Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita kuwa matar jitakeyi kamar anabude jikinta iskar tana fita daga jikinta gakuma wani gurnane da takeji Wanda shiyafi komi daga mata hankalin andau awanni ana haka kafin daga baya komi ya lafa take barci mai nauyi yadauke su Dan dama bakaramin gigita sukayiba wannan kenan. Bayan sallah asuba Yusuf ya gama komi yashiga yayiwa kowa sallah ma ananne mom dinshi ta tureshi da tanbaya wai ina zakajene my son baka gaya minba mai yasa kacan zamin ne kwana biyu menene haka bakomi mom zamuje aikine nida Habib kwana hudu zamuyi ya juya zaifita, haba my son kasanfa bazan iya jute rashin ganinka ba har na kwana hudu, juyowa yayi yawa samata wani kallo Wanda said a tasha jikin jikinta kafin daga bisani yacigaba da tafiya abunshi mar mota Abu yarakashi itakuwa mom dinshi jitayi tafiyar bata gamshe taba amma sai kawai tabasar dan tasan Yusuf mutumme wada baya Karya aduk kan lamarinshi, sosai Abu yayi mai adduoi sannan yatafi zuwa gidan su Habib ya daukoshi suka dauki hangar garin suna zuwa wani address ananne suka kwana Sannan suka cigaba da tafiya har zuwa wani address din shine suka nemi wadda zaikaosu gidan malamin basu sha wahalaba wajen gidan malam musa yayi masu tarba ta musamman sannan suka huta sannan suka dauki hanyar zuwa tsangayar zakawanu bakaramin tafiya suka shaba wannan suka shigo garin gaba daya garin babu gidan bulo sai dai nakara da bukkoki suna shiga garin akafara kallansu dan tunda suke akauyen mota bata taba shigowa ba sai yau, abaki gidan suka yi parking suka fito tare da hamdalah sannan suka shiga bakin tsangayar suka zauna babban dalibinshine ashiru yashiga yasanar da malam sannan yace masu sukaraso bayan sun gaisa ya kalli malam Musa yace harda kai kenan eh malam dama malam Aminu Baki ne ya aikosu to shikenan bari akawo maku abinsha, bayan sungama kammala komi naciye ciye dama sunyi sallah insha to ahanya sannan Yusuf ya shiga rerawa malam bayani, malam ya jinjina lamarin sosai yace amma ayau da daddare kowa zai tuno da ita insha Allah, bayan sungama tattaunawa yace zaku iya zuwa kukanta malam Yusuf ga dakinan ya nuna masu daki shikuma malam Musa ya nuna masa nashi kowa yashige nashi, shikuwa banganen malam zakawano betaba jin lamarin daya fusata shi irin wannan ba amma zayyiwa wanan mata sassaucine saboda mahaifiyar Yusuf ce amma banda haka saiya nuna mata hankalin, daki yashiga ya kade buzunshi ya daura da alwalah sannan yayiwa mai dakinshi sallama yashige nashi dakin ya zauna kan buzunshi yafara aiki dama hausawa suna cewa 'bafada da malam ba dare: aikamdai yau ga malam ga boka saita Allah wannan kenan, yajima sosai yana aikin gaba daya yayi gumi dan rigar jikinshi tuni ta jike sosai, candai yasaki hamdalah tare da tashi dan zuwa dakinsu Yusuf aikuwa yana zuwa yaji Yusuf yana ta salloli ya tsagaita yace malam lafiya kuwa be bashi amsaba aka kirashi awaya Abu ne yagayawa malam yace dauki kaji mai zaicemaka, my son kasan inda Khadija take kuwa katunata son ina 'yanta Khadija Abu ka kwantar da hankalinka insha Allah Khadija tana hanyar gida kaji fashe mai da kuka yayi yace dan Allah Abu sai yayi shiru yakashe wayar take yan fada suka dinga shigowa dakin sarki suna tambayarshi Khadija amma yakasa gane komi suna haka sukaji amuryar tana magana mijin Khadija ne Auwal yace Abu ina Khadija Abu ina take ina cikin dake jikinta dan Allah Abu kamin sassauci wllh inasan matata Abu ya dagoshi yace kai zan tambaya Auwal ina 'yata shiru suka yi kowa nakallan kowa, kafin Abu yace muje zuwa dakin mamina Dan asan yadda za,ayi anazuwa akaganta abakin farfajiya tanata safa da marwa tana ganin Abu tace mai ina Khadija mami abinda nazu tanbayarki kenan to tabbas akwai gagarumar matsalah da shekara nawa mukayi batare da itaba mami ta fada, inalillahi wainna ilaihirraji,un tabbasa muna cikin damuwa da tashin hakanli mara misaltuwa amma akira malamai asasu sufara addua ko Allah ya kawo mana dauki sunjima sosai suna tattaunawa kafin daga bisani suyi sallah ma kowa yatafi neman mafitah adarendai babu wanda yayi cikakken barci kowa addua yaketayi hakama Yusuf da Habib basuyi barci ba sunata zuba adduoi da salloli wannan kenan, Bangaren Abu ko takan mom bebi ba wadda da baya iya awadaya batare da yasa ta,a idon sabah amma yau yama manta da lamarinta amma yau ko nemanta awajen kwanciya beba, ita kanta mamaki yabun yabata tace tabbas akwai gagarumar matsalah, kardai ace aikinta nashekara dashekarune yake kokarin warware wa dole tafita zuwa gobe dan bazata bar wanna gagarumar matsalabah hakadai barci yadauke dasake sake azuciyarta. Washe gari da safe bayan su Yusuf sun dawo daga masallaci malam ya zauna agabansu bayan sun gama karyawa yace tabbs Yusuf abinda zan fadamaka nasan bazai yimaka dadiba amma balaifina bane dole bayadda za,ayi sai mahifiyarka ta haukace kuma Mara warkewa amma da izuni Allah yau dinnan Khadija zata dawo cikin ahalinta dan yanzun nasaka manya aljanu suyi fada dana jikinta sukawomin ita amma bani zangantaba zaku dauki hanyar gidane yau da izunin Allah to fa ananne Allah zaiyi ikonshi ya hadaku da ita insha Allah, Yusuf yaji badadi sosai amma sai yace to malam Allah yayafe mana kurakuranta amin duk suka amsa dashi sosai sukayiwa malam alheri sannan suka dauki hanya amma Yusuf jiki ba kwari tagiya sukeyi cikin manyan dajuka masu duhuwa har dukazu garin su malam Musa suka ajeshi sannan gida sannan yayi masu fatan nasarah suka cigaba da tafiya, sosai dare ya tsalah tafiya sukeyi babu kakkautawa saboda suna cikin daji sosai sunata sheka gudu, Ita kuwa wannan barcin dasukayi sai yanzun suka tashi atare sai kowa yake kallan kowa Khadija ce tafara magana inane nan, ita kuma yarinya tace WACECENI, kallanta Khadija takeyi sosai kafin tace wa yarin yar waceceke, itakuwa bata gani komiba tayimata shiru Khadija takara da cewa inane wannan tashi tayi yafito yarinya nabiye da ita, aikuwa dataga inda suke take tasaka gudu yarin yar nabinta abaya gudu sukayi sosai Wanda subasu saniba bayin kansubane malam zakawanune yake umartarsu, sukuwa Yusuf tafiya suka farayi ahankali har suka I so wani waje ananne Habib yace Yusuf zamu kwana anan da asubah sai mucigaba da tafiya to kawai yace mashi danshi haryanzu yana cikin tashin hankali, sukuwa wata babbar hanya suka iso sunata gudu Wanda ko gabasu basa gani wani haskeni ya kashemasu idanu wanda basu ankaraba sai ji sukayi sunfadi kasa a gigice Yusuf ya dago yacewa Habib baka gani munbuge mutane Habib cikin tsoro yace Yusuf karmu tsaya adajinnan mugudu dan Allah aa Habib mufita kawai musa Allah aranmu kai kana tunanin akwai dan Adam airin wannan waje kai wllh Habib sai nafita, aikuwa sukasa kai suka fitan sukakarasa suka kunnan fitulun wayarsu bana mota aikuwa Yusuf ya kafesu da ido sukuwa Kansu nakasa yace sannu munbugeku bamusaniba cikin tsoru yake maganar basuke komiba harsuka kara magana, Khadija ta dago tace dan Allah kutaimaka mana jin muryarne yasa Yusuf hasketa tabbas idan ba gizu idanunshi suke mashiba wannan Khadija ce, kafin ya ambata Habib yarigashi da cewa Khadija ta dago kanta sosai tana kallanshi, take idanunta suka zuba da hawaye tace yaya Yusuf na,am Khadija aikuwa sunci kuka awajen kafin daga bisani sukashige mota anane yarinya tasakai zata shiga motar Khadija tace ina zakine wadannanfa 'yan uwanane,kallanta sukayi da ammaki Khadija wannan aikece ba 'yarkibace ni bansantaba, itakuwa yarinya bakinta ne yafurta WACECENI, Habib ne yabude mata gaba tashiga dama Yusuf Yakima baya tazauna sannan suka hautafiya bakama hannun yaru, sai dai gaba daya motar wari dauda takeyi saboda su dasuka shigo, har,asuba sannan suka shigo gari inda zasu dauki hanya garinsu annanne Habib yace sukama daki awani hotel haka kuwa akayi suka kaisu sukace suyiwanka suna zuwa kaitsaye boutique sukaje suka suyomasu kaya sannan suka kaimasu suka kawo masu abinci sannan suka yiwanka anasu dakin sannan suka fito sutafi suma sungama komi karkaso kaga yarin yar nan yadda wata abaya tayimata bala,in kyau amma ita takicin abincin ruwa kawai tasha sukazu suna jiransu anannune Yusuf yakalli kyakkyawar yarinyar nan gaskiya wannan Khadija ce zam dan hartafi Khadija haske, tagayamasu taking cin abinci gashi bata magana sai dai WACECENI kawai taiya fadi, sukajijina lamarin sannan suka dauki hanya gida, yarinya ta kwanta ajikin mota babu abinda yake damunta sai yinwa Khadija tafahimci hakan nandanan tausayinta yacikata ta dago ta kalli Yusuf race yaya Yusuf yinwa takejifa to me za,asemata komi ansiya takici kafan fruit to aikuwa suna rufe baki saiga masukayan fruit nan aikuwa akasiya mata masu yawa sosai aikuwa jiki narawa tafaraci harsaida sukatausayamata dama tanajin yinwa harhaka Khadija kuma tasaki hawaye, batasantaba amma tanajin tausayinta, sukan tsaya suyi sallah sannan sucigab da tafiya sannan kenan sunshigo unguwarsu yanzun suna gabda gida. Shikuwa Abu yauranshi a bace yashiga dakin mom yakai kanshi kenan yaji tana cewa nagaya maku bazan bar Khadija ta dawo gidannan ba tatafi kenan daga ita har abinda ke cikinta aibazan jure ganin wani akan dukiyar mijina ba, aikuwa take yadaki kofar saida tafadi kara ballalliya tana ganinshi kuwa takwashe da wata irin dariya kajiko eh hakane nice nakaika Khadija duniya ita da abinda kecikinta nakusa kuka manta da ita nanfa tafara zayyano bayanai kalakalah shikuwa Abu yakaimata wasu lafiyayyun Marika amma saiyaji ta fashe da dariya tace karamana harka gaji take tafara yage kayan jikinta tafadin kalolin sharrikan data aikata tayiwaje Ashe kowa yanajinsu duk abinda yake faruwa nanfa tafito gidan sarkin tsirarah tanata hauwa kowa sai kallanta yakeyi anahaka saiga motar Yusuf tashigo idanuwan Yusuf sukayi tozali da mahifiyarshi sosai yafashe da kuka yafita adaga motar tunbata tsayaba, take Habib yayi parking duk sukafito mom sunayi ido biyu da Khadija tayo kanta tace Khadija nina haukatakifa wannan babarkice Khadija kika haifeta saikuma tasa samata duk aikuwa akarirtiketa Yusuf yafadi kasa yafashe da kuka take akaje akagayawa Abu da mamki da kowa dukkan family din gidan sarkin kowa yafito, Abu yana zuwa ya rungume yarshi tare da fashe wa da kukan tausayinta mami ma hakan tayi kowama haka sannan akashiga gida annanne mijin Khadija yazu shima yaci kuka yana ganin yarinya yace wllh "wannan jininaice", aban angama komi anhuta, ananne Kadija tabasu labarin komi Wanda tasani amma banda labarin yarnan,malam zakawanu yana gida amma yana ganin komi yaturu wata aljana yace ta haukan Khadija tayi bayanin wannan yarin yar hanakan kuwa akayi ananne yarinya akace aringa kiranta da sunan kakarta wato Fatima zarah wannan kenan, saidai bata magana kuma bata gane komi dan haka malam zakawanu yaturo mata wata jinjirar aljana yace tadinga koyamata komi harzuwa randa zata iya saitbar jikinta, tofa annanne yarinya tafara magana dakuma cin abinci, Abu bakaramin so yakeyiwa zarah bah saboda sunan mamarsane, Yaketa godewa Yusuf tare da cewa kasa Wanda yakuma tunanin Yusuf badanshi baneba danshine nahar abadah, dakuma yafahimci Yusuf yanaran zarah take yace yabashi ita halak malam kuma za,ayi gagarumin biki alokacin zarah tana da shekaru sha hudu aduniya, Abu yacewa mijin Khadija sai dai yadawo gidan sarkin abasu waje indai yansan Khadija aikuwa ya amince saboda yanasan marshi wannan kenan. Wanine Yusuf ? Yusuf dane ga hajiya suwaiba wadda takasance aminiyar mahaifiyar Khadija to suna yara ba,ajin Kansu komi nasu daya Fatima mahaifiyar Khadija mahaifinta maikudina tare yakeyiwa Fatima komi da suwaiba sakamakon ita kadai ya Haifa aduniya kuma mahaifiyar ta tarasu, duk wanda yasan Fatima yasan suwaiba saboda Fatima tanasan suwaiba sosai zakumata iya mallakamata komi idan farincikin suwaiba ne, bayan sungirma sosai Allah yakawowa Fatima wani saurayi kyakkyawar waishi Abdallah Fatima tana masifar sanshi amma suwaiba batasanshi kullum suwaiba acikin kushe Abdallah take data gadai Fatima tayinisa shine ta janye jikinta daga Fatima, Fatima tadamu taje tanbayar ko lafiya ananne take gayamata itace wadda takesan Abdallah Fatima tashiga tashin hankali sosai saboda saura sati uku bikinsu amma yace bakomi suwaiba nabar maki shi zansameshi nayimai bayani, data koma gida tayi kukanta mai isarta sannan takira Abdallah tafadamai komi yaki yarda amma saboda san dayakewa Fatima yahakura, tafadawa mahaifinta shiya dayar yararda saura sati biyu biki Fatima taje wani waje siyayyar kayan bikin suwaiba taga wash motoci ludi market din nanefa akecemata yarima Sadiq ne yake suyan kayan akahanata shiga dakyardai akabarta saboda tana siyayya ashagon sosai tana shiga yana fitowa ananne yaji yakamu da San Fatima sosai take yasaka akarakashi gidansu yayi magana da mahifinata yanashi damar magana da ita aikuwa Fatima tana dawowa taga wannan motoci tayimamaki sosai bayan tashiga gida babanta yayimata bayaninkomi, aikuwa taje suka gaisa mutumne maisaukin kai Wanda bedau kanshi waniba take taji halayansa sunmata zuwa daya biyu yaturu da magana tansa aikayi maganarar aure nanfa akahade bikin dana suwaiba, ansha sha,ani sosai akakai kowacce gidanta, suna zumunci sosai amma abinda suwaiba bata saniba shine shi Abdallah ma mijin Fatima yake taimakamashi saboda bashida karfi anahaka suwaiba tasamu ciki harta haifin da namiji amma Fatima shiru bayan shekara takwas Fatima Allah ya azurtata da ciki zukaga murna gun Sadiq da kuma mahaifinahi danshima shikadai Allah yabawa mahifinshi, Fatima tasamu kulawa sosai har Allah yasauketa lafiya ta haifi yar mace akasamata sunan mamar sadiq wato Khadija amma tunda Fatima ta haihu shikenan batada lafiya waje akafita akace masu cancer ce da ita kuma nanda watanni zata iya mutuwa, bayansun dawone ananne yake cemasu Allah yayiwa Abdallah rasuwa, Fatima tayi kuka tayi kuka dan hartafi suwaiba damuwa, ita kuma tadauko dan Abdallah wato Yusuf tarikeshi da Amana batare da tsangwamaba lokacin Khadija tanada shekara biyu aduniya ciwan Fatima ya tsananta annane takira suwaiba face mata Dan Allah ta auri Sadiq da taki amincewa amma ta amince tace saboda nasan Khadija bazatayi maraicin uwaba zakiriketa da amana ga Yusuf Dan Allah kidena nunamai kiyayya ailefin mahifinshi banashi bane umma shima mahaifinshi bemaki komiba Dan Allah kigera suwaiba har kuka suwaiba tasha sannan tatafi, shikuwa Abu yana zuwa tafadamai komi bayyi musuba yace idan zaisaki farinciki na ,amince mace tagari bayan haka da sati biyu aka dauramasu aure sosai taji dadi abun, kwanansu biyu da auren Fatima ta rasu aikuwa Abu yashiga damuwa, bayan share makoki yafadawa mahaifinshi zaitafi kasar wajen shan iska kuma da Khadija zaitafi nanfa sarki ya hana saboda idan yatafi da Khadija bazai dawo garin da wuriba yauwa tafi, ananne suwaiba tafara ganawa Khadija azaba kalakala kwanciya akan tayal gakuma shafamata barkono ajiki gayarinya fara, watarana sarki yagani yako maidata wajen kakarta anane tasamu sawaba Yusuf yansan Khadija Sosai Dan bayasan damuwarta, itakuwa suwaiba take tayiwa Abu asiri yadawo gida sannan kuma bayajin maganar kowa sai tata, ahakane mahifinshi yarasu akamaidashi sarki nanma Takara samun damarynikomi harda rabashi da mahifiyarsa, shikuwama Yusuf yatafi kasar wajen karatu kafin yadawone akayiwa Khadija aure wannan dalilinne yasashi gamuwa daciwan zuciya saida akayimasa aiki yawarke yakuma hakura da Khadija wannan kenan. Abu ne yayiwa Habib babbar kyauta mai tsoka dan satinshi daya dadawowa akayi bikinshi kuma hargida yaje danyiwa iyayenshi godiya. Yaune bikin Yusuf da zarah sosai ake sha,ani, zarah tanasan Yusuf sosai dan yayi mata duk da kankantar shekarunta sosai ake kaita gurun manya manya malamai tama suna sanarda ita menene aure dakuma hakokinshi, biki yazagaye ko,ina afadin kasar harma da wajenta dan Abu BBC news yakai wan asanar da abokanshi nanesa kasan BBC badai cika alkawariba dakuma girmama costormas ba. Ansha biki akakai amarya gidanta dare dayin alkawari awajen zaikata dumin tayi karatu banda kuma kwararrun malaman addini dana boko daya dauko mata, yau satinsu daya da aure dan haka zasuji gida domin duba Abu dakuma mami da Khadija ahanyarsu tatafiya Yusuf ya hango mom dinshi abakin wata bolah sai cinkashi takeyi aikuwa ya tsaida motar yafito itama zarah tatake mashi suka fito yayiwajen bilar yana kiran mom cikin kuka tataso tayo inda yake aitana kusa zuwa wajen shi saitayi titi take wata mota tamaketa tataketa wata gigitacciyar kara yaji yana juyawa yaga wata katuwar motace ta maketa yayi daga daga Wanda bazaka iya tantamce maceceba ko namiji,Yusuf yakarasa wajen yadinga kuka yasa aka kwasheta akasamu likafani akatatare namanta aciki aka yayafa ruwa aka kaita makabarta wajen, Yusuf yayi mata addua taneman gafara sannan suka dauki hanya jiki asalube sukaje gidan Abu ananne suke gayamasa bace WACECENI

written by Fatima alaramma alaramma

Bismillahi,rahamanurrahim Book one

Yau ma kamar kullum, ahankali nafara bude idona dan ganin aina nake cikin nutsuwa nabude idona ban saukeshi ako inaba sai awata katuwar bishiya, danake kasanta wadda yawan reshanta yacika gaba da bayan ta cikin, dimaucewa nameke zaune tare dakafe wajen da idanuna, da jin Allah ne Wanda ba kowa kuma bakomai acikinshi face manyan duwatsu da kuma manya manyan bishiyu, tun danake bantaba ganin gigitaccen daji maiduhu irinshi ba take idanuna sukacika da hawaye na tausayin kaina, wannan wacce irin kaddara ce nake cikinta ni sabrah, tasha kuka sosai sannan tamike daga kasan bishiyar tafara tafiya ahankali gakuma tsoro dayake mamaye azuciyarta, ta kasan bishiyun takebi har tafita, kasan wannan bishiya tashiga wata, daidai wata katuwar bishiya ta tsaya chak sakamakon wani matsi da takejih acikin bishiyar nantake jikinta yahau tsuma cikinta yahau kugi gumi yafara ketumata tako'ina ta kuma kasa ko motsawah, ahankali taga gefen bishiyar dake gabanta wani katan kogo nabishiya ta kurawa wajen idanu dangani takeyi kamar daga cikin bishiyar motsin yake fitowa aikuwa cikin nutsuwa na hango wata matashiyar yarin ya tana fitowa daga kogon cikin tsoro take kallan yarin yar dan ganinake tamkar ba mutum bace dama za,asamu dan Adam awannan dajin gaskiya banyardaba, sosai nake kallan yarin yar har takarasa bakin wata bishiyar nan ma hankalina yakara tashi dan wata mata nagani azaune abakin wata bishiyar yarin yar nagani tatsugunna agaban matar ta dauki hannunta tana tayimata wani abun batajima tanayimata ba nagatamiki tabi wata bayan bishiya ahankali na karaso wajen matar dan ganewa idanuna abinda yake gani daga nesa, sai alokacin ne ma nafahimci matar makauni yace batagani dan harda sanda nagani agefenta, kallo daya zakayiwa matar kasan ba wani cikakken hankaline da itabah gashi kuma duk jikinta dau dace gakuma kanta da yayi kurah wannan kenan, da hanzari nabi bayan wannan yarin ya dana gani inata sauri inabin shatar kafarta harna kai bakin wani katan dutse na hangota zata shiga cikinshi dasauri nakuma binta har tashige kasan dutsen nikuwa ina kaiwa bakin dutsen zanshiga naga wani irin duhu Mara misaltuwa Wanda ko hannu baka iyagani take tsoro yamama yemin zuciya da kuma tuna nunnuka daban daban dasuka shiga zuciyata, amma sbd inasan sanin wacece wannan yarin ya dakuma waccen matar sai kawai wani kwarin gwiya yazumin sai kawai na saka kai na bita nayi tafiya mai nisan ba tare da nasan inda nakesa kaina ba ko kafata kafin daga bisani nafara gani haske kadan kadan, ahankali nafara kallan ko ina acikin dutsen ba komai acikishi sai wasu irin bishiyu masu ban tsoro, ahaka dai har na karaso bakin kogon ananne naga haske yamamaye ko ina sai kuma nafara ganin kyawawan bishiyu masu saka nishadi da farinciki na shagala da kallan bishiyun ne ban auneba naga yarin yar agabana tareda tarin kayan fruit ahan nun ta, take tsoru yacikani jiki na yadauki rawa marata tacika da fitsari saboda irin kallan da yarin yar take min itakuwa yarin yar kallanda takeyi saboda abin da yabata mamaki shine bata taba ganin halitta irin ta taba dama akwai mai irinsu aduniya dama basu kadaine suke rayuwa ba, ni kuma sai alokacin nake kallanta sosai yarin yace karama wadda bazata wuce shekara goma sha biyu ba amma kyakkyawar gaske ce tahadu tako ina duk da kan kantar shekarunta amma behana fito da kyau din taba sai dai babu wata suttura ajikinta saita ganyayakin bishiya Wanda susuka zamemata sutturah, ahankali ta kara matsowa inda nake tare da daga hannunta zata shafamin fuska nan ne hankalina ya dauke nakasa gane komi, itakuwa yarin ya kawai nemata tayi tasara dan wa'yanda suka kawoni sun dauke ni, ita kuwa yarin ya girgiza kai kawai tayi tacigaba da tafiya amma aranta lamarin yabata mamaki, to wacce wannan yarin ya? Kuma waccen matar? Meyasa bata gani? Menene ya kawo su wannan dajin? Shin mutanene su? Meyasa basa magana? Wane yake kawo sabrah dajin? Wane ya dauke ta? saboda me zai dauke ta? Dan amsa wadannan tan bayuyi kubiyuni kuji yadda zata kaya Ahankali taci gaba da tafiyar ta harta karaso bakin bishiyar wadda tazame musa tamkar daki tashiga bata jimaba tafito tare da wannan matar tariko hannunta ta kawota bakin bishiyar tazaunar da ita sannan ta koma dakin ta dauko wannan fruit din tasoma bata abaki tanaci cikin nutsuwa daga Baya can kawai wannan mata tafashe da kuka mai abin tausayi takuma taune harshenta take Jini yafara zuba sosai, yarin yar nagani ta zubamata idanu tana kallanta saboda idan da sabo tasaba ganin kullum idan tana bata abinci saitayi wannan kukan nan tsananin kukanne yasanya idanunta suka dena gani amman kullun idan yarin yarnan tatanbayeta dalilin bansabajin sai tace nimadin bansan maiyasa nake kukaba, kuma akoda yaushe yarin yar takan tanbayi wannan matar tace "wai wacceni"? Kuma kema "wacce awajena"? Amma amsar daya ce akullum nima bansaniba abinda matar take gayamata ke nan ,acikin kowanne karshen wata na ranar Friday hanka linta yakan iya dawowa jikinta har tayiwa yarin yar magana amma daga ranar ta wuce tofa shikenan babu magana sai dai sudinga yin magana ta hannayensu, sai da tayi mai isarta sannan tayijn shiru itakuwa yarin yar ta tashi ta dauko maganin da take sakawa matar tazo tabude bakinnata tasaka mata sannan ta mike takoma gefenta itama taci fruit sannan ta dawo takwanta akan cinyar wannan matar. tayi shiru tana tunanin abinda ya faru jiyah wannan kenan. Katafaran falo nashigo Wanda yaji kayan alatu acikinshi ba karamar tafiya naciba a falon kafin inkaraso inda wata lafiyayyar hajiya ke zaune ba Karya, taci wani arnen lace sarka da dan kunnan da agogon hannunta duk na diamond ne takalmin dake kafar tama anyimai ado da diamond din harta gilas din idon ta, sai zuba uban kamshi ta keyi tana latsa wayar ta ahankali gefe wasu mutane ne azaune sun baibaye ta duk kan nunsu kan su akasa yake suna dan fifitata ahankali, daga gani batan baya wannan gidan, gidan mulkine dakuma sarauta amma gidan ya hadu ba karya, yauma kamar kullum Yusuf ne yashigo agigice da alama daga barci ya tashi yafadu falon ahauka ce bai tsaya ko inaba sai kan cinyar wannan hajjiya yakuma fashe mata da kuka, dago watayi tace wa wadannan bayinnata kutashi kuje aikuwa take suka fuce, shikuwa Yusuf din kara kukan yayi yace mom why why me yasa mom, dagowa tayi tana kallansa cin nutsuwa Yusuf nagaji da lamarinka ya kake so nayi kasan zan iya komi akanka Dan Allah kafadamin meke damunka yau kimanin wata daya kenan agigice kake tashi daga barci kadinga fadamin irin wannan magan ganun anya ba aljanune suka fara taba kaba, alokacin ne Yusuf ya dago jajayen idanunsa yafara magana mom kinyi abinda baki kyau taba mom meyasa kika aikata hakan mom kinsan wanne haline take ciki kawai dan duniya haba mom yana kaiwa nan yakara fashewa da wani kukan tamkar karamin yaro, me kake nufi Yusuf menene abun da kake nufi ban fahim ce kaba pls mom karki nuna baki gane ba nasan kinsan mena kenufi amma kike nuna kamar baki sani ba, mom wllh kiji tsoran Allah wllh baki yiwa mama Fatima adalci ba duk abin da tayi maki aduniya ko maki yinta ba zaiyi mata haka ba dan Allah mama ki warware abindaba ika aikata haba mom, kara fashewa yayi da kukan wannan wacce irin rayuwa ce mom kika dauka, nasani Allah yayi Khadija ba matata bace kuma har yanzun inasan yar uwata dan Allah mom kasa karasawa yayi saboda tsabar kuka da bakin ciki, ya kuma daura da cewa sannan kika saka mutane suka manta da lamarinta suka manta da anhalicce ta aduniya hatta yan uwanta da mijinta hatta mahaifinta ba kyatunanin cikin dake jikinta, wani banzan kallo ta watsamai sannan ta dura da cewa Yusuf anyakuwa baka hauka ce ba wai akan wa kake magana ban gane bah wacce kuma Khadija Yusuf dama kanada wata yar uwa, wadda kaso aura aka hanaka to yaushe ma ka isa auren shika runka nawa kwata kwata me ka tara aduniya meka ke dashi wanda nida kai zamu rayu dashi haba Yusuf ya kakeso kazama sha

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment