yana son tuno waye da waye ya gani daga bagaren maamah?.
Bai samu nasarar kaiwa qarshen tunaninsa ba knocking da aka yiwa glass din motar ta sakashi bude ido,ya ganshi farouq ne,yana daga kwancen ya danna remote ya bude mass murfin.
Dubansa yayi sanda yake qoqarin shigowa
"Reception zamu wuce.... Already wasu sun fara yin gaba,musaddiq da saddiq tun dazu suna ta wajen". Shi sai a sannan ya tuna ma.baiga kowa cikin su ba,ason ranshi farouq din ya barshi ya koma masauki ya kwanta ya rama baccin dake.kansa,ya kuma rage hayaniyar mutane da yakeji har cikin kansa,saidai kuma ya sani koda yace zai masa bayani ma farouq din ba fahimtarsa zaiyi ba,yadai fadi abu daya
"Ina fatan daga can duk wata hidima ya qare baku qirqiri komai ba kuma......don bazan iya jure zuwa wajen komai ba".
" Wanda baisan halinka bane zai wahalar da kansa shirya wani abu......walimar.ma saboda cika sunna ne da neman albarkar auren" Farouq ya amsa masa yana daga kiran abokinsa da yake gaya musu sun isa wajen
"Muma muna dab......ka jirani" Yace yana sauke wayar. Siririn murmushi kawai fuad ya saki,farouq.....farouq..... Idan ba farouq babu shi.......kaman yadda yasan idan babu shi babu farouq din.
Tunda momma bahijja ta tilastata tayi wanka,ta kuma shirya cikin wata sabuwar atamfar Hilton wax. Cikin kayan da momma ta zare cikin lefen ta bayar aka dinka ba tare da sanin sabreen din ba. Tun tana shiryawa taji shigowar uncle abdulhakeem da tun jiya suka iso suka kwana a tahir guests palace. Zancan duka ya shafi aurenta ne,wanda duk kalma daya da zata fita daga bakin uncle din nata sai taji kanta ya wani sara mata. Zazzafan mutum ne da ta jima bataga mutum me zafi da kafiya akan gaskiya ba irinsa. Ta jima tana tunanin idan ta kammala deal dinta ta tashi matsawa daga gurbin da take zuwa wani ta yaya zata bacewa idanunsa?,ta kuma zullewa duk wata tuhuma tashi?. Taji ya ambaci sunan su huda da nadra da tafi sati tana tunanin ina za'ayi da rayuwarsu?,amma tasan tayi kadan ta tsaya gabansu ta musu wannan tambayar,bata kuma samu jin abinda suke cewa ba sanadiyyar hayaniyar yan tafiya daurin auren data qaru. Ta gama shiryawar taji wani zazzabi ya sauko mata bayan ciwon kanta daya dinga gaba gaba saboda tunanin data matsawa kanta dashi,sai kawai ta lallaba can gadonsu nadra dake qarshe ta haye can ta qudundune.
ððŪð§ðĒðēððð ð§ð ðĪðŪððĒ ð§ð
ððððððððððð
ð ð ð ð ð ð ð ð
ðĄðĒð§ðĒð§ðĒðĢðŠðšðĒðģ
ĖķBĖķOĖķOĖķK Ėķ2
âą§ÉâēÉâĨâģ
ððžðð 10
Page 10
Can cikin tsakiyar kanta maganganun mutane ke mata yawo sanda motar ke tafiya cikin nutsuwa saman lafiyayyar kwaltar dake shimfide a kanta. Muryoyin mutane daban daban da sukayi mata fadan shiga gidan miji wai a cewarsu
"Allah yasa dai ki iya zama......don zaman aure daban da zaman bariki,zaman gidan miji daban da yawon bariki" Muryar bibo kenan da nata salon fadan da yafi kama da turun mutuwa
"Da dadi ba dadi kiyi haquri ki zauna......Allah yasa mutuwa ce zata raba,kiji kiqi ji,ki gani kiqi gani" Muryar daada kenan wadda ta kama hannuwanta tana fada muryarta a sanyaye. Ko da can ba zatace ga wani mummunan abu da daada ta taba musu ba,ita dai barta da shariya da rashin shiga lamari da sabgar kowa cikin gidan. Idan ka ganta kuwa a ciki to tabbas abu yaci tura,amma bibo da yaabi koda dan wani akeyi suna iya ara su yafa tun usul.
