ruwan ta da kwadayi irin na yan matan zamani,kullum ina cikin kuɗi kuma ta sani amma bata taɓa daura mun lalurar MILLION daya ba,idan da wasu yan matan ne da yanzu har mota sun mallaka na kansu.
Kallon juna suka yi da mamaki"uhmm Alhaji ai kasan mu YAN ZURU tarbiyyar mu ta bambanta da sauran yan mata,ba'a yi mana irin Wanan tarbiyyar ba na amsan abun hanun namiji burin mu kawai ka samu kulawa fiye da yadda kake tunani shine ake ganin kamar asiri muke yiwa samari ko maza wanda ba haka bane tsabar kulawa ne da tattali.
Gaskiya ne Fatima wallahi kun ciri tuta ai,yanzu dai akwai inda zamu fara biyawa ne ko mu kama hanya?
Banza farida tayi tana shan kamshi"ammm inaga mu tafi kawai saboda 4pm ne walima kuma sai mun shiga kasuwa da mun isa.
Addu'a yayi tare da fara jan motar wanda ke rufe ruf sanyin air conditioner da kanshi ke tashi.
Watau Fatima Allah ya jarabce Ni da son abokiyar ki wallahi domin kin ganni nan,ban taɓa samun mace da hankalina na kwanta da ita irin abokiyar ki ba,nasha wahala sosai a hanun mata tunda na yi aure ban taɓa sanin dadin aure ba tsakani na da matata sai zagi da cin mutumci har kwala na take ci tana zargin iyayena idan nayi magana tace sai na sake ta...
Subhanallah Alhaji!
Dama b auren soyayya kuma yi ba kenan?
_Wallahi tana sona ina son ta muka yi aure,kawai dai wasu matan idan suka samu kulawa da kyautatawa a wurin miji fiye da misali sai mu mayar da mijin ɗan iska wanda bai san ciwon kanshi ba,ina baki labari har ta yi haihuwar fari muka samu baby girl babu abinda ya canza tun ina hakuri har na fara kai ƙarar ta gidan su,sai a bani hakuri wai quruciya ce.babban tashin hankali uwata mugun sonta take saboda irin kyautatawa da take mata Ni kuma gana muzguna mun a boye, anyi lokacin da ta mare Ni tana faɗin idan na cika haihuwar uwata da ubansa dake kabari in sake ta.....,ban iya furta komi ba na nufi wurin mahaifiyata ina kuka tare da nan izinin ka akan zan saki matata"ranar naga tashin hankali uwata na kuka wai an faɗa mata nike muzguna wa matata idan na sake ta bata yafe ba!,hakuri Fatima babu irin wanda bani ba har Baby ta Kai shekaru goma a duniya babu abinda ya canja kawai na yanke shawarar ƙarin aure ai lokacin har wuta ta sawa gida na tana iƙirarin zata kashe Ni duk ban damu ba na kyale ta kawai na nemi admission na koma "BUK KANO" na fara master's degree sai naga dama nake zuwa har na kamala bata fasa hauka ba lokacin aka haɗa Ni da wata yarinya mai hankali wace bata wuce 17yrs ba Fulani ke tayi karatu har junior secondary School loakcin mahaifinta ya rasu,ban bata lokaci ba na nemi izinin ƙarin aure wurin mahaifiyata ai kuwa ta sanya albarka.cikin ɗan lokaci na kai kuɗin aure da kayan lefe tare na nuna ma mahaifiyarta bana son komi nasu zan yimata idan yazo gida na,cikin sirri aka ɗaura aure na da Hafsah kafin a kawo ta na da aka gyara mata daki ɗaya da palourn ta sosai da dare aka kawo amarya"watau Fatima ranar bamu yi bacci ba domin aisha uwar gidata wuka ta nufo Hafsah gadan gadan dashi zata kashe ta",da kyar na fitar da Hafsah a gidan muka nufi gidan mahaifiyata na sanar da ita komi a lokacin ta bani baki in saki Aisha idan har ba zan iya zama da ita ba;da safe dana koma yankin ta kunna ashe tun cikin daren ta jona tiyo ta saka dakin amarya koda gari ya waye ruwa ya kusa taɓa silin komi la jike sharkaf!,a A ranar na yiwa aisha saki biyu nan take kuma na amshe diyata,in takaice miji sai da Hafsah tayi sati ɗaya a wurin mahaifiyata na gyara komi sanan ta dawo,can gidan su aisha kuwa babu wanda ya tambayi dalilin saki har ta gama idda basu ganni ba lokacin aka fara zuwa bada hakuri fafur naki mayar da ita;Fatima labarin nan da nake baki anyi shekaru shidda kenan yanzu haka haihuwar Hafsah biyu tana da cikin na uku kuma tunda muka yi aure ba'a taba jin kan mu ba saboda hakur da biyayya irin nata,ita kuma baby tana"FEDERAL GOVERNMENT COLLAGE GWANDU ss2"._
Kana nufin har Baby ta shekara goma sha shidda kenan baka mayar da uwar gidan ka ba ko tayi wani auren ne?
Uhmmm!,har yau mutune na zuwa suna bani hakuri in mayar da ita Dakin ta wallahi Fatima ba zan iya zama da ita ba kuma,cikin ikon Allah da yake banda alhakin ta har yanzu bata samu mijin aure ba,Ni kuma ina zaune lafiya da mata ta...
"Menene yasa kake don ƙara aure bayan matar ka bata da matsala?"
Saboda ina son farida,saboda uwata ta gindaya mun sharadi lallai idan ba zan dawo da uwar gida ta ba dole in Kara aure,saboda Hafsah yar ƙauye ce har yanzu bata waye ba,babu iya dressing,girki na zamani,kwalliya,kula da miji da sauran su.
Kallon juna suka yi da farida Fatima ta tintsire da dariya"domin dai ko shi ba ƙauye ne,bagidaje wanda bai ko ya magana mai daɗi ba bare kula da mace kuma a haka yake son wayayar mace".
Sun Yi nisa da tafiya Ita dai farida komi bata tofa ba hira shi da Fatima kawai suke yi har suka iso Sokoto ana hada hadan sallar juma'a.
"Bakin wani tsadadden restaurant ya Parker don su ci abinci wanda Fatima ta buka ci hakan,nan take ta baje basirar ta tayi masu order abinci mai kyau da tsada suka ci a hankali sai bin su aka da kallo domin a ƙalla sun yi order kusan na 20k,abunda ya Kara janyo hankalin mutane a kansu shine yadda suka ɗan tsakura suka bar shi,Alhaji na zaune gefe yana kallon su cikin kulawa domin wayewar da jan ajin su na daga daga cikin abinda yasa yake mugun son farida"waiter ta zo ta wurin shi,Alhaji me za'a yi serving naka?,kada ki damu Ni driver su ne da sun gama zamu wuce"nan kallo ya koma kan su da zasu fita wasu gayun da yan mata har leken su ake musamman da aka ga ya buɗe masu gidan baya sun shiga ya ja.
"Aminiyar mu yanzu sai ina?"
Yauri flat zaka fara kai mu mu gaisa da mutane idan an dawo Masallaci sai mu tafi kasuwa ko?"tana kallon farida"
An gama ranki ya dade.
Suna isa ta kira wata budurwa a waya tayi masu bayanin gidan,ai kuwa yana Parker wa Fatima tace"lallai wa zai kwana a wanan tsohon gida?",gaskiya Alhaji ba girman mu bane sauka a gidan buki ga mutane sun yi yawa kuma muna bukatar privacy".
GASKIYA kamar kin shiga zuciyata,yanzu dai ku shiga a ganku,zan tafi masallaci daga nan zan kama maku d'aki a "GIGINYA HOTEL"kun ga da daga kasuwa mu nufi can kawai kuyi baccin ku.
Godiya muke,suka fita da hand bag nasu zuwa ciki,ai kuwa nan dangi suka yi chaa kan Fatima da surutu banza tayi dasu suka shige Dakin yan mata anata raha daga baya suka yi sallah,duk kayan ciye fiye da aka tara masu kome basu taɓa ba har ya dawo suka yi sallama da yan gidan tace a gidan wata friend nasu zasu kwana amma anjima zasu haɗu wurin walima.
Suna fita yan mata sai gulmar su ake yi har ya tadda mota suka nufi tsohuwar kasuwa wani babban shago na sayar da kwala kwalai nan Fatima ta zabo babban set ɗaya na pure gold Wanda ya haɗa da yan kunne,sarka,zobe da Bangles Manya biyu,koda aka auna ya kama 3500,000 naira ta umurci farida da tayi mashi transfer na kuɗin cikin kuɗin da Alhaji shamsu ya tura mata.
"Nan take ya bada account number tayi mashi transfer Amma zuciyarta cike da tunani irin irin".
Wasu zobe ta ƙara zaɓo wa guda biyu masu shegen kyau da shek'i aka auna mata sun kama 70k,still sai farida tayi mashi transfer yayi wrapping komi tare da masu godiya suka fita.
Fitowa suka yi farida dai na kallon ikon Allah"Alhaji mu tafi sabuwar kasuwa ko?"
Okey ran ki ya Dade naga kun yi saurin fitowa ne?
Ahhhh Alhaji talaka ina zai dade cikin kasuwa,ai dole mu fito da sauri saboda kada haushi ya kashe mu ga kaya babu cash.
Don Allah ki bari hajia Fatima kamar mu manya masu ƙasa ace babu caSh a wurin ku ai harka ta lalace,yanzu dai Bara nayi Mata transfer Koda 50k ne ku samu na riƙe wa nima bana yawo da cash.
Ahhj gaskiya ta gode sosai Alhaji nasan zai isheta sai na raka ta ta saya abinda take so..
"Ka jiki da wata magana ai da kai da kaya mallakar wuya ce"
Haka ne Alhaji gani nayi kasuwan Sokoto dai ko MILLION aminiyata ta shigoe dashi tana iya kashewa tas basu isheta ba bare Ni yar rakiya.
"Ya gane bak'ar magana ta sakar masu,su yar haka ne?",zan maku na 100k kuyi manage kwana kin Nan wasu project ke gabana suke cinye mun kuɗi wallahi.
Yanzu naji zance Alhaji"Godiya muke".
Nan take ya Mata transfer kuwa suka ji alert.
Yana parking suka fita,dama tana cike da haushin Fatima data kwashe nata kuɗi aka saya set na gold,a ganinta Fatima na using Bata ne tana gina kanta"yanzu ke Fatima don Allah wane irin rashin kunya kenan da yada kai wurin namiji?,kina wani kashe murya kamar saurayin ki yanzu yanzu har kin amshi dubu dari a wurin shi me zakiyi dasu?
Dariya sosai Fatima keyi a cikin kasuwa kamar zata shede saboda yadda farida ta haɗe rai kishi ƙarara kwance a fuskar ta"hajia ta kwantar da hankalin ki,saurayi dai baki ne mama ya zama dole aci kuɗin shi domin shi ya saka kanshi BAUTAR MATA,an sanar dashi bai yi qualifying ba,amma yana kokarin saka kanshi a BATCH A LIST Wanda Kuma babu sunan shi a ciki shi yasa na faɗa maku ko a cikin CORPERS wanan special one ne,Allah ne ya kawo mana shi har gida dole na lakaci arziki hajia ta,beside ma yanzu fa ya gama faɗa mana ya a da makudan kuɗi amma bashi da abun yi dasu,da bakin shi yake faɗin da wata budurwa ce da yanzu ta mallaki motar hawa na kanta da kuɗin shi"rik'o ganinta tayi farida ta shi mai bayar wa bai yi raki ba sai ke mai amsa zaki fara raki tun ba'a kai ko ina ba!!!
"Tsaki taja domin gani tayi Fatima na neman raina mata da hankali ta mayar da ita ƙaramar yarinya wace bata da wayau".
KWALLIYA COSMETICS SUPER MARKET suka shiga aka basu wurin zama,set ɗin"FAIR AND WHITE,ALTIMATE GOLD"ta dauka wanda akalla kudin shi ya kai 15k cuz ko cream din kaɗai kudin shi 6k ne a super market d'in,CLEAR SKIN hand and feet lotion ta ɗauko,MEDIUM MAKE UP KIT,SET NA ANACONDAR HAIR KIT TA ƊAUKA wanda ya haɗa da relaxer, shampoo, conditioner,hair cream and oil"haka dai ta tura gidan tarkacen gyaran jiki sai da ta kashe 70k"farida kamar tayi kuka ,akayi parkeging komi suka nufi wani shago na kayan takalma da jakuna ta kwashi takalma biyu na 7k each sanan suka fito likis around 5pm.
GIGINYA HOTEL ya fara nufa dasu already ya kama room biyu kusa da juna, ɗaya nashi da farida,ɗaya kuma fatima.
Suka shiga ya masu bayani"Fatima tace haka yayi Alhaji yau ango kake kenan,Ni kuma za'a varni da rungumar pillow ai dana dan haka ne da na gayato Baby na...
Kada ki damu ai Sokoto gida ne idan kina don abokin kwana akwai wani tight friend Dina zan kira shi!
Wasa nake yi Alhaji ai babu komi kuji daɗin ku,yanzu dai zan shiga dakin na da kaya ke farida ku shiga naku kiyi wanka mu nufi wurin walima.
Wani irin kallon tsana ta watsa ma Fatima"irin ashe dama haka kike ban sani ba?"
Ko'a jikinta ta shige nata room din babba ta sa nashi key tare da faɗa wa saman makeken family bed d'in"daga ganin Dakin yana da tsada sosai", softly ta furta READY FOR THE NEXT STEP.
~_KUYI TA HAKURI DANI DON ALLAH TYPING SAI DA NATSUWA_~
_HALIMATU SADIYA MUHAMMAD_
*L££MA*
[7/27, 6:22 AM] Hayat: *🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*CORPER*
_{Ɗan bautar mata}_
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_~A Romantic Love Story~_
*BY*
*L££MA*
*DEDICATED TO MEELAT AND HUBBEEY*
*_A MADA DIN BRILLIANT WRITER'S ASSOCIATION MUNA GAYATAR YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI ZUWA BUKIN AURE NA ƊAYA DAGA CIKIN MEMEBER NAMU"SADIYA MUHAMMAD BEJI"(AUTA BEJI MARUBUCI YAR"KAR KA MANTA DANI"),WANDA ZAA YI GOBE A NIGER STATE,MINNA OPPOSITE CHALLENGE INTERNATIONAL SCHOOL.ALLAH YA BADA IKON HALARTA AMIN_*
~MAMAN MU,MARYAM MUHAMMAD HASSAN, SURRAYAHMS,MEELAT MUSA,SIS OGANNIYA DA SAURAN YAN UWA MUSULMAI DAKE KWANCE GIDA DA ASIBITI BABU LAFIYA,ALLAH KA BASU LAFIYA YASA KAFFARA CE AMIN~
*All right reserved unauthorized copying, changing and translation of any part of this story in any form is prohibited.*
*🅿EIGHT*
A hasale ta shiga bugun kofar dakin Fatima kamar zata balle shi tana faɗin"bana son irin haka Fatima me yasa zaki mun haka,saboda na biyo ki shine zaki haɗa kai dashi ku wulakanta Ni Ko??".
"Yadda take magana cikin magiya Muryar nata cike da rauni yasa Alhaji shamsu jin matukar tausayin ta",kwantar da hankalin ki farida wasa Fatima ke yi wallahi ba zan taɓa aikata abinda baki so ba har sai zuciyar ki ta aminta dani,Ni masoyin ki ne na gaskiya bana burin cutar da rayuwar ki.
Yi tayi hankalin ta ya kwanta dai dai lokacin Fatima ta bude kofar tana kasar dariya hada riƙe ciki"ashe dama haka kike da tsoro farida?"
Ban sani ba,ta bata amsa tana kokarin shiga d'aki...
Fatima ta mayar da kofar ta rufe kafin ta isa wurin farida har ta faɗa toilet,ai kuwa ta ci gaba da dariya...,ai da kin fito mallama kin cire kayan ki Daura towel na rufe kofa ba biyo ki zai yi ba!
Banza tayi mata sai jin alamar saukar ruwa tayi,kenan har farida ta sakar wa kanta shower.
Bata wani ɗauki lokaci mai tsayi ba ta fito daure daure da veil nata fuskar nan murtuke!
"Gaba tawan ai kin san ba zan taɓa yin abinda zai cutar dake ba,wallahi tallafi bada wata manufa na aikata hakan ba,kawai don in nuna mashi kina son shi ne cuz na fuskanci mutumin yana son ki da gaskiya ba zai cutar dake ba kin ji besty na."
Tsaki taja tana dube dube inda zata ga bag d'in kayan su ta shirya zuwa walima.
Rik'o hanuwan ta tayi, believe me farida wallahi bana da niyar cutar dake,ina son ki har ga Allah ki yarda da dani zan maki bayanin komi kin ji?
Cikin sanyin murya ta amsa"shike nan Fatima wallahi ke ɗin ce yau duk kin caza mun ƙwaƙwalwa na rasa gane inda kuma dosa.
Wait lemme fresh up,zamu tattauna akan duk wani abu dana aikata yau,idan zaki amince ba lallai sai mun tafi walimar ba kawai dama nayi alkawarin baki tarihin rayuwata in shaa Allah zan yi anfani da wanan dama domin sanar dake koni wacece.
"Kina ganin rashin zuwar mu wurin walima ba zai zama matsala ba?"
Ko ɗaya zan yiwa mummy bayani.
Shike nan Bara na dan shirya kafin ki fito ..
Fatima na shiga toilet ITA kuma ta feshe jikinta da turaruka ta saka wata yar armless free gown ta faɗa saman bed d'in.
zuwA wani lokaci Fatima ta fito daure da towel tayi shafe shafen ta data saba ta saka ƙaramar riga itama sanan ta janyo sayayyar da suka yi duka a kasuwa ta hauro saman bed din.
Farida ki buɗe kunnuwan ki da kyau ki sauraren Ni kuma ki natsu ki fahimci dalili na nayin haka;set na gold dana saya da wasu zobe guda biyu wanda suka kama dubu ɗari huɗu da ashiri duka naki ne ..
Zaro idanu farida tayi!
Kada kiyi magana nasan zaki tambayi dalilin sayan su,kuma kina jin tsoro a gani a gidan ku,zan so ki aje tsoro" at your age yanzu kin isa ki ɗauki dawainiyar kan ki da iyayen ki saboda kuna aikin gwamnati,kin isa yi yiwa kanki abinda kike so koda ya kai na million ne babu wanda zai tuhume ki saboda ansan kina da hanyar samun kuɗi kuma kina iya juya su yadda kike so saboda haka maganar tsoro ko gudun surutan mutane ki aje shi gefe.
Ta Daga set na zinarin,ban sayi wanan saboda ki saka shi yanzu ba ko ki aje a gida ba,bank ɗin da kike operating zamu kai su ajiya koda zai kai shekaru ashirin ne babu abinda zai sake su har sai lokacin da kika buƙata,su wanan zobe guda biyu zaki saka su a hanun ki (70k kenan).duk wanda ya tambaye ki adashi kika kwasa kin rasa abun saya kika sayi zinari dasu zuwa gaba idan lalurar kuɗi ya taso maki ki sayar"dubi yatsuna",ta daga mata,ina fatan tunda muka haɗu kina lura dasu?,duka uku zinari ne da muka tafi Saudiya da daddy na sayar da guda biyu nawa kana na,na canza manya biyu na(40k each) da karami ɗaya na(30k) ,sanan ina da set biyu a bank manya wanda babu wanda ya saya mun a cikin ahli na duka kuɗin samari"CORPER'S"wanda basu bauta wa matan su na Sunnah sai matan waje.
Farida bana so ki sanar da kowa kina da jiyar zinari A bank,wallahi nasan nan gaba zai maki amfani matuƙa saboda halin rayuwa,baki da uba,umma bata da ƙarfi,yaya jamilu rufin asirin Allah ne kawai;misali auren ki ya tashi kina bukatar kayan more rayuwa a gyara maki gida dashi wanda baku da wanan ƙarfi lokacin duk wani tanadi naki zai yi amfani.
"Farida dai na riƙe da zobuna na zinari tana juya maganar Fatima a zuciyarta domin duk abinda ta faɗa gaskiya ne,itama tana sha'awar yadda taga Fatima na ado da kwaliya cia komi nata mai tsada ne,a nata wautar Fatima tayi mata zarra ƙarfin su ba ɗaya ba,bai kamata ta haɗa kanta da diyar commissioner ba!
"Hajiya ta bani hannu kin ji bana son dogon tunani idan kuma basu yi bane sai a mayar kawai a baki kudin ki".
Miƙa ganinta tayi,Fatima na isa ince basu yi ba wanan hidima da kike yi dani ai ko ciki ɗaya muka fito sai haka.Allah ya zaba mana mazaje na gari wanda zasu riƙe mu akan gaskiya da amana Amin.
Ɗas suka zauna a zara zarar yatsun ta suna shek'i,dama akwai azurfa da Fatima ta saya mata a Saudiya sai suka ƙara haska yatsun ta"murmushi mai kayatar wa ta saki"
Kin ga yadda kika haɗu kuwa Hajiya ta?,zinari a baki,zinari a hannu!
Suka saka dariya suna tafawa.
Sauran kayan data saya a "KWALLIYA COSMETICS"ta fitar duka,farida ba zancen cin fuska ba gaskiya kina bukatar kyara na Musamman dubi skin nayi don Allah kamar ba budurwa ba, especially yr face dark spot sun bata maki,kullum fuska fayau babu make up, suman kanki gashi da yawa amma babu gyara yadda ya kamata and lastly wodrob naki ma dole zamu canja nan gaba.
Fair and white gold nasan zai amshi jikin ki yana da kyau sosai nayi amfani dasu duka zan nuna maki yadda zaki yi amfani dasu,hand and feet lotion nasan kin san amfanin su,ga set na ANACONDAR HAIR KIT akwai relaxer, shampoo ,conditioner and hair cream.idan mun koma zamu tafi SALOON d'in da nake zuwa a maki gyaran kai na musamman,ga takalma nan dasu za muyi amfani.
Hawayen farin ciki ne ya wanke fuskan farida tana istigfari cikin zuciyarta domin zargin da tayi wa Fatima ba gaskiya bane,ashe saboda ita tayi wanan hidima baiwar Allah ciki Dubu ɗari da aka basu takalmin 7k kawai ta saya wa kanta.
Share mata hawaye ta shiga yi,common stop it,bana son ganin hawayen ki komi na maki nayi ne saboda Allah saboda soyayyar dake a tsakanin mu"plz no more tears".
Nodding tayi "ki yafe mun Fatima wallahi na zarge ki akan cin amanata...
Shiiiii!,ya isa haka nan komi ya wuce yanzu dai kiyi magana da shi mun gaji ba zamu fita ba sai Allah ya kai mu gobe,abinci ko nan ciki za muyi order.
Waya ta daga ta kira shi,ashe ma har ya fita abun shi.
Har kun shirya ne in dawo?
"A'a ba zamu fita ba a gajiye muke,take Your time".
Akwai wani abu da kuke buƙata ne?
Sai dai zuwa anjima yanzu a koshe muke.
Kallo Fatima take Binta dashi ganin yadda take yatsina fuska da take waya"oh farida idan baki son mutum ya shiga uku a duniya wanan yatsina haka?"
Uhmmm bari ke dai Fatima Allah ko Muryar bawan Allah nan bana son ji!
Yanzu dai barin kira mummy kafun wanan munafukan FAMILY namu su kira ta.
Number tayi dialing Yana ta ringing bata ɗaya ba,ta kira na anisa (younger sister ta)har ya kusa katsewa ta daga"hello aunty teemo ya skt?
LAFIYA,ina mummy?
Tana d'akin Daddy.
Ok idan ta fito kice ta kira ni cuz muna kasuwa da farida ba zan samu zuwa wurin walimar ba naga har lokaci yayi kuma bamu kamala abinda muke yi ba....
Gata nan ma ta fito"mummy ga aunty teemo a ways",hello Fatima bana son rainin wayau fa ina kuma shige auntie's naku sai kira suke tunda kika shiga gidan kuja fita ba'a sake ganin ku ba har sun wuce wurin walima!
Calm down mummy,Dama nasan sai anyi munafurci na,kawai gidan friend din farida muka tafi daga nan muka shiga kasuwa,kuma Ni bayan koma gidan nan ba ko wurin bacci babu mutane sun yi yawa zamu kwana wurin friend din farida...
Ya maku kyau dama duk abinda zaki ja mun zagi da cin mutumci a wurin dangin baban mu shi kike da burin yi Allah baki Sa'a.kut ta kashe wayar.
Tsaki taja,sai me a mutu har liman.
Keeee Fatima bana son Rashin kunya kawai ki tashi mu tafi wurin walima daga nan mu koma gidan...
Wallahi babu inda zamu domin babu wacce nake tsoro ko shakka a cikin su har mummyn.
Farida riƙe da baki tana mamakin tsaurin ido da rashin tsoro irin na Fatima.
Farida ki sauraren Ni da kyau zan baki labarin rayuwa ta domin ya zama darasi da iznah a gare ki,kuma nasan idan kika saurarar zaki gane manufata na yin duk wani abu da nake yi a yanzu.
*WACECE FATIMA?*
_ALHAJI MAHMUD SHARIF DA HAJIYA MARYAM MAHMUD SHARIF (DADDY DA MUMMY)BA SUNE IYAYEN FATIMA BA_
Cikin kaɗuwa da tashin hankali farida ta kalle ta!
Yes
Fatima A Ladan haifafiyar garin ZURU ce ƙaramar hukumar jahar kebbi,mahaifina teacher ne a (government day secondary School zuru),mahaifiyata asalin yar fakai,mahuta ce bata yi karatun boko ba.
Mu hudu iyayena suka haifa; Ni Fatima nice babba,faiza,zainab sai Kabir).mun taso cikin rufin asiri da kulawa inda nayi karatu na primary a cikin zuru daga nan na tafi government girls comprehensive secondary School aleru Ina jss 2 Allah ya yiwa mahaifiyar mu rasuwa wurin haihuwar kabir wanda ba ƙaramin tashin hankali muka shiga musamman ni da nake da wayau kuma nice babba saboda faiza da zainab primary schl suke a lokacin"mun ci kuka sosai daga baya na bar wa Allah komi aka tarkata Ni na koma makaranta,lokacin aka damk'a Kabir a hannun kanuwar maman mu ta shayar da shi.
A kwana a tashi har mama ta shekara da rasuwa baban mu bashi da niyyar ƙara aure kawai aka sa nashi idanu,duk wani kulawa da uwa zata ba yaranta yana ba su faiza har girki yake masu.
Cikin ikon Allah nonon gwaggo Asiya ya amshi kabir yayi kiba abun shi lokacin ya shekara da watani bakwai ta yaye shi,duk weekend sai baban mu ya kai su faiza family house d'in su mama su yi kwana biyu a dawo dasu har aka shekara biyu lokacin ina ss1 su faiza sun shiga secondary ciwon ajali ya taso wa baban mu,sosai yayi jinya har rai yayi halin sa.
Tun daga lokacin muka shiga maraici na gaskiya saboda kowa yasan ba wani abu baban mu ya mutu ya bari ba sai gidan da muke ciki wanda na gwamnati ne nan aka tara mu tsakanin dangin uwa dana uba za'a raba domin a tallafi rayuwar mu;Ni da faiza aka damk'a rik'on mu hanun Alhaji Mahmud wanda shine elder brother na baban mu,lokacin yana aiki da"ministry for agriculture and rural development birnin kebbi",zainab da Kabir aka bar su nan zuru wurin aunty rukkayah(wacce ta shekara goma da aure amma Allah bai bata haihuwa ba kuma mijinta hamshaqin attajiri ne a cikin zuru),sai dai kash bata da hali,muguwa ce ta buga wa a jarida.
Haka taro ya watse muka rabu muna kuka aka wuto damu kebbi lokacin daddy yaran shi biyu(Abdul Rahman da Anisa) a lokacin yana zama a legislative Quarters ne,da yake mun saba da matar shi bamu wani sha wahalar zama da ita ba hutu na ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 12