Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 10
Fatima sun koma Dubai ita da jalil yana karatun sa duk da ita ya hana ta. Sai dai har zuwa wannan lokaci Fatima ko B'ari bata taɓa yi ba. Kullum suna addu'ar samu sbd duk kan nun su masu san yara ne. A yanzu duk wanda ya kalli Fatima yasan tana hutawa tayi kiba tayi haske sosai. Ga kuma wata kauna da soyayya da Su Ammy da Mamy da papy kan shi suke nuna mata. A yan zu sun koma kano da zama ma gaba ɗaya. A yau ne su Jamal suka samu hutun watan ni huɗu a makaranta dan haka gobe shida Jamal da jalil da Fatima zasu koma gida. Washe gari karfe 11:00 am suka sauka Jawad ne da jawahir suka zo daukan su, kai tsaye gidan papy suka wuce suka huta kafin da yamma suka wuce gidan su. Fatima suna ta hira da Aminiyar ta Jalil wadda ba,a taɓa jin tsakanin su. *Bayan sati ɗaya* Jawad ne da Jamal suka zo gidan Jalil a zaune suke suna hira hada Fatima saboda suma suna kaunar ta kuma suna ganin girman ta duk da yarin ya ce karama. "Jawad Bebyn Jalil dama haka su ke ce mata. "Ta ce na,am yaya Jawad". " Kina ganin babu matsala ni da Jamal idan muka yiwa papy maganar auran mu da su Jawahir, sbd kinga papa ake jirah kuma papa shiru gwara muyi auren mu sbd gaskiya mu a shirye muke wata biyu muke so a saka". " Dariya Fatima ta yi tace hakan ya yi babu matsala koni ma ai zanyi farincikin hakan tun kana nima zaman kad'aici ya ishe ni idan 'yar uwa ta ta zo." Duk ka suka ware ido suna kallon ta da mamaki. "Jawad mai me kike nufi? Kina nufin a gidan nan zamu zauna?". "A'a ina nufin idan yar uwa ta tazo mana". "Au jalil aure zaka yi bamu sa ni ba". "A'a wllh ni ma bani da masaniyar hakan." "Fatima yaya Jawad zaka auri jawahir, yaya Jamal zai aure Jamla. shi kenan ita my dear Jalila ba zatayi aure ba? To ita ma tare za,ayi zata auri my love." Gaba ɗaya ji sukayi jikin su ya yi wani mugun sanya, a kuma ɓangaren Jawad ya yi farincikin amma bazai nuna hakan ba. "A'a bebyn Jalil ba za,ayi haka ba ta ce ai kuwa haka za,ayi. Jalil ya yi shiru ya kasa magana ya ce wato ni bani da zaɓi na sai abun da kullum aka zab'a mun. Amma bazai iyya yiwa Fatima hakan ba sbd ita din mace ta gari ce. Haka sukai ta bata bakin kartayi haka ta ce anyi ma. Daga karshe suka mata sallah ma suka tafi jiki ba nauyi. Suna fita jalil ya juyo ya ce wannan zaɓin ki ne amma ni bazan wa matata kishi ya ba. Ya shige ya barta a falon tana murmushi. Shin jalil zai Amin ce da wannan haɗin a karo na biyu? ✍️✍️✍️💥💥💥 *GAYYA CE!* *Written by* *Fatima alaramma lafazi* *(Falaramma)* https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ *Sadaukar kar wane ga iyaye na da 'yan uwa na 'yayan Alaramma baki d'aya ina alfahari da su* 💖✨✨✨💞💋💋 Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan. 💥💥💥 Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya littafin, ina alfahari da ku ges nagode. PG 2️⃣ 9️⃣💥3️⃣0️⃣ Fatima ta dad'e a wajen tana tuna ni kafin daga bisani ta meke ta bishi dakin shi. A kwance ta same shi ya daga kan shi sama da alama ya yi nisa a tuna nin da ya keyi, a hankali ta zauna gyefen shi sannan ta jawo hannun shi. Ya kuwa d'ago da kan shi suka haɗa ido sai ya yi kasa da idon shi fuska ba bu annuri. "A hankali ta kama hannun shi tana murzama cikin wani rin salo da wata kallar murya Fatima ta fara magana" my dear Husband ta kira sunan shi ya dago yana kallan ta alamar yana bi bata re da ya ce komi ba. Idan Allah ka hauri Jalila wallah mutuniyar kirkice ga addini da san 'yan uwa. Yan zu ka duba kaga ya kamata su yaya Jamal su jewa papa da wannan maganar ba yan ita yarsa bata samu ba, kai ne mijin jalila my dear kawai Ubangijin ya saka ni a tsakanin ku ne amma kai ne wanda Allah ya bata in sha Allah. Kasan yadda papa ke san beby wllh hakan da zakayi zai karawa papy da Ammy kaunarka. Kuma ka duba kaga ko acikin su sun fisan ka kuwa soyayyar da suke maka ya kasa boyuwa kuma suna yin hakane sbd kai din mai biyayya ne da nuna masu kauna. My dear dalilin san da su Ammy ke maka ne yake tabbani, ko da basa san abu na saka baki a ciki sun hakura da lamarin yadda na faɗa haka zasu yi haka ta dinga bashi baki tana masa wani irin abu da hannu ta a jikin shi wanda hakan ya kashe masa jiki sosai ya rungumo ta kawai a jikin shi. Murya a sanyaye ta ce dan Allah kayimin wannan Alfarmar my dear. Kasa bata amsa ya yi dan tuni ya faɗa wani shafin ita kuma tana taya shi ya yin da take dad'a rikita shi. Cikin wata irin murya mai cike da galaba ita da lamarin da take masa ya ce "na amince da batun ki my wife. Bai iyya furta koda uffan daga haka ba ya faɗa cikin salon matar tasa. ***** ** Da yamma ta shirya ita da jalil suka hufi gidan papy tayi masa bayanin abin da zai ce sannan ta ce kada ya sake ya faɗa masu ita ce ta ce ya aure ta. Amma ya ce ta amince da auran. Shi dai jalil da mamakin lamarin matar tasa suka ƙara sa gidan. Tun daga bakin falo Ammy ke mata murmushi da sakakkiyar fuskarta ta har ta k'araso wajen ta rungume Ammy tana gaida ta. "Ammy nayi missing din ki my dear ello" "Ammy missing you too, I love you so much my dear Ammy suka saka dariya." Jamal da jalil da ke gyefe suma sukayi dariya suka ce Ammy gaskiya kuna san juna keda bebyn jalil. "Ammy ta ce ai my dear ello ta cancanci fin haka daga gareni, Ubangijin ya kawo min jikokin lpy Fatima tayi kasa da kanta. Su Ammy suna yi mata zargin mai ciki ne amma ita tasan bata da komi. Mamy ce ta shigo gidan sakama kon ta main falon gidan a kwai k'ofar da zata sadaka da gidan papa. Fatima sauka tayi daga kujerar ta gaida Ammy ta amsa cike da far,a da kaunar ta . Jawad ne ya shigo falon ya ce yau baƙi muke da shi ne, sannu da zuwa Bebyn Jalil ya gida, ta ce Alhmdllh sannan suka wuce dakin papy dukkan nin su. Ammy ta kalli Fatima ta ce bebyn papy fa bata san kunzo ba. Bari na kirata na sanar da ita dan tana sama yau gaba ɗaya bata sauko ba, Fatima ta ce a'a Ammyna bari naje dakin na ta, tayi sama ta barsu Ammy da yabon hali irin na surukar ta su. Ta na shiga ta yi sallah ma ta sameta a kwance tana ganin ta ta mik'a ta rungume ta ce my dear Anty, cikin far,a"Fatima ce ta dago tana kallan ta tace lpy kike kuwa Baby kinga yadda ke ka rame kuwa. Anya kina cin abinci ? My Anty wllh bana iyya ci kwana nan. "Faɗa mun mai ke damun ki " dan Allah kada ki boye min komi inji" "My dear ello Wallahi wani matsananci ciwon mara ne ke damuna naje wajen doctor ya ce min idan banyi aure ba wannan ciwon