yaye tare da buɗe glass window na d'aki haske ya bayan...,cikin jan tsaki zata fara masifa suka haɗa ido da Farida.
"Ai dama nasan babu wanda zai mun wanan rainin wayau sai ke"
Nayi maki baccin tun jya har yanzu 11:30am!
"Kada kiga laifin na tunda muka tafi Saudiya babu hutu kullum cikin ibada ba dole in Yi bacci ba tunda na dawo gida".
"Yanzu dai tashi ki watsa ruwa zan amso breakfast d'in ki wurin innah hussai (mai girki gidan)".
Yaye bedcover tayi daga cikin ta ta zuro ƙafa ƙasa,daga ita sai wata yar figaggiyar net sleeping dress komi na jikinta a bayanne,towel ta ɗauko cikin wodrob ta dauka.
"Sai Binta da idanu farida ke yi domin ta kara haske da shek'i fatar ta yayi luuuu alamar hutu ya bayyana a jikinta".
Tana shiga toilet farida ta kyara gadon tare da gyara komi a mazaunin shi domin tasan halin Fatima lazy girl CE ta karshe.
Wani corridor ta nufa ya sada ta da open kitchen inda masu aikin gidan ke girki,taga sabbin fuskoki kawowa ta tambaye su innah hussai?,suka ce tana ƙaramin kitchen na cikin gida.
"Ai kuwa nan ta sake ta kace kace tana haɗa wa mai gidan breakfast,tsaye tayi shiru tana tausayin yar tsohuwar"(wai ace mace ba zata iya haɗa ma mijin ta ko ruwan shayi ba sai masu aiki??).
_KALUBALE GARE KU MATA AURE:-musamman matan masu kuɗi,mulki,yan siyasa ko wani babban ɗan kasuwa.sai kaga mace a gidan mijinta ko kara bata iya kawar wa sai masu aiki!,mai aiki itace. Shara,wanke wanke,girki,wanki,guga da sauran su"ke a matsayin ki na matar gida menene amfanin ki?"waya faɗa maki ana yin aure ne don a huta?,shin a gidan ku ba'a sanar dake aure kacokan gaba ɗayan ta aure ibada bace,ko haka kika taso kika ga mahaifiyar ki nayi?,wallahi akwai mace da na sani tunda mijinta ya aure ta bai san daɗin taba,bai san daɗin abincin ta ba haka suke zaune shekaru shida kenan, tare da mai aiki aka haɗo ta daga gidan su.sobada haka a gidan ta mai Aiki take komi,kwanciyar aure sai yayi dakyar yake kwatar hakkin shi tun yana matsawa har ya hakura ya kyale ta wanda idan ya fita waje bata san da irin matan da yake hulɗa ba.,akwai wace kuma saboda ta manyanta(45yrs old) ta bar kwana d'akin mijin kwata kwata,girki,gyaran dakin shi,wankin under wears nashi duka yan aikin gida ne" shima idan ya fita bata san abinda yake aikatawa ba domin dai duk girma da shekarun namiji yana da bukatar mace a kusa dashi,haka mace duk shekarun ta tana bukatar namiji._
*Ya yan uwa mata zan su ku natsu ku saurari abinda zan faɗa,don Allah ki wanke zuciyar ki,keyi duba da nazari da tunani,kiji wanan bayani ki auna ki gani shin abin da zan faɗa gaskiya ne?,mu sani wanan duniya da Allah mai girma da buwaya ya halicce mu a cikinta ƙararriya ce,in kika duba a cikin annabawa;Ina Annabi Adam,Annabi Nuhu,Annabi Musa da Annabi Muhammad(SAW)??,duk sun Koma ga Allah*
*Ina kuma wa ɗan da suka keta haddin Allah,su kayi barna a bayan ƙasa,suka yi fasadi son ran su irin su;Fir'auna da hamana,Namruzu,kan'ana,abu jahil da abu lahab.suma duk sun koma ga Allah.*
_Don haka babu wani grantee da kike dashi a duniya na samun tsira a lahira face mace tabi Allah da Manzon sa, taji tsoron Allah a cikin rayuwar auren ta da rayuwar ta na yau da kullum,domin duk wani abu da zaki samu a nan duniya ɗaya biyu ne zai faru"ko ki mutu ki bar shi a duniya ko kuma kina kallo abun da kika tara ya fi ƙarfin ki saboda tsufa ko halin rashin lafiya"dole kuma idan kin mutu ki Haɗu da Allah akan abubuwa da kika aikata..,Amma idan kika yi hakuri a zaman auren ki,wallahi koda cutar ki mijin ki keyi Allah zai maki sakayya ta hanyar da baki yi zato ba kuma ki mutu ki sadu da rahamar Allah,ban san wani irin rashin natsuwa da surutun ke damun matan yanzu ba, sun mayar da sirrin auren su kamar wani shahararren series film ne wanda a dole kowa sai ya sani ko ya ji duk inda suka zauna "mijina kaza,mijina kaz,.......,ALLAH YA BAMU IKON GYARA WA._
"Sannu da aiki innalillahi Hussain?"
Ahhhh farida ce yau agidan namu?,ya mutanen gida yar albarka?
Lafiya kau suke ,ya aiki?
Gashi nan muna fama farida.
Sannu innalillahi hussai Bara in kama maki....
Ayah da kin barshi ai na kuwa kammalawa ma!
"Ɗan jimm tayi,dama kayan karin kumalon fatima nazo ɗauka."
Wai!,ai.kuwa ban haɗa ba saboda naga tana bacci kada a dafa ya huce Bata tashi ba...
Dama me zaki dafa mata?
Ai kin san mutumiyar taki abincin ta baya wuce indomie ne .
Bari zan haɗa mata ci gaba da aikin ki.
"Nan take ta diba fresh tattasai da attarugu haɗe da albashi tayi blending nashi a manual hand blender,Dama akwai ruwan zafi cikin warmer,Kawai ta haɗa ta kunna gas cooker ta ɗaura nan da nan ya tafasa ta zuba indomie kawai....
Saman electric cooker ta soya masu wai omlet,suna ɗan taɓa hira da innalillahi hussai har indomie ya dafu ta kwashe a babban round tray ta nufi dakin dashi.
"GIMBIYA har ta shirya cikin yellow armles short gown sai kamshi take zuba wa".
Lafiya dai kika dade?
Na taya inna hussai hira ne...
Ko dai kin taya ta aiki ba tana leka plate d'in"daga Nan wanan indomie ba itace ta dafa shi ba...,"ta FAƊI cikin ɓacin rai".
Koma dai menene kedai ba an dafa maki ba sai ki hau ci"lazy girl"
Kwafa tayi ta fara ci a hankali can har tayi rabi ta dago"KE ba Zaki ci bane?
Oho sai da cikin ki ya ɗauka ko?,acikin daɗi lafiya.
Sai da ta kammala ta ture saura gefe tare tana kwala wa mai aiki kira...
Wata yarinya ta shigo"kwashi plate d'in ki fitar akwai wani lemo cikin babban gora dana dawo dashi jiya ki daura saman tray da cups biyu ki kawo.
"Farida sai kallon bakin Fatima take yadda take wani bada order Kamar matar Governor".
Wani babban jaka ta janyo tare da Najeriya kayan ciki a ƙasa saman tyies"wanan tsarabar ki ce saboda kayan basu iso ba...
Cike da farin ciki ta sauko wurin kayan"kai Fatima hadda wasu tsaraba kuma?
Ai in faɗa maki Kaya SOSAI na jido sai faɗa daddy keyi dole aka rage wasu daga baya za'a sako mun.
_duba kayan ta shiga ki,akwai abaya guda biyu masu kyau sosai da gani suna da tsada,hijab guda biyu madaidaita farare masu igiya a baya,takalmin maza,kayan bacci biyu da wani box mai kyau.zoben azurfa ne Mai stone fari kal an zagane babban stone ɗin da ƙananan stones kaloli masu daukar ido,wrist watch golden colour Mai stone Shima sai hakurin Makka na ainihin zinari cikin ƙaramin container_
Rungume Fatima tayi cikin farin ciki domin Allah ya yi ta mace mai don hakorin Makka sosai,domin ko wanda ke bakin ta lokacin da mumyn su Fatima ta tafi maka ta sayo mata shi amma ba ainun zinari bane"Nagode sosai Fatima Allah ya bar zumunci ya nuna mana mun shiga gidajen mazajen mu lafiya".
Farida kenan!,wallahi jin ki nake kamar ciki ɗaya muka fito,Allah ya sanya mun sonki da tausayin ki a zuciyata saboda haka komi zan iya maki domin faranta zuciyar ki,wani leda ta dauko kayan wasan yara ne"wanan na ihsan ne domin dai na duba banda tabbacin size dinga na takalmi ko kaya",kinga takalmi na abban ihsan ne,riguna naki da aunty,hijab Kuma naki da nafisa kayan bacci duka naki ne da sauran tarkace in shaa Allah idan kayan can sun iso akwai abinda na tanadar wa umma ciki.
Shiru kawai tayi tana kallon bakin Fatima domin ta rasa me zata mata wanda zai nuna mata irin farin ciki da take ciki...
Malama kallon lafiya?,don Allah cire hauren nan mu saka sabo kinga irin nawa ne wallahi 35k na saye shi a kuɗin Nigeria.
"Cire wa tayi Fatima ta ciro wani auduga da farin gari a container din ta goge wurin da zasu saka ɗin sosai take murzawa kafin ta ciro shi ta saka mata, ɗas kamar an auna da hakori ta ya zauna sai shek'i yake yi a bakin ta".
Hajia farida kinga yadda ya amshi bakin ki kuwa?,masha Allah.
Dariya tayi suna tattara kayan cikin bag d'in.
Gyaran murya tayi,farida Allah yasan a yanzu bani da wani buri da ya wuce mu yi aure ko wacce ta zauna a dakin mijinta cikin kwanciyar hankali,sai dai kash"love seems not to favor us,ko wane dan iska da irin tashi salon yaudara yake zuwa,babu mai gaskiya babu na aure sai iskanci burin ko wane namiji a yanzu mace ta yarda ta bashi jikinta,akan zai bata wani jin daɗi na duniya,wanda da kin yarda kin bashi jikin ki shike nan kun yi hanun riga,soyayar da yake nuna maki zai fara raguwa to THE extent da kwata kwata ba zaki sake saka shi a ido ba.
Wallahi!wallahi!!wallahi!!!,wanan dalili na ɗaya daga cikin abinda yasa na mayar da ko wane namiji"CORPER",dole ya bauta mun kuma ba zai taɓa samun abinda yake so ba da yardar Allah,domin Allah yaga zuciyata kuma yasan manufa ta na yin hakan.
Farida ba zan so ki auri Alhaji shamsu ba saboda ba mijin aure bane ko rantsuwa nayi banda ƙaffara akan Alhaji shamsu jikin ki yake so!,idan har ya samu zaki ga WULAKANCI duniya farida!
Amma dai akwai hanya da zamu bi ta yadda zamu gane tsakani da Allah yake don ki ko jikin ki yake so.
"Ina so idan kin koma gida ki buɗe layin ki,kice yazo kina son ganin shi,idan yazo ki nuna mashi Kina son shi amma ƙaddara ta riga fata saboda zuwa da kuka yi sallah gida an maki miji Dan uwan ki har yazo kun ga juna ɗan lokaci ake jira idan kun fahimci juna a saka lokacin aure,kuma ke bakya son wanan ɗan uwan naki niyya kawai za kiyi"
Amma Fatima kina ganin zai amince?
Farida idan da gaske auren ki yake Ba zai taɓa rabuwa dake akan wanan dalili ba,idan kuma dama jikin ki yake so zai kokarin ganin yabi ta ko wane hanya a cikin ɗan lokaci ya samu kawai ya rabu dake.
Shike nan zan jaraba.
Fatima wallahi na matsu ki sanar sani dalilin da yasa kika mayar da ko wane namiji"CORPER"!
Uhmmmmm!
Farida lokaci nake jira da zarar yayi zan sanar daki nan bana dade wa ba.
Hira suka ci gaba da yi har aka kammala girkin rana suka ci ko wanne yayi Sallah sanan Fatima ta saka driver ya mayar da Farida gida.
Sosai aunty Salma taji daɗi tsarabar sai godiya take yi.
Da yamma kuwa ta buɗe layin ta na mtn ta kira shi,ya wani marairaice a dole shi yayi missing nata ya kamata yau su huta tare...
Maganar ta matukar yi mata ciwo amma kawai ta daure ta sanar dashi yazo su tattauna akan alkawarin da tayi mashi idan ta dawo zata sanar dashi hukuncin da aka yanke a gida.
Around 8:30pm alhaji shamsu tare da farida ranshi a matukar ɓace bayan ya gama sauraren bayanin da tayi mashi na auren gida da ake son mata da ɗan uwanta wanda bata so...
Sosai zuciyar shi tayi baƙi yana ganin wankin hula zai kai shi dare!
[7/25, 6:39 AM] Hayat: *🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*CORPER*
_{Ɗan bautar mata}_
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_~A Romantic Love Story~_
*BY*
*L££MA*
*DEDICATED TO MEELAT AND HUBBEEY*
*~UMMU FARHANA ban san da wani irin kalma zan yi amfani ba wurin nuna godiya ta a gare ki,kin nuna mun soyayya da kulawar Allah ya bar zumunci ya raya mana zuri'a Amin.Masu kira a waya da masu chat kuma ina godiya sosai~*
*All right reserved unauthorized copying, changing and translation of any part of this story in any form is prohibited.*
*🅿SEVEN*
Gyaran murya Alhaji shamsu yayi"yanzu me kike so ayi?"
Banza ta masa domin haushi shi take ji kamar me.
Maganar gaskiya farida ba zan iya rabuwa dake ba, saboda Allah ya jarabce Ni da son ki wanda idan ban ganki ko ji daga gare ki ba bana samun sukuni!
"Alhaji kenan!,amma kasan babu kyau neman aure kan neman aure ko?"
Ƙara matsowa yayi daf da ita yana ƙoƙarin rik'o ganinta...,ta fizge ranta a ɓace!
Kiyi hakuri farida soyayyar ki na matukar azabtar da zuciyata, Don girman Allah kada kice rabuwa za kiyi dani zan shiga mawuyacin hali...
Katse shi tayi"Me kake so nayi Alhaji bayan na sanar da kai auren dole za'a mun mutumin nan ko sonshi bana yi,cike da shagwaba take maganar tare da sakin wani kukan ƙarya mai tsuma zuciyar mai sauraro..
It okey farida,nayi alkawarin ba zan rabuwa dake ke ba,zan kasance tare dake har sai ranar da aka daura auren ki da wanan ɗan uwa naki.
Wani irin abu ya taso ya tukare mata zuciya cuz kwata kwata Bata Yi expecting jin haka daga bakin shi ba,wallahi ita hanyar rabuwa dashi kawai take nema ko Allah zai kawo mata wani dai dai ita.
"Kin yi shiru?"
Uhmmm shike nan Nagode da soyayyar daka nuna mun,kawai muci gaba da neman zaɓin Allah.
Har cikin zuciyar shi yaji daɗin magana ta,hannu ya saka kojerar baya ya dauko wani baban leda"Ga wanan nikam har yau ban san choice naki ba Koma baki sanar dani ba".
Cikin jin nauyin shi ta amsa tana godiya suka yi sallama.
A palour ta zazage ledan;turaruka be designers masu kyau da tsada,shower gel "WHITE CARE GOLD" babba guda ɗaya,roll on kala kala da su chocolate.
"Rike baki aunty Salma tayi,shi wanan mutum baya gajiya da hidima?"
Shiru kawai tayi!
Ina fata kun tattauna magana mai muhimmanci dashi?
Eh aunty salma mun yi magana gaskiya amma ba yanzu zan gabatar dashi ba sai mun fahimci juna,kin ga kwata kwata fa satin mu uku da haɗu wa.
"Haka ne,Allah ya shige mana gaba Amin".
Washe gari tun da safe sai ga Fatima nan a gidan nasu,gaisawa suka yi cikin mutunci da aunty Salma tana yi mata godiyar tsaraba da ta basu,daga bisani suka kebe a dakin farida.
"Farida ta sanar da ita yadda suka yi da Alhaji shamsu"
Dariya sosai Fatima tayi"dama nasan ba zai rabu dake ta sauki ba saboda yana ganin hidimar da yayi dake zai tashi a banza,yanzu ne zai zage damtse yaga ya samu biyan buƙata daga haka wallahi ba zaki sake ganin shi ba na tabbata ba auren ki yake so ba kuma baya kishin ki",idan ba haka ba ta yaya zaki sanar dashi bakya son wanda zaki aure shi yace yana tare dake har sai an daura maki aure!,shi ba auren naki yake so ba kenan?
Kema kya faɗa fatima mutumin nan kamar maye yake da naci...
Mu kuma zamu zame mashi kamar kaska!
Yanzu dai ga wanan gobe ba zan fita aiki ba.
Koda ta buɗe ledar;bagaruwa ɗan Saudiya da dabino ke ciki sai invitation card na aure"daga ina?"
Yan office Zaki Kai wa gobe tsarabar su kenan, invitation card Kuma naki ne na auren uncle salim din mu!
Wani shewa ta saki domin sun cima auren nan buri mai tarin yawa"yanzu kenan zuru zamu wuce ko?
A'a Sokoto dai saboda can amarya take,za'a raba hannu ne wasu zasu Sokoto ayi WALIMA da SWARD CROSSING dasu sai su dauko amarya zuwa zuru,sauran mutane zasu tsaya zuru.
Eh gidan gwaggo Hadiza za'a sauka a YAURI FLAT,saboda haka lokaci yayi da Alhaji shamsu zai mana amfani!
"Allah ko Aminiyar?"
Sosai ma saboda shi zai kai mu kuma ya dawo da mu...
Kina ganin zai amince?
Bura'uba kenan!,cewa fa yayi yana tare dake har sai ranar da aka ɗaura auren ki!
Yanzu dai gobe su aunty kubra zasu wuce da kayan sa lalle, already lefe na wurin su tun last week aka kai.
Mummy da mutanen ta sai Wednesday zasu wuce zuru,shi daddy sai Friday SABIDA aiki kinya yana barin gida ranar zamu wuce Sokoto mu dawo Saturday idan an gama SWARD CROSSING daga nan zasu wuce zuru da amarya,mu kuma mu juyo kebbi.
Shike nan zan sanar da aunty Salma.
"Anko na wurina an gama dunki,sanan dubu ɗari biyar din nan na wurin Alhaji shamsu da kika amsa idan mun isa Sokoto za muyi shawarar yadda za'a yi dasu cuz naga umma ta dau zafi damu a yanzu duk wani kyautatawa da za kiyi ba zata ji daɗi ba idanun ta ya riga da ya rufe akan maganar auren ki".
Fatima na rasa me yasa umma take mun haka bayan tafi kowa sanin auren nan lokaci ne,Ni kai na yanzu nafi kowa bukatar auren nan amma idan Allah bai kawo na gari ba ya zaka yi?.
Idan na zauna wata zuciya na bani shawarar in fitar da Alhaji shamsu kawai ayi komi tunda yana sona nasan zan samu kulawa da kyautatawa wanda a hankali zan fara son shi
"Koda wasa kada ki Yadda ki bashi dama farida, na rantse maki da Allah sai kin yi nadama mara amfani a kurarren lokaci!"
Wai Fatima kina bani mamaki,ke ba auren nan kuma taɓa yi ba,gidan ku babu abinda kika rasa,babu irin gata da kulawa da baki samu,babu wanda ya matsa ma rayuwar ki shike nan saboda baki da niyyar aure ba zaki hana Ni aure???
Dariya sosai Fatima ta keyi sai da hawaye Masu zafi suka fara zuba daga idanun ta"Ni Fatima ce bana son aure ko?,nice bani da damuwar komi ko?,nice baa matsawa akan maganar aure ko?
"Dama lokaci nake jira in shaa Allah idan muka tafi Sokoto zan baki tarihin rayuwata wanda ta nan ne kawai zaki iya gane koni wacece!"
Jikin ta sanyi yayi ganin Fatima na hawaye,kiyi hakuri ke ɗin ce wani lokaci abubuwan ki kama wata mai jinnu ko mai wankin idanu!
Ko ɗaya farida"am only talking out of experience and u will soon understand my reason behind this motive".
Uhmmm in shaa Allah it shall be well with us.
Shiru suka yi na ɗan lokaci saba suka nufi kitchen wurin aunty Salma fake kokarin haɗa lunch.
"Aunty ga invitation card na auren uncle salim Fatima ta kawo"
Goge hannuwan ta tayi da hand towel ta amsa tana dubawa..."masha Allah abu yayi kyau haddasa SWARD CROSSING?'
Eh aunty ai AIR FORCE NE"Fatima ta amsa"
Zaki sha buki kenan,zurun zaku ko Sokoto?
Sokoto zamu aunty Salma don Allah ki Taya Ni Sanar da abban ihsan nasan zai amince tunda daga gidan su Fatima ne.
Yan matana kada ku samu damuwa idan ya kai daga nan har birnin sin zan tsaya maki farida ku tafi,Ni dai addu'a ta ko riƙe mutuncin kan ku Allah na sane daki shi zai zaba maku mazaje na gari dai dai da ku.
Shi yasa nake son ki aunty na ko don addu'oin ki"cewar Fatima"zan tafi aunty sai wani lokaci.
Au na kusa kamala girkin fa!
Nagode aunty zannisa gida rana tayi..
"Ba wani nan dama haka kike idan kinzo gidan mutane kamar saman ƙaya kike ko don bamu da air conditioner ne"
Amma farida ban ji dadin wanan magana ba koda yake bana ganin laifin ki sai mun haɗu a Sokoto zan warware maki tsakanin zare da abawa.
Har bakin gare ta raka ta,wata jibgegiyar TOYOTA new model ki jiran fitowar ta"ke Fatima ina kuma kika samo wanan?
Wani sabon CORPER ne farida idan kika ganshi yayi jika ta goma dani wai shi Nan sex yake son Yi Dani at any cost!
Uhmmm maza mutanen mu,Allah ya tsare Fatima,plz take good care of yourself for me.
I will in shaa Allah,suka rabo.
Ranar Wednesday shine ranar da ya kamata suyi resuming aiki amma fafur Fatima taƙi fita aiki,bayan farida ta basu tsarabar Fatima taci gaba da aikin ta har suka tashi ta biya gidan su Fatima wanda babu kowa sai mai gadi saboda mummyn su ta kwashe yan aikinta sun tafi.
Yanzu ke ɗaya ke zama cikin wanan tafkeken gida?
Eh amma ai daddy na nan anjima zai dawo daga office.
"Amma wa zai maku girki?"
Wai girki tab!,akwai miyar kala kala a cikin freezer har white rice da beans Wanda inna hussai tayi warming Kawai zan masu idan ya dawo,dama idan ba week end ba baya break fast a gida dinner Kawai yake ci.
Uhmmm daddy na kokari ace mutum nada dukiya,wadata da mata amma baya samun kulawa yadda ya kamata!
Matsalar su ai shi yaga zai iya hakuri zama da mace ɗaya tana iskanci son ranta,kuma kika san tsiyar da yake tsulawa a waje?
"Fatima amma baki da hankali iyayen ki ne fa!"
Dariya kawai ta saki domin tabbas farida ba zata fahimta komi ba sai taji labarin nan da take son Bata shi.
"Ya kinyi magana da Alhaji shamsu akan tafiyar mu kuwa?"
Yau dai zan sanar dashi idan yazo,saboda Bana son takura shi yasa ban bashi fuskar zuwa hira kullum ba.
Ok bara na ɗauko ankon ki gani,cikin akwatin kayan ta ta ciro wasu kaya"atamfa ce irin na 3k ɗin nan mai kyau an masu ɗinkin dogaye riguna".
Warware rigunan tayi"Wow gaskiya style ɗin sun yi kyau,nan take ta gane Bata cuz tafi Fatima tsayi da structure".
Tattaunawa suka ci gaba dayi har la'asar Fatima ta kira wani CORPER ya mayar da farida gida.
Da dare tsaf ta shirya cikin free gown na yadi Mai sulbi ta feshe jikinta da turaruka masu kanshi sosai ta nufi gare wurin mutumin..
Bakauye sai washe baki yake yana hadiyar yawo yadda yaga kayan yabi jikinta duk wani surar ta ya bayyana.
Langwabe kai tayi cikin uwar shagwaba suka gaisa;,ai kuwa ya saki baki kamar wani soko yana Binta da kalo....
Farri baby kina kashe Ni da kyawo anya zan iya hakuri wani ya aure ki kuwa??
Wani shaidaniyar dariya ta saki"Alhaji na kenan, bana so kana kawo wanan magana zuciyata na kuna kawai muyi abinda ta shafe mu.
Okey as u wish my princess,yanzu dai me kine son ci?
Kamar me fa"ta fadi cikin ɓaci rai!
Gasasshen kaza,kifi,rago ko shawarma?
Ko ɗaya a koshe nake...
Katse ta tayi"amma ya kamata mu ɗan fita mana ko zafi na rage farry baby!",Yana magana hanun shi na yawo saman santala santalar cinyoyin ta yana kokarin haura wa dsu saman boobs nata.
Da sauri ta riƙe hanun"menene haka Alhaji?"
Kaji tsoron Allah mana,kai fa uba ne kana da yarinya wace ta kai munzalin aure idan wani ya aikata haka da ita a kofar gidan ka ya zaka ji cikin zuciyar ka?
Kicin kicin yayi da rai"luk farida ba nazo wurin ki bane ki mun wa'azi,wallahi tun kafin a haife ki nake neman ilimi Addini har yau ban fasa ba,babban mallamin izala nake,ina bada Sallah kuma sani ake tafsir masallacin"MALLAM ABBAS JEGA",din me zaki tasa Ni a gaba kina mun wa'azi?
ZUNUBIN nan fa kowa na aikata ta a aduniya wallahi,illa kawai daka gama ka kiymta istigfari kawai.
"Sassauta murya yayi,ina maki kallon wace ta waye ashe ba haka ba ne?
Sosai tayi kokarin danne zuciyarta"Alhaji ba wai bana son faranta maka bane,kada ka manta a kofar gidan mu kake yanzu idan wani ya fito ya gamu fa?
Shi yasa nace dake mu samu wani wuri na daban da zamu rinƙa zuwa kawai!
Naji amma ba yau ba domin nayi maka wani tanadi mai zafi a daren juma'a!
Allah ko yar gari?
Sosai ma saboda akwai aure da zamu tafi na gidan su aminiyata fatima daga Ni sai ita kaga sai ita na zaɓi ka kaimu ne saboda mu samu isasshen lokaci na kebe wa.
Washe baki ya fara yi,ranar yaushe zamu tafi koma yaushe zamu dawo?
Ranar juma'a da safe mu dawo Saturday da yamma.
Ai wanan ba matsala bace, Sokoto gida ne idan kun shirya ranar juma'a sai ki sanar dani.
Yaso ko kisa ne ya samu amma keme me taki sakin jiki har suka rabu.
Aunty Salma ta samu abban ihsan da maganar tafiyar su farida wanda da kyar ya yadda domin ya ɗauki laifi kacokan ya ɗora mata gani yake itace ke mara wa farida baya tana yadda take so.
Ranar Alhamis basu fita wurin aiki ba saloon suka nufa aka masu gyaran suka da farta sanan suka nufi gidan su farida har dare Fatima na gidan ta amsa abayar farida da zata yi amfani dashi wurin walima da sauran tarkace nasu na mata ta tafi dashi gida saboda jaka ɗaya za suyi amfani dashi.
Ranar juma'a da safe yan matan tsaf suke cikin dry lace ash colour Wanda ya Sha surfani pink sai tashin kamshin suke,sallama suka yi da aunty bayan ta gama masu nsiha suka fito bakin gate.
Sake baki yayi yana kallon irin kwaliyar da suka sha kamar wasu matan shugaban ƙasa, buɗe masu yayi ko wace ta Hakimce a gidan baya"yau gani ga aminiyar mu Fatima"
Gimtse dariyar ta tayi sosai ta amsa"Alhajin mu kenan, kullum my farry Bata da hira sai naka ka saye zuciyarta da soyayar ka,don Allah a rike mun ita da amana Alhaji!
Baki da matsala aminiyar mu,wallahi soyayar da nake mata tafi nata kinga kuwa dole zan jajirce domin samun mace irin farida a wanan zamani sai an tona,ga kyau da dari,jan aji da iya kalamai,babban abun burge wa atattare da ita babu
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 12