zata nuna masa ya tuna duka
abinda ya faru a baya a tsakaninsu da ita. Ni na san
sato Amzad daga cikin birnin misira abune mai sauqi
a wajen mutanenka, ya kai sarkin varayi ya za ai a
sato sarqar dake wajen gimbiya lashmin alhalin dare
da rana tana wuyanta a xaure, kuma ko wanka zata
shiga kewaye bata cireta? Ko sau xaya bata tava cireta
ba tun sanda ta cire sarqa a wuyan Amzad sa’ar da
suna yara a lokacin da aka rabasu. Idan na samu
Amzad da sarqa na samu cikaken lagonta kuma duka
umarnin dana bata dole ta bi saboda zata iya salwantar
da rayuwarta da mulkinta saboda Amzad.
97
BAYAN MUTUWA
Naji ka tambayi wai mene nawa lagon? Zan iya
sanar da kai nawa lagon amman sai idan kaima ka
sanar da ni naka lagon” Koda jin haka sai sarkin
varayi ya bushe da dariya sannan ya risina gaban
Attajiri Huzulu yace “Tuba nake ya shugabana haqiqa
na yi kuskure kuma ba zan qara ba, yanzu ina neman
izininka a yau xinan zan tura zaqaquran yarana guda
biyu izuwa cikin birnin misira. Mace xaya namiji xaya
su ne Inzal da Karimat. Imzal zai sato Amzad ita
kuma Karimat zata sato wannan sarqa dake wuyan
Gimbiya Lashmin” Lokacin da sarkin varayi ya zo
nan a zancensa sai attajiri huzulu ya yi shiru yana
tunani har izuwa tsawon ‘yan daqiqu sannan ya miqe
tsaye ya yi xan taku uku ya juyo ya fuskanci sarkin
varayi yace.
“Ko shakka banayi Imzal zai iya sato Amzad
amma karimat ba zata iya sato sarqa gimbiya lashmin
ba, idan kuma ta samu nasara satota zan kuwa bata
kyautar dukiyar da babu ita babu talauci har izuwa
qarshen rayuwarta. Maza a kirawo Inzal sa Karimat su
98
BAYAN MUTUWA
yi shiri su tafi izuwa birnin misira” Kafin Attajiri
huzulu ya gama rufe bakinsa tuni an kirawo Inzal sa
Karimat sun bayyana a gaban sarki varayi.
Shi dai Inzal wani kyakkyawan saurayi ne mai
kwarjinin gaske kuma ya cava ado kai da ganinsa
kasan cewa xan sarkine ko wani xan babban attajiri
kuma fuskarsa tana xauke na xauke da alamun mutum
mai tausayi da jin qai sai dai kash akasin hakanne a
cikin zuciyarsa domin mutune mai tsananin mugunta
da rashin imani.
Ita kuma karimat mace ce doguwa mai qirar
kalangu kuma baqar fata. Ba za a kirata kyakkyawa ba
kuma ba za a kirata mummuna ba. Tana da yalwar
gashin kai domin ya zubo har qasan kwankwasonta,
kaurin jikinta madaidaicine ba yabo ba falasa, duk da
kasancewar karima a qarqashin sarkin varayi take ba
zaman kanta take ba, amma jikinta luwai-luwai yake
kamar na jarirai, hakane zai tabbatar maka tana samun
jin daxi da hutu sosai. Karimat tana xaya daga cikin
manya-manya hadiman sarkin varayi wanda ya aminta
99
BAYAN MUTUWA
da su, kuma yana qaunarta yana son ma ya mallaketa a
matsayin matarsa ta uku, amma saboda yana da wani
buri guda xaya wanda ita kaxai zata iya cire masa shi
don haka ya dakata da batun aurenta. Saboda gaba
xaya hadiman sarkin varayi sun san yana sonta don
haka ko kusantarta basa yi, shima sarkin varayin baya
zuwa inda take idan ta zo fadarsa to zata je aiwatar da
wani aiki na musamman.
Lokacin da karimat da inzal suka tsaya a gaban su
sarkin varayi, attajiri Huzulu ya yi arba da ita sai ya ji
ya kamu da tsananin sha’awarta don haka bai san
lokacin daya qura mata idanu ko qiftawa baya yi ba.
Sai da sarkin varayi ya tava hannunsa ya yi firgigi
kamar ya tashi daga bacci sannan ya basar sarkin
varayi ya yi murmushin qarfin hali.
“Amman wannan hadimar taka mai kyauce”
Sarkin varayi ya murmushi yace “Ai wannan ne aiki
na qarshe da zata yi ta zama matata”Koda jin haka sai
jikin Attajiri Huzulu ya yi sanyi ya kauda kai ga barin
100
BAYAN MUTUWA
kallonta, shima sarki varayi yace “Ya ka ganta? Zata
iya wannan aikin ko ba zata iya ba?”.
Attajiri Huzulu ya yi murmushi yace “Ai da ganin
kura zata ci mutum” sarkin varayi yace “Ta qware
wajen iya qissa da shirya makirci ga iya magana na
turata izuwa qasashe saba’in da biyu ta jagoranci
gagarumar sata a masarautun amma ko sau xaya ba a
tava samun rashin nasara ba, karimat mace ce mai
tsananin sa’a aduk abinda ta saka a gaba, wannan ce
sata ta saba’in da uku na kuma yi mata alqawarin shi
ne aikinta na qarshe wanda zan ‘yanta ta na
aureta”Koda sarkin varayi ya zo qarshen maganarsa
sai murmushi ya suvuce wa karimat ta kamu da
tsananin farin ciki amma a farin cikinta babu batun
aure da sarkin varayi domin shi ne mutum na qarshe
data tsana a duniya, ba komai ya saka ta tsaneshi ba
face tun tana da shekara shida a duniya ya xaukota
daga qasarsu bayan ya kashe iyayenta ya kwshe
dukiyarsu, ya tafi da ita ya baiwa matarsa ita ta riqeta
ta riqa bata horo na koyon sata, yaqi da jarumta a haka
101
BAYAN MUTUWA
ta girma ta cika shekara ashirin da xaya ta zama
gagarumar varauniya mashahuriya.
Abinda sarkin varayi bai sani ba ko yaushe da
dare sai karimat ta yi mafarkin abinda ya faru ga
iyayenta tun tana shekara shida, amafarki tana ganin
lokacin da sarkin varayi ya zare takobi ya sare
mahaifiyarta da mahaifinta ita kuma tana zaune tana
kuka ya sureta ya fice da ita daga cikin gidan tana ihu
tana kiran sunan iyayenta. A kan idanunta sarki varayi
ya saka aka cinawa gidansu wuta ya qone qurmus. A
qarqashin zuciyar karimat ta ci burin cewar komai
daxewa sai ta xauki fansar ran iyayenta a kan sarkin
varayi.
Sarkin varayi ya dubi inzal da karimat yace “Za
ku tafi izuwa birnin misira yanzu kai zaka sato Amzad
wanda ake shari’arsa da maigirma Huzulu ita kuma
karimat zaki sato mana sarqa wuyan Gimbiya lashmin,
bana son ku shafe sama da kwanaki bakwai a cikin
birni ba tare da kun kammala aikinku ba, maza kuje
sarkin gida ya baku dawakai da guzuri yanzu ku tafi”
102
BAYAN MUTUWA
Da jin haka sai Inzal da Karimat suka rusuna sannan
suka juya tare ficewa daga cikin fadar. Fitarsu ke da
wuya sai attajiri Huzulu da sarkin varayi suka dubi
juna suka bushe da dariya farin ciki saboda ji suke
kamar buqatarsu ta gama biya.
Wannan shi ne abinda ya faru a fadar sarkin
varayi, fadar da ake yiwa laqabi da darul uzur inda
attajiri huzulu ya vuya bayan ya gudu daga babbar
kurkuku na birnin misira.
A can birnin misira kuma lokacin da sarki yaqi ya
baro gidan sarauta bayan ya gana da gimbiya lashmin
sai zuciyarsa ta cika maqil da wasi-wasi gami da
103
BAYAN MUTUWA
firgici. Ba komai ne yasa ya tsinci kansa a cikin wasuwasu gami da fargaba. Ba komai ne yasa ya tsinci
kansa ba face tunanin hanyar fa ya kamata yabi ya
samu nasarar taimakon lashmin domin ta cika burinta.
