan biyun hajiya bada kunku asare Kuje gida kuce yafadi habeeba ce kadai me cewa sannunku Samarai barka da war haka ita kuma bintu sai murmushi take nan naga sun nufo wata kykkyawar mata wacce zatakai shekara 40 habeeba tafada kan cinyar matar Tace mommy shine kikayi tafiyarki kika barmu matar da aka Kira da mommy naga tayi murmushi nan naga tsananin kamanta da habeeba tace ba dole natafi ba Kun tsaya kunata shirme kuma kunsan yau ranar biyan ma'aikata ne Mommy ai bintu ce ta tsayar damu kinsan yanayinta dayin Abu kamar karkashi Aa karki sake kizagammin ya zo maya my bintu kizauna anan Bintu tayi murmushi tace mom inason yau zanyi stew da kaima Mom tace Haba bintu yazaki gajiyar da kanki kizauna kihuta kinji my bintu Aa mom kibari zanyi Toshikenan bazan hanakiba jekiyi Ahmad dama nayi niyan tafiya yau amma bazan iya tafiya nabarka awannan yanayin ba Nagode habeeb Allah yabarmin kai dan Allah habeeb ko bayan na mutu idan kasamu my teemah dan Allah ka aureta sabida kai Kadai nayadda dakai Kai Kadai nasan zaka riketa da amana tinda kasan bakar wuyar datasha kasan na zalinceta naci amana dan Allah kayimin wannan alkawarin🙏🏻 _see me next page_ [6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story/written by Jiddah s mapi _dedicated To fateemahsardauna_ _wattpad_ Jiddahpretty Page 5&6 Ahmad kadaina irin wadannan maganganun Banajin dadinsu Sam meyasa kake maganar mutuwa bayan bakaga fateemahn kaba Ahmad insha Allah Bazaka mutu ba seka ga fateema Ka nemi yafiyanta Sannan ku Gina rayuwa me kyau Kuma inada tabbacin fateemah zata yafe maka Habeeb bana tinanin my teemah Zata yafemin koda bayan raina ne Habeeb babu abinda yake damina kamar yanda mommy tadau Zancennan da zafi ka duba kagani Yau kusan shekara daya ban sa mommy a idona ba Yazanyi da rayuwa ta ya karashe maganan yana me hawaye Abin tausayi Habeeb kam ba bakin magana Shi mamaki ma abun yake bashi wai ace yau Ahmad ne yake kuka yana fada mishi damuwanshi Shida magana ma be dameshi ba Gsky dayana da yanda ze taimaka mishi daya yayi Amma shi besan ma ta ina ze fara ba Allah ka gaggauta kawo mana karshen Matsalarnan Ameen *BINTU* Mommy wai meyasa bintu take zubar mana da class ne Kiduba fa yanzu wajen masu aiki zataje suyi tare Gsky mom abinda takeyi bata kyautawa wannan aji down ne😏 Habeeba kibi rayuwa a hankali Ita duniya a hankali ake binta Wanda batazo bama Tana jiranshi bale muda muke cikinta Ni gsky mom kina daurewa bintu gindi dama nasan Niba sona kike ba Bawai bana sonki bane beebah babu Wanda ze haifi da Yakishi sede idan kaddara ne mom tafada idonta yana cika da hawaye A hankali tajuya kanta yanda bintu bazata ganta ba ta goge idonta Bintu kuwa iyayen son aiki tanata girki suna dan hira da ma aikatan Dan ita ba ma'abociyar son magana bace Cikin hiranne wata Wanda suka dan saba da bintu Take tambayan bintu Friend dama inason inyi miki wata tambaya Ok nabeela inajinki Amma Allah yasa ranki baze baci ba Aa ba komai yi maganarki ok Dama inason tambayanki tum bayau ba Hajiyace ta haifeki!!!? Haba