Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

min ajiya,a guje ta dauro towel ta fito ta manta,shi ta tsorata shi ma yanda ta fito da mugun gudu,sai ya mike ya rigata yin waje,tace Kai ka dawo zo ka gani

Ya bita da kallo kuwa tun daga kafafu har sama,jikinsa ne ya mutu ganin cinyoyin Jamilu lukuta lukuta na mata,tana jibga uban kaya, Jikin nata ma yafi fuskar haske sosai, sharewa yayi kar ta gane Bai kalleta ba yace Jamilu lafiya? tace Abu ne a cikin toilet din kazo ka gani,ta tararrabe fuska,Spark yace Kai kamar ba namiji ba wai Yana satar kallonta ya bita ciki,yace mene? pad ta nuna masa da yatsa yace mene wannan din Bready kika kawo mana Kuma toilet?,Naila a haukarta tayi mamaki taji dadi Kuma da bai San ma mene ba,tace ban taba ganinsa ba sai yau,Spark yace baka kula ba dai, ai ni na dade Ina ganinsa na zaci ma kaine ka kawo,Naila sai ta fara rantse rantse duk ta zargi kanta tace wallahi Allah ba ni bane, kaji na rantse Maka da zatin Allah bani bane sai kace mace me zanyi da wannan ni kuwa,itace take magana amma ita yake kallo ya zuba mata mayun idanuwansa, yace to tun zuwa na gidan Yari nake ganinsa a toilet din nan maybe wani ne ya kawo ya ajiye,Naila tace okay na gane,yace idan kayi wankan Dan Allah karka sa kayan Nan sunyi nauyi da yawa baka tunanin cuta ta kamaka ta skin,fita yayi ya barta yaje ya dakko mata jallabiya yace ungo kasa kasa wannan, Naila ta karba tana ta zargin kanta tace wai me yasa yanzu ya daina takurawa sai ya Kalli jikina ne,karfa ko ya gano, tace a'a ai da ya gano ai bazai kirani da Jamilu ba,Kai Naila kema kinyi shirme kin fita da towel ,Naila tace to ai ya Saba dani shi yasa ma Bai ko kalleni ba ai ya hakura ne ya gama yarda namijine,dariya tayi harda tafi tace Ina Shege ni Jamilu Tantiriya,tace yau zan sha iska, ta cire seletape din da bandage Wanda take nannadowa tun daga gadon bayanta ta zagayo da shi, ta taho da wani daga dakinsu amma yau bata sa ta manne nonuwan ba tace yau ku huta Kuma,tayi wanka ta gama kenan,yayi mata knocking yace bude Dan Jamilu me zamani ga lotion ka shafa,Naila ta bude kadan tare da miko hannunta waje,tsokanarta yayi ya rike hannun yace wa na kama yau sai na kalleka Jamilu,Kara ta saki tana ja hannunta

Body lotion ya bata ta karba,yace Jamilu badai katon hannu ba,tace wallahi a'a bani da katon hannu ni ta rufe kofar,tana dubawa sai taga ba irin nasa bane,ta zaro ido ganin hoton mace a jiki ta bude kofar kadan ta jefo man waje tace ni Macece da zaka bani man mata? kafa sa min Ido Spark tam, ta rufe kofarta garam ta shirya haka aka sa vest me kauri da wando gajere na Maza ta zura Jallabiyya taga Boobs cako cako a tsaye ana Gani,cirewa tayi tasa bandage dinta da Seletape tun daga gadon baya take lafka uban mannewa ta gama ta Maida vest ta Dora jallabiya,Naila ita tayi Imanin Spark bai ganta bai Kuma gane cewar mace bace

Ta fito ta ganshi a Palo a kwance ya fara bacci ma,tashinsa tayi tace kaje ka hau gadonka ni a nan zan Kwana, Spark yace jeka Kai bed din ni zan kwana a Nan,Naila tace ni wai wanne Imani ne yazo Maka ne Aboki Banga kana haka ba da,ka fara acting daban,Kaje ka kwanta,kaga Jamilu ni bana son surutu idan Kuma dakin naku zaka tafi ga kofa Nan, Naila tayi tunanin wani abin ke damunsa baya son surutu, ta koma dakin tana murna tayi kwanciyarta ita kadai,tunda tazo gidan yari sai yau ta Sha bacci na mamaki ta saki jiki,amma duk a dakin malamai ne bata baccin kirki a tsorace take kar a kamata.

Yau kuwa har yaje sallah ya dawo bata tashi ba tana uban bacci,shima bai tashe taba ya koma baccinsa a Palo sai 9am ya tashi yayi wanka duk tana bacci har ya shirya cikin Jallabiya shima fara irin ta jikinta ya dauki Flask ya tafi siyo musu tea mutumin da Jamilu ke siyo masa baya komai Jamilu ke yi amma yau ya dauki Flask dinsa karami me kyau na Yan gayu yaje ya siyo komai,Chips ya siyo me shegiyar tsada kamar me ya dawo, yaji karar ruwa alamar tana toilet tayi brush da wanka,ledar pad din data gani jiya ta farke ta dauki biyu tace yau ranar rushing ce har biyu zan saka ko ta waye ma sakawa zanyi,ta shirya abinta ,Yar kofar ta bude kadan ta zuro hannunta tace Friend miko min bakar leda,Yana sani yace ba baka ya mika mata fara,tace baka nake so,ya koma ya dakko ya mika mata ta karba ta rufe kofa ta daure pad din data cire ta fito ta leka waje Yana kallonta ta jefa a Dustbin sannan ta dawo,Jamilu yazo sanye da jallabiyarsa.

Gani tayi sunyi anko,shi kuwa gani yayi tayi mugun kyau,tashi tayi ta koma toilet ta hada wayo sai ta leko tace innalillahi Spark zo ka gani,ya Mike ya leka yaga an bude pad din an dauki wasu,yace ikon Allah,Jamilu yace mutanen boye ne suka dauka wata aljanar ce ta dauka,Spark yace to a dauketa a jefar ya dauka zai jefar ta kwace tace Ina ruwanka mutanen boye sunyi ajiyar su zaka jefar musu ka kyale musu suyi amfani da abinsu, Spark dariya yayi yace to a barta Jamilu.

Suka fito Jamilu yace wai Kai ka siyo tea din? Kai ya daga kawai,tace uhmm ajebo anji masifu a gidan yari an goge,Spark yace a dole nake Shan tea din nan na gaji da shi gashi zazzabi ma nake ji,Jamilu ya kalle shi yace shi yasa jiya baka da sukuni? Kai ya daga mata tare da furta tun wurin magrib,da kulawa Jamilu yace sannu ko sauro ya isa ya sa mutum zazzabi a gidan nan, maybe Malaria ce,daurewa yayi Yana Shan tea din amma kamar zaiyi amai,Yana gama Sha da sauri ya shiga toilet sai amai ya dinga kwararawa, Naila da sauri ta tashi ta bishi ciki, ta tsaya a gefensa ya gama tsaf tare da wanke bakinsa yayi flowshing sannan suka fito tana Masa sannu, muje ka kwanta kasha paracetamol sai anjima muje asibiti, yace duba ledar can akwai a ciki,ta duba ta dakko Masa wani me kyau ba irin na yaku bayi,ta ballo ta kawo Masa ruwan da yake Sha na roba,hannu ya mika mata,tace bude bakin,ya bude ta zuba masa da kanta guda biyu ya kora da ruwa,hannayenta ya rike Sanyi yake ji ya furta Yana sake kankame hannayenta cikin nasa. wuyansa ta taba da bayan hannunta ta cire hannunta tace wannan uban zafin jikin fa.

