Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mai gurbina.. Kuttumar ubancan to ga hanya nan tafi akwai wanda ya rike ki, kin manta ranar da na kira ki , kika ji daukan waya da yake a lokacin kina cikin kwanciyar hankali ga UMMEE yar iya daukan dukkan wani tension bara ki faɗa min ko to ke da ita sai naci takazar uban ku ke , wallahi ki kiyaye ni kinfi kowa sanin wace ni kallon ke kawai nake naga iya ina film din bake zai kare a wacce chapter ne ita kuwa shegiya ta samu guri ko bara ta sheka ayar ta lafiya qalau jinin farida zai zo waje batare da ya hargitsa gurin ba farida bakar annoba ce fa na tsane ta , wallahi na tsani duk wani tsatson ta shima so yake ransa ya ɓaci shi ya saka har yanzu be mai da mata da annobar ta gida ba wallahi ku bini a sannu ko ayi yakin duniya na uku a *DAN BUZU* ita kan'ta innar kallon ta kawai nake dan haka wannen ke ta shafa jawad ko yanka naman jikin yake ba abin da zai dame ni duk wanda ya iya allon sa ya wanke ya sha idan kuwa kika nemi raba ni da , ɗana wallahi sai kin bar gidan nan.., UMMEE ɗa ko dan rana ta fada a zuciyar'ta amma afili sai tace '' ummee wallahi ba haka ba ne akwai abin da nake shiryawa ne takarda biyu ce ta rage min ban gama haɗa miki komai ba sai mu tafi plan na gama kiyi hakuri.. yanzu ma zan turo miki wasu kudade.., UMMEE wani sanyi taji tace '' oh to maza turo min su ita kuma zanci uban'ta wallahi...farida kamar mayya ta kasa rabuwa da duk wanda ya shafe ni..tasani sarai bana kaunar ta , bana kaunar duk wani me kaunar ta amma da yake mayya ce taki rabuwa da ɗana.., jawaher tace '' bashi take so ba kudin hannunsa take so..., zanyi maganin ta kuwa sai an jima, ta faɗa tana kashe wayar wani sanyi ne ya ratsa jawaher ta fita tana yar waka. cikin daki kuwa najlah fita za tayi jawad yace '' ina zaki..?, yaya zuwa zanyi nayi breakfast..., zauna muci tare wannan yayi min yawa kina so nayi nauyi da yawa ko..? kizo kina nayi nauyi na tsofa. kallon sa tayi ta gefen ido tana cewa to ka riga da kayi dan kaci wannan ba abin da zai ƙara maka kuma kai kace nayi maka shi. hmmm haka ne amma kinsan kayan kiba ne ko me makon ki ban shawara kar nace to nadai ƙara tsofa kece a ciki ni ba ruwana.. ni kuma ko aunty jawaher. ta faɗa tana nuna kan'ta.. dafa kan'sa yayi yace "' ashe mugunta kika shirya..," zama tayi a ƙasa tace '' uhmm uhmm kai fa kace nayi maka yanzu kuma kazo kana challenging dina to dena ci na hado maka salad kace sai ka rame sannan kayi exercise shikkenan..., hannun'ta ya riƙe yace '' a'a barshi nagode daga magana sai kuka.., ƙoƙarin kwace hannun'ta tayi amma sai ya hanata haka ya riƙe hannun'ta gam bin hannun'ta tayi da kallo tace '' yaya zaka karya min hannu tun dazu kake riƙe min hannu..., ina jin daɗin rikewar ne idan na riƙe sai naji zazzaɓin da nake ji ya ragu ko bakya so na samu lafiya ne. kallon sa tayi tace '' to ka sassauta min rikon nan kuma ka dena shafa min fatar hannu bana jin dad'i wani iri nake ji kamar shocking.., da sauri ya kalle ta yace " da gaske..?, Allah yaya to nima cika ni na ci abincin. cika ta yayi tare suka soma ci ba wanda ya kara cewa kowa komai dakin ya dauki shiru zare hannun ta , tayi tace '' na ƙoshi.., kin koshi kuma guda nawa kika ci..?, ya faɗa yana haɗe ran sa tamkar bashi ne ɗazu yake wannan maganar ba. walllahi na koshi bara naje na wanko hannu na shikkenan ai ba abin da zan maka ko zan koma daki na. okay wanko ki dawo , kin manta dazu me nace miki.. turo baki tayi ta , tashi ta wanko hannun ta, ta dawo sosai take jin bacci kwantar da kan'ta tayi a kan kujera jawad yace '' bacci kike ji..?, kai ta daga mai yace '' okay kwashe kayan nan ki zo ki kwanta a kan gado.., to tace mai ta , tashi domin jikin ta duk yayi la'asar bata san dalili ba dauke kayan tayi ta kai kitchen ta dawo kwanciya tayi akan gadon tana limshe idon'ta wani irin bacci ke fusgarta. lokaci guda bacci ya dauke ta jawad tashi yayi ya wanko hannun sa ya dawo fita yayi daga dakin gaba ki ɗaya ya hau sama takardu ya dauko da laptop yana cije lips din'sa ji yake kamar ciwon na ƙaruwa saukowa yayi ya tarar da su rose yace '' ba abin da za ku girka yau.., gaishe da suka soma yi amsawa yayi yana barin gurin. to suka ce suka bar gurin tare da rofe kofar parlour. ajiyewa yayi ya soma aikin sa yayi lokaci zuwa lokaci yana juyowa ya kalle najlah da take baccin ta cikin kwanciyar hankali. tunowa yayi bata sha maganin ta ba tashi yayi ya tafi daki ya dauko mata tare da dauko mata ruwa wata kwaya ya jefa a cikin ruwan lokaci ɗaya ta narke batare da ta canza kalar ruwan ba. ajiye wa yayi ya soma tashi ta , tashi tayi tana turo baki tace '' idan na tashi zan sha yanzu kaina zai fara ciwo wallahi.., haɗe rai yayi yace "zaki sha ko sai ranki ya ɓaci...," ɓallo mata yayi ya bata amsa tayi ta sha tare da ƙara kwanciya yace '' najlah ki tashi ki zauna ya ɗan faɗa miki sai ki kwanta.., yaya bacci wallahi nake ji. to shikkenan ya fada yana janyo laptop din'sa. wannan kenan. *DEEYA NAILAH EMAN* mafita nake nema ko kalli P test din nan result din da ya bayar ciki ne fa dani.. Hmmmm wallahi kin ban mamaki ke daman akan wannan kika tara mu ni wallahi na zata wata maganar ce kina hana da aure ba baki da shi ba mene abin damuwa.. cewar deeeya. wani kallo tayi mata tace '' bafa na Jawad ba ne.., idan ba nashi bane sai me aure ai ya bashi Na'ilah ta faɗa tana danna wayar ta. EMAN tace '' calm down jawaher wannan fa cikin Ubangiji ne ya baki kuma yayi haka ne domin karki tashi a tutar babu randa Jawad ya mutu tofa idan ba tumulin taka ba , ba ba abin da zaki samu, kuma kinsan yana gab da mutuwa ko da ace be shaki poison din da aka saka mai ba gubar da kike bashi kullum tana fa aiki a jikin sa , sannan kinsan dai komai nisan jifa kasa zai dawo idan asirin ki ya tono ko dan wannan yaron wallahi zai kalle yaron nan ya kasa komai bangaren UMMEE bata da komai domin a lokacin zaki nuna mata ruwa ba sa'an kwando bane ki buda komai ki juya komai ya koma kan'ta ke ce barazana tayi miki, wallahi JAWAHEER wayon ki na banza ne yasin kwata kwata baki da wayo ko kaɗan sannan mu kuma yan bada shawara sai asan yadda za a yi damu bayan komai ya lafa sai ki dawo kan TJ kici uban sa dole yayi wa dan da wahala kinga da wannan cikin baƙaramin alkairi zaki samu ba wallahi.., DEEYA tace '' wallahi EMAN bansan kina fa ƙwaƙwalwa haka ba sai yau idan kuwa dukkan wannan plan din ya tafi dai-dai ni ma kashe nawa auren zan yi tas wallahi na aika shi barzahu naci dukiya ga ta gurina ga ta gurin jawaher wallahi zaman kasar nan nafi karfin sa.., Na'ilah tace '' to wani hanzari ba gudu ba wannan abin duk yayi daidai amma bana goyan bayan kisa haba zunubin ina zaku kai shi muma fa sai mun samu namu kason wallahi...., jawaher tace '' gaskiya ina tausayin Jawad wallahi yana kaunar yara idan na kawo mai dan shege cikin gidan sa ban kyau ta.., dallacan rufewa Mutane baki ashe daman baki da hankali to wallahi idan kikai mana bakin cikin shiga daular nan, yasin sai na fasa kwai kalli motar da nake hawa jiya na samu wani dan rainin hankalin saboda yana kallo na talaka zai neme ni ta baya zai bani miliyan hamsin..miliyan hamsin din taci abu takazar uban ta haka nace masa na duddura masa ashar yanzu haka wani bokan ne zai ce yayi haka zai samu kujerar dan majalisar tarayya da yake nema.., cewar EMAN. Na'ilah tace '' lallai eman to ai yanzu abin da ake kenan biya mun bukata na baki abin duniya kin zama two SIM kenan to su karima jos abin da suke kenan wallahi...kike ganin su suke baki sha'awa nima dan dai bana son na haɗa DAZ da kowa ne amma da wallahi kudi zan samu.., kash amma gaskiya Na'ilah baki da hankali ko kaɗan sarai nasan abin da suke aikatawa kenan wata ran fa sai an dinga sakawa mutum pampas saboda mutum zama yake uncontrol Cewar jawaher. DEEYA tace '' kunga wannan duk matsalar ku ce ga wannan babban issues da muke tattaunawa ki bar cikin nan muga abin da Allah zai yi.., wallahi bazan bari ba sai dai duk abin da za kuyo baku da hankali idan fa na mutu nazo haihuwa nace wa Ubangiji me...? idan yaron ya taso ya girma yasan gaskiya da wanne ido zan kalle sa haba gaskiya kun ban mamaki wallahi wato ku biyan buƙatar ku, kawai kuke dubawa.. tashi DEEYA tayi tace '' kan bala'i lallai JAWAHEER aikuwa idan kin ki ji ba zaki ƙi gani ba wato daman kin zo ki lasa mana zuma a baki ne ko duk kudin Jawad mi tashi a banza a wofi tumunin takaba kaɗai za a baki insha'Allahu wannan cikin namiji ne ni daman kullum addu'a nake Ubangiji ya azurta ki da samun ciki irin wannan gida ne ake sakar jiki a haihu domin gobe.. NAILAH tace '' DEEYA waya san gawar fari ban da Ubangiji...?, kinga bana son tsohon wa'azin ki, ki zauna kiyi wa kanki idan kika dawo dai-dai sannan sai kizo ki yi min gwara ni ina zaman gidan miji ke zaman gidan mahaifinki ma ,ya gagare ki zama dan haka baki isa ba ko faɗa min dabarun zaman duniya magana ake ta kudade ma kuɗai mazaje.. sosai ran Na'ilah ya ɓaci wato daman zaman gidan mahaifi daraja ne dashi koda kuwa ke karuwa ce kina cikin sutturar ki ta kalli eman mana ta fadawa haka , ita da iyayen ta karatu suka turo ta basu san me take aikatawa ba idan zata koma gida ko mota bata zuwa da ita waya kuwa tun wayar da mahaifinta ya siya mata alokacin da za'a kawo ta makaranta, bata siyar da ita ba cire kayi kan ta , take ta ɗora ta komar musu da ita su gani..tace... '' amma deeya kin ban mamaki har idon ki ya rufe ki faɗa min haka...?, EMAN tace '' Please be kamata dan mun samu banbancin ra'ayi ba kuzo kuna fadawa junan ku magana kamar ba classis ladies ba kalle mu, mu hudu abin sha'awa ko wa zancen mu yake bamu taɓa samun sabani ba muna zaune tsakani da junan mu tsakani da Allah...., zama suka yi dukkan nu daman jawaher ita a zaune take ta zuba ta gumi, tana cikin tsaka me wuya bata san ya za tayi ba gashi suna barazanar tona mata asiri tayi sake da suka san sirrin ta amma bakomai idab sun san wata basu san wata ba dukkan nin su tana da video su tace '' *DEEYA NAILAH EMAN* lallai idan kuka ce zaku tona min asiri to fa zamu tonawa juna asiri kun saka rigar karya, kun fake da business kun mai da da dalin tiktok wajen sheka ayar ku, wajen kawalci mayan mutane su ganku suyi muku DM ko kuma su bawa wani yayi muku magana ya haɗa ku da su dan haka yadda ake ganin ku da mutunci wallahi sai na tona muku asiri....za ayi yar tone tone a tiktok ko wacce update dinta zai baza duniya kowa ya gani ni za kuyi wa barazana..., da sauri ko wacce ta kalli yar uwar ta deeya ta cire dankwali taja ɗamara tace ''miko wayar ki ko muci kuttumar uban ki.., wallahi deeya saɓa mata kamannin za muyi ke kin manta mu su waye duk tashancin ki mun fiki.. cewar Na'ilah. Eman tace '' wallahi da asirin mu ya tonu gwara mu aika ki rahira karshen mu gidan yari baza dai ace dukkan mu za a kashe mu ba balle ma muna da manya a hannun mu maza dauko wayar nan da hannun ki ma zaki goge shi.., wanne ta goge tayi restor din wayar gaba ki ɗaya fakat ba kare bin damu.. cewar DEEYA. Na'ilah tace '' ya kika tsaya kina kallon mu ko sai kin ga mun dauko muciya da taɓarya mu sauke miki gaɓoɓin jikin ki yar akuya..., KARUWAN CIKIN GIDA Ga channel dina kuyi min subscribe Dan Allah wai ina masoya na suke. https://www.youtube.com/@nasreenminallah https://vm.tiktok.com/ZSBRtRQmN/ Domin samun update kuyi following dina Book ¹ EPISODE ²⁴ Na'ilah uwa tace akuya.. JAWAHEER ta faɗa tana nuna kan'ta. DEEYA tace '' to ai tayi miki da sauki daba tace yar tinkiya ba maza fito da video nan.., jawaher tashi tsaye tayi kallon abin take yawa almara tace '' ni zaku daka wallahi kunsan ko giwa ta rame tafi karfin rami.., kunga ku dakata kar wacce ta , taba da hannu mu nemi icce domin tace wa xeey wani yana da kanjamau idan ba tare suke shan magani ba, ya akai ta sani...?, cewar EMAN. da sauri jawaher ta kalle ta , tace '' eman ni kike faɗawa haka..?, kinga jawaher ke kika takalo wannan faɗan da kinsan ba zaki iya ba kika fara dan haka maza ki fito da wayar ki ko yanzu wallahi mu aika ki lahira dukkan mu kinsan tsofaffun crimenal ne ba wacce bata da record a police tasion.. cewar DEEYA. kan jawaher ne ya soma wa juyawa idan wani ya faɗa mata haka zata faru zata ƙaryata dafe kan'ta tayi da sauri deeya ta shiga kitchen kafin ta tantance ta buga mata muciya a gadon baya ta dura wani uban ashar tace '' tun kafin nayi miki irin wannan guda dari shidda har sai naga kin dena motsi ki fito da wayar ki.., da sauri jawaher ta ɗurƙusawa domin ba karamin jin dukan nan tayi ba. jawaher shawara nake baki karki kiyi taurin kai ki fito da wata sahunki a likkafa ki bayar ayi mata restor. Cewar EMAN. kinga eman ke kika tsaya lallaɓata wallahi mu da ita shege ka fasa duk wanda ya safa kuttumar uban sa ba dan halak bane gwara muyi rugu rugu da naman ta idan ya so muce hatsari ne mu kwashe ta mu kaita asibiti.. cewar DEEYA. Na'ilah tace '' tsaya tsaya DEEYA mubi komai a sannu karfa garun wannan dukan cikin da muka kwallafawa rai ya zube ayi biyu babu., EMAN tace '' au ke magana ma kike ayi biyu ba bu ai daman niyar zubar da dan banza take gwara mu ,mu muzubar mata dashi magana ake fa ta tonan asiri yar rigar mutuncin da muke da ita a gurin masu mutunci ta yaye kowa ya koma mana kallon sheɗanu dan haka yau ko mu ko ke dan takazar ubanki..,, kunga samo min abu mu rufe mata baki karta tara mana jama'a..? daure ta sukai tamau suka dinga jibgar ta , tamkar Allah ya aiko su. kamar ace kalli can suka hango inda ta wurga wayar eman daukan ta , tayi tai mata kwatsatsa sannan ta dauraye ta , tas a cikin ruwa yadda ko wajen uban waye aka kai ta baza ta moru ba ɗagowa tayi tana haki tace '' ku dakata kamar jini ya balle mata.., kallon ƙasa suka yi da sauri deeya tace '' maza dauko mota kwara mu kaita asibiti cikin ya zube a can idan ya so ma kira shi.., da wannan shawarar suka kunce ta , tas Na'ilah ta gyara parlour tamkar ba'a yi komai ba jawaher ko iya ɗaga hannu bata yi suka zurata a bayan mota eman da deeya da Na'ilah suka shiga gaban mota suka gwamutsa. basu tsaya a ko ina ba sai a asibiti suka fito fuskar su, cike da alhini deeya da eman har da kuka Na'ilah ke rarrashin su tana basu baki. aguje likitoci sukai kan'ta da yake asibitin nan take da folder cikin sauri suka shiga emergency room da ita deeya zama suka yi tamkar basu zaman makoki suka zuba ta gumi eman tace '' ke ya za ayi da motar ta..?, ta faɗa ƙasa ƙasa. deeya kifta mata ido tayi tana nuna kan'ta subarta da komai kar su yi magana fahimtar hakan da suka yi suka ja bakin su, suka tsuke. Na'ilah tace '' ya kamata fa a sanar da mijin ta.., what baki da hankali haka kurum za a ɗaga mai hankali sai gobe zai sani wallahi. cewar eman. DEEYA tace "' gaskiya Na'ilah shaye shayen da kike ya fara taɓa miki ƙwaƙwalwa yanzu sai mu sanar dashi yazo kulle ya farke gwara mu ƙara kafa mata worning da kyau ko da wasa tace tak to wallahi can zata , tafi...,, Na'ilah jan bakin ta tayi ta tsuke jikin ta yayi sanyi. idan sunga wani zai huce sai su kara dada sautin kukan su tamkar basu, suka aikata haka ba.. wata doctor ce ta , fito sanye da labcort hannun ta da wasu takardu tace '' Please kuyi hakuri ku dena kuka abin ya zowa mrs Jawad da sauki duk da cikin jikin ta ta zube sakamakon bugawar da yayi insha'Allahu yanzu zamu ɗorata ta samu karaya uku a cinya ɗaya a hannu wuyan tama ya karya gaskiya wallahi Allah ne yayu da rayuwar ta domin ba'a fiye samun mutum yayi irin wannan hatsarin ba ya tashi..., share hawaye eman tayi deeeya kuwa wani bakin ciki ne ya durar mata da taji cikin da suka kwallafawa rai ya zube, zubewa tayi a ƙasa tana kuka har da buga kan'ta tana ganin duk wani mafarkin rayuwar ta ya rushe kai Allah ya tsinewa JAWAHEER duk taurin kan'ta ne ya jamusu. mamaki ne ya kama su eman to wannan kukan fa ko duk a cikin shiri yake to suma bara su bita karta, tashi ta tsine musu tas fara rokota suka yi suna kuka doctor wasu nurse ta kirawo guda uku suka dinga rarrashin su dawowa doctor tayi ta shiga dakin fito da Jawaher akai duk ta fita hayyacin ta suka shiga da ita dakin theater. ★★★★ BINYERI. kai wallahi yau ko ubanka be isa ya hanani zuwa gidan ya'ta ba. inna ta fadi haka tana haɗa kayan tsubbun da takarbu a gun malamin ta. da niyar idan takaiwa jawa ta cake mata kudin ta a lokacin. ɗaga wani abu tayi tana cewa wannan shi ne na yar iskar yarinyar da malam yace min tana cikin gidan yar uwar ka idan ba akawar da ita ba to zata zame mata babbar matsala kawai sai nace a haɗa ta cutar hauka mutukar wannan abin ta shake shi shikkenan an gama kai sai nayi wata tara sannan zan dawo. ta karashe fadar haka tana mai da kwalbar cikin jakar ta. jujal yace '' insha'Allahu ba zaki gano gidan ba bata ce karki zo ba , zata zo salon kije ki kashe mata aure..,ni gani nan a zaune ko mashin shini babu.., da sauri inna ta juyo domin jin abin da yace tace '' juburu ni zan kashewa jawa aure..?, to ke iya bala'in ki wa ya bari..? yanzu ga yar ɗagwas nan sai da kika ga ta fito hankalin'ki ya kwanta.., jan kujera yar tsuguno tayi ta zauna tace '' jaburu na lura duk karatun da nake maka tabayan kunne yake shiga yake fita humaira da kake gani mijin ta talaka ne malamin makaranta me na ƙasa yaci balle ya bawa na sama...? shi ya saka na doka sammako na siya biro da nemi alfarma aka bani takarda naje na miƙa mai ya sakar min ya'ta jawa kuma idan Allah ya azurtata da haihuwa a cikin gidan nan hmmmm jaburu wallahi makka sai dai kayi kyautar ka dan haka saki zuciyar ka , ba kashe mata aure zan yi ba wannan ma kayan gyaran aure ne naje gurin malam me gobe da nisa me aiki kamar yankan huƙa nakai mai naira na gugar naira yayi min wannan hadin na manta da uwa da dangi.. idan bake ba sai rijiya akan ki saina kashe uban kowa ke nake gani.., kut billahilazi wannan wakar soyayya ya biya miki jaburu ya faɗa yana rufe bakin sa saboda ganin yadda inna ta dage tana karanto kalaman soyayya kamar irin yar yau din nan. INNA tace '' kai da hallacan abin da yake nufi da ya fadan haka ba wanda ya isa ya faɗa mai yaji.., hmmm wallahi karya yake fada miki. a'uzubillahi minar sheɗanir rajim, bakin ka ya sari ɗanyan kashi dan uwar ka fice min a gidan nan wallahi bansan kai ba mutumin kirki bane ba sai yau. cewar inna. tashi yayi yana wallahi karya ne wallahi. haka kurum ya ci miki kudi a banza dama ni kika bani nayi miki kuluboto tunda shi suke muku da surkulle abu ta dauka zata bugo mai da sauri ya fita a gije yana dariya. karasa hada kayanta, tayi tas tana ƙoƙarin fito dasu tsakar gida humaira ya shigo da malam malam yace '' ina zaki..?, mayafinta ta rufa tace '' gidan jawa..., da sauri ya kalli kayan da yake gaban ta yana mamaki yace '' baki faɗan ba , kuma gidan surukinki za kije da wannan uwar jakar da wanne ido zaki kalle sa to ban amince ba.., malam wallahi tafiya ba fashi dai nayi. Allah ya shirye ki bazan baki ko sisi ba kudin mota Allah ya kiyaye hanya. dariya inna tayi tace '' wannan maganar amin in da gaske kake amma malam tun lafin na haifi jawa ka dena bani kudin unguwa cefa ne ma sai da wallahi tallahi dan haka kaga baka isa ka faɗa min naji ba.., Malam yace '' gani nayi yawon ki bana kare bane shi ya saka nace bada kudina ba wallahi cefane kuma ina yi muku iya daidai karfina sai dai rashin godiyar Allah irin naki, wallahi a kullum dana sanin auren ki nake.., ahayye ras cas kas to mana ka sake ni sai a raba gadon ya'yana a bani idan kana da guri ka yanki naka idan kuma baka dashi ka ƙara gaba wallahi jibe ni cas dani kana sakina, wallahi saurayi zan aura me jini a jika na mori kuruciya mu yini mu kwana muna sunna. kasa cewa komai yayi ya shiga daki domin halin inna yana saka shi a cikin tunani gaban yar ta , take fadar haka shi ya saka ga ya'yan su ne gaba ki ɗaya babu na Allah be sani ba ko yanzu aure ya gyara jawa, daman ance wanda be ji bari ba , ba yaki gani ba iyayensa basa so haka ya aure ta da zummar zai musuluntar da ita zai yi shahada irin su ake son aura gashi nan abu yana bin ya'yan sa a haka ma tun da ran iyayen sa ta nemi afuwa. kuma sun yafe mai shi ya saka a kullum jan hankalin sa ga matasa su dinga yiwa iyayensu biyayya ba abin da iyaye zasu kawowa ɗan su wanda zai cutar dasu sunfi kowa sanin me ya dace da ya'yan su. Ya Allah ka bamu ikon yiwa iyayen mu biyayya wa yanda suka rigamu gidan gaskiya Ubangiji ya saka aljanna ce makomar su. mu da namu suke raye Allah ya azurta su da lafiya yayi musu nisan kwana me albarka ya bamu ikon yi musu biyayya idan tamu tazo Allah ya saka mu cika da imani. amin summa amin 🤲🏻🤲🏻 yana zaune yana wannan tunanin yaji tayiwa humaira sallama ta fita. *★*★*★ ABUJA OSOKORO. ASIBITI. 3:00 aka fito da Jawaher daga dakin theater agwanin ban tausayi duk an like mata jiki da bandeji wuyanta ma wani abu suka saka mata ya tsaya chak kikam. shiga da ita daki aka yi..su deeya suka shiga dakin suna ci gaba da kuka Samuel yace '' idan baku dena kuka ba zaku fita a yanzu bata san karar komai.., tsit suka yi suka nemi guri suka zauna. fita yayi yana cewa ya kamata mijin ta ya zo domin muna bukatar sa da gaggawa... kallon kallo a ka shiga ba wanda ya , iya ce mai komai har ya fita. Na'ilah tace '' deeya taso mu tafi gurin aikin sa domin ina tunanin ba me number sa a cikin mu.., a'a ina wayar ta cire layin

Chapter 17 of 20