Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
saman ya zama kusan nata,tunda aka fara mata aikin gyaran jikin ko qasan gidan bata saukowa. An killace muhallin da komai da zata buqata,kaman yadda aka ajiye mata cima kala kala wanda sam basu taba birgeta ba koda qanqani. Hasalima ita a yanzu cin abinci ya zame mata daya daga cikin horon da mamma bahijja keyi mata. Koda kuwa ta kauda kai ta kuma kafe akan ba zataci ba,mamman bahijjan data tsaya a bigiren da akan buqaci uwa saita nemo wani abu daban ta bata,takance "Aure zakiyi fa sabreena,gidan miji zakije,anata gyaran fata amma can cikin ko oho?,kinsan yadda yunwa ke kassara ni'imar mace kuwa?" A duk sanda ta furta hakan sai sabreen taji kaman wani abu ya shaqe mata wuya. Wai halan basu kula kuma basu lura da dukkan komai?,sunata magana akan auren da ba komai a cikinsa face zallar rudani?,rarrabuwar burika da kuma tarin biyan buqatar rayuka masu yawa a cikinsa?. A yanxun data dawo daga dauraye jikinta da tayi daga gyaran jikin da kullum kwanan duniya takeji kaman ana mannawa fatarta wuta.....duk inda ta gifta kota zauna wani irin fitinannen qamshi take barwa gurin. Wani irin mayen qamshi me matuqar naci da mannewa jiki dama dukkan wani abu da mutum zaiyi mu'amala dashi. Qawatattun idanun nan nata da a yanzun suka koma rusunannu ta daga a nutse tana duban me gyaran jikin dake faman gyara wutar da zata sake turareta da ita. Ta zama wata kurmar qarfi da yaji,magana na mata wahalar gaske,kwanyarta da nazarinta harma da dukka tunaninkan da takan raba dare tana yinsu.....dukkansu sunfi ta'allaqa da kuma rinjaye akan YAYA WASAN ZAI KAYA?......wa zata fuskanta cikin fuskoki muryoyi dama ruhikan dake zagaye da wannan game din?. Idan ta tuna da mariya maamah.......tana jin wani abu sosai qasan ranta......jikinta kuma yana bata wani lamari me nauyi da batasan mene shi ba,amma kuma wani sashe na zuciyarta yana gaya mata ita din ba komai bace......tayi ganganci ne ma kawai data kutso kanta cikin rayuwarta......batasan wacece sabreen ba da gaske da bata aikata hakan ba.......bata kuma san meye da meye zata iya aikatawa ba. Motsawar sunan muhammad fu'ad kawai cikin kwanyarta shine abinda yafi sanyawa wani tsagi na zuciyarta damuwa.........lalata dukkan wata alaqa da kuma dangantaka cikin aurensu shine abu mafi sauqi da zata iya aiwatarwa......to amma kuma saki fa?.....A HANNUNSA YAKE!,amsar da akowacce rana take qara yawan adadin fargabarta. Lumshe ido tayi taja iska sosai cikin huhunta sanda muryoyi biyu suka sauka a tsakiyar kanta "Turaren ya hadu kona miqo miki ki zauna akai da kanki....." Cewar basudaniyar me gyaran jikin,yayin da nata maganar ya cakuda dana mamma bahijja data miqa mata wani bowl na tangaran "Bata din.....kafin hayaqin ya gama bin jikin ki saiki qoqari ki shanye wannan". Dara daran fararen idanunta ta daga tana kallon mamma bahijja kafin ta maida dubanta kan abinda take miqo mata,itama ita take kallo wannan ya hanata katabus na musanta mata,sai kawai ta miqa hannu ta karba,saidai kuma data fakaici ta juya,saita maidashi daga gefanta ta ajiye. Sanda tururin hayaqin ke ratsa sassan jikinta haka kowanne lungu da saqo