An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels Group
Hausa novels and fashion Group
Cool novel, makeup and kitchen1 Group
And
WOMEN24 TV Group
WHATSAPP NO:+2349030159301
[7/16, 6:39 AM] Hayat: *🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*CORPER*
_{Dan bautar mata}_
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
~_A Romantic love story_~
*BY*
*LEEMA*
*DEDICATED TO MEELAT & HUBBEEY*
*_All right reserved unauthorized copying, changing and translation of any part of this story in any form is prohibited._*
*🅿ONE.*
A natse take tako wa daga harabar gidan nasu ta doshi gate sai kare fuskar ta take yi da tafin hanun ta na hagu saboda ranar da ake kwala wa agarin, tana buɗe gate din wani wawan tsaki taja kasan cewa babu mota ko ɗaya a layin nasu,ta duba gabas da yamma,kudu da arewa bata ga kowa ba, musamman da yake weekend ne kowa na cikin gidan shi duba da yanayin anguwar nasu(G.R.A NEPA)babu hayaniya ko yawan mutane.
Ringing d'in da wayar hanun ta ya fara yi ne yasa ta koma jikin gate ta din ta jingina,hanun ta ɗaya riƙe da kugun ta tayi receiving call ɗin"HEY"shine abunda ta furta idanun ta a lumshe.
Daga ɗaya ɓangaren ya amsa"ranki ya daɗe gani na shigo area Amma ban gane gidan ba".
"House No 7" ta furta instantly tayi ending call d'in,a karo na biyu ta sake jan wani dogon tsaki alamar ta soma gajiya da tsayuwar.
Ba'a fi mintuna biyu ba wata ash colour Camry new model Tasha tink ta shigo layin,ɗan nesa da gidan akayi parking.
A karo na uku ta sake jan wani tsakin tare da ɗauke kanta daga kallon motar duk da ya tafi da imanin ta,gani da yayi bata da niyar ƙara sowa wurin motar yasa kawai ya yanke shawarar fitowa ya same ta,Bata ga zuwan shi ba sai maganar shi taji "ranki ya daɗe ya rana?"
Suna haɗa ido ko wanne ya kafe ɗan uwan shi da kallo zuciyoyin su na ayyana abubuwa da dama...
Wani irin tashin hankali ne kwance a fuskar ta,cikin zuciyarta tace"kan bala'i Wanan shine waje da kallo ciki da mamaki!
Shi kam yaba kyawun surarta yake yi ganin yadda jikinta ya matukar amsa doguwar rigar atamfa chiganvy pitch colour mai manyan patterns Yellow ta yane kanta da ƙaramin veil yellow,doguwa CE sosai ba za'a kirata ainihin fara ba domin jikinta irin karuwar jikin nan ne wanda ke riƙe dewa,wani lokaci ta koma jaja musamman idan ranta a b'ace yake,wani lokaci jikinta yafi fuskarta haske wanda ba shafe shafe bane haka Allah ya halicce.
Ba wani kyau fuska take dashi ba amma akwai structure komi yaji sai godiyar Allah.
Katse shirun tayi tare da ɗan rusunawa tana dube dube to make sure babu wani ɗan layin su da ya ganta tsaye dashi,at the same time ta yatsina fuska"ina wuni daddy....
Wani mugun dariya ya saki,farry baby yau kuma ni ne Daddy?
Shiru tayi mashi domin dogon surutu baya cikin dabi'ar ta"uhmmm" kawai tace.
Ya gyara tsayuwar suit nashi wanda botri yaki rufuwa saboda girman cikin shi,yau dai gani ga farry baby kyakkyawar yarinya wanda ganin ta a fili yafi ganin ta a hoto, am sorry for not coming on time as I promise,mun shiga meeting da wasu government officials ne a presidential Lodge akan issue na minimum wage Wanda har aka kammala bamu samu matsaya ba tunda governor bai samu halarta ba sanan anjima akwai dinner da matar Governor ta haɗa ma.....
Dafe kanta tayi cikin ɓacin rai taja tsaki "plz sir Are we hear to discuss political issues?"
Calm down farry I thought u feel offended that I keep u waiting (ya FAƊI cikin irin turanci mallam bahaushe)
Luk alhaji I don't owe you any explanation so let discuss something relevant to us.
