Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gida a cetar wa ta cire hannun ta a dukan abinda ya shafe Ni daga yau! ZAINAB ce ta ci gaba da kwantar mun da hankali har doctor ya shigo ward round, faɗa sosai yayi saboda babu wani improvement ko break fast ban Yi ba Kuma magunguna da allurai yake so a mun na yau. Babu mai waya a cikin mu,zainab na kokarin komawa gida tayi magana daddy,faiza,aunty Salma,inna rabi suka iso da breakfast,,Nan take aka zuba mun da kyar na iya shan team saboda zuciyata zugi take mun,bakina kamar madaci bana jin daɗin komi,bana son ganin kowa nafi kaunar mutuwa ta da wanan hali da nake ciki! Sannu kowa ya shiga mun ana ƙara kwantar mun da hankali har na samu bacci. Ashe mummy na komawa gida ta fashe da kuka a gaban kowa ta bada labarin fasa aure na da doctor yayi da kuma wai irin cin mutunci dana mata a Hospital daga taimako na da tayi niyyar yi,,daddy ya fito rai a ɓace ya wanka mata mari sabida ba haka suka yi da ita ba a jiya,itace ta bada shawara kada a faɗa ma kowa a nemi Alhaji tanimu tunda ya jima yana sona daddy bai bashi fuska ba,shine yanzu tazo tana tonon asiri a cikin mutane har kawaye na kowa yaji abinda ya faru,wasu na tausaya mun wasu kuma daɗi suka ji domin ganin yadda na samu ɗaukaka a dare ɗaya. Abinda yasa daddy basu iso wurin aiki da wuri ba gidan Alhaji tanimu ya biya ya bashi check din shi kuma da ban hakuri ba za'a daura auren dashi ba saboda na nuna bana so,shi kuma ba zai tauye Ni ba,wayar shi yaba UNCLE Ansar a tura text ma duk contact na shi babu maganar daurin auren da za'a yi a gidan shi yau. Yan buki duk sun watse sai yan uwa na jiki sosai suka rage,dama ita faiza tazo gaba ɗaya ne sai ta haihu already wayar haihuwar ta ya tsaya,haka nayita jinya mutane na tururuwa zuwa duba Ni,wasu gulma ke kawo su har nayi sati Daya cur.mumny bata sake leko Hospital ba Wai tana fushi! ZAINAB ma an barta ta ƙara sati Daya a wuri na saboda hutu suke yi,cikin ikon Allah yan uwana biyu ke ɗebe mun kewa,amma fa idan na kebe nakan sha kuka mai isata,nayi nadama sosai mara amfani farida idan kika ganni nayi laushi sosai,daga ibada sai hira da yan uwana ko ina Bama zuwa har zainab ta koma Lagos. Na cire duka layukan wayoyi na nayi flooshing nasu,yanzu bana d anumber ko wane CORPER ko kawa! Haka mummy Bata shiga tsabgata kowa zaman kanshi yake,tayi harkar ta,nayi nawa idan kaga gidana da wani a gidan sai yaranta da faiza sister ta. Wata rana Samuel yazo har gida ya aiko mai gadi a kira Ni kama a faɗa mun shine,hijab na saka na same shi a harabar gidan mu wanda rabo na ta fitowa wurin tun ranar da zainab zata koma muka rako ta wurin mota. Bayan mun gaisa yake sanar dani wai yan fashi sun shiga gidan philo sun yashe komi yanzu haka tana Hospital sun sare ta a hannu da ƙafa data hana su key na mota na! Tausayi ta bani sosai,nace idan ya tafi ya gaishe ta domin yanzu bana zuwa ko ina kuma na yanke alaƙa ta da kowa ce kawa musamman ita data kai ni ga halaka,kaya da aka ɗauke nawa da mota na yafe;kawai na shige gida abuna. Sosai na tauye kaina,na koma tsohuwar karfi da yaji,bana kwalliya ko wani ado domin banga amfanin haka ba faiza ke tursasa Ni wani lokaci domin a cewar ta bata da wani buri daya wuce taga Allah ya kawo mun miji na gari nayi aure na bar gidan mummy! Mijinta na kiran ta sosai suna waya kuma yan uwan shi na zuwa duba ta akai akai har nakuda ta taso mata muka nufi Hospital kwana ɗaya da yini ɗaya tayi tana abu daya kasancewar haihuwar farko ce,Allah ya taimaka ta haihu da dare aka samu Baby boy mai kyau dashi amma ɗan karami duk girman cikin ta!. Awanni huɗu tayi a Federal medical center aka sallamo mu zuwa gida Wanda daddy ya saka an mata wani extra room and palour na. Zata zauna. Ganin mummy na wani cika tana batse wa yasa ya kira kaka a waya a ɗauko ta itace zata kula da faiza tunda tana da saurin ƙarfin ta,kuma a ranar hajia Turai(mummyn Faisal) ta aiko da motan daukar kaya ɗaya da itace na wankan mai jego,gero buhu uku,shinkafa uku da saniya ɗaya na barka. Mummy na ganin harkar arziki ta washe baki tare da sakin jiki ta shiga jama'a ana gudanar da komi da ita. Kaka na isowa ta wanke yaro da uwar shi yasa aka ci gaba da kula dasu abubuwan arziki zai faruwa yake har uban yaro ya iso cike da zumudi. Ana gobe suna aka kawo raguna manya biyu,set na kayan baby,faiza ma set aka mata na kayan fitar suna;mai girma minister ya Bata kyautar mota karamar mai kyau tukuici saboda Faisal ya mashi takara za'a rinƙa kiran yaron da Nawaz. Sai da faiza ta nuna ɓaci ranta sanan naci kwalliya cikin kayan da daddyn yamun na fitar buki muka fito shar kamar yan biyu. Anyi shagali sosai cikin kawaye na Habibah kawai tazo,itama ban gayace ta ba gulmar ta ya kawo ta domin tunda abun ya faru ta ɗauke ƙafa a gidan mu sai yau. Ban wani nuna mata komi ba na saki jiki da ita akayi shagali kowa ya watse. A kwana a tashi babu wuya wurin Ubangiji faiza tayi watanni biyu cur a gida wanda aka fara shirye shiryen komawar ta Abuja tare da mai rainon baby Nawaz,saboda Faisal na Tanzania. Cikin yan rakiya har dani saboda ban taɓa zuwa ba. Kwana biyu muka yi a Abuja gida kam barakallah komi yaji,shawarwari sosai na bata akan yadda zata kula da kanta da mijinta ba wai don ta haihu ta saki jiki dukan wani kulawa da tattalin ta ya koma kan baby kaɗai ba,yanzu ne zata ƙara tighting belt nata wurin ba Faisal kulawa na musamman fiye da lokacin farko saboda ɗan zuwa da yake yi gida lokcin data haihu na lura dashi mutum ne wayayya mai son a kula dashi,ita kuma faiza matsalar ta kunya da rashin mayar da hankali akan ABUBUWAN da yake so. Koda muka dawo gida babu abinda ya canza a zamana da mummy kowa ta kanshi yake,na zauna nayi nazarin rayuwa sosai naga zaman haka ba zai fishe Ni ba,doctor ya manta da wata Fatima a rayuwar shi,nima ya kamata in manta da komi in fuskanci rayuwa domin akwai abubuwa da dama a gabada. Kawai na yi ƙarfin hali na cire komi a zuciyata da taimakon Allah na canza layukan wayoyi na,bani da wani aiki daga ibada sai karance karancen littafai da neman ilimin zaman duniya a yanar gizo har result din mu ya fito wanda ban samu matsalar komi ba na amso statement of result na kawo ma daddy. Farin ciki sosai yayi da sanya mun albarka lokcin ya fara fafutukar nema mun aiki ban sani ba,,cikin ikon Allah na samu aiki a birnin Kebbi local gv wanda tunda nayi reporting ban sake zuwa ba kuma babu wanda ya takura min sai na tafi. Albashi na nafarko na raba ma yan uwa duka har na nesa na tura masu catin waya,mummy na saya mata wani dankareren lace Mai Kyau da tsada ai kuwa ta washe baki tana godiya. Watanni uku da samun aiki ban taɓa zuwa ba lura da haka da head of department dina yayi yasa aka mun transfer zuwa wurin aikin ku farida,wanan shine takaitaccen tarihin rayuwata. Hawaye Masu zafi Farida ta share,lallai fatima kin tafka babban kuskure a rayuwa,kuma Kinga jarabawar rayuwa sai fatan Allahu ya yafe maki Kuma ya tsare gaba. Amma zan tambaye ki mana! Murmushi Fatima tayi, faɗi duk abinda ke cikin zuciyar ki inada amsar tambayar ki aminiyata. Gyara zama farida tayi;bayan duka abubuwan nan da suka faru samarin ki na baya sun dawo gare ki?,kin sake samun labarin doctor Nadeem?,ITA Kuma Philo ya ta kare da rayuwar ta?,sanan yaya akayi kika ci gaba da sauraren samari???? Dariya sosai Fatima tayi,dama nasan sai kin mun wanan tambaya;idan baki manta ba ai na faɗa maki cikin su babu wanda na taɓa bari yasan gidan da nake,illa appointment nake Basu muna haɗu wa wani joint ko restaurant haka and na cire duka layukan wayoyi na Kinga babu ta hanyar da zasu sake Ni! Nadeem!,Nadeem!!, Nadeem!!!,,,Koda wasa ban sake samun labarin shi ba har yau saboda ban san kowa nashi ba,kuma ya koma Jos da aiki! Philomina (NOKIA connecting people),poor her,yanke ƙafan ta ɗaya akayi wanda tasha jinya sosai har komi data tanada ya kare,samuel na ganin haka ya sanar da yan uwanta ya ƙara gaba domin duniya yanzu sai kana dashi za'a yi da kai,idan babu ka zama hoto!,yanzu haka wai yadda nau'i labari shagon SALOON wani tsohon saurayin ta ya buɗe mata a zuru amma ba maganar aure tunda ta gama lalata kanta a bariki irin su ba ko wane namiji ke iya auren ta ba. Samari ko ince CORPER'S(yan bautar mata)kamar yadda nayi make yiwa mazan wanan zamani lakabi,bani ce na koma hulɗa dasu ba,farida sune suka kasa haɗe miyan su,suka kasa riƙe kwadayin su ko wane saurayi,yaro da tsoho a wanan zamani burin shi ya aikata zina da budurwa,bazawara har matan aure! Wanan mummunar dabi'a ya zama ruwan dare,shine dalilin da yasa na ɗauki alwashin sai na zame masu karfen gada,zan koya masu hankali ta yadda basu tunani!,,farida na ɗauki alwashin kafin namiji na yaudare Ni,sai na yaudare shi,kafin namiji yaci amana ta sai naci amanar shi,kafin namiji Ya tona mun asiri sai na tona asirin shi a bainar duniya,kafin namiji ya ci mutunci na sai na cinye nashi mutuncin kaf Farida wanan dalili yasa na faɗa wanan rayuwa na amsar abun hanun namiji babu tausayi,ba gudu kuma ba jada baya har sai Allah ya kawo wanda zai soni da gaskiya kuma da niyyar aure na! *🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊 _{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_ 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *CORPER* _{Ɗan bautar mata}_ 🌷🌷🌷🌷🌷🌷 🌸🌸🌸🌸🌸🌸 _~A Romantic Love Story~_ *BY* *L££MA* *DEDICATED TO MEELAT AND HUBBEEY* *All right reserved unauthorized copying, changing and translation of any part of this story in any form is prohibited.* ♥♥♫♪Happy Birthday to you ♪♫•*¨*•.¸¸♥¸¸.•*¨*•♫♪ Happy Birthday to you ♪♫•*¨*•.¸¸♥ ¸¸.•*¨*•♫♪ Happy Birthday !!!!! ♪♫•*¨*•.¸¸♥ ¸¸.•*¨*•♫♪ Happy Birthday to you! ♪♫•*¨*•.¸¸♥🎂🎂🎂🎉🎊🎄🎐🎁 *_HAPPY BIRTHDAY MUMMYN MUFEEDAH_* *🅿 SIXTEEN* Fatima na rasa wanan irin jaraba na mazan wanan zamani, musamman mazan aure burin su dai su aikata zinah,wani ma har mata uku zuwa huɗu ya aje a gida amma basu ishe shi ba,ko menene aibin matan su na gida? Farida kenan,wani lokaci da laifin matan gida sai kiga mace bata san ta kula da hakkin aure ba,babu tsafta,iya kwalliya,hirar soyayya,girki,ladabi da biyayya! Wani lokaci kuma babu abinda macen gida ke raga mijinta dashi amma idanun shi bai taɓa tsayawa wuri ɗaya,baya appreciating efforts na matan gida. Uhmmmm,Allah yasa mufi karfin zukatan mu Amin! Tadda sallar asuba yasa ko wacce ta mike suka shige toilet domin dauro alwala su gabatar da sallah,bayan sun idan ne suka samu bacci da basu yi ba a daren jiya. Karfe goma na safe kiran mummy ya tashi Fatima daga dogon baccin da suke yi"hello mummy ya koka tashi?" Ban sani ba Fatima,wai menene yasa bakya jin magana?,jiya baku leƙa wurin walima ba,yau gashi har an fara shirye shiryen daurin aure ba'a gan ku ba! Mummy don Allah ki daina biye wa tsegumin mutane mana,daurin auren nan sai karfe biyu za'a yi ta daga nan a wuce wurin SWORD CROSSING CEREMONY.... Koma dai menene ya kamata Ku shiga cikin mutane ko wani aikin ne ku kama. Shike nan mummy yanzu zamu fita,,,ok ki gaida mun da farida ta kashe. Tsaki taja, Allah yasan bacci bai isheni ba,wallahi idan na isa sai na ci mutuncin ko wace munafukar mata dake kai gulmata wurin mummy,wanka ta faɗa. Ta ɗauki lokaci mai tsayi kafun ta fito dai dai farida ta tashi,tana zaune gefen gado"er fara har kin tashi?" Uhmmmm, Fatima ya gajiya?,,namu ne duka ki shirya yanzu muyi break fast sai mu isa gidan bukin mummy ta Kira ana jiran mu. Towel ta ɗaura ta faɗa toilet sharp Sharp tayi wanka ta fito suka shiga tsara kwalliya da kayan da suka sayo a kasuwa jiya,Fatima uwar iya make up ta kashe lokaci sosai ta watsa ma farida light make up,ITA ko ta shiga fuskar ta da heavy make up. Text ya shigo wayar farida,kamar haka;- _Barka da asuba gimbiya farry,ya ƙarfin jikin da fatan kin samu lafiya?,me kuke buƙata na break fast?_ Tsaki taja wanda ya dawo da hankalin Fatima wurin ta,lafiya dai? Text ɗin ta nuna mata,murmushi ta saki tare da amsar wayar ta mashi reply. Ba'a fi mintuna talatin ba kiran Alhaji CORPER ya shigo wayar farko da,,ta wani kashe murya cike da shagwaba"morning baby na,ok Ina zuwa". Duguwar rigar material pitch wanda suka yi anko ta zura a gagauce,ta yafa ƙaramin Veil sky blue,Fatima dai na kallon ikon Allah. Jamlock ta murɗa ya buɗe,ta wani toge jikin kofar tare da langwabe kai gefe ɗaya tana kashe mai idanu"ranka ya dade da girman kojerar ka". Tare dake gimbiya,wanan irin kwalliya haka kamar mai zuwa gasar sarauniyar kyau? Fari tayi da dara darar idanun ta,saboda kai akayi ko bai yi bane a canza wata? Wane mutum,dole zan biya tukuici mai tsoka idan mun fita"yana magana yana wani shafa gefen fuskarta",kawar da zancen tayi...,har ka fita ne? Ba dole ba gimbiya na bukatar abun kari dole a nemo ko a ina ne,ya miko manyan ledodi guda biyu. Godiya muke ran goga na farida ya dade,,, ƙara washe shegen bakin nan yayi shi yasa nake mugun son ki saboda iya tsara kalamai masu ratsa zuciya,wallahi tallahi da ace dake na fara haɗuwa da bazai auri waccan guzumar bakauyar ta gida ba,wacce babu abinda ta iya sai ci daukar ciki da haihuwar yara mata duk shekara!! Nan take gaban farida ya fadi,domin ta tsani namiji mai aibata matar shi ta gida"yanzu dai ka yi breakfast ko sai nazo nayi feeding naka,bayan an gama in wanke ka tas kamar sabon jariri"! Wuhohoooo, daɗi kashe shi! Kugunta ya rik'o da hanun shi na hagu yana kokarin haɗe jikin su wuri ɗaya wata dibara ta fado mata"na'am Fatima gani nan shigowa mana". Saurin sakinta yayi,yanzu dai zan shirya naga har kun shirya karfe nawa zamu fita? A shirye muke daka gama ka sanar damu kawai. Juyawa yayi zai tafi nashi d'akin ya ɗan waigo suka haɗa ido,nan take ta kashe ido ɗaya tare da yin kiss ta hura mai ta shige d'aki...,mutuwar tsaye yayi a wurin kawai. Tana shiga fatima ta fashe da wani irin dariyar mugunta.....,lallai farida ashe Juliet CE ke ban sani ba?,dole zan fara ɗaukar darasi wurin ki wannan irin kashe murya haka,ai sai Alhaji ya banka wa uwar gida saki goma bai san yayi ba! Tafawa suka yi,bari kedai Fatima wallahi bana son mutumin nan, Allah ya sani wani irin haushi yake bani amma duk ya wani nace mun kamar tare aka haife mu,,wani tunani nayi kawai shi yasa na canja ra'ayi naga gwara na daina wulakanta shi tunda na lura wawa ne ko a cikin CORPER'S he's not qualify Amma ya naci sai yayi service! Abinda nake ta so ki gane kenan farida,wallahi bakar magana,zagi ko cin mutunci ba zai taɓa sa namiji ya rabu da nacin sonki ba , musamman irin su wa yanda basu da wani buri da ya wuce su aikata zinah dake da kuma wanan bukata tasu ta biya wallahi zaki neme su ki rasa ne"gwara ki nuna mai kin fishi zama yar bariki kuma.kin fishi bukatar zinar a lokacin zai buɗe bakin aljihu shi da kyau yana maku barin nairaro kina adanawa har ranar da zaki zame shi daga jikin ki a hankali ba tare da wanan buƙata tashi ta biya ba. Haka ne kam,suka janyo ledodi suka buɗe take away ne guda hudu,biyu na chips and a omlet,biyu na peppe soup din kaji ne,sai sandwich guda biyu da fresh milk gora biyu. Ko wacce ta buɗe wanda zata iya ci suka fara karyawa a natse har suka kammala sanan suka haɗa sauran kayan su duka a bag ɗaya,sauran kayan ciye ciye kuma a babban leda ɗaya. Fatima ta ƙara gyara masu make up d'in su sanan ta ɗaura ma farida dankali wanda ya zauna daram kamar an naɗa gwagwaro,itama ta ɗaura nata suka yafa mayafi a gefen kafada sai kamshi ke tashi. Text ya masu yana cikin mota yana jiran su idan sun kammala....,suka fito cike da ƙasaita kamar wasu matan shugaban ƙasa! A hanzarce ya fito ya buɗe booth ya saka kayan su tare da buɗe masu gidan baya suka kame ya ja motar sai da suka bar harabar hotel ɗin yayi karanci murya"gimbiya ina muka nufa?" Sai da ta ɗan basar ta amsa a takaice,gidan buki! Ko wace hankalin ta na kan waya suna chat har aka isa Quarters d'in dai dai kofar FLAT ɗin yayi parking a gurguje ya fito tare da buɗe masu mota,suka fito a yangance....,kayan za'a fito dasu ne? Bar su kawai kuma kana iya zuwa ka dawo don ba yanzu zamu sake fita ba sai zuwa karfe biyu"ta faɗa cikin jan hankali. Ko zamu koma can ne ki tayani bacci?,,,common kaga tun jiya baku sake leko wa ba dole zamu tsaya tare dasu har a daura aure. Shike nan ki kula da kanki,nasan idan mun koma gida zamu deme ma juna kewa. Sosai ma"ta bashi amsa",cikin mota ya koma yaja bayan sun ɗauki hand bag Kawai suka nufi steps na hawa flat d'in. Babban palour gidan cike yake da yan uwa da abokan arziki sai ciye ciye da shaye shaye ake yi,,nan take Fatima ta shiga gaisawa da yan uwan su,tana gabatar da farida a matsayin aminiyar ta kuma tare suka zo. Cikin sakin fuska aka gaisa daga nan suka shige Dakin yan mata wanda ko wace budurwa dake ji da kanta ta ɗauki wanka cikin shiga ta alfarma cikin ankon,kamshin su Fatima ya fara sanar da isowar su dakin sai kallo ya koma sama domin tun daga kan make up dake fuskar su,style na ankon su zuwa gwala-gwalai dake jikin su abun kallo ne,uwa uba wayoyin hanun su ga designer hand bag! Kuskus ya fara tashi tsakanin yan mata ,ko wace ba tambayar yar uwar ta su wanene wa yan nan yan mata masu aji,daga ina suka fito? Iklima cousin sister su Fatima ta fito kenan daga wanka tayi tsalle ta rungume Fatima"oyayo sister na sai yanzu wallahi nayi fushi ace tun jiya da kuka bar gidan nan ba'a sake ganin ku ba har wurin walima sai yan zu",,,sorry iklims kasuwa muka shiga basu samu fitowa da wuri vane. Rik'o hanun farida Tayi,yi hakuri bakuwar mu ga wurin zama"ta kwashe tarkacen dake saman wani curshin ta zaunar da farida sama",bari na samu maku abun taɓa wa ko? A'a mun gode sai da muka ya breakfast muka fito"cewar farida",,kai sister ko masa ai kwa ɗanɗana. Wai dole ne tace bata ci kije ki shirya mana....,kefa teema matsalar ki kenan zafin rai! Yan matan dakin dai ko wace idanu ta zuba masu sai santin haɗu War su take suna ji ina ma sune da wanan baiwar, wasu kuma hasada ke cin su saboda idan suka jera da wa yan nan yan mata dole tauraruwar su ta dakushe,, musamman ma Farida wace tafi Fatima kyau da tsari(ita Allah ya haɗa mata komi "kyaun fuska,surar jiki da dari duk da baka ce),Fatima kuma fara ce sosai,akwai boobs amma babu kyaun fuska. Tunda suka gama hayaniya da iklima basu sake magana cikin dakin ba duka hankalin su na kan wayoyin su har aka fara kiraye kirayen sallah,palour Fatima ta janyo Farida suka aje hand bag din su inda gwaggo Hadiza ke zaune saboda tsaro,nan ta nuna ma Farida wurin da zata dauro alwala...,bayan ta gama itama ta dauro suka gabatar da sallah tare da kyara kwalliya fuskar su. Suna cikin haka angwaye suka fara shigowa gida ya kaure da guda ana Masha Allah an ɗaura yau officer an zama babban mutum. Tare yake da sujoji birjik cikin kaki suna Bara masa baya har cikin palour,yana sanya da babban riga na shadda wagambari ruwan ƙasa sai shek'i yake,ga sauran abokan shi sun rufa masa baya cikin farar shadda da bakar hula sai kamshi ke tashi! Aje kayan kwalliya Fatima tayi tare da rungume dan uwan ta"congratulations my dear brother,may ALMIGHTY Allah bless your union"aka amsa da amin! Tattara kayan Farida tayi ta kayar cikin jakar su aka shiga daukar hotuna awayoyi da camera Wanda kusan ko wane suna ciki hakan ya ƙara hasala yan matan dake wurin. A gagauce aka kamala ɗaukar hotuna ango yace don Allah mummy ki shirya da wuri suna can suna jiran mu za'a fara ne,an tura motaci gidan amarya za'a wuce da ita can Barack ɗin,nima yanzu can zamu wuce mu shirya ,plz kuyi sauri saboda da zarar 2:30pm tayi za'a rufe gate sai na barrack din Wanda bai samu shigowa ba shike nan. Gwaggo Hadiza ta rike baki TAUUUU!,ai dole mu hanzarta gamu nan tafi sai ku bar motocin da zasu tafi damu a fara kwashe wa yan nan yan matan kafin mu gama Kimtsa gidan. Iklima ta kwala wa sauran yan matan kira"ku fito a fara kwasar mu motoci na waje",ruuuuuuu suka fito kamar ɗiyan awakai! Ta kalli inda muke zaune,ko ba zaku bane?,,Fatima ta yatsina fuska,muna da driver yanzu zai iso ya tafi damu. Ok zamu kira shi saboda bai san wuri ba kada a hana ku shiga. Ran sauran yan matan ya matukar ɓaci da jin wai za'a bata masu lokaci saboda jiran mu har wata mai kaurin wuya a cikin su ta fara yada habaici!! Ganin bamu tanka ba yasa suka fara fito zuwa cikin katuwar luxurious bus na barrack inda yan mata,yara da tsofaffi suka cika damm mu ake jira a wuce. Text Farida ta tura wa CORPER Alhaji shamsu suna jiran shi....,ya mata reply ai tunda ya dawo Masallaci yake waje yana jira! A yangance suke sauko wa daga steps din benen gidan har suka iso wurin motar ya fito da sauri ya buɗe masu gidan baya"ai kowa yan mata suka ƙara rude wa da irin matsayin mu! Horn yayi wa soja dake jan Bus din,alamar yayi gaba...ya tadda motar muka bisu a baya har Barrack d'in. Wurin kam ya kayatu sosai da sosai inda aka yi rumfar hudu(ɗaya yan uwan ango, ɗaya na amarya,ɗaya abokan ango da amarya, ɗaya kuma duk wani mai uniform Nan zai zauna),anyi indicating komi gwanin sha'awa,gefe ɗaya kuma abinci da abun sha ne kala kala saman dogon table! Ba'a fi mintuna goma da shigowar mu ba aka fara gabatar da bukin inda ango da amarya suka shigo yana sanye da uniform nashi na air Force,amarya cikin white gown,sauran abokan aikin shi na take masu baya ana busa har wurin zaman su. Bayan sun zauna aka gabatar da addu'a sai tarihin ango da amarya daga bakin manyan abokan su. Paret aka gabatar kala kala daga bisani aka shirya gabatar da SWARD CROSSING Inda aka umurci kawayen amarya da abokan ango su fito a jeru a bayan su,masu uniform suka jera layi biyu ko wanne riƙe da takobi suka daga sama tare da harde su wuri ɗaya,ta ciki amarya da ango da sauran mabiya bayan su ke shiga suna tafiya har suka kai ƙarshe sanan suka sauke hannu aka tafa,daga nan aka yi jawabi dai tare da ba ango wanan takobi suka yanka cake dashi aka fara refreshments tare da ɗaukar hotona lokacin anyi sallah La'asar. Tashi msuka yi ko wacce tayi sarving kanta idanu na kansu ko wanne namiji hankalin shi ya dauko har suka koma mazaunin su! Bayan ciye ciye da shaye shaye aka buɗe fili duk mai bukatar taka rawa ya fito,,nan wuce ya kaure masu rawa nayi,masu zuba kuɗi nayi. Sai a wurin Fatima taga daddyn su da sauran uncle's nasu,,a natse suka fito fili sai barin naira Yan ɗari biyu,biyu sababbi da CORPER ya basu ko wace bounch na dubu goma suka ta zuba kuɗin babu ji babu gani..... Nan M.C ya shiga watsa kirari,yana koda Kyan su da haɗuwar su,burin ko wane namiji a wurin ya su damar Zamfara dasu ko number wYa ya amsa amma babu fuska. Amarya dama mutuniyar Fatima ce ai kowa ta rik'o hanun ta dana angon ta suka shiga chashewa"Fatima gwanar rawa,an su abinda ake so",Farida kuɗi ta ci gaba da zuba masu fili ya watse aka barsu

Chapter 11 of 12