yatsunta dake dauke da dan baqin lalle dan kadan saman farcenta,ragowar lallen data yiwa adon yatsunta wata biyu baya da suka shude.
"Zuba......amma kada kisa miya.....mai zaki saka da dan maggi kadan" Ta yiwa huda bayani a taqaice tana zare idanunta daga sashen da suke. Sauka idonta yayi kan wayarta dake ajiye wadda a qalla ta kusa kwana biyu a wajen. Sam bata da sha'awarta ma don batajin zuwa yanzu tana da wani uzuri da ita. Jib,ayshatu,qannenta da sauran mutanen da takejin sun Ta'allaqa a wuyanta kadai zuciyarta ke mata amsa kuwwar ta nemesu.......tayi sallama da kowannensu.....saidai kuma wani sashen daban yana bata qwarin gwiwar bata da buqatar hakan!. Tana ji a rai zuciya dama jikinta tamkar wani gajeran balaguro ne kawai zatayi daga tata duniyar zuwa wata duniyar,balaguron da bai wuce misalin qifatawar idanu daga rufewar zuwa budewar ba. Bataji kwata kwata cewa wai auren zai zama wani dogon aiki da zata kasa yakiceshi cikin qanqanin lokaci. A yanzun zata zubawa komai da kowa idanu.....kwadin me kwadayi......burin me buri......da tsarin me tsari a kanta ya kwanta.....sannan ne ita kuma zata aiwatar da nata shirin hankali kwance( nikam nace uhmmm....qaddara dai ta rigayi fataπ₯Ίπ).
Da plate huda ta dawo,wanda tsara zuba abincin gwanin sha'awa. Sabreen tasan duka tayi ne don taci,ta jera soyayyen kifin saman shinkafa da waken,sannan ta mata roban yaji da magi daban. Da kallo kawai tabi plate din,don tasan yafi qarfinta koda duniya ma tana kwance bare yanzu da wani abu waishi abinci baya burgeta.
Sallamar kawu rufa'i da sautin muryarsa kadai ya sanya abincin data sanya a bakinta ya tsaya mata cak a maqogaronta,sauran na bakinta kuma taste dinsa ya canza mata,har tana jin ba zata iya taunawashi ba,har sai data tattara dukkan juriyarta sannan ta tauna ta turashi zuwa maqogaronta wanda ta samu ya wuce da qyar,sai kawai ta yanke hukuncin ajiye abincin. Idanunta ya sauka kan kawun sanda take ajiye plate din a qasa,wanda yake jaye da wata mini luxury luggage me azabar kyau da kuma daukan idanu. Koda bakasan me duniya ke ciki ba,koda bakasan darajar abinda yake janye dashi ba tabbas zata fahimci luggage ne me tsada da madaukakiyar daraja.
Wajen zama mamma bahijja tayi masa tana sanya nadra ta ajiye masa drink da ruwa.
"Ya hidima ya kuma shirye shirye?" Kawun ya furta da muryar dake nuni da zallar farincikin da yake ciki
"Alhamdulillah.......ai kune da hidima,tunda mu nan ba abinda zamuyi" Kai kawu rufa'i ya girgiza yana satar kallon sabreen da tunda ta gaidashi bata sake koda kallon sashen da yake ba.
"Allah ya yiwa yarinyar nan taurin kai bahijja......idan kinga abubuwan da sukaso gabatarwa zakisha mamaki......har yanzu quruciya ke dawainiya da ita,inda tasan girman matsayi da darajar mutumin da zata aura,na rantse miki saita qare rayuwarta tana godemin.....attajirin matashin da babu irinsa a wannan qarnin da muke ciki?" Dan murmushi kasan momma bahijja tayi,adan zamanta ta fahimci kawun yana sa son abun duniya
"Duk bama wannan ba rufa'i,indai har bincikenku ya tabbatar da nagartarsa ai magana ta qare.....dukiya wannan wani abune na daban ai"
"Habawa.....idan ana batun nagarta ma da dattako har ayi magana wadannan dattijan?"