bazai tafi ba, ga kuma wani azabebben felling amma maganin da nake sha yaƙi dauka ta, gashi bana so a sanarwa da papy halin da nake ciki sbd hankali shi tashi zaiyyi. Wllh Anty ni banga mijin da ya yi mun ba wanda kuma nake so ya yi mun nisa. "Fatima ta dafata tana share mata hawayen ta ce, my kinga kowanne bawa da inda Allah yake jarrabar shi. Dan Allah ki cire komi a ranki jinki in sha Allah kwanan zakiyi aure ki huta da wannan cikin. Har ki haifo mana kyakkyawa beby kamar ki, kuma in sha Allah ni zanyi rainan ta . Da kalamai masu dad'i Fatima ta mantar da jalil damuwar ta sannan ta hanata amfani da magungunan rage felling din . ****** Falon papy a Zazzau suke a gaban mahaifin na su, ba wanda ya ce wani abu, can dai jawad ya nisa ya ce papy dama munzo da wata magana ne, Tom shikenn in jinku. Dama ni papy ina san Jawahir ne, shi kuma Jamal ya ce ni papy Jamal nake so a ne momin auran ta. Papy fuska dauke da murmushi yace ma sha Allah nayi farincikin da jin wannan batu naku amma ku sani duk sai na tambaye su dan bazanyiwa 'yayan auren dole ba. Suka ce sun Amince. Can kuma papy ya yi shiru da alamu wani abu ya duno sai ji sukayi yace nima Ubangijin ya kawo wa beby na miji na gari, sai lokacin tuna jin jalil ya dawo jikin shi, wanda duk da baima san mai ake cewa ba. A hankali ya bude baki ya ce ni..,.ni cikin k'ink'ina ya dama ni jalilah nake so papy!!!. A ɗan tsorace papy ke kallan jalil ya ce jalil wannan wacce kalar Magana ce kana nufin Fatima zakayiwa kishi ya gaskiya ba zan lamun ce da wannan batun naka ba, kai Jawad kira min Ammyn ku. Ammy tana zuwa aka labarta ma ta nan ta taki amince wa ta dinga masa faɗa tana ce wa ba, ayi wa Fatima adalci ba, sai dai idan ya sakar mata 'ya ta samu inda baza ayi mata rashi adalci ba, shi kan sa Jawad bai taɓa ganin bacci rain Ammy irin na yau ba tsawon shekaru da suke da shi. Sai da suka gama caf sannan jalil ya ce Abun da baku sani ba Ammy shine ita Fatima da kanta ta bukaci hakan, idan kuma baku yarda ba to ku kira ta ku tambaye ta. Suna ta mamakin abun amma haka suka kirah ta. Bayan ta gaida papy ta ce ani Ammy my dear ello wata magana naji a bakin mijinki wai da gaske ne?. "Ammy na kiyi hakuri da abinda zan ce tabbas wannan maganar da gaske ne kuma shima ba,a san ranshi ba ni ce na bakaci hakan sbd babu wani wanda ya dace da jalila idan ba shi ba. kuma ita kanta jalilan ina matukar kaunar ta shiyasa nake so mu kasance a waje ɗaya, kuma nasan ku kan ku zakuyi farincikin da wannan auren, fatana dai ku amince mana kuyi magana wannan al'farmar ni da miji na". Gaba ɗaya sun yi tsakanin mamaki da maganar ta ta amma kuma sunyi farincikin da Wannan aure. Papy ne ya ce Fatima bubu wata al'farma da bazan iyya yimiki ita ba my ello Ubangijin ya sa haka shine yafi alkairi Ubangijin ya haɗa kan ku ya haɗe fitina ta ce Ameen tare da musu sallah ma ta fita. Wannan lamarin ya karawa su Ammy da papy kaunar Fatima, hatta su Jamal da Jawad sunyi mamakin abun kuma sun karah ganin darajar ta. Ita kuwa tana fitowa daga d'akin wasu zafafan hawaye suka biyo kuncin ta sbd tana matukar kaunar mijin barazana masa so mara misaltuwa tana san ta kasance ita kadai a tare da shi amma ƙaddara ta riga fata. Ta sha kukan ta sannan ta wuce dakin jalila. Tana shiga dakin Toilet ta shiga ta wanke fuskarta ta shirya kanta sannan ta fito ta cigaba da al,amuran ta. Sune basu bar gidan su Ammy ba sai misalin ƙarfe 10:00pm suka wuce gidan su. Ranar kwana sukayi sallah ita da jalil suna addu'ar abun da yafi Alkairai. Sai bayan sallah asuba suka koma barci a bun su ita da shi tana kwance a kirjin shi yana shafa bayanta. Har barci ya dauke ta. Yana jin karin kaunar matar tasa ji yake zai iyya komi sbd ita. *Bayan kwana biyu* Tunda daga wannan rana Jalil ya dinga shigewa jalila ko ina idan zataje shi yake kai ta ya yi ta mata hira. Ita kan ta lamarin na shi har mamaki ya ke bata, wani lokaci kuma ya kira ta ya yi ma mata hira tun tana dan jin nauyin sa harta saki jikin ta. Wata ranar fariday sun fita da ita wani wajen sha iska, a hankali ya kirah sunan ta ta amsa masa ya ce wata magana nake so muyi dake mai mahimmanci jalila dan Allah ki fahimce ce. Ta ke ya faɗa mata yana santa, ko kallan shi bata yi ba ta tashi tayi tafiyar ta yana kiran ta amma ina mota ya shiga ya bita tuni ya hango ta a napep ta shige, shi kuma ya bita a baya suka wuce gida, tana sauka ta shige gidan babu kuɗi a hannun dan haka ta ce ya tsaya ta kawo masa tana shiga gidan ya bawa mai napep kudin shi ya shige gidan ya sameta falon Ammy tana karɓar kudin yace mata ya biya kai tsaye ta shige dakin ta ta bashi a wajen. Ammy ta kalle shi tayi murmushi dan ta fahimci komi, shi kuma wai wani b'ata lokacin ba ya wuce gidan sa wajen hasken idaniyar sa. Kallan yana yin shi kawai tayi tace bata amince ba yace kwai kuwa my wife kin sani a matsala kinga abun da tamun kuwa dan Allah kayi hakuri yanzu kira ta, har 3 miss call ya yi take daga wa. Fatima da kanta ta kira ta amma taki daga wa. Tayi murmushi karfin halin sannan ta ce ka barta zuwa gobe. Yau kwana biyu da faruwar hakan ko ya zo gidan baya ganin ta, yau da kan shi ya taka ya shiga d'akin ya yi sa,a kuwa d'aki a bud'e ya ke. Tana kwance idan ta a rufe, ya k'arasa inda take ya zauna ita kuwa tana jin shi tayi masa banza. "Jalilah nasan idan ki biyu ba barci kike ba ina san kifad'an laifin da ɗan uwan ki ya yi dan yace yana sanki, jalila auranki fa nace zanyi bawai nai manki nayi da sab'on Allah ba dabar kike gudu na." "Na sani yaya Jalil amma da wane ido kake so Anty ta kalle ni kasan wani irin muradi take dashi a kai na? Kullum burin ta na haifi 'yayan wanda ita da hannun ta zata raine su." Dan Allah yaya Jalil mu hakura da batun nan, ina sanka amma bazan iyya auren ka ba." Ta mike zata fice ya riko ta tafad'o jikin shi, jalil Fatima ta amince da auren ki kece kadai yan zu naje jira hatta papy da papa sun san da Maganar. "Tom shikenn kaje zanyi tuna ni, sai kuma naji tabbacin daga Aunty." Ranar kuwa kasa barci jalila tayi tana ganin kamar batayiwa Aunty Fatima adalci ba. *Washe gari* 10:20Am a gidan tayiwa Fatima sbd farincikin Amin ce war jalil. Kai tsaye dakin ta ta wuce ta shiga tana shiga suka haɗa ido Fatima ta sakar mata wani murmushi ta ce Amaryar mu, jalila tayi karasa da kanta. Fatima haka ta tabbatar mata da amincewar ta akan auren su, sannan ta dinga ce mata kin san yadda yake sanki da kaunar ki, tun tana jin kunyar ta da haka harta saki jiki tana mamakin Fatima. Papy ma aranar ya kira su ya ambaye su suka ce sun Amince ce. Daga nan papy ya dauki kafa Shida abokan da Babba mijin inna suka je wajen Dad dan nema wa Jamal auren Jamal dan papa da Mamy sun ce sun bar masu ita duniya da lahira. Dad ya yi farincikin abu daga nan aka tsaida biki wata daya ( one month) . Nan suka kawo kudi duba dari biyu suka bayar suka karba tare da saka albarka. Shima jalil da Jawad suma anka karba kuɗi aka tsaida rana kamar tasu Jamal. ******Fatima ma taje gida suka shirya koma mom ta karah shirya ta sannan ta dawo gida tamkar Amaryar sbd tasha gyera wajen mom. Anata shirye-shiryen biki ne saura sati daya papa ya dawo duk ya zama abu tausayi haka ya dinga ne man yafiyar 'yayan na shi da 'yan uwa na shi. Haka ya dinga ne man gafarar Mamy ya ce ba komi ta yafe masa. Ranar juma'a kuwa aka shaida daurin Auren, Jawad da jawahir Jamal da Jamal Jalil da jalila Alhmdllh daga nan suka wuce dasu sabon family Hause din su da aka gina harda su papa da papy da su kwanan su 5 da tare wa gida na Alfarma. ✍️✍️✍️💥💥💥 *GAYYA CE!* *Written by* *Fatima alaramma lafazi* *(Falaramma)* https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ *Sadaukar kar wane ga iyaye na da 'yan uwa na 'yayan Alaramma baki d'aya ina alfahari da su* 💖✨✨✨💞💋💋 Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan. ✨✨✨ Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya littafin, ina alfahari da ku ges nagode. PG 3️⃣1️⃣💥3️⃣2️⃣ Fatima da Amarya jalil kuwa baka gane su sbd sunyi kwalliya iri ɗaya hatta sutturah duk iri ɗaya suka saka babu bambanci, ko laifema da ya tashi iri ɗaya ya yi ma su. Jalil ne ya haɗa su a falo duk ya musu nasiha da a girmama juna sannan suka tashi ko wacce ta shiga dakin ta. D'akin Fatima ya shiga ya kawo mata wasu manyan ledoji sannan ya zauna gyefen ta ya jawo ta jikin shi, a kunnan ta ya shiga faɗa mata wasu maganganu wanda Nima ban samu damar ji mai duke tattauna wa ba, amma da alama tana jin dadin zance nata dan sai murmushi ta ke, da kan shi ya bata jougut ta sha da ɗan naman ya haɗa mata ruwa wanka, ya ce ta shigo ya mata "tace a'a kayiwa amarya, kaje haka kartayi fushi ya ce a'a sai kinyi barci zan tafi". Tana fitowa ta taddashi a zaune rike da rigar bacci mai shegen kyau, haka ya taimaka mata ta shafa mai masu dad'i da kan shi ya saka mata rigar barcin ya dauke ta cak sai kan gadon, ya kwantar da ita ya lullubeta da wani tamtausan bargo ya barshi shafa gashi kanta, sai da yaga tayi barci sannan ya zuba mata kiss mai zafi a lips din ta sannan ya tufa mata addu'a ya kashe mata wutaya fita daga d'akin. Abun da bai sani ba Fatima na jin shi, tana jin fitar sa ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. Koda ya koma bangaren jalil zaune ya same ta tayi tagumi, ni kuwa nace Allah sarki baiwar Allah ta shigo gidan wata. Shi kan shi Jalil yana yin da yagan ta sai ta bashi tausayi a hankali ya k'arasa dan bata ma san ya shigo d'akin ba, ya janye hannun ta dake fuskantar ta ya jawo ta jikin shi ya haɗe ta da kirjin shi, sai kawai tayi ƙasa da kan ta. "A hankali ya fara magana kin gani da jira na ko my love" kiyi hakuri kinji pulet din da ya shigo da su ya jawo batare da ya sake ta ba ya jawo ledoji da ya shigo da su da cups nan ya shiga ciyar da ita bata wani ciga ta daure kan ta, daga nan suka shiga ibadojin su sosai ya tambaye ta abun daga addinin Alhmdllh kuma ya samu, daganan ya kuma masu addu'a sannan ya umarci ta da taje ta kwanta, sai da ya gama al,amuran sa sannan ya shirya kan shi cikin kaya irin na jikin ta ya koma ya kashe wutar d'akin ya kwanta kan gadon ya jawo ta jinkin shi, ya fara antaya mata wasu abubuwa masu wuyar fassarawa a rayuwar ta wanda bata taɓa cin karo da su ba, ni kuma na wuce gidan Jamal dan ganin mai ke faruwa. Suma dai a hakan na tadda su dan da Alama sun duniyar mabanbanciya daga nan nayi masu sallama na wuce gidan su Jawad. Ina shiga bakin kofar wata karah da naji Jawahir tayi ne ya sani daka tawa a wajen na koma gidan su Ammy. Ammy ce gyefen papy fuska ɗauke da farincikin "tace papy kaga hukunci Ubangijin ko, Ubangijin ya wanzar damu cikin farincikin. Wannan hajin in sha Allah dukkan nin mu zamu wuce Makkah dan yin ibadojin mu. Kuma harda Babba da inna in sha Allah. *Washe gari* Jawahir kwance gaba ɗaya jikin ta a mace ya ke bata da wani sauran kuzari Jawad ne ya shigo yaga yana yin ta, ya kawo mata tea ta sha kad'an da hawaye wani na biyu wani, can dai da yaga abun nata ya yi yawa sai ya ce tashi suke hospital shi ya taimaka mata ta saka hijabi sannan ya dauke ta har cikin motar suka wuce hospital din da yake aiki. Yana parking ya ga motar Jamal da yake hawa amma baiyi magana ba sai ya shige kai tsaye officer din mama Rabi ya wuce ta. " Gaida mama Rabi ya yi fuska a sake sannan ya ce mama ta faɗa maki abun da yake damunta tun da ni ƙaramin doctor ne ta rainani" . "A'a yau she zata ce haka nayan kana ɗaya daga cikin waɗan muke ji dasu a Hospital din nan, aka ce min tun dazu ka shigo ina fita nace gaskiya ba kai bane ɗan uwan ka ne, shima ya kawo matar sa ba lfy tana officer din mama jummai tana mata dinki". "Ya ce eh shine Allah ya bata lpy. Ita ma dai haka Jawahir abinda bata so ba sai da aka yi mata dinki sbd tasha wahala sosai a wajen Jawad. Ita kuwa baiwar Allah jalila shida kan shi ya kullah da ita, kuma ya gyerah ta ya gasa mata jiki. Fatima ma abinci ta kawo mata na musamman da Farfesun kayan ciki taci sosai dama da yinwa ta tashi. Sukuwa su Jamal da Jawad wuni sukayi a Hospital da 'yar aka sallame su suka dawo gidan dan basa son kowa ya sani amma su Ammy time din da suka zo gaida su bayan su dawo daga Hospital suka fahimci akwai wani abu. Fatima da yamma ta ce wa jalila ta ƙarah gasa jikin ta ta kuma bata wasu magungunan wanda zasu taimaka ma ta. Ita dai jalila sai kunyar Fatima ta ce ji amma ita Fatiman komi yi take tsakanin da Allah. *Bayan wata daya* *After one month* Tuni su Fatima da jalila suka bi mijin su suka koma Ingilan ya cigaba da karatun sa. Amma gabaki dayan su ya hana su karatu ya ce indai shi zaiyi suma suyi to mai ne amfanin nasan. Fatima da jalil zama sukeyi na amana gaba ɗaya sun hade kan su suna kyautata mijin su bayayi ayuwar su gwanin sha,awa. Shima Jamal ya dawo Ingila din amma gidan shi da ban inda kuma ya ke karatun shi, shida matar sa.

Chapter 9 of 10