Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 10
Fatima ta bashi dukiyar ta domin ya yi mata kasuwanci da ita, ta kuma dorah shi kan wata harka duk wata harka ta ta shi ne ta dauki mota halak malak ta bashi. Shi kuwa Jamal Babur ne da shi da ya siya da halak din shi da yake sana,ar funichace. Idan kuma ka gan shi da muta to ta Jamla ce ya hau, kuma baya hawanta sai dad ya aike shi ko zai karbo mai wani sako, ko zai kai Jamla makaranta. *Cigaba labarin* *Kaduna* Tun daga wannan rana Jawad sai yaje gidan Mamy dan ganin halin da take ciki, ya kan bata lokaci a wajen su na hira, musamman idan papa baya nan Yau ma kamar kullum ya shiga ya same ta zaune, ya gaida ta sannan ya shiga tambayar ta ko mai yake da mun ta. "Ta ce ba komi my son" kawai yau tun da na tashi gaba na keta faduwa na rasa dalilin haka wllh. "Bakomi Mamy na karki damu in Sha Allah Alkairai ne, haka Ammy ma ta faɗa mun". "Yawwa dama ina san zan je gaisuwa" "To Mamy na yau she zaki je". "Yan zu haka a shirye nake kawai drive nake jirah". "Tom mamy fito na kai ki mana, Anjima naje office din tun da baki ma papy zaiyi daga Kaduna nasan har mun dawo basu zoba". "Tom shikenn na gode my son." Da kan shi ya kai ta gidan mutuwar sai gararan biyu suka dawo gida, tana ta masa godiya ya ce ba komi. Kai tsaye gidan ya shaga yayi wanka ya sake shirya wa sannan ya fito falon Ammyn sa. "Ammy yana ji gidan sai kamshi ya ke ne?". "Eh girme kasan dai papy zaiyi baƙi da ga Kaduna kuma ma sun sauka suna Company yan zu gida zasu wuto". "Ammy to ina papy yake, dama yau be fita ba? ". "Eh bai fita ba wai bayajin daɗi ne " "Tom shikenn bari na shiga na duba shi". Tuni su Jamal sun sauka a Company papy Amma a bun da basu fahimta ba shi ne, suna zuwa Dad ya basu wata hula ya ce su saka wadda iyya idan su ake gani, suna ta mamakin abun duk da sun san dad bazai taɓa cutar da suba. Sun huta a Company inda daga bisa ni wani yazo ya dauke su suka wuce gidan papy. Wani abu da yake bashi mamaki idan Jalil ko Jamal ya yi magana sai yaji tamkar yallabai Jawad ne. Yana sauke su comput din gidan, drive ya juya yace su cire abun su mai da cap din su, hakan kuwa sukayi ba musu. Dad ya kirah papy ya ce gamu a gidan ya ce bari Jawad ya zo ya shigo da ku. Gida ne mai matukar kyau da tsaruwa k'atan gida ne, wannan da iyya girman sa abun mamaki ne sai wasu man yan bishiyo da suka zagaye gidan ta ko ina, batun na faɗa maku kyauwun sa da girma sa bata lokaci ne. Wasu kuje ru dake gyefe suka Zazzau na suna jiran mai tafiya da su din ya k'araso. Jamal da Jalil sun ci wata farar shadda wadda ta masu mugun kyau, ga sabun fuskantar su ya kwanta luf, sai wani shek'i ya keyi. Papy na sauke wayar Jawad na shigowa, nan take ya masa baya ni. Kawai ma sai suka fito tare. Da yake sun ɗan juyawa kofar baya hakan bai basu damar ganin junan su ba, har suka k'araso gurin gaban su naɗan bugawa dad ya dafa Jawad suka juyo a tare!!. Suna kallan junan su, ya yin da jikin papy ya dauki rawa, ya tafi suuuuu zai fadi su Jamal suka rik'o shi, tuni Jawad ya yi suman tsaye. Jawad kallan su yake yi inda suma shid'in suke kallah, kallan jikin su suka din ga yi dan ganin wani banbanci amma basu hango shi ba. Da 'yar suka k'arasa falon papy, papy ya rungume su ya kasa sakin ko ɗaya daga cikin su yana jin wata kaunar su na ratsa shi, ko ba,a faɗa masa ba yasan wadandan 'yayan shi ne, kawai sai suka ga hawaye na bin idon shi suka rungume shi, suma hawaye na bin nasu idon, Jawad ma ya k'araso ya rungume su wannan kennan. Sun dade a hakan kafin su saki juna papy ya dinga shafasu wanda har yan zu ya kasa furta ko uffan. "Kwai sai yace ku tashi mu shiga ciki". Ta dakin aka bude wata kofa suka shiga babban falon gidan, suna shiga falon "papy ya farah kiran Ammy Ammy!! Ki fito kiga ikon Allah. Ammy ta fito jiki na rawa sai ta daskare a wajen da tayi tuzafi da su Jamal. Da gudun ta ta k'araso falon ta rungume su ta na fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi. Jawad ya tsaya yana kallon su. Har kasa Ammy ta kai, tana kuka mai tabba zuciya suka rike ta, sosai suna jin kukan nata har cikin zuciyar su. Tabbas ko ba,a faɗa masu ba wannan mahaifiya ce, uwa wandda tasan ciwan ɗan ta, sosai suka dinga kuka ajikin ta ba kuma wanda ya yi kokarin hana su. "Ammy ya isa kokan haka ce war Jawad dan Allah Ammy na ki bari kadda kiyi ciwan kai". Sai lokacin Ammy ta tsagayta da kukan sannan ta shiga shafa fuskokin su hawaye na anbaliya a kan fuskar ta. "Jamal ne ya dauki hannun shi ya kira kan fuskar Ammy, Ammy na dan Allah ki dena kukan nan ba gamu ba, a gaban ki, Ammy ba zamu taba barin ki ba, dan Allah Ammy ki maida komi ba komi ba, kinji. Sosai taji daɗin yadda Jamal ɗin ke gogye mata hawayen. Sai kuma ta mike ta shiga cikin ta shiga kawo musu abinci, da kayan tsaye tsaye, suna taya ta daukowa ita da su Jamal har suka gama. Cikin sanyin murya ta ce kuje kuci abinci nasan zuwa yan zu kuna jin yinwa sosai. "Jamal ya dafata ya ce to Ammy na". Nan suka shiga cin abinci, duk kan nun su Jawad ne ya kirah Mamy bata daga ba ya ce yasan maybe barci take yi amma bari ya karah kiran ta yana kiran ta kuwa ta daga"my son dama yan zu zan kira ka barci nakeyi ne sai yan zu na tashi naga kiran ka. Mamy bebyn papy bata nan ne, eh bata nan amma nasan tana hanya in sha Allah. "Tom mamy ki shigo yan zu ana neman ki". "Tom shikenn gani nan Allah yasa lpy". Dad ya yi shiru tausayi Ammy da papy ne ya gama kama shi tabbas waɗan nan sune iyayen su jalil to amma su waye su inna. Rashin wanda zai amsa masa tambayoyi da ne yasa ya yi shiru ya cigaba da cin abinci shi wanda ya yi masa daɗi ba kadan ba. "Papy ne ya kalli dad ya ce bani da abin da zan biya ka da shi Alhaji Bashir Allah ina mata fatan Alkairi a rayuwar ka data iyalan ka, tabbas iron ku suna da wahala na gode da dawai niya. "A'a papy ni banji dawainiya da su Jamal ba asalima sune sukayi da ni. Zasu baku labarin da kan su na sani. "Amma papy kana nufin ba kada wasu 'yayan bayan Jawad. "Eh babu ". Sai 'yar ɗan uwan na, guda daya sai ɗan uwan na. "To amma ina ɗan uwan na ka? Da yar tasa? . "Yaje Abuja ne, sai zuwa anjima zai dawo kuma bana so na kira shi ne nafiso yanzo ya gani da kan sa. "Yar tasa fa, dad ya kuma jefa mashi tambaya. " "Ta je unguwa amma yan zu zata shigo". mamy ce tayi sallah ma ta shigo d'akin, bakin ta ya tsaya cak sbd abun da idon ta ke gani, "my son wadan nan su wane haka, Mamy na ki shigo ya tashi ya shigo da ita ya ce ki zauna sannan ya ce 'yan uwa na ne Mamy amma ban san komi game da su ba. Su kuwa tunda suka ga Mamy suke kallan kallo dajuna, ba wanda ya iyya bayyana komi a kan ta. Sobda zahirin kallon da suke mata, na wata fuska ne da suke tare da ita. Nan take suka shiga basu labarin a hannun wadan da suke da kuma rayuwar da sukayi har zuwa yan zu da Jalil ke da auran Fatima. Ammy tayi farincikin da auran sosai tana ta addu'ar Ubangijin ya sa da rabo a tsakanin su zuwa yan zu, Ammy Allah take ruko ya nuna mata Fatima taga gata a wajen ta. Misalin ƙarfe 4:00 na yamma Dad ya yi masu sallah ma ya ce zai wuce gida sai bayan kwana biyu kuma, Zai dawo. Shima jalil ya ce zai bishi ko dan sbd iyalin shi, amma Ammy ta fashe masa da kuka ta ce dan Allah kar ya yi mata haka dan Allah kada ya tafi ya barta daga nan Dad ya tafi, sannan ya ce nan da kwana biyu zasu dawo shi da su inna da sauran su. Amma shi jalil take ya kirah Fatima ya sanar da ita kwana zaiyi, nan fa ta dinga masa rigima da 'yar ta hakura da niyar gobe zata taho Kano in sha Allah, ta shirya komi drive zai zo ya dauke ta, tayi farincikin sosai sbd ce mata ya yi sun samu aikin. Sun dade sosai suna hira daga bisani sukayi sallah ma. Ranar haka suka wani cikin farinciki, hatta Mamy jin daɗin ta yaƙi boyuwa sai kiran jalila take a waya tana ce mata tayi sauri fa ta dawo. Jawad ya ce Jamal ku tashi muje kuyi wanka ku huta, suka mike suka bishi sai da suka zo daidai saitin Ammy suka matso daf da ita suka sakar mata kiss a gishi, musamman Jamal yana matuƙar jin Ammy ta sa a ran shi. Ba wani bata lokaci suka shirya cikin kayan Jawad sannan suka dawo falo, lokacin har an kirah magariba dan haka suka wuce masallaci baki dayan su suka sa papy a tsakiya. Tun da aka shiga Masallacin ake kallan su, da matukar mamaki wasu na tambayar papy yana basu amsa da ya'ya na ne. Fuskar papy ta kasa dena murmushi sbd wanzuwar 'yayan shi a tare da shi, daga nan suka wuce gidan. Suna shiga falon sukayi karo da abin da ya tayar masu da hankali, wato Jalila cikin matukar mamaki Jamal ya ce Jamla ya yin da Jalil ya ce jawahir!!!. Mai ya kawo ki nan? Typing 📲 GAYYA CE! *Free page* *Written by* *Fatima alaramma lafazi* *(Falaramma)* https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ *Sadaukar kar wane ga Sadiq Abubakar CEO din lafazi Allah ya Kara masa lpy, da nisan kwana mai albarka, godiya ta musamman* 💖✨✨✨💞💋💋 Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan. ✨✨✨ Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya littafin, ina alfahari da ku ges nagode. PG 2️⃣3️⃣&2️⃣4️⃣ Ta so wa tayi ta rike su, tana kallon su ya yin da take sakar masu wani k'ayataccen murmushi. Batayi wani mamaki ba kuma bata kawo komi a ranta ba sbd Ammy ta sanar da ita komi. "Yaya ba suna na jawahir ba sunana jalila. Nan suka cigaba da kallan junan su, kafin daga bisa ni suka ce, papy akwai matsala. Falon suka k'arasa hannun Jalila rike da na Jamal, ya zuba mata manyan idon sa yana kallan ta. Juyowa sukayi suna kallan papy, duk kan nin su dan sun fahimci wannan din ba Jamla ba ce ba kuma jawahir ba ce. Take jalil ya kirah Fatima ya ce, my dear turumin pics din nan da mukayi keda su Jamal randa suka zo gidan ki, "ok tom my husband. Ba wani b'ata lokacin ta turo masa ya budesa nan take ya koma bangaren papy ya ce "papy su wane waɗan nan?" Papy ta tashi tsaye cikin tashin hankali, ya yin da ya mikawa Jawad waya, Jawad ya gani ya mikawa Ammy da ita kanta jalilan. Duk kan nin su cikin firgice da tashin hankali suke kallan junan su. Jawad ne ya fita ya kira Mamy ya sanar mata halin da ake ciki sannan suka shigo gidan, aka nuna mata pics din ta fashe da kuka ta rungume Ammy tana faɗin Ammy wane ya aikata ma na wannan abu?, Ammy wane wanda baya san farincikin mu? Ta kuma fashe wa da kuka. Ammy ce ta shiga bawa Mamy hakuri, tana rarrashin ta. Suna haka papa ya yi sallah ma, idon sa ya sauka kan su Jamal, baki na rawa yace kune, kunne kuka dawo ta inna kuka bayya na, nan take hankali kowa ya dawo kan papa sbd magan ganun da yake faɗa. "Papy ya ce wa papa dama kasan su ne?" Nan take hankalin shi ya dawo jikin shi. "Ya cewa papy ni ban sansuba, kaddai ka ce 'yayan ka ne, baka tuna nin wannan wata sabuwar hanyar dan Farah ce, aka fito maka da ita, ni gaskiya ban yadda da wannan maganar ba. "Ammy ce ta bude bakin rai ɓace ta ce wannan wacce irin magana kake yi papa, an ya kuwa kana cikin tuna nin ka ta faɗa rai bacce. "Mamy ta ce kwai kuwa Ammy dan wannan ba maganar hankali ba ce. Papy cikin matsanancin fushi ya farama gana, karfa ku manta papa ne yake Magana yayana. Su Jawad suwa sai kallan shi suke dan basuga wani banbanci da papy ba. Papy ne ya jawo papa ya zaunar da shi, sannan ya farah masa bayani, nan fa ya nuna mashi pic din su jawahir, nan take papy ya farah faɗa yana ce wa Ni za,a zalin ta, da kai za,ahad'a baki a cuceni papy, tom wllh ba zan yarda ba sai ana kai ƙarah koto wllh kotu zan kai, wannan ai haɗin baki ne. Gaba daya ya gigice ya fita hankalin shi, sai wani san batu yake kamar tsohon mahaukaci, ai ni ba haka nayi ba, wannan shirme ne. Papy ne ya cigaba da bashi hakuri yana lallabashi daga bisani ya fita sai gashi da mota sai a yau zai je ya tawo da 'yayan shi ba zasu ƙarah kwana ba tare da mahaifinsu ba. Da yar aka shawo kan shi ya hakura, ya barwa gobe, sbd sosai dare ya farah yi. Papy ne ya kirah Dad ya sanar da shi komi nan take hankali Dad shima ya tashi, ya ce shima wllh bazai lamun ce ba. Dan haka ya dauki hanyar gidan inna. Yanazu kuwa ya yi tozali da jawahir tsaye tana zan ce, cikin matsanancin mamaki ya k'arasa gaban ta, ya rike hannun ta, yana mata magana, shi kuwa baƙon ba haiba ya gaida shi ya wuce ya tafi. Sosai ya lamarin papa ya farah bawa Kowa tsoru, tuni kowa ya farah mamaki da lamarin shi, papy kuwa ya kasa kewa komi sbd mamakin ɗan uwan na shi, ko su Jawad ya kasa kallah sai ruwan masifa ya ke ana bashi hakuri. Shi kam Dad kwana ya yi cikin al,ajabi sannan ya ce shi koto zai kai dan bazai lamun ci wannan lamuran a kwai rainin hankali a cikin shi. Tuni su Jamal sun shiga lamuran su a gidan musamman Jawad wanda har dakin Ammy shiga yake, shi dama tun ba yau ba yake zargin su inna da tantamar kasan ce warsu iyaye a gabe su, saboda babu wata alama da zata nuna hakan. Hakan ne yasa ya saki jiki sosai a gidan iyayen na sa. *Kaduna* Fatima tuni sun dauko hanyar Kaduna har mom din ta ma sbd suma suna da 'yan uwa hatta wan mom ma anan Kano ya ke. Suma su Dad da su inna Babba jawahir da Jamla su nufu Kano cikin yarda Allah suna dak da ƙarah sowa cikin ta. "Jalil ne ya kirah Fatima ya ce kun kusa k'araso wa ne, tace eh gamu a unguwar Nassarawa G. R.A tom shikenan amma dan Allah ku shigo da mom sai su gaisa da Ammy kinji, Tom shikenn ba damuwa. "Sai kun dawo". Suna shigo wa gidan Fatima ta ga Jawad da gudu ta k'arasa gaban shi ta murmushi ta kai hannu zata taɓa shi ya yi saurin janye jikin shi. "Tare da ce mata sannu da zuwa ku shi go suna ciki. Yaya Jamal ina yaya Jalil din yake, murmushi ya mata sannan ya ce ni Jawad ne duk suna ciki. Nan ta dinga kallon shi cike da mamaki maganar shi. Amma bata iyya furta ko da alifun ba. Sai kallan girma gidan ta keyi da kuma haduwar sa, ga kuma wasu manyan motoci na ban mamaki inda kasan ba da kudi ake siyan su ba. Sallah mar da sukayi a Fallon ne ya sa papy saurin dagowa sakamakon shine kaɗai a falon, sau ran duk suna main falon. Jiki na rawa su Fatima ke kallon papy shi kam sai sakar masu murmushi ya ke Fatima da mom ce suka tsugun na suka gaida shi ya amsa cike da farincikin, sosai ya ke kallon mom ya ce kamar Hajiya Maryam ko, matar Alhaji Bashir marigayi. "Mom tayi murmushi ta ce ni ce". "Allah ya gafarta wa Alhaji Bashir". "Jawad ya ce papy wannan fa matar jalil ce" nan Dad ya karah faɗa murmushi sa ya ce kace 'yata ce matsu kusa da ni 'yata fadimatu Allah ya maki albarka. Jawad ya shiga cikin ya barsu da papy dan papy mutum ne mai san muta ne jalil ne kuma ya yi irin halin shi kaf cikin 'yayan na shi. Haka dai sauran 'yan gidan suka shigo falon gaban Fatima ya sake bugawa sbd ganin su Jamal ɗin su uku gashi sai murmushi suke sakar masu a tare. Ammy ta rungume Fatima da mom tana ta gaida ta, ta na masu sannu da zuwa sannan ta shiga da su daki dan basu abubuwan tabbawa. Su Jawad da Jamal da jalil suka zo suka gaida mom sannan suka tafi, Jalil ya zauna gyefe yana magana da matar sa. Ammy ce da kanta ta zo ta masu baya ni sannan ta kai su wani daki dan su huta. Sai misalin ƙarfe 1:30 daidai su Dad suka sauka, a kan idon papa tuni ya rungumo 'yayan shi yana ta masifar shi, ya na shiga falon ya dinga kiran jalila kizo ga 'yan uwa ki, wanda aka rabaki da su tun yarah. Ita nan ta zo ta rike su suna ta kuka da jin tausayi junan su. Bayan komi ya lafa aka yiwa kowa baya ni sannan Dad da papa suka ce duk basu yadda ba, dan haka suka ce kotu zasu kai, sun da har abun nasu yakai musayar yawu da fad'awa junan su bakakin magan ganu. Ba wani bata lokaci a ka shigar da karah kotu, cikin gaggawa. Aka basu ranar Monday domin Farah shari,a. Daga nan Dad ya yi gidan shi da 'yarsa. Wanda ita ma ta kasa juya masa baya, tabbas tana jin tausayi Dad din ta in dai ya kasance ba shine mahaifin ta ba, sbd ya dauki buri na duniya ya daura a kan ta. Su kuma su inna ba wani abu da suka ce dan zan cen na manya ne. Duk da Jamal ya samu Babba ya ce kadda su lamun ce ya ce shima yarsa ce. Kuma su a gidan aka basu guri suka zauna. Inna kuwa ta lamun ce da su Jamal ba ya'yan ta bane, sbd daga zarar ka kalli papy kasan shine mahaifin su ko shakka babu. Amma abu guda daya daya ke bata mamaki shi ne to ina ɗan da ta haifa, ina cikin da taje Hospital da shi?. Ta lamun ce sbd ta fahimci shi papy mutum ne mai sauƙin kai da hakuri. Ko da wannan abun ya faru, ce mata yake inna karki damu ko a yanzu 'yayan ki ne su Jamal haihuwa su kawai mukayi amma komi kune. Ubangijin ya saka maku da mafificin Alkairi daniya da lahira, shida Ammy sun rasa ina zasu saka inna. *Mamy* Lokacin da ta dora ida nun ta kan su Jamal ta tabbatar da waɗan 'yayan ta ne ko ba,a faɗa ba. Sosai su jawahir da jamla suka zuba mata ido suna kallon ta ya yin da ita Mamy tayi ƙasa da kanta ta fashe da wani marayan kuka mai taɓa zuciya. Su jawahir da jamla ne su karah sa gaban ta suka rungume ta suna lallashin ta basu taɓa jin wani dad'i da nutsuwa ba irin na yau da suke jikin mahaifiyar su. Take suka Farah bata hakuri suna lallashin ta har tayi shi, jawahir ta kwanta a jikin ta tanajin wani dad'i na ziyar tatta ta ko inna. Ko bayan da aka gaba jawabi bin Mamy sukayi gidan ta suka dinga mata hira suna kwantar mata da hankali. Har daga bisani suka dawo gidan Ammy. Tun da wannan abu ya faru Mamy ta kasa ce wa komi, duk wanda ya kalli mamy ya kalli su jawahir kasan mahaifiyar su ce. Amma ita duk wannan abun daya faru bata rasa nasaba da papa. Sbd papa mugun mutum ne Mamy ita kadai ce tasan zahirin halin sa sai Jawad, kuma tayi shiru ne badan komi ba sbd yadda taga papa ya daga hankali shi, ita ke bawa su Dad hakuri ma, kuma ita ce ta cewa Jamla tabi Dad din ta, da Amincewar Mamy tayi komi. Duk da a zahiri gaskiya Mamy tasan waɗan nan jinin ta ne daka jikin ta suka fito. *B'an garen Dad* Koda su Jamal suka koma gida su dake garin kano, Dad cikin tashin hankali ya wuce gidan wanshi ya sanar da shi halin da ake cin. Sosai Abban Yusuf ya jinjina lamari amma ya cewa Dad zan baka wata shawara karkayi faɗa da wannan family ɗin ba zaka iyya Shari'a da suba. Amma fafur Dad ya ce sai yayi haka ya barshi tare da musu addu'a. Sun dai dai ta lamarin shi da Jamla in da su ka kifad'awa mom gaskiya sbd a yan zu ta shiga watan haihuwar ta ba,asan wata damuwa a tattare da ita. Kuma Jamla tana ta kwantar wa da Dad hankali harya sa mu ya nutsu sosai. Su kuwa su Fatima da jalil wata sabuwar babin soyayya suka bude, inda kuma ko umm ta ce sai Mamy ta tambaye ta mai take so. Hatta mom Fatima mamakin yadda Ammy ke kaunar Fatima take. Ga kuma kullum idan suka fito falo suka haɗu da papy ya dinga wa mom godiya kenan. Har kunya kamata take yi sbd godiya da papy da Ammy ke mata, kuma tuni ta kirah Farouk ya sanar da shi komi yace zai dawo nan da kwana biyu. *Bayan kwana biyu* An shiga kotu, an Farah tattaunawa akan komi. Inda kowa yake kawo hujjojin shi, ma su kwari. Gidan Radio da TV da jaridu da newsperper sun naɗa tuni abu ya farah yawo a duniya. *America* Doctor Adam ne ke kwance jikin na shi da sauki sosai yan zu an tabbatar da kansa ce ta kama shi kuma taci ƙarfin shi sosai. Ahmad ne

Chapter 7 of 10