Ok farry kamar yadda kika sani tunda kika yi accepting friend request nawa a facebook Allah ya jarabce Ni da son ki Wanda burina ki kasance uwar y'a y'a na....
Wani irin dariya ya kwace mata hada tafa hannu domin ita kam bata ga mijin aure a wurin ba cuz Nan da suke tsaye a matse take da ta koma cikin gida kada wani ya ganta dashi GP ta ya ragu.
Shima dariya yayi a nashi wautar maganar daɗi tayi mata,amm Daddy maganar aure ta wuce gaban wasa after all yau muka fara haɗuwa in person,Ina so ka bani lokaci in Yi shawara zan neme ka.
"Washe baki yayi,I will be glad idan kika amince da bukata ta ko million nawa ne zan iya kashe maki domin kuɗi ba Matsala ta bace.
A hankali ta ja tsaki,zan shiga daga ciki...
Da wuri haka?
Kayi hakuri kawai ka dawo wani lokaci idan nayi shawara ta juya abunta...
Ɗan tsaya mana farry a hanzarce ya isa wurin motar shi ya dauko wani kedar madaidaici mai ɗauke da tambarin *_SHA'ABAN SUPERMARKET_* tana tsaye tana kallon shi.
Ga wanan turaruka ne ba yawa da fatan zasu maki tunda ba sanin zaɓin ki nayi ba.
Hannu biyu tasa ta amsa tare da godiya ta shige gida yana tsaye yana kallon yadda waist d'in ta KE shaking.
Banko gate d'in tayi cike da jin zafin shi cuz ba abunda tayi expecting ta gani ba,har ta isa dakin aunty da salama ta faɗa saman bed tana furta"wash Allah na kwaso rana!
Cikin kulawa ta kalle ta "har ina kika tafi?"
"Aunty ai kin san banda wurin daya wuce bakin gate d'in gidan nan..."
"Naji kina kiran wash ne kamar wada ta Yi tafiyan ƙasa mai nisa."
"Ke dai aunty wani na haɗu dashi a facebook ya matsa sai yazo wuri na, shine fa yazo ya cika mutum da surutu.
"Uhmmm!,amma fa da dukan alama*CORPER* ne...
Katse ta tayi "yanzu farida ki rasa wanda zaki kula sai *CORPER?*
Ɗan bautar ƙasa wanda bashi da ko sisi sai turanci,mai na sama yaci bare yaba na ƙasa?
"Kaji aunty da wani zance ,ba *CORPER* dan bautar ƙasa ake nufi ba.
Idan kin ji budurwa tace *CORPER* ana nufin dan bautar mata!
Ki gane mana aunty wanan wani sabon lakabi ne da ake yiwa wawan namiji mara wayau."
"Su farida manya adon gari,nikam bara muga ledar ko akwai abun motsa baki a ciki."
Mika mata tayi ai kuwa ta zazage saman bed nan arabian performs suka zuba kusa kala biyar,sake baki aunty tayi cikin zaro idanu domin ko wane daga ciki kuɗin ta ya haura dubu biyar.
"Lallai Farida wanan babban *CORPER* ne, kin san kuɗin turarukar nan kuwa?"
"Ina ruwa na da kuɗin su Aunty kin ji bagidajen wai aure na yake so...."
"Ke me kaki ce dashi?"
"Tab ai banda bakin magana domin yayi jika Dani, aunty baki ganshi bane wallahi baƙi wulik,mumuna,da damammen fuskar duk farin gashi."
"Ai irin su sun fi daɗi aure farida wallahi zasu tarairaye ki fiye da tunanin ki saboda ga kuɗi ga soyayya."
"Kai dan Allah aunty wani SOYAYYA a wurin mutum da wani katon ciki, haƙora duk sun dafe sun yi ja sai uban surutun tsiya."
"Farida da sauran ki ashe,yanzu wa ya rage yana auren soyayya?"
"Ko wace mace burin ta a yanzu ta samu gidan kuɗi inda zata huta iyayen ta su huta."
"Over my death body aunty KE dai zaɓi turarai ki daukar wa mijin ki."
Ruwan ido aunty ta shiga yi domin ta rasa na ɗauka saboda tsadar su.
Dubawa ta shiga yi;HARAMAIN BUKHOOR OUDH BARAKAH, HARAMAIN BUKHOOR AL AROOSE,HARAMAIN BUKHOOR OYUNY,SOLITAIRE HARAMAIN BUKHOOR MARYAM,AMIR AL OUDH VIP MAI DEODORANT A CIKI.
