Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya furta Alhmdllh. Cikin farin cikin da yakara mamaye sa Jin dariyar Mahaifin nasa abun kaunarsa ya yakara furta Alhamdulillah..

Ammar ne yake Tambayar Ina Nurul hayat bayan sun gama musayar gaisuwar ta yaushe Gamo,"Nurul hayat Dinka na nan lafiya,Ni yanzu ma Ina Fada ne "sarki Ali yabasa Amsa.

Shiru dukkaninsu sukayi akan furucin sarki Ali na karshen musamman Ammar domin Gaban sane yayi mummunar faduwa A tunanin sa zancen Baya ne zai dawo duk da Bai ga alamar hakan atare da yanayin Mahaifin nasa ba ...

Sarki Ali ne yayi murmushi Jin shirun da Ammar yayi akan furucinsa nakarshe Wanda dama yayi hakan ne Dan yakara ganin Yana yin Ammar din da dauki kiyayyar duniya yadaurawa sarauta.

Katse shirun nasu yayi bayan yagama tu ajjabin Al amarin Ammar din,Anan yasanar Masa da batun janye murabus dinsa har sai lokacin da yaji Yana Ra'ayin ayimasa murabus din,tare da furta Masa ya yafe Masa laifin da yayi Masa na Rashin Neman sa,duk da yasan Shima yana da laifin sa taurin kan ne iri Daya like father like son.😀

Farin ciki ne Mai yawa Ammar ya tsinci kansa aciki Jin Abunda Bai tab'a zato ba agurin Mahaifin nasa,sai Kuma gist na biyu da yakara Sanya sa farin ciki shine katafaren Asibitin da aka Gina da sunansa wadda har an kammalata tun da sarki Ali yafara maganar Ammar ya fincike blanket dinsa k'asa yasauko daga kan had'add'en bed dinsa na Alfarma, k'ak'k'arfar surar jikinsa ta Bayyana tare da kwantaccen gashin kirjinsa da yakara lafewa guri Daya sanadin Hutun Dake jikin sa komai gwanin buurgewa atare dashi abun son kowace mace 🤫 harta da six spack dinsa dama daga shii sai short ne fari k'al ajikinsa.

Jin cewa mafarkinsu shida d'an uwansa. ya cika nason Gina hospital ta Alfarma anigeria duk da suna da Abunda zasuyi constructing da kansu musamman ma shi Ammar din farin ciki ne kwance akan kyakkyawar fuskarsa and he's speechless about the gist.

Ficewa yayi daga bed room din nasa.
Cikin sassarfar sa ta gwarazan maza yake saukowa daga upstairs din sa har Yana hada steps biyu,Kuma wayar na akunnensa Yana furta thank you ABBA! thank you ABBA! you are the best father in the world cikin shauki na soyayyar mahaifinsa da farin cikin wannan albishir.

Hakuri yabawa mahifin nasa na Rashin Neman sa da baiyi ba cikin natsuwa,cikin farinciki dukkaninsu suka Yanke Kiran bayan sunyi sallama da juna.

💃💃💃💃🙌🙌Finally dai Ammar ya shirya da mahifin sa yanzu sai maganar dawowa Nigeria✈️✈️Allah yasa dai su dawo kasar su ta gado don nikam nagaji da kasar India zafinsu yayi yawa arado 🤭🧐🤫

🚴🚴🚴🚴🚴MUJE ZUWA akuya ta sace kura😆.Ko A mafarki Nasan hakan bazai faru ba....Nima nabi maganar bahaushe 😹


Komai Nisan jifa.....🤗🤗

*Hasbunallu wa ni'imal wakil*
*Hasbunallu wa ni'imal wakil*
*Hasbunallu wa ni'imal wakil*


YA ALLAH DUK WANDA YAKE DA WANI SAB'ANI DA IYAYENSA ALLAH KA DAI DAITA TSAKANINSU🤲🤲

DOMIN ABUNDA WASUN MU BASU CIKA KULA DASHI BANE BABBAR MATSALACE ARAYUWA YIN FUSHI DA IYAYE DOMIN HAKAN NA SANYA ZUCIYA RAUNI,YAKAN HANA JIN DADIN DUNIYA WALLAHI,FUSHIN IYAYE BALA'I NE.WAL IYAZUBILLAH😥