A wannan lokaci yana tafiyane yana ta sauri domin ya
isa gidansa ya zauna yayi tunani mai zurfi domin
samun mafita kwatsam sai yaga mutum tsaye akansa
nan take zuciyar sarki yaqi ta buga da qarfi tsaya cak a
inda yake suka fara kallon-kallo da mutumin dake
tsaye a gabansa.
Ba wani bane wannan mutum face sarki Raihan
wato mahaifin gimbiya lashmin cikin alamun tsananin
mamaki gami da tsoro sarki yaqi ya qaraso kusa da
sarki Raihan ya zube qasa ya kwashi gaisuwa sannan
ya miqe tsaye ya dubeshi kansa na sunkuye cikin
biyayya yace “Ya shugabana mene ne ya fito da kai
daga gidan sarauta ka shigo cikin gari a wannan
lokacin? Sa’ar da sarki Raihan ya ji wannan tambayar
sai ya yi ajiyar zuciya sai yace “Na xauki karagata na
baiwa ‘yaarta a ranar data hau ta yi abinda na kasa yi a
104
BAYAN MUTUWA
shekara ashirin da biyar tunda ta sami nasarar kawar
da babban maqiyina daga cikin birnina amma kuma ta
tsokano mana tsoliyar dodone, na samu labarin cewar
atttajiri Husulu ya gudu daga kurkuku, tunda na samu
wannan labarin na kasa ci da sha kuma na kasa bacci,
saboda nasan cewar qarshen mulkinmu ya zo kuma
adalci ga talakawa ya qare ni da duka zuri’arta da
dukkan masu biyayya a gareni ta su ta qare domin
attajiri Huzulu ba zai barmu muci gaba da rayuwa ba,
ko dai a murqushe qasarmu gaba xaya ko muyu ragas
mu da attajiri Huzulu da jama’arsa
Yanzu dai kaine kaxai abin dogarot a shin zaka
iya taimakon ‘yarta akan aiwatar da shirinta na daqile
attajiri Huzulu? Abune na siyar da rai domin babu
tabbacin nasara a cikinsa, abune mai matuqar wahala
idan kana ganin ba zaka iya taimakonta ba to ina da
zavi na biyu, shi ne dani da gimbiya da duk masoyana
mu bi dare mu sulale mu gudu mu yi qaura daga
garin”.
105
BAYAN MUTUWA
Lokacin da sarki ya zo nan sai hankalin sarkin
yaqi ya dugunzuma ainun fiye da kowanne lokaci ya
rasa abinda ke masa daxi a duniya ya yi shiru suna
kallon juna har izuwa tsawon daqiqa biyar daga bisani
kuma sai sarki yaqi ya kalli sarki cikin nutsuwa yace.
“Ya shugabana nan ba wajen da za mu yi wannan
maganar bane, saboda babu sirri kuma ka yi ganganci
da kake fitowa daga gida a irin wannan lokacin saboda
maqiya za su iya sakawa a saceka” Sarki raihan ya yi
murmushi yace “Babu wani maqiyi daya fini sanin
birni misira da kuma mutanen da suke cikinsa, nasan
hanyoyin da zanbi ba tare dana haxu da wani tsautsayi
ba, duk wani baqo da zai shigo garinan ina ganinsa
kuma ko da zai voye fuskarsa sai da na ganka yanzu
sannan na buxe fuskarta koma na gama nazarin
wannan wurin da muke tsaye. Yanzu mu wuce izuwa
gidankaa domin mu zauna mu tattauna tabbas akwai
shawarwari da zan baka za su yi matuqar taimaka
maka”.
106
BAYAN MUTUWA
Sarki Raihan yana gama faxar haka sai ya xauki
mayafin dake kafaxarsa ya xora akan fuskarsa ya rufe
fuskarsa da shi yadda idanunsa kaxai ake gani sannan
ya kama hannun sarki yaqi ya jashi suka nausa cikin
gari izuwa hanyar da zata kaisu gidan sarki yaqi.
Al’amarin Gimbiya lashmin kuwa bayan sun rabu
da sarki yaqi ta shiga turakarta sai ta shiga sabon
tunani mai zurfi inda ta ji cewar babu abinda take so a
cikin faxin duniya sama da mallakar Amzad a
matsayin abokin rayuwarta. Nan take ta tambayi kanta
a cikin zuciya tace ta yaya zan kwato dukanin dukiyar
Amzad daga hannun Attajiri Huzulu a cikin kwanaki
biyu kacal? Ta yaya zan gani inda attajiri Huzulu yaje
ya voye na saka a kamoshi a gurfana da shi a gabana a
tsakanin yau zuwa gobe? Yin haka abune mai wuya
amma kuma ai mulki ba wasabane. Me mulki yana yin
komai indai abun mai yiwuwane a doron qasa.
Matakin da zan bi ya zama dole a gobe a zo da Amzad
fada na ganshi ya ganni kuma na tuno masa da koni
wacce a gareshi, mataki na biyu a daren yau dolene na
107
BAYAN MUTUWA
gana da babban bokan attajiri Huzulu wato boka
zallazi domin ziyara zan kai masa ta bazata tunda
shima nasan lagonsa lallai zai taimakamin akan attajiri
Huzulu koda gama aiyana wannan al’amarin sai
gimbiya lashmin ta qwalawa ilela kira ta shigo turakar
da gudu ta zube qasa a gabanta, lashmin ta dubeta tace.
“Mike tsaye muyi magana ki kalleni ido cikin ido”
Da jin haka sai Illela ta miqe ta dubeta cikin nutsuwa
Gimbiya Lashmin tace.
“Ina son a cikin darenan na kai ziyara can bayan
gari wajen boka zillazi a sirrance ba tare da wani ya
ganmu ba, kece kaxai zaki rakani, bana son a ga
fitarmu daga cikin gidanan ko dawowarmu sannan
kuma ina son mu tafi da akwatinan ta lu’u lu’un sarki
ki riqe mu tafi da ita” Koda jin wannan maganar sai
Ilela ta firgita ainun jikinta ya kama rawa a lokacin da
idanunta suka zaro tamkar tayi arba da mutuwa tace.
“Haba ya shugabata ki sani ya shugabata duka
dukiyar sarki babu abu mai darajar wannan akwatin ta
108
BAYAN MUTUWA
lu’u lu’u a duk nahiyar nan gaba xaya, shin saceta
kike so muyi?” Gimbiya Lashmin ta girgiza kai
alamar cewar ba haka ba tace.
“Fansa zan bayar a matsayin raina dana Abbana da
kuma amzadm ki sani ba domin komai boka zulazi
yake taimakon attajiri Huzulu sai saboda ya yi masa
alqawarin cewa da zarar ya karvi karagar gidannan zai
bashi akwatin lu’u lu’un sarki. Ita kuma wannan
akwatin babu mai tavashi da hannunsa ba tare da
hannun ya guntule ba har sai ya zama sarki garinan
duk wanda ya mallaki wannan akwatin zai zama duka
nahiyar babu mai kuxinsa, kuma dole sai mai mikin
garin ya xauketa da hannunsa ya damqa maka sannan
zaka ci gajiyarta. An turo varayi sama da dubu ashirin
izuwa gidan sarautar domin su sace wannan akwati
amma dukansu da guntulallen hannu suke komawa, ki
sani idan na xauketa na saka a cikin jakarnan ta akwati
zan iya baki ki riqe, duk abinda nake buqata nasan
zaki iya shi yasa na umarceki da ki ruga kije ki
aiwatar da shirye-shirye na wannan fitar da za mu yi a
109
BAYAN MUTUWA
cikin wannan dare” Ba tare da wata gardama ba Ilela
ta risina tace.
“Angama ya shugabata” Cikin hanzari Ilela ta juya
ta fice, ita kuma Gimbiya lashmin sai ta juya ta shiga
cikin turakarta ta soma shirin fita.
Al’amarin Inzal da karimat da xan saqo makanu
suka baro fadar Darul uzu amma da ya rage sauran
baifi tafiyar rabin sa’aba a iso birni misira sai suka
tsaya suka yada zango shi kuma makanu ya wuce gaba
izuwa birni misira. Bayan tafiyar makanu ne Inzal da
Karimat suka fara hira inda ya dubeta yace.
“To ke yanzu ta yaya zaki sami damar sato sarqa
dake wuyanta?” Koda jin wannan tambayar sai
karimat ta sauke ajiyar zuciya cikin alamun karayar
zuciya sannan ta dubi Inzal tace “Bani da wta dabara a
cikin zuciyata amma kuma ka sani cewa ni ban tava
karaya bisa kowane irin aiki da zanyi ba komai
110
BAYAN MUTUWA
wahalarsa da haxarinsa, kai kuma fa? Shin kana ganin
sato Amzad abune mai sauqi, alhalin dole Gimbiya
lashmin ta saka cikaken tsaro tunda tasan dole attajiri
Huzulu ya saka a farauceshi” Inzal ya numfasa yace.
“Maganarki gaskiyace amma ki sani indai gari
yayi duhu a lokacin da na shiga cikin birni misira to
ko da gaba xaya dakarun qasar suka kewaye xakin to
sai na shiga” Koda gama faxin haka sai suka ga wata
gada ta giftasu cikin hanzari Inzal ya miqe tsaye
zumbur yace.
“Ke jirani anan ina zuwa” A guje ya bi wannan
gadar izuwa cikin daji karimat ta bishi da kallo har sai
daya qule ya vace mata da gani faruwar hakan ke da
wuya sai taji motsin tafiya a can bayanta nesa kaxan
da sauri ta juya ta ruga ta vuya a can bayan bishiya
kawai sai taga wasu mutane sun nufi can hanyar da ta
nufi wani qaton kogo, nan take zuciyarta ta cika da
tambayoyi su wane waxannan mutanen kuma me su
ka zo yi alhalin gari ya soma duhu kuma akan hanyar
da babu mai binta domin hanya ce data nufi gidan
111
BAYAN MUTUWA
boka zullazi tana gama faxin haka sai ta bi bayansu da
sauri don kada su vace mata da gani amma da taga ta
soma hangosu sai ta riqa binsu a hankali don kar suji
motsinta su waigo su ganta.
Haka suka ci gaba har suka iso bakin kogon tana
ganin haka sai ta kuma voyewa a bayan wani dutse, ba
wasu bane waxannan matan face Gimbiya lashmin da
kuyangarta koda suka qarasa sai tace “Ya shugaban
bokaye buxe mun qofa” Kafin Gimbiya Lashmin ta
gama rufe bakinta sai ga tsaunin ya rabe gida biyu
wata qofa ta bayyana, su Gimbiya Lashmin suka shiga
bisa ga mamakin Karimat sai taga qofar bata rufe ba
don haka sai ta nufi wajen da azama ta shige, ai kuwa
tana shiga sai qofar ta koma ta rufe karimat ta juya a
xan tsorace ta kalli qofar amma sai ta dake ta juya ta
kunna kai cikin gidan.
Wani falo ne qawatacce wanda komai na cikinsa
anyisa da zallar zunare, wata karagace guda xaya jal
wacce aka yita da shuxin zinare aka yita, zaune akan
karagar wani dogon mutum ne mai matuqar kwarjini
112
BAYAN MUTUWA
da cikar haiba, gashin kansa sajensa gami da gashin
baki duk farare fat. Kallo xaya zaka yi masa kasan
cewar ya haura shekara tamanin a duniya koda ya
gango Gimbiya lashmin da Ilaila sun nufo shi hannun
Ilaila xauke da akwatin lu’u lu’u sai fuskarshi ta
faxaxa zuwa ga murmushi kafin su qaraso tuni ya
miqe ya taresu fuskarsa cike da murmushi.
Cikin girmamawa boka zillazi yace “Barka da
zuwa ya sarauniyar duniya, ki sani cewar ya Gimbiya
yau shekara sittin kenan ina zaune ina jiran wannan
ranar da za ki zo ki damqa mun wannan akwatin ta
zinare da hannunki, tabbas kin gama cika mun
wannnan burin nawa na duniya ke ma ki sani cewar
zuwa gobe da yamma naki burin zai cika” Da jin haka
sai Gimbiya lashmin ta yi murmushi ta amshi akwatin
lu’u lu’u daga hannun ilaila ta miqa masa koda ya
amsa sai suka ji an zabga wata tsawa mai qarfi wacce
ta tsorata Gimbiya lashmin amma sai suka ga boka
zallazi ya qyalqyale da dariya ya juya ya nufi inda aka
ajiye wata bishiyar qarfe ta zinare, yana zuwa ya xora
113
BAYAN MUTUWA
akwatin akan bishiyar faruwar haka sai akwatin ta
narke ta haxe da bishiyar kamar ba’a tava xorata a
wajenba kuma sai aka sake zabga tsawa a karo na biyu
wacce tasa gidan gaba xaya ya girgiza Gimbiya
lashmin da ilaila sai da suka faxi suka yi saurin
miqewa.
A lokacin boka zallazi ya waigo ya dubi su
Gimbiya ya yi murmushi sannan ya taho zuwa ya
garesu yace mata “Yake gimbiya kiyi sani cewar yau
ko raina kike so zan baki, domin kin cika mun burina
daya gagari iyayena da kakanina, nasan cewar baki da
buri daya wuce ki amso dukiyar Amzad daga hannun
attajiri Huzulu kuma ki kawo qarshen zalluncinsa,
kuma kina son mallakar amzad a matsayin abokin
zamanki na dindin” Koda Gimbiya taji haka sai ta yi
murmushi tace.
“Duk abinda ka faxa gaskiya ka faxa”.
“To nima dole na sallama komai nawa bisa sa’a
kuma wanda zai miki jagora wajen cika wannan burin
114
BAYAN MUTUWA
naki mutum xaya yana nan cikin kogon tare da mu”Jin
haka sai su Gimbiya lashmin suka soma waige-waige
amma ba su ga kowa ba sai tace masa.
“Kace mu huxu ne amma ni banga kowa ba, sai
mu uku” Jin haka sai ya qyalqyale da dariya kafin
kuma ya murtuke fuska yace.
“Ya karimat mai sa’a ya kamata ki fito haka ai ina
sane na bar qofar a buxe kika shigo” Koda jin haka sai
tabar bayan ginin data vuya ta fito su Gimbiya da
Ilaila suka qare mata kallo suka ga basu tava ganin
mace kamarta ba.
Boka zallazi ya tako ya qaraso zuwa gareta ya zo
ya tsaya yadda suna jin numfashin juna yace mata
“Yau shekara goma sha shida kenan ina jiran rana da
zaki xauki fansa iyayenki da sarki varayi ya kashe
miki to yau ga dama ta samu mudin zaki yadda ki
haxa kai da sarauniyata, shin za ki yi amfani da
wannan damar ne ko za ki zavi xan abinda attajiri
Huzulu yace zai baki? Ki sani idan kika taimaki
115
BAYAN MUTUWA
sarauniya zata baki dukiyar ba zaki kasheta ba har
qarshen rayuwari kuma ba zaki iya kasheta kuma zaki
zama maxaukakiya wato za ki zauna a cikin ma su
mulki riba biyu kenan kin jefi tsuntsu biyu da dutse
xaya”Koda boka zullazi ya zo nan a maganarsa sai
karimat ta yi murmushi tace.
“Ya maxaukakin boka ai ka fini sanin kaina shin
yanzu ta yaya zan bada gudumawa a cikin wannan
maxaukakin aikin?” Koda ya ji haka sai ya yi
murmushi yace.
“Zan baku wani taimako yanzu nan yadda ku uku
nan za ku tafi can fadar Darul uzur ku yaqi duka
dakarun ku kamo sarki varayi da attajiri Huzulu ku
kawo su cikin birnin misira a wulaqance ku yi masa
hukunci da kuka ga dama” Ya dubi karimat yace
“Yanzu zan baki amsar tambayarki” Yana rufe baki ya
nufi wata qofa ya buxe ya shiga jim kaxan sai ya
dawo xauke da kayan yaqi guda uku da takobi, mashi
da kuma wata hular qarfe zalla ya miqawa lashmin
takobin ita kuma karimat sai ya abata mashi sannan ya
116
BAYAN MUTUWA
miqawa ilela hular qarfe duk su uku suna riqe da
kayan yaqin sai suka ji wani irin qarfi na musamman
ya shiga jikinsu cikin matuqar mamaki lashmin ta
dubi boka zallazi tace.
“Ya kai babban boka wannan wanne irin kayan
yaqi ne haka na ma su qarfi sihiri. Na rantse da gemun
mahaifina yanzu ina jin zan iya shafe kwana da yini
ina yaqi” Ya bushe da dariya yace.
“Ai kwana bakwai za ki yi batare da kin gaji ba, ki
sani babu wani kaifi ko tsini da zai tava tasiri a tare
dake, wannan takobin dana baiwa gimbiya sunanta
saiful lujara, mashin dana baiwa karimat sunan shi
galilil haras, ita kuma hular dana baiwa Ilaila sunanta
Lamsara, ba a tava yin kayan yaqi da suka kai wannan
daraja da kuma sihiri ba, kuma sunfi shekara dubu
xaya da xari uku a hannun kakanin kakanina, yanzu
na baku wannan kayan domin ku kawo qarshen
zallunci attajiri Huzulu domin idan aka sake ya
mallaki birnin misira to zai mallaki tsafina da kuma
kayan yaqinan, ku sani kuma idan kun gama yaqi kun
117
BAYAN MUTUWA
samu nasara waxannan kayan yaqi za su vace su koma
can qasan teku su ci gaba da zamansu kuma har abada
ba za a kuma samun wani mahaluki da zai xauko su
ba har duniya ta gushe, maza ku tafi fadar darul uzur
domin aiwatar da wannan babban aikin” Koda jin
haka sai Gimbiya lashmin da karimat da Ilala suka
juya suka nufi hanyar fita.
Lashmin ta zare takobin saiful daga cikin kubeta,
ilela ta saka hular lamsara, ita kuma karimat ta
wulwula mashin galilin haras, bisa ga mamaki sai
sukaga sun fice fit ta cikin garu sun nausa da gudu
cikin daji wani irin gudu ban al’ajabi suke yi.
Saboda qarfin gudun ya kai na tauraruwa mai
wutsiya koma duk abinda suka riska a gabansu
tsalleke shi suke su wuce komai faxinsa da tsawonsa
maimakon su shafe rabin sa’a kafin su isa fadar Darul
uzut sai gashi cikin daqiqa biyar kacal sun isa ai kuwa
sai dakarun sarki varayi suka ta so musu aka
ruguntsume da wani azababben yaqi, kamar mace ta
saka tsintsiya ta share qofar xakinta haka Gimbiya
118
BAYAN MUTUWA
lashmin da Ilela da karimat suka karkashe dakaru
dubu uku da xoriya.
Sai gasu a cikin fadar tsulum sun bayyana a gaban
su attjiri Huzulu da sarkin varayi, cikin firgici sarkin
varayi da attajiri Huzulu suka zare makamai suka yi
xauki kansu lashmin da sara da suka, ko da
takubbansu suka haxu da saiful lujara da galili haras
sai suka narke suka zama ruwa abinda ya yi matuqar
ranazana su ke nan, nan suka zube qasa kafin su taso
tuni Ilela ya bayyana a gabansu ta gwara musu hular
lamshara nan take suka baje a wajen sumammu.
Lokacin da sarkin varayi da attajiri Huzulu suka
farfaxo sai suka tsinci kansu a zube a qasa a tsakiyar
fadar birnin misira, attajiri Huzulu na duba gabansa
sai ya yi arba da Gimbiya Lashmin da Amzad a zaune
akan karaga xaya yana kallonsa yana masa murmushin
mugunta, nan take Amzad ya miqa wa gimbiya hannu
ya ta saka masa sarqa a cikin hannunsa ya soma juyata
akan fuskar attajiri Huzulu yace.
119
BAYAN MUTUWA
“Wannan sarqa ta amso mun haqqina dake
wajenka kuma ta samar mun matsayi da xaukaka,
duka dukiyar daka tara yanzu ta zama tawa kai kuma
tsireka za ai bisa laifin fashi da makami tare da
abokinka sarkin varayi” Yana rufe baki sai ga sarki
sairan ya shigo fuskarsa cike da murmushi yace.
“Tabbas yanzu za a tsireka”
Masha Allah.
QARSHE.
120
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook :