ta riqa xagawa
Amzad hannu shima sai ya rinqa xaga mata hannu har
aka hau kan doki da ita aka ruga da gudu suka qule ya
daina hangota, a sannan ne mahaifin Amzad ya kama
hannunsa ya jashi suka nausa cikin birni.
47
BAYAN MUTUWA
A lokacin da sarki salhan ya zo nan a
tunaninsa sai hawaye ya zubo masa ya dubi Gimbiya
Lashmin yace.
“Yanzu ashe tun daga wannan ranar da
Amzad ya ceci rayuwarki kika kamu da son shi?”
koda jin wannan tambayar sai itama Gimbiya Lashmin
ta zubar da hawaye sannan ta zura hannu aljihun
rigarta ta fiddo wannan sarqa ta Amzad ta nunawa
sarki tace.
“Qwarai kuwa tsawon waxannan shekarun
ina ajiye da sarqa Amzad kuma ina begensa a cikin
zuciyata dare da rana. Tambayar da nake son na yi
maka mene ne ya hana Amzad zuwa wajen da nake ya
karvi sarqarsa dake hannuna? Mene ne dalilin daya
saka duk sa’adda nace kasa aje a nemo Amzad da
mahaifinsa sai kace har izuwa tsawon waxannan
shekarun kace an halaka shi, nima kuma ka saka aka
tsare ni a cikin gidan sarauta baka barina na fita sai da
sharaxin wajen da zani nan xin zanje, ka hanani
samun sakewa da zan yi bincike akan sa har zuwa
girmana.
Tabbas ka jefani a cikin kurkukun soyayya
wanda yafi rijiya gaba dubu, ka sanya min xaci a
zuciya wanda yafi azabar fitar rai, kuma ka dusashe
48
BAYAN MUTUWA
min hasken idanu da baqin ciki da yafi dare duhu,
tsawon shekaru sha xaya kenan ban ga masoyina ba
Amzad rabona da shi tun ina da shekaru bakwai a
duniya sai yau da aka gurfanar dashi a gabana domin
na yi masa shari’a da azzalumin attajiri Huzulu.
To ka sani ko ka bani amsar tambayoyina ko
kaqi a yau xinnan sai naje na baiwa Amzad sarqarsa
wacce na cire a wuyansa tun muna yara a ranar day a
ceci rayuwata. Ko kana so ko baka so yakai Abbana
sai na cika alqawarina a gareshi na bashi abin da yafi
komai daraja a wajena kuma ba komaibane face
soyayyata da kuma aurena”.
Lokacin da Gimbiya Lashmin ta zo nan a
zancenta sai shima sarki sairan ya ji hawaye sun
suvuce masa don haka sai ya kamo Gimbiya Lashmin
ya rungumeta a qirjinsa yana kuka yace.
“Ki gafarta min yake ‘yarta kiyi sani cewa
akwai dalili mai qarfi wanda yasa na raba rayuwarki
da Amzad xan Nazmir waxanda suka ceto rayuwarmu
a tare kuma a lokaci guda, dalili kuwa shi ne bayan
anyi mana magani ni da sarkin yaqi wato an cire
kibiyoyin dake jikinmu an sa mana magani don kashe
dafin kibiyar sai kawai muka ga bokana wato Darzas
ya baiyana tsulum a gabanmu.
49
BAYAN MUTUWA
Boka Darzas ya dubeni cikin damuwa yace
“Ya shugabana kayi sani cewar ba wani bane ya turo
dakarun sumame su kasheka ba face sarki zardar na
birnin mailus, kuma munafikin da ya sanar da su
cewar zaka fita yawon rangaxi ba wani bane face
bawanka yunus mai kula da dawakanka na hawa,
musamman sarki mailas ya siyar da shi izuwa fa
farakenku suka zo dashi nan qasar,kai kuma ka siye
shi a matsayin bawa har ka aminta da shi, saboda
qwazon shi a wajen aiki da qwarewarsa wajen kiwon
dawakai.ban gano wannan sirrin ba sai yanzu da zan
zo wajenka na yi bincike akan kawo wannan harin.