IYAYE BA ABUN WASA BANE,AKWAI HADISSAI DA DAMA DA SUKAYI MAGANA AKAN HAKKIN IYAYEN MU KUMA INGANTATTU,AKWAI HADISIN ANNABI SAW DA WANI SAHABI YA. RUWAITO INDA HADISIN YAKE CEWA "FUSHIN ALLAH NATARE DA FUSHIN IYAYE "KUJIFA ALLAH MA YANA FUSHI DA WANDA IYAYENSA SUKE FUSHI DASHI TO INAGA WANDA SHI YAKE FUSHI DA NASA SUBHANALLAH..😥

ALLAH KA KARE MU DA WATA MUMMUNAR ZUCIYA🤲 DAN HAKA MU SAKA HAKURI, DUK ABUNDA SUKAYI MUNA MU MAI DASA BA KOMAI BA IN SHA ALLAH ZAMU GA RIBAR ABUN..
TABBAS DUK ABUNDA MUKAYI MUSU BAZAMU TABA BIYANSU BA A CIKIN WANNAN DUNIYAR ,DAN HAKA MUDAGE DA KYAUTATA MUSU DOMIN SAMUN RIBAR DUNIYA DA LAFIRA DOMIN IDAN KIKA GAMA DA IYAYE KI LAFIYA TO DAYARDAR ALLAH ITAMA DUNIYA KINGAMA DA ITA LAFIYA.
ABUN DA KAWAI BA,A YIWA IYAYE BIYAYYA ACIKIN SA SHINE SABON ALLAH.✍️✍️

ALLAH YASA MUDACE🤲
ALLAH KUMA KASAKAWA IYAYENMU DA GIDAN ALJANNAR FIDDAUSI.🤲
WAYEN DA SUKA RIGA MU GIDAN GASKIYA ALLAH KA HASKAKA KABARINSU KASA HUTUCE AGARESU.

AMIN YA HAYYU YA QAYYUM✍️ ✍️

💫Fa'eehbg 💫
The first lady 🙌🙌

Fad'awa dakin Aj yayi cikin yanayin farin ciki Wanda ko sallama Bai tsaya Yi ba adakin na Aj.

Dr Aj da fitowarsa daga bathroom kenan ta cikin mirror yaga mutun atsaye tsakiyar bedroom din nasa...
Cikin mamaki yake kallon ganin Yana ta faman sakin murmushin mai kayatarwa

'Ammar ne yake ta sakin murmushi har ya tako ya rungume Dr.Aj Tsam ajikinsa cikin wani yanayi.
Dr Aj abun yaji sa banbarakwai duk da duk da yasan d'abi'ar Ammar ce Rungumarsa inda sabo yasaba da hakan dan duk lokacin da yake cikin farin ciki yakan yi Masa hakan tun suna Yara yake Masa hakan,har yayi niyyar Ture sa sai ya tuna yanayin da yaga fuskar Ammar din da yanayin farin ciki Dake kwance akan fuskar sa Kuma yasan ayanzu bakaramin Abu zai Sanya sa shiga irin wannan yanayin ba...

Bayan kamar minti uku Ammar yad'ago daga jikin Dr.Aj Yana sakin wani k'ayataccen murmushi "Guess who called me right now"? Ya furta ma Aj cikin kafe sa da manyan idanunsa masu haske cikin zak'uwa Dr. Aj ya furta "su Lubna ne Dan saboda yasanar Masa haduwarsu alokacin da ya rubuta musu numbantasa...

Hararar wasa Dr.Ammar yasakar Masa kamar wata mace eyes ball dinsa har wani kyau suka Kara,sannan ya furta
No cikin yatsinar fuska yana tab'e d'an karamin bakinsa Mai dauke pink lips masu taushi kamar wani karamin yaro
Cikin wani murmushin ya Kara furta guess! guess! Yana Kara ware idanun kan Aj Dake tsaye Yana kallonsa kamar wani hoto yakasa gane Wanda yake nufi....

Ganin Aj Bai gane inda ya dosa bane yasake furta

" guessing" had'add'iyar wayarsa k'irar 15pro max Dake runk'e ahannunsa kamar itace Mahaifin nasa yad'ago yayi showing dinta afuskar Dr.Aj Sunan da Dr Aj ya Gani ne arubuce b'aro b'aro a last call ne yasanya sa rungume Dr.Ammar cikin farin ciki,Yana furta congratulations man tare da taping bayansa kamar karamin yaro Bayan sun gama murnar ne yasanar dashi duk maganar da sukayi da Sarki Ali,Dukkaninsu sun kasan cikin farin ciki a wannan Rana duk ka Kalli fuskokinsu zaka San da hakan.

WATA MATSALAR TAZAMA TARIHI
IN SHA ALLAH✍️✍️
A HANKALI DAI AHANKALI....✍️✍️✍️
ZAMU JE INDA MUKE SO MU ISA...

⭐⭐⭐⭐⭐

*NIGERIA*
*BUG*


Yau takasance lahadi,Rana ta farko da dr.yusuf janyau zai fara zuwa gurin Halee,Bayan Neman izinin da yayi gun Baba Adee.
Tarba Mai kyau yasamu garesu.
Shigifar gidan Anan aka shimfid'a Masa k'atuwar dadduma Mai taushi Mai cin mutun hud'u...

Musamman Khady ta girka Masa had'add'iyar jallof ta shinkafa wadda taji kayan Had'i tare da taimakon Halee sai mango juice da suka yimasa da yaji kayan Had'i Shima na musamman da damammiyar fura Mai d'ansd'anon dadi da sanyaya Rai,Anan kan carpet din suka baje Masa madai daciyar kulan da suka shirya Masa da Kuma manyan jugs din da suka shirya Masa kayan sanyaya zuciya.



A d'aki Bayan Khady ta Masa iso,ta dawo d'akin cikin rad'a take furta toh Mrs Yusuf sai ki fito muje ko Kar mushanya angon naki ....
Takai karshen maganar tana sakin karaamar dariyarta .

Halee da Tasha uwar kyau kamar wata sabuwar amarya kamar kasace ta ka gudu cikin Jan material Mai kyau an mata fitted gown yakwanta ajikinta d'ass material din yasaje da fatar fatar ta yakara mata wani kyau na musamman..
.harar Khady Tayi kawai cikin wasa batace mata k'ala ba...

Karamin farin hijab din da Khady ta lura Halee tasanya ne cikin Jin haushi ta furta mata sannunki tana hararar ta,itama Haleen harar Khady Ahankali Kuma cikin zazzakar muryarta ta furta "Yawwa"Dan tasan dalilin wannan maganar ta Khady ,tsuke kyakkyawar fuskarta tayi tare da Kara matse d'an karamin bakinta Dan karma Khady tasamu damar kawo mata wani zancen kan hijab din.

Khady Dake rike da k'ugu ce ta tako cikin tana furta narantse bazaki fita dashi ba,tana Kara murtuke fuska irin dagaske tayi rantsuwar..
Cikin Jin haushin rantsuwar da Khady tayi Halee tacire Da'n madai daicin hijab dinta Wanda yake kullum haka take da Abunta har cikin gidan..

Hijab din tacire tayi wurgi dashi gefe Wanda sanadin hakan yakara bayyanar da albarkatun jikin ta da kyakkyawar surarta wadda ko acikin hijab din bata boyuwa domin Halee irin matan nanne da Allah yayiwa baiwar halitta tako Ina ba makusa.

Itakuwa Khady boyayyen murmushi tayi domin dama tasan inta rantse dole zata cire sa shiyasa ta mata haka nan domin tasan ta da kafiya awasu lokuttan.

K'ugu ta kama irin yadda Khady tayi bayan ta mike daga karamar kujerar Dake Gaban madubin dakin nasu datake zaune akan sa,cikin Jin haushin Khadyn ta furta cikin sanyinta "wai nikam ba yayar ki bace dakike rantse mini tana maganar tana karkad'a jiki irin na masifar nan,Dan kinsan dole zan cire shiyasa kika rantse Koh,Tau gobe in ance ki Kara rantsewa bazaki k'ara ba bazan Kara yarda ba nikam ki ka Kara wata Rana zakiyi kaffara takai karshen maganar cikin kyafci,wai ita nan masifa ce takeyi cikin ruwan sanyi fa take maganar bazaka tab'a zato n ma Fada bane in ba kana kusa da ita ba...Khady Dake ta kallonta da dariyar da tacika mata cikine tana kokarin boye dariyar tadake..
Dasauri ta rike hannun Halee ganin tajawo hijab din zata mayar,Khady ce cikin marairaicewa take furta "Anty Halee sorry;bazan k'ara ba tana maganar tana marairaicewa kamar zatayi kuka dagaske.

Dariya Dukkaninsu suka kece da ita na shiriritarsu,Baba Asabe ce ta lek'o cikin masifa tana fad'in ke Halimatu ubanwa kika barwa bako azaure ne eh!?takarashe maganar cikin Jin zafi da da'ga murya,shirun da Taga sun mata ne yasanya ta Jan katon tsaki mtsww
Tajuya fuuu tabar kofar dakin nasu tare da sakin labule.

Bayan ta wuce ne dukkaninsu suka Kalli juna suna rike Baki na ganin lokacin da suka ja bayan Duba Dan madaidaicin agogon bangon dakin.

Babu tsaitsayawa Khady tajawo Jan gyalen rigar ta Halee dake kan yashe kan katifarsu ta Yi mata rolling dinsa akan yalwataccen gashin kanta da yasha gyara har kalabar da Khady tamata ta warware da kanta saboda santsin gashin ta kitso iyakarsa Yan kwanakki yake fara warwarewa,da sunga hakan kuwa sai su idasa warwaresa su biyu saboda tana da tsawon gashi sosai dole sai da taimako gurin tsifar.

K'ara feffesa mata turare Khady tayi bayan tayi mata rolling gyalen Dan tace batason yafawa tana son ta rufe jikinta.

Sak kuwa tafito kamar wata balarabiyar etopia duk da bawata kwalliya da tayi daga Kajol ne sai powder da pink lipsglow da yakara k'awata small mouth nata Mai dauke da pink lips,eyes lashes dinta sunji mascara sun Kara curewa,gyarar ta kuwa Tasha gyara gwanin buurgewa sai dai muce Masha Allah kyawo ne ke magana Anan...
Dan Allah yayi ma Halee baiwar Kyau...

Flatshoes ta Sanya black da suka k'ara ma kafar ta kyau dukkaninsu sunyi kyau kamar kasace su ka gudu itama Khady tayi shigarta irin ta Halee material Daya sai dai banbanci nata ash color ne sai din ki ita nata straight ce bisa ga Halee dake da fitted gown.

Fitowa sukayi Dan Isa inda yake suna zuba kamshi,musamman Halee kunsan mutuniyar taku akwai son k'amshi....

A b'angaren Dr Yusuf kuwa kallon agogo kadai yake yi duk bayan Dan lokaci ganin har minti biyar ya Shure basu fitoba,bayan Khady tace yabata minti biyu zata kawo masa ita bayan tamasa ison..


hankalin sa yaji ya tashi Yana Jin sagewar gwiwa na zuciyarsa da ta raya Masa kila bata ma son had'uwa dashi...

Hango Khady yayi tafe ..rege rege yafara na Rashin hango Halee,fahimtar hakan da Khady tayi ne yasanyata d'an ja gefe yadda zai hango Halee da kyau Dan ta fahimci ita yake so yagani...

Kyakkyawar fuskarta yahango Mai cike da murmushiinsa Wanda bako yaushe ake samunsa ba sai Alokutta kalilan,tafiyarta takeyi cikin natsuwa tana kallon k'asa,siraran kyawawan yatsunta take ta faman murzawa har suka k'araso gurin fahimtar abun da Khady Dake gabanta tayi da Kuma idanun sa da takeji na yawo ajikin ta duk sai taji jikin ta yayi sanyi tana Jin wani yanayi daban.
Idanunsa akanta Suke ko isowar ta Khady Dake farko Bai Gani ba...

Sallamar da Khady tayi ce tadawo dashi dai dai daga sumar zaunen da yayi na kallon kyakkyawar surarta da ta bayyana duk da rufe jikinta da tasa akayi da Vail dinta ..

Ajiyar zuciya yasauke Mai nauyi aboye Yana amsa Sallamar su harda ta Halee da tayi k'asa k'asa wadda Kuma sarai yajita domin sautin ya Isar Masa har inda baiyi zato .......

Finally dai Haleen zata fara dating❤️

Allah yasa anshiga da kafar Dama Dr. Yusuf....

Me kuke hasashe a wannan Rana shinko Halee zata karbi tayin Dr Yusuf?

Baba Asabe zata kyale wannan lamari kuwa ganin tata diyar son shiru...?
Hmmm

Mutanen India ko zasu baro kasar ko kodai?✍️✍️😒😒

Bakina da goro....🤭
Kudai kucigaba da bibiyar alkalamina*

*Message to my big fan♥️ this page is belongs to you*🥰🥰 *maman Abbah*
Allah ya bar k'auna tabbas amafarki Nasanta Shima yana kaunarki kamar yadda kike nuna mishi one love,🩷🩷Allah yabar k'auna✍️
Masu korafin short page yau dai ansamu long page narufe bakin magana🥱
Yau nayi typing har na gode Allah🥹
🚴🚴🚴🚴
Mu hadu
Anext page 🤗


Like share and comment pls
https://chat.whatsapp.com/IjZCle5c6V3BGRlnZ0yKim

💫A MAFARKI NASANTA💫
I know her in my dreams
By
Pha'eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫Fa'eeh BG💫

Dedicated to my lovely sis lailat Almustapha Murai💔

------------------------------------------------------------------
--------------------------------------------------------------------

*PERFECT ESSENTIAL WRITER'S ASSOCITION📚🖊️*

*💫P.E.W.A💫*

*Home of perfect essential writer's together we stand🤝*

*ESSENTIAL WRITER'S📚🖊*

*Pen🖊️*is migthier than the sword *🗡️*


*Free* 📙

EPISODE1️⃣
PAGE4️⃣1️⃣


TYPING📲📲📲

♥️♥️♥️♥️♥️♥️♥️

Ur are my everything sister sumayya Almustapha Murai🤩🤩♥️my life is nothing without 😘you indeed this page is belongs to you baby girl 🤩I love you dear.🥰🥰

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


*Barkanku da Shan ruwa fatan kowa yasha ruwa lafiya*
*Allah yakarb'amuna ibada🤲🤲Allah* *yabiya wa kowa da bukatun sa na alkhairi,Amin*✍️✍️✍️

<<<<<<<< >>>>><<<<<<<<<<>>>>>>>>>

D'an murmushi yayi bayan ya Amsa Sallamar tasu Yana furta shine kanwar mu kika shanya ni Baki kawo mun mata ta da wuri ba so kike nayi kuka Anan ne?yakai karshen maganar cikin Kara sakin murmushi Yana yawo da idanunsa akan Halee wadda take a tsaye sagado ba wani kuzari..

Murmushi Khady tayi tana furta Afwan Dr.ka rufamun asiri Kar hukumar lafiya ta duniya tazo yin yaki Dani saboda nasaka Daya daga cikin masu Yiwa Al umma hidima akarkashinta kuka takai karshen maganar tana sakin karamar dariya, Shima kansa Dr.yusuf dariyar yayi Jin maganar ta Khady,cigaba da magana khady tayi tana furta
" Afwan Dr na tsaya Kara gyara maka matar Kane "....takai karshen maganar tana murmushi.

'Dr Yusuf wani murmushin yasaki najin dadi Mai hade da dariya kana ya furta korafi yakarb'u barrister Khadija yakai karshen maganar kamar irin a court,dariya Dukkaninsu dariya sukayi Jin yadda ya mayar mata da amsar harda wani barrister Khadija.


Harta Halee da tazauna yanzu take jinta akan k'aya kan carpet d'in itaama sai da tad'an Yi k'aramin murmushinta Mai kashe zuciya.



Sallama Khady tayi Masa Bayan sun d'anyi barkwanci ta wucewarta.

A hankali yatsin Muryar Halee tana furta "Ina wuni " cikin wata silent voice Mai Sanya bacci ga Mai sauraro bayan d'an shirun da yabiyo baya tsakaninsu.

K'ara sunne kanta Dake k'asa tayi,Jin yayi shiru Bai amsa ba.
Sautin murmushin sa da taji ne yasanya ta d'an d'ago da kyakkyawar fuskarta Dan ganin Abunda yasanyasa murmushin Had'a idon da tayi dashi ne ne Yakafe ta da idanunsa masu cike da shaukin Sonta da alama Bai baida niyyar amsawa mata gaisuwar,shi yasanya dasauri tak'ara yin k'asa da nata idanun tana sakin guntun murmushi,cikin natsuwa Dr. Yusuf da ya Kara sauke ajiyar zuciya a bayyane wadda har sai da Halee taji sai dai bazata iya d'agowa ta kalle sa ba.

"Masha Allah kinyi kyau har nakasa dauke idanuna akanki,Dan Allah ki rik'a mun irin wannan kwalliyar da murmushin " ya furta.

Kunya maganar sa tabata Dan bata tab'a soyayya da kowanne namiji ba ko tsayuwa da wani duk da turuwar da ake mata damasu tsaidata akan hanya ko masu aikowa agida Baba Adee na dakatar dasu.

Tafin tattausan hannunta ta Sanya tana rufe kyakkyawar fuskarta najin kunya tana Kara sakin murmushinta Mai kyau Wanda har sai da side dimples dinta suka lob'a.fuskar sa yad'an matso da ita kad'an Shima Yana sakin murmushin..

Ta kusurwar Zara Zaran yatsunta ta lek'o sa Had'a idon da sukayi ne tacikin yatsarta Babba yasanya ta duk'unk'une kyakkyawar fuskarta cikin gwiwowinta tana sakin k'aramar dariya Shima kansa dariyar yakeyi na farin ciki Ganin ta cikin wannan yanayi.

Cikin wani yanayi ya koma mazauninsa Yana furta"nidai wannnan kunyar zata takurani yanzu idan munyi Aure haka za'a dinga yimun ana rufe mun wannan kyakkyawar fuskar...samun kanta tayi da d'ago kanta ta kalle sa cikin wani yanayi Jin furucinsa Wanda take jin duka maganganun nasa wani iri kasancewarta farin shiga.. sannan takoma mayar wa k'asa Bayan cire fuskarta ta akan jikinta.

Pls Dan Allah ki d'ago inga kwalliyar nan Koh,ko rowarta za,a Yi mun ne yakai karshen maganar Yana Kara sakin murmushi cikin wani salo shi komai
takeyi burgesa takeyi yasan cewa Allah ne kawai ja daura Masa son Halee Yana Jin ajikinsa Babu irin son ma da yakeyiwa Halee aduniyar nan..

Hmmm Dr.Yusuf kenan da alama kaima fara shiga ne 😹😹


🚴🚴🚴🚴MUJE ZUWA
Wai ansace jakar b'arawo🤣

Jin ya Had'a ta da Allah ne yasanyata d'ago da Dara daran idanunta tana sauke su akan kyakkyawar fuskar Dr.yusuf Dan Shima Dr Yusuf ba Baya bane gurin kyau Shima farin bafullace ne Yana da kyau sa gwargwado irin nasa sai dai tsawo ne Bai cika ba...

Subhanallah Masha Allah yake furtawa aransa cikin wani yanayi Ashe duk sauran lokuttan kallon tsoro yamata sai ayanzu ne yake Kara ganin zallar kyawunta zubin da Allah ya mata.

Kallon dataga Yana binta dashine lokacin da tadaura idanunta kan nasa yasanyata Jin tsikar jikinta zuba, cikin cikin wani yanayi na sanyin jiki da yakara dabibayeta ta furta "A zuba maka abincin" tayi hakan ne Dan kawar da yanayin da take ji atattare da ita dakuma kallon da yake yimata,A jiyar zuciya ya Kara sauke wa akaro na biyu Yana k'ara Jin sa acikin kogin soyayyarta acikin zuciyarsa..

A hankali cikin wata sassarkar murya ya furta "Alhamdulillah Allal Ni'imati"tare da furzar da wani iska Mai zafi acikin bakinsa take kasala tasaukar Masa wadda Bai San dalilinta ba,tare da kawar da kansa gefe.

Kai kawai ya iya d'agawa Halee wadda ayanzu ta d'an fara sakewa kad'an ganin ya dauke idanunsa akanta Kuma Baya kallonta,Wanda shikuma yayi hakan ne gudun faruwar wani Abu,shiyasa yayi gaggawar kawar da idanunsa akanta jinsa awani yanayin daban..

kunsan zuciya musamman ga Abunda
take so....

'kai kawai ya iya d'agawa Halee dake Jiran Amsar sa.

Abincin ta zubamasa..
A hankali Bayan yayi Bismillah yake cin abincinsa hankali kwance har ya kammala, Amma duka Rabin hankalinsa na akanta a fakaice.

Itakuwa Halee baiwar Allah sai faman tankwasar kyawawan yatsunta takeyi tana sakin murmushinta aboye da ita kanta bata San ko na mene ne ba.

Bayan gama cin abincinsa ne yayi hamdala..

Yagabatar da kansa agareta da soyayyarsa da Abunda yake ji agame da ita,D'an shiru yayi Yana sauke ajiyar zuciya sai Kuma Ahankali yacigaba da magana Yana "furta Dan Allah Halimatu sadiya kisoni kinji yakai karshen maganar cikin marairaice fuska kamar wani karamin yaro.

Halee dake sauraron sa ne tunda ya fara magana ta d'ago tana yin dariyar da bata shirya yiba wadda ta fito mata abazata Jin yadda ya marairaice mata.

Anasa bangaren Shima dariyar yakeyi ta farinciki ganin alamun nasara a atattare da lamarin, kyakkyawar fuskarta yake kallo tana dariyar fararen hak'oranta sai walkiya sukeyi gwanin burgewa.
A hankali Yak'ara furta naji dadin Dana Sanya wannan kyakkyawar halittar dariya ma'ana mata ta yakai karshen maganar Yana sakin kyakkyawan murmushiinsa..

Murmushin itama tayi tare da k'ara sunne kanta k'asa Bayan Jin wannan furucin nasa na matarsa Wanda kesakata Jin kunyarsa.

Kawar da wancen zancen yayi Yana tambayarta Amincewarta,shiru tayi tana Jin nauyin tambayar tasa da amsar da zata Basa,Dan tasan tabbas itama tanajin wani Abu akansa duk da bata san ko mene ne ba .

Kamar wata k'adangarwa haka tad'aga Masa kanta cikin Jin nauyinsa da kunyarsa ta furta "tunda ya baka damar zuwa gurina na amince domin Nasan baba bazai mun zaben mij....
Shiru tayi Jin kamar tadauke hanya

Murmushi ne ya subucewa Dr.yusuf

Sai yayi Kuma kamar baiji Abunda tace ba Dan ta iyar da maganar ta...

Ganin Bai nuna alamar yaji bane yasanyata cig aba da maganar ta cikin silent voice nata tana furta "Allah yatabbarmtar muna da alkhairi"

"Amin "
Ya ya furta afili cikin farin ciki duk da baha ka yaso jiba,Amma yasan A hankali hak'arsa zata cimma ruwa..

Firarsu suka d'an tab'a duk da yawan firar shine Mai Yinta ita iyakarta murmushi da uhm,aah sai d'aga Kai ..
A haka sukayi firar inda Bai barta ba harsai da yaga tafara sakin jikinta dashi har sun d'an San wasu daga cikin halayen junansu...

Sallama yayi musu itada Khady bayan Halee ta Kira ta..

Manya manyan jakunkuna ne na Alfarma ya Mik'a wa Khady bayan yaciro su daga cikin motarsa. Dakyar ta karba tana godiya bayan ya tillasta mata karbar ledojin ...shigowarta tayi tabar Halee atsaye bayan sun Kara yin Sallamar akaro na biyu.

Ita yake kallo har ya tada motar sa yakasa dauke idanunsa akanta,ita kuwa tsaye tayi ta kasa tafiya sai faman sunne Kai take Yi Kuma takasa shiga gida..

Har ya fara tafiya da motar tasa yadawo da Baya bayan hango ta da yayi atsaye takasa tafiya tinted glass din sa yasauke sannan Ahankali ya Kira sunanta cikin wata kasalalliyar murya Dan ayanzu har ta juya bata lura da dawowarsu ba.

Chak ta tsaya daga d'an takawar da tafarayi Jin tsayuwar motarsa dakuma sautin kasalalliyar Muryar sa "please Halee Kar ki cire ni a tunaninki,ki soni har k'arshen rayuwarki yakai karshen maganar tasa cikin sakin wani smile,tare da Jan motarsa.

Halee wadda ke tsaye bayan ta juyo Ahankali ta bi motar tasa da ido,takasa yin Koda kwakkaran motsi ne,ta tsaya Chak kamar andasata a gurin Jin furucinsa dakuma irin kallon da yayi mata,Wanda ta hango wani abu acikin idanun nasa mai wuyar fassaruwa,kallo ne yayi mata Mai kashe mata jiki Wanda har yanzu tana jinsa ajikinta.

'Murmushi tayi A hankali na dalilin da ita kad'an tabarwa kanta sani.
Ahankali tashige gidan ,inda ta tarar da Baba Asabe rungume da ledojin da Khady tashigo dasu da alama kwace su tayi duka,gasu nan duk ta zazzage komai akan tabarma,ga Khady a gefe tsaye tana ta faman turar Baki.

Wani k'aton chocolate ne Wanda akalla zai Kai 30k Baba Asabe ta sungume kwallin ta re da wani biscuits Shima Mai tsada duka sai da ta zab'i Abunda take so tabar sauran nan,bayan ta mike ta furta ke Halimatu zoki kwashi kayan,Halee dake a chan gefe rakub'e ta matso a hankali tana tattara sauran kwalayen chocolate din cikin Rashin nuna damuwarta,Har tajuya ta fara magana tana furtawa Khady "sakarya ai sai kizauna nan ki zama yar aike ko ince yar dako har tarigaki Aure yanzu haka keda dadi ace yar tsintuwa ko yar riko ta Riga yar masu gida goshi,wad'annan kayan da kika Gani ke ya kamata akawo wa su, kece Mai gata ba ita ba gaskiya Hadizatu da sake,yanzu ki duba uwar dukiyar da ya kashe mata Mtssw taja mugun tsaki tana kyabe Baki,ganin yanayin fuskar Halee da Khady tana k'ara furta ai gwara intsira ko da wannan ma takai karshen maganar tana Saka kanta acikin d'akinta har ta shiga tasake dawo da kanta tana furta "ke Halimatu inkin gama tattara kayan nan kije ki debo muna ruwa sannan inkin gama kiyi shara sannan ki d'ora girkin dare,"

"Tou" kawai Halee ta furta
Hawayen Dake kwaranya a idanunta tun lokacinda Baba Asabe ntafara yimata sakin magana tashare tana d'ungumawa Khady ledar guda da saura n kayan da ta Had'a..

A hankali

Please Login or Register in order to submit comment