Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne zai fita shima, Clashing suka yi da Ashraf Spark kenan Nan ma bai kulashi ba shima Alhajin bai kula Spark ba kowa ya wuce abinsa ba Wanda ya nuna alamar yaga wani,direct part din Mummy ya nufa,har yayi nisa yaga bai dace ba sai ya juya ya samu me gidan Yana bude mota yace Ina Kwana Daddy,Ko kulashi dattijon baiyi ba,shima sai juya abinsa ya tafi wajen Mummy, sallama yayi a katafaren palonta ya shiga Wanda kamshi ke tashi ta ko Ina,tana Dining cikin shiga ta alfarma cikin Less me tsada white and Golden,Ransa a hade ya isa wajenta yace good morning...kanta ta dago a hankali ta kare Masa kallo sannan ta hade rai itama

Ta mike tsaye tace bari na mike Kafi ganin tsayi na sai ka raina min hankali da kyau, wato sabo da wulakanci shine jiya kayiwa Asmau korar kare ka sani aure ba fashi gwara ma ka so ta, wallahi ka kiyaye ni karka ga wai ubanka babban Soja ne,kaima ka fara aikin soja kayi resine ba abinda ya dameni,ni na raineka Mahaifiyarka kawai haifarka tayi baka isa ka min iskanci ba,Dan karamin bakinsa ya tsuke yace Ohhh Mummy kin san bana sonta, ki daina jawowa Ina bata miki rai a kanta,ni fa ba yaro bane babba ne,Ina aiki Ina da kudi ku daina rainani komai kice sai yanda kika tsara zanyi bazai yuwu ba fa Ina fada miki kar kuyi Kuskuren daura auren nan wlh zan iya sakinta a wajen nan take,zaku ji kunya ki daina turota gidana haba ai ba tsari ba class mace tana bin namiji har gidansa Kuma gida ni kadai a ciki,duk ranar da ta sake zuwa sai na mata tsirara sannan zan jefota waje idan baku yarda ba ta sake zuwa ku gani, Kai ya girgiza kamar Wanda ya Sha kwaya yace nayi warning naku a daina takura min bana so a kiyaye, ya juya ya fice abinsa ba tare da ya saurari me zata ce ba.

Mummy ta zauna jiki a sanyaye tace innalillahi na cuci kaina Dana dinga barin yaron nan a kasar waje gashi nan yafi karfina ayi yaro duk ya gagari kowa ta zuba uban tagumi.

Shi kuwa gogan gidan Mima ya nufa wacce itace ta haife shi,gidan ko Ina sojoji ne birjik sabo da Babansa Babban Soja ne,sannan yayansa da kannensa ma mazan Sojoji ne, Yana shiga ya iske kannensa mata da Maza har da matan duk da kayan sojoji a jikinsu suna ta faman rawa a Palo sabo da tabara,Yana shiga suka kashe kidan sabo da sun san rashin mutuncinsa ba Wanda ya bari, part din Mima ya shiga tana bedroom tana shiryawa mijinta kayan tafiya zai bar kasar, sallama yayi ya shiga itama a tsaye yace morning Sweety

Murmushi tayi tace ka tashi lafiya? Ni fa bana son gaisuwa yanzu da ba lafiya nake ba ai bazanzo ba,to zauna mana ,bashi ya kawo ni ba,ki fadawa Kanwarki tunda ke yayarta ce ta daina matsa min bana son Asmau ki fada mata Ina ganin girmanta tunda ita kuka bawa rukona kawai an bata ni kyauta duk ta matsa min,bana so a fada mata.

Kai Dana ne dama? ai ni sanda na mallaka mata Kai har abada na bata ni ba ruwana da safgarku, ku kuka sani kunfi kusa ai,kar ka sake kawo min karar uwarka, Kai da Rafeeq me yasa bakwa son a zauna lafiya ne,ga Rafeeq Kuma ma ko Yan Nan gidan bai saurara sai yaga dama daga shi sai Islam abokinsa to ya fika ta wani bangaren shi Yana yiwa wacce ta rike shi biyayya baida kamarta,amma banda Kai you are so stubborn.

To kuwa an kusa sawa na fara neman mata nima indai za a aura min Asmau neman mata zan fara,Yar uwarka ce fa cewar Mima,yace Yar uwar me ni Ina ruwana da wasu Yan uwa,tace toooo zagi ya matso kaina,juyawa yayi ya fice abinsa ko bangaren mahaifinsa bai saurara ba ma yasan ba zama yake ba,duk Yan gidan basa gaisuwa daga Hey shike nan,ba Wanda ke safgar wani sai da dalili,ko sun hadu baza ka gane Yan uwa bane sai dai a kamanni,shi kuwa Spark bai ma fiye kama da su ba,kamar ba Dan kasa ba haka yake kamar a wata kasar aka haife shi can Jinin nasara,ga tsirfa wani irin murdadden mutum ne.

Bayan sati daya Spark yayi shiri ya bar kasar ya tafi Germany,ba wanda ya fadawa sai dai aga baya nan kawai, Kamal kadai ya fadawa,Indai suka ga shuru bai zo ba to baya kasar kowa yasan wannan amma indai Yana gari dole sai yaje ko fada anyi da shi.

Naila dai Umma ta sata gaba sai tabi Hajiya Tagwadas zuwa Abuja haka Mohsin yace tayi hakuri taje tunda sati biyu ne kawai zata yi,waya Yar karama keypad ya siya mata da layi rike wayarta na farko a duniya kenan ya koya mata yanda ake amfani da ita,ta hada kayanta a Yar jaka da Umma ta Bata.

Yau zasu tafi da wuri ta shirya taje har dakin Abban su ta same shi Yana Shirin fita aikin gadinsa da ya Saba tace Abba zan tafi ayi mana addua,yaran yanzu ana musu addua ma ya muka kare kana dai gani yanda dole sai mun lalace bare ace ba a yi min addua ai lalacewar Abba sai tafi haka,ni kaina tsoron kaina nake yi,Abba in kana jin Yar hau to nice sabo da haka a surfa min addua ta cire mayafinta tace dafa Abba sa min albarka.

Abba yace to.. to ya dafa kanta yanda tace ya furta Naila Allah ya tsare,iya albarkar kenan?ta tambaya, ya zazzaro idanuwansa Wanda suke kamar yayi zawo na shekaru yace a dai dinga kula,abi duniya a sannu,a Dinka taka duniya a hankali,yawwa na gama shike nan jeki cewar Abba, Naila bata gane hausar ba tace to Abba sai ta fito tana sanda tana tafiya kamar barauniya zata saci kayan wani.

Lokacin Mohsin ya shugo gidan ya iske abinda Naila keyi tana faman sanda yace ke Kuma mene haka? tace Abba ne yace nabi duniya a sannu na takata a hankali,dariya ta kama Mohsin ya dinga sheka dariya yace to Yar kauye ba haka yake nufi ba fada ya miki fa lokacin ya ganar da Naila me ake nufi,ta dinga dariya da maganarta ta yan Fulani tace aradu ni kwai wawiya bani da Kai sai na daukan kaya ai Affa shi baya min haka sai dai ya dinga washe min Baki.

Tace Abba kuwa harda zazzaro Ido duk akan zai sa min addua ya Ilahi wlh sai naga kamar Wanda ya Shekara a gadon asibiti yana jinya,gaskiya Umma tayi babban Jihadi data iya auren Abbanmu kan uba wlh da nice gwara na tafi yawon ta zubar, Mohsin yayi dariya kamar ba gobe,Naila tace Allah Yaya kirjin Abba kamar na fara,baki ta toshe da hannunta tana dariya a hankali tace a haka wai shine bargon Umma ai yasin ko quarter din Umma bazai rufe ba,ya Umma take yi da Sanyi? Allah ya bani kudi na siyo mata bargo babba na gaske karta dogara da kirjin Abba,ta sake rufe bakinta da tafin hannu tana dariya Kallon Mohsin ta yi tace Yaya da alama Kun shirya da matarka ko?

Rada ya mata a kunne yace ae maganin gargajiya za a bani,dariya tayi tace bana murna kishi nake yi da hassada me yasa kuka Jone? Ai tunda naga ka shugo kana yaye mana hakora nasan jiya an rufe kofa,baki ya make mata, tace nidai kishi nake ta fada tana harararsa.

Mohsin yace baki tambayi Amal yarki ba yau,Naila tace wai Kai Yaya Nan murna kake yi kayi abin kunya ya fito fili? Ban gane ba ya furta,tace abinda kayiwa Hanan matarka ta samu ciki ta haifo Amal ai rashin kunya kuka yi a daki sannan aka samu cikin gashi ta haihu kaga kowa yasan me kuka yi abin kunya ya fito fili,Mohsin dariya yayi yace ke kika sani ni dai na haifi 'yata, kallonsa Naila tayi tace uhmm kaji da shi, nifa shi yasa Sam ba sosai nake kiranka da Yaya Mohsin ba tunda ka haifi Amal nasan kaima A ne kana rufe kofa,Mohsin gashinsa me yawa ya shafa.

Hidaya yau ba school su hudun suna gida,tana ta aikin gida Hidaya komai ba abinda bata iya ba a rayuwa na aikin gida,ita kuwa Naila ko wanke wanke komai sai dai ayi mata.

Mohsin ne yaja Naila gefe yace ai dai gidan Yan uwanta zaki raka kawar Umma ko? Naila tace ae haka tace shine fa Umma tace masu kudi ne gidan suna da Maza wai na bude Ido na kalle su ko zanyi saurayi,wai yaran dangi ne gida gida duk dangi ne,Mohsin yace kina Jin wahala ko baza ki iya ba ko da matsala ki gudo gida kinji ko ki kirani a waya kinji ko? Tace ae naji Yaya,I will miss you,ka kular min da kanka,Jikin Nan natural a adana shi,zan tsananta bincike ko Kai ba Dan Abba da Umma bane ya kamata ayi bincike,zai wahala ma ba musaya aka yi musu a asibiti ba,Dariya suka yi Mohsin yace a gida aka haife ni ba a asibiti ba kinga dansu ne ma, kiyi hakuri ki samu wani yarinya, Nooo... rayuwa sai dai Yaya ta furta tana dariya,wasan su kenan tun Umma tana kulasu yanzu zuba musu Ido take yi.

Hajiya Tagwadas ce ta shigo da uwar akwati anci uban gogoro kamar Yar yorubawa tace yawwa ke 'yata fito mu wuce me napep zai kaimu tasha,Umma tace to kuje Naila Allah ya tsare,Naila tace ke Umma Tagwadas daukar min jakata ai ke zan raka unguwar bazanyi wahala ba, ni sandata kawai zan dauka waye yace kice na rakaki shike nan jakar ma sai na dauka ,Naila dai da kyar aka lallabata ta saka riga da skert na atamfa sabuwar da aka Dinka mata,tayi mata masifar kyau,ai suna ficewa daga gidan ta ja skert dinta sama ya dawo wajen gwiwa duk kaurinta a waje ana kallo,Tagwadas tasan taurin kan Naila yanzu sai tace ta fasa zuwa, ita da take so a can ta samu me kudi yace Yana son Naila cikin Yan uwan nasu shike nan ta samu hanyar shigar su burinta kenan shi yasa ta zuga Umman Naila tace zasu samo kudi da miji na gari me Naira.

Suna cikin Napep Tagwadas tace gidan da zamu je basu taba haihuwa ba,Kuma ance matsalar a mijin ne,Naila ta zaro ido tace to ga shawara ta samun kudi Umma Tagwadas,tace Ina jinki Naila,me zai Hana muje ayi min askin Maza me kyau ayi min Daadaa, nayi shigar Maza kawai na koma namiji sai na basu magani ko zasu dace Kinga idan suka dace mun zama masu kudi musamman ke da kika yi hanyar magani,idan naje a mace baza suyi Amanna da maganin ba

Hajiya Tagwadas tace wannan maganar taki ta kama hankalina muje kawai shagon aski akwai gidan kawata a can layin sai mu siyo kaya a gwanjo na Maza ki shirya tsaf, Naila taji dadi sai suka wuce shagon aski, Naila ta zauna tace ayi mata askin zaratan samari masu ji da kansu ta zabi wani kala Daadaa,aka rage gashin kuwa tare da kwashe gefe da gefe aka tura gashin ya koma baki wuluk sannan aka yi mata Daadaa a wajen gashin me yawa, ba karamin kyau tayi ba, suna fitowa suka wuce Kasuwar Kofar Wambai Gwanjo suka siya na Maza kala biyu manya manya kayan masu Fadi,gidan Kawar Tagwadas suka je a can Naila ta fara shirinta, ta samu Bandage ta tube rigarta ba bra ta nade kirjinta tana zagayowa dashi ta gadon bayanta ta manne breast dinta da fatar jikinta ta sake mannewa da seletape,kirjinta ya dame daf kamar bata da Breast sannan ta saka kayan mazan barma barma,sai ga Naila ta fito a Dan matashin saurayi me kama da mace.

Naila tana fitowa Hajiya Tagwadas ta tafa mata tana dariya,Naila tace daga yau Sunana Jamilu,karki manta fa Jamilu nake,tafiya suka yi sai tasha.
Naila har suka karasa tasha bata yiwa Hajiya Tagwadas magana ba ko sau daya,ta fito daga Napep tana wulwula sandarta tana wasa da ita da gani ta kware da wasa da Sanda salo salo take wulwula sandar,kafin kace me duk ta ja Yan kallo an taru ana kallonta ana ta dariya, zaton kowa Namiji ne, sai da ta gaji ta daina lokacin sun samu motarsu me kyau aka sa musu kayansu suka shiga mota sandarta akace ta kawo a sata a bayan mota tace aradu ban badawa,ai sai naji kamar nayi wata mummunar mantuwa bada ni ba.

Ana fara tafiya Naila tayi bacci har akaje bata San anje ba sai da zasu sauka aka tashe ta,sai ta tuna ashe fa Abuja zasu,Hajiya Tagwadas tuni ta sauka ta fito musu da kayansu,sannan Naila ta fita itama tace garin kamshi iri iri uhmmmm,sai munje gidan ma zaki gani tun bama gidan sojojin ba,Naila tace uhmm yanzu mene next? Taxi suka shiga ta kaisu katafariyar unguwar gidan Mummy ta nufa direct sabo da sunfi dasawa ta dan fi saukin Kai,Hajiya Tagwadas tana buga gate me gadi ya leko ya ganta ya Santa Nan take ya bude kofa Yana washe baki,Suka shiga suka ce ah sabon Dan aiki aka kawo mana ne suna kallon Naila Jamilu.

Naila tace wuce nan yaro ni da nake da shanu nafi karfin aikatau,shuru suka yi, Tagwadas tiryan tiryan ta kaisu har palon Hajiya suna shiga suka sameta zaune a kujera ta kafa tulun shisha a palon tana faman zuka tana feso hayakin waje, Naila ta zaro ido tare da furta kaga dattijuyar banza, ke Inna kiji tsoron Allah tsofai tsofai ai idan lokacinka ya wuce to ya wuce,ko kara'i kike yi ne? Hajiya Tagwadas ce tace Kai Jamilu dalla rufe mana baki,Mummy ko ta tasu bata yi ba bata San ma Allah yayi mutane ba a wajen a haka itace me saukin Kai.

Tagwadas ta Fadi a gabanta tare da mika gaisuwa kamar taga sarauniya tace ranki ya Dade ajiyar Dana na kawo miki Dan kawata ce ki dan bashi dakin zama ya zauna kafin naje na dawo,Naila ta bude baki mamaki ya kamata,zata yi magana Tagwadas tace karka ce komai Jamilu zamu raba gari,Mummy tana ta bulbulawa huhunta shisha tace okay fine barshi kije,tace godiya nake uwar dakina,kudi a zube a gefen Mummy ta irgo wasu ta mikawa Tagwadas tace ya mutan kauye? Tagwadas ta furta Naje kauyen waccen satin kuwa suka ce a gaishe ku,hannu ta daga mata tace ya isa tashi ki tafi,ko kallon Naila bata yi ba,Naila tana kallo Tagwadas tace Kai Jamilu ka zauna a nan zanje na dawo,Naila ta tabe baki tace to tare da cakewa a Jikin sandarta tayi wata tsaiwa akan sandarta yanda Fulani ke yi,Mummy Yan aiki ta kira tace gashi Nan ku kaishi masauki ku bashi abinci ya koshi a nuna masa komai,Naila dai tana kallon ikon Allah.

Me aikin ce tace muje ko part din maza ta nuna mata, sannan ta kawo mata abinci ta nuna mata toilet a cikin dakin sannan ta fice,Naila taci ta koshi tayi wanka ta kulle kofar da key sannan ta canja kayanta na mata doguwar riga marar nauyi ta material tare da saka hijab ta gabatar sallolin da ake binta tayi addua, bayan tayi Sallar Isha ta kwanta bacci dake dare yayi.

Bata farka ba sai washe gari da safe bayan tayi Sallar asuba take ta koma bacci tana sharara uban bacci har 11am sannan yunwa ta tasheta,wanka tayi ta sake nannade kirjinta ta manne da Seletape ta Maida kayanta na Maza Wanda ta zo dasu a jikinta, kayan matan Kuma cikin Inda ake ajiye kaya a dakin sip Nan ta bude ta boye su a ciki sabo da kar a kamata sai ta bar kayan mazan kala daya kacal da magungunanta na siyarwa na gargajiya duk suna cikin Jakarta,ta nufi part din Mummy,tazo shiga kenan taji suna ta fada da mijinta.

Mijinta Alhaji Aliyu yace wallahi aure babu fashi sai nayi shi,ni Kuma baka isa ka Kara aure ba sai dai idan bana raye ko baka raye,Kai zan iya kisan Kai,zan iya kashe ka na kashe kaina wlh,indai ka Kara auren Nan sai kaga ba dai dai ba zaka San wa ka aura,ba a abinda kika isa kiyi karamar Yar iska,tace to mu zuba mu gani waye zaiyi kasa,yace mu zuba ya fito a fusace ya kusa yaci karo da Naila tace cikin Muryar maza Sannu kayi hakuri,Ina kwana? Hannu kawai ya daga mata ya wuce abinsa dake gidan ko Maza ma free to enter ne.

Palon ta shiga da sallama ta samu Mummy ta zube a kasa tare da Kifa kanta a Saman kujera tana rusa uban kuka,Naila tace akan kishiyar wlh kin bada mata ai ko ni Jamilu da ace macece ni to bazan yi haka ba,baki hadu ba,Mummy kishi na cinta ta manta ma yaro ne Jamilu sai tace baza ka gane ba,wlh wlh tunda na aure shi bai fi a irga ba muke saduwar aure bashi da lafiya gabansa baya aiki sosai gashi ban taba haihuwa ba duk nayi hakuri dashi na zauna a haka shine zai min kishiya,Naila kamar babba tace share hawayenki Waraka tazo miki Allah ne ya kawo miki magani har gida Inshaallah daga yau sai kince Hallare ta isheki,Dan Nan mene Hallare? Naila tace Abar da kike kuka a kanta.

Naila taci ga yanzu ni Kinganni sabo da sanin kan aikina ba kalar da ban sani ba,ke me ya kaiki auren gajere?,irin tasu fa shape din kubewa garesu,kin san okro? Kubewar Miya Banda me kahon barewa,kin san a kubewa ma akwai doguwa to ba kalar doguwar ba, Yar gujub din itace irin ta mijinki,Ina ganinsa nasan tasa ba pole bace,ni fa muna hada Ido da namiji to tsirara nake ganinsa, harda tafa hannu tace duk wani Dan uwana namiji zigidir nake ganinsa,Mummy tace wallahi Dan nan ta megidana haka take kubewa sak,ah na fada miki ai muna yin clashing dashi na hango shi tumbir Zigidir, Mummy tace Allah da baiwa yake,Naila tace a daji na girma ni a Nan fagen na kware,ai gado nayi a wajen kakana tun na goma Sha biyar baya da suka shude sana'arsu ce,ba wanda yayi gado a kaf dangin mu sai ni nan Jamilu,Ina bada magani idan ta kama ma dole sai na gani to sai na ganta nayi mata aiki da kaina da hannuna,Hajiya ta saki baki tana kallon Jamilu,Naila tace ae fa idan ta kama to sai kalleta,ta nuna idonta da hannu tace akwai wani sirri a idona Ina kallonta lalurar dake wajen zata fito sabo da taga abinda ta gani a cikin idona.

Tace kina so na baki maganin ki yarda da Allah,bani zan warkar dashi ba Allah ne amma idan ya zama Sila sai Kiga kin dace,Mummy tace kawo na gani,akan sana'ata kice sai na kawo kin gani ma,in kina so sadaka zan baki in bakya so ki bar min abina wannan maganin da kin san aikinsa da ko million nace siya zaki yi.

Fita Naila tayi ta bude Jakarta ta kwaso su gasu nan a kulle a leda Dan mitsil mitsil gari ne green da wani red,ta kawowa Mummy tace gashi wannan kala biyu ne,Dan girki zaki Masa shi kadai dai dai cikinsa ki juye Masa ki tabbatar ya cinye tas shike nan daga lokacin ki tafi bedroom ranar kika yi wasa sai an kaiki asibiti an miki dinki,Mummy dai badan ta yarda ba ta karba,Naila tace to ai kunyi fada ta ya zai ci girkinki yau? tace kiransa zanyi na bashi hakuri,kina tunanin Hakan zai sa ya yarda Dake ai zaiyi tunanin da wata a kasa wai ya kike hakane kin fa haife ni duk da ni namiji ne amma baki da wayo,Mummy ta Kalli Naila da sauri wannan gatsali da yaron yake yi sai kace danta Spark babu mutunci a harkar su.

Naila tace ki jira shi ya sakko da kansa sannan ki Dan bashi hakuri sama sama sannan ki sa Masa amma da wuri haka ai sai ya raina ki,nifa da ace ni macece ba Dan iskan namijin da zanwa biyayya ni mamaki ma kuke bani da kuke nacewa mutum haba,Mummy ta saki Baki tace ikon Allah kai nifa na haifi yayanka ma ko yayarka ta biyu bare kai,ka kula kana gidana Ina taimaka maka da abinci kana fada min magana ba ladabi,Naila ta kalleta tace bani maganina na bar miki gidanki ni haka nake Ina da kirki Ina da zafi, kaina da kwari idan na birkice hmmm.

Mummy sama ta haura abinta Naila ta baje a kujera kamar gidan ubanta harda kiran Yan aiki,wata tazo a ciki tace zubo min abinci ki hado da hantar kifi, Yar aiki tace babu hantar kifi,tace to hantar kaza fa? Babu itama,zabo? Babu hantar zabo?,Naila tace shima comon zabon abin banza? tace ae,tace to ta Dan maraki? Akace babu,tace ta rago fa? Yar aiki tace sai ta Sa gaskiya,Naila tace uhm uhm bana cin Naman Sa sabo da ai cin Amana nayi shanu dabbobinmu kawai sabo da cin Amana naci namansu Bada ni ba,Yar aiki tace sai kace me bautar saniya, a'a daga India nake Naila ta furta da Muryar maza,Uhmm me zan kawo yanzu? Nasan ma babu Koko kawo min abinda kuka dafa banda shayi.

Naila dai tana gida har kwana uku suna shiri da Mummy sabo da maganin da Naila ta bata,Kuma mijinta ya fara sakkowa sun ma kusa shiryawa gaba daya shi yasa yau Mummy zata Masa girki da magani,taci gyaran jiki sosai za a angwance,yau wankan data dauka ma na musamman ne, Naila tana kallonta sai shanawa take a gidan masu hanu da shuni har yanzu Kuma bata ga wani namiji yazo gidan ba basu je gidan sojojin ba,ta dai kira Mohsin ta fada Masa komai normal.

Mummy Dan faten wake da doya tayima Alhajinta yaji kifi,Yana son kifi iya cikinsa yanda Naila tace haka tayi,part dinsa ta nufa ta Kai Masa yace zo Halima,ta koma zata zauna ya jawota jikinsa yace Hali dubu tawa ko kefa ai gwara da kika hakura nayi auren mene aciki kece fa ta gaban goshi,wallahi ba wacce zan so sama da ke a duniya,Mummy tace uhm ta kakalo murmushin dole tayi dai tace ci abincinka ko na baka a baki,yace da zan fi son Hakan,ta dauki spoon ta fara bashi a hankali Yana ci,har ya kusa cinyewa bai sani ba sabo da dadi sai da ya cinye tas sannan ya Sha ruwa sosai,har zai kwanta yace naji na gaji ne sai ya dauki carbinsa Yana tasbihi ya kwanta a Saman bed dinsa,Mummy ta kwashe kwanikanta tas ta fice ta wanke Kal ta Adana sannan ta koma wajen me gidanta,carbin ta samu ya jefosa kasa tana zuwa ta daga hannunsa taji ya saki alamar ya mutu rai yayi halinsa, murmushi ta saki tace akan kamin kishiya wallahi gwara ka sheka can Kai ka isa mutumin banza butulu,Kuma dole group na company naku su ajiye million goma in Sha bushasha ta,Hannu ta Dora a Kai da kururuwa ta fito tana ihu tana bako ya kashe min miji,Magani ya bani na karfin Maza ashe guba ya bani Mummy ta zunduma waje ta tara mutane ta kirawo makwafta,ta hau kiraye kiraye na Yan uwa da abokan arziki sannan ta kira police suka dungumo gidan, gida ya cika makil,Har Hajiya Tagwadas ta kira a waya ta taho hankali tashe domin ita har ga Allah burinta ta samu shiga a cikin masu kudin danginsu ta dinga samun kudade shi yasa ta kawo Naila ko zata Saba da su ta samu saurayi a cikin Yan gidan tunda suna yawan zuwa gidan sannan tasan watarana Mummy zata iya tafiya da ita cikin dangi kuma sai suka canja su gwada maganin ko

Please Login or Register in order to submit comment