na zuciyarta ke qoqarin bata mafita a lamarin dake tunkarota nan da kwanaki biyar masu zuwa. Zuwan mamman bahijja ya zame mata wani babban katanga daya hanata aiwatar da kowanne shiri da zai nesantata da auren.....duk da tarin bayanan da kawu yayi mata na ba inda zata shiga a duniya ta iya tserewa me jadda........saidai ta dauki.maganar tasa a wasan yara ne. Koshi waye.....ko kuma da meye yake taqama tayi imanin saidai idan bata sakashi cikin plan dinta ba..... "Adda baki sha bafa" Muryar huda da ke zaune gefanta ta fada,wadda kusan kowanne shirye shirye da ita ake aiwatar dashi. Maida idanunta tayi ta sake lumshewa muryar huda na dawo mata,ta fahimci dari bisa dari ba wani me adawa da auren,kusan kai tsaye ma zata iya cewa dukkaninsu maraba suke da abun,duba da irin walwalar da suke ciki gaba dayansu. "Ki nutsu sabreen.......ki nutsu.....karkiyi abinda zargi zai dawo kanki......karkiyi abinda su mamma bahijja xasu kasa karbarki da wankeki daga laifi duk sanda kika kammala da wancan game din kika dawo musu" Wata murya daga can qasan zuciyarta ta soma gaya mata. Idanunta ta bude ta aza kan huda har sai da hudan tadan sha jinin jikinta. Sunyi mata farin sani,daga kallonta kawai suna iya karantar umarni da kuma hani,amma ga sabanin tunaninta sai tayi mata nuni data miqo mata abun. A hanzarce kuwa ta ajiye littafin hannunta ta miqe ta dauko ta miqa mata. Tsure abun tayi da kallo wanda batasan da meye da meye aka hadasu ba,to amma koda meye aka hada din,ta tabbatar mamma tana asarar kudinta ne kawai,don haka ta kafa kai ta soma kurba a hankali gardin abun yana ratsa kunnenta duk kuwa da bakinta ba taste,haka zuciyarta a quntace take. *******Doguwar tafiya,hawa da kuma sauka,kutsawa cikin surquqi dukka ba damuwar maamah bane. Fatanta da burinta ta dangana ga mubata.160 data miqawa al'amarinta gaba daya,ta kuma sanya hope me yawa a kansa. A yanayin data ganshi a yau ya sake saka mata tabbacin samun cikakkiyar nasara. A hargitse yake yau din cikin zafin ayyukan mutanen da suka zabi ya zame musu abun dogaro kuma hanyar samun duniyarsu ba tare da damuwa da meye makomarsu ta lahira ba?. Bayan shafe shafensa da buge bugensa,ta hautsina dukkanin kayan aikinsa da yayi,ya kalleta da jajayen idanunsa qananun ainun dake cike da rashin tauhidi da kuma zallar sabo fajirci da fasiqanci. Dubane daya sake tabbatar mata ba rahama ko tausayi ko misqala zarratin a cikin ransa "Akwai tarin sarqaqiya......akwai tarin qalubale......akwai al'amura da yawa da zasu iya wanzuwa ko su biyo baya........ita din taurarinta nada tsananin haske da wahalar kutsa kai a cikinsu........tana da wahalar sha'ani na gaske......tabata kuma abune da zai iya zuwa da nasara da akasin haka.......kaman zan iya cewa KINYI KUSKUREN ZABINTA.......to amma kuma ba wani tauraro da zai iya shiga nasa taurarin sai natan......tamkar itace mahadi masarrafi kuma barin nasa taurarin......taurarinta sune abokan tafiyar nasa.........sunyi matuqar dacewa da juna.......wanda hakan shine zai bada damar tafiyar umarninmu da haninmu a kansa......kusan komai nasu suna matuqar kamanceceniya dana juna......ITACE TA DACE DA CIKAR BURINKI MUDDIN AKA SAMI GUSHEWAR AKASIN DA NAKE HANGOWA......saidai na gaya miki.....kamar akwai alamun KUSKURE DA NADAMA.......akwai babban waqeee'a......juyewar komai da lullubewar mayanin duhu bisa faifan qaddara". Tunda ya fara maganar gabanta ke wani irin faduwa. Hajja da suka gama sauraron bayanan a tare ta dora hannunta a kafadar maamah da zummar yin magana da ita da neman qarin bayani......saidai da sauri maamah ta zame hannunta daga kafadarta......tayi nisan da batajin zataji kira......zuwa yanzu nasara take nema ta kowacce fuska,ta kuma kowanne yanayi......bata buqatar tsaiko fashin baqi ko qarin bayani a yayin da take dab da cimma nasararta........bayan kuma a baya ya bata tabbacin ta wannan hanyar ce kawai nasara zatazo mata babu ko kwanto "Amma dai akwai hasken nasara ko dan kadanne?". Kansa dake cike da wasu irin gasussuka ya jinjina ba tare daya koda dubi idanunta ba. Cikin samun qwarin gwiwa tace "Nasara duk nasara ce komai qanqantarta,baa canza mata suna daga nasarar dai,hakanan daga qaramar nasara ake cimma babba......ayimin komai da ake da iko a kansa.......a sakamin yarinyar a tafin hannuna kafin samuwar fu'ad.......itace tsanin......ita zan fara mallaka don ta zama hannuna tsani na kuma idona zuwa ga wancan babban burin nawa!". Ta fadi muryarta na raunana tana tsoron jin akasin abinda zuciyarta ke muradi. "An gama!" Ya fada da wata kakkaurar murya maras dadin amo. Saita sauke ajiyar zuciya tana yi relax ganin yadda ya soma maida hankali akan aikinta. Boyayyar ajiyar zuciya hajja itama ta saki. Ba haka taso lamarin ya kasance ba,taso tana kuma so taji cikakken fashin baqi da qarin bayani daga bakinsa. Wacce irin sarqaqiya ce? Wanne irin duhu ne?. Wani irin baqin lullubin mayafi ne haka?. Wacce nadama ce zata biyo baya?. Meye kuskure a cikin zabin nata?. Dukka wadannan amsoshin tana buqatar saninsu ne don tasan daga ina zata dasa nata harsashin?. Daga ina tata TAFIYAR zata fara?. Ta wacce fuska zata saita tata DUNIYAR?,ta aza duniyar SHALELENTA?. Bata data cewa ko wani motsi,ta sani cikin aikinsa ba shishshigi,ke me rakiya kuma baki data cewa......hakanan baki da damar yin komayya kiyi tambaya akan aikin daba naki ba.....wannan kadai ya kashe mata jiki,ta zurfafa a cikin saqe saqe har ya kammala aikin maamah,ya kuma shaida mata su wuce zasu tadda komai cikin motarsu da qarin bayani. Bata sake gasgatawa da imani da zancansa ba saida suka samu komai a mota a ajjiye kaman yadda yace. Ta sake tsinkewa da lamarin aikinsa,inda da wani suka je wajen.....ko akwai gilmawar dan adam ta wajen sai tace an ajiye musu ne. "Kings abun mamaki hajja?,kullum mutumin nan sake dauren kai lamarinsa yakeyi" Ta fada tana juya kayan tsatsubar dake hannunta. "Kina zaton gurin qaramin mutum na kawoki......amma mariya?,me yasa kikaqi tambayarsa dukka qalubale da matsalolin daya hango miki?" Hajja tayi tambayar da tafi tsaya mata a rai. 