An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
BAYAN MUTUWA
BAYAN MUTUWA
Abdul-aziz Madakin Gini
1
BAYAN MUTUWA
HAKKIN MALLAKA
2022
BUGU NA BIYU
2023
Bugu na uku
2024
2
BAYAN MUTUWA
Bayan mutuwa
K
wance take akan luntsumeman gado
irin na su na sarakuna tana ta faman
sharar barci tamkar wata gawa, ko
alamar tashi bata da niya, kallo xaya za ka yi mata a
cikin rigar barcin da take sanye kasan Allah ya yi
baiwarsa domin indai batu na kyau ne bata da tsara a
nahiyar gaba xaya.
Gimbiya lashmin ta kasance doguwar mace
mai matsakaicin kaurin jiki,qirjinta a cike yake kuma
tana da tudun baya, wuyanta dogo ne, tana da daradaran idanuwa gami da siririn dogon hanci, bakinta
xan qarami ne kamar an yanka da wuqa mai xauke da
lava masu tashin gaske.
A yanzu haka da take kwance tana barci
fuskarta cike take da annuri gamida wani irin
murmushi irin wanda ka iya sabauta duk xa namiji
daya haxa idanu da ita.
3
BAYAN MUTUWA
A wannan lokacin gari yaw aye har hasken
rana ya hudo ta cikin tagar xakin, gaba xaya
kuyanginta na tsaitsaye zagaye da gadon da take
kwance suna son su tasheta daga barci amma tsoro ya
hanasu duk da cewar kuwa mahaifiyar Lashmin xince
ta bayar da umarnin a rinka tashinta daga barcin a
daidai irin wannan lokacin. Ba komai ne yasa
kuyangin suke tsoron Gimbiya Lashmin ba face ita a
rayuwarta ta tsani ayi mata bauta tafi son tayi komai
da kanta.
Sarauta da kuma daular data ke ciki ko
kaxan bata dameta ba, inda son ranta ne tafi son tayi
rayuwa irin ta sauran talakawan gari, kai inda za a
qyaleta zata iya barin birinsu na Basra ta tafi can wani
garin inda ba a santa ba tayi sabuwar rayuwa cikin
qasqanci ba tare da wani yasan matsayinta ba.
Kuyangin na tsaitsaye cikin halin tsananin
tsoro da damuwa saboda gudun kada su yi laifi biyu.
Laifin na farko shi ne basu bi umarnin mahaifiyar
Lashmin ba sun tashe ta daga barci. Laifi na biyu
kuma suna tsoron karya dokar Gimbiya Lashmin ta
cewar kada wanda ya sake tashinta daga barci har sai
ta farka da kanta.
4
BAYAN MUTUWA
Kwatsam sai suka ga Gimbiya Lashmin ta yi
juyi akan gadon kuma ta miqe zaune zumbur daga
kwance kamar wadda ta farka daga mugun mafarki.
Koda taga kuyanginta a tsaitsaiye kewaye da ita sai ya
qyalqyale da dariya tace.
“Na tashi da kaina ko? Babu wanda ya tashe
ni daga barci ko?” koda jin wannan tambayar sai
shugaban kuyangin nata mai suna Ilela ta dubeta cikin
murmushi da girmamawa tace.
“Ya shugabata babu wanda ya tasheki daga
barci kece kika farka da kanki” koda jin haka sai farin
ciki ya lulluve Gimbiya Lashmin tace.
“Yauwa haka nake so ya kasance ina iya yin
komai da kaina ba sai kunyi min ba,yanzu kuma zanje
kewaye na yi wa kaina wanka” Koda jin haka sai
hankalin ilela dana sauran kuyangin ya duguzunma
ainun.
Ilela ta dubi Gimbiya Lashmin a lokacin da
idanunta suka zazzaro, fuskarta na nuna alamun
tsananin tsoro tace.
“Gimbiya ki rufa mana asiri kiyi sani cewa
idan mahaifiyarki ta samu labarin cewar yau kinyi
wanka da kanki sai tasa anyi mana horo mai tsanani...”
Kafin Ilela ta gama rufe bakinta tuni Gimbiya
5
BAYAN MUTUWA
Lashmin ta tari numfashinta tana mai doka mata tsawa
tace.
“Yanzu shi kenan ni har abada bazan tava
samun ‘yancina ba? Tun ina jaririya ake yi min komai
ba’a tava barina na yi wani abu ba, hatta goge haqora
das a takalmi. Ni kam na tsani gidannan na tsani
komai da kowa dake cikinsa”. Koda Gimbiya Lashmin
ta zo nan a zancenta sai kawai ta ji muryar
mahaifiyarta tana mai cewa.
“Qwarai kuwa duk abinda kike faxa gaskiya
ne, kuma kisani bama ke ba hatta mahaifinki ma sau
xaya ya tava sa takalmi da hannunsa wannan itace
al’adar gidannan kuma wannan al’adae ba zata tava
sauyawa ba har abada muddin ire-iren gidan na raye a
doron qasa” Cikin matuqar damuwa Gimbiya
Lashmin ta waiga bayanta ta dubi mahaifiyarta a
lokacin da ta shigo cikin turakar kuma ta durfafo inda
take da isowarta gareta sai ta kama hannunta ta jata
izuwa cikin kewaye kuma ta yafito kuyangin da
hannun suka biyo bayansu.
Haka dai taci gaba da lallava Gimbiya
Lashmin tana faxa mata kalmomi masu taushi gami da
kwantar da hankali har suka iso gaban bahon
wankanta wanda aka yi shi da zinare cike da ruwan
6
BAYAN MUTUWA
xumi ga qamshin turaren miski na tashi a cikinsa
kuma ga waxansu ganyayen fure ruwan xorawa a
kansa.
Ba tare da vata wani lokaci ba kuyangi huxu
suka kwavewa Gimbiya Lashmin rigarta ta barci suka
shigar da ita cikin bahon wanka suka shiga yi mata
wanka suna cuxa sassan jikinta a lokacin da
mahaifiyarta ta koma gefe xaya ta zuba musu idanu
kawai.
Nan take Gimbiya Lashmin ta ji wani irin
mugun baqin ciki yayi mata katutu a cikin ranta don
haka bata san sa’adda idanunta suka ciko da qwalla ba
har hawaye ya suvuce mata. Haka dai ta haqura bisa
dole har aka gama yi mata wanka.
Bayan an gama wanka wankanne aka fito da
ita daga ciki aka tsane dukkan danshin dake jikinta
sannan aka shafe duka jikinta da man zaitun. Daganan
kuma sai aka kawo tufafi irin nasu na ‘ya ‘yan
sarakuna mai tsananin kyau da tsada aka sanya mata.
Koda aka kawo Gimbiya Lashmin gaban madubi ta
kalli kanta taga irin tsananin kyau da Allah ya bata da
kuma yadda tufafin jikinta ya dace da kyawun nata
bata san sanda ta saki murmushi ba.
7
BAYAN MUTUWA
Tace a cikin ranta haqiqa duk ‘xa namijin
daya sameni a matsayin abokiyar rayuwarsa ba
qaramin dace ya yi ba”.
Bayan Gimbiya Lashmin ta gama duba
kyawunta a gaban madubi sai kuma aka tafi da iya
izuwa cikin wani dogon xaki wanda ananne suke cin
abinci ita da iyayenta.
Babu komai a cikin wannan xakin face wani
dogon teburi wanda tsawonsa yakai kamu saba’in
faxinsa kuma kamu ashirin ne kacal. Duk girman
wannan tebur kujeru uku ne kacal a qarqashinsa.
Biyuu na can qarshensa a jere, xaya kuma na farkonsa,
bisa teburin an zuba kwanukan abinci sama da kala
xari biyu kowane kwanon na xauke da abinci iri
daban-daban.
A gaban kowane kwanon akwai kuyanga
guda xaya wacce ta ruqe falan da cokali, kawai jira
take a bata umarni ta zubo abinci ta kawo.
Da shigowar Gimbiya Lashmin cikin
wannan xakin cin abinci sai ta iske iyayenta zaune
akan waxannan kujerun guda biyu dake can qarshen
teburin, tuni sun rigata halattar xakin koda suma suka
yi arba da ita sai sarki Sairan ya dubi matarsa Gimbiya
Marita yace.
8
BAYAN MUTUWA
‘Yau kuma me aka yiwa Gimbiya Lashmin
naga ko kaxan babu annuri akan fuskarta?” koda jin
wannan tambayar sai Marita ta yi xan guntun
murmushi tace.