Ruwa ta ebo me dan dumi a bowl na roba ta saka towel din karami a ciki ta matse kadan tace cire rigar a goge Jikin nan ko zaiyi Sanyi,Yace kana namiji gardi zaka taba min jiki naki ya furta ,Yana lulluba da bargo a Saman bed din,Naila ta fisge bargon tare da haurawa Saman bed din ,a zuciyar Spark dadi yake ji,a zahiri Kuma da kyar ya yarda,ya cire rigarsa daga shi sai boxers,jikinsa me tsananin kyau Wanda ya tafi da imanin Naila,shi kanshi wani farin ciki yake ji a ransa marar misaltuwa,kansa ya dora a Saman pillow ya juya mata baya gaba daya,gashi da kwailo baida juriya a cuta, ya dinga dishi uhmm...uhm...wash....Naila a hankali ta shiga goge Masa jikinsa, Hallare tuni ta mike sai da ta gama bayan nasa tace juyo gaba,Yana Jin kunya taga yanda ya mike,yace ai haka ma ya isa thanks,ka juyo in zaka juyo,bargon ya ja ya rufe daga kugunsa sannan ya juyo,Naila jikinta har rawa yake itakam bata taba ganin namiji haka ba,da sauri ta rufe idonta a haka take yi Ido a rufe,shi kuwa Spark fuskarta yake kallo kawai kamar maye ya lashi lips dinsa a hankali Yana wani kallonta ba ko kyaftawa kamar wani wawa, har ta gama Ido a rufe,da sauri ta dauke Bowl din ta zubar da ruwan ta wanke towel din tare da shanyawa kafin ta dawo yayi bacci ma.

Bangaren nasa ta gyara ta fice abinta ta koma dakinsu na malamai,tana shiga suka ce wai yanzu Jamilu Ina kake zuwa ne? ga budurwarka ta ishemu da nemanka ta jikin bango Beauty, Naila tace Ina wajen Budurwata ta number one a raina Spark muna zuba love,kasan ni both side ce in buga da mata in buga da Maza,Malam Sharu yace Muna addua Allah ya shiryeka Jamilu, gobe fa akwai maulidi muna gayyatarka Jamilu,Jamilu yace wai dama watan ya tsaya ne? Suka ce ae baka ga ana ta yanka shanu ba a gidan nan zamu ci dadi, kazo kaima a baka sura ka karanta,Jamilu yace idan dai Yan Mandiri sunzo masu kida zan shiga na chashe sabo da haka ba wani gardi da zaiji Muryata ni Jamilu Tantiriya,Malam Sharu yace Allah ya shiryeka Kai sai dai sai abin shagala ka iya,Jamilu yace sosai ma kuwa ranar akwai dukan kirji inyi rawa itace zata kaini,Malam Jilani ya furta Allah ya shiryeka ka daina harkar Daudu kana bin Maza Yan uwanka, kaima idan kana so mu dan samu waje mu kebe malam,Malam Sharu yace ai gwara mu mutu,Dariya Jamilu yayi harda shewa irin ta Yan Daudu.

Ranar maulidi tun yamma aka fara Maulidi a gidan, Naila bata je ba amma ana saka Mandiri ta tafi wajen,Maza an samu rana sai shagali akeyi suna ta tikar rawa,wurin Spark ta koma yaji sauki suka je asibiti aka bashi magunguna bayan an tabbatar malaria ce, bai fi kwana uku ba ya warke,lokacin Beauty ma ana shirin barin gidan yari domin Daddy dinta ya shiga ya fita shekarar ta biyar a gidan yari, sai yanzu Allah yayi,shi yasa take ta neman Jamilunta ta fada Masa,amma bata same shi ba sai yau,Jamilu Yana daga wayar yace tuba nake gimbiya sarautar mata,kaina bisa wuya,Spark Yana zaune Yana jinta kawai shi bai so yaji Naila da wani ko wata, fushi ya fara ya kwanta kawai Yana jinsu Beauty tace Allah fa yayi nima nan da kwana uku zan fita an gama komai,Jamilu ya furta wow,tace murna nakeyi zanzo Maka ziyara na ganka,Naila tace na miki murna Baby Allah ya samu a danshinku, Beauty tace Ameen .

Naila a ranta tace ni yaushe zan fita ne? Kawai sai hankalinta ya tashi, Spark kuma ana ta kiransa a waya a fada masa labari me dadi yaki dagawa gashi har an fara zama a kotu,Mama zama daya ganin asirinta ya tonu kawai ta Fadi gaskiya bata Musa ba,Yan uwanta da suke uwa daya uba daya da Kuma Wanda ma uba suka hada suna ta jimami har kuka suke ta faman yi,ba kamar Mima da Mummy,Mummy harda refefe baki tace kinyi asara Kaltume,me ke damun mu ne? Mu yanzu mata sabo da son zuciya mune zaluntar yaran kishiya,shi yaro ma me yayi Maka,yaro Amana ne, uwarsa bata gida ko ta mutu sai mata su zauna sabo da son Kai su dinga zaluntar yaran kishiya,wasu su nakasa yaro ko yarinya,wasu Kuma suyi ta gana musu azaba wannan zalunci ne Kuma Allah bazai bar mutum ba,wasu har da kisan Kai a kashe Dan kishiya,kishi hauka ne,kishiyar ma da ta mutu amma baza a hakura ba sai kishin ya koma kan yaranta,yanzu mene ribarki Kaltume dan kin kashe Yar kishiya sabo da ta auri Spark wato yarki kike so ya aura sabo da yana da kudi,tirr da hali irin naki Kaltume,ganin ke kika raineta har ta girma na zaci ta zama Yar uwa,na zaci mun zama daya da Asmau,yarinya tana mutuntamu,Kai Kaltume kuma kin yarda Dan Yar uwarki uwa daya uba daya yayi life in prison,to Allah ya Toni asirinki,Mummy ana ta kallonta a mutuniyar arziki ana cewa gaskiya ne,su kuwa sauran magana ma ta gagara.

Kotu zaman ta dage zuwa sati biyu sannan ta nemi a kawo mata Spark tare da ci gaba da tsare Mama, Mummy harda cewa alkali sati biyu yayi yawa Dan Allah a fito min da Dana dama na gama takaba ni Kam Alhmdllh,alkali ya kalleta yace to da kika gama takabar aurensa zaki yi kema? Dana ne fa yanlabai,yace ai naji kince kin gama takaba a fito miki da shi,zata yi magana alkali ya dakatar da Mummy da ta damu kowa a ciki da surutu.

Abba bayan ya dawo daga zance komai sai da ya kwashe ya fadawa Umma amma yaki fada mata zai mata anko,Yana runfar kayan miyansa Mohsin yazo wajen,bayan ya gaisar da Abba,Abba yace yau ba aiki ne? Yace ae,to madalla dama Batoola ce za ayi mata anko suna da biki ka kawo dubu goma a Kai mata ko kakai mata da kanka,Mohsin yace Abba kasan wata yayi nisa sannan kasuwar ma Bata tafiya yanzu ga me gidan nawa yayi tafiya,Kuma ma daga zuwa sai ace za ayi mata anko har na dubu goma,zagina zaka yi Mohsin? yace haba Abba ni na isa,to kaje ko rance ka samo ka kai mata kaji na fada Maka, Mohsin ba yanda ya iya yace ni na jawa kaina dana hada shi da Fatima.

Naila ce ta kira Mohsin lokacin daya shiga gidan wajen Umma, Mohsin yace na manta ban fada miki ba Abba fa zai kara aure sis,Naila tace na shiga uku kishiya zai wa Umma? Kuma kuka yarda? ya za ayi da shi shi yasa muka yanke hukunci cewar a samo me hankali a aura Masa kar ya kwaso mana jaraba,Naila tace Ina wani me hankali a kishiya,yanzu ma zuwan farko har tace ayi mata anko na dubu goma Kuma yace ni zan biya gashi ni yanzu ma dubu daya ma bani da ita cewar Mohsin,abincin gidana ya kare na su Umman ma ya kare,Naila tace ku rike auren Nan Sweetheart sai Allah yayi na fito ni nasan tuggun da zan hadawa Batoola da kanta ta fasa,sabo da Allah dame zamu ji ana fama da shi da gida, zai Kuma karo mana wani masifar salon tana zuwa ta haifo wasu yaran,Kai Yaya me yasa zaka yiwa Umma haka,duk da tana yiwa Abba masifa amma ai tana kokari tun Kuna yara itace cinku da shanku ta Sha wahala kullum a teaching Dan a rufawa Kai asiri amma kuce yayi wani aure da me za aji, magana ta Allah a nan baka yi tunani ba,ni bana goyon baya wlh kuma ko an aurota na dawo sai ta bar gidan nan kaji na rantse.

Mohsin yace gashi yanzu ashe kaina na nemowa aure ban sani ba,Naila tace yanzu baka da Sisi Yaya? Yace ae sai kayan kyau da wanka? dariya yayi tace Allah gwara ayoka mummuna a baka kudi,turo accnt number Yaya kaga kudin Daddy din Beauty ya bani ban kashe ba Kuma na samu wasu a wajen Spark Yana yawan bani kudi,ko bai bani bama sai nace ya bani rabona,yanzu sai da na Tara 50k,Banda kudin da su Dan Indo ke bani duk Tarawa nake yi,yace ke da zan kawo miki ni zaki bawa kina gidan yari,Naila tace Malam ka karba, ni I can survive macece ana so na a gidan Ina samu ba laifi,mene amfaninsu idan ban baka ba,Mohsin yace to Naila ai naji kunya,idan zaka karba ka karba ni da Kai akwai kunya ne Hallare ma ta kama ganin taka zanyi tsaf,zanci ubanki Naila tam,dariya tayi tace ka turo accnt karka bata min lokaci,ba a dade ba ya turo accnt,a cikin gidan yari suna da komai nasu sai taje Wajen masu POS ta tura Masa 50k din cass sannan ta koma dakinsu na malamai.

Spark yayi baki su Kamal sunzo suna fada Masa labari me dadi,yayi farin ciki matuka sai dai Kuma mummunan labarin Mummy suna fada Masa ta bude cin duniya da tsinke har kana nan kaya take sawa ta tsuke kamar Yar arna ta fice,itace gidan Shan shisha da Kuma yawo da kawayen banza suna cinye mata kudi,kullum suna gidanta sun tare,gefe daya Kuma tunanin Jamilu yake ta ya zai bar gidan ya barta,yace ai ko an yanke hukunci ni ba yanzu zan fito ba,Banga ta tafiya yanzu ba,su Kamal suka bude baki,yace ae ni yanzu banyi niyyar fita ba yanzu dadin gidan nake ji nafi nishadi a nan,Su Kamal haka suka koma gida da mummunan labarin cewar Spark yace Bai shirya barin gidan yari ba shi yafi son can,an Kuma rasa dalili sai Rafeeq ne ya tuna yace ai wlh a uzura Masa ya bar gidan ana yanke hukunci sabo da namiji yake so,kowa bai gane ba Daddy yace kamar ya? Rafeeq yace Gay yake so ya fara wlh wani Dandaudu yake kauna,yace ma shi zai aura,Mima zumbur ta mike tare da furta Yana hauka ne wlh dole sai ya bar gidan nan ana yanke hukunci,Kun san dai halinsa baya Jin magana ku San yanda zakuyi wlh ya bar gidan.

Chikar Gayu sai da aka dan yawata da ita taga gari,tace to kaini tasha aka kaita tashar mota,motar Kaduna ta shiga har ta shiga ciki tace na fasa katsina zanje yes Katsina zani na fara zuwa wajen Uwata tukun na dawo naje Kaduna din gwara na fara cin uban me unguwar layinmu sannan naje gidan Ubana,fitowa tayi ta canja tasha ta hau motar Katsina suka ware birnin katsina, bayan awanni ta sauka a motar ta biya me napep yayi parking a kofar gidan me unguwar Layin,taci sa'a a waje ta ganshi,a gabansa ta tsaya,ya zaci fatalwa ce ya ja da baya Yana salati harda faduwa a kasa Yana Nuna Chikar Gayu da hannu, Chikar gayu tace nice ba Aljana bace Dan gyatumin ubanka,ai dama nace zan fito sharrin daka kulla min to na fito,Mikewa tsaye yayi yace karya kike gudowa kika yi Kuma sai na sake kiran police sun Maida ke,shegiya Yar iska haihuwar kwararo.

Ubanka aka Haifa a kwaroro cewar chika,me unguwa ya jawo sandarsa wai zai kwalawa Chikar gayu ya zaci a baya ne sanda tana karama, Chikar gayu taci kwalarsa dama gashi wani Dan figigi ta yanka Masa Mari,Mutane suka taru a wajen ana labari Chikar gayu ta dawo, Me unguwa ya dafe kumatunsa yace ni kika mara? tana rike da kwalar me unguwan ta lakace Masa hanci tace an mareka,baka ga na girma ba to na balaga dattijon banza, ta zaro Masa idanu tare da furta balaga ce ta jawo, na rika na tatira na tumbatsa, tayi fatali da rawaninsa ta shake shi sosai,mutane suka taho suna cewa dan Allah Chikar gayu sake shi kina mace a unguwar Nan kowa yasan ke saliha ce,Chikar gayu tace duk Wanda ya rabamu Allah ya isa,kar Wanda ya sake ya rabamu wlh duk Wanda ya rabamu iyalansa ma sun shiga uku,mutane suna ta mamaki, wani a ciki yace Chikar gayu da a baya ko yatsa aka sa mata baza ta iya cizawa ba ita dai barta da gayu.

Chikar Gayu tace to yanzu gartsa yatsan zanyi,mutum ya sa min yatsan a baki ya Gani idan ban gartsa Masa cizo ba kafira nake, koma na fille yatsan,Kuma wallahi fada bai mutu ba bari naje na huta zanzo har gida sai na hanaka Shan ruwa a layin Nan,bari naje naga dangi zan dawo a Yar dabata zanzo,Me Unguwa yace sai na daure ki,ta hankada shi tana haki tayi cikin gidan Me unguwa mata suna girkinsu a murhu sai kawai Ganin Chikar gayu suka yi ta daki tukunyar tayi foli foli da ita abincin Dake ciki ya juye a kasa,Mata da yara sai kowacce ta nufi dakinta ta rufe,Chikar gayu ta duba kajin gidan gonar me Unguwa da yawa a katon cage Yana kiwo ta bude su tare da Koro su waje tace duk ku fice Dan ubanku,sai Kaji suka yo waje tatatata suka yo waje suna kuka kuyat... kuyat...kut..kutt..kut,ta kwance akuyoyin me unguwa ta Koro su waje kofar gida suma,fitowa tayi ta ce zan dawo ne sai ka fada min abinda na Maka kayi min sharri zan dawo ne,gashi Nan kullum tsiya tsiya da kai kana cikin birni kana kiwon akuyoyi gidanka kamar na kauye, daga yanzu gaba ni da ku har yarana da jikokina da iyali na,Me unguwa Yana dafe da kumatu Inda yasha Mari yace sai naga bayanki,idan har Ina sallah to ni Kuma sai na nuna Maka banje gidan yari a banza ba,gidan yarin da kayi sanadin shigata to Kai na shigarwa,idan ba Kai asararre bane muna alaka da Kai ta jini amma Kaine munafuki ko,zaka ga tantirin iskanci me maiko.
gidansu ta nufa ana ta cewa ga Chikar Gayu ta fito ga Chikar gayu.

Bayan kwana uku Beauty ma Allah yayi tayi sallama da kowa itama,ranar da Beauty zata fita aka kawo wata budurwar,Beauty tace yanzu duk ba kuka kike ba sai nan gaba zaki fada,ki saki ranki ki tsula tsiyarki Yar nan duk Nan mu da kika ganmu tantirai ne,mu da kanmu mun san ta wani bangaren ba kyau bama ji gidan masu laifi ai gidan tatirarrun Yan iska ne,budurwar ta Kalli Beauty kawai tana Jin wani kunya,Beauty ta Dora hannu a Kai tare da furta Laaaaaaaa Kunga kunya take ji cewar Beauty,su Azima suka ce da sauranta lallai,ke a Nan ba kunya Dan ubanki wallahi ki warware ko kici duka a gidan nan ba a mana kunya yanzu kyaji jiki cewar Azima da wata dattijuwa Yar duniya.

A ranar da yamma Beauty ta fita taje Wajen signing,ma'aikatan suna tayata murna,Beauty baki yaki rufuwa kowa ta gani sai gaisuwa Ina Kwana,idan ya amsa ma sai tace Dan Allah mu sake gaisawa Kuma gaisuwar da wani Shoky take kwasota ta duka ta kwaso tace Ina Kwana ta watsawa mutum shokynta,dariya ta dinga basu, Daddynta da kansa yazo daukanta suna ta murna ta shiga hadaddiyar mota suka tafi gida.

Naila bata San Spark shima Yana Shirin fita ba sunyi muguwar shakuwa kullum suna tare, tare suke yin komai Kuma Bai nuna yasan ba mace bace, Ranar da za a tafi dashi kotu ranar ya samu Naila a part dinsa tana zaune tana Shan lemo da cake,ya fito cikin shirinsa ,a gefe ya zauna a kusa da ita yace Jamilu zanje kotu,gaskiya ta bayyana akan sharrin da aka min

Naila zumbur ta mike tsaya tayi rau rau zata yi kuka,shima tsayen ya mike tare da rike hannayenta biyu ya bata labarin me Mama tayi, ya fada mata halin da ake ciki a nutse,ai Jamilu sai kuka sai kurruwa da burburwa,kasa ta sulale tayi zaman Yan bori tana tumami a kasa wayyo Allah na shiga uku kowa sai ficewa yake Yana barina,Ina zan sa kaina Beauty ta fita itama gashi kaima, hawaye rabe rabe a fuskarta sharkaf tana kuka harda shidewa tana furta way way way way ihihihihi wayyo zuciyata ta dafe kirjinta tana uban kuka,tausayi ta bawa Spark yace bance fa zan tafi na barka ba ka daina kuka,ya tasheta tsaye ta mike da kyar tana tangadi kamar Yar giya,rungumeta yayi a hankali a kirjinsa tana ta kuka Yana bubbuga bayanta a hankali,a nutse yasa hannayensa masu taushi tare da tallafo fuskarta ya shiga goge mata hawayenta amma wasu bulbulowa suke kawai, hannu biyu ta sa ta riko rigarsa gaban kirjinsa tayi baya da kanta tana rasgas uban kuka, yace amma da nasan haza zaka min bazan fada Maka ba,kayi shuru Jamilu,Naila tace sunana Naila ni ba namiji bane wlh, Spark ya kalleta sosai yayi dariya yace ai na sani tuntuni, kawai kallonki nake,tana shesheka ta furta yaushe ka sani a Ina? murmushi ya saki yace nasan kai mace ne ba tun yanzu ba sunanki ne kawai ban sani ba,Ashe sunanki Naila nice name,Naila duk a rude take tace na cire abinda nake daure kirjinta da shi taba kaji ni Macece,Spark yace ni da na kalla wai with my two Kworo Kworo eye,kallo fa nayi ni Kinga gani ya kori ji,ki bari na dawo zamuyi zancen,kici gaba da zama a jamilunki

Please Login or Register in order to submit comment