ya kama muzurai yana mai qus-qus.
Gimbiya Lashmin ta gyara zama kuma tayi
gyaran murya sannan ta dubi Safwan tace.
“Tsakanin attajiri Huzulu da Saurayi Amzad
waye ya kawo qarar wani?” Safwan yace.
“Ubangiji Dullas ya taimakeki Gimbiya ai
yaro Amzad ne ya kawo qarar attajiri Huzulu” Koda
jin haka sai Lashmin tayi murmushi sannan tace.
“Ai dama abune mayuwanci attajiri ya kawo
qarar talaka sai dai talakan ya kawo qarar attajiri
saboda har kullum talaka ba zai iya danne haqqin
attajiri ba tunda anfishi sanin komai da kowa kuma an
fishi qima da daraja, maza a karantomin wannan qarar
doming a dukkan alamu zan yanke hukuncinta a cikin
qanqanin lokaci”. Koda jin wannan batu sai hankalin
attajiri Huzulu ya dugunzuma ainun ya buxe baki
kamar zaice wani abu amma sai Gimbiya Lashmin
tayi masa nini da yayi shiru tace.
“Kai ba’a magana a gaban kotu face an baka
izinin yi” cikin alamun kunya da rashin gaskiya attajiri
Huzulu ya yi shiru yana mai sunkuyar da kansa qas.
Mai gabatar da qara Safwan bin ma’aruf yayi
gyaran murya a lokacin da fadar ta suka yi tsit tamkar
24
BAYAN MUTUWA
ruwa ya ci kowa sannan yace saurayi Amzad yana
qarar attajiri Huzulu akan cewa ya kwace masa
gidansa nag ado wanda mahaifinsa ya mutu ya bari a
matsayin bashin da yake bin mahaifinsa, bayan
mahaifinsa ya mutu, baya ga wannan gidan akwai
rumfunan kasuwa guda uku wadanda yace tun kafin
mahaifin Amzad ya mutu ya bashi su jingina kuma bai
dawo da kuxin da ya araba har ajalinsa ya cika.
Bayan rumfuna uku akwai babbar gona guda
xaya wacce ke can kusa da kogin Luzim a bayan gari.
A yanzu haka duk faxin garinnan babu inda ake
noman kayan lambu sama da wannan gona kuma a
tsawon shekaru ashirin da biyar da mutuwar mahaifin
Amzad daidai da rana xaya ba a tava daina noma a
cikin gonar ba kuma duk amfanin da aka samu Attajiri
Huzulu ne yake riqewa.
Bai tava baiwa mahaifiyar Amzad koda sisin
kwabo ba, tun kafin ma ta haifi Amzad saboda tana
xauke da junan biyun Amzad da watanni shida Allah
ya yi wa mahaifinsa rasuwa” Koda Safwan ya zo nan
a bayaninsa sai Gimbiya Lashmin tayi sauri ta xaga
masa hannu tace.
“Dakata haka haba ai wannan shari’ar ta
wuce duk yadda nake zato, ina mai tabbatar muku za
25
BAYAN MUTUWA
mu iya shafe wata guda muna yinta bamu qare ba duk
da cewar za mu iya gano mai gaskiya a tsakanin
attajirin da saurayin a cikin sa’a xaya jal” koda jin
wannan batun sai kowa ya kamu da tsananin mamaki
a cikin fadar.
Su kansu manyan alqalai na qasar sai suka
kasa gano manufar Gimbiya Lashmin da kuma yadda
zata yi ta iya warware wannan qara da kuma dalilin da
yasa tace za a iya gano mai gaskiya a cikin sa a xaya
saboda basuga hujjojin da zata iya amfani da su ba.
Kamar Lashmin tasan abin dake zukatan
jama’a da sauran alqalan qasar sai kawai aka ga ta
miqe tsaye daga kan karagar mulki ta tako kafafunta ta
zo har gaban attajiri Huzulu ta dubeshi a cikin
nutsuwa tace.
“Shin gaskiya ne kana bin mahaifin Amzad
bashin da darajarsa ta kai ta gidansa, rumfunan
kasuwarsa guda uku da kuma babbar gonarsa dake can
bayan gari, gonar da babu kamarta a duk faxin qasar
nan?” koda jin wannan tambayar sai attajiri Huzulu ya
gyaxa kai yace.
“Wannan gaskiya ne kuma ina da shaidu akan
haka gami da rubutacciyar takarda mai xauke da saka
hannunsa da kuma saka hannuna akan duk kuxaxen
26
BAYAN MUTUWA
da ya zo ya karva a hannuna da zumar zai biyanio
kafin cikar wani wa’adi na kwanaki har ajalinsa ya
riske shi bai gama biyana waxannan kuxaxen ba shi
dalilin daya saka na riqe gidajensa, gonarsa da
rumfunansa na kasuwa” Koda jin wannan batun sai
Gimbiya Lashmin ta gyaxa kai kuma tayi murmushi
sannan ta sake duban attajiri Huzulu tace.
“Shin kuxaxen da mahaifin Amzad ya karva
a hannunka duka ya karve su ne a rana guda ko kuma
ya karve sune daban-daban akan ko wacce kadara
tasa?” Hazalu yace.
“Ai ya karve sune daban-daban, misali
lokacin da yake so zai gina waxannan rumfuna na
kasuwa guda uku bashi da kuxin aikin sai ya zo
wurina na bashi rancen dinare dubu xari biyu da
arba’in bisa sharaxin cewa idan ya kammala ginin zai
bayar da hayar rumfar duk wata zai riqa bani dinare
dubu hamsin har tsawon wata shida a sananne zai
kammala biyana, a watan farko da zai fara biyana
wannan kuxin ajalinsa ya same shi, tsawon shekara
guda ba a bani ko kwabo ba.
Duk sanda naje wajen matarsa na nemi
haqqina sai tace dani itama ba a bata ko sisi ba ta ma
san a hannun wa rumfunan suke ba, ya shugabata
27
BAYAN MUTUWA
kinga kenan na tafka asara na tsawon watanni shida
kuma inda kuxina a hannuna suke da sun ninka kansu,
bisa wannan dalilin na riqe duk kadarorinsa a
maimakon kuxaxena daya karva na fitar da matarsa
daga cikin gidan na zuba ‘yan haya a ciki.
Dangane da yadda aka yi na mallake
rumfunan kasuwarsa kuwa guda uku shi ne bayan ya
karvi wannan kuxin na farko dinare dubu xari biyu da
arba’in, a tsakiyar watan da zai biyani ya sake
dawowa ya ranci dinare dubu xari biyar ya sayi irin da
zai shuka a wannan gona tasa wadda ya gada a wajen
ubansa kuma ya biya ma’aikata suka nomata bisa
sharaxin cewar bayan yayi girbi zai biyani dunare
dubu xari takwas. Har bayan shekara biyu da
mutuwarsa ba a bani kuxina ba, bisa wannan dalilin na
riqe takardun rumfuna guda uku.
Ana I gobe zai rasu Mahaifin Amzad ya sake
dawowa gareni ya ranci dinare miliyan xaya ya sayi
raquma,alfadarai da jakuna waxanda za su riqa safarar
amfanin gonarsa izuwa qauyuka da birane dake cikin
qasar nan kuma ya biya ma’aikata da za su yi masa
wannan aikin rabin wahalarsu tun ma kafin kaka ta zo,
da sharaxin wata biyu da shuxewar kaka zai biyani
dinare miliyan xaya da rabi, sai da aka yi kaka uku ba
28
BAYAN MUTUWA
a bani ko dinare xaya ba, bisa wannan dalilin na riqe
gonarsa ta zama tawa”.
Lokacin da attajiri Huzulu ya zo nan ciki
dogon jawabinsa sai kawai aka ga hawaye yana
zubowa daga idanuwan Gimbiya Lashmin nan take ta
dubi Attajiri Huzulu cikin alamun tsananin fushi tana
mai daka masa tsawa tace.
“Tabbas ka cika shugaban azzaluman duniya,
da farko dai na yarda cewar mahaifin Amzad ya ranci
duk kuxaxen da ka faxa a hannunka bisa amincewar
zai biyaka kuxin ruwa to amma idan aka yi la’akari da
irin kuxaxen da aka samu a rumfunansa na kasuwa da
kuma gonarsa a wannan tsawon shekaru ashirin da
xaya ai kaci ribar data ninka kuxin daka bashi sau
dubunnai.
Kawai don kana binsa bashin kuxaxen da
gaba xaya adadinsu bai haura dinare miliyan biyu ba
sai ka cinye masa gaba xayan dukiyarsa wacce a halin
yanzu idan idan qiyasta darajarta za a yi darajarta tafi
dinare miliyan xari biyar sannan kuma dukiyar ta
haura miliyan dubu goma.
Sannan kuma kowa a garin nan ya sa ni kafin
ka mallaki rumfunan kasuwa da waxan nan gonakin
baka da jarin daya fi dinare miliyan biyar amma yau
29
BAYAN MUTUWA
an wayi gari babu mai cinikin gidaje da gonakai
wanda ya fika qarfin jari.
To idan baka sani ba yanzu ka sani cewar
wannan matsala taku kai da Amzad tun ina yarinya
qarama na san da ita. Ansha kawo wannan qarar
gaban mahaifina amma sai wasu daga cikin ‘yan
majalisarsa su sa a kori qarar a baka gaskiya, badan
komai ba sai don kana binsu izuwa gidajen su a
sirrance xaya bayan xaya kana shaka musu cin hanci
na maqudan kuxaxe.
Na daxe ina jiran wannan ranar da zan samu
damar cikakken bincike akan wannan qarar na
qwatowa Amzad da mahaifiyarsa haqqinsu amma ban
samu ba sai yau, ka sani babu cuta babu cutarwa, kaje
ka zo da duk takardu da kuma shaidun bashin daka
baiwa Mahaifin Amzad, shima Amzad zai zo da irinsu
waxanda mahaifinsa ya mutu ya bari, bayan an zo da
su kotu zata saka a yi lissafi na iya adadin hakkinka
daya kamata a biyaka a cikin dukiyar da mahaifin
Amzad ya bari sannan ayi lisafin a gani, tsakanin kai
da shi wane zai yiwa wani ciko a tsawon waxannan
shekaru ashirin da xaya” Koda jin wannan batu sai
Attajiri Huzulu ya taqarqare ya kwarara uban ihu
tamkar mahaukaci sabon shiga.
30
BAYAN MUTUWA
Sannan ya kalli Gimbiya Lashmin cikin
tsananin fushi da qiyayya yace.
BAYAN MUTUWA 3
‘K
e yarinya ce abinda mahaifinki
yabarshi a rufe baki isa ki tona shi
ba...” Kafin Huzulu ya gama rufe
bakinsa tuni Gimbiya Lashmin ta sharara masa mari,
ta dubi wasu dakaru uku dake tsaye kusa da shi tace
musu.
Koda ganin wannan al’amari sai hankalin
lashmin ya dugunzuma ainun tace a cikin ranta, anya
kuwa sarki ba yaudarata yayi bay ace jarrabawa zai yi,
babu mamaki ya sauka ne daga kan karagarsa ya bar
mata, koda gama ayyana hakan sai idanunta suka ciko
da hawaye, koda taji qwallah tana shirin suvice masa
sai tayi sauri ta sunkuyar da kanta qas don kada wani
ya gani ta share hawayen. Tace a cikin ranta ina ma
Allah bai yiyota ‘yar sarki ba. Da dai ace ita ba
kowabace face ‘yar talakawa fitik masu neman abin da
31
BAYAN MUTUWA
za suci kullum da ya fiye mata farin ciki da kwanciyar
hankali a rayuwarta
Haka dai su Gimbiya Lashmin suka ci gaba
da tafiya a cikin gidan sarautar ana biye da ita xu
tamkar wata tauraruwa mai tsananin haske a tsakiyar
dubunnan taurari har aka iso cikin babbar fada ta
gidan sarautar.
Daga dakarun tsaron sai qananan fadawa sai
kuma mutanen gari a zazzaune wato a tsaitsaye a cikin
fadar. Koda shigowar Gimbiya Lashmin tare da
ma’aikata masu take mata baya sai duk mutanen dake
zaune suka miqe. Koda aka ga Gimbiya Lashmin ta
fito a maimakon sarki sai kowa ya cika da mamaki,
aka wangame baki ana kallonta kawai, kai tsaye
Lashmin ta nufi wajen da karagar mulki take tana
tafiyar qasaita kamar wani toron giwa.
Hatta yanayin tafiyarta irin ta sarki sairan ce.
Haqiqa komai yana bin jini in da ace shigar maza
Lashmin ta yi kuma ta rufe fuskarta to da kowa zai
xauka sarki ne ya shigo fadar ba Gimbiya Lashmin ba.
Da isar gimbiya Lashmin kan karagar
mulkin sai ta zauna ta harxe qafa xaya bisa xaya
tamkar dama can ta saba zama akan karagar. A
sannane sauran jama’a kowa ya koma inda yake ya
32
BAYAN MUTUWA
zauna kuma a daidai wannan lokacin manya fadawa
da ‘yan majalisu qasar suka fara shigowa. Duk wanda
ya shigo yayi arba da Gimbiya Lashmin zaune akan
karaga mulki sai ya kamu da tsananin mamaki gami
da tsoro don ba a san dalilin faruwar wannan canjin ba
alhalin sarki yana raye.
Koda ganin wannan al’amari sai hankalin
lashmin ya dugunzuma ainun tace a cikin ranta, anya
kuwa sarki ba yaudarata yayi bay ace jarrabawa zai yi,
babu mamaki ya sauka ne daga kan karagarsa ya bar
mata, koda gama ayyana hakan sai idanunta suka ciko
da hawaye, koda taji qwallah tana shirin suvice masa
sai tayi sauri ta sunkuyar da kanta qas don kada wani
ya gani ta share hawayen. Tace a cikin ranta ina ma
Allah bai yiyota ‘yar sarki ba. Da dai ace ita ba
kowabace face ‘yar talakawa fitik masu neman abin da
za suci kullum da ya fiye mata farin ciki da kwanciyar
hankali a rayuwarta
Haka dai su Gimbiya Lashmin suka ci gaba
da tafiya a cikin gidan sarautar ana biye da ita xu
tamkar wata tauraruwa mai tsananin haske a tsakiyar
dubunnan taurari har aka iso cikin babbar fada ta
gidan sarautar.
33
BAYAN MUTUWA
Daga dakarun tsaron sai qananan fadawa sai
kuma mutanen gari a zazzaune wato a tsaitsaye a cikin
fadar. Koda shigowar Gimbiya Lashmin tare da
ma’aikata masu take mata baya sai duk mutanen dake
zaune suka miqe. Koda aka ga Gimbiya Lashmin ta
fito a maimakon sarki sai kowa ya cika da mamaki,
aka wangame baki ana kallonta kawai, kai tsaye
Lashmin ta nufi wajen da karagar mulki take tana
tafiyar qasaita kamar wani toron giwa.
Hatta yanayin tafiyarta irin ta sarki sairan ce.
Haqiqa komai yana bin jini in da ace shigar maza
Lashmin ta yi kuma ta rufe fuskarta to da kowa zai
xauka sarki ne ya shigo fadar ba Gimbiya Lashmin ba.
Da isar gimbiya Lashmin kan karagar
mulkin sai ta zauna ta harxe qafa xaya bisa xaya
tamkar dama can ta saba zama akan karagar. A
sannane sauran jama’a kowa ya koma inda yake ya
zauna kuma a daidai wannan lokacin manya fadawa
da ‘yan majalisu qasar suka fara shigowa. Duk wanda
ya shigo yayi arba da Gimbiya Lashmin zaune akan
karaga mulki sai ya kamu da tsananin mamaki gami
da tsoro don ba a san dalilin faruwar wannan canjin ba
alhalin sarki yana raye.
34
BAYAN MUTUWA
K
awai sai sarkin yaqi ya miqe ya qwalawa
dakarunsa kira, nan take sai ga Dakaru sama da
mutum xari uku sun rugo izuwa gabansa Lashmin ta
sake duban sarkin yaqi tace.
“Idan kuka kai shi can kurkuku ku sanar da
cewar kar abar kowa ya kawo masa ziyara koda kuwa
iyalansa ne kuma koda mai kawo masa abinci kada ya
shiga wajensa shi kaxai kuma sai an tabbatar da cewar
an cajeshi yayin shigarsa da fitowarsa.
Sarkin yaqi ya risina yace “Angama ya
shugabata” Nan take aka tusa qeyar attajiri Huzulu
aka fice da shi daga cikin fadar a wulaqance abin da
ko a mafarki ba a tava zaton cewar zai tava faruwa ba.
Bayan an fice da attajiri Huzulu sai Gimbiya
Lashmin tasa aka sallami kowa a fadar har da saurayi
Amzad kuwa amman kafin ya tafi sai ya faxi qasa a
35
BAYAN MUTUWA
gaban Lashmin ya fashe da kukan farin ciki kuma ya
kama yi mata godiya kamar bazai daina ba har sai da
ta daka masa tsawa a gaban Dakaru da kuyanginta
sannan ya shiga taitayinsa sannan ta dubeshi tace.
“Ban taimakeka domin komai ba sai domin
na kawo sauyi a wannan qasar tamu na kawar da
zalunci na shimfixa adalci, ko kai na kama da rashin
gaskiya sai na hukunta ka, ka sani cewar kaima yanzu
rayuwarka na cikin hatsari saboda haka dolene na
haxaka da Dakaru waxanda za su baka kariya kuma ba
zaka ci gaba da zama a wannan gidan hayan ba” Koda
jin haka sai Amzad ya dubi Gimbiya Lashmin cikin
alamun tsananin damuwa yace.
“To mahaifiyata fa? Wacce yanzu haka tana
can gidan tana jiran dawowata? Kin san cewa ta tsufa
ainun bata gani kuma bata iya tafiya” Koda jin haka
sai Lashmin tayi murmushi tace.
“Kada ka damu tuni tun kafin ma a fara yin
wannan shari’a taku nasa an xauketa an akita can
gidan sarki dake bayan gari, kuma yanzu can za a
kaika wajenta. Na tabbatar da cewar can za ku sami
cikakken tsaro har izuwa ranar da za a kammala
wannan shari’a taku” Koda gama faxin haka sai
Lashmin ta dubi mataimakin sarkin yaqi tace.
36
BAYAN MUTUWA
“Yakai muzainu wannan aikin kane, ka
jagoranci Dakaru xari ku raka Amzad izuwa can gidan
sarki na bayan gari kuma ka zauna tare da shi acan har
izuwa tsawon lokacin dana neme ku” koda jin haka sai
Muzainu ya dubeta cikin tsananin damuwa yace mata.
“Ya shugabata idan sarkin yaqi baya nan
nima bana nan akwai matsala ta tsaro a gidanna fa”
Gimbiya Lashmin tace.
“Ai nasan da haka amman kada ka manta
cewa kafin kafin ma ka isa can inda na aikeka tuni
sarkin yaqi ya dawo daga can kurkuku ko kuma kana
zaton cewa za a kawo mana harin sumame a cikin
wannan xan tsukukun lokacin?” Muzainu ya yi
murmushi yace.
“Aa bah aka bane kawai dai bana son ni da
sarkin yaqi muyi laifi ne a wajen mahaifinki” koda jin
haka sai Lashmin ta yi murmushi tace.
“Ai yanzu ni ce akan karagar mulki ba
mahaifina ba, saboda haka idan ma laifi ne ni za
kuyiwa bashi ba, indai kana tsoron tuggun attajiri
Huzulu ne to ka kwantar da hankalinka domin na
xauki matakan tsaro tsaurara akan hakan”.
Nan take Muzainu ya kama hannun Amzad
ya jashi suka nufi qofar fita daga fadar dakaru na take
37
BAYAN MUTUWA
musu baya. Sauran qiris Amzad ya fice ta cikin qofar
fadar sai ya juyo suka haxa idanu shi da Gimbiya
Lashmin take yaga ta yi masa wani irin kallo wanda
ya ximataushi ya jefashi ciki tsananin, mamaki,wasuwasu, fargaba da rashin fahimta lokaci guda duk su
biyun suka juyawa junansu baya ta nufi hanyar da zata
kaita cikin gidan sarautar shi kuma ya fice daga fadar
yana mai bin Muzainu a baya.
Da sauri, dakaru sun kewaye shi suna gudugudu sauri-sauri.
Lokacin da Gimbiya Lashmin ta shiga cikin
gidan sarauta sai ta nufi turakar mahaifinta sarki
Salhan kai tsaye tana isa babban falonsa sai ta iske shi
a zaune tare da mahaifiyarta a cikin nishaxi suna ciyeciye da shaye-shaye har suna yin soyayya irin tasu ta
manya.
Al’amarin day a yi matuqar bata mamaki
kenan domin a zatonta zata zo ta riskeshi ne a cikin
tsananin fushi bisa abinda ta aikata yau a fada domin
ta tabbatar da cewar tuni labari ya riskeshi. Koda sarki
Salhan yaga Gimbiya Lashmin ta durfafo inda suke
zaune sai ya miqe tsaye zumbur cikin matuqar farin
ciki ya tarbeta yana mai rungumeta gami da sumbatar
goshinta sannan yace.
38
BAYAN MUTUWA
“Yake ‘yarta kiyi sani cewar yaune nayi
alfahari dake a matsayin ‘yarta wacce zata iya gadata.
Sai yaune na tabbatar da cewar ke jinina ce. Domin
kin cire min qaton dutsen daya danne ni tsawon
shekaru ashirin da biyar, na daxe ina son hukunta
attajiri Huzulu amma na kasa amma ke gashi cikin
daqiqu kaxan kin hukunta shi kuma a lokacin da ya
dace ya karvi irin hukuncin da kika yi masa.
A iya tunanina duk wanda ya mutu shi kenan
komai na shi ya tafi kenan. Nazmir mahaifin Amzad
ya mutu da tsawon shakaru ashirin da biyar dukiyarsa
ta tafi ga hannun azzalumi Huzulu amma yau gashi za
ki dawo da wannan dukiyar izuwa hannun tsatsonsa,
wannan fa shi ne RAYUWA BAYAN MUTUWA sai
yanzu a bayan mutuwar Nazmir sannan iyalansa za su
yi sabuwar rayuwa irin wacce basu tava yinta ba,
domin idan wannan dukiyar ta koma hannun su, babu
sa’ansu a tarin dukiya a gaba xaya wannan nahiyar
tamu.
Lallai kuwa idan kika samu wannan nasara
kinyi abinda har abada ba za a manta da ke ba a tarihin
qasar nan, shi kuma Amzad ba shi da abinda zai iya
biyanki da shi har izuwa qarshen rayuwarsa” Koda jin
39
BAYAN MUTUWA
wannan batu sai gimbiya Lashmin tayi murmushi
sannan tace.
“Akwai abinda Amzad zai iya biyana da shi,
ba komai bane face zuciyarsa da soyayyarsa, burina
kawai ya so ni kuma ya qauna ce ni qaunar da babu
algus a cikinta, ya riqe min alqawari na soyayya har
izuwa ranar da zamu zamo abokan rayuwar juna
domin mu samu zuri’a ta gari” koda Gimbiya Lashmin
ta zo nan a jawabinta sai mamaki ya turniqe sarki da
mahaifiyar Lashmin suka zazzaro idanuwa suka kasa
cewa komai.
Daga can sai sarki ya dubeta yace mata
“Yaushe kika fara ganin Amzad hard a za ki ce kin
kamu da son sa haka?” Koda jin wannan tambaya sai
hawaye ya zubo wa gimbiya Lashmin sannan tace.
‘Na fara son Amzad tun ina da shekara
bakwai a duniya, yakai Abbana shin zaka iya tunawa
da wata rana da yammaci sakaliya sa’adda ka fita
wani rangadi tare da ni” Koda jin wannan batu sai
sarki salhan ya xaga kansa sama ya faxa kogin tunani.
Kimanin shekaru goma sha xaya da suka
gabata sarki salhan ya fita rangaxi a cikin keken
dokinsa tare da ‘yarsa Gimbiya Lashmin a lokacin
40
BAYAN MUTUWA
tana da shekara bakwai kacal a duniya. Dakaru
kimanin xari uku ne ke kwaye da su suna tafiya a
gefen wani daji dake daf da birnin nasu na misra sai
kawai suka ji ana harbor musu kibiyoyi.
Ashe Dakarun sumame ne suka kawo wa
sarki hari. Nan take cikin gaggawa dakaru suka
yanyame keken dokin sarki suka kareshi da manyan
garkuwoyinsu don kada wata kibiyar ta zo ta sameshi
ko ta soki Gimbiya Lashmin.
Ana cikin hakanne sarkin yaqi ya leqo cikin
keken dokin ya dube shi cikin alamun tsananin tashin
hankali yace.
“Ya shugabana maqiyane suka kawo mana
harin bazato, duk yadda aka yi suna da xan leqen asiri
a cikin fadarmu ta haka ne suka samu labarin wannan
fitowar ta mu” Koda jin haka sai sarki salham ya
girgiza kai yace.
“Tabbas zancenka gaskiya ne amma sai
bayan mun tsira sannan za mu yi bincike mu gano ko
wanene wannan munafikin,wai shin adadin dakarun
sumamen zai kai nawa?” Sarkin yaqi yace.
“Ya shugabana sun ninkamu sau uku idan
muka bari suka iso nan suka riskeka bani da tabbacin
kai da Gimbiya za ku tsira, abu mafi kyau shi ne
41
BAYAN MUTUWA
yanzu ku fito mu ruga izuwa cikin daji mu da tsirarun
dakaru inyaso sauran Dakarun mu suyi kamar kana
cikin wannan keken dokin su ci gaba da tsoronsa.
Kafin a cim masu munyi nisa a cikin dajin
mun zagaya tacan mun koma cikin birnin mu” Koda
jin wannan batu sai sarki salham ya dubi sarkin yaqi
cikin fushi yace.
“Yanzu kana nufin mu gudu mubar sauran
jama’ar mu anan a kashe su a banza kenan?” Sarkin
yaqi yace.
“Ai tun tuni sun siyar da rayukan su domin
kare naka dana iyalinka don tsare darajar qasarmu, ka
tuna cewar idan aka kasheka anan cikin dajin tamkar
anci birnin mu da yaqine. Idan waxan nan abokan
gabar suka san cewar sun gama da kai ai kuwa
komawa za su yi suyi gaggarumin shirin yaqi su zo su
baje birnin namu gaba xaya, jinin mutanen mu nawa
ne zai zuba anan? Adadin dukiya nawa ne zata
salwanta, kaga kenan ashe rayuwarka zata kuvutar da
miliyoyin mutane da miliyoyin dukiya”.
Koda jin wannan batun sai sarki salhim ya
yi wuf ya xauki Gimbiya Lashmin ya goyata a
bayansa ya xaureta tamau sannan ya zare takobinsa
42
BAYAN MUTUWA
kuma ya xauki garkuwarsa ya fito daga cikin keken
dokin.
Nan yake shi da sarkin yaqi da tsirarun
dakarun waxanda basufi su arba’inba suka ruga izuwa
cikin daji suka bar sauran dakarun tsaye a gaban
keken dokin suna gadinsa.
Tafiyar su sarki ke da wuya sai ga dakarun
sumamen sun iso bisa dawakansu da yawa. Koda suka
hango keken dokin sarki sai dukkaninsu suka zare
takubbansu suka afkawa dakarun dake tsaron keken
dokin aka ruguntsime da yaqi.
Duk da cewar dakarun sumamen sun ninka
dakarun sarki salhan sau uku sai da aka shafe sa a
guda cif ana baqin gumurzu sannan aka qarar da
dakarun sarki.koda aka gama karkashe su aka leqa
cikin keken dokin sai aka ga wayam. Nan take
shugaban dakarun sumamen ya kurma ihu! Yace.
“Tabbas waxannan mutanen yaudarar mu
suka yi, tun xa zu sarkin misra ya fice daga cikin
keken dokinnan ya gudu ku zo mu bi sawun su” Yana
gama faxin hakan sai ya zaburi dokinsa yabi hanyar
da su sarki salhan suka bi.
43
BAYAN MUTUWA
Suma saran dakarun sai suka rufa musu baya
suka rinka tsala gudu tamkar dawakan nasu za su tashi
sama.
**
Al’amarin sarki salhan da sarkin yaqi da
tsirarun dakaru kuwa tunda suka fara gudu basu tsaya
ba, cikin sa a kuwa suka hango qofar birnin misra
daga can nesa tazarar kimanin zango xari.
Nan take farin ciki ya lulluve su suka qara
gudun su, sai daya kasance bai fi sauran taku baifi
saba’in ba tsakaninsu da bakin qofar garin sai kawai
suka hango dakarun sumame acan bayan su kaxan sun
durfafo inda suke a guje bisa dawakai.
A daidai wannan lokacin Nazmin mahaifin
Amzad ya dawo daga gona yana save da fatanya a
kafaxarsa kuma yana riqe da hannun xansa Amzad
yaron da bai wuce shekara tara ba a duniya.
Lokacin da su sarki salhan suka waiga
bayansu yana goye da Gimbiya Lashmin suka hango
dakarun sumame a bayansu sai suka qara qarfin
gudunsu, koda ganin haka sai dakarun sumamen suka
soma xana kibiyoyi akan baka suna harbinsu kuma
suna daxa kusanto su. Nan fa suka soma yiwa dakarun
44
BAYAN MUTUWA
sarki salhan xauki xai-xai suka riqa faxuwa qasa
matattu.
Har ya kasance sauran sarkin yaqi da sarki
salhan kaxai suka rage a raye suna ta gudu. Tun daga
nesa sarkin yaqi ya riqa qwalawa masu gadin qofar
gari kira yana basu umarnin su buxe qofar amma da
yake masu gadin basu shaida ko su wayeba sai sukaqi
buxe qofar.
A wannan lokacin Nazmir da xansa Amzad
kuwa na daf da isa bakin qofar birnin Misra.koda suka
jiyo gudun mutane biyu a bayansu sai suka waiwaya a
firgice, take Nazmir yaga ashe sarki ne da sarkin yaqi
suke wannan gudun na ceton ransu, kuma ga dakarun
sumame can a bayansu sun durfafo sauran qiris su
cimmasu, kawai sai Nazmir ya juya yana dakawa
masu gadin tsawa yana musu ishira cewar sarki ne fa,
nan take masu gadin suka yi sauri suka buxe qofar.
Amman kuma sai masu gadin suka kasa
fitowa domin kawowa sarki xauki saboda ganin
yawan abokan gaba domin idan suka fito za a samu
galabar shiga cikin birnin.
45
BAYAN MUTUWA
BAYAN MUTUWA 4
Kawai sai gani aka yi kibiya ta soki sarki a
cinya ya kife qasa, Lashmin dake goye a bayanshi sai
ta faxi qasa ta riqa mirginawa izuwa baya can wajen
da maqiya ke tahowa tana ihu, shima sarkin yaqi sai
kibiya ta soke shi a gadon baya ya kife qasa.
Koda ganin abinda ya faru sai Nazmir ya
saki hannun xansa Amzad ya ruga da gudu izuwa inda
sarki yake kwance ya sunkuceshi ya azashi a kaxarsa
ya ruga da gudu dashi izuwa cikin birnin misra ko
tunawa da batun xansa bai yi ba.
Shima yaro Amzad sai ya ruga da gudu ya
xauko Gimbiya Lashmin a kafaxarsa ya nufi qofar
birnin misra, yana gudu ana harbor masa kibiyoyi har
kibiya guda ta soke shi a hannu sai ya yi matuqar
dauriya yaci gaba da gudu a haka jini na zuba a
hannunsa ga lashmin a kafaxarsa yana layi jiri na
xibansa amma sai daya shige cikin qofar birnin.
46
BAYAN MUTUWA
Sarkin yaqi ne ya qaraso da qyar da gudu
yana faxuwa yana tashi har ya shiga cikin qofar, ai
kuwa yana shiga sai dakarun dake tsaron qofar garin
suka yi sauri suka mayar da qofar suka rufeta kuma
suka hau kan ganuwa suka xana kwari da bakansu.
Koda ganin haka sai dakarun sumamen suka
yi tirjiya, bisa dole suka kaxa dawakansu suka juya da
baya cikin baqin cikin rashin samun nasarar kashe
sarki salhan.
A cikin birni kuwa ranga-ranga aka xauki
sarki da sarkin yaqi aka tafi da su izuwa gidan sarauta.
A lokacin wani bafaxe ya zo ya fizge
Gimbiya Lashmin daga kan kafaxar Amzad sai tayi
wuf ta fizge wata qaramar sarqa dake wuyan Amzad
ta dubeshi cikin murmushi tace.
“Har abada ba zan mance da kai ba, ka zo
gidan sarki ka amshi sarqarka a hannuna, ni kuma zan
saka maka da abinda yafi komai daraja a wajena”.
Tana gama faxin haka sai