“Babu abinda aka yi mata, halin natane dai
wanda kasanta da shi. Har yanzu taki karvar ni’imar
da Allah ya bata, kullum so take a barta ta yi komai da
kanta” Koda jin wannan batun sai nan da nan fuskar
sarki Sairan ta sauya yanayi daga annuri zuwa fushi,
bai san sanda ya doki teburin ba da tafin hannunsa
al’amarin daya razana Marita.
Gimbiya Lashmin da gaba xaya kuyangin
dake tsaitsaye a gabansu, kawai sai ya miqe tsaye ya
taho izuwa ga Gimbiya Lashmin ya tareta tun gabanin
ta zauna akan kujerarta, take jikin Gimbiya Lashmin
ya kama karkarwa saboda tsananin tsoron mahaifinta
data ji ya kamata.
Koda sarki sairan ya iso daf da lashmin
yadda suna iya jin numfashin juna sai ya dubi gaba
xaya kuyangin dake cikin xakin yayi musu wata
inkiya. Take kuyangin suka fice suka barsu su uku
kacal. Fitarsu ke da wuya sai sarki Sairan ya dakawa
Lashmin tsawa ta sake firgita ainun taji kamar hantar
cikinta zata faso cikinta ta faxo qasa yace.
9
BAYAN MUTUWA
“Sau nawa zan gaya miki cewar kada ki qara
nunawa kuyanginki cewar bakya son ayi miki hidima?
Sau nawa zan gaya miki cewar ki zamo mai
izza,girman kai da nuna isa?” koda jin waxannan
tambayoyin sai Lashmin ta sunkuyar da kanta ta kas
tayi shiru kamar wadda ruwa ya ci kuma jikinta ya ci
gaba da karkarwa fiye da farko.
Cikin xaga murya sarki sairan yace
“Wannan shi ne cikar mulki da iko, idan baki da su ba
za ki iya hawa kan karagata ba, dole mai mulki ya
zama yafi kowa tausayi da rashin imani, domin ya iya
zarta da mulkinsa daidai, ke kuma tausayi gareki
zallah ba ki da rashin imani, dole mai mulki ya zama
mai girman kai gami da izza, ke kuma sauqin kai ne
dake tamkar ruwan sanyi. Dole ne ki zamo mai zafi ga
talakawanki kuma ki zamo mai jin qansu da
taimakonsu.
Babu irin horon da bansa an baki ba akan
haka amma ba kya amfani da su. To ki sani cewa daga
yau na kafa miki doka ba zaki sake fita ko ina ba daga
cikin gidannan har sai kin fara aiwatar da horon da
nasa aka baki a aikace saboda haka zan baki riqon
karagata na tsawon kwana bakwai, idan kika tsalake
wannan jarrabawa za ki ci gaba da fita rangwadinki
10
BAYAN MUTUWA
zuwa duk inda kike so, idan kuma kika kasa hayewa
wannan jarrabawar har abada kin daina fita koda daga
cikin turakarki har zuwa ranar da zan bar wannan
duniyar”.
Koda gama faxin hakan sai sarki sairan ya
juya ya koma can inda matarsa marita ke zaune ya
zauna yana mai tafa hannayensa biyu.
Nan take kuyangin suka dawo cikin xakin
kowacce ta tsaya a inda take da, a sannan ne itama
Gimbiya Lashmin ta zauna akan kujera jikinta a
matuqar sanyaye kuma hankalinta ya dugunzuma
saboda tasan halin mahaifinta, indai ya furta zai yi abu
tofa sai ya aiwatar da shi.
Ba tare da vata wani lokaci ba suka fara cin
abinci duka su uku. Nan take Gimbiya Lashmin ta yi
abinda basu tava ganin tayi ba domin kuyangar dake
kusa da ita ta duba ta daka mata tsawa tace.
‘Maza ki xebo min abinci da na saba
faraway da shi mana, ko kuma sai na hamvareki da
qafata tukunna” Jikin kuyangar yana rawa tayi sauri ta
zuba mata abinci akan falan ta ajiye a gabanta.
Koda ganin haka sai farin ciki ya lulluve
sarki saihan ya dubi marita yace.
11
BAYAN MUTUWA
“Ta fara sauyawa fa” Koda jin haka sai
marita ta yi dariya tace.
“Ai kasan duk duniya babu abinda Gimbiya
Lashmin take so sama da zuwa cikin jeji kuma ta
yawata izuwa sauran birane da qauyukan qasar nan”
Sa’adda sarki saihan ya ji haka sai ya yi murmushi
yace.
“Ai duk wannan mai sauqi ne muddin zata
zama kamar ni” Koda jin haka sai marita tayi sauri ta
ajiye cokalin da take cin abinci da shi ta dubi sarki
saihan cikin alamun razani tace.
“Ta yaya ‘yarta zata zama kamar ka? Alhalin
ta kasance ‘ya mace kuma bata kasance jaruma ba?”
Da jin haka sai sarki saihan ya bushe da dariya sannan
yace.
“Ai ba ina nufin ta zama jaruma ba, ko
mayaqiya ina nufin zuciyarta ta zamo dakakkiya irin
ta sarakai wadanxa za su iya tafiyar da mulkinsu”
Marita tayi ajiyar zuciya tace.
“Da sannu ‘yarta zata kai wannan matsayin
da kake so ammafa dolene sai kayi haquri kuma ka
jira lokacin, ni yanzu babban abinda yake damuna
batun auren wannan yarinya. A gaba xaya qasar nan
babu wata ‘ya mace mai kyau da farin jininta ‘ya ‘yan
12
BAYAN MUTUWA
sarakai da ‘ya ‘yan manya attajirai da yawa sun nemi
auren Gimbiya amma kaqi basu. Shin kamanta cewa
itace kaxai ‘ya a garemu? Shin ka manta cewa girma
ya fara kamamu? Me yasa baka son muga jikokin mu?
Kasani cewa ko Lashmin ta zama sarauniyar qasar nan
dole ne tayi aure.
Zaifi kyau tun yanzu ma ka sauka daga kan
karagarta ka bata kuma ka zava mata mijin daya dace
da ita. Koda jin wannan batu sai sarki saihan ya gyaxa
kai sanan ya kawo gwauron numfashi ya ajiye yace.
“Ina nan ina tunani da aiki akan haka kuma
nan bada daxewa ba komai zai kammala. Kinsani
cewa dolene nayi wa ‘yarmu zave mai kyau kuma
mafi alheri a gareta domin bayanmu ta yi kyau kuma
ta xore” Haka dai sarki sairan da marita suka yi ta
tattaunawa akan gimbiya Lashmin ita kuma lashmin
sai ta ci gaba da cin abincinta kawai tunda bata jin
abinda suke tattauna saboda nisan dake tsakaninsu
amman kuma ta tsargu cewa akanta suke magana bisa
ganin yadda suke yawan kallonta.
Bayan sun kammala cin abinci kowanne su
an wanke hannunsa an goge maiqon dake bakinsa sai
suka miqe tsaye tare, sarki ya fito Lashmin da hannu
ta taho garesu. Da zuwanta sai ta faxa kan qirjinsa
13
BAYAN MUTUWA
suka rungume juna sannan ya janye jikinsa daga cikin
nata ya sumbaci goshinta yace.
“Kamar yanda na gaya miki xazu yaune za
ki fara yin jarrabawar don haka nan da cikar rabin sa’a
kije ki gama shiri ina son ki shammaci kowa kawai sai
dai fadawa na da sauran jama’ar gari su ganki akan
karagata, bayanin farko da za ki soma yi musu ina
kwance bana jin daxi shi yasa kika wakilceni, daga
nan sai kici gaba da gudanar da al’amuranki na mulki
kamar yadda kika ga ina yi kullum” koda gama faxin
haka sai sarki ya kama hannun marita ya jata suka fice
daga cikin xakin cin abinci suka bar Gimbiya Lashmin
a tsaye cikin fargaba, tunani gami da mamakin dalilin
da yasa yau rana xaya sarki ya yanke wannan
hukuncin na yi mata wannan jarrabawa.
Babban tashin hankalita shi ne yadda zata
gabatar da shari’a a fada tayi hukunci ga wanda aka
zallunta kowa wanda ya aikata laifi. Duk abin da ya
shafi sai an zubar da jini ko an musgunawa wani
Lashmin bata son shi, saboda tsananin tausayinta
amma kuma yanzu bata da wani zavi wanda yafi tayi
wannan hukunci bisa dole don kada sarki ya kafa mata
takunkumi fita rangadi da koma katse mata burinta na
son yawantawa a cikin kasar.