"To alhamdulillah.....haka akeson ji...."
"Yanzu haka ma aike ne......saqo ne na musamman daga surukarta......kaya ne tace a kawo mata da zata sanya a gobe kenan"
"Tofa.....ikon Allah,kuma dai?,basa gajiya?"Momma bahijja ta fada duba da irin kudaden da aka narkar,tun daga dukiyar aure har izuwa batun lefen dasu kansu har yanzu basu gama sanin komai da komai dake cikin akwatunan ba. Tana qara ganin girman qaunar da suke gwadawa sabreen din,a gefe guda har ranta tana jin tamkar sabreen din tayi sa'ar inda zata rayu cikin qauna da kulawa.
"Wai wai.....ma sha Allah" Momma bahijja ta furta tana daga lafiyayyen applique lace da kudi suka koka qwarai wajen siyensa. Daga qasanshi kuma wata bazin ce data amsa sunanta sai super Sheraton da iya ado da gayu da kashema kai kudi irin na momma bahijja bata taba katarin ganin irinta ba. Daga qarshe set ne na banguls earrings da sarqa da zobensu duka na danyen gold me matuqar daraja(nikam nace masu abu da abinsu).
Ko qwaqwqqwaran motsi sabreen batayi ba ballanta ta daga kanta ko zata nuna alamun tasan bidirin da akeyi,har sanda hadiyya tayi sallama tana shigowa falon da guntuwar fara'arta.
Sunan kayan kawai ya gaya mata darajar abinda aka sako a ciki saidai hakan bai dadata da qasa harta daga kai ta basu darajar kallo ba,don batajin zata iya rabasu a jikinta. Komai daya fito daga hannunsu duhu yake mata,baya mata haske ko kadan.....musamman da take kyautata zaton kayan sun fito ne daga hannun waccar matar maras daraja. Still shigowar hadiyya bata sakata daga kai ta dubeta. Can qarshen zuciyarta danqare da mamaki,yadda kudi ke iya sauya dabi'un mutanen duniya cikin qanqanin lokaci,duk da wannan karatun ta jima da haddaceshi......kusan shi ya zama sila na sauyawar DUNIYARTA.
Hadiyyan ta sauya kamar ba ita ba,abinda bata taba tsammanin zaya faru nan kusa ba. Bata zaqe da yawa ba wanda tasa tasirin karatu ne wala'alla da salon gogewa......hakanan kowanne taku kadan tana yunqurin kutsa kai jikinsu ne.
Hadiyya ita ta qarasa daga kayan matsanancin mamaki yana sake kasheta. Hidima sosai suke gwadawa sabreen din kaman rijiyar kudi garesu. Ba wanda yakai me kudi sanin darajar kudi,saidai ga wadannan bataga alamun hakan sam daga garesu ba.
"Gashi zakiyi magana da surukarki" Momma bahijja ta fada tana sauke wayarta daga kunne gami da miqawa sabreen. Dan turus tayi tana sauke fararen idanunta akan fuskar momma bahijja din. Muddin wannan matar ce sam bata da sha'awar wata magana da ita. Komai nata bisa gadara ne iko izza da kuma nuna qarfin dukiya,don me zata zauna tana gwada mata tata izzar bayan ba ita ta gayyaceta cikin rayuwarta ba.
Idanu sunyi yawa a kanta,don haka ta sanya hannu ta karba tana kauda fuskarta daga kallon idanuwan.
Sallamarta kadai ya gaya mata ba wadda take zato bace,cikakkiyar sallamar data saukar da duk wani zafi da zuciya da kuma halshenta suka dauka,saita amsa mata a nutse matuqa
"Kina yini lafiya diyata?" Anni ta fada daga nata bangaren jin sabreen din tayi shuru. Karon farko sai taji nauyin matar ya saukar mata,batasan me yasa a iya waya kawai takejin girma da kwarjininta ba......shin itace asalin mahaifiyarsa ko yaya?.....itadin wacece a wajensa?,waccan ma wacece a wajensa?. Iya wannan tambayoyin da bata da amsa kadai suna sakata a jikinta tana jin tabbas akwai wani gagarumin abu birne a qasa.....duk da zuciyarta tana gaya mata ba wani babban abu bane da zai gagari sarrafawarta ba.