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 ð˜Ąð˜Ē𝘧ð˜Ē𝘧ð˜Ēð˜Ģ𝘊𝘚ð˜Ēð˜ģ ĖķBĖķOĖķOĖķK Ėķ2 ⱧɄâ‚ēɄâ‚Ĩâ‚ģ 𝙋𝘞𝙂𝙀 4 A nutse ta daga kai tana kallon hajjan "Na tsani matsala ko akasi hajja......musamman a wannan matsayin da nake kai a yanzu......me zanyi da ita ballantana na buqaci sharhi a kanta?,bana buqatar dukkan wani jawabi da zai alamta min FADUWA ko MATSALA akan cikar burina a yanzu.......inaji a jikina da raina cewa......zan iya kauda kowacce matsala da zata tunkaro muddin na samu nasarar tsallake wannan matakin da muke kai a yanzu......da qwanjina....da kuma fikirata". Jinjina kai kawai hajja keyi.......tanason taji wanne tanadi da tsari tayi akan hakan?,amma kuma bataso ta zafafa tambaya akai har maamah ta zargi wani abun,saita tattarewa ranta komai tana jiran lokaci.....domin kuwa ta san cewa qwace goruba a hannun kuturu ba abu bane me wahala ba. ********Abune sananne a wajen kowa......sharar biki da yawan maganarsa a bakunan mutanen mu ya ta'allaqa da suna da sharar iyali dangi ko zuri'ar da za'a gudanar da bikin diyoyinsu. Hakan itace ta kasance akan MUHAMMAD FU'AD JADDA mamallakin JADDA DIAMONDCHORE RESOURCES. Daga qishin qishin zuwa samun tabbacin tasowar maganar aurensa,wanda tabbacin ya samu ne daga yadda farouq musaddiq saddiq da uban family alhaji hamza kibiya sukewa bikin shiri na gasken gaske. Daga abokansu saddiq maganan ya fara yaduwa,kafin kace meye wannan labarin ya fara kewaye kowacce kafar sada zumunta. Duk da a qurataccen lokaci labarin ya fasu.....to amma labari ne me dumin gaske daya bawa mutane da dama mamaki.......ya girgiza zukata da zuciyoyin 'yammata da dama......musamman yaran masu kudin da suke kwana su tashi da mutuwar sonshi......suke kuma da qaqqarfan hope din samun shiga a wajensa kodon matsayi da mahaifansu ke dashi......walau na dukiya ko na siyasa......ko kuma kasancewarsu abokan kasuwancin gold da diamond dinsa. A gefe guda kuma wajen 'yammatan da suka hada duk wata sura kyau da isa.....wadanda sukasan basu da wani tsanin isa zuwa gareshi......saidai sunyi mutuwar murus akan mayatacciyar soyayyarsa......abun ya sake bude musu topic of discussion......qarqashin kowanne posting na labarin bikin dake dauke da qawataccen IV na bikinsa da aka qawata da zallar ruwan gold,yake kuma wani irin sheqi da daukan idanun da zai gaya maka bikin ba na yaro bane......tarin cincirindon comments ne da mabanbantan kalamai masu yawan gaske. Da yawansu suna fatan inama zasu samu hotunan amaryar?,ina free wedding pics da sauransu,saidai ko daya basu samu ba face kunji kunji da shaidar zur daga wasu daga cikin commentators na qarya,sai luguden labba da tsabar kyan IV din bikin da aka kashesu dashi.......sai videos na lefen da aka samu wadda ta qwarewa gulma da munafurci ta ba bajesu dashi......abinda ya sake hura wutar tattaunawar. Sam wadanda ake abin dominsu basusan anayi bama......daga angon har amaryar ba ma'abota social media bane........idan kaga ta qulla abota da waya to akwai sabon mission a gabanta........data gama ta ajiye wayar dama layukan da tayi aikin dasu,wani ta karya ta zubar.......wani kuma sai bayan wani zamanin.......yayin da oga fu'ad sam sam ayyukansa basa ma bashi damar tunawa da wani media......koda WhatsApp dinsa idan ka ganshi akai wani abune ya kama da lallai yake da buqatar hawa yayi a can din. Koda yana free ma ko yana annual leave dinsa.......yanayin tsaro da dukka rayuwarsa ke buqata ya sanya ya sake nesa nesa da duk wani harkoki irin wadannan......don komai nasa a matakin rayuwar daya taka yanzu yana buqatar privacy. A daren da ya rage ayyuka sosai......abu daya tak ya rage masa ya kammala yabar qasar. Yana zaune saman bean bag chair,daga gefansa ruwan wolfberry ne me dumi yake sipping yana kuma chewing berries din idan sun shigo bakinsa. Haka kawai yayi shaawar shiga yaga me duniya ke ciki don duka schedule dinsa na yau ya kammalasu. Da wani personal account yake amfani,wanda bai taba ba baya kuma wallafa komai a ciki bare ka iya gano waye mamallakinsa. Akwai account na company dinsa kala daban daban dake qarqashin kulawar ma'aikatansu dake kula da wannan fannin,so amma ko su baya bi ta kansu tunda yayi imanin zasuyi handling dinsa ya dace da abubuwan da ya kamata ace an sanya din. "Ya salam" Ya fada yana miqewa daga relaxing din da yayi cikin bean bag din yana kallon yadda hotunan katinan daurin auren ke shawagi cikin media. Da farko ma bai fahimta ba,saidai daga bisani da suka yita jeho masa ire iren posting din.....kamar sunayi da gayya sunsan shike da alhakin abun har sai da hankalinsa yakai. Shuru yayi yana sauka gami da furzar da iska daga bakinsa. Yasan aikin mutum uku ne wannan farouq saddiq da musaddiq,sai amna ta hudunsu. Kamar jira akeyi ya gani kira ya shigo masa,a nutse ya jawo yana dubawa......farouq ne,kusan tun randa yace ya zaba kaya bai sake barin wayarsa yadda za'a sameshi ba sai yau,sai ya katse kiran,ya koma ya laluboshi video call. Ta signal ya shiga,amintaccen app din da mafi yawan manyan mutane ke ta'ammali dashi saboda samun cikakken tsaro. Shigan farko ya daga,fuskarsa ta fito tarwai kaman yana gabansa. "Hey...." Ya fada qasa qasa yana duban fu'ad "Don't tell me baka ma taso ba?" Yayi masa tambayar yana tsuke fuska tare da bata fara'ar fuskarsa "Zuwa ina kuma dude?.....bakaga abinda kuka jawo ba?,baka ga abinda ke trending ba?" Ya masa tambayar shima hana dan bata fuska kadan. Kai farouq ya jujjuya hagu da dama yana yarfar da hannu "Am asking you seriously fa.....where are you?" "Ask media users......farouq,you take it very serious fa.....wannan fa auren ba wani abu bane da za'a damu dashi har haka ba.....ba wani babban abu bane da zai zama ya yada ko ina ba......it's just a temporary......." "Kai kasan wannan......mu bamu sanshi ba......in fact ma idan ka matsa da yawa zan fiddo komai.....just ka dauko hanya gobe kawai......if not,bazan gaya maka abinda zai faru ba". Datse kiran farouq din yayi,abinda ya sanya fu'ad sakin murmushi ba tare daya motsa daga inda yake ba. Da alama farouq din a qufule yake dashi sosai,shi yasa yayi masa abinda yafi tsana kashe masa kira. Ya kasa fahimtarsa ne,shi sam baiga me yasa zai damu da abinda baida wani muhimmanci ba,baiga abun daurawa kai hidima har haka ba......already sun gama diban kudin komai da komai uban da 'yar,daurin aure kuwa ko aike yayi cikin ma'aikatansa za'a daurashi,gidan da zai ajeta ko ba yanzun ba zai iya bada umarnin tarewarta idan ya gama sabgogin gabanshi,for god sake zai bata lokacinsa ne da ranshi akai?. Bai sake bi takan farouq ba don yasan fushinsu da juna ba wani abu bane me dorewa ba. Saidai yadda farouq din yace idan bai dawo ba washegari baisan me zaya faru ba,yana tsaka da ayyukansa da yake sanya ran sune na qarshe kiran anni ya sameshi. Abdul_haleem daya daya cikin guard dinsa ya miqawa folder din hannunsa,ya koma gefan table din da yake ajiyar takardun ya zauna yana daga wayar. Cikin nutsuwar nan tata da ko yaushe take qara mata kima da kwarjini tayi masa sallama cikin tsantsar kulawa da qauna irin ta uwa da d'a. Kaman ko yaushe shima,cikin tausasawa da matuqar bada kima ya amsa mata sallamar. "Barka da warhaka anni......anni ayyuka sun sani gaba,ayimin afuwa" Yayi riga malam masallaci wajen fada. Murmushi ta saki cikin nutsuwa tace "Anyi maka Muhammadu........ya aikin?,fatan komai yana tafiya daidai?" "Alhamdulillah anni.....komai alhamdulillah,saidai muna buqatar qarin addu'a" Ya furta maganar jerin saqonnin daya gani shekaran jiya suna fado masa. Ba'a raina kaidin maqiyi,kuma abokin adawa ko wanda bai sonka ba'a rainashi komai qanqantarsa. "Kullum a cikinta muke,ba abinda zai faru in sha Allah sai alkhairi......amma nayi zaton samun baquncinka a yau......tuntuni mun sauka a sabon gida.....duka duka jibi ne daurin auren nan......ga baqi a gidan kowa kai yake tambaya". Hannu ya sanya ya shafi sumarsa,har yanzu ya gaza gano abinda yasa suka daukaki sabgar nan haka.....har wani taron gayyar jama'a anni itama tayi kenan bayan ta maamah?. "Jibi din zan shigo in sha Allah anni" "Anni jibi yayi kusa.....gobe ko yau ya kamata....private jet ne,baida buqatar samun wani issue ko ya kawo excuse" Ya jiyo muryar farouq daga gefe tana shigo masa. Murmushi ya saki da sautinsa ya gaza boyuwa,wato zuwa yayi ya hadashi da anni kenan?. "Bani shi anni please" Ya fada da sauri,bata ce komai ba ta miqawa farouq wayar tana murmushi. Drama din fu'ad da farouq babu me shiga,idanma kace zaka shiga din kunya zakaji. "Definitely idan ka samu dama saika shiga tsakanina da anni......ka canza hali wallahi" Ya fada yana dan daure murya. "Kome zaka fada ka fada.....ina nan ina jiranka" "Kaci gaba da jira.....at last idan bakayi wasa ba kai zan daurawa auren nan da yarinyar......tunda naga ka damu da lamarin ta da yawa" Daga haka ya katse kiran yana dariya ciki ciki. Yasan ya kunno farouq din,don ba wanda zai rabashi da fannah dinsa sai Allah. Haka kawai ya samu kansa dason cika alqawarin daya yiwa anni,ya maida hankalinsa qwarai kan qoqarin kammala abubuwan da suke gabansa don ya samu isa nigeria kaman yadda ya alqawarta. Hannu anni ta miqa tana karbar wayarta daga wajen farouq dake mita. Duk da mitar da yakeyi din saidai ya kiyaye dukkan wani abu da zai saka anni ta fahimci akwai lauje cikin nadi.....boyayyen manufa da qudurin data hana fu'ad damuwa da dukkan wani lamari daya shafi auren. "Anni kina sauqaqa masa da yawa........hatta da friends dinmu gobe zasu iso.....amma ace shi yana can neman kudi?.....har yau ya kasa sanin kalmar hutu a rayuwarsa?.....ta yaya zai kula da diyar mutane?" Murmushi anni ta sake,yadda farouq din keta mita ke bata dariya "Banda abinka farouq.....na tabbatar ya fika damuwan ya iso fa.....sannan tunda kaga haka din ba yadda zai taho dinne,da yau gobe da jibin dukka na Allah ne,kuma kaman yau ne.......ina da saqo ma da nakeson ka miqawa d'iyata...." Anni ta fada tana yunqurawa ta miqe. "Ina amna ta shiga ne?" Farouq ya tambayi anni dake qoqarin bude wani side na wata qawatacciyar cupboard ta daban dake cikin aljannar duniyar bedroom din nata. "Tana bangaren beauty spa" ð˜ŋ𝙊ð™Ģ𝙞ð™Ū𝙖 ð™Đ𝙖 ð™Ģ𝙖 𝙠𝙊𝙙𝙞 ð™Ģ𝙚. 08187255862 𝐃 𝐔 𝐍 𝐈 𝐘 𝐀 𝐓 𝐀 ð˜Ąð˜Ē𝘧ð˜Ē𝘧ð˜Ēð˜Ģ𝘊𝘚ð˜Ēð˜ģ ĖķBĖķOĖķOĖķK Ėķ2 ⱧɄâ‚ēɄâ‚Ĩâ‚ģ 𝙋𝘞𝙂𝙀 5 "Okay" Ya fadi kawai a taqaice,don ita kanta yadda yaga alamun ta dauki bikin kamar yafi yadda kowa a gidan ya dauka. ******A duk bugawar daqiqa,wucewar kowacce saa da kuma bugawar agogo sake kusantar da ita kawai yakeyi zuwa ga duniyar mamakin abinda ke shirin faruwa da ita. Sannu sannu taga gidan ya fara cika da baqin fuskokin da da yawansu ta manta da kasancewarsu ahalinta. Wasunsu tun ana taron alhinin rasa mahaifinsu mamallakin gidan gaba daya,yau sai gasu da daya da daya suna bullowa da sunan halarta taron bikin da tayi imanin ba wani bane ya gayyacesu. Dondai mamma bahijja ba wata mu'amala ke tsakaninsu ba,hasalima ba sanin kaso casa'in da tara a cikinsu tayi ba. Ba sanin jiya ko yau ta yiwa duniya ba,ta sani....kusan mafi rinjaye a cikinsu sanin waye yake shirin aurenta shi ya kawosu bikin,bikin da babu wani abu guda daya da take da masaniyar ita ko mamma bahijja ta tsarayi,koda an tsara din ta tabbatar aikin kawu rufa'i ne,wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye,komai yana gaba gaba a kai,hakanan ya saki kudi anata hidima cikin gidan. Yanayin yadda ya saki bakin aljihunsa ya dasawa sabreen qaqqarfan yaqinin kudade ya samu ko ya karba daga wajen mutanen daya sadaukarwa da ita. Bata cewa da kowa komai ba,amma tana karance da kowanne motsi na cikin gidan. Yadda bibo tayi uwa tayi makarbiya,a rana takan hauro saman da zummar dubasu har babu adadi,saman da a baya sai da akasha dambarwa da ita kafin ta daga qafan kasancewarta a can,sai da sukayi baram baram da kawun,ya wanke mata zanin mutuncinta tas tare da buga mata gori nau'i daban daban,yau din sai gata tana zarya tsakanin hidimar da ba tata ba bata kuma shafeta ba. Sanye take da wata simple dubai gown me rangeamen nauyi da sassauqan ado me daukan hankali,cotton ce me yankakken hannu da ya tsaya iya damtsenta,sai siririn mayafinta data maidashi tamkar dankwali ta yane sassalkan gashinta dake zube gadon bayanta ba tare data daureshi da komai ba. Cikin jikinta sam babu qwari,tana jin kamar iska zata iya dibanta ta kayas da ita,hakan kuwa ta sani baya rasa nasaba da qauracewa abinci da tayi akan yadda ta saba cin abinci,duk da dama can ita din ba ma'abociyar cin abincin bace. Ta samu huda ta dafa shinkafa da wake,sai miya da soyayyen kifi daban. Goshinta ta dafe tana zama,kanta tun jiya yake sara mata bayan data jiyo mamma bahijja na magana da qannen mahaifiyarta da kuma kawu Abdul Hakeem,tana shaida masa jibi gobe kenan shine ranar daurin aurenta bayan sallar juma'a. "A zuba miki adda?" Huda ta tambayeta cike da fatan ta amsa cewa zataci din. Hannuwan huda da sukasha lalle tabi da kallo. Ko nata hannuwan farare suke sidik da zara zaran

Chapter 2 of 5