gaban su. Mai pic ya ce ki tsaya kiji zaki rungume mijin naki ne kinga ne ta daga mashi kai.
Tafiya take tana kallan su suma ita suke kallah amma tafi gazgata Jamal ne a matsayin jalil da Jamal ya fuskanci shi take nufa sai ya daga mata girah batare da kowa ya an karah ba aikuwa ta faɗa jikin Jalil nan fa guri aka saki dariya. Shima haka ya rungume ta a jikin shi yana sakar mata murmushi mai k'ayatarwa, ya farah mata magana a kunne kinyi matukar kyau matata ked'in ta dabance my love kin hadu sosai, na godewa Allah da ya bani ke a matsayin mata, my love. Ubangijin ya wanzar da zaman lafiya a tsakanin mu mata ta.
Duk jikin ta ya yi sanyi tabbas tayi sa,ar miji, ga kuma wata nutsuwa data shiga jikin ta lokacin ɗaya.
Hatta Farouk sakin baki ya yi yana kallan su, inda kasan wasu masoyan da suke farincikin mallakar junan su. Kai Alhmdllh ko yan zu nasan yar uwar zata samu farincikin a wajen jalil.
Tom a dago haka masoya. Cewar Tahir da Hafsah.
An sha pics cikin burgewa da nuna kaunar juna Alhmdllh inda su Hafsah da su Khadijah da sauran 'yan matan wajen suke ta nuna wa Jamal sosai yana basarwa.
*Kano*
Yau she ne ranar karin haihuwa Jawad sanda shi kan shi ya sha,afa da ranar sai da safe ne yaga MTN sun turah masa sakon sannan ya ankarah, amma shi a nashi lissafin wannan bata zama wata muhimmiyar rana a gare shi ba, dan Rayuwarsa ce ke tafiya. Dan Allah ya kirah mai gadin Company yace zai turah masa da kudi dan Allah ayi abinci a raba sadaka.
Ubangijin ya k'arah masa shekaru masu albarka, amma ba tare da ya faɗa masa manufar hakan ba
Ya kashe wayar ya cigaba da harkokin gaban shi.
Jalilah ce ta shigo dakin fuska dauke da farinciki tace yaya Jawad murnar karin shekara, kallan ta ya yi fuska ɗauke da murmushi yace au murna ki kemun.
Itama murmushi tayi ta ce wish you rayuwa mai albarka and mace ta gari da 'ya'ya masu albarka .
Dan jan kuma tun ta ya yi sannan ya ce ngd my dear sister. Tare da ke my dear ya bani mace ta gari mai kamar ki da kyawun zuciya irin ta ki. Axuciyar sa yace ba irin ta mugun mahaifinki ba.
*Kaduna*
An shirya komi Alhmdllh kuma a yau ne Amarya zata tafi dakin mijin ta.
Kuma Alhmdllh Amarya a yanzu hankalin ta ya kwanta dan yadda Jalil ke nuna mata kulawa Alhmdllh.
Mom ce ta kirah jalil da Jamal ga Fatima ta ce, jalil ina k'arah godiya gareka da karamcin da kamun jalil Ubangijin ya saka maka da mafificin Alkairi. Sai dai ina san amarya ta tare yau a gidan ta da izinin Allah, idan kana ganin babu wata matsala? "Mom gaskiya akwai matsala gidan da muke ginawa nida Jamal bamu kammalah shi ba amma idan ba damuwa akwai na kusa da shi da aka gama zan kama hanyar shi sai mu zauna kafin na kammala nawa in sha Allah".
"Tom ma sha Allah Ubangijin ya sanya alkairi da albarka a auran ku my son. Ina da gida amma na fiso ta kasan ce a naka saboda, hakan shine zata k'arah sanin darajar ka". Fatima kiyiwa mijinki biyayya dan Allah kinga dai halaccin da ya yi mana.
Jamal ya dago da kanshi ya ce dan Allah mom mubar wannan maganar komi ya wuce fa banda tada zance.
Haka kuwa akayi wa a ranar aka kai kayan Fatima. Da dare kuma aka kai Amarya dakin ta. Cikin saka albarka iyaye da 'yan uwan ta. Tayi kuka harta barwa Allah.
Shima b'an garen jalil ya sha addu'a da saka albarka iyaye.
Sannan kuma su Jamal da abokan su suka fito raka shi gidan shi. Har sun fito Jamal ya koma ya dauko wata k'aramar jaka yasa a bayan mutar suka tafi.
Bakin gidan sukayi parking ko da suka shi gidan shiru da alamar ba kowa a cikin gidan sai amarya.
Madaidaicin falo ne mai dakuna biyu a cikin shi sai kicin. Ko wanne d'aki da ban d'akin cikin shi, gidan ne madaidaici kuma mai madaidaicin kyau amma ya tsaru.
Sukuwa zama sukayi kan wasu kyawawan kujeru wanda kana ganin su kasan da kudi aka siye su.
Jamal ne ya tabo jalil ya ce tashi kaje ka kira Amaryar mana dare fa yanayi karka manta ba kwana zamuyi ba.
D'akin da ke gaban shiya shiga wanda yana saran ganinta aciki, Amma bai same ta ba, sai kuwa tsayawa ya yi yana kallon wani k'ayataccen bedroom mai matukar kyau ga wani kan shi mai daɗi da yake ratsa shi.
Fitowa ya yi sannan ya shiga daya dakin bakin shi dauke da Sallah. Ta amsa mashi a nutse gyefenta ya zauna sannan yace ki taso ana jiran mu a falo ta tashi ya rike hannunta cikin salon soyayya yana faɗa mata magan ganu masu dad'i har suka k'arasa falon fuskarta a k'asa sannan kuma a rufe.
Nasiha da addu'oi suka masu sannan suka masu sallah ma tare da aje masu manyan ledoji wanda ko biyar dinsa babu acikin wannan kayan.
Ya raka su bakin kofar gida Jamal ya jawo ɗan uwan na shi ya shiga yi masa nasiha da rikon amanar da aka bashi ya gamsu sosai sannan ya rungume shi hawaye na bin idon shi dan wannan ita ce ranar ta farko da zasu taɓa kwana ba tare ba, wannan shine lokacin na ɗaya.
Shima rungume shi ya yi zuciyar shi tayi rauni yace kaje yanzu kaga suna jarah na. Kai ma kuma jiran ka tare kabarta ita kad'ai.
Sallah ya yi musu sannan ya wuce gidan cike da kewar d'an uwa shi.
Kayan ya shigar mata dasu, basu wani b'ata lokacin ba suka Farah ci komi shike bata tare da faɗa mata dad'ad'an malamai har suka kammala. Sannan suka yi alwala sukayi sallah . Nan ya shiga tambayar ta abinda ya shafi addini tana bashi amsa yaji dad'in yadda ya sameta da ilimin.
Sannan ya shiga hira da ita, tana kwance a jikin shi, ta kanyi murmushi idan ya faɗi wani abu, da ya fahimci tana tsoran shi yace kije ki kwanta sai da safe. Ta meke zata kwanta yace ki ragye kayan jikin ki dan Allah, Sai dasafe ya fice, ta sauke ajiyar zuciya.
Typing 📲
GAYYA CE!
*Free page*
*Written by*
*Fatima alaramma lafazi*
*(Falaramma)*
https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ
*Sadaukar kar wane ga Sadiq Abubakar CEO din lafazi Allah ya Kara masa lpy, da nisan kwana mai albarka, godiya ta musamman*
💖✨✨✨💞💋💋
Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan.
✨✨✨
Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya littafin, ina alfahari da ku ges nagode.
PG 1️⃣7️⃣& 1️⃣8️⃣
Ranar Jamal kasa barci ya yi gaba ɗaya ya rasa mai ke damun shi. Yau hatta jamla ta sa ya kasa waya da ita. Ga kuma barci daya kaura ce wa idon shi, dan haka kawai ya yi alwala ya tada sallah yana yiwa ɗan uwan na shi fatan kasan ce cikin farinciki, sbd a zahiri gaskiya yana matuƙar kaunar ɗan uwan sa, sbd yadda yake mashi biyayya koda kuwa baya so.
Washe gari
Ko da asuba da Fatima ta tashi bata ga jalil ba, hakan kuma bai bata mamaki ba, sbd tunda sukayi sallah ma bata karajin motsin shi ba.
Da asuba ne data tashi taji mutsin shi da alama masallaci yaje.
Amarya da sassafe ta tashi tayi wanka ta shirya cikin wata shaddar wadda tasha aiki, ba karamin kyau tayi ba. Duk da dama Fatima kyakkyawa ce bata da makusa.
Koda ta fito falo bata gan shi ba dan haka ta shige cikin.
Dubawa ta fara yi a nutse ta samu kayan da take buƙata, nan take ta daura musu tea da dankali. Ba wani lkcn ta bata ba ta kammala, ta koma kan gidan ta gyerah shi tsaf sannan ta shiga dakin da yake dan har lokacin ba mutsin shi. Kwance ta tarar da shi yanata barci cikin nutsuwa, a hankali ta k'arasa bakin gadon ta zauna tana kare masa kallo, duk da jikin shi a rufe yake fuskar shi ce kawai a buɗe. Ta jima tana kallan shi daga bisani ta mike ta fita daga d'akin.
D'akin ta takoma ta sake wani wankan sannan ta kuma shirya wa cikin wani tsadadden Les blue tayi daurin ture kaga tsiya inda ta saki gashin ta tabaya ta feshe jikin ta da turaruka masu dad'i sannan ta fito falon da sauri sbd mutsin da take jiyo wa.
Tana fito wa idan su ya sauka a kan juna.
Suka sakarwa juna murmushi a tare.
Ta kowa ya shiga yi har ya kara so inda take fuskar shi dauke da murmushi yace morning my beautiful wife. Kasa tayi da kanta sbd irin kallon da yake mata.
"Cikin sarke war murya ta ce morning too my dear husband.
Hannun ta ya ka ma suka kara so falon kan kujera ya zaunar da ita sannan ya ce. My Teema ta dago ta kalle shi ya ce. Daga yau bana san irin wannan gaisuwar kinji ta daga masa kai alamar eh ya ce yawwa.
Yau she ki ka tashi ki kayi aiki da yawa haka mai makon ki jira na tayaki.
Kai haba yaya Jalil ai aikin ba shi da yawwa, kuma yau she zan barka da aiki ma.
Kalla ta yake sannan ya ce mema naji kin kirani da shi.
"Ta ce yaya Jalil fa na ce ta faɗa a shakwabe tare da turu baki.
Murmushi ya yi mata Sannan yace bana san wannan sunan fa.
"Ta kuma toru baki, ta ce to yaya Jalil bata karasa ba ya haɗe bakin shi da nata yana masa Mani irin tsotsa.
Gaba daya jikin ta rawa yake ga kuma wani hawaye da yake biyo idon ta. Jikin ta ya yi wani mugun san yi.
A hankali ya fara sakin bakin nata, ya saka hannu ya dago da kanka yace daga yau idan ki ka kuma fadar haka hum, yan zu tashi muje kimin wanka sai muyi breakfast.
Bai jira abin da zata ce ba yaja hanun ta suka shiga d'aki.
Kai tsaye Toilet ta shiga ta haɗa masa ruwa Sannan ta fito kai a ƙasa ta ce na gama, kallan ta ya yi yace eh amma saura wanka.
Ta ce dan Allah kayi da kan ka kaji, rabuwa ya yi da ita ya shiga wanka sbd ya fahimci a tsora ce take da shi.
Jakar da ta gani a ajiye ta dauko, ta shiga bude ta, wata shadda ta dauko masa white color. Ragowar kayan ta shiga jera mashi a cikin wadirop din dakin sannan ta fito sbd jin a lamun fito warsa.
Fatima yarin ya ce karama wadda ba zata wuce 21 yaes ba. Yarin ya ce mai ilimi Addini da na boko. Yarin ya ce nutsatsiya mai ciki da kuruci da shagwab'a sakamakon ita ce auta a wajen mom dinta.
Shirya wa ya yi cikin kayan da yaga ta aje masa sannan ya fito zuwa falon ya ganta a zau ne da alama tuna ni ya keyi dan ya fahimci bata masan yazo wajen ya zau na ba.
Hannun shi ya daura kan fuskar ta, ya ce my dear tuna nin mai ki keyi. Bai k'arasa magana ba yaga hawaye na zuba daga idon ta, ta faɗa kirjin shi ta fashe da kuka.
Cikin tausayi da girmama wa yake shafa bayan ta ya farah magana a hankali ya ce dan Allah my dear ki faɗan mai nayi miki har na saki kuka haka ko kina so na kasa yafewa kai na ne.
Cikin hanzari ta dago da kanta daga jikin shi tace my husband baka mun komi ba, asalima jin dadi kasan ce wa da kai ne ya sani hakan.
"Kai din ka kasan ce haske ne a gare ni".
kuma abun alfaharin na. kai ɗin muradin ko wacce uwa ne. Kuma alfaharin co wacce 'ya, ina sanka miji na ina kuma alfahari da samunka a matsayin miji na. Ubangijin ya bani ikon yimaka biyayya.
Sosai shima ya rungume ta ya ce kema haka my dear. Ubangijin ya sanya alkairi da albarka a auran mu ya bamu zuri,a d'ayya ba.
Amma fa ki sani ni 'yan uku nake so.
Dariya tayi ta ce kai my husband, ai nayi yarin ya bazan iyya haihuwa yan zu ba, kuma ciki na bazai iyya daukan uku ba fa, ta ƙare maganar cikin wata irin murya.
"Au haka ma zaki ce my dear tom Allah ya kai mu anjima zamu gani.
Ya kare maganar yana mata dariya sbd ganin yadda ta hade fuska.
Ta shi tayi ta kawo musu breakfast, wanda gaba ɗaya sun ma man ce suna jin yinwa, suka Farah ci yana bata a baki shima yana ci, Ya nata mata santi sannan suka kammalah ta kwace kayan ta kai kichin, ya taya ta da wasu.
Tare suka gama wanke kayan, cikin farinciki da jin daɗi.
Falo suka dawo suka zau na, suna hira lokacin har 12:9 tayi, wayar sa ya d'auko ya farah dan na number Jamal, ita kuma Fatima na kwance a kafadar sa.
Bugu ɗaya ya dauka.
Bakin shi ɗauke da Sallah ma yace Ango kasha kamshi.
"Jalil ne ya amsa masa yana dariya ya ce kai Jamal a kwai ka da tsokana.
"Jamal ya ce danaji shiru ai nace ba zaka kirah mu ba.
"Dariya jalil ya yi yace ni a wa zank'i kiran ka.
"Jamal ya ce fatan dai baka wahalar mun da k'anwar ba ko?
"Dariya jalil ya yi yace ummm.
Da ta fahimci hirar ta su sai ta mike ta shiga d'aki.
"Jalil ya ce kadai san ni da tausayi.
"Jamal ne ya kwashe da dariya yace a ina, idan kuma haka ne to ka barta tayi one week mana.
"Jalil cab ai wllh jiyan ma nayi kokari, dan daga kyau na gama hakuri.
"Kai mugu, wllh ka bi mana k'anwa a hankali ta,
" Kai dai kawai sai abun da kuka ji.
Da haka dai suka yi ta hira suka canza akalar maganar zuwa wata hirar.
Sannan sukayi sallah ma.
Haka suka wani suna hira basuyi wasu baki ba, karfe 2:00 mom ta aiko direver ta ya kawo masu abinci. Suka kirata suka mata godiya ta tambayi Fatima tace Alhmdllh sai godiyar Allah.
Da yamma karfe hudu ya ƙarah shirya wa sannan ya yi mata sallah ma ya fita, har bakin kofar ta rakoshi tana ta mashi addu'a, da fatan alkairi tana a gaida inna da jawahir kuma yan she zasu zo.
*KANO*
Haka ita ma Ammy ba,a barta a baya ba wajen yiwa ɗan nata sada,ka da addu'a fatan alheri da samun mace ta gari kamar yadda suke fata.
Yan zuma zau ne ya ke kusa da ita yana mata Magana cikin nutsuwa, tana bashi amsa.
"Ammy Jawad kasan wani mafarki da nayi jiya.
" A'a Ammy ban sani ba sai kin faɗa"
Wallahi nayi mafarki kayi aure har an kai maka matar kuma kuna cikin farinciki.
"Murmushi Jawad ya yi mata".
"Ammy kawai sbd kina muradin hakan ne yasa amma, ai in sha Allah zanyi noma kamar yadda ki ke fata."
Allah yasa amma gaskiya jiya na kasance cikin farin ciki mara misaltuwa bana jin ko wacce irin damuwa a tattare da ni".
"Alhmdllh Ammy Allah yasa Alkairai".
"Ta ce Ameen".
Jalila ce tayi sallah ma ta shigo d'akin gyefen Jawad ta zauna.
"yaya ina wuni"
"Lpy lau Alhmdllh my dear sister"
Amma dama tuni sun gaisa tun dazu, sbd dazun ta shigo baya nan.
Jalilah dazu Tahir yazo abokin Jawad yake faɗan wata magana, wato Jalila ke da yayin ki bazaku yiwa kan ku faɗa ba kuyi aure, aure fa shine mutum cin mutum. Ta kare magana ran ta a ɗan b'ace.
"Ammy ni nafi so idan yaya Jawad ya yi ni ma sai nayi tunda kin ga shi ne babban, kuma ni har yanzu ban samu wanda ya yi min ba.
"Ammy ai ke da yayan ki ba zaku taba samun wanda ya yi maku ba".
" Wallahi zan haɗa ku da Papan ku, nagaji da rashin jikoki a gaba na.
*Kaduna*
Yau ta kama ranar Monday kwana ɗaya da dawowar su Dad da mom din jamlah, daga Lagos, sbd a can take komi na cikin jikin ta wanda a yan zu ya fito sosai. Dar baya barin ta yin komi inda kuma jamlah ma bata bari sosai take farincikin da cikin, ga kuma wani kaunarsa da take ji.
Ita kuwa mom sosai take jin kunyar cikin a cewar ta wai tayi girma da haihuwa wanda ba ko wane ma yasa akwai cikin ba, sai shakikan kannan ta da yayyen ta sai kawar ta.
Dad ne ya shiga falon ya samu su Jamal a zaune tana dan na wa mom ƙafa, suna tabba hira kadan kadan.
Dad mom jamal kin san wani abu mamaki ashe yaran nan ya yi aure, wa kenan? Mom ta tambaya, jamal mana, "a'a Dad jalil ne fa" jamla ta bashi amsa.
"Kai masha Allah gaskiya nayi farincikin da wannan maganar, Ubangijin ya sanya alkairi da albarka.
"Mom wadda ya aura ma Fatima Abubakar ce fa yar makarantar mu, na ce zanje ma gidan nata nan da kwana biyu in sha Allah nida jawahir kan warsa.
" Ma sha Allah kinga kuwa sai ki wakilce ni, sbd ni yanzu ba wani san fitar nake ba. Gashi jiki na ya yi mun nauyi.
Haka dai sukayi ta hirar auran nasu in da mom keta yabo ta na ta samu miji na gari.
Mom dama nima yau nace zan je gidan su Jamal na gaida inna, kin ga baki daya banje ba daga nan sai na masu Allah ya sanya alkairi kafin lokacin, zuwa gidan yaya Jalil din.
"Tom shikenn, Allah ya kai mu anjimar sai ki kira Jamal ya kai ki.
"Dad ya ce wllh yaran nan akwai kirki ki duba ki gani yanzu ko kuɗin na ma sun dena karba. Haka suke ce wa sun samu aiki Alhmdllh."
Ta shi tayi ta koma d'aki ta barsu a falon suna hira.
Yaya Jamal kazo nan da minti 30 na gama shirya wa, Tom shikenn yau Madam zata je gaida sutukarta, "kai yaya Jamal ni fa ba surukata ba ce wllh, kuma idan ka takura sai na fasa zuwa eheeeee", ta kashe Maganar cike da shagwab'a, shi kuma yasa dariya, haka dai suka yi ta hira cike da farincikin, daga karshe ya mata sallah ma.
Misali karfe4:39 dai dai Jamal ya zu ya dauke ta.
Sanye take da Les blue color tayi matukar kyau, ta ɗora mayafin a kan ta. Sai wani sihirtaccen kamshi da yake fita a jikin ta, shi kan shi tunda ta shigo motar yake binta da kallo sbd tayi masifar kyau.
"D'ago da kan shi ya yi ya ce wow beby kinga yadda ki ka hadu kuwa kamar ba ke ba.
"Ta yi masa murmushi "
Tafi ya suke ba wanda yake ce wa kowa komi har suka k'araso bakin k'ofar gidan ya hango motar jalil yace kinga jalil ma yana nan, tayi murmushi kawai ba tare da tace komi ba.
Gaba ɗaya jikin ta rawa yake yi ta rasa dalilin jin faduwar gaban ta, wanda bata san dalilin hakan ba.
Tun daga nesa take jiyo Muryar yar idan anata hira, nan ma gaban ta ya ƙarah bugawa.
Da Sallah ma suka shigo dakin idan kowa ya dawo kan su kafin su Amsa masu sallah mar. Inna ce ta mike tsaye jiki na rawa ya yin da ita jamla ta tsaya cak sbd tsabar mamaki da al,ajabin abun ashe da gaske ne akwai wata mai irin ta sak haka.
Jawahir gaba ɗaya ita ma jikin ta ya yi sanyi ta kara so wajen ta, ta rungume ta, ta rasa dalilin ita kawai taji soyayyar jamla a zuciyar ta, haka inna ma ta taso ta rike ta.
Suka zauna da ita a tsakiyar su.
"Ya sunan ki, a hankali suke tambayar" ta, jalil da ke gyefen ya ce inna ita ce fa jamla, yar gidan Alhaji.
"Kai ma sha Allah.
"Jamal cikin sanyi jiki ta zame kasa ta zauna tace inna ina wuni", lpy lau Alhmdllh yar albarka",
"Anty jawahir ina wuni, tace lpy lau Alhmdllh Anty Jamal ai kece Anty tamu"
Nan ta shiga gaida su jalil cikin nutsuwa suna amsawa, har lokacin basu dena kallon ta ba, babu wani banbanci tsakanin ta da jawahir. Ita kuwa inna gaba ɗaya jikin ta ya yi sanyi, ga kuma wasu abubuwa da suke bijiromata a zuciyar ta. Inna ta meke tsaye bayan ta gama tambayar ta mutan gidan ta shiga d'aki ta barta sbd take sake wa.
Jalil ne ya dago da kan sa yace, jamla yau she zaki je gida na ne ke da Jamal, tayi murmushi ta ce in sha Allah zamu zo nida Aunty jawahir.
Nan dai sukai ta hira sama sama inda aka kawo mata abun tabawa suka fita suka bata waje ita da jawahir dan tafi dake wa tana ci tana mata hira ba wani ci tayiba, ta ce ta koshi.
Nan suka cigaba da hirar su, sosai sun saki jiki da juna inda har suka yi change contact, sosai suke jin kaunar junan su, sannan suka yanke ranar zuwa gidan jalil.
Inna kwan ce take a kan gadon ta inda jikin ta duk ya yi sanyi, duk ta rasa abun da yake damun ta ga wani ciwan kai da ya saukar mata lokaci ɗaya.
Koda su Jamal suka dawo suka same su sunata jira, abun su, gwanin sha,awa.
"Jamal ya ce ina inna"
" suka ce tana barci".
Fita suka kuma yi sukayi sallah magriba Sannan suka dawo gidan. Time din duka suna falo har inna, suna ɗan taɓa hira kaɗan-kad'an ita da Jamala.
Baba ma da ya shigo d'akin yan zu suka gaida shi, sannan ya zauna yana tambayar jalil wannan Amarya ce.
"Jalil ya ce a'a wannan jamla ce yar dad"
"Ya ma sha Allah ya manyan naki"
Ta dago da kanta a bisa rashin sani suka haɗa ido da Babba!!.
Typing 📲
GAYYA CE!
*Free page*
*Written by*
*Fatima alaramma lafazi*
*(Falaramma)*
https://youtube.com/@fatimaalaramma?si=v_EK6JyH_nkqroPZ
*Sadaukar kar wane ga Sadiq Abubakar CEO din lafazi Allah ya Kara masa lpy, da nisan kwana mai albarka, godiya ta musamman*
💖✨✨✨💞💋💋
Wanan sabon littafi ne, dana farashi kwanan, ina rokon Ubangiji ya bani ikon gamawa lpy, ina rukun Ubangiji ya bani da mar rubuta abun da mutane zasu amfana dashi wannan kenan.
✨✨✨
Wannan labarin na musamman ne ba gama garin labari bane, GAYYA CE! kuna ji kun San abun sai Wanda ya karan ta, labarin ban dariya da kuma soyayya, tsan tsar cin amana da kuma Butulci, San zuciya da kuma hassada, duk acikin book din GAYYA CE! kunaji kun San ba karya littafin, ina alfahari da ku ges nagode.
PG 1️⃣9️⃣ & 2️⃣0️⃣
...........Bakin Babba har rawa ya ke yi ya bude bakin sa yace jawahir wacce wannan mai kama da ke haka.
"Babba wannan fa sunan ta