nabeela wannan wace irin magana ce yazakimin wannan tambayar? Bacin kinsan mu 'yan biyune nice babba Gsky bintu ba kowane ze yadda ba Duba da irin yanayinki Kiga beebah mana Tana Kama da hajiya Amma ke Sam babu abinda yahadaki da hajiya ta kamanni ko hali gsky akwai abun dubawa anan What are you saying nabeela!!!? Cewar mom Wanda tin farkon maganarsu takejinsu Ta taso tambayar bintu kota gama hadin? See me next page _Wattpad_ Jiddahpretty [6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story/written_by Jiddah S mapi _dedicated to fateemahsardauna_ Page 7&8 A take suka juyo ganin yadda mommy tayi maganan da karfi Nan take jikin nabeelah yayi sanyi ganin yadda yananayin mommy yacanza a lokaci kankani Haba nabeelah wannan wace irin magana ce meyasa kike son sa shakku a zuciyar 'Yar da Nina haifeta a cikina? shin bakida labarin Akwai 'yan biyun da Sam basa Kama da juna?" "meyasa ku mutane Bakwa gane abune yanzu da ace bani na haifi bintu ba dazaki hada abinda Baza'a taba cewa ke kika hada ba" saikuma tsaya "Gsky bana son irin wannan tambayar" Kai daga yau ma kada nakara ganinki da bintu Dan nan gaba bansan mezaki ce mata ba "Kiyi hakuri hajiya in Allah ya yadda hakan bazata Kara faruwa ba...." inji Nabeela "Banason dogon magana nabeela nariga nagama magana" hajiya ta mayar mata "Bintu wuce mutafi" Tafada cikin bacin rai "To mommy" cewar bintu wacce tinda mommy tafara fada ta Sunkuyar da kai saida zasu tafi ne takuma ɗaga kai tadubi Nabila wacce duk kunyar momy ya isheta *AHMAD* Dakyar habeeb yasamu ya lallabashi yai shiru "Ahmad gobe idan Allah yakaimu kafin in tafi dan Allah inason muje asibiti Aduba lfyrka dubi yadda karame" inji Habeeb "Aa base naje asibiti ba maganin cutana bana asibi bane Maganin cutana my teemah ne idan nasameta zan warke insha Allah" inji Ahmad "Toshikenan yanzu de ka kwanta kahuta sannan karage damuwa saboda zata haddasa maka cuta" inji Habeeb "Nima Bari nakira agida nafada musu na shaida bazan samu dawowa ba sai gobe" Mommy na isowa wajen Beebah tasamu sit nata ta zauna rai ɓace Beebah bataga fuskar tambaya ba Sai takarasa wajen Bintu tace "Bintu yanaga ran mommy a bace" "babu komai sis" inji Bintu saboda tasan idan Beebah taji maganarnan bazata ɗauka da sauki "Yazakice min ba komi bayan gashi ranta a matukar ɓace" "Nace miki ba komai ke meyasa kin fiye naci ne? Inji Bintu "Ko zaki dake nine to?" cewar Beebah "Nibance zan dake kiba dan haka kimatsa min anan" Bintu ta mayar mata "Zaki fara ko beebah meyasa bakya girmama tane tagirmeki fa" inji mommy Beebah ta zumburo baki tana kunkuni wai datayi magana sai ace ta girmeta abinda baifi ƴan mintuna ba "Yanzu de kutashi mutafi gida sabida yau yayanku ze dawo" cewar mommy "Yee mommy dagaske kik?"cewar beebah "Dama nataba miki karyane?" Nan wayan mommy yafara ringing "Yawwa ga shima yana Kira" amsawa tayi takara a kunnenta "Hello my son yakake? ok se gobe? Amma meyasa yau bazaka dawo ba? Ok to Allah yakaimu goben" saikuma ta kashe wayar "Kunga yayan nakuma yace se gobe ze dawo" mommy tafaɗa musu "Kai amma naji haushi mommy" cewar beebah Mommy tace "Yau da gobe duk dayane beebah kawai muyi addu'a Allah yakawo shi lafiya" "Ameen" cewar bintu _See me next page_ _wattpad_ Jiddahpretty [6/23, 12:44 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story by_ jiddah S mapi _dedicated to fateemah sardauna_ Page 9&10 Washe gari bayan sun gama breakfast ne, Habeeb yake cewa Ahmad "To kaga ni yau zan tafi kuma bazan dawo nan dawuri ba" Saboda wannan zuwanma dakyar mommy tabarni. Acewarta bataso nayi nesa da ita Dan Allah Ahmad kada kasa tinani a ranka Sannan kuma karka gaji da Zuwa gidanku neman tuba a wajen Mommynka "Aa Habeeb bazan iya zuwa inda mom take ba gsky" Sabida mom idan taganni bacin ranta karuwa yake Har Tana barazanar Zata tsinemin idan harna sake zuwa inda take Ba tareda Fateemah ba Kai innalillahi wa'inna ilaihiraji'un abun haryana kai da hakane Ahmad Wlh Habeeb shiyasa kaga damuwan sunyi min yawa narasa yanda zanyi Yanzu ma tafiyar da zakayi banso ba Koba komai kana debemin kewa. Amma yana iya, idan kaje ka gaida mommy Da kannan ka duka Nagode Allah yabar zumunci Habeeb yace Ameen Ahmad yace "Kashirya nakaika airport karkayi missing flight" Ok Bintu kinga yau broh ze dawo "Kizo mushiga kitchen dakanmu muhada mishi delicious" Bintu tace "Ok sis karki sami damuwa muje" Suka tashi suka shiga kitchen suna ta hira Mommy Tana kallonsu Tana Mejin farin ciki a zuciyarta tace "Allah yasake hada kanku my twins" *AHMAD* Tafiya suke a mota suna hira shida Habeeb. Nan Habeeb yake kara jaddada masa akan yakula da kanshi yadaina yawan tinani. Ahmad yace "kaga karka dameni tin jiya kana ta maimaitamin kalma daya kamar karatu" Ohh "dama nasan bazaka taba canza haliba Ahmad" Eh naji bazan canza ba Dahaka har suka isa airport *BINTU* Bintu kuwa anata aiki a kitchen bebba se surutu take zubawa. Banda eh, aa, to, Ba abinda Bintu take cewa har suka gama hada frid rice da kaji Bintu tahada sobo me cucumber Mommy tace "yanzu natura driver yaje dauko shi a airport Wai ya karaso" Yeeeee mommy "Aida kin fadamin da tare zamu tafi dashi" Kai Beebah kin fiye gaggawa Haba mommy "yabazanyi gaggawa ba yaufa kusan 2weeks ban ganshi ba sede waya" Bintu kuma murmushi kawai tayi Horn sukaji abakin gate Nan Beebah tafita da gudu Tana oyoyo yaya oyoyo Kafin driver yagama parking harta fara Bubbuga motan Seda yafito da sauri yana oyoyo my sis Nan ta rungumeshi kamkam Tana murna Yace ina dayarki? Tana falo itada mommy Ok mushiga daga ciki Suna tafiya Tana rike da waist nashi har suka shiga falon. Tana cewa "yaya kadauko tsaraban toh" Mushiga de tukun kinsan tsarabarki ta daban ce. Mommy tace "oyoyo my son sannu da zuwa nan itama ta rungumeshi tana murna" Bintu ta tsaya Tana tayi mishi murmushi Yace "kekam meyasa bazaki Waye ba Bintu" kullum kina cikin rashin sabo da mutum. Cheww Allah yakyauta halinnan naki. Kina gani fa 'yar uwarki tazo tayi min oyoyo Amma ke kina tsaye Daga nanne Bintu taje ta rungumeshi Yahada su duka uku ya rungume