Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 10
ne ya ɗaga cup din yakai bakinsa. Baiyi tunanin komai ba Dan haka ya kurba da yawa, ai baisan sadda yayi saurin fesar-waba. sabida yan'da yaji wani azabar gishirin daya kusa cire masa har-she kan tsabar kaifinsa, cikin tsananin bacin rai ya kalli Jalilah tare dayin kwafa, Tsaki yayi ransa idan yayi dubu abace yake. Ammy da papy ne sukashiga tam-bayar'sa ko lafiya? kasa magana yayi sabida tsananin bacin rai, idanun-sa sun kada sunyi jajir, makoshinsa har daci yakemasa tsabar takai-ci, baice kala ba ya mike ya bar fallon. Binsa sukayi da kallo cikin mamakin ko lpy? *GARIN KADU NA* "Jawahir! ki fito haka mana kafin dare yayi kin san fa bana san ki dinga kaiwa dare suyar Awarar nan ko?" "ganinan mama azkar din nan nake son na karasa kafin na fito." " kuma insha Allahu zata kare da wuri, " "insha Allah." cewar mama, Kyakykyawar datti juwar-da aka kirah da mamace na kallah, bawata babbar mace bace dan ashe karu bazata Fi 40 da haihuwa ba, amman kana ganin ta kasan akwai wahalah a tattare da ita, ga kuma wata rama dan abushe take sosai zanin jikin'ta duk yabi ya kode ya jeme, mataccen gida ne mai daki biyu da wani gajeran ban daki idan kafiye tsayi ka shiga wanka tsab Wanda kekusa zaigan'ka, Tsakar gidan bayada Fili kokadan . duk ya farfashe dagani kaga gidan talaka wanda kekar-bar rayuwa, "Jawahir!". "gani mama." "haba ki fito mana zaman ya isa haka," " gasu SANI sun kai maki kayan suyya tun dazu kilama man yayi zafi," " dan nasan SANI zai hura wutar", "kifito dare fa yanasakeyi," mama ta kare zan cen cikin gajiyawa da surutu. "To mama gani nan." Kyakykyawar budur war da mama kekira Jawahir tafada, "yauwa fito haka", mama dake wanke wanken tayi maganar. "yauwa mama gani zan tafi kiyimin addu a", "Tom Jawahir Allah ya tsare ki a kula dan Allah ki kama kan ki kinji?" "sabida shi talauci ba hauka bane kuma ki ƙara kula sosai Allah yayi maki albarka," addu,ar da mahaifiyar ta ta kemata a kullum idan zata fita suyya kenan Kuma tana matukar tasiri aran'ta, Lokacin da nakarewa Jawahir kallo Saida Al kalamina yakusa faduwa domin-ko batada ban-banci da bebyn Papy, Komai Nasu iri dayane tamkar an tsaga Kara. KUBIYO NI DAN JIN WACECE WANNAN DAKE MATUKAR KAMA DA BEBYN PAPY ?????? INA GODIYA SOSAI MASU BIBIYAR WANNAN LITTAFIN TAKU HAR KULLUM FALARAMMA *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• Typing 📲 GAYYA CE! *Free page* *Written by* *Fatima alaramma lafazi* *(Falaramma)* https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan. ✨✨✨ Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya littafin, ina alfahari da ku ges nagode. PG5⃣&6⃣ Tabbas wannnan ba bebyn papa bace to maima zai kawo bebyn papa nan. Ita kuwa jawahir sakai tayi tafita wani karamin mataccen soran su wanda ko rufi babu asaman shi. Kai tsaye bakin yar kasuwar dake gefen gidan nasu ta tsaya ta zauna kan kujerarta ta suyya dan kuwa tayi sa,a man yayi zafi sosai ta farah zuba awarar, nan da nan aka farah siya Alhmdllh. misalin takwas da rabi na 8:30pm suka gama ita da sani suka haɗa kayan zuwa gida. Da sallama ta shiga ɗakin mama ta zauna gefen wata lametsatsiyar katifa yar bodin, "mama na dawo" "sannu da dawowa jawahir ya kasuwar? Alhmdllh sai godiya, "ma sha Allah cewar mama tare da karɓar kudin da jawahir ɗin ke miƙomata tafarah irgawa nairah dubu goma ne da ɗari biyar da hamsin kudin, " mama ce ta kalli ƴar tata tace Allah ya maki albarka tashi kije ki kwanta sai Allah ya kaimu kiyi addua kafin ki kwanta" idan kuma zakiyi wanka ga ruwan zafi can, "banajin daɗine kai na ke ciwo, "to mama Allah ya baki lpy sannan ta fice abunta tare da taisayawa mahaifiyarta ta wannan kenan. Yau ne ya kama ranar monday ranar da bebyn papa zata farah zuwa company dan aiki da ɗan,uwan ta Jawad. Tsaf ta shirya cikin doguwar rigar Atamfa da kalar pinky mayafinta da jakarta duk pinky tayi kyau sosai dan bebyn papa kyakyawace ta ajin farko. A babban falo tayiwa kanta masauki dan jiran fitowar papa, batafi minti 2 a wajen ba papa ya fito riƙe da jakar shi a hannun Ammy, cikin farinciki beby ta ƙarasa gaban papa ta rungume shi tana mashi barka da fitowa "Kallanta yayi cikin farinciki sannan yace bebyn kinyi kyau sosai fa", mushi mushi tayi tace ngd papana. "sannan ta kalli Ammy tace sorry Amma na ina fatan kin tashi lpy, "Dariya Amma tayi tace wato sai yanzu kika ganni ko" Dariya bebyn papa tayi tace kinsan babu wani abun gani muddun papana na kusa dani wannan kenan. Kai tsaye bakin motar papa suka tsaya, yayin da beby tuni ta shige papa kuma sukayi sallama da Ammy sannan suka ɗauki hanyar (J. U. J) company beby ce a gyefen papa tana ta zuba mashi surutu can kuma tace papa na, tafaɗi cikin wata murya, "kallanta ya ɗago yayi dan ya fahimci magana zatayi yace na,am bebyn ya akayi" Papa wai maiyyasa yaya jawad bazaiyi aure ba?, papa akwai ƴan mata da dama da suke san yaya jawad fa, kuma ayanzu yaya jawad yanada shekarun daya dace yayi hakan, musamman idan kafahimci yadda bayasan yawan shigarsa jama,a papa a tunani na ya kamata asamu wadda zata saka yaya jawad farinciki koyaya ne ta ƙare maganar tana kallan papa, wanda shima ita yake kallo" "Tabbas wannan maganar taki akan gaskiya take beby Amma matsalah guda ɗaya ce wacce zata iyya zama da jawad a irin halin nan nashi yaro saiya wuni baice kallaba, ya ƙare zancen cikin jimami" haka ne papa amma wllh nasan za,asamu sbd yaya jawad ne mutum ne na musamman ga addini da sanin ya kamata" Tom shikenan beby in sha Allah za,asan yadda za,ayi yawwa beby yau da safiyar nan mrst Obey ya kirani za,aje garin kaduna dan tabbatar da wannan yarjejeniyar ta haɗa kwangilar mu dasu amma inaso keda jawad kuje tare nan da sati ɗaya dan ni bazan samu dama ba", Ba damuwa papa na Allah ya nuna mana lokacin, daidai nan kuma sukayi parking harabar company. "Mom na faɗa makifa ni makaran tar da yaya yusuf yake koyarwa nake so a kai ne haba Jamlah wllh bana so akai ki makarantar da yusuf yake wllh sbd takura ma shi zakiya sam bakiji wllh nifa mom indai ba canba na fasa, aa aa meyake faruwa a falon nan haka wani matashin dattijo yafaɗa, "yauwa Dad kwarah da kazo mom ce wai baza,a kaini makarantar da yaya yusuf ke koyarwa ba, ta ƙare maganar cikin tsagwaɓa, mom dake zaune tace wllh kasani dad indai aka kai jamlah makarantar da yusuf ke koyarwa an ɗauki hakkin shin sbd sam jamlah bataji sai dai shirin Allah, " zama yayi kan kugerar gefen shi sannan ya jawo jamlah jikin shi yace mamana ki kwantar da hankalin ki, yau da safiyar nan natashi da canjin wajen aiki an maida ni kaduna kuma nan da kwana uku zamu koma da izinin Allah sannan akwai wani makaranta a kaduna dana sama maki zaki farah zuwa na kuma siya maki motar d za,adinga kaiki makaranta da itta dan banason kina driving,"cikin farinciki Jamlah ta rungume mahaifina nata tace dad nagode fa sosai ta kuma fashe da kuka tace dad ubangiji ya maka abunda kamana Allah yasaka maka da mafifincin Alheri ina sanka my dad, "ya ƙara rungeta jikin shi yace nima hk my jamlah, daga nan zance ya ƙare wannaan kenan. Da misalin ƙarfe biyar na yamma jamlah tafito dan zuwa wajen gidan yayan mahaifin nata wato gidan su yaya yusuf a bakin kofar gidan ta tsaya tana kallan ko inna kafin daga bisani naga tayi murshi ta ɗibi ƙasa tashiga gidan bakin ta ɗau ke da sallah ma tayi kuwa sa,a babu kowa a tsakar gidan dan hk tasa kai zuwa ciki kai tsaye har zata shiga falon taji ana buɗe kofar banɗaki tayi saurin tsaya wa yaya yusuf ne yafito da alamar wanka zanyi harya shiga ya manta wani abu sai ya fito, kai tsaye ɗakin shi ya faɗa ko kulah ta ɓeba sbd sanin hali. Tana hangar haka tayi sauri komawa da baya ta shige ban ɗakin ta juye wannan ƙasar ta hanunta a cikin ruwan wankan shi sannan ta fito da sauri ta faɗa falon mama, kan kugera ta zauna ta kalli mama tace mama ina wuni mama "lpy lau jamlah ya mom ya kuma sanyi sanyi dama lokacin lokacin sanyi ne, " mama duk lpy suke sanyi kuma Alhmdllh", amma mama naji gidan shiru ina safiya ne" " ohhhhh safiyya taje gidan yata ne may be anjima ki ganta", yayan ku kuma ya shiga wanka" haka dai suka cigaba da hirar su, sbd ita mama mutumce ta jamma,a gashi kuma Allah yasa tana san jamlah, bayan misalin mintina 15 sukaji an bugo ƙofa a ɗan tsorace mama ta ɗago tana kallan yusuf dake tsaye bakin falon ransa amatuƙar ɓace," ya fara magana wai maiyasa jamlah kin rainani ne arayuwarki kin hanani jin daɗin rayuwata kullum acikin haduwa da ƙalubalen ki nake haba jamlah," " mama wai yusuf mai yarinyar nan ta maka ne daga shigowar ta gidan nan gaba ɗaya ka takurah mata meta maka?" " mama sai da nakai ruwa na zan shiga wanka fitowar da zanyi naga jamlah dama duk jikina yayi sanyi sbd ganin yarinyar nan ba alkairi bane a gare ni, nashiga wanka na farah kenan naga ruwan nawa duk ƙasa gashi nariga na saɓe jikina haka na watsa na fito gashi babu wani ruwan zafin ga sanyi ta kyauta min kenan?" "yaya yusuf nifa ban san ruwan ka bane nashi banɗaki wanke hannu na amma bada ganganba" "mama tom kaji dai abinda ta faɗa bada niya tayi maka hakan ba sai kayi hkr" yajuya zai fita tayi mashi gwalo nan mafa rashi ya ƙaraɓaci, kaɗan daga takurar da jamlah kewa yusuf kenan, wanda ya kasance ɗan wan baban ta. Cikin ikon Allah dad ya gama shirya komi nashi yau ne zasu koma garin Kaduna dan cigaba da aikin shi, mom ce abakin mota ita da dad sai jamlah dake gefenta idon ta cike da kwallah gefe safiyya ce ƙanwar yusuf sai yusuf wanda murmushin kan fuskar shi ya kasa ɗaukewa, yayin da yake tayiwa su mom fatan nasarah, mom tuni ta shige muta yayin da Dad ke jiran jamlah, " jamlah ki ƙarasa mana ki shiga mom na jiranki fa, ta tsinci muryar Yusuf na faɗa mata, fuska dauke da murmushi, kallan shi takeyi sai kuma ta fashe da kuka tace nasan yaya yusuf daɗi kakeji sbd zan tafi, Ummm jamlah kenan ba haka bane yaza,ayi da abinda Ubangiji ya tsarah, amma gaskiya jamlah naji matuƙar farincikin tafiyar ki duk da bazanyi kewar ki ba. ya ƙare maganar yana murmushi", wannan magan ganun duk yana yinsu ne yayin da yazu daidai kun nan ta, tafaɗa mutar tacigaba da kuka yayin da dad ya jah mutar suka bar layin yusuf yanata ɗagawa jamlah hannun fuska ɗauke da murmushi. "Dad mom kinsan wani abu? aa dad sai ka faɗi akwai wasu samari ƴan biyu sune waɗan da zasu dinga kai jamlah makaranta, yaran nan muta nan kirki ne baki ga yadda suka burgeni ba mey be ma kigan su yau idan mun isa. "Mom tom dad Allah ya kaimu lpy sai na gan su kasan ina san yan biyu wllh, da haka dai suka cigaba da hirar su abun sha,awa yayin da tuni jamlah tayi barci abin ta. Misalin ƙarfe 5:00 na yamma suka sauka garin kaduna, gida ne mai matukar yau da tsaruwa duk da part-part ne gidan kana gani kasan na ma,aikata ne wannan kenan. "Yau ne bebyn papa ta farah aiki company papa hatta ma,aikatan company sun ji daɗin ka san ce war ta agare su sbd beby mutum ce mai girmama manya da san muta ne. shiyasa sukaji daɗinta kuma sosai ta maida hankalinta wajen aiki da yayan nata batasa wasaba ko tsokana duk da taɗauki aniyar in sha Allah sai company papan ta yafi na kowa, acikin garin kano, kuma saiya zama wanda za,ayi alfahari dashi, duk da batasan wannan shine mafarkin jawad gabaki ɗaya ma wannan kenan. "Dad ku shigo zaku gaisa da mom jamlah nakuma yi mata bayanin ku, gakuma ƙanwar taku itama" Jalil da jamal sai Allah juna sukeyi suna dariya, dayake suɗin muta ne ne masu abin dariya musamman jalil nidai ban wani ƙare masu kallo ba nayi bayan su zuwa ɗakin dan gari yayi duhu sosai bana iyya kallan su yadda ya kamata. Zau ne suke a katafaren falon ƙansu a kasa sunata hirah, "jalil ne kecewa jamal kagafa kwarah da muka karɓe aikin nan wllh ko Abinci zasu na bamu munaci muna ƙoshi ai mun samu, jamal kai jalil dallah kayi mana shiru sai yarin yar tazu ta raina mu, idan taji maimuke cewa, Banza acici kawai", kafin ya ƙara wata maganar mom tayi sallah ma ita da dad suka kun na hasken ɗakin baki ɗaya nan take ida nuna suka sauka kan jalil da jamal wanda ganin nasu ya rikitar dani baki ɗaya, sbd tsan-tsar kama da Allah ya masu, amma wani babban dimaucewa danayi shine ganin zatin jawad din papa a tattare da waɗan nan bayin Allah. wannan kenan.😜😜 TAKU HAR KULLUM 😍FATIMA ALARAMMA 😍 INA ALFAHARI DA KU Typing 📲 GAYYA CE! *Free page* *Written by* *Fatima alaramma lafazi* *(Falaramma)* *_🔥✍️ The Expert Pen's 🔥_* 1. _Uwar Batool._ 2. _Fatima Alaramma._ Gayya ce! 3. _Habibty Muhab._ 4. _Fateyzahraah._ _*Gwanayen Marubuta✍️🫶🥰.*_ *Sadaukar kar wane ga Sadiq Abubakar CEO din lafazi Allah ya Kara masa lpy, da nisan kwana mai albarka, godiya ta musamman* 💖✨✨✨💞💋💋 Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan. ✨✨✨ Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya littafin, ina alfahari da ku ges nagode. PG 7⃣&8⃣ ...............Cikin satin nan sosai bebyn papa ta maida hankaki wajen aikin nata, duk da a wannan satin ta fuskanci abubuwa da dama wanda ta gani daga papi din nata wanda ya nuna mata tsan-tsar rashin jin daɗin sa ga,aikin nata a company sbd beby yarinya ce mai basirah sosai. Kuma a wannan satin sosai suke zaman lpy da jawad wanda ya zaman to har lokaci yake bata suyi hira dashi, tare ma suke komawa gida shida ita sosai abun yayiwa Ammy daɗi dan ganin yaron nata ya farah can zawa Alhmdllh. Yau ma kamar kullum a bakin kaskon Awarar ta na taddata cikin nutauwa kamar yadda ta saba, sai dai kullum idan nazo wajen Awarar ta ina matukar al,ajabin yadda magana bata dameta ba ko yawan kallan mutane abinda yake ga ban ta shi kaɗai takeyi, kana kallan yarin yar kasan baiwar Allah ce ta ƙarshe, sai dai rayuwa ta saka ta gaba, ga kuma rashin lpyr mahaifiyar tata, wanda shiya ƙarah dagulah mata lissafi. Kamar daga sama najiyo muryar jalil yayi sallah ma, tare da kiran sunan jawahir ya kasuwar ya kuma jikin mama "Ɗagowa tayi ta kalle shi sannan tace da sauƙi sosai wllh yaya jalil yau ina yaya jamal ɗin", "kin gashi can wllh yana hutawa abin shi waishi baya so azo a dameki sbd karki daɗe a nan, nikuma nace sai nazo kin sanni da surutu." "Ɗa gowa ta yi dauke da murmu kan fuskarta tace yaya jalil kenan." Haka dai sukayi ta hira a tsaka nin su kuma duk hirar tasu hirar jamal ce, Anan ne jalil ke bawa jawahir labarin gidan aikin da suka samu, sosai tayi masu murna inda kuma shima yake mata tallan idan zata dinga zuwa tana masu girki suna ne man mai girki tace zata faɗawa Mama taji mai zata ce. " Nan fa yace tabar shi ma zaije wajen Maman da kan sa. Jalil wai jawahir na tanbaye ki mana?" " ina jinka yaya jalil ankai Mama Asibiti kuwa?" "A,a wllh ni kuma nayi tunanin hakan bani da kuɗi ne ga kuma Babba baya gari amma insha Allah gobe za,a kaita ta bashi amsa", "kinga insha Allah idan mukaje muka kai yar Alaji makaran ta sai nataho da mutar sa mukai mama asibiti, zan tanbaye Shi". "kana ganin ba matsalah" "eh babu in sha Allah," Da wannan suka cigaba da tattaunawa. MENENE ALAƘAR SU JALIL DA JAWAHIR? ........Asali dai sun zauna gida ɗaya suda iyayen su a kwanakin baya ne da akayi wani damuna mai ƙarfi ta rushe ɗaku nan su Inna su jawad suka zube shine suka koma makotan su da zama a yan zu ma maƙota suke da juna, jalil da jamal sun kasan ce muta ne ne masu san junan su da kuma tausayin iyayen su, duk da duk kan nun su talaka wane na karshe wanda duk tsawan rayuwar su suka ƙareta a haya suda mahaifin su wanda shima yanzu watan shi ɗaya da mutuwa sai innar su wadda ita ba batada wata isha-shiyar lafiya sbd fama da hawan jini. Ita kuwa jawahir sun zamema ta tamkar katan gane a gareta sbd tun tana ƙarama tasan su a gida ɗaya kuma kallan yayye take masu, kuma tana matuƙar sannu dan jinsu take tamkar jinin ta, wannan kenan. Bayan ta kammalah siyar ya ta ya ta kwa she ka ya suka wuce gida wanda shi kuma jamal tuni ya koma gidan, amma ga mamakin su sallah mar da zasuyi gidan su sukaji shi a ɗaki shida mama anata hira kaɗan-kaɗan shi kuma yanta jarah mata sannu. Suma ɓuɗe labulan sukayi bakin su ɗauke da sallah ma suka shiga suka zauna, suma tare da jerawa mama sannu, "Nan take ta meke zaune cike da ƙarfin hali "tace karku damu ƴaƴan ai naji sauƙi Alhmdllh kuta tayamu da addu,a dai, "In sha Allah cewar su baki ɗaya, nanfa jalil ya labar ta mata maganar aikin nace ta Amince tunda dasu ne ba matsalah, shi dai jamal ɓeji daɗin hakan ba amma bayadda zaiyi, yakuma gayamata zance asibitin nace da sun barshi amma sukaƙi yar dah sai da ta amince. wannan kenan. ..........Yau ki manin sati biyu kenan da farah aikin Bebyn papa kuma a yau ranar friday su jawad da jalila zasu wuce garin lagos da ka nan suyi Abuja inda anan ne zasu haɗu da papa da papi zasuje ɗaurin auren ɗan uwan mahaifiyar su. Tsaf sun shirya bebyn papa cikin wani dogon hijabi jalbab pink wanda yayi mata kyau sosai sannan zasu nufi airport driver papa ne zai kai su, sosai sukayi sallah ma da iyayen nasu inda papa yace wa jawad gafa ƴata nan amana zaku sauka gidan baba yasir anan ne zakuyi komi naku har kwana akwai fadilah yar sa saisu dinga kwana da beby, sosai yayi masu baya ni yayin saka maƙon shi bai taɓa zuwa gidan ba, daga wannan suka wuce ko kaɗan ban hangi papi a wajen ba shi kansa papa ya kasa gane kan papi kwana biyu nan gashi kuma sai karɓar kuɗaɗe yakeyi a wajen shi wanda shiɗin ya kasa gane meyake yi da kuɗin amma ko ba komi yana fatan Ubangiji yasa ɗan uwan nashi yana lpy wannan kenan. Cikin ikon Allah sun sauka garin lagos lapiya inda basu wani ɓata lokaci ba aka ɗauke su zuwa gidan Alhaji yasir, kuma Alhmdllh sun samu tarba ta musamman musaman da akwai jafar wanda zaiyi sa,an jawad, ita kuma jalilah akwai faɗilah Alhmdllh. Yan zun haka zaune suke kan daining table inda suke diner suna hira gwanin sha,awa duk da shi jawad baya cewa ko ƙalah sai dai kawai idan maganar taɗan burgeshi ya ɗago ya kalle su ya juya, a haka har aka gamacin abincin inda jawad yayi ma su Alhaji yasir da kallah sallah ma ya shige ɗaki abin shi sbd dama agajiye yake, bai jima da tafiya ba suma faɗilah da jalilah suka miƙe tare da sallah ma suka wuce ɗakin su. Jalilah bush kawai tayi takwanta abinta, yayi da faɗilah ta dameta da tanbayar yayan nata, wai ya burget sosai tayi murmushi tace dasafe zamuyi magana wannan kennan. ..........Cikin shigarta mai kyau fuska ɗauke da liƙaf, hannun ta ɗaule sa school bag jamlah ta fito faton, dama tuni ta ƙarya dan haka babu ko ɓata lokaci tayiwa su mom da dad sallah ma, su kuma suka bita da nasihar riƙe matumcin ta tare da mata fatan Alkairi. Harabar gidan tafi to, nan take idanun ta suka sauka kan kyakkyawan saurayin dake gabanta wanda ya haɗu ta ko,ina ba ƙarya sosai ta kafe shi da idanu tana kallan shi kafin daga bisani shi kuma jamal ya fahimci kallan da take mashi, gyeran murya yayi nan take ta dawo tunan nin ta. Jalil daya ƙara so wajen ne tayi saurin kallan shi ciki da tsantsar mamaki, tayi ƙarfin halin cewa ina kwanan ku, murya na rawa, cikin mamaki suka ɗago suna kallanta suka ce "kin tashi lpy," "kawai ɗaga masu kai tayi alamar eh" ta shige mutar gabanta sbd gaba ɗaya jikinta asanyaye yake, bayan ta shiga ne jalil yace wa jamal, " jamal kaji muryar yarinyar nan inda lasan jawahir, ummm kawai jamal yace, "kaga jamal muyi sauri kasan zamuje kai mama asibiti kagayawa Alhaji? "eh na faɗa mashi yace babu matsalah suka shige motar suna cigaba da hirar. Har suka sauke jamlah A school bawanda yace wa wani ƙalah, ita kuma batayi magana ba saboda yadda jikin ta yake a san yaye. wannan kenan. Jamal ne da jalil ke gaban likita yana mashi ba ya ni kan abunda ke damun mama, sosai abun yayiwa mama yawa dole ta jigata haka, amma yanzu Alhmdllh an ɗorah ta kan wasu magunguna amma zata kwanta a hospitak ɗin na tsawan kwanci ko mako ɗaya dan ƙarah tabbatar da lpyr tata. Alhmdllh sun biya komi na aikin batare da jawahir ta sa ni ba sannan suka fita dan sanar da ita halin da ake ciki. lokacin da suke faɗa mata sosai hanakalinta ya tashi amma suka kwantar mata dashi, sannan suka ce taje

Chapter 2 of 10