Abu na gaba da zan sanar maka kar ka sake
kabar wata alaqa ta soyayya ta qulu a tsakanin
Gimbiya Lashmin da Amzad xan Nazmir waxanda
suka ceci rayuwarka xa zu a qofar birninnan daga
hannun dakarun sumame, domin bincike ya nuna ba
za su tava zama abokan rayuwar juna ba, kuma
qarshen soyayyar tasu tana qunshe da baqin ciki a
gare su da duk masoyansu” Boka Darzas yana gama
faxin haka sai ya vace vat.
50
BAYAN MUTUWA
S
arki Salhan ya dubi Gimbiya Lashmin
ya ci gaba da magana “Bisa wannan
dalilin tun daga wannan ranar na
sanya hijabi a tsakaninki da Amzad har mahaifinsa ya
rasu ban bari kun sake ganin junaba. Ki yafe min yake
‘yarta, lallai ki yafe min na yi miki babban laifi amma
son da nake miki ne gami da son ganin kyakkyawar
rayuwarki a gaba yasa na yanke wannan hukunci”.
koda sarki salhan ya zo nan a zancensa sai
Gimbiya Lashmin ta fashe da matsanancin kuka,
al’amarin daya karya zukatan iyayenta kenan suka
kamu da tsananin tausayinta.
Don haka sai mahaifiyarta ta janyota ta
rungumeta a kan qirjinta tana mai rarrashinta tana bata
baki har izuwa tsawon ‘yan daqiqai amma bata daina
kukan ba, daga can sai Lashmin ta janye jikinta daga
cikin na mahaifiyarta ta miqe tsaye ta dubi sarqa tace.
“Ya kai Abbana kayi sani cewar babu wani
qarfi wanda ya isa ya dates so na gaskiya a tsakanin
masoya,addini ko sihiri, dukiya ko talauci,wuya da
daxi basa raba masoya sai dai mutuwa da qaddara. ni
banyi imani da dukkan abinda bokayen ku ke faxaba
muddin ya shafi soyayyata, idan kuma har abinda suka
faxa ya zama gaskiya to na yarda na mutu akan qirjin
51
BAYAN MUTUWA
masoyina domin shi ne abinda ya fiye min komai farin
ciki a rayuwata” koda gama faxin haka sai Gimbiya
Lashmin ta miqe tsaye da sauri ta juya ta fice daga
cikin turakar mahaifiyarta na kwala mata kira amman
ko waigowa ba.
Koda ganin haka sai mahaifiyar tata ta miqe
da sauri da nufin taje ta ruqo ta amman sai sarki ya yi
wuf ya runqota ya dakatar da ita yace mata.
“Kar ki kuskura ki dakatar da zuciyarta da
take ruruwa da wutar soyayya, domin daidai take da
mahaukacin zakin da ya fusata a cikin daji a lokacin
da yake fama da tsananin yunwa,kinsa cewa idanunta
a rufe suke zai iya banke kowa” Koda jin wannan
batun sai mahaifiyar Lashmin ta koma ta zauna kusa
dashi ta xora kanta akan qirjinsa a lokacin da hawaye
ya zubo mata shi kuma ya qanqameta a jikinsa tana
mai cewa.
“Haqiqa ‘ya tayi gadon ubanta akan zafin
soyayya ko kuwa ka mance ne da yadda muka mallaki
junanmu, mun sha baqar wahala da gwagwarmaya?”
koda jin wannan batu sai hawaye ya suvutowa sarki
salhan yace.
“Zan iya mancewa da komai na rayuwata
amma ba zan iya mancewa da tarihin soyayyata ba
52
BAYAN MUTUWA
yake matata, a duniya banga abin da yafi soyayya daxi
da haxari ba, kuma babban kuskure da mutum zai yi a
rayuwarsa shi ne yace zai shiga tsakanin masoya”
Koda jin wannan batun sai hankalin mahaifiyar
Lashmin ya dugunzuma ainun ta janye jikinta daga na
sarki suka fuskanci juna ta dubeshi cikin alamun
tsananin damuwa tace.
“Wai shin yanzu kana nufin kenan zaka
kyale Lashmin ta yi soyayya da Amzad xan Nazmir
alhalin kasan cewar qarshen soyayyar tasu mummun
qarshe ne da mugun baqin ciki?” Koda jin wannan
tambayar sai hawaye ya sake suvuce wa sarki sairan
yace.
“Y azan yi da qaddara? ko na bar Gimbiya
ko na hanata saduwa da Amzad ba zan iya cire son sa
ba daga zuciyarta, idan kuwa akwai sonsa a ranta idan
muka matsa akan rabu su za mu iya rasata gaba xaya,
wanne za mu zava a ciki yanzu? Ni dake muna son
farin cikinta a yanzu idan muka hanata kuma a qarshe
mu rasata ko kuwa mu barta ta mutu a cikin farin ciki.
Shi kansa mahaifin Amzad yasan da wannan
matsalar tun kafin ya rasu kuma mahaifiyarsa ma ta
sani,bisa wannan dalilin suka nemi taimakon boka
marigayi zardash ya saka Amzad ya mance da duk
53
BAYAN MUTUWA
abinda ya faru tsakaninsa da Lashmin a wannan
lokacin da suke yara amman ya tabbatar mana da cewa
duk ranar da yaga wannan sarqa tasa wacce Lashmin
ta cire a wuyansa to sai ya tuna da komai” Koda jin
wannan batu sai hankalin mahaifiyar Lashmin ya
dugunzuma ainun fiye da koyaushe ta kamu da
tsananin baqin ciki kuma ta fashe da matsanancin
kuka tana mai cewa.
“Mene ne dalilin daya sa tuntuni baka sanar
da ni wannan sirrinba, lallai inda nasan dashi da sai
nasan hanyar da na bi nasa Gimbiya ta manta da
Amzad kuma da sai nasa ta yi aure domin mu ga jikan
mu da idanuwa kafin mutuwarmu amma yanzu baqin
alwalami ya gama bushewa domin wannan burin na
mu ba zai tava cika ba” Koda jin wannan batun sai
sarki salhan ya sake kamo matar tasa ya rungumeta a
kan qirjinsa suka fashe da kuka a tare.
Komai rashin tausayin zuciyar mutum idan
ya dubi waxannan ma’aurata a wannan lokacin da
suke yin wannan kuka na takaici da baqin ciki dolene
ya kamu da tsananin tausayinsu ba zai san sa’adda
shima zai zubar da hawaye ba. Wannan shi ne abinda
ya faru tsakanin Gimbiya Lashmin da iyayenta a can
gidan sarauta.
54
BAYAN MUTUWA
Al’amarin Amzad kuwa lokacin da
mataimakin sarkin yaqi tare da dakarunsa suka tafi das
hi izuwa can gidan sarki na bayan gari sai kansa ya
xaure kuma mamaki da wasi-wasi suka turnuqeshi,
abu na farko daya fara tambayar kansa shi ne wai shin
mene ne dalilin da yasa sarki ya sauka daga kan
karagarsa ya baiwa ‘yarsa Gimbiya Lashmin hart a
kwato masa ‘yancinsa alhalin a tsawon shekaru baya
sarki ya kasa yi masa wannan taimakon.
Amzad ya sani cewa mahaifinsa gagarumin
attajirine domin ya mutu ya bar dukiya mai tsananin
yawan da babu mai kamarta a gaba xaya birnin misra
amma bayan mutuwar tasa ne shi da mahaifiyarsa
suka faxa cikin tarkon attajiri Huzulu har ya zamana
cewa sun rasa komai nasu suka zama talakawan da
suka fi kowa babu domin da qyar da sixin goshi
Amzad ya tsira da jaki guda xaya wanda yake sana’ar
dakon tubalin gini dashi.
Da hakane yake samo abinda za su ci abinci
shi da mahaifiyarsa, sai dai ta kai basu da gidan kwana
kuma basu da komai basu da kowa face jakin nasa
guda xaya.
55
BAYAN MUTUWA
Komai zafi komai sanyi sai dai su rakave a
kangwaye ko rusashen gida su kwana, sau tari idan zai
tafi sana’arsa ta dako sai dai yakai mahaifiyarsa ajiya
izuwa maqotansu,inya dawo sai ya zo ya xauketa akan
jakinsa su tafi inda za su kwana.
Kullum haka suke yin wannan rayuwa cikin
qunci, talauci da matsanancin baqin ciki, a duk
sa’adda mahaifiyarsa ta tuno da irin daular da suke
ciki sa’adda mahaifinsa ke raye sai tayi ta kuka tana
tsinnewa attajiri Huzulu.
Da qyar Amzad ke rarashinta yana gaya
mata maganganu masu daxi domin hankalinta ya
kwanta.
Abu na biyu daya jefa Amzad cikin tsananin
mamaki shi ne wannan kallon da Gimbiya Lashmin ta
yi masa a lokacin da zai fita daga cikin fada. Shi dai a
rayuwarsa babu waya ‘ya mace data tava yi masa
irinsa face Gimbiya Lashmin. Kallo ne wanda indai
aka yiwa mutum sai ya tabbatar da cewa akwai qauna
ga wanda yayi masa akan wane dalili Gimbiya zata so
ni ina matsayin talaka fitik wanda bai shafi jinin
sarauta ba.
Ai ko a mafarki soyayya ba zata qullu a
tsakanin mu ba, domin qwarya sai dai tabi qwarya,
56
BAYAN MUTUWA
dan tabi akwashi kuwa fashewa zata yi. Haka dai
Amzad ya yi ta wannan tunanin gami da saukar da
ajiyar zuciya, a haka har suka iso wannan gidan na
sarki salhan dake can bayan gari. Kai tsaye
mataimakin sarkin yaqi ya shige dashi har can cikin
gidan.
Suna isa babban falo na gidan sai Amzad ya
hango mahaifiyarsa zaune bisa teburin cin abinci an
cava mata ado da tufafi na isa sannan ga abinci kalakala irin na manyan attajirai da sarakai a gabanta,
kuyangi na zuba mata dukanin kalar abinci da take so
tana ci cikin tsananin farin ciki.
Yanayin tafiyar Amzad kawai mahaifiyar
tasa taji sai ta miqe tsaye cikin murna ta buxe
hannayenta tana mai cewa.
“Taho gareni ya kai xana, zo ka bani labari
wane gaggarumin aiki ka yi ga sarki wanda ya saka
har aka bamu wannan daular?” Cikin tsananin farin
ciki Amzad ya qarasa wajen mahaifiyar tasa ya
rungumeta sannan ya zaunar da ita akan kujerar da
take zaune da.
A sannan ne mataimakin sarkin yaqi ya
sallami gaba xaya kuyangin dake wajen suka fice daga
falon suka barsu su uku kacal. Kafin Amzad ya buxe
57
BAYAN MUTUWA
baki ya baiwa mahaifiyar tasa amsar tambayarta sai
mataimakin sarkin yaqin ya tari numfashinsa yace.
“Yake ummul Amzad kiyi sani cewa Allah
ne ya dube ku ya yi muku rahama bisa tsohon
zalluncin da aka yi muku na tsawon shekaru, a yau ne
‘yar sarki Gimbiya Lashmin ta karvi aro karagar sarki
saboda shi bashi da lafiya, a yau xin ta saka aka fito
da duk takardun shari’oin da ake kawowa fada ta
dubasu amma sai ya zavo taku shari’ar kacal ta saka
aka kirawo attajiri Huzulu tare da xanki Amzad aka
gabatar da shari’ar a gaban mutanen fada.
A yanzu haka maganar da nake yi miki
Gimbiya tasa an aika da attajiri Huzulu kurkuku an
tsareshi kuma za a ci gaba da bincike har a gano
gaskiyarku a karve duk dukiyar ku dake hannunsa a
dawo muku da ita” Koda mataimakin sarkin yaqi ya
zo nan a jawabinsa sai mahaifiyar Amzad ta kamu da
tsananin farin ciki bata san sa’adda ta fashe da kuka ba,
kuma tayi suvutar baki tace.
“Yanzu ashe dama akwai ranar da ‘yar sarki
zata tuno da halaccin da muka yi mata?” koda jin
wannan batu sai mamaki ya turniqe Amzad ya dubi
mahaifiyar tasa yace.
58
BAYAN MUTUWA
“Yake Umma wane irin halacci ne muka
yiwa Gimbiya Lashmin?” koda jin wannan tambayar
sai tayi saurin ta wayance tace.
“Aa ina nufin nace dama sarki zai tuno da
irin biyayyar da mahaifinka yayi masa a rayuwa, ai a
lokacin da mahaifinka yana raye yayi hidima da
dukiyarsa a gidan sarauta sosai don haka na yi
mamakin yadda aka yi sarki ya mance da bayansa yaqi
ya neme mu ya taimaka mana” Koda jin wannan batu
sai Amzad ya yi murmushi yace.
“Haba yake umma, in banda abinki kuma ai
su masu mulki suna da yawan mantuwa, sannan kuma
kinsan ance ba a mugun sarki sai mugun bafade ai
makusantansu ne suke hanasu yin aikin alheri. Wata
qila yana son ya taimaka mana koma yana aiko mana
da taimakon fadawansa na dannewa bamu sani ba”.
Koda jin haka sai mataimakin sarkin yaqi
yace.
“Qwarai kuwa ai abin dake faruwa kenan”
Amzad yace.
59
BAYAN MUTUWA
BAYAN MUTUWA
5
‘To amma mene ne dalilin dayasa duk a
tsawon shekarunnan ko sau xaya sarki bai tuno da
shari’armu bad a attajiri Huzulu sai a yau rana xaya da
‘yarsa ta hau karagar mulki ta tuno damu kuma har
tayi mana wannan gagarumin taimako tamkar muna
binta bashin wani abu a rayuwa? Alhalin bata ma san
mahaifina ba bata irin gudumawar daya basu” Koda
jin wannan tambayar sai mataimakin sarkin yaqi ya yi
caraf yace.
“Ai kasan babu mamaki shi sarki baya son
ya vatawa fadawansa shi yasa ya kasa yin komai akan
wannan shari’a taku tsawon shekarun da aka xiba
musamman tunda duk manya fadawansa yaran attajiri
Huzulu ne amma ai ita Gimbiya Lashmin babu
ruwanta da fadawan sarki tunda yarinyace, duk abinda
ya zo mata a cikin rai shi zata aiwatar”.
Koda jin haka sai mahaifiyar Amzad ta
gyaxa kai tace.
“Na yarda da maganar ka” Nan take
mataimakin sarkin yaqi ya miqe tsaye ya dubi Amzad
yace masa.
60
BAYAN MUTUWA
“Ni zan koma wajen dakaru domin na daxa
tabbatar da tsaro kamar yadda aka uwarceni, ina son
ku saki jikinku kuji daxinku duk abinda kuke buqata
akwaishi a cikin gidannan kawai ku tambayi kuyangi”
Amzad ya yi murmushi gami da godiya ga
mataimakin sarkin yaqi shi kuma sai yace.
“Ai bani za ka yiwa godiya ba face Gimbiya
Lashmin kuma kusani cewa a koyaushe zata iya kawo
muku ziyara ba zato” Koda jin haka sai Amzad ya
dube shi cike da mamaki yace.
“Haba ya za a yi Gimbiya Lashmin ta zo nan
saboda mu kawai” Mataimakin sarkin yaqi ya yi xan
guntun murmushi yace.
“Baka yi mamakin yanda ta wulaqanta
attajiri Huzulu ba saboda kai sai zuwanta nan? Ina yi
muku sallama kuyi barci mai daxi sai da safe” Koda
gama faxin hakan sai mataimakin sarkin yaqi ya juya
ya fice daga cikin falon ya bar Amzad da mahaifiyarsa
nan dai suka qarasa cin abinci nasu.
Suna gamawa sai kuyangi suka kawo musu
ruwa da qyalle mai kyau suka wanke hannayensu suka
goge danshin hannunsu. A sannan ne xaya daga cikin
kuyangin ta dubesu tace.
61
BAYAN MUTUWA
“Yanzu zan sa a raka ku izuwa xakin barcin
kowannanku” Koda jin haka sai Amzad yace.
“Aa kada ku rabani da mahaifiyata, ban tava
kwana ba tare da ita ba” Koda jin haka sai gaba xaya
kuyangin suka bushe da dariya, babbar cikin su wacce
ta fara magana da farko ta dubeshi cikin mamaki tace.
“Yanzu kai da girma nan naka kana
cikakken saurayi amma baka tava rabuwa da
shimfixar mahaifiyar ka ba, sai kace wani qaramin
yaro?” Amzad ya gyaxa kai cikin murmushi yace.
“Qwarai kuwa domin bani da kowa a cikin
wannan duniya face wannan mahaifiyar tawa, bani da
uwa bani da uba maraya na taso, bani da damuwa ko
‘yar uwa kuma ban tava yin aboki ba ko qawa. Bani
da budurwa ta yaya kike tsammanin zan iya rabuwa da
uwata a dare xaya alhalin tun sa’adda take dauke da
cikina muke tare kawo i yanzu?” koda Amzad ya zo
nan a zancensa sai jikin gaba xayan kuyangin ya yi
sanyi suka kamu da tsananin mamakinsa gami da
tausayinsa cikin qaramar murya shugabar kuyangin ta
dubi wata daga cikinsu tace.
“Maza ki kai su babban xakin barci na
gidannan, haqiqa raba wannan uwa da xanta ba
qaramin aiki bane” Nan take aka yiwa Amzad da
62
BAYAN MUTUWA
mahaifiyarsa jagora izuwa cikin wani qaton xakin
barci maixauke da wani shimfixexen luntsumemen
gado wanda yasha shimfixu masu taushi gami da
qaton bargo da kuma matasan kai guda huxu.
Da yake lokaci ne na sanyi sai Amzad ya
kama mahaifiyarsa ya kwantar da ita akan gadon
sannan shima ya kwanta a kusa da ita ya janyo qaton
bargon ya lulluve jikinsu gaba xaya.
Koda mahaifiyar tasa taji tsananin taushin
katifar da suke kwance akai kuma taji xumin qaton
bargon da suke lulluve das hi sai ta kama kuka tace.
“Yakai xana ka yi sani cewa a rayuwata ban
tava zaton cewa za mu sake tsintar kanmu a cikin irin
wannan daular ba wacce rabon mu da ita tsawon
shekaru ashirin da biyar kenan tun kafin ka zo wannan
duniya lokacin da mahaifinka ke raye” koda jin
wannan batu sai hawaye ya zubowa Amzad yace.
‘Yake Ummina na so ace kina gani da
idanunki domin kiga irin hawayen farincikin dake
zubo akan kumatuna kuma kiga irin kayan alatun dake
cikin gidannan, ki tuna cewa munsha kwana a kasa
bisa tabarma kuma a filin Allah inda ruwa da iska ke
qarewa a kan mu amman yau gamu a cikin qereren
63
BAYAN MUTUWA
gida na kwatance bisa gado na alfarma kuma munci
irin abinci da sai mai isane ke cinsa.
Wai shin da me za mu iya sakawa wannan
‘yar sarki?” koda jin wannan tambayar sai hankalin
Mahaifiyar tasa ya dugunzuma ta rasa abinda za ta ce
masa, kawai sai tace ai.
“ Kawai sai dai muce Allah ya saka masa da
alheri” ta xan yi shiru taci gaba da cewa da shi.
‘Kai kar ka cikani da tambaya ka hanani
barci akan wannan daddaxan gado sai da safe” Tana
gama faxin hakan sai ta sake jan bargo ta lulluve
fuskarta gaba xaua ko da ganin haka sai shima Amzad
ya lulluve fuskarsa nan danan kawai barci ya sacesu
ba tare da sun sani ba.
Al’amarin sarkin yaqi kuwa lokacin da ya
tafi da attajiri Huzulu izuwa can babban kurkuku na
birnin Misra basu fuskanci wata matsala ba babu wani
hari da aka kai musu har suka isa kurkuku.
Da zuwan su sai sarkin yaqi ya isar da saqon
gimbiya Lashmin izuwa ga shugaban masu gadin
kurkukun cikin biyayya shugaban wani narkeken qato
mai qirar mutanen farko ya risina ga sarkin yaqi cikin
biyayya yace,
64
BAYAN MUTUWA
‘An gama ya shugabana” Nan take aka saka
wasu masu gadin kurkukun subiyo suka karvi attajiri
Huzulu daga hannun dakarun sarkin yaqi aka zuba
masa sarqi a hannunsa da kafafunsa kawai sai suka ji
attajiri Hauzulu ya taqarqare ya bushe da dariyar
mugunta, al’amarin da ya yi matuqar baiwa sarkin
yaqi tsoro da mamaki kenan.
Daga can attajiri Huzulu ya murtuke fuska
ya dubi sarkin yaqi yace masa.
“Wannan gidan da kuka kawoni ji nake
kamar a cikin gidana kuka kawoni, na rantse da
darajar iyayena da kuma darajar abin bautarmu kana
barin nan da tazarar sa’a xaya jal za a zo a fitar da ni
daga cikin wannan kurkukun”.
D
aga can sai attajiri Huzulu ya murtuke
fuskarsa ya dubi sarkin yaqi yace
“Wannan gidan da kuka kawoni ji
nake kamar a cikin gidana nake. Na
rantse da darajar iyayena da kuma darajar abin
bautarmu kana barin nan da tazarar sa’a xaya jal za’a
zo a fitar da ni daga cikin wannan kurkuku” Ya xan yi
65
BAYAN MUTUWA
shiru na wani xan lokaci yana kallonsa sannan ya ci
gaba da magana cikin izza.
“Ga saqo kaje ka gayawa Gimbiya kace da ita
ni attajiri Huzulu na rantse da jinin uwata da ubana ita
bata isa ta iya tozartani ba a cikin wannan duniyar, ka
yaga mata cewa na gaba ya yi gaba na baya sai labari.
Sannan ka shaida mata cewa lallai ta tabbatar
da cewar ta mori jin daxin wannan mulki da take kai a
iya tsawon ‘yan kwanakin da sarki ya ara mata domin
kwanakin na qarewa zata zama baiwata, domin misra
gaba xaya zata zama tawa.
Saqo na qarshe a gareta ka gaya mata cewa
wannan wulaqancin da tayi mini saboda tsohon
masoyinta tun quruciya ta yi shi a banza domin bazata
iya karve dukiyarsa dake hannuna ba ta damqa masa,
kuma har abada ita da shi ba za su tava zama abokan
rayuwa ba” Koda attajiri Huzulu ya zo nan a zancensa
sai sarkin yaqi ya fusata ainun ya gabza masa naushi a
fuska.
Saboda qarfin naushin sai da attajiri Huzulu
ya faxi qasa jini ya furzo waje daga bakinsa. Attajiri
Huzulu ya miqe tsaye ya shafa bakinsa yaga jini kawai
sai ya sake bushewa da dariya sannan yace.
66
BAYAN MUTUWA
“Kayi babbar nasara hard a ka samu ka naushi
babban maqiyinka. Yau zan sanar dakai babban sirrin
da baka sani ba, ni ne na kashe ubanka domin na
sauya tsarin gidan sarauta mu saboda shi ne kaxai
baya bani haxin kai a cikin ‘yan majalisar sarki” Koda
jin wannan batu sai sarkin yaqi ya daddage ya kurma
ihu kuma ya zare takobinsa ya xagata sama ya kaiwa
attajiri Huzulu sara amma sai shugaban kurkukun ya
yi wuf ya zare tasa takobin ya kare saran ya dube shi a
fusace yace.
“Ai yanzu baka da sauran iko akan wannan
fursuna face mun sami umarni daga wajen sarki ko
Gimbiya” Koda jin wannan batu sai sarkin yaqi ya
kamu da tsananin baqin ciki gami da takaici domin
inda yasan cewa attajiri Huzulu ne ya kashe masa
mahaifinsa da tun xa zu akan hanya zai kashe shi sai
dai ya fuskanci kowane irin hukunci daga wajen sarki.
Cikin tsananin fushi sarkin yaqi ya dakawa
shugaban dakarun gidan kurkukun tsawa yace.
“Ka bani attajiri Huzulu na kashe shi yanzu
take anan ko kuma kai na yaqeqa na kasheka” Koda
jin haka sai gaba xaya Dakarun dake tsaron kurkukun
suka rugo da gudu izuwa bayan shugaban nasu suka
67
BAYAN MUTUWA
zazzare takubbansu sai gashi sarkin yaqi da dukkan
dakarunsa sun zama ‘yan kaxan a cikinsu.
Attajiri Huzulu ya sake bushewa da dariyar
mugunta a karo na biyu ya dubi sarkin yaqi yace masa.
“Kai yaro ni murucin kan dutse ne ban fito ba
sai dana shirya. Bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane.