sunata murna "Ahmad yana komawa gida ya kwanta agado yana tinanin mommynshi da kanwarshi" Wai yau shine Kanwarshi wanda yafi so aduniya take gudunshi? "Yau shine mommynshi take ikirarin tsine mishi" "Idan yatuna rayuwarshi na da se yayi kuka" *WANENE AHMAD*? AHMAD KABEER yarone awajen alhaji kabeer. Alh kabeer shahararren dan kasuwane "Wanda yayi suna a duniya" Alhaji kabeer de dan asalin garin adamawa ne Shi asalin fulani ne Wanda yafara harkar kasuwanci tin yana saurayi Allah kuma ya buda "mishi sabida yanda yake da kyauta da taimakon talakawa" Alh kabeer yabude gidan marayu tin yana saurayi, sabida yadda Allah yasa mishi tausayin marayu a zuciyarshi. Dan hakane har yaki yin aure " dan yana gudun kar ya auri matar dazata hanashi taimakon marayu" Iyayenshi ne suka nema mishi aure Agidan marayu Wanda shiya bude da kanshi Acewarsu zatafi jin tausayin marayu 'yan uwanta "Inda suka nema mishi wata kyakkyawar yarinya me Suna mariya" "Ba matsala a auren mariya da alhaji kabeer sabida mariya Yarinyar kirkice" Bayan shekara hudu Allah be kawo musu haihuwa ba Har abun yafara damin mariya Inda alhaji kabeer yake cemata "karki damu mariya haihuwa na Allah ne" "Idan ma Allah be bamu b! Baga gidan marayu ba, semu dau daya murike kaman mu muka haifa Mariya tace "haba Alhaji kasan fa akwai banbanci tsakanin ɗa da kuma ɗan riko" Aa mariya ɗa na kowa Ne! Ganin yahau matsifane mariya tayi shiru "To dahakane har Allah yakawo ranar haihuwanta inda aka sha shagali akayi murna" Akasawa yaro sunan baban alhaji kabeer wato AHMAD. Ahmad de yasamu gata dan kota ina anaji dashi "Ahmad kyakkyawa ne" Fari Ne shi, dogo, da dogon hanci, ga karamin baki, Atakaicede shi yayi kama da larabawa. Sede kuma matsalar shi nada yawa Yanada girman kai sosai Ga kallon banza "Ga zama da abokan banza" Wasu abubuwan dayake yi abokai ne suke zigashi "Sai yayi ta tsula rashin kunya son ranshi" Dafarko yasamu daurin gindi awajen iyayenshi Se daga baya abun yafara damunsu *bayan wasu shekaru* "Dahakane har allah yasake basu haihuwa" "Yarinya taci sunan wacce take kula da gidan marayu na mahaifinsu wato FAREEDAH" Fareeda de kykkyawa ce tana Kama da Ahmad sosai. "Sannan kuma tinda aka haifi fareeda Ahmad yakara bude sabon rashin kunya" Shi adole yana da kanwa Bayan haihuwar fareeda fareeda ne Alhaji kabeer yafara diban yaranshi suna zuwa gidan marayu kai tallafi. Acewarshi idan sun girma suma zasu taimaki marayu. "Ranar farko dasukaje gidan marayun" Ahmad yasa fararen kaya masu kyau yanata Hada rai danshi beso zuwa ba. "Bayan an tara yara ana raba musu kudi ne" Alhaji kabeer yahango wata kyakkyawar yarinya. "Tana zaune a gefe tana kallonsu tana murmushi" Alhaji Kabeer yaɗan tsaya da rabiyar yana kallonta. Se ya yafito ta da hannu yace zo! Yarinyan ta tashi a hankali tana tafiya Harta iso su, seta durkusa tace gani. "Alhaji Kabeer yayi mamakin wannan yarinya batafi shekara goma ba" Amma take da natsuwa haka gata dakyau. Shi kuma Ahmad se harara yake tayi wai ana bata mishi lokaci Alhaji yace "ya sunanki?" Ahankali tace "sunana Fateemah" ✍️🗒️ *JIDDAH S MAPI* [6/23, 12:45 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 Story/written by Jiddah S mapi _dedicated to walidation S mapi_ Wattpad Jiddahpretty Page 11&12 Wow nice name inji Fareedah, Gsky Daddy yarinyannan kyakkyawa ce, gata fara ga ido wow. Daddy yace meyasa ana raba kudi amma baki zo kin karɓa ba? Tace "banada bukatar kudinne shiyasa, duk abunda nake so mama tana bani. "To ay zaki iya ajiye kudin sabida watarana cewar Fareedah" Shi kuma Ahmad se duba agogo yake yanata tsaki, ba abun yacewa Daddy ze tafi ba, se harara yake ta bankawa yarinyan. Gani yake kamar ita take kara delaying nasu. Daddy ya ciro kudi masu yawa ya bawa yarinyan, ta girgiza kai tace "aa nagode abawa sauran" Kikarɓa ni na baki ay, a hankali tasa hanu ta karba tace"nagode Allah yasaka da alheri" Ameen ************* Tin daga wannan rana idan daddy yaje gidan marayu sai yace a kira mishi Fateemah yadau kudi yabata. To fa dahaka suka saba da Fareedah sosai watarana ma Fareedah takan zuwa gidab Marayun suyi ta hira da Fateemah, har yazama idan Fareedah bataje taga Fateemah! ba batajin dadi a ranta, sunyi muguwar shakuwa da Fateemah.. Ta ɓangaren Ahmad kuma yana dada lalacewa sabida abokai dayake tare dasu, mutane suna yawan kawowa Alh Kabeer karan Ahmad amma baya taɓa yadda se yace suyi hakuri yaranta ne daya girma ze daina. Abun yana taɓa zuciyar Mariya taya za'ace yarinta bacin yaro yakai shekara 29 ina maganan yarinta anan? yauma kamar kullum Alh Kabeer ne da yaranshi zasuje gidan marayu, yayinda Fareedah take ta rokon mom tashirya suje taga kawarta kuma Bestyn ta. To Fareedah naji tashi muje yawwa Mom ko kefah A hanyarsu tazuwa gidan marayu ne Alh kabeer yake tambayan Ahmad "Wai kai son yaushe ne zakayi Aure? Ahmad yahada fuska yana hararan Fareedah wai ana tambayanshi Aure a idon yarinya karama. Ba tambayanka nake ba?. Am daddy insha Allah very soon zan kawo muku matar dazan Aura. Mommy tace "udan ma be kawo ba mu sai mu nema mishi"Fareedah tace "yess mommy nizan nema mishi ma dakaina. Daya juya ya banka mata harara tayi tsitt Bayan sun shiga gidan marayu ne Fareedah tafara neman Fateemah a inda tasaba ganinta amma bata ganta ba! Ta tambayi wasu yara su biyu suna wasa tace"ina Fateema? " Sukace Fateemah batada lafiya tanata kuka tin ɗazu taki amata allura. A wana ɗaki take? cewar Fareedah cikin tashin hankali tayi tambayar? muje nakaiki cewar wata yarinya Suna shiga dakin taga Fateemah tana ta kuka tana rawan sanyi Da gudu tafita tana kiran mommy! Mommy naganin Fareedah ta fito da gudu, tafara tambaya lafiya? Fareedah batayi magana ba se nuna daki take! Mommy tace kiyi magana, dakyar tace Fateemah, wace Fateeman? Cewar Daddy..... Nan suka shiga dakin da gudu. Suna zuwa sukaga Fateemah bata motsi nan Fareedah ta tsala ihu Mommy tace kira yayanki awaje Fareedah ta taso da gudu tana kiran yaya yaya Ya dago kanshi yace ke me haka? Kinata kiran sunana kamar wani sa'anki "Yaya wai kaje inji mommy" Yaja wata doguwar tsaki yace muje Suna zuwa Daddy yace oya Ahmad dauke ta dawuri mutafi asibiti😳 Haba Daddy kaduba fa farin kayane ajikina ta yaya zan fara daukanta? Dubi jikinta fa duk datti....... Zaka dauketa ne ko sai ranka ya ɓaci cewar daddy. A hankali yaɗauketa yana yatsina fuska Yariketa kamar kashi ya ɗauka sai yayi sauri sauri ya wurgata a motar da iya karfinshi. Har saida kanta ya bugu Daddy yace shiga mutafi, dakyar yadaure yashiga yanata kunkuni. Ita kuma Fareedah sai kuka take tana kiran sunan Fateema tana cewa ta tashi karta mutu A haka har suka iso specialist hospital. Suna zuwa ba ɓata lokaci aka karbesu Likitoci suka shiga ciki da ita, Ahmad yace dama daddy inason naje wani waje na karɓi sako, babu inda zaka kana gani mun kawo yarinya ba lafiya rai a hanun Allah kace zaka tafi, baka da imani ne? Ahmad ya haɗa rai yasamu waje ya zauna yanata kunkuni me haɗi na da ita da za'a hanani yin uzirina akanta? Yarinya kucaka ma da ita Suna cikin zama wata nurse ta fito tace doctor yana magana dakai. Alh kabeer yace to, nan yashiga ciki, doctor yace kaine baban yarinyan daka kawo? Alhkabeer yace eh nine Ok amma kasan da ciwon dayake daminta? Yace Aa Doctor yagyara zama yace Alh rayuwar 'yarka tana cikin matsala "Ka taɓa zama da ita ka tambayi matsalarta? Daddy yace Aa Tofa akwai babbar matsala! Am sorry to say, 'yarka tana dauke da ciwon zuciya wanda idan har aka barta cikin tunani tayi nisa zata iya rasa ranta a ko wani lokaci. ✍️🗒️ *JIDDAH S MAPI* [6/23, 12:45 PM] Ummi Tandama: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 *A GIDANMU TAKE!!!* 🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _story written by_ Jiddah S mapi _dedicated to my lovly sister @walidation_ _✅ote me on_ _wattpad Jiddahpretty_ Page 15&16 Da kyar Fareedah ta janye Fateemah zuwa gefen hanya ta kwantar da ita tace "ki zauna anan bara naje na kama mana Napep" A haka ta kama musu Napep ta rike Fateemah suka shiga se gida. Shi kuma Ahmad yana jan motarsa ya wuce carwash yace a wanke mishi ita, Alh Kabeer kuwa da mariya suna zuwa gidan marayu yacewa mama yanason magana da ita, Tace "ok ba komai ina jinka Alh" Yace dama so nake na ɗauke Fateemah na ɗan wani lokaci idan ba matsala, Mama tace ba komai Alh. Ay duk an zama ɗaya, Da haka suka tafi gida. *************** Shakuwa me tsanani ta shiga tsakanin Fareedah da Fateemah, Dan Fareedah sosai takeson Fateemah har cikin Ranta komai za'a siya mata zatace sai an siyawa Fateemah. Shi kuma Ahmad a duniya babu abinda yatsani gani kamar Fateemah, kwata kwata Allah be haɗa jininsu da ita ba, Ko abinci Fateemah ta dafa baya ci idan har ya san ita tadafa. Yauma kamar kullum Fateemah ce take goge goge a falo, tana kan goge TV ne taji ance mata "ke baki da hankali ne ko kin taɓa ganin inda ake goge TV da tsumma? Koda shike ba laifinki bane laifin iyayenki ne dasuka haifeki a titi, daga baya suka yadda ki" Nasan da agaban iyayen ki kike, dakin iya goge TV. Wawiyar banza. Tunda Fateemah take a rayuwarta ba'a taɓa faɗa mata

Chapter 1 of 6