14
BAYAN MUTUWA
Lashmin na tsaye a cikin xakin cin abinci
tana ta tunani har izuwa tsawon daqiqu masu xan
yawa har sai da shugabar kuyanginta ta shigo ta dafa
kafaxarta sannan ta dawo cikin haiyacinta ta dubeta a
razane kamar wacce ta farka daga mafarkin ban tsoro,
shugabar kuyangan tace.
“Ranki ya daxe shin kin manta ne cewa za
mu yi miki shirin zuwa fada?” koda jin haka sai
Lashmin ta saukar da ajiyar zuciya tace.
“Haka ne fa muje mana” Nan take shugabar
kuyanginta ta wuce gaba Lashmin na biye da ita
sannan sauran kuyangin suka take musu baya.
Cikin qanqanin lokaci aka sauyawa Gimbiya
Lashmin tufafi aka sanya mata irin tufafin shiga dafa.
Aka kawo mata alkyabba irin ta mata mai darajar
gaske aka yafa mata kuma aka xora mata hular mulki
ta lu’u lu’u akanta.
Hakan ne ita kanta Lashmin da ta dubi kanta
a cikin madubi taga yadda wannan shigar tayi mata
kyau sai ta dubi shugabar kuyanginta tace.
“Tabbas mulki yana da daxi, amman bana
son shi saboda har naji wani irin girman kai ya fara
shiga jikina saboda kawai na sanya wannan tufafin na
alfarma. To idan kuma na shiga fada fa naga
15
BAYAN MUTUWA
fadawa,bayi da hadimai sun fara gaisheni suna
girmamani? Ni kam idan na gama wannan jarrabawar
da sarki zai yi min bazan sake yarda na sanya irin
wannan tufafin ba har abada, maza mu wuce zuwa
fada.
Saboda sarki ya bani umarnin lallai na riga
fadawansa zuwa fada” Nan take shugaban kunyangi ta
sake yiwa Gimbiya Lashmin jagora suka fice daga
cikin turakarta suna fita sai dakarun dake tsaron
lafiyarta su arba’in suka rufa mata baya, tun a qofar
turakarta Lashmin taga sabon sauyi, domin gaba xaya
hadiman da suke binta sarki duk wajen da zai je ta
gani tsaye suna jiranta.
Ai kuwa tana fitowa sai dukkansu suka zube
qasa gabanta suka kwashi gaisuwa sannan kowannen
su ya kama aikinsa kamar yadda suka saba. Duk inda
suka wuce a cikin gidan sarautar sai taga ana
girmamata ainun fiye da yadda aka saba yiwa sarki shi
ake yi mata domin nan take aka fara buga mata
tambura ana busa kakaki da algaita, kuma gaba xaya
jama’ar gidan suka rinqa zuwa suna zubewa qasa suna
kwasar gaisuwa.
16
BAYAN MUTUWA
BAYAN MUTUWA 2
oda ganin wannan al’amari sai
hankalin lashmin ya dugunzuma
ainun tace a cikin ranta, anya kuwa
sarki ba yaudarata yayi bay ace jarrabawa zai yi, babu
mamaki ya sauka ne daga kan karagarsa ya bar mata,
koda gama ayyana hakan sai idanunta suka ciko da
hawaye, koda taji qwallah tana shirin suvice masa sai
tayi sauri ta sunkuyar da kanta qas don kada wani ya
gani ta share hawayen. Tace a cikin ranta ina ma Allah
bai yiyota ‘yar sarki ba. Da dai ace ita ba kowabace
face ‘yar talakawa fitik masu neman abin da za suci
kullum da ya fiye mata farin ciki da kwanciyar hankali
a rayuwarta
Haka dai su Gimbiya Lashmin suka ci gaba
da tafiya a cikin gidan sarautar ana biye da ita xu
tamkar wata tauraruwa mai tsananin haske a tsakiyar
dubunnan taurari har aka iso cikin babbar fada ta
gidan sarautar.
Daga dakarun tsaron sai qananan fadawa sai
kuma mutanen gari a zazzaune wato a tsaitsaye a cikin
fadar. Koda shigowar Gimbiya Lashmin tare da
ma’aikata masu take mata baya sai duk mutanen dake
K
17
BAYAN MUTUWA
zaune suka miqe. Koda aka ga Gimbiya Lashmin ta
fito a maimakon sarki sai kowa ya cika da mamaki,
aka wangame baki ana kallonta kawai, kai tsaye
Lashmin ta nufi wajen da karagar mulki take tana
tafiyar qasaita kamar wani toron giwa.
Hatta yanayin tafiyarta irin ta sarki sairan ce.
Haqiqa komai yana bin jini in da ace shigar maza
Lashmin ta yi kuma ta rufe fuskarta to da kowa zai
xauka sarki ne ya shigo fadar ba Gimbiya Lashmin ba.
Da isar gimbiya Lashmin kan karagar
mulkin sai ta zauna ta harxe qafa xaya bisa xaya
tamkar dama can ta saba zama akan karagar. A
sannane sauran jama’a kowa ya koma inda yake ya
zauna kuma a daidai wannan lokacin manya fadawa
da ‘yan majalisu qasar suka fara shigowa. Duk wanda
ya shigo yayi arba da Gimbiya Lashmin zaune akan
karaga mulki sai ya kamu da tsananin mamaki gami
da tsoro don ba a san dalilin faruwar wannan canjin ba
alhalin sarki yana raye.
okacin da Gimbiya Lashmin ta lura da
gaba xaya fadawa da ‘yan majalisu sun
hallara sai ta yi gyaran murya take fadar
tayi tsit aka saurara domin aji abinda zai fito daga
bakinta. Duk wanda ta kalla sai taga yana muzurai
L
18
BAYAN MUTUWA
gami da haxiyar miyau kamar su tashi su matse
bakinta tayi bayanin dole.
A zuciyarta sai tace oh kaga miyagun banza
kawai so suke suji wata maganar ta sharri bata alheri
ba, domin su san yadda za su qula wani mugun
makircin.
Kawai sai aka ga Lashmin ta fara da yin
murmushi sannan tace.
“Yaku jama’ar wannan birni na sham kuyi
sani cewar mahaifina bashi da lafiya amma duba ba
wani ciwo mai tsanani bane don haka zan ci gaba da
wakiltarsa har izuwa tsawon xan lokaci kafin ya
warware, ina mai yi muku alqawari da cewar zan
tafiyar da mulki bisa adalci kamar yadda mahaifina ke
zarta da shi.
Saboda haka ina fatan cewar ‘yan majalisa da
dukkan dakaru da sauran shugabanni na birni da
qauye za su bani haxin kai kamar yadda suka saba
baiwa mahaifina.
Yanzu take ina son a ci gaba da zarta da
komai kamar yadda aka saba kuma zan saurari qara
guda uku kacal a zaman da za mu yi yanzu, ina masu
gabatar da qara?” Koda jin wannan tambayar sai wani
dattijo daga cikin fadawan ya matso gaba kusa da
19
BAYAN MUTUWA
karagar mulkinta a vangaren hannun dama ya zube
qasa ya kwashi gaisuwa sannan yace.
“Ya shugabata ni ne mai gabatar da qara a
wannan fadar tsawon shekara talatin baya kamar
yadda kika sani” Koda jin haka sai Lashmin ta yi
murmushi tace.
“Gaskiya ya kai Safwan bin ma’aruf bin
kananata, tun kafin a auri mahafiyata kake wannan
aikin. Kai ne ka gabatar da qarar waziri Dulnur wanda
ya kashe amininsa ya aure matarsa kuma ya mallake
dukiyarsa kimanin shekara talatin da shida baya anan
fadar, da taimakon ka ne gaskiya ta bayyana har ka
saka sarki kan’an ya yankewa waziri Dainur hukuncin
kisa aka tsireshi a tsakiyar kasuwa ko ba haka abin ya
faru ba?” Safwan ya risina yace.
“Haka yake ranki ya daxe” Nan take jama’ar
da suke cikin fadar suka kamu da tsananin mamaki
bisa jin yadda Gimbiya Lashmin ta riqe wannan
tsohon tarihin domin lokacin da al’amarin ya faru ba a
ma san zata zo duniya ba.
Lashmin ta dubi Safwan bin ma’aruf tace.
“Karanto mini shari’ar farko na ji a kuma
shigo da wanda ya kawo qarar da kuma wanda ake
qara” koda jin wannan umarni sai Safwan ya miqe
20
BAYAN MUTUWA
tsaye yaje bakin qofar da ake shigowa da masu shari’a
yace.
“Ina attajiri Huzulu da kuma saurayi Amzad a
shigo da su”.
Nan take sai ga wani dogon mutum
ma’abocin kwarjini a cikin suture masu tsada ya shigo
cikin fadar fuskarsa cike da annuri. Kallo xaya zaka yi
masa kasan cewar babu wani abu da yake damunsa a
rayuwa, yana tafe yana murmushi.
Wanda ke biye da shi kuwa wani matashin
kyakkyawan saurayine wanda kana yi masa kallo xaya
zaka gane cewa in ba don talauci ba da bai kasance
ramamme ba kuma da kyawunsa ya ninka hakan sau
uku.
Kai da ganinsa kasan yana fama da aikin
wahala kafin ya samu abinda zai kai bakinsa, biye da
waxannan mutane biyu dakarun fada ne.
Koda Gimbiya da wannan matashin saurayin
mai suna Amzad suka haxa idanuwa karon farko sai
kowannensu yaji zuciyarsa ta buga da qarfi. Cikin
hanzari Amzad ya sunkuyar da kansa qas don kada
qurawa Lashmin idanu ya zama laifi ayi masa wani
hukunci akan haka.
21
BAYAN MUTUWA
Batare da vata wani lokaci ba aka gurfana da
attajiri Huzulu da Saurayi Amzad a gaban Gimbiya
Lashmin. Nanfa fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta
sai da Lashmin ta qarewa attajirin Huzulu da Amzad
kallo, tayi nazarinsu sosai sannan ta dubi Safwan bin
ma’aruf tace.
“Kafin a gabatar da wannan qarar ina son ayi
mini bayani akan matsayin wanda ake qarar da wanda
ya kawo qarar, ina son nasan sana’o’insu,
mu’amalarsu da mutane da koma inda kowannensu ke
da zama” koda jin haka sai mamaki ya kama gaba
xayan jama’ar dake cikin fadar hatta manyan alqalai
kuma na dukan kotunan qasar saboda wannan wani
sabon salone bisa tsarin shari’ar qasar, Lashmin tazo
da shi.
Mai gabatar da qara Safwan bin mu’aruf ya
juya ya fuskanci Gimbiya Lashmin yace.
“Da farko dais hi wannan attajiri wanda kowa
a garinnan ya sani da suna Huzulu yana zaune ne a
unguwar sarakai kuma bashi da wata sana’a wacce ta
wuce siye da siyar da gidaje da kuma bayar da hayar
gida ko gona ko rumfar kasuwa. A cikin wannan
birnin namu na Misra an tabbatar da cewa yafi kowa
yawon gidaje da gonakai da kuma rumfunan kasuwa
22
BAYAN MUTUWA
don haka ko sauran attajirai masu yin harkokin fatauci
kalilan ne suka fishi yawan tsabar kuxi a hannu a
qasar nan gaba xaya.
Shi kuma wannan saurayi mai suna Amzad
bashi da wata sana’a wacce tafi dakon tubalin gini ya
kanje ya nemi aikin dakon tubali yana kaiwa inda ake
gini abiyashi, wannan ita kaxai ce mu’amalar data
haxashi da mutane. A kullum idan ya tashi daga aiki
da yamma da zarar ya wanke jikinshi zai tafi ne izuwa
can gidansu wanda ke kusa da gidan attajiri Huzulu a
unguwar sarakai ya kaiwa mahaifiyarsa abincin da
zata ci. Ita dai wannan mahaifiya tasu ta kasance
tsohuwa tukuf, saboda tsufan ma bata gani da idanunta
kuma bata iya taka qafafunta, ko kewaye zata shiga
sai dai Amzad ya xauketa a hannunsa ya kaita” koda
Safwan ya zo daidai nan a bayaninsa sai Gimbiya
Lashmin ta xaga masa hannu kuma ta tari
numfashinsa tana mai cewa.
“Me yasa kake wuce gona da iri akan bayanin
Amzad, amma sa’adda kake bayanin attajiri Huzulu
sai ka taqaita komai yasa?” Koda jin wannan
tambayar sai idanun Safwan suka zazzaro gaba xayan
jama’ar dake cikin fadarma sai suka kama muzurai.
23
BAYAN MUTUWA
Shi kansa attajiri Huzulu sai yayi fiqi-fiqi da
shi