"Ta kari ruwan idonta kawai ta zaɓi AMIR AL OUDH VIP da SOLITAIRE.
"Ci gaba suka yi da tattaunawa tana ƙara wayar mata da kai yadda zata samu ta wawuri rabonta a wurin shi cikin sauki har aka kira sallah ta kwashi tarkacen ta zuwa dakin ta.
Misalin ƙarfe takwas na dare suna zaune a palour ita da ihsan(diyar brother nata) suna kallo,aunty na d'aki da mijinta ringing na wayarta ya ishe su....
"Tsaki tana,ihsan ɗauki wayar kice nayi bacci.
Yarinya da ba zata wuce shekaru shidda ba ta latsa green a screen na wayar tare da yin salama,"hello aunty Farida tace ace tana bacci...
"Dariya ya saki kawai,ok kice masoyina ya Kira Yana missing d'in ta don Allah ta amsa wayar!
"Haramta kawai take kwada was ihsan Wanda tasan yau Allah kaɗai zai hana auntyn nata waska mata mari tunda ta kwafsa mata.
Bani waya ta wawuyar yarinya kawai!
"Kashe wa tayi gaba ɗaya suka ci gaba da kallo.
Washe gari ya kasance Monday da sun idar da sallah asuba basa komawa bacci ta shiga gyaran gidan aunty kuwa ta shirya ihsan ta haɗa masu breakfast.
" A hanzarce ta ɗan sha kunun alkama ta rik'o hanun ihsan suka yi sallama da aunty.
A daidai karshen layin su ta samu mai adaidaita wanda ya fara aje ihsan a"ALL BRIGHTER KID'S ACADEMY NURSERY AND PRIMARY SCHOOL,sanan ya wuce da ita BELLO WAY bakin wani babban building da naga an yi rubutu a sama kamar haka"AGENCY FOR MASS EDUCATION IN PROMOTING ADULT EDUCATION".
Bayan ta salami Mai adaidaita ta kama hanya zuwa cikin ma'aikatan a hankali tana gaisawa da mutane har ta isa department nasu wanda kusan kullum tana riga kowa zuwa saboda da wuri take fitowa bayan ta aje ihsan a school.
"Sunanta da lokacin da ta zo ta rubuta a staff REGISTER sanan tayi sign-in tana kokarin aje hand bag nata taji sallamar cleaner....
Da fara'a ta amsa"Barka da isowa innah"
Barka dai Farida ya mutanen gida?
Lafiya klau suke"tana kokarin fita ta bata wuri ta gyara, waiting area ta Koma tare da fito da wayarta tayi dialing wata number...
"Ar fara tawa" aka furta cikin Muryar bacci..
Katse ta tayi lallai ma ar fara har yanzu baki tashi daga bacci ba?
"Uhmmm ke dai wallahi kiran ki ya tada,ba dai har kin fita office ba?"
Me zan jira?,ta bata amsa
"Sannu da kokari yanzu zan shiga wanka kafin 8:30am na iso...
Kullum haka kike cewa yanzu sai kin ɗauki kusan awa biyu baki iso ba...
"Allah ba zan jima ba kin san yau Monday akwai ayyuka da dama a office.
Ok don Allah ki fito da wuri akwai labari..
"Don Allah!
Wallahi kuwa,ke dai sai kin iso,"tayi hanging call din"
Ta ɗan jima zaune a wurin tana latsa wayarta taji alamar tsayuwar mota" mrs arzika kenan"HEAD OF DEPARTMENT"na su ce ta iso da mutane biyu da take ba lift.
Gaisawa suka yi kamar kullum dai dai inah ta kamala gyara wurin suka shiga kowa yayi sign-in tare da nan wurin zaman shi.
"Mrs arzika ta aiko secretary nata da tarin takardu zuwa table din su farida,wanda ya kun shi aikin da wasu daga cikin staff din nasu suka yi monitoring a nearby community akan horar wa da ake bawa almajirai wurin koyar dasu lissafi a harshen turanci.
"Aikin tane ta shigar da report din zuwa babban head quarter nasu dake garin abuja through desk top computer.
"Tasan da ta tsaya jiran fatima"abokiyar aiki ta kuma babban Aminiyar ta"suyi aikin tare ba zasu gama shi a ranar ba saboda shiriri ta irin na Fatima,kwata kwata bata son aiki.
Cikin kwarewa wa ta haɗa komi ta fara aikin a gefen ta wayarta ne ke rera karatun Alqur'ani mai girma cikin suratul bak'ara.
"Fatima bata iso ba sai wurin karfe 9:00am cikin kwalliya mai ɗaukar hankali"
Gaisawa tayi da sauran abokan aikin su tayi wuce warta gefen su.
"Tun da Farida taji Muryar ta murmushi kawai ta saki tare da duba agogon dake makale a tsuntsayar hanunta ta kada kai tana ci gaba da aikin ta.
"Runguma taji ta baya,hajia ar fara sannu da aiki!
Banza tayi da ita tana ci gaba da aikin ta...
"Haba ar fara rawa in banda ke wake fushi da masoyin sa?
"Murmushi ta saki sai da haure Makkah ta na zinari ya bayyana"uhm su ar fara maman latti,bakya jin tsoro a samu bak'i daga head office baa same ki ba?
Tsaki taja, su suke bak'i Ni yar gida ce kuma regular customer...
"Uhmm Allah ya maki sauki,wait incharge ta ganki kuwa?
Tab Wallahi ban shiga office d'in ta haka kawai in Sha masifa tunda sanyin safiya idan ta fito ma gaisa....
"Fatima kiji tsoron Allah tana head of department ko arzikin gaisawa ba zata samu ba?
"Mtswwwww taja tsaki tare da jan kujerar ta zauna a gefen ta.
Tarin files ta jibge mata saman desk"gasu Nan ki shigar suna expecting report d'in a yau...
"Wallahi kada mu fara daga zuwa na,babu wani report da zan tura sai gobe saboda ayau ba fito da niyar yin aikin komi ba,daga nan ma zaki raka Ni gidan su beebah.
Tsame hanunta tayi daga aikin da take tare da dago Kai fuska dauke da mamaki.
"Wai ke Fatima wace irin lazy mace ce?"
Idan kin san ba zaki iya aikin nan ba tun farko me yasa kika nemi aiki?
"Heeee don't start!
Wata faɗa maki nice na nemi aikin gomnati?
"Wallahi ina kwance a gida cikin daki na Daddy ya kawo mun offer na aiki,wanda bani da niyyar yi don haka dole suyi hakuri da hali na.
"Uhmm banga laifin ki ba saboda daddyn ki commissioner ne shine yasa kike abinda kike so ki taka kowa don ranki,hatta head of department baki bari ba,wasu na can da qualification da yafi naki suna neman aikin nan amma basu samu ba.
"Bismillah mallam farida...
Kai baba Dan Bala miko min register Nan in rubuta attendance...
Farida aikinta taci gaba dayi har head if department d'in su ta leko...
"Fatima yaushe kika shigo?
Yatsina fuska tayi"mummy tun dazu,nazo na samu aiki shi yasa ban shigo mun gaisa ba...
"Dariya ta yi, kaji jan fata nunar rana,diyan masu gari fitowa nku na dabam ne.
Banza tayi mata tana kokarin kunna desktop computer nata ta shiga facebook,kullum aikin kenan chatting uploading pictures nata kala kala a social media,tana haɗuwa da manyan mutane daga garuruwa da dama suna zuba soyayya.
" Tun abun baya ba Farida sha'awa har aka koya mata salon cin kudin samari ta hanyar mai sauki through social media"A CEWAR FATIMA".
Farida aikinta take har ta kamala ta ake gefe,Fatima sai kwasan dariya take tana chat.
Can dai Farisa tace"miko sauran files din in taimaka maki ba Dan halin ki ba"
"Na kuwa gode ar fara tawa,Kinga Dama bango breakfast ba,Bata na Kira wani CORPER ya kawo mana wani abun ko?
"Farida tace har kin tuna mun dawani sugar daddy da muka haɗu a facebook kwana biyu da suka wuce ,jiya yazo har gida...
"Don Allah?,,Fatima ta katse ta.
Wallahi kuwa sai kin ganshi waje da kallo ciki da mamaki, kuɗi dai kam akwai su daga Kani amma fa tsoho ne sai muni...
"Dariya sosai Fatima tayi, ai kuwa kin yi babban Sa'a domin ko a CORPER irin su ne FIRST BATCH...
Suka tafa tare da tinstire wa da wata dariyar ...
Suna tsagaita wa Fatima tace,kada ki mashi riƙon wasa farida wallahi yagi rabon ki Allah ne ya baki domin irin su basu wadata na gida ba,matan waje ke ci.
"Uhmm ai naga alama domin turaruka daya kawo mun jiya kusan kala biyar,aunty ta ɗauki biyu,ga set ɗaya na wuto dashi naki ne.
Wani shewa Fatima ta saki tana duba sunan turaren domin ta san kuɗin su irin su mummyn su ke amfani dasu,masu tsada ne sosai.
"amma Fatima wani hanzarin ba gudu ba da maganar aure yazo,kuma wallahi bana son shi....
"Amma kina son kuɗin shi right?"
Nodding tayi!
Ar fara tawa kada ki samu damuwa zan baki course akan yadda zaki ci kudin duk wani dan iskan CORPER hankali kwance ba tare da koda ganin ki ya rike ba bare wani lalata ya shiga tsakanin ku ba don uban shi idan yaji wuya shi da kanshi zai nemi hanyar gudu wa lokacin kin ci shi har ƙashi.
"Uhmm Fatima kina ganin a zamanin nan akwai namiji da zai yadda ya sake Mali kuɗi ba tare da nemi wani abu a tare dake ba?
Sanin kanki ne samarin yanzu cikin 💯% dake zuwa wurin budurwa only 10%ke zuwa da niyyar aure,sauran duk yaudara ce da lalata ke kawo su.
"Ni zan baki wanna labari farida domin na fiki waye wa da hulda da manyan mutane,nasan a zama na dake kina mun kallon wata babban ar duniya wace idanun ta ya buɗe da kuɗi,ta saba da harka da maza.
Wallahi ko ɗaya ba haka bane hasali ma inada babban dalilin da yasa na tsunduma kai na a cikin irin wanan rayuwar,insha Allah zan samu lokaci in baki labari.
"Nannauyar ajiyar zuciya Farisa ta sauke,"gaskiya Fatima na daɗe ina zargin abubuwa da dama akan rayuwar ki,yadda kika san manyan mutane,kina abinda kike so,ga kuɗi ba matsalar ki bane....
Haka ne Farida saboda kwata kwata ba muyi wattani biyu cikakke da sanin juna ba,shi yasa baki san komi game da personal life Dina ba.
" Duk da mahaifina babba ne a garin nan kuma mai arziki ne soyayya hakan bai hana Ni son abun hanun maza ba wanda yana da nasaba da wani buri nawa na dabam da nake son cimma akan maza.
" a hankali Zan warware maki komi Wanda nasan Zaki fahimce Ni Kuma ki goya mun baya akan kuduri na".
Riko hanun ta tayi,shike nan zan jira har lokacin da kika Ni niyya ki sanar dani,ta ci gaba da aikin Fatima,ita kuma Fatima na chat har lokacin tashi yayi suka nufi Masallaci gefen mata suka gabatar da sallah.
Suna fitowa wata Range rubber spot fara ce Parker a gefe tana jiran su,ai kuwa suna isa wurin motar wani dattijo ya fito jiki na rawa"ranki ya daɗe Aminiyar mu ya aiki?
Cikin jin kunya farida tace alhamdulillah Alhaji,ita kam uwar gaya sai shan Kamshi take ya buɗe masu gidan baya suka shige ya ja mota.
Wasu maza dake zaune bakin ma'aikata suka ce lallai yaran nan na cikin lokacin su,Mallam sale ko ka gane wanda yazo daukan su?
Na gane shi mana babban dan kasuwa ne,kwana kin nan ya buɗe wani gidan shakatawa a hanyar bypass babba wanda duk garin nan babu irin shi.
Tsohon banza yanzu haka yayi jika dasu fa amma dubi yadda yake rawar ƙafa yara ƙanana sun mayar dashi driver. "mtswwwww suka ci gaba da tattaunawa akan alhajin.....
Sai da aka yau titin sosai ya tsaita front mirror dai dai fuskar fatima"Madam Barka da rana?
"A ciki ta amsa Barka dai.
Farida mamakin duniya ya cika mata zuciya domin tunda akayi posting Fatima a department din su Allah ya haɗa jinin su kasan cewa su biyu ne yan mata,sauran daga matan aure sai maxan aure da samari,kullum kwanan duniya samari kala kala ke kawo Fatima wurin aiki babban abun mamaki wanda ya kawo ta ba shi zai zo daukar ta ba kusan watan ta na biyu kenan a ma'aikatar nasu.
"A kullum da mamakin Fatima take kwana ko a ina take samo irin wanan manyan mutane masu kuɗi kuma tana wulakanta su,gata dai ba kyau ba sai farin fata ɗaya gyara ta amma akwai farin jini da iya sarrafa maza da bakin ta.
Duniyar tunani farida ta shiga ta yadda itama zata zage damtse ta yi amfani da daman ta a matsayin ta na budurwa a fantama da ita.
_masu karatu ku biyo NI a cikin wanan labari mai ɗauke da sabon salo domin jin yadda zata kaya tsakanin wa yan nan yan mata biyu da samarin zamani" shin sune da riba ko samrin??_
_HALIMATU SADIYA MUHAMMAD_
_~L££MA~_.
[7/16, 6:40 AM] Hayat: *🅱RILLIANT WRITER'S ASSOCIATION*🖊
_{Pens of freedom,home of exceptional and magnificent writer's}_
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*CORPER*
_{Ɗan bautar mata}_
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
_~A Romantic Love Story~_
*BY*
*L££MA*
*DEDICATED TO MEELAT AND HUBBEEY*
*All right reserved unauthorized copying, changing and translation of any part of this story in any form is prohibited.*
*🅿TWO*
Gida suka fara aje Farida tayi godiya,suka wuce abun su domin Fatima ba gida zata ba.
A palour ta samu aunty salma suna homework da ihsan.
"Barka da gida aunty?"
Barka dai farida, ya aikin?
Alhamdulillah har yanzu baban ihsan bai dawo ba?
"Eh wallahi kin san yanzu over time suke yi a wurin aiki sai 4:0pm".
Allah ya taimaka,"tayi jugum kamar mai nazari....
"Hawaye dake bin fuskar ta ya dauki hankalin aunty salma ta have hanunta zuwa bedroom.
Farida menene damuwar ki?,,da quruciyar ki zaki sama kanki wani ciwon?
Kuka ta fashe dashi,aunty Ina cikin matsakaici tashin hankali da damuwa!
Share mata hawaye tayi,Farida ke amana ce a wurin mu ba zan so ganin ki cikin ɓaci rai ba,ki sanar damu damuwar ki!
Aunty shike nan aure ya buwaye Ni?,ki duba tunda na kamala karatu duk wani namiji da zai zo wurina bada niyar aure yake zuwa ba sai yaudara da lalata!
"Kullum kwanan duba fa ƙara shekaru nike,kyawu na yana raguwa....
Shiiiiii!"ta katse ta,bana son Jin wanan maganar kwata kwata shekarun ki nawa farida?
"24years"
Shine kike damun kanki?,ki gode wa Allah U luk younger than your age ma,ga Yan mata nan birjik wanda suka yi shekarun ki biyo shiru babu mai so bare ya taya,amma ke kina samun masu zuwa wurin ki amma kina ɗaga hankalin ki!
Aunty dole zan daga hankali na musamman idan na tuna da mafarkin da nayi kwana ki akan abban mu,yana kuka yana roƙon gafara,yana sanar dani irin azabtar da shi da akeyi a kabari musamman lokacin al'adata saboda rashin aure da ban yi ba.
Jikinta sanyi yayi sosai domin sai da tayi tambaya akan mafarkin nan da Farida tayi aka nuna mata yana iya zama gaskiya domin Allah kan nuna ma bawa ishara a mafarki wanda hakan na iya kasancewa gaskiya musamman akan mamaci.
"Farida ki cire wanan magana a zuciyar ki,mafarki ne kawai ba komi ba,zan so kici gaba da rike mutuncin kan ki,kada ki yadda kwadayi da don abun duniya ya rufe maku idanu ki aikata sab'on Allah,rabon ka baya wuce ka haka aure lokaci ne kuma nufi ne na Allah.
Ajiyar zuciya ta sauke,shike nan aunty Nagode kuma zan kula.
"Zan so kiba wanan Alhajin dama idan Allah yasa kun
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 12