Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 6
xaya daga cikin aljanun yana qyaqyata dariyar farin ciki, take aljanin ya zube qasa a gaban sa shi kuma sai ya haye bayan aljanin ya tashi dashi sama. Gaba xaya sauran aljanun ma sai suka tashi saman suna masu rufa masa baya. Kafin cikar daqiqu sun luluqa izuwa qololuwar sararin samaniya. 71 BAYAN MUTUWA Suka vace vat! A cikin gajimare,a sannane sarkin yaqi ya miqe tsaye zumbur ya shiga karanta waxansu xalasiman tsafi yana tofawa yaransa waxanda suka haukace da waxanda suka suma sakamakon ganin waxannan mugayen aljanun. Da qyar da sixin goshi ya dawo da su cikin haiyacinsu sannan suka sauko daga kan wannan tsaunin suka koma izuwa cikin gari cikin tsananin fargaba da tashin hankali. Amzad yana cikin xakinsa a kwance ya yi shiru lokaci zuwa lokaci yana juyawa ya kalli mahaifiyarsa dake kwance, tana barci cikin kwanciyar hankali ga mamakinsa sai ya ji wani daxi ya lulluve masa zuciya. Tun tsawon lokacin daya taso a duniya bai tava ganin mahaifiyarsa yana yin barci mai daxi da nutsuwa kamar daren wannan lokacin ba. Hakan yasa shi ya miqe a hankali ya komo tsakiyar xakin ya zauna yana dube-dube. A lokacin mamaki kuma ya kama shi, ba komai ne yasa yake wannan mamakin ba face har yanzu ya kasa gano dalilin daya saka Gimbiya 72 BAYAN MUTUWA Lashmin ta yi musu wannan taimakon, tabbas yasan ruwa baya tsami banza. Duk da haka kuma sai ya ji wani tsoro ya lulluve masa zuciya, ba komai ne yasa fargabar a zuciyarsa ba face tunano attajiri Huzulu da kuma tsananin hatsabibancinsa, tabbas yasan ba zai barsu a haka ba, saboda har yanzu yana tuna irin arangamar da suka yi da shi a farkon lokacin da aka kai masa samace akan Amzad ya kai qarasar gaban sarki domin kwato musu dukiyarsu. Sun haxu da attajiri Huzulu ne a kasuwa yana zaune a wata rumfarsa shi kuma Amzad ya koro jakunan xauke da qasa yana zagaya kasuwa da su, cikin sauri ya saka aka kirawo masa Amzad, bai yi wata-wata ba ya shiga rumfar ya same shi. A wulaqance ya dubi Amzad yace masa “Har girman wuyanka ya kai da zaka shigar da ni qara gaban sarki? To ka sani kai baka isa ka amshi ko sisi daga wajena ba, kuma duk duniyar nan babu wanda zai iya kwato maka koda sisin kwabo daga hannuna”. Jin haka sai Amzad yace masa. “Ai duk taqamarka baka fi qarfin hukuma ba” Jin haka sai attajiri Huzulu ya qyalqyale da dariya. 73 BAYAN MUTUWA “Yaro man kare, tabbas har yanzu baka san wane attajiri Huzulu ba, don haka idan kana cin qasa ka kiyayi ta shuri, na kara da mahaifinka ma bai samu nasara ba bare kuma kai, ai tsiya dai ka gamu da ita kuma haka za ka ci gaba da rayuwa a cikin tsananin talauci har zuwa qarshen rayuwarka, ni kuma attajiri Huzulu hasken rana ne idan na fito tafin hannu baya tava kare shi” Jin haka yasa Amzad ya juya cikin fushi yana faxin. “Ni kuma zan tabbatar maka sarki goma zamani goma, duk yadda ka kai ga samun nasara akan wasu to ni zan samu nasara akan ka” Ya fice daga rumfar yabar attajiri Huzulu zaune cikin vacin rai. Amzad ya sauke numfashi a hankali sannan ya soma girgiza kansa, tabbas yasan shu’umanci attajiri Huzulu kuma yasan ba zai tava barin su ba dole ya nemi kawo musu hari, don haka a daren yau ya kamata ya yi tunanin mafita tun kafin gari ya waye. ** Al’amarin gimbiya Lashmin kuwa lokacin da ta baro turakar mahaifinta sarki sairan cikin tsananin baqin ciki sai ta koma can tata turakar ta zauna tana 74 BAYAN MUTUWA tunani da nazari. Da farko sai ta miqe tsaye zumbur da nufin ta fito ta kirawo dakarun dake tsaron lafiyarta su rakata izuwa can gidan sarki dake bayan gari domin taje ta nunawa Amzad wanan sarqa tasa dake hannunta ta tuna masa da duk abinda ya faru sa’adda suna yara. Domin su qulla sabuwar soyayya a yanzu amma data tuno da batun attajiri Huzulu sai ta fasa fitar ta kama kai kawo a cikin turakarta kawai jira take taga dawowar sarkin yaqi domin ta ji abinda ya faru. BAYAN MUTUWA 6 Ai kuwa tana cikin wannan haline shugabar kuyanginta ta shigo cikin turakarta a ximauce da sarki tace. “Ya shugabata ga sarkin yaqi can ya shigo falonki da gudu yana ta faman haki”. 75 BAYAN MUTUWA Koda jin haka sai Lashmin tayi murmushi tace ai nasan haka zata faru. “Bari naje naji daga bakinsa” Nan take Gimbiya Lashmin ta nufi babban falo na turakarta da sauri. Da zuwa sai ta iske sarkin yaqi a tsaye yana kai kawo cikin alamun tsananin damuwa. Koda sarkin yaqi yaga Gimbiya ta fito sai ya taho gareta da sauri ya zube qasa bisa gwiwoyinsa saboda biyayya sannan ya buxe baki da nufin ya yi mata bayanin abinda ya faru amma sai yaji ta tari numfashinsa tana mai cewa. ‘Kada ka vata miyan bakinka ya kai sarkin yaqi, na sani cewa attajiri Huzulu ya gudu daga kurkuku a halin yanzu, abin da nake so na sani kawai shi ne shin aljanune suka zo suka kuvutar das hi ko kuwa dakarune na mutane?” Cikin tsananin mamaki sarkin yaqi ya xago kai ya dubi Gimbiya Lashmin yace. “Ya shugabata yaya aka yi kika san duk wannan al’amarin?” Lashmin ta yi doguwar ajiyar zuciya tace. “Ai mutum baya fita yaqi sai ya yi tanadi gami da nazarin abokin gabansa, dole kasan maqiyinka ka kuma san qarfinsa da qarfin shirinsa 76 BAYAN MUTUWA kafin ka tunkare shi, ko ba haka bane?” Sarkin yaqi ya gyaxa kai yace. “Wannan haka yake ya shugabata” Gimbiya Lashmin ta zuba masa idanu tana kallon shugaban sarkin yaqi qasar cike da jimamin abinda ya faru kana kallonta kasan ranta ba qaramin vaci ya yi ba, musamman domin tun tsawon zamani babu wani mahaluki daya tava guduwa daga wannan kurkukun sai yau da attajiri Huzulu ya tsere. Suka yi shiru na wani lokaci kafin can ta furza da numfashi cikin vacin rai. 77 BAYAN MUTUWA G imbiya Lashmin taje ta zauna akan wata kujera sannan ta dubi sarkin yaqi ta yi masa umarnin shima ya zauna, ya miqe ya zauna akan kujerar ba tare da vata wani lokaci ba ko gardama ba sai ya miqe ya zauna akan kujerar dake fuskantar tata. Take sai wata kuyanga ta kawo musu shayi,kowannansu ya karva suka fara sha, sai da gimbiya Lashmin ta kurvi shayin sau uku sannan ta ajiye kofin akan teburin dake gabanta sannan ta dubi sarkin yaqi a cikin nutsuwa tace. “Tun ina yarinya qarama yar shekara bakwai na gane cewa attajiri Huzulu yafi qarfin kowa a qasarnan domin hatta mahaifina tsoronsa yake ji, tun a sannan na fara tunanin hanyoyin da zan bi na yaqe shi, bisa dole na riqa bincike cikin sirri akansa har sai dana gano iya qarfin arziqinsa. Iyakakar qarfin sihirinsa na tsafi da kuma dukkanin mutunen dake yi masa biyayya a cikin 78 BAYAN MUTUWA qasarnan da wajenta, hakan yasa na gano ba zan iya yaqarsa ba ko kawar da shi ba face na nuna masa kaidi irin na mu na mata, wato fanin siyasa da kuma gano babban lagonsa guda xaya. Ta hanyar siyasa na soma dakushe girmansa da kimarsa a idon mutane, bisa wannan daliline nasa aka kamashi aka kai shi kurkuku, ina sane zai iya guduwa daga kurkukun amma kuma bazai yi saurin xaukar mataki ba a kaina saboda ana kasheni yanzu kowa yasan shi ne,haka idan yace zai zo ya yi juyin mulki a qasar farat xaya mutane za su gane cewa bashi da gaskiya kuma har abada ba zai samu haxin kan sub a. Dole yanzu ya voya a wani wurin sannan ya fara tunanin hanyoyin da zai bi yaga bayana da mahaifina da kuma Amzad, kaga kenan a karon farko ya zama mai laifi ya gudu daga kurkuku, guduwarsa daga kurkukun zatasa jama’ar gari su fara zarginsa da rashin gaskiya a lokacin da ni kuma nake ci gaba da tafiyar da shari’arsa dake tsakaninsa da Amzad ina fitowa da dukkan tuggun daya shiryawa mahaifinsa qarara a baina jama’a kowa yana ji, hakan zai saka kowa yasan rashin imaninsa da rashin gaskiyarsa. 79 BAYAN MUTUWA Hakan zai sa jama’ar gari su tsane shi,tofa a daidai wannan lokaci ne zai harzuqa yace zai yi amfani da qarfin sa wajen ganin ya gama dani da kuma mahaifina ya yi juyin mulki. Ni kuma a sannan ne zan kawo qarshensa ta hanyar amfani da babban lagonsa dana gano, yakai sarkin yaqi kayi sa ni cewa bazan iya gaya maka komene ne wannan lagon na attajiri Huzulu har sai bayan n agama dashi sannan zaka ga lagon nasa da idanunka. Yanzu zaka iya tafiya izuwa gidanka domin kaje wajen iyalinka su ganka su sami nutsuwa, ina son ka kwantar da hankalinka ka sani cewa babu abinda zai sake samun waninku har izuwa sa’adda zamu ga bayan wannan babban maqiyin na mu wanda ya kashe mahaifinka”. Koda Gimbiya Lashmin ta zo nan a zancenta sai mamaki ya turnuke sarkin yaqi yace. “Yaya aka yi kika san cewa attajiri Huzulu ne ya kashe mahaifina alhalin ni kaina bansani ba sai a yau xinnan da ya faxa min da bakinsa acan kurkuku?” Sa’adda Lashmin taji wannan tambaya sai ta yi murmushi tace. 80 BAYAN MUTUWA “Shin ka mance na gaya maka cewa tun ina yarinya nake bincike akan duk abubuwan da attajiri Huzulu ke aikatawa? To kasani cewa tun a sannane ma na gano cewa hatta dakarun sumame da suka tava kawowa sarki hari sa’adda muka fita wani rangadi attajiri Huzulu ne ya aiko su, kuma a wannan ranar ne Nazmir mahaifin Amzad ya ceci rayuwar sarki shi kuma Amzad ya ceci rayuwata. Kaima da qyar ka tsira da rayuwarka bayan an harbeka da kibiya a gadon bayanka, mahaifin Amzad ya saka anyi wani sihiri ga Amzad wanda ya saka ya mance da duk abinda ya faru tsakanina dashi a wannan rana, kuskuren da mahaifina ya yikenan da nima bai sa anyi mini irin wannan sihirin ba domin daidai da rana xaya ban tava mantawa da Amzad ba a cikin zuciyata. Ina tuna kamannin fuskarsa bayan kowace daqiqa guda. Sarqar wuyansa kuwa wacce na fizgo a lokacin da aka rabamu har yau har gobe da ita nake kwana da ita nake tashi ban tava rabuwa da ita ba” Koda Gimbiya Lashmin ta zo nan a zancenta sai hawaye ya zubo mata nan take ta zura hannunta izuwa cikin rigarta ta zaro wannan sarqa ta Amzad ta nunawa sarkin yaqi. 81 BAYAN MUTUWA Koda sarkin yaqi ya yi arba da sarqa sai ya kamu da tsananin mamakin gami da al’jabi kuma ya kamu da tsananin tausayin Gimbiya Lashmin. Nan take shima hawaye ya zubo masa yace “Ya shugabata tabbas qwaqwalwarki daban take data kowa a wannan zamani, basirarki da hangen nesanki sunfi gaban tunani. Tabbas a gaban idanuna kika cire wannan sarqa daga wuyan Amzad a lokacin kina da shekara bakwai a duniya shi kuma baifi shekara taraba. Ina kwance a qas jini yana zuba a gadon bayana na xago kain naga sa’adda Amzad ya savaki a kafaxarsa ya ruga dake izuwa cikin qofar birninmu, bazan tava mantawa ba a wannan lokaci ma said a kibiya ta sokeshi a hannu ya kwallara uban ihu amma duk da haka bai yarda ke qasa ba sai yaci gaba da gudu dake xauke har sai da ya tserar dake, shin yanzu saboda haka ne kema yanzu kike son ki qwato masa dukiyarsa daga hannun attajiri Huzulu?” koda jin wannan tambayar sai Gimbiya Lashmin ta share hawayenta sannan ta girgiza kanta tace. “A’a bawai don na yi masa sakaiya bane bisa ceton rayuwata da ya yi sai saboda tun a wannan ranar na kamu da tsananin son sa, ina mai tabbatar maka da cewar idan kaga ban auri Amzad ba to sai dai idan 82 BAYAN MUTUWA bana numfashi a doron qasa” Koda jin wannan batu sai hankalin sarkin yaqi ya dugunzuma ainun hawaye ya sake zubo masa yace. ‘Babu yadda mahaifinki baiyi ba akan kada wannan ranar ta zo, bisa hakane ya nisantaki da Amzad ya toshe duk hanyoyin da za ku iya haxuwa muma ya gargaxemu akan kada mu kuskura mu yi zancen Amzad tare dake ko mu sanar dake inda yake, saboda bayanin da Bokansa ya yi masa na cewar indai kika yi soyayya da Amzad a qarshe babu ribar da za a samu face nadama da baqin ciki...” Caraf! Sai Gimbiya Lashmin tace. “Duk nasan da wannan al’amarin domin shi kansa sarki ya shaida mini hakan da bakinsa amma na zavi nadamar da baqin ciki kowane irine da dai a rabani da masoyina. Idan ma ba mu yi soyayya ba ta rayuwar aure a wannan rayuwa ta yanzu ba to lallai za mu yi ta a bayan Mutuwa saboda na yi imani cewa an halici ruhinmu da zukatan mu domin su so juna. Ina mai tabbatar maka da cewar idan ma mun mutu ba mu yi aure ba za a sake tashin mu a wani vangaren daban na duniya kuma sai mun haxu da juna mun yi aure kamar yadda Amzad ya mance da ni a yanzu, muna 83 BAYAN MUTUWA haxuwa ni ce zan shaida shi tunda ni ban tava mantawa da fuskarsa ba. Ruhina da ruhim Amzad ba za su tava rabuwa ba, lallai akwai RAYUWA BAYAN MUTUWA ni dashi” Ko da Gimbiya Lashmin ta zo nan a zancenta sai ta fashe da kuka ta faxa akan qirjin sarkin yaqi ta rungume shi. Nan take tausayinta ya turnuqeshi shima ya qanqameta a jikinsa yana mai kuka gami da rarrashinta. Sai da suka shafe tsawon ‘yan daqiqu suna manned a juna sannan sarkin yaqi ya janyeta daga cikin jikinsa ya dubeta yace. “Ya shugabata yanzu yaushene za ki nunawa Amzad wannan sarqa tasa domin ya tuno da duk abubuwan da suka faru a baya tsakaninki dashi ku kafa tubalin soyayyarku?” Koda jin wannan tambaya sai farin ciki ya lulluve Gimbiya Lashim ta qyalqyale da dariya daga can kuma sai ta nutsu tace. “Bazan nunawa Amzad wannan sarqaba sai bayan na kawar da babban maqiyinsa wato attajiri Huzulu, sai naga cewar duk dukiyar ta dawo hannunsa yana cikin daula da kwanciyar hankali a sannanne 84 BAYAN MUTUWA nima zan sami nutsuwa har na iya aza tubalin soyayyarmu na baiyana shi a fili kowa ya gani”. Koda jin wannan batun sai sarkin yaqi ya yi doguwar ajiyar zuciya sannan hawaye ya suvuce masa yace. ‘Na ji ajikina za ki iya samun nasara akan azzaluminnan attajiri Huzulu amma maganar Bokan mahaifinki tana yawo a cikin ruhina, zuciyata tana bugawa da qarfi tana tabbatar mini da cewar wannan tubalin soyayya naku ke da Amzad ba zai kai ga ginuwa ba, tabbas rushewa zai yi”. Koda jin haka sai Gimbiya Lashmin ta sake faxawa kan qirjin sarkin yaqi ta fashe da sabon matsanancin kuka sannan tace. “Ni ma na sha yin mugun mafarki akan haka, mummunan abinda nake gani a cikin mafarkin nawa bazan iya gaya maka shi ba, sai dai zan faxa maka wani daga cikinsa sauran kuma na barshi ya zama sirri a cikin zuciyata” Ta xan yi shiru na taqin lokaci tana kallon sarkin yaqi sannan ta ja numfashi tace masa. “Na tava yin wani mafarki bayan na kwanta barci na gani tare da ni da Amzad muna zaune a cikin wani lambu muna hira cikin tsananin soyayyar juna da kulawa, kwasam sai muka ga wani mahari ya kawo 85 BAYAN MUTUWA mana sumame ya na zuwa ya kawo wa Amzad sara da zumar cire masa kai amman bai samu nasarar yin haka ba sai ya kauce saran ya bi iska. Suka tsaya suka yi carko-carko kamar wasu zakaru suna kallon junansu, nima ganin haka ba qaramin xaga min hankali ya yi ba cikin sauri na miqe ina kallon wannan mahayin wanda ya rufe fuskarsa da qyale sai idanunsa kawai ake gani cikin tsawa nace masa. “Kai wane?” Ya xauke kai daga kaina yana kallon Amzad yace masa. “Ba ke na kawo wa hari ba, wannan baqin azzalumin masoyin na ki na kawo wa hari, kuma ba zan tava barinsa ba har sai na farauce rayuwarsa” Jin haka sai Amzad ya juyo a fusace yana kallonsa. “Kai wane?” Shima ya tambaye shi. “Masoyiyarka zata san ko ni wane bayan na halaka ka” Yana gama faxin haka sai ya sauko daga kan dokinsa ya yi xauki zuwa kan Amzad nan suka soma fafatawa ni kuma na tsana ina kallon yanda suke wannan faxan cikin tsananin fargaba da tsoron abinda ka iya faruwa akan masoyina. 86 BAYAN MUTUWA Ganin yadda wannan jarumin yake neman farauce rayuwar masoyina Amzad sai na suri wuqa nima na kai masa xauki, nan fa wani sabon gumurzu ya varke, shima mahayin ya zare wata takobi ya far mana da wani azababen faxan nasa mun xauki lokaci mai tsawo muna wannan azababen faxan kafin ya samu nasarar sarar Amzad a qirji nan take ya faxi qasa ganin haka ya xaga takobinsa sama da zumar suke shi, ina ganin haka na faxa kansa na bashi kariya nan take ya suka mini takobin ta huda qirjina ta volo ta shiga cikin jikin Amzad da wani murmushi na dubi Amzad nace mas. “Masoyina ba zan tava aminta ka riga ni mutuwa ba, zan so mu mutu a tare lokaci guda wannan shi ne cikar burin soyayya da qaunar juna” Shima ya yi murmushi. “Tabbas kin nuna min ke masoyiyace ta gaske wacce ba za a tava mancewa da ita ba, ina ma zan yi nisan kwana dana nuna wa duniya cewar mu masoyane waxanda ba a tava yin kamarsu ba, amman a yanzu hakan ma ina godiya ga abin bauta domin duk wanda ya samu tarihin wannan soyayyar tamu zai san lallai duk wajen da masoya suke mun kai”. 87 BAYAN MUTUWA Tana kawo nan ta yi shiru tana duban sarkin yaqi, wannan karon idanunta sun ciko da hawaye. Su duka suka yi shiru duk jikin sarkin yaqi ya gama yin sanyi a hankali Gimbiya Lashmin ta ce. “Idan har wannan mafarkin nawa ya faru da gaske to tabbas haka qaddararmu take ba za mu iya sauyawa ba, yakai sarkin yaqi ina neman alfarma guda a wajenka” Koda jin haka sai sarkin yaqi yai sauri ya janye jikinsa daga cikin na Gimbiya Lashmin ya dubet a cikin kaxuwa yace. ‘Ke kuwa wace irin alfarma kike nema a wajena?” Gimbiya Lashmin ta goge hawayenta sannan tace. ‘Idan har ni da masoyina Amzad mun mutu a lokaci guda to duk yadda za a yi kar ka bari a binne mu a kabari daban-daban, ka tabbatar da cewar an binnemu a cikin kabari guda kuma hannuna na daman a cikin hannunsa na dama wannan itace kaxai alfarmar da nake nema a wajenka. Ina son yanzu ka yi min alqawarin cika min wannan burin nawa” Koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa sarkin yaqi yace. 88 BAYAN MUTUWA ‘Kamar yadda na rinqa tsaron lafiyar mahaifinki da taki tsawon shekaru na yi alqawarin zan cika miki wannan burin naki indai na kai wannan lokacin amma ina fatan cewa ke da masoyinki ba za ku mutu ba harsai kunyi aure kun bar zuri’a tagari”. Dajine fetal iya ganin mutum wanda ke xauke da tsaunika,bishiyoyi da duhuwoyi masu ban tsoro. Shi dai wannan daji tazararsa da birnin misira ya kai tafiyar kwana goma sha shida.kuma fatakema sai sun haxa babbar runduna sanna suke iya ketawa saboda mugun fashin da ake yi a wajen. Kai tsaye wani mahayin doki ya ratsa farkon wannnan daji ya nausa cikinsa ba tare da wani jin tsoro ba tamkar yana tafiya a cikin harabar gidansa, abin tambayar shi ne shin ya san dajin kuwa ko kuwa yana da wata alaka da yan fashi dake cikin dajin? Haka dai wannan mahayin yaci gaba da kutsawa cikin dajin ba tsayawa ba waige har sai daya shafe sa’a uku yana tafiya a cikinsa yana kallon tsiran dabbobin daji msu gifta masa da kuma tsintsaye da kai komo a cikin 89 BAYAN MUTUWA sararin samaniya. Kwatsam sai yaga waxansu mutane suna faxowa kasa daga saman bishiya waxanda adadinsu ya kai xari kuma suna sanye da wani koren tufafi wanda ya saje da ganyen bishiyar wajen babu ta yadda za a yi mutum ya gane cewar akwai mutum a wajen. Nan da nan waxannan mayaqa suka yiwa mahayin qawanya. Nan take rabinsu suka zare kebiyoyi suka xana akan baka suka ritsashi, wasu kuma suka zare takubba. Bisa dole mahayin ya ja linzami dokinsa ya tsaya cak. Shugaban dakarun ya dube shi da kyau yace masa. “Waye kai kuma ina zakaje?” Ba tare da nuna wata alamar firgita ko tsoro ba mahayin ya yi murmushi yace. “Ni manzo attajiri Huzulu ne shi ne ya bani umarni na zo nan darul uzut na same shi a yau xinnan” Ko da jin haka sai gaba xaya dakarun suka mayar da makamansu sannnan suka koma gefe da gefe 90 BAYAN MUTUWA suka tsaya. Shi kuma shugabansu sai ya mayarwa da mahayin martanin murmushi sannan yace. “Biyoni a baya na kaika wajensa”Take ya juya suka sake nausawa cikin daji shi kuma mahayin ya sakarwa dokinsa linzami ya bishi a baya. Sai da suka wuce rukuni-rukuni bakwai na ‘yan fashi waxanda adadinsu ya kai mutum dubu-dubu kuma dukkansu a cikin shigar yaqi suke ga tarin makamai na yaqi kala-kala har da irin wanda mahayin bai tava gani ba sannan suka qaraso darul uzut. Darul uzut wata fadace wacce aka ginata da zallar dutsen wuta, girmanta yafi na gidan sarautar sarki sairan haka ma kayan qawa dana alatun dake cikinta sun ninka na gidan sarautar sarki sairan sau goma. Suna shiga cikin fadar suka isketa cike da barori da kuyangi mata iri-iri baqaqe da farare kyawawan gaske tamkar zavosu aka yi daga cikin matan duniya suna ta hidima da kai kawo. Abin haushi shi ne 91 BAYAN MUTUWA mutum biyu ne rak a cikin fadar kuma suna zaune akan karagar mulki baabba guda xaya an tara musu kayan ciye-ciye dana shaye-shaye iri-iri na alfarma babu kalar da babu. Ba waxansu bane waxannan mutanen biyu face Attajiri Huzulu da kuma sarkin varayi nahiyar gaba xaya wanda ake kira da suna Ranzalar. Koda Attajiri huzulu ya hango wannan mahayin an tsaida shi a farkon qofar shigowa fadar, wanda ya rakoshi ya kama dokin ya sauka ya juya baya sai ya miqe yana murmushi ya buxe baki yace “Lalle marhabun da makanu lallai ina farin ciki da isowarka akan lokaci, maza ka qaraso nan gareni” Koda jin haka sai makanu ya saki fuska cikin sauri ya qarasa wajen su Huzulu, koda ya rage sauran taku huxu ya qarasa wajen sai ya zube qasa ya kwashi gaisuwa. Huzulu ya taso da sauri ya rungume shi, sanan ya janye jikinsa daga cikin nasa kafin ya kama hannunsa ya ja shi zuwa wata kujera dake kusa da shi suka zauna. 92 BAYAN MUTUWA Faruwar hake ke da wuya sai matarnan suka kawowa makanu abinci da abinsha sama da kala ashirin suka ajiye a teburin dake gabansa. Nan fa makanu ya shiga cin abinci da abin sha har sai daya qoshi sannan ya sha ruwan inbi ya yi gyatsa. Ko da Attajiri Huzulu yaga makanu ya samu nutsuwa sai ya bushe da dariya yace “Yauwa yanzu lokaci ya yi daya kamata ka bamu labarin duk abinda yake faruwa a cikin gidan sarautar birnin misira da wajenta” Makanu ya yi gyaran murya gami da gyara zama yace. “A halin yanzu Gimbiya lashmin tasa ranar yanke maka hukunci a bisa guduwa da ka yi daga gidan kurkuku amma har yanzu shi sarki Raihan baisan cewar ka gudu ba, ka sani idan wannan ranar ta yanke maka hukunci ta zo kuma aka zarta da hukunci a fada to alqadarinka ya karye saboda a wannan ranar Gimbiya lashmin zata tona maka asiri ta faxi dukan laifukan da ka aikata a garin na sirri, hakan zai matuqar zubar maka da mutunci da kuma darajarka” 93 BAYAN MUTUWA Koda makanu ya zo wajenan a maganarsa sai jikin Attajiri Huzulu ya soma tsuma, zuciyarsa ta rinqa tafarfasa kamar zata qone. Cikin tsananin fushi ya miqe tsaye zumbur ya dakawa makanu tsawa yace “Rufe bakinka ko yanzu na zare takobi na sare maka kai” Cikin hanzari makanu ya sunkuyar da kanshi qasa ya tsuke bakinsa. Da ganin abinda ya faru sai sarkin varayi ya miqe tsaye da sauri ya kama kafaxar Attajiri Huzulu ya riqe yace. “Haba Attajiri Huzulu uban ma su kuxi, duk wani attajiri da ma su mulki a qarqashinka suke, jarumai da matsafa duka yaranka ne, akan wane dalili wata ‘yar qaramar qwaruwa zata tayar maka da hankali alhalin kaine uba kuma uwa ga duk wani mahaluki a wannan nahiyar gaba xaya, ai tunda wannan labarin ya zo garemu ba za mu tava barin mutuncinka da qimarka su zube ba. Dole mu ruguza duka shirye-shiryen Gimbiya Lashmin kafin wannan ranar ta zo wacce take son kaika qasa”. 94 BAYAN MUTUWA Sarkin varayi ya juya ya dubi makanu a lokacin da zuciyar Attajiri Huzulu ta xanyi sanyi yace “Ya kai makanu ina son ka sanar da ni yau sauran kwana nawa gimbiya Lashmin ya rage ta yankewa mai girma Attajiri Huzulu hukuncin qarshe a fadarta?” Makanu ya xago ya dubi sarkin varayi yace “Yau sauran kwana ashirin da xaya” Jin haka sarkin varayi ya yi murmushi sannan ya juya ya koma kan karagar ya zauna kusa da Attajiri Huzulu ya dubeshi yana mai dafa hannunsa yace. “Ai tayi kuskure data xauki dogon lokaci, ina mai tabbatar maka, nan da cikar sati xaya rak za mu kawo qarshen mulkin wannan yarinyar sannan kuma zamu kama mahaifinta da hannunmu mu kawoshi cikin kurkukun gidanmu mu voyeshi kai kuma ka xare karagarsa ka zauna”. Lokacin da sarkin varayi ya zo nan a maganarsa sai Attajiri Huzulu ya xan yi murmushi mai kama da yaqe yace “Faxar wannan qudurin a baki yana da sauqi amma ka sani aikata shi a aikace ba abune mai 95 BAYAN MUTUWA sauqi ba, ina mai tabbatar maka cewar wannan yarinya Lashin ta daxe tana tanayi akaina ba tun yanzu ba tun tana yarinya qarama, ban san da haka ba sai da bokayena suka yi bincike akanta suka gano haka, duk faxin nahiyar nan babu wanda yasan sirrrina sama da ita kuma ita kaxai tasan lagona wanda idan ta riqeshi to ta gama da ni, amma riqe wannan lagon nawa daidai yake data faxa cikin wutar data shekara tana ruruwa? Nima kuma yanzu na gano lagonta da shi kuma zan yi amfani na hanata ci gaba da aiwatar da mugun nufi akaina?” Cikin hanzari sarki varayi yace. “Mene ne lagonta? Kuma kaima mene naka lagon?” Sa’ar da attajiri Huzulu ya ji wannan tambayar sai ya qyalqyale da dariya sannan lokaci guda ya turvune fuska yace “Ya kai sarkin varayi mai fadar Darul uzur kayi sani cewar babban lagon gimbiya lashmin shi ne wannan yaron Amzad wanda take son ta karve dukiyarsa daga hannuna. Tun suna yara ita da shi ta kamu da tsananin sonsa sa’adda ya ceci rayuwarta amma sai sarki ya shiga tsakaninsu ya 96 BAYAN MUTUWA yiwa Amzad sihirin da ya manta da ita gaba xaya, kuskuren da sarki ya yi shi ne bai yiwa gimbiya lashmin irin asirin da ya yiwa Amzad ba don haka ita bata manta da shi ba don haka kullum a cikin begensa take dare da rana,matakin daya kamata na xauka shi ne na saka a sato Amzad yanzu a kawo shi nan, sannan na saka a sato wata sarqa ta musamman dake wajen gimbiya lashmin, ita dai wannan sarqa ta Amzad ce kuma ita kaxai

Chapter 4 of 6