Kaje ka rungumi qaddara ka qarasa rayuwarka a
matsayin bawan sarki idan kuwa kace zaka tavo
tsuliyar dodo wanda a halin yanzu barci ya keyi, tofa
idan ya farka sunanka gawa” koda gama faxin hakan
sai attajiri Huzulu ya dubi wannan narkeken qato wato
shugaban Dakarun kurkukun yace.
“Yakai mandazi maza kasa a kaini xakina” Ba
tare da wata gardama ba kuwa mandazi yasa aka
kwance sarqoqin dake jikin hannun attajiri Huzulu da
qafafunsa aka ruke hannayensa aka tafi dashi, su kuwa
su sarkin yaqi sai aka ritsasu da makamai har sai da
aka ga sun juya sun fice daga cikin kurkukun gaba
xaya sannan aka rabu dasu aka maida qofa aka rufe.
Nan fa baqin ciki ya turnuke sarkin yaqi ya
dubi gaba xaya yaransa yace “Haqiqa birnin misra
bata sarki bace, ta attajiri Huzulu ce, Gimbiya ba zata
iya yaqi da attajiri Huzulu ba tunda sarki ya kasa, mu
qalilan ne a cikin wannan masarautar bama tare da
68
BAYAN MUTUWA
Huzulu, duk abinda ya faxa sai ya faru, tabbas nan da
cikar sa’a guda za a fitar da shi daga cikin wannan
kurkuku” Koda jin wannan batun sai xaya daga cikin
yaran nasa ya dube shi yace.
“Haba ya shugabana ta yaya za a iya zuwa a
fitar da attajiri Huzulu daga cikin wannan kurkuku
mai tsananin tsaro haka alhalin sama da shekaru xari
baya ba a tava samun fursunan daya tava guduwa ba
daga cikinsa?” Koda jin wannan batun sai sarkin yaqi
ya jinjina kai yace.
“Ai kuwa yau za ka ga abin mamaki da
idanunka, lallai abinda bai tava faruwa ba a qasarnan
yau zai faru, yanzu abinda zai faru za mu samu waje
mu voye mu zuba idanu muyi kallo kawai” Koda
gama faxin haka sai sarkin yaqi yaja gaba xayan
dakarunsa suka ruga izuwa can saman wani tsauni
dake can nesa kaxan da inda kurkukun yake suka
kwanta.
Da yake akwai tarin bishiyoyi masu duhuwa
akan tsaunin kuma gashi darene babu yadda za a iya
mutum ya gane cewa akwai mutum a saman tsaunin.
Haka dai su sarkin yaqi suka ci gaba da lamvo
akan tsaunin har tsawon sa a guda basu ga wani abu
ya faru ba, har sarkin yaqi ya yunqura zai tashi tsaye
69
BAYAN MUTUWA
sai kawai ya hango wasu xaruruwan waxansu manya
aljanu a can qololuwar sama sun tun karo wannan
kurkukun tun da sarkin yaqi da dakarunsa suka zo
duniya ba su tava ganin aljanu masu tsananin girma da
muni irin su ba.
Nan take wasu daga cikin yaran sarkin yaqi
suka zube a sume,wasu suka haukace, shi kansa sarkin
yaqi ba don yana da qarfin sihirin tsafiba da nan take
zai haukace shima.
70
BAYAN MUTUWA
**
Kai tsaye jibga-jibgan aljanun suka duro qasa
bisa turba a tsakiyar kurkukun. Duk badakaren daya
sha gabansu da nufin ya yaqesu sai dai aga naman
jikinsa ya zagwanye ya zama kwarangwal,sutural
jikinsa ce kaxai take ragewa zube a qasa.
Al’amarin daya razana dukkanin dakarun
kurkukun kenan suka rinqa rugawa da gudu suna vuya,
kai bama dakarun kurkukun ba hatta fursunoni vuya
suka rinqa yi duk da cewa sun sami damar guduwa
saboda tsoron yin arba da waxannan mugayen aljanun.
Ko bango aljanun suka dosa sai dai kaga
yarushe ya zube qasa, qofar qarfe kuwa narkewa take
ta zama ruwa. Shugaban Dakarun kurkukun kuwa
wato mandazi da hannunsa ya buxe xakin da attajiri
Huzulu ke ciki ya fito das hi ya damqawa aljanun.
Ba tare da attajirin Huzulu ya yi wata razana
ba kawai sai ya nufi