"Barka da yamma.....lafiya alhamdulillah" Ta hade gaisuwar da amsar tambayarta.
"Ma sha Allah"
"Naga saqo,na gode" Tayi hanzarin fada,don a cikin ranta takejin bai kyautu ba har sai ta magantu.
"Ba komai......inaso ne kawai kiyimin alfarmar sanyasu a duk sanda zaki shigo ahalinmu" Tayi maganar a tausashe cikin kuma nuna kulawa,kulawar data bayyana kanta sosai cikin sautin muryarta
"In sha Allah" Ta sake amsa mata
"Ina fatan hakan ba takura?"
"Ba komai....in sha Allah"
"To alhamdulillah......ina roqon ubangiji ya tattara dukkan alkhairanku ga junanku......ya kauda kowacce irin fitina da abunqi a tsakaninku". Batasan me yasa ma......amma har tsakiyar qirjinta taji saukar addu'ar......batayi kuskure ba idan tace kunnuwanta itace mutum ta farko data fara jin addu'ar daga bakinta,sai taji labbanta sunyi nauyi bare su tallafeta ta amsa.....yayin da anni tayi zaton kunya da kawaici suka hanata amsawar......a haka tace ya baiwa momma din wayar.
Zuciyarta tayi nisa qwarai da zurfi wajen tunani,har batajin ma meke wakana cikin falon,sai kawai ta yanke nesanta kanta dasu ta hanyar komawa daki kaman yadda ta maida hakan dabi'arta.
Bata jima cikin duniyar dakin data maida mazauninta ha nadra ta shigo dauke da wayarta a hannu.
"Ana kiranki" Ta fada tana miqa mata wayar. Kamar tace mata ta koma da ita sai ta fasa,ta saka hannu ta karba tana daga kwancen tana duba me kiran.
Sunan data gani ya sanyata miqewa ta zauna sosai babu shiri,hannunta na gaggawa wajen amsa kiran ta sakashi a kunnenta
"Kicemin kun dawo titi don Allah,kicemin ayshatu ta warke"
"Na warke adda......na samu sauqi" Muryar yarinyar ya saukar mata a kunne. Wani hawaye me sanyi ne ya kubce mata,kullum da lamarin yarinyar take kwana take kuma tashi,daga yadda taji muryarta tasan cewa tabbas lafiya cikakkiya ta samu a gareta
"Muna cikin sabon gidanmu yanzu aunty.....na gayawa titi bazan yarda na fara ganin kowa ba sai ke".
"Yanzu kuwa zaki ganni ayshatu" Ta bata amsa kai tsaye kaman ta manta a wanne yanayi ita din take.....kaman ta manta rabonta da taka qasar waje wasu kwanaki ne masu yawa.
Da wani irin excitement ta ajiye wayar,ta zura qafafunta qasan gadon da hanzari zara miqe da nufin shiryawa,sai kuma ta dakata cak saboda dawowa hayyacinta da tayi.
Tayi imanin wadannan mutum mutumin har yanzu suna tsaye a qofar gidansu suna gadinta,yawan mutanen dake kai kawo a gidan bai sanyasu sun tafi ba......don ko dazu ita iya jiyo baqin tsagin abbansu suna tambaya a kansu.
"Saina fita kota halin qaqa wannan karon......ko meye zai faru saidai ya faru" Ta fadi tana qarasa saukowa,ta kuma fito kai tsaye zuwa ga falon tana nufar doguwar veranda din dake saman wanda tacan zata samu hanyar gangarawa qasa ta koma ainihin dakinsu.
_DUNIYA TA na kudi ne_
08187255862
π π π π π π π π
π‘π’π§π’π§π’π£πͺπΊπ’π³
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 6
Page 06
Batasan gidan ya fara daukan mutane ba sam sai data sauko din. Gomayyar idanuwa sukayi kanta caaa ana qare mata kallo. Kowa da nashi tunanin cikin ranshi,wasu na kallon tsantsra kyan data qara saboda gyaran jiki na musamman data samu tsahon kwanaki daga wajen qaararriyar me gyaran jiki......wasu kuma na mata kallon sha'awa suna fadin inama su ko 'ya'yansu keda wannan sa'ar ta auren irin mijinta?,yayin da wasu nasu kallon na bin qwaqwafi ne hassada da tarin tambayoyin ta yaya KARUWAR GIDA.....WADDA TA GAMA RABA MUTUNCINTA WA MAZAN TITI TA SAMU BABBAN MUTUM.IRIN MUHAMMAD JADDA DIN?.
Miskilanci da shariya kusan cikin jininta suke,don haka tayi kaman bata gansu ba ta wuce dakinsu kai tsaye.....ballantana kusan dukansu tana cike dasu. Ba wanda yabi takan rayuwarsu.....qaqa suka kwanta qaqa zasu tashi?,amma sai gasu yanzu zube da sunan sunzo auren yarinyar da basusan yaya ta girma ba?,me taci har takai wadannan shekarun?.
A gaggauce ta shirya cikin wata luxury Egyptian abaya datayi masifar karbarta,wadda inda cikin nutsuwarta da hayyacinta take itama ya kamata ace taga yadda rigar ta karbeta.
Tun daga nesa kana iya ganin mugun kyan da fatarta tayi,wani irin haske da glowing kawai takeyi,saika rantse da Allah diyar wani hamshaqin ce. Qaramar handbag kawai ta dauka ta jefa wayarta a ciki da dan canjin da zata riqa saboda mota,ta fito daga dakin a nutse tana isowa falon,daidai sannan momma bahijja ta shigo rungume da dinkakkun atamfofin da tasa aka dinkawa su haneefa duk da tarin suturunsu.
"Ina zuwa kuma?" Momma din ta jefa mata tambayar tana kallon yadda take komai a gaggauce. Batasan da wanne harshe zata yiwa momma bayanin aysha da muhimmancinta a wajen ta,don haka a taqaice tace
"Dubiya zani momma...."
"Zuwa ina?.....kuma dubiya a irin wannan lokacin?" Kai ta langabe kadan tana fargabar kada momma din ta hanata fita,don a irin wannan lokacin ita kadai takejin zata hanata fitar ta hanu
"Ba niss momma.....ba jimawa zanyi ba".
"Nadra ta rakaki,kuma kada ki wuce awa daya" Ta fada tana qarasawa tana zube dinkunan hannun nata saman kujera.
Mayafi kawai ta figowa nadra,ta sanya wasu plate shoe nata sannan suka fito. Sam bata damu da yadda idanuwa keci gaba da binta da kallo ba,har wasu na qoqarin gaisawa da ita,a haka ta doshi qofar gidan nasu tana tsara yadda zata kaya tsakaninta da qedarun da aka tsaida a qofar gidan.
Tana takawa zuwa qofan tana jin fargabar yau dame zasu zo mata?,don dai yadda takeji a ranta yau koda sama da qasa zasu hade sai ta fita.......don ba wani mahaluqi daya taba saka mata dokar zama cikin gida har haka tsahon rayuwarta......sai yau gashi sama ta ka wani mutum can da baisan ciwonta ko darajarta ba......yanason yayi amfani da giyar kudi ya yiwa rayuwar karan tsaye.
Tana tura qofar yana riqeta kana aka qarasa budeta. Fuskar kakkauran mutumin ta bayyana har abun yana bawa sabreen mamaki. Bata taba kawowa a lokacin irin wannan zata sameshi tsaye bakin qofar ba kamar wanda aka tsaiguntawa zata fita......waisu basa zama?,ko basa hutawa da jiddin suna tsaye suna gadin duk wani motsinta.
"Good evening madam" Abdulgaffar ya furta cikin matuqar girmamawar nan da suka saba mata magana da ita saidai kuma a dabarance yana matse kowacce hanya da zata iya rabawa ta fice daga gidan.
Ta gama karantar motsinsa kaf.......bata wani damu da gaisuwarsa ba ta azawa fuskarta wani irin halakakken bacin rai da kuma d'aurewa
"Kiramin boss dinku" Ta bashi umarni nakai tsaye da wani irin sauti da babu wasa ko kadan a ciki. Tanaso ta gwada musu girman abinda zata iya aikatawa.......tanaso ta gwada musu basu ba......koda boss dinsu ma bata daukeshi da wani tarin muhimmanci ba.
"Bani da connection dashi......idan zan kirashi saina jira anyimin iso kafin na samu magana dashi......amma ga jordan zai kira miki shi" Abdulgaffar yayi mata bayanin cikin girmamawa yana matsawa da baya.
Can qasan ranta mamaki yake kamata,wanne irin girman mulki da izzar kudi gareshi da har yaransa ma ba kowa da kowa keda daman magana kai tsaye dashi ba
"Good evening madam.......kiyi haquri ki jira kadan,yanzu in sha Allah zai amsa" Jordan ya fada yana rusuna mata. A ranta tanaso ta gaya musu ne a fili
"Qattin banza.....kun zauna kuna yiwa mutum qwaya daya bauta saboda yana da dukiya" Abinda zataso gaya musu kenan ganin yadda jordan ke lalubar muhammad fuad jadda cikin girmamawa.
A lokacin yana tsaka da hada duk wasu muhimman abubuwa nashi da kanshi,ba tare da ya bari hidiminsa ya masa ba wato me sunan malam. Akwai wasu abubuwan da da kanshi yake yinsu,duk da tarin hadiman dake gareshi. Yana sanye da fara qal din t.shirt me laushi Vshape neck,hannunta iya dantsensa wanda hakan ya sanya murdaddun damtsensa dake nuna girman daga qarfe da yakeyi suka bayyana,wandon jikinsa ma farinne duka duka tsahonsa iya qaurinsa,sai lausasan fararen flip-flops masu tsananin haske da taushi.
Cikin kowanne irin yanayi tsarinsa na dabanne,kai tsaye zaka iya cewa gayu ya ratsa jikinsa da gasken gaske.....koda kuwa bacci zai shiga zaka sameshi neat....komai nashi kuma completed kai kace ba bacci zai kwanta ba. Yadda yake a nutse cikin wani irin tsari haka komai nashi yake kasancewa,waya.yake amsawa wadda ya sakata a hands free ya ajiye saman wani zagayayyen kujera me siffar qwallo dake a gefe. Kadan ya kalli wayar,sai ya fahimci kiran jordan keson shigowa amma yana buqatar izinin haka,don haka ya katse wancan kiran ya bawa kira jordan din dama
"Barka da wannan lokaci sir" Jordan yayi maganar cikin girmamawan data bata ran sabreen,ta cika fal da mamakin wanne irin ban girma ne haka kaman yana a gabansa?,ya kasa miqewa da dukka tsahonsa ya amsa wayar.
"Yauwa Jordan......ya akayi?" Ya tambayeshi kai tsaye. Sai daya dan daga idanu ya kalli sabreen din da idanunta ke cike tab da fushi,sannan qasa qasa yace
"Madam daka tura a yiwa aiki ce keson magana dakai sir"
"Madam?" Ya tambaya yanason tuna abun don ba komai yake baiwa muhimmanci ba
"Eh sir....."
"Bata wayar" Ya umarceshi kai tsaye don ya tuna inda zancan ya dosa.
"Ka matsa a wajen idan ka bata" Ya sake fadiwa jordan don bayason yayi involving yaransa cikin abinda bai shafesu ba.....hakanan yana ganin ba girmansa bane su fahimci komai ba.
Kaman ba zata karba wayar ba don tana jin kamar ta zuba a qasa data nema magana dashi......saidai kuma girma da martabar inda zataje din ya shafe komai a idanunta,don haka ta sanya nadra ta karbo wayar daga hannunsa sannan ta karba a hannun nadra din,ta taka a nutse tana dan komawa ciki duk da jordan ya matsa daga inda zai iya jinta.
A kunnenta ta kara wayar,saidai har kusan shudewar mintuna guda tim ba wanda ya cewa da dan uwansa komai.
ππππππ ππ ππͺπ΅π΅π’π§πͺπ― π¬πΆπ₯πͺ π―π¦
08187255862
π π π π π π π π
π‘π’π§π’π§π’π£πͺπΊπ’π³
ΜΆBΜΆOΜΆOΜΆK ΜΆ2
β±§Ιβ²Ιβ₯β³
ππΌππ 7
Tana tsananin buqatar ta fita,ta kumayi imanin wadannan gumakan ba wanda zai musu magana suji sai wanda ya turosu.....tana jin kuma faduwar fara yin magana dashi. Sanda taji ya motsa da bisa alamun ajiye kiran zaiyi,a nutse ta bude baki ta soma magana dashi da qaramar muryar nan tata me wani irin tone
"Ban kasance daya daya daga cikin hajojin kamfaninka ba ballantana ka sanya min masu tsaro na......'yantacciyar d'iya ce kamar kowa,hakanan mutum ce dake da nata tsarin da qa'idojin da ba komai take jurewa ba......ka yiwa wadannan gumakan magana da suyi gaggawar matsawa subar qofar gidanmu". Tsayawa yayi cak da abinda yakeyi,ya harde hannayensa a qirji yana sauraronta da muryar dake nuna tamkar gargadinsa kawai takeyi kai tsaye.
Idanunsa ya lumshe kai tsaye na sakanni sannan ya budesu,yana ci gaba da jin qaramin sautinta dake magana cikin yanayi na tsiwa har sai data qarasa maganarta.
"Bakisan waye ni ba.....i can't tolerate it,dole ki koyi manners......bawai na zama dani kawai ba,manners akan komai ma,tabbas kina buqatar tarbiyya,Your attitude needs a serious adjustment.....and im not going to put up with anymore nonsense,I won't tolerate any more of your nonsense,its time to get in line" Yayi furucin harshly muryarsa cike da seriousness. Din din din da taji wayar nayi shi ya tabbatar ya yanke kiran. Ta sauke wayar daga kunnenta tana jin wani irin daci yana taso masa tun daga cikin maqogoranta har zuwa saman harshenta. Tabi wayar da kallo ranta yana mugun baci,tana jin maganganun daya gasa mata suna yawo cikin kunnuwanta.
Tana jin kamar tayi cilli da wayar ko zata samu sauqin radadin dake cisgar zuciyarta......to amma saita tuna idan tayi hakan bata kyautawa ainihin me wayar ba,wanda shima da alama komai nasa yana yine bisa tsoro da kyakkyawan bin umarni ba tare da sabawa ba.
"Kai mishi wayarsa" Tace da nadra tana miqa mata wayar,sannan ta miqe tana gyara jakarta tabi bayan nadra zuwa qofar gidan,tana jin yau saita nuna masa iyakarsa ta hanyar fita,idan yaso ya tashi duniyar a yau kowa ya huta.
Nadra ta rigata isa,ta bashi wayar dake ringing,yana duba me kiran yayi hanzarin dagawa tare da matuqar rusunawa yana fadin
"Hello sir" Idanunshi suna sauka kan sabreen,sai ya miqe yana sauraron umarni daga wayar yana kuma kallon sabreen wadda ke tafiya cikin tsananin fushi,har kuma ta samu nasarar sanya qafafunta a qofar gidan.
"......idan naga sabanin haka ka kuka da kanka" Qarshen maganarsa kenan data jawo hankalinsa zuwa ga sabreen wadda ta dauki hanyar barin layin sosai bata tsaya koda waiwayarsa ba ballantana wayarsa da yakeyi,tana jin bata da lokacinsu gaba dayansu.
Da sassarfa abdulgafar ya jefa wayar a aljihunsa ya juya da sassarfa yabi bayanta. Daga yadda yau boss din ya masa magana ya tabbatar akwai magana a qasa. He's speaking seriously,yasan abinda ya fada da gaske yake.
"Madam.....ah.....am,madam sorry......listen please" Ya furta bayan ya cimma bayanta. Nuna ma tasan yana biye da ita a wajenta bata lokaci ne,bata da lokacin batawa ta saurareshi daga shi har boss din nasa
"Madam please ki tsaya ki saurareni,am going to loose my job.....please listen to me". Maganar ya taba mata zuciya........yanzun nar rashin imaninsa yakai ace ya kori mutum bakin aikinsa saboda wani abu daban ya faru?. Daga yadda yake maganan kawai ya gaya mata da gaske yake fadi,don haka tadan sassauta tafiyar ba tare data kalleshi ba tace
"Ina jinka"
"Please madam ki koma gida.....kiyi haquri ba yadda muka iya.....haka boss ya tsara......"
"Wannan kuma bazai yiwu ba,idan baka da abun fada ka koma yafi maka sauqi" Daga hakan taci gaba da tafiyanta. A nutse take ratsa layin,yayin da idanun 'yan sanya ido ya soma yin caa a kanta. Ba yadda zaka kalleta ita da abdulgaffar din kace ba body guard dinta bane,saboda yake take mata baya yana maida takunsa duk inda ta dauke ba tare da sunsan abinda ya sanya ya biyota ba,take tsegungumi suka fara tashi,masu rade radi akan irin mijin da zata aura a yau suka samu tabbacin hakan
Da alama zazzafa ce itama tamkar boss din nasu,ya hanga ya hango babu wani sauran abinda ya rage masa illa ya kira oga farouq,don haka yana biye da itan yayi kiransa,yayi kuma bayani a taqaice.
"Turawa hood location ta watsapp...zaizo da mota ya kaita.....idan yazo din give me a call.....zanyi magana da ita" Yayi maganar haushin fu'ad yana kamashi.
A ganinsa tunda batu ake na aure koma meye ya kamata ya ajiyeshi a gefe,batun aure ya wuce wasa.....ya kuma wuce tunanin mutum.
Wani irin aiki ne da ake yinsa da umarni da kuma doka. Iya tsaiwar da tayi tana jiran ababen hawan da batasan dalilin da yasa duk wanda ta tsaida sai ya wuce ba.....wanda qwarewar aiki irin na abdulgaffar ya sanya yake musu alama me nuna gargadi kan tsaiwar tasu,take suke wucewa abinsu.
A hankali motar ta rage gudu tana qarasowa gabansu,wanda tun kafin takai ga qarasowar abdulgaffar ya ganeta. Motocin da dukka suka jibanci familyn muhammad jadda da kuma gidan alhj hamza kibiya ba boyayyu bane,don hatta da plate number dinsu na dabanne da wani irin kebantaccen tsari na daban.
Bai bari motar ta qaraso gabansu ba ya kirayi farouq din,sai komai yazo a daidai,isowar motar gabansu da kuma matsawa da yayi daura da ita ya saka wayar a handfree yadda idanunta zasu iya ganin wayar
"Ranki ya dade......Allah ya taimakeki,tuba muke,kunyi magana da boss yana cikin fushi ne.......ayi mana alfarma kiyi haquri,ga driver da mota nan ya iso,ki shiga ya kaiki duk inda kikeso,tuba muke,tuba muke" Ya maimaita har sau biyu yana hade tafukan hannayensa guri daya.
Batasan me ysaa ba,amma sai taji tasss ta sauka daga fushin da takeji. Yanayin maganarsu dama komai nasu ba daya bane,batasan kuma waye ba......sannan batasan nasabarsa dashi ba.....amma da iya lafuzan bakinsa kadai ta tabbatarwa kanta yasha banban dashi tako ina.
Batace komai ba ta soma takawa tana nufar motar da tuntuni suka wagale