"Mommaa......nadra.....haneefa.....huda" Sunayen data iya kirawa momma kenan sanda take yunqurin sakata a cikin motar da zata yi musu jagora zuwa inda zasuje.
"Ina sane dasu......kuna su din ba nauyinki bane" Ta amsa masa a tausashe.
Ta cikin lafayar jikinta take iya hangen yadda motar ke tsala gudu abinta,amma saboda lafiyar motar da irin tsarin da akayi mata zaka rantse ba gudun takeyi ba.
Ta maida idanunta ta lumshe,wasu hawaye da batasan sanda suka taru ba suka biyo kuncinta suka diga bayan hannunta dake ajiye saman cinyarta. Har yanzu dai ta kasa gasgata abinda take gani,har yanzu ta kasa gasgata abinda kunnuwanta da zuciyarta ke nanata mata.
Da gaske mutumin nan yaci galaba a kanta da dukka tsarikansa.....da gaske shike da nasara ba ita ba.......da gaske ya cinye wasan a wannan gabar.....saidai kuma hakan baya nufin zaita nasara kenan a kanta,hakan baya nufin ta fadi kenan har abada.....lallai zata canza labarin......zata canza qaddarar da dukkan iyawarta.
"Gidan mamarshi zamu fara shiga.......sai gidan riqonsa,kamar haka matar data shigo dazu tace ko?" Daada ta fadi tana dan duban momma bahijja da hannun sabreen yake cikin nata.
"Eh haka ne" Ta amsa mata idanunta sauke kan faffadan sabon gate din gidan maamah dake nuna zallar dukiyar dake narke cikin gidan.
A nutse jerin gwanon motocin suka cusa kai makekiyar harabar gidan data kasance mafarkin maamah na shekara da shekaru,gidan daya dauki hankula da bakunan dukkan jama'arta dake hulda da ita. Gidan da a cikin ranta ita kanta ta gamsu da dukiyar daya lashe,amma zuciyarta bata gama nutsuwa da hakan ba saboda har yanzu gidan alhj hamza kibiya da iyalinsa yafi nata girma yalwa da kuma tsari,ba tare data duba yawan da suka darata dashi ba,da kuma yawan al'umman da gidan ke dauka suke riqo a yanzu haka.
Tunda motar ta tsaya a parking lot na gidan gabanta yake wani irin faduwa,ta maida idonta ta lumshe tana sauraren bugun da zuciyarta keyi da bata taba jin irinsa ba,sai taji bugun har kusa da maqogoronta. Sake runtse idanunta tayi sanda momma bahijja ke fadin ta fito,tana jin bugun zuciyar na sake daduwa amma kuma ta rasa me ya kamata ta karanta?,wacce addu'a ce ta dace da irin wannan yanayin da takejin kanta a ciki?.
Riqon hannunta da momma din tayi shine ya sassauta mata abinda takeji kadan,ta sake riqe momma din itama da kyau ba tare tasan ta yadda zata gaya mata abinda takeji cikin qirjinta ba.
A dan hanzarce ta shigo dakin nata,sannan ta maida qofar ta kulle ta kuma murza key. Da dan hanzarin still ta isa gaban madubin nata dake manne da wasu lafiyayyun lockers. Ta murza daya daga ciki ta bude ta,sannan ta saka hannu ta ciro baqar ledar dake a ciki ta dora saman madubi. Ko ina a jikinta amsawa yakeyi da wani irin doki da son fara aiwatar da nata aikin,a yau batasan sau dubu nawa tana addu'ar samun wannan sa'ar ba......batasan sau nawa ta roqi samun nasara a wannan ranar ba,nasarar da indai ta rasata kamar wadancan kwanakin ta tabbatar komai zaizo mata da wahalar gaske.....batasan kuma ta yadda zata tari abun ba.
Kusan leda shidda ce,kowacce sai data kunceta sannan ta saka hannu ta fara ciro kayan ciki. Kusan tarkace ne a idanun me kallo,amma a wajen maamah gwara rashin million dubu da rasa daya daga cikin kayan. Wasu kwalabe ne masu dauke da wani irin baqin abu a ciki,wani kuma kore kore ne,saidai yana da dan qamshi qamshi kadan a ciki mara qarfi. Ta bude kowanne ta tsiyaya cikin tafin hannunta,ta kuma mulke hannun nata da kyau kamar yadda aka umarceta da tayi,sannan ta maida komai muhallinsa kamar bata taba komai ba cikin dakin.
Gaban madubin ta tsaya tana qoqarin controlling kanta da daidaita nutsuwarta. Idanun ta fes cikin fuskarta tana maganar zucci da kanta da kanta,wanda batayi wani nisa ba knocking din da ake mata ya isa kunnuwanta. Adan fusace tace tambaya don bata buqatar doguwar mu'amala da kowa har sai wadda tayi shirin saboda ita ta iso
"Zuwaira ce" Ta bata amsa a tsanake.
"Sun iso,suna falon qasa sun......."
"Gani nan" Ta tari numfashin zuwairan ba tare data jira sauran bayaninta ba. Ba sauran bayaninta take da buqatar ji ba,tunda taji abinda take buqatar jin,ta waiwaya tana zura takalmanta data cire tare da kallon tsadajjen mayafin data lullube jikinta dashi ta tabbatar ya zauna a jikinta......ya sanyata tayi kwarjini da wata irin kamala da sam zai wahala ka kawo wani abu me muni a kanta. Kyanta ya bayyana.....kamanninta da musaddiq sosai,yanayin jin dadin da kulawar data samu wadda take rainawa ta sake sanyawa jikinta ya murje sosai,hutu da quruciya sun bayyanar mata.
Murmushi ta sakarwa kanta da kanta,sannan ta juya a hankali tana fita a dakin.
Tun daga saman stairs din take raba idanunta tana son hangota. Bata wani sha wahala ba,ta hangeta zaune saman lallausan carpet din da aka qawata tsakiyar falon dashi. Qafafunta a tanqwashe suke,kanta a qasa cikin shigar laffayar da tazo mahadin lace din da aka zauna akyi dukka adon jikinsa da hannu(handmade lace),kamar yadda lafayar jikinta itama duk wani zare da duwatsun jiki da hannu aka gameshi. Abune na masu dashi,ba wani cikar jama'a masu yawa ko cinkoso,kowa yana zaune a nutse,yayin da gaisuwa ke wakana tsakaninsu momma da jama'ar da suka samu cikin falon.
Da wani irin kirki na gasken gaske saman fuskarta,faffadan murmushi da fara'a me nuna tsantsar maraba da baqo ta iso rukunin kujerun tana furta
"Lale maraba......sannunku da zuwa......sannunku da qoqari" Da murmushi a fuskar momma ta amshe maraban tana duban maamah tsaf tare da karantar yanayinta.
"Bari na zauna kusa da diyata" Ta fadi tana zama kujerar dake kusa da sabreen din.
Gaisuwa akayi cikin mutunci dason nuna ainihin zallar kirkinta,suka gabatar mata da amanar sabreen tare da dan qaramin jawabin girmama kowa ga sabreen din
"Itama diyata ce ai tunda yarona take aure,kuma in sha Allah zakuyi alfahari da hada alaqa damu,Allah ya bada zaman lafiya,shi kuma Allah ya tayashi riqo" Maamah ta furta cikin zaquwa da gajiya da bayanan. So take kawai ta isa ga muradinta.
"Am nace ba.....idan ba damuwa inason ganin diyata a kebance,minti biyar don Allah" Maamah ta fada tana murmushi. Ba tare da tunanin komai ba ko kawo komai ba momma bahijja tace
"Bismillah mana......haba hajiya ai diyarku ce" Daada ta fadi yadda momma din ta karbi sabreen yana burgeta.
Duk da tayi gaba zuwaira ke mata jagora zuwa wani daki na daban a saman benen.....amma saita dinga jin wani irin yanayi yana bibiyar gabobinta.
Kasa zama tayi,tana a tsaye sanda taji zuwaira taja musu qofar ta fice.
"Zauna mana.....ki yaye wannan lullubin kan naki......don fahimtata nakeso kiyi sosai tamkar yau ne karon farko da kika fara fahimta ko haddace wani abu a rayuwarki" Tayi maganar cikin jerarrun kalmomin da kana jinsu zakasan ko meye zata fada yana da matuqar muhimmanci a wajenta.
Sai data fara janye lullubin nata baya,sannan ta sulale a wajen ta zauna. Tana jin kamar babu wani sauran qwarin gwiwa daya rage mata a rayuwa,duk da yadda take kokawa da zuciyarta da qoqarin qarfafawa kanta gwiwa.
"To alhamdulillah.......komai ya kammala,kuma komai yazomin da sauqi fiye da yadda nayi zato ko kuma tsammani........ina fata baki manta meye manufar aurenmu ba?" A nutse sabreen din ta daga kai sannan ta zube mata idanunta saman fuskarta. Kallonta tayi na second kusan goma sannan ta gyada kai
"Da kyau.....da farko abinda zan fara gaya miki shine abinda na maimaita miki a baya.......qaidar contract dina na farko shine sirri.......inason sirri,don muddin aikin nan ya fita daga da'irar sirri zuwa wata da'ira ta daban.....to tamkar kin wargaza rayuwarki da hannunki ne......bayan taki rayuwar da kika wargaza kuma......kin wargaza ta 'yan uwanki suma...." Daga ma maamah hannu tayi da hanzari tana zare idanunta daga kanta
"Ki tsaya iya kan ameenatu kawai......huda,nadra da haneefa,tabasu ko sako sunansu cikin sabgarki da ameenatu tamkar ganganci ce"
"Da kyau!" Maamah ta furta tana sakin murmushi,abubuwa biyu zuwa uku suna jan hankalinta. Gyara zamanta tayi tana ci gaba da murmushi
"Ashe ameenatu ce....abu yayi kyau..ameenatu ta bata,wata ameenatun zata gyara,wannan abun yayimin dadi.......qwarin gwiwarki da rashin sarewarki ya burgeni......kariyar da kike bawa qannenki tana da yawa,kuma ita dai ta isa ta bani yaqini da tabbacin ba zaki bari a samu failure ba ko don saboda su......."
"Shiga maganarki kai tsaye" Sabreen ta fadi mata tana kauda kanta zuwa wani sashe na daban. Idanu maamah tadan zuba mata har yanzu tana murmushi,sai kuma ta miqa hannu ta zaro wata paper da abun rubutu ta ajiye a gabanta.
"Inaso ki rubuta adadin kudaden da kike da burin mallaka a rayuwarki......ni kuma zan mallaka miki su a madadin sadakin aikinki,zan kuma qara miki kwatankwacinsu muddin komai yayi daidai".
Fararen manyan idanunta ta daga ta watsawa maamah su,karon farko da idanun suka yiwa maamah din wani kwarjini da bata taba jin irinsa ba. Murmushin da ya subuce kuma a fuskar sabreen ya sanya mata kokwanto
"Ki fadi magana me muhimmanci saboda mutanen dake zaman jiranki a qasa" . Maganar tata tadan daure mata kai,a nata ganin ba wata magana da zata zama me muhimmanci a wajen sabreen sama da maganar kudin aikinta,wanda take ganin shi kadai ya isa ya bata azama akan aiwatar mata da komai. To amma akance......shi yaqi dan zamba ne,don haka ta gyada kai
ðððŧðķððŪððŪ ðŧðŪ ðļððąðķ ðŧðē
ðŽðīððīðģðŪðąðąðīðēðŪ
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels