muka zauna,tana magana tana kallon a tayi murmushi, tace (ko ba haka ba yar uwa), gaskiya tana da barkwance da son mutane...,bayan an tashi breakfast kowa ya fita daga ni sai ita.
Fatima amma kina kama da yan zuru?, Murmushi nayi"yan zuru har kama ne dasu?"na bata amsa.
Sosai ma,natsuwar ki,da kamun kai ya bambanta da sauran course mate naki,Kinga Nima Yar zuru ce karatu ya kai Ni sokoto Wanda na mallaki gidan kai na a nan saboda yadda nake juya maza kuma basu isa ko hannu na su rike ba!
Jin haka kuwa yasa na sake na bude wa philo ciki na tun daga haɗuwa ta da doctor,soyayar mu ,wulakanci da ya mun a Sokoto har rabuwar mu da matsalar da na fuskanta a gida.
Dariya tayi sosai kamar zata kware!
Haushi da baƙin ciki ya cika sani domin na tsani dariya,kamar ta raina mun hankali ne bayan ta gama jin sirri na.
Kada ki damu Fatima, doctor zai zo hannu,zan baki wasu trick da zaki yi amfani dasu wallahi DOCTOR will definitely come back to u by all means!!
Babu namiji da zai sake wulakanta ki a rayuwa,itama mummyn taki da yar uwar taki sai sun dawo karkashin ki sai yadda kika juya su!!!
Jin haka na gyara zama domin na kagu banji ko menene ba,tell me Philo zan iya yin komi domin ganin na mallaki DOCTOR Kuma I'm DAWO da martaba ta a idon duniya!!
*🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*CORPER*
_{Ɗan bautar mata}_
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_~A Romantic Love Story~_
*BY*
*L££MA*
*DEDICATED TO MEELAT AND HUBBEEY*
*All right reserved unauthorized copying, changing and translation of any part of this story in any form is prohibited.*
*_Alhamdulillah bayan dogon hutu dana ɗauka Allah ya dawo dani lafiya,ina yiwa duka nin al'ummar musulmi Barka da sallah Allah ya maimaita mana Amin fatan alheri zuwa ga yan uwa da abokan arziki._*
*🅿13*
Kada ki damu Fatima zan baki wasu tricks da zasu taimaka maki wurin mallakar DOCTOR Kuma ya dawo da martaba da darajar ki a idon duniya.
Faɗa mun koma menene zan iya yi Philo idan har doctor zai dawo gare Ni!
Murmushi tayi,ai ba wani abu mai wahala bane fati kuɗi zaki tara cuz a duniya yanzu idan baki da kuɗi ke ba kowa bace,idan baki da kuɗi ba zaki taɓa yin daraja a gidan ku ma duba da labarin da kika bani ,a farko mummy taga doctor Yana da kuɗi idan kika aure shi zata huta sai gashi all of a sudden an neme shi an rasa,within short period of a time younger sister naki ta samo wanda yafi DOCTOR kuɗi wanan dalili yasa aka juya maki baya har aka haɗa ki faɗa da yar uwarki....
Ta wane hanya zan samu kuɗi?,"na katse ta.
Common Fatima kina magana kamar wacce bata taɓa shiga class ba,KE mace ce mai kyau da tsari,yi amfani da baiwar da Allah ya maki Mana tun kina da dama kafin ta wuce!
Bata rai nayi,kina nufin inyi karuwan ci kenan ko?,wallahi ko zinace zinacen da nayi da doctor soyayya ce ta rufe mun ido yanzu kuma na gane gaskiya...
Ni,ba haka ba ai na faɗa maki Ina da gida nawa na kai na a Sokoto kuma bata hanyar karuwan ci na samu ba,duk da dai na haɗa da tsafi ina zuwa rafin girmace(sha da wanka) duk karshen shekara in Yi offering sacrifice domin samun ɗaukaka da farin jini a harka ta,amma nasan ke ba zaki yadda da haka ba saboda addinin ku despite musulmi da yawa suna zuwa neman biyan buƙata kuma ana dace wa daga baya su tuba.
Dakata philo,ba zan iya aikata shirka ba saboda son abun duniya!
Ok let's make it this way,zan tafi on your behalf Kuma za'a dace doctor zai dawo gare ki ,amma fa idan baki amince ba babu dole cuz I was only trying to help u Fatima.
Shiru nayi Farida ina tunanin irin dimbin zunubi da zan kwasa,gashi bana son rasa doctor a karo na biyu!
Na amince Philo amma fa bani da kuɗi a hannu na.
Don't worry I will do anything for friendship seek.
KE dai farida muka ya exchanging contact da philo kafin sauran mu su dawo breakfast.
Tun daga ranar kullum idan nazo bayan mun gama ma yara lesson muke kebe wa da philo(NOKIA connecting people),tana bani shawarwari yadda zan gyara jiki na a saukake wani lokaci har mamaki nake yi tana Christian ya akayi ta san kayan gyaran jiki irin namu na Hausa/fulani!
Babban abun mamaki da motoci kala kala ake kawo philo duk da ba yar birnin Kebbi bace daga Sokoto ta zo teaching practice Nan,Amma yau wanan alhajin ya kawo ta,idan an tashi wani zai zo daukar ta kuma duk suka zo sai ta kira Ni a waya in fito mu gaisa saboda bata zuwa da wuri,wani lokaci idan suka kawo mata breakfast nice Yar rakiya"tana INTRODUCING dina as her best friend" .
Ashe hakan dake faruwa yana matukar bata wa Habibah rai,ranar ta same Ni da surutai;,ban da hankali in rasa wacce zan kulla abota da ita sai Christian,wacce babu wanda bai san halin ta ba karuwa ce kuma kanwanu wa ce(tana haɗa maza da mata a biya ta) dalilin sunan NOKIA connecting people kenan.
Zagewa nayi na ci mutuncin HABIBAH domin ita da mummy suka kai Ni ga halaka har na faɗa tarkon doctor said yanzu zata nemi gaya mun magana.
Bayan kwana biyu philo ta tafi zuru domin aiwatar da aiki na sai data ɗauki kwana ki uku cur ana tsafi da zub da jini kafin aiki yaa kamala, wanda sai da ta zuba kuɗi sosai bokan ya amince ,a cewar shi sai nazo da kai na aikin zai fi lasting a jikina,Wanan da akayi na ɗan lokaci ne zai iya lalace wa ko wane lokaci.
Rokon shi ta shiga yi har ya amince zai masu aiki mai inganci.
Watau farida na yadda Allah ya ara ma ɗan adam dama a duniya kuma ya zuba maka idanun kayi iskancin ka son ranka wanda hakan ne ya faru.
Farida wani irin farin jini Allah ya dauro mun banda halin fita koda cikin area mune samari da manyan mutane kamar su sace Ni su gudu,kowa dai Ni yake so!
Kuma kada kice irin area boys d'in Nan mara sa aikin yi ko student",graduate masu ji da kuɗi da muka mi,ga irin sugar daddyn Nan masu faɗa aji a gwamnati.
Ban boye wa philo komi ba ,ta nuna aikin da akayi ne yayi tasiri sharadi aiki dama Banda ɗaukar ciki,kuma hanya ɗaya ne zan bi da ba zan ɗauki ciki ba shine rashin amincewa da ko wane ɗa namiji muyi sex.
Zama muka yi ta bani shawarwari kamar haka:-
Duk wanda yace yana son ki Fatima kada ki kuskura ki wulakanta shi,dole ki amince ki saki ranki kuyi soyayya koda bakya son shi,ta haka ne kawai zaki amshi abun hanun shi cikin sauki.
On no condition zaki yadda sex ya shiga tsakanin ki da wani!
Cike da mamaki na kalle ta,"ta yaya namiji zai rinƙa bani kuɗi ba tare da na mashi komi ba NOKIA?
Farida kada mu bata lokaci dare yayi sosai bana so gari ya waye ban gama baki labari ba,duk abubuwan dana koya maki Philo ta koya mun yadda zan ci kuɗin namiji a saukaka tun ina jin tsoro har na zage cikin sati biyu na fita iyawa.
Babu irin nasiha da Habibah bata mun ba nayi biris da ita sai facaka nake da kuɗi,kafin ka sani na saya abubuwa da dama na more rayuwa ina shanawa.
A lokacin iPhone 7+ ya fito sabo wani CORPER ɗan majalisa ya saya mun.
Kin ga duk karshen wata inada salary wuri uku zan rinƙa amsan Wanda wasu daga cikin masu sona suka bani offer na aiki amma ban taɓa zuwa ba kuma gida babu wanda ya sani,lokacin ne philo ta bani shawara muka tafi Sokoto shagon mutumin nan na saka set na zinari ɗaya a lokacin da zobe guda biyu extra sai wasu kayan kyale kyale namu na mata.
A gida kuma sosai mummy taga canji cuz bana cin abinci gida order ake mun daga restaurant ana kawo wa,ga kuɗi banda matsalar shi,na canza tofafi na masu tsada,sai dai taga muna facakan mu dasu Anisa ban taɓa mata tayin komi ba.
Wanda nasan hakan na bata mata rai kasancewar ta mace mai shegen kwadayi,sai ta fara shishige mun,tana shiga lamurran na ko a jiki na!
Ga farin jini dai Allah ya Daura mun babu ranar da zan fita ban haɗu da masu sona ba,haka babu ranar da za'a wayi gari ban rabu da wasu ba cuz da zaran na amshi abun hanun ka yadda nake so naga zaka takurawa rayuwata da neman biyan buƙatar kananan yanka maka red card saboda waya uku ke hannu na akwai karama mai 3 sim idan ka dame Ni zan saka ka a Black list,ko in canza layi wanda ban ɗauke shi a bakin komi ba.
Amma Fatima ta yaya kike hira dasu duka a kullum nasan dole wani na iya zuwa ya same ki da wani"farida ta tambaye ta".
Ahhhh,wanan ba matsala bane kin san Allah babu wanda ya san gidan mu a cikin su,duk wanda muka haɗu zan ce masa ba'a bari na hira idan zai iya zan rinƙa ware nashi ranar da zamu rinƙa haduwa a wani wurin irin park ko restaurant muna hira once in a while haka.
Uhmmmm lallai fatima ashe kin yi bura'uba!
Sosai farida ai yanzu komi ya ƙare ma sai yan kame kame tunda kika ga ina haɗa wa da facebook ai kema kin san babu harka.
Ke dai byan wata ɗaya da yin aiki wata ranar weekend Ina Shan bacci na kasancewa yanzu aikin uwar komi bana yi a gida daga tashi zan haɗa ruwan wanka in Yi,in zaɓi abinda nake son CI a dafa mun inyi fice wa ta gidan kawaye na sai lokacin da naga daman dawo wa saboda tun ranar dana ci ma mummy mutunci ta kama kanta dani bata shiga tsabgata,daddy Kuma baya zama bare yasan abinda ke faruwa a gidan.
Wayata ta isheni da ruri wanda dole na tashi daga bacci na mai daɗi ,ganin new number yasa na ja WATA doguwar tsaki naci gaba da bacci,ai kuwa mai kira bai fasa ba kashe wayar nayi gaba ɗaya.
Bayan wani lokaci na tashi nayi wanka na yi breakfast kafin na buɗe wayar,missed calls sun Kai goma ,ga texties kamar haka;-
_There are no words to explain how sorry i am for doubting you.it is just impossible for me to believe that such an amazing,sexy lady could ever be interested in me.plz find a space in your wonderful heart to forgive!!!_
Tsaki naja domin new number ne ban san mai ita ba,sauran na shiga buɗe wa...
_Saying sorry is the purest cure of all heart aches and heart breaks! Admit to yourself that you have done wrong and say sorry. It does not only touches the heart but also touches the soul. It's the greatest thing to do that will give you the greatest feeling to enjoy_
_You are the kindest person I have met baby teemo.Forgive this fool(nadeema) who can’t live without you._
Zaro idanu nayi,wani nadeem ɗin???
"Babu shiri na kira Philo a waya"....
Hello teema how far?
Not too far NOKIA, guess what?
Doctor ya Kira ko?
Kin cinka dai dai wallahi da new number ya Kira ni,ga wasu texties na ban hakuri.
Kada kiyi saurin bada kai yanzu ne lokacin da zaki kwaci yan cin kanki wanda baki samu ba a baya,idan ya matsa da waya kice yazo yaga iyayen ki idan sun yi hakuri shike nan.
Anya zan iya kowa philo?
Zaki iya mana ta haka ne kawai mummy zata ci gaba da ganin mutuncin ki.
Zan yi kokari philo na gode sosai Allah ya bar mu a tare.
Yinin ranar waya kan waya amma ko ɗaya ban daga ba farida har dare da naga ma zai takura mun na rufe wayar gaba ɗaya na koma palour wurin su anisa muka sha kallon mu zuciyata tas.
Washe gari Monday tun da wuri na shirya da yake driver daddy KE aje Ni makarantar ya wuce dasu Anisa School,cikin kwalliya sosai na fito saboda ina cikin farin ciki har mummy taga canji har d'aki na same ta muka gaisa sosai cikin wasa da dariya nayi mata sallama wanda rabon da muyi haka tun kafun auren faiza.
Ina fitowa wa zan gani wajen gate???
Doctor Nadeem sanye cikin logslik silver colour da Black trouser ya Kara kyau da kwarjini kamar ba shi ba,idanun shi fes cikin nawa ...,nan take wani irin son shi ya taso mun naji kamar in rungume shi amma wani zuciya ya hana shi kawai na nufi motar mu.
A gurguje ya riƙe hanuna,haba baby ki zama mai yafiya mana,nasan nayi kuskure believe me WALLAHI ina son ki am ready to make u my wife Fatima!
Tsaki na ja tare da fizge hanunna kawai na shige mota already su Anisa na cikin motar muka tafi,ashe ya biyo bayan mu....
Su Anisa sai tambaya na suke ba shine doctor Nan da yake zuwa gida ba?,nayi banza dasu duk da har cikin zuciyata naji daɗi yace zai aure ni.
Suna aje Ni ya sha gaba na da motar,idan na juya nan ya sake bina da mota muna cikin haka sai ga wata range Rover sport fara sol ta sauke philo muka gaisa dasu take tambaya Wane ne wanan kuma?
"Ban san shi ba",shine amsa dana bata zan wuce ya fito daga cikin motar ya riƙe hanaye na gama!
Wallahi idan baka sake Ni ba sai na wanka maka mari!
Sir please let's go of her hands.
Only if she will listen to me,ya FAƊI Kamar zai kuka.
Nodding Kawai ta sake mun hannu,a guje na shige gate d'in school,Yana ƙoƙarin biyo NI philo ta tare hanya.
Sir kayi hakuri duk da ban san ko kai wanene ba, from all indication ranta a ɓace yake ka same ta a gida anjima ko ka samu iyayen ta kuyi magana.
Ko Nagode my sister ,don Allah ki Kara Bata hakuri ban kyauta mata ba yanzu zan tafi gidan su.
"Okey",ta FAƊI ta shiga daga ciki.
Babban SUPER MARKET ya nufa aka shake Mai leda da kayan ciye ciye zuwa COSMETICS ya nufi gidan mu lokcin daddy ya fita office,mummy ta mai iso palour tare da ba inna hussai dama ta kawo mai kayan motsa baki kafun ta fito.
Tayi mamaki sosai da aka ce wai doctor Nadeem na sallama,cikin kwalliya ta fito nan take ya zube ƙasa suka gaisa komi bai taɓa ba cikin kayan da aka aje mai na ci.
Ya bayan rabo doctor,kwatsam ma samu labari ka koma makaranta?
Eh wallahi MUMMY,Yana sosa keya!
Allah Sarki,ya parents naka da family,nasan dai kayi aure yanzu?
Lafiya klau suke mummy Dama ai Ina da aure yanzu haka yara na biyu,yanzu dai na kamala karatuna har naci gaba da aiki...
All that while kana da aure bamu sani ba?
Eh wallahi MUMMY lokacin kwata kwata ban wuce watanni shida da aure ba shi yasa ba na ɗan jinkirta maganar Fatima amma yanzu na dawo da shirin auren ta.
Ikon Allah,yanzu dai ka bari daddyn ta idan ya dawo sai kuyi magana,amma ka samu ganin ta kuwa?
Eh tau mummy Bata saurare Ni ba ne!
Allah Sarki ka bata lokaci in shaa Allah zamu dai dai ta.
Nagode sosai zan koma bakin aiki na,ga wanan ba yawa ana yara"ya aje ledan da bounch na kuɗi.
Hada dawainiya?, Allah ya saka da alheri .
Amin ya fita, ɗaukar ledan da kuɗi tayi zuwa cikin daki...,lallai fatima ta raina Ni da yawa dama doctor ya dawo gare ta shine bata sanar dani ba,waya san ko don haka nema ta sauya halin ta tunda yanzu da alama idanun ta sun buɗe da kuɗi sai facaka take dasu!
A school kuwa philo take bani shawara idan har ya kai magana gida kada in Bata lokaci kawai in Amince tunda bukata ta biya.
Dana dawo gida a ranar mummy da kanta ta girka mun abinda nafi so(dambun shinkafa) har d'aki na ta kawo mun tana gaishe Ni da gajiyar aiki...
Sama sama na amsa dai na shige wanka sanan na gabatar da sallah haka naci abinci kada tace ban kyauta mata ba.
Bayan na gama ta dawo ɗauke da leda a hanun ta,dama inaso muyi magana kafun daddyn ku ya dawo.
Hankali na kawai na tattara wurin ta"ina saurara mummy".
Doctor Nadeem yazo har GIDAN nan neman auren ki!
Uhmmmm,kawai nace.
Zan so kiyi hakuri tunda ya gane kuskure shi beside ma ai har yanzu masana kina son shi.
Naji mummy Amma Ina so a bani dama zan yi shawara a kai domin Ni yanzu nadeema baya gabana karatu na kawai na saka a gaba.
Riko Ni tayi cikin tsigar rarashi,common teema karatu baya hana aure yanzu Baga yar uwar ki faiza ba suna Laberiya da mijinta a can ya sama mata admission tana karatu hankali kwance,bare ke da semester biyu ya rage maki ki kammala!
Duniya kenan yanzu har faiza ta samu abun alheri a rayuwa ban da labari!,lallai matar nan ta cika babban Ingilishi ya tayi nasarar raba Ni da yar uwata zama ɗaya.
Mummy mu bar shi a haka kawai zan ɗan kwanta...
Shike nan ga kaya daya kawo na ɗauki kuɗin sama ki duba kayan duk da nasaba yanzu kuɗi da kaya ba matsalar ki bane (ta faɗa cikin gatse).
Bana bukatar komi a ciki mummy ki tafi dasu"shine amsa dana bata,na kwanta kawai.
Ba kunya ta kwashe ta fita dasu.
Yinin ranar doctor ya hana Ni sakat da kiraye kirayen waya banda sakon ni na soyayya amma ko ɗaya ban duba ba.
Around 8:30pm abdul ya shigo d'aki na"aunty teema daddy na Kira a palour",Ina zuwa.
Hijab d'in da nayi sallah na saka zuwa palour da sallama na shiga.
Mummy da daddy zaune saman kujera,doctor nadeem na zaune ƙasa carpet.
Sai da naji faduwar gaba ya ziyarce ni,gefe na zauna a ƙasa"gani daddy".
Fatima Dama akwai alaka na soyayya ne tsakanin ki da doctor ban sani ba?
Jin tambayar nayi kamar saukar aradu,tsintar kai na nayi da cewa A'a Daddy,bamu taɓa yin soyayya dashi ba.
Da mamaki kowa ya kalle Ni,wanda Ni kai na a ƙasa yake.
Yanzu dai yazo neman izinin turo magabatan shine su zo neman auren ki kuma ya sanar dani yana da mata ɗaya da yara biyu!
Kuka na fashe dashi wani irin kishin shine ya turmuke zuciyata yadda nake son shi ba zan iya zama dashi da wata mace ba,na gwammace mutuwa ta da auren shi da wata matar,daddy bana son shi ba zan iya auren shi ba.
Mummy ta amshi,saboda me Fatima,wanda yace yana son ka ya gama maka komi a duniya bare mutum kamar doctor ɗan asali ga nagarta(a ganin ta saboda WULAKANCI da ya mun a baya ne).
Shima kuka ya shiga yi da magiya idan ban aure shi ba zai iya rasa ran shi wallahi yana mugun sona,kuma ai matar shi tana Jos nan zai aje ni tare dashi.
Ganin abu yaƙi ci yaƙi cinye wa Daddy ya bashi hakuri bayan kwana biyu ya dawo za'a yi shawara.
Haka dai aka watse taron kowa rai a ɓace.
Ban wani runtsa ba a daren tunani kala kala,ga doctor ya dame Ni waya haka na kashe wayoyi na.
Allah yasan ina son doctor Amma ba zan iya sharing na shi da kowa ba.
An ɗauki wurin sati Ɗaya ana abu ɗaya domin naki amincewa da doctor ga dai zuciyata na matukar son shi bukatar shi amma kishi ya rufe mun idanu,dole daga baya na amince saboda aikin sihiri ne idan banyi amfani da damar dana samu ba komi na iya lalacewa nan gaba.
Ranar dana fara ɗaukar wayar shi mun sha soyayya sosai kamar zai cinye Ni da alƙawarin zai kula dani bayan auren mu.
Tun daga lokacin kullum muna manne dashi a gida ko a waya tana zuwa sosai take romancing ɗina saboda dakikan ci irin nawa na manta da wulakanci da ya mun a baya har na sake sakar mashi jiki a karo na biyu amma bai samu daman yin sex Dani ba,da yayi yunkurin yi sai na tuna da sharadin aikin da akayi in hana ranar haka zamu rabu ranshi a ɓace,bai hana gobe ya sake nema.
Bayan wani lokaci iyayen shi suka zo daga Jos aka nema mashi aure na a zuru can suka tafi dasu daddy Wanda yaso sai na kamala karatu bayan watanni shida amma doctor ya ki amincewa aka saka watanni uku masu zuwa.
Da yake yana mun ruwan kuɗi duk ATM nashi guda uku hanu na suke sai yadda nayi da salary nashi mummy ta fara shishige mun tana so in saka ta a gaba wurin harkar aure na,fafur na share ta sai ta kai ƙara ta wurin kaka na zuru.
Kaca kaca suka mun wanda yasa na yafe ma mummy komi ya wuce amma ba har cikin zuciyata ba.
Babu laifi ta gyara tsakani na da faiza wacce ta kira Ni ta bani hakuri koma ta sanar dani tana da shigar ciki,na taya ta murna.
Shirye shirye ake yi sosai a gidan mu duk abinda nake so na sanar da kadara ta na saya ma kai na a boye muka aje gidan su Habibah saboda mun shirya da ita,ragamar haɗa lefe kuwa doctor ya sakar mun a cewar shi in debi kuɗi son Raina in HAƊA irin kayan da nake so na lefe.
Lokacin ko teaching practice d'in ban damu da zuwa ba a week sau ɗaya nake fita wanda kullum sai na fita gida da sunan zani amma wasu samari na nake gani ina yagar arziki a cewar philo tana so aure na ya kafa Tarihi a garin birnin kebbi har ya wuce na faiza ta haka ne kawai faiza,mummy da sauran yan uwana zamu girmama Ni da mijina.
Wanda a zahiri na fara ganin haka domin yanzu mummy Bata da abokiyar shawara sai Ni haka faiza komi ya same ta tana kira na mu tattauna haɗa matsalolin da take ciki tun farkon aure mijinta ya bar sakar mata kuɗi,ko sisi baya bata ita dai bata rasa ci,sha,sutura da muhallin kwarai ba amma sisin kwabon shi baya shiga hanun ta,,ga uban neman mata tun suna Abuja ake kawo mata gulma yadda yake hulɗa da mata a wurin aiki wanda a farko bata yadda ba sai data saci wayar shi ta gani ranar kuka sosai taci,,har yanzu ya kai baya wani sauke hakkin auren su yadda ya kamata yana iya wata bai neme ta ba,idan ta kai kanta zagi da gori shine zai biyo baya har yanzu da suke Laberiya babu wani canji sauƙin ta ɗaya iyayen shi na matukar sonta kuma suna kyautata mata shine suka matsa mashi ya sama mata admission tana karatun nursing a can.
Na tambaye ta ko mummy ta sani?,,tace babu abinda ta boye mata sai zuga ta tayi wai ta mashi rashin mutumci,idan ya hana ta kuɗi ta kai ƙara wurin iyayen shi kota diba, Allah ya taimake ta ko ɗaya bata yi a ciki ba saboda ta gane kuɗin nan kawai mummy KE so Koda auren ta ya lalace bata da matsala da hakan.
Shawarwari na bata yadda zata kula da gidan ta ,ta karkato hankalin mijin ta a gare ta kuma taci gaba da hakuri da biyayya aure zata ci riba.
Mun kwashe wattani biyu muna tafka soyayya mai cike da tsayawa a rai da doctor Wanda auren mu saura wata ɗaya kacal abubuwa suka fara canja wa;,ta rage kula dani kamar lokcin farko,wanda ke kira na kusan sau biyar a rana,banda chat, video call kuma yana zuwa hira da dare kullum sai aka wayi gari da kyar yake kira na sau ɗaya a rana!
Cikin hikima ya amshe ATM nashi a hanuna ,da nayi magana ban gama haɗa kayan ba yace ayi hakuri da wanda kasa samu,gashi muna son haɗa kaya na ƙarya dole cikin kuɗi na na idda sayan kayan.
Kullum nike kiran shi,chat ma yana gani na online baya mun magana sai na mashi shima sama sama yake amsa wa,sai kuma ya ɗauke ƙafa ya bar zuwa hira idan nayi magana yace yanayin aiki har muka kwashe sati biyu a haka saura sati biyu aure lokcin mun kamala teaching practice da mun koma SCHOOL sai exams Wanda sati biyu zamu yi ana yi sai hutu daga nan sai final semester.
Abun duniya duk ya isheni kuɗi sosai philo ta ware muka tafi Sokoto aka haɗu muna kayan gyaran jiki na amare haka dai muke shirye shirye amma hankali na ba'a kwance ba.
Wata ranar na yanke shawara in same shi a office muyi magana na fahimta,da kyar na samu ganin shi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 12