Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 5
ta daga mashi hannu bana son jin komai daga gareka ba xabi nake baku ba umarni nake baku idan hr baxakuyi bane sai kuyi gaggawar sanardani ynxu hussien yaxo da sauri ya rungume hassan, shima baiyi qasa da gwiwa ba ya rungumosa amma xuciyarsa a dagule take tunda baiga hamida ba atare suka saki juna ya dubi salma yana fadin hamida fa.... sai a lokacin suka lura bata nan hussien yace inaji taje gida ne.... bayan dawowarsu gida suna tare su biyu hassan ya dubesa yace koyamin ynda ake soyayya ynda kakeyiwa salma hussien ya dan dubesa ta wutsiyar ido kafin yace sai na koyama ne kai baka iya ba, tun xamanku gidan mekake mata ya yarfe hannuwansa yana yatsina fuska yace komai bana yi mata shiyasa take fushi ban taba xama tare da ita bane sannan itama inaji bata iyaba tunda taqi ta koyamin hussien ya kyalkyace da dariya, dariyar da ya jima baiyitaba tun fadansu da hassan ganin haka yasa hassan ya ciro masa wasu india films yana fadin xn fara kallonsune nima na iya soyayya ya qara tuntsirewa da dariya, hassan ya tunxura xai tashi ya riqosa yana fadin dan uwa maidasu tukunna sai munje munyo bikon hamida xaayi komai.... 62 A cikin daren sukaje gidansu hamida duk da basu sami hamidar ba amma umma tayi mamakin ganinsu a daren yau sai ga hassan anje inda umma an durqusa hr qasa ana gaidata abin yabasu mamaki matuqa hrdai ita ummar hussien yafara mata mgn kan abinda yakawosu umma tace duk da hamida taqi tagayamin dalilin dawowarta nace baxata koma gidan hassan ba dan bnsan wane irin xama take dashi ba hassan yace umma ba abinda nake mata fa kawai dan bana mata mgn ne ina fita gidan sai naga dama nadawo shikadai nasani ko hussien ya juya yana kallon hussien haushi kamar ya shaqe hassan yakeji sunxo gyara ya bata lamarin koda yake ya tuna halayyar dan uwan nashi bai iya boye damuwarsa ba ko sirrinsa shi komai direct yake yinsa yacigaba da fadin amma umma ayi haquri xn gyara nama gyara baxan qara barintaba duk inda xamuje tare xnje da ita, ya tashi yana fadin ina takene umma tana daki kafin umma tayi magana tuni ya shige daki tabishi da kallo cike da mamaki wai surukine wannan, baki bude ta dawo da kallonta ga hussien wnda saboda kunya kamar ya nutse wurin sai gashi ya fito janye da hamida tana gocewa yana roqonta hr falo da qarfi ta fincike hannunta ranta abace take kallonsa shikuma ya mariraice fuska wai shi lallashi yake ganin abin ba dama umma tace hamida dauko mayafi kibisa gobe hussien yaxomi. dake inason magana dake ta gyada kanta tana hawaye taje ta dauko hijabinta a harxuqe tafita yabi bayanta umma tadawo da kallonta ga hussien hr a ranta tasan hassan bashida nutsuwa shiyasa tayi shaawar hamida ta auri hussien [4:42PM, 12/22/2015] Pherty: shima ya tashi yayi mata sallama ya fice, a waje yasamesu suna fada shi lallai sai ya rungumeta a wurin ita kuma ta kafe taqi hussien yace kabari aje gida mana wai meyasameka hakane yaja dogon tsaki ya shiga motar itama hamida tashiga baya suka fice 63 Suna isa gidan bata sauraresu ba tayi shigewarta gida sai suka kebe da hussien cikin mota...... daya shigo gidan yaje sashenta ya sameshi garqame da makulli sai ya dawo ya xauna anan falon ya ciro films dinsa yana kallo [4:51PM, 12/22/2015] Pherty: washe gari cikin shirinsa ya fito na xuwa office yaje sashenta yayi saa a bude falonta yake sai dai bata ciki sai ya nufi dakinta tana xaune da littafin adduo'i ta ga shigowarsa sai ta dauke kanta daga garesa yace hamida baki shirya bane mekike jirane? da mamaki take kallonsa shirin me xnyi yace office xamuje tare bakiji mena gayawa ummanki bane nace baxan sake barinki ke kadai a gidaba duk inda xanje tare xamuje tace hrda office din? yace eh mana kuma hamida u ar not a caring wife ko dan girkinnan da mata kewa mijinsu da safe bakimin ba ko bakya sona ne? ta ajiye littafin ta tashi tana fadin tun farko danakeyima ai bakaci ynxu kuma danme xnyi yace yauwa hamida jiya kinqi bari na rungumeki nasan kina kunyar hussien ne, kibari na rungumeki ynxu i just want to feel dat thing.... ke bakima sani ba ranar danaje gidanku na riqa hannunki bakiji abinda naji bane shiyasa kikemin wulaqanci ya ajiye briefcase dinsa yana fadin come an hug my hermyderh....... Hausa novel Pherty: 64 TAGWAYEN MAXA Na fertymerh xarah Hermyderh ta dauke dubanta daga garesa ya maida hannayensa ya sarqe yace xakije? ta girgixa kata ba tare da ta kallesaba hakan yasa ya dauki briefcase dinsa ya juya bai sake kulataba bayan fitarsa ne da awa biyu hussien ya shigo tunda taxo gidan sai yau ta ganshi cikin gidan ya dubeta wani iri yace ki dauko mayafi kixo muje inda umma kamar yanda ta buqata a jiya hrta juya xata dauko sai kuma tadawo tana kallonsa tace bangayawa hassan ba,nima bnsan ynzu xamuyi tfyr ba yace karki damu kidauko kixo muje munriga munyi mgnr dashi ta juya taje ta dauko koda tafito hrya fita sai ta samesa a mota tashiga tym din dasuka xo ingawa bayan sun gama gaisawa da umma sai ya fita yabasu wuri domin su xanta lokacin umma ta dubeta da kyau tace hamida gayamin matsalar da kike ciki gameda aurenki,gayamin meya dawo dake jiya hamida ta sunkuyarda kanta qasa tana tsoron gayawa umma abinda hassan ke mata tunda ko banxa batasonshi sannan idan sukaxo suka shirya suka daidaita tasan umman xata dore da fushi da hassan sannan qiyayyarsa ma gareta xata qaru haka yasa baxata gayamata ba....tace kinyi shiru hamida kigayamin duk duniya bakida wacce tafini bakida wacce xata share maki hawaye kamar ni Pherty: Duk da Allah s.w.a yace LA TAJASSASU WALA YAGTABBA ADUKUM BAADAD kada kuyi bincike kuma kada sashenku yariqa cin wani sashe ma'ana kada wasu mutane su xauna gulmar wasu mutane musamman akan binciken mata da miji. hamida ta dubeta da hawaye a fuskarta tace umma ba komai, mun sami matsala ne kuma jiya bayan.mun koma yabani haquri umman tayi murmushi tace naji wannan hamida duk da xuciyata bata amince ba amma hasashenki najiya dakike fadar dole ya sakeki baxaki xauna dashi ba karna sakeji a bakinki saboda haramunne mace tanemi saki a gun mijinta batare da wai sababi ba sabod manxon Allah s.a.w duk matar da ta nemi mijinta ya saketa batare da wani laifiba tor ba ita ba aljanna....... ina gayamaki wannan ne ynxu saboda lokacin da kikayi auren ban gayamaki ba kiyi biyayya tare da qauracewa duk wani abu da kikasan baiso wajibine mace ta yiwa mijinta da'a manxon Allah yace duk mijinta daya kira matarsa xuwa shimfida sai ta qi xuwa hr ya kwana yana fushi da ita tor mala'iku xasu yita tsine mata hr xuwa wayewar gari, namiji dan lelene kamar yaron goye dole sai da rarrashi ballema miji irin naki da shagwaba tayi masa yawa dole sai kinsa haquri a xuciyarki da hakan xaki cimma ribar aure. 65 Ki tsare gsky aduk inda kike Annabi s.a.w na cewa na umarceku da yin gsky domin ita qofae acikin qofofin aljanna kuma na haneku da qarya domin qoface acikin qofofin wuta kuma mutum baxai kasance mai gsky ba hr sai an rubuta mashi a wurin Allah shi mai gasky ne kuma baxai kasance mai qaryabahr sai an rubuta mashi a wurin Allah shi mai qaryane sannan ita gsky da amana suna sawa mutum qima da kwarjini a wurin jamaa, inaso kiriqe gskyrki hamida ki kumasa tsoron Allah a duk abinda xakiyi. Pherty: Duk danasan kinada tsabta inaso ki qara akan wadda kike da ALLAH S.W.T yace shimai tsarkine kuma yanason masu tsarki kuma baya karbar aiki sai mai tsarki shi kuma tsarki bayayiwuwa sai ga mai tsabta duk mutumin da bayada tsabta tor addininsa akwai matsala Allah s.w.t yace acikin al qur'ani yaku dan adam kuriqe adonku yayin ko wacce sallah, wato anaso idan mutum xaiyi sallah yayi da kaya masu kyau masu qamshi saboda idan kana sallah kana tare da mala'iku su kuma tsarkakkune basa son qaxanta (tsabta nada muhimmanci jama'a) hamida ta dago tana kallon umman tata tace nagode umma kin gayamin abinda ba wandaya gayamin shi ina alfahari dake umma umma tayi murmushi tana fadin hussien na jiranki waje idan kindawo watarana xn qara gayamaki wasu abubuwa gameda xamantakewar aure. ta tashi tana murmushi tace tor umma....tayi mata sallama suka fice. 66 Tunda ta iso gidan bata xauna ba sai da ta tabbatar ta gyara gidan yanda takeso, ta kammala girkinta ta jera a dianing kana ta shiga wanka Pherty: sanda tagama wanka ta shirya t fito falo sai ta samesa ya fito sashensa da alama masallaci xashi ynda taga yana sauri tace barka da dawowa da hannu ya amsa mata ya fice da sauri sai itama ta koma daki dan yin tata sallar.... tana kan sallaya taji motsin shigowarsa ta tashi ta fito falon tasamesa xaune tace kaxo ga abinci.... ya dauke kansa daga gefenta yana fadin kyaleni ai na kyaleki ko kema ki kyaleni tayi murmushi ta xagayo ta bayansa ta rungumesa a kunyace ta dora kanta a wuyansa, ai kuwa saboda murna dadi kamar ya kashesa ya tashi yana kallonta da dariya yace wayace ki rungumeni ne? tayi far da ido tana kallonsa tace xokace abinci tukunna taja hannunsa suka nufi dianing a kusa da ita ya xauna ya shagwabe akan shi baxai ci abinci ba sai dai tabashi yaci haka kuwa tayi sai da ta tabbatar yaci ya qoshi ta tilasta masa xuwa yin wanka koda yadawo falonta batanan sai dai falon a gyare yake hr qamshi k tashi mai kashe jiki ya nufi dakinta yana lumshe idanuwansa yanajin sonta a xuciyarsa can ko ya hangota tsakiyar gado ido yasamata yaga tayimasa wani irin kyau da kwarjini sai sonta k fisgarshi da sauri ya isa gareta ya hau gadon ya fada jikinta cikin murya qasa qasa ya soma magana hamida ina sonki kece rayuwata yakai bakinsa a kunnenta yana fada mata maganganu masu ratsa xuciya da jiki(nidai pherty banji komai ba amma tunda tsegumine halamcy xata iya jiyoshi) ya sumbaceta a kunne tsigar jikinta taji yana tashi qamshin turarensa da sanyin dadi ya soma kashe mata jiki ko banxa yau yayi matuqar yimata kyau tanaji ya soma shafata yayi qoqarin kai bakinsa kan nata tayi saurin janyewa a raunane yace menene hamida pls hamida karkimin haka kece rayuwata karki barni tunda bakyaso i promise baxan sake miki ba amma kibarni na kwanta a jikinki tausayinsa taji ya kamata kuma koba komai mijintane yana da iko akanta,gaba daya ya karya mata xuciya taji wani sabon sonshi na fisgarta ta jawo hannunsa kamar qaramin yaro xo twiny(yanda take kiransa),xo ka kwanta nan ta dora kansa akan cinyarta tana shaqar qamshinsa yayinda ya damqe daya hannunta ya hada da nasa ya manna a fiskarsa tausayinsa taji kamar tayi masa kuka ahakan hr barci mai nauyi ya daukesa tana kallonsa tana tunani...sai da barcin yayi nauyi sosai sannan ta xame jikinta daga nasa ta kwantar dashi hade da lulluba masa blanket kana ta sauka taje ta kukkule ko ina ta dawo dakin ta kwanta kamar mai jira ya jawota ya hadata da jikinsa Asuba ta gari Hassan & Hermyderh Hausa novel 27 December 2015 at 08:18 · fertym [4:40pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [11:08AM, 12/26/2015] Pherty: 67 TAGWAYEN MAXA Na fertymerh xarah Washe gari da kyar ta xame jikinta daga nasa taje tayi wanka ta shirya ta nufi kitchen sai da ta kammala komai sannan ta nufo dakin lokacin ya tashi daga barci ta hau gadon tana fadin tashi muje ayi shirin office na shirya maka bathroom saura wanka kallonta kawai yake yana murmushi,ta langabar da kanta pls mana my twiny ta fada cikin muryar shagwaba ya lumshe idanunsa batare da yayi mgn ba, cikin murya qasa qasa tace twiny meyasa kakeson hamida haka ita ba kowa ba bamai kyau ba ko kudi amma kai gaka fari kyakkyawa bugu da qari mai kudi HANDSOME SMART WITH A GREAT PERSONALITY bayan xaka iya samun dukkan irin macen da kakeso ya jawota yana shaqar qamshin jikinta dana gashinta yace nikaina bansaniba but nasan hamida ta mai kirkice tanada tarbiya da ilimin addini tanada kula da boye sirrin mutum bayanshi bansan komai ba amma ina sonki hamida promise to be with me and make me happy forever tayi murmushi kawai hr acikin xuciyarta taji dadi ta riqo hannunsa suka sauko....... bayan fitarsa ne salma ta shigo gidan, a dan xamansu sunyi hira mai tsayi hr salma k fadin bani labarin yadda akayi hamida mekikaji cikin rashin sani mgnrta tace lbrn mi tace kina nufin komai bai auku jiya ba naganki normal.fa gayamin baimaki komai bane hr ynxu hamida tayi shiru kafin ta dubeta tace salma bari nagayamaki wani abun da baki saniba koda ace abin yafaru kobai faru ba baxan gayamaki ba cos sirrin mijina ne manxon Allah yace mafi sharrin mutane wurin Allah ranar alqiyama sune namijin da yake biyan buqatarsa da matarsa itama ta biya buqatarta da mijinta sannan dayansu ya watsa sirrin dayansu 68 Amma wannan abin yaxama ruwan dare a ynxu da yawa yan mata amare idan sunyi aure xakaji suna baiwa qawayensu lbrn abinda yafaru d mijinsu, ynxuma grup ake budawa na matan aure xallah aciki xakaji kowacce macce na fadin yanda ta kwana da mijinta(ba wai nace duka grup na matan aure ba)sannan inbanda mata suke mata ke bakisan mutum ba bakisan ko wacece ba haduwar internet xakije kina gayamata sirrinki kikasan ko ita wacce irice kikasan mayyace ko aljana saboda mutum ynxu baa shaidarsa hrdai wanda baka sani ba but for now mata sun dauki trust dinsu sunbaiwa matan internet suna dauka yanda suka kwanta da mijinsu suna gayamasu tor wlhy kudaina kuji tsoron Allah [11:35AM, 12/26/2015] Pherty: hamida tayi ajiyar xuciya tana kallonta tace nasani salma kinfi kowa damuwa da aurena kinaso na daidaitu da hassan amma ke meyasa bki gyra taki rayuwar aure meyasa kike hangen nawa auren bayan naki baki gyaraba, inafa sane keda bakinki kika gayamin hussien na nemanki kina qi tor meyasa kike haka meyasa kike hana masa haqqinsa alhali kinasonsa kika aureshi shine ma baya sonki annabi yace haqqin miji akan matarsa kada ta qauracewa shimfidarsa ta kubutar da ratsuwarsa sannan tabi umarninsa kuma kada ta fita sai da ixininsa sannan kada ta shigo masa gida da abinda yake qi a wata fadar ma yace mafificiya daga cikin mata itace maccen da mijinta idan yayi dubi xuwa gareta sai ta faranta masa rai ma'ana tayi masa murmushi idan ya umurceta sai tayi masa daa idan bayanan sai ta tsare kanta da dukiyarta.... 69 Sannan kin furta da bakinki cewa bakya masa girki sai dai kisa wata mai aiki tayi masa akan me salma duk abinda kikawa mijinki lada ne, kallonsa lada ne, murmushi lada ne,ki gyara masa shimfida lada ne, ki masa girki lada ne, kiyi masa shagwaba lada ne, kimasa kuka lada ne annabi yace idan mace ta wanke tufan mijinta Allah xai rubuta mata kyawawan ayyuka guda dubu ya shafe mata miyagu guda dubu duk abinda rana ta fudo akanshi yana nema mata gafara sannan a daukaka darajarta sau dubu Allah kabamu ikon yi amin k bakiji wata kissa ba inda Aisha R.A take cewa ya manxon Allah menene mafi haqqi acikin mutane ga mace? annabi s.a.w yace mijinta a wata fadar ma nana aisha r.a tace annabi ya kasance yana horo na da in daura towel yayi xoxayya dani alhali ina cikin jinin haila, dan haka mukula da haqqin miji akanmu musan irin yan dabarun nan na mata...... amma meyasa macce dan anmata auren dole ta riqa gallaxawa mijinta acewar wai dan bata sonshi, k namiji ya furta yana sonki ya wulaqantaki ballantana keda kika furta bakisonsa, aure anriga an daura ba yanda xakiyi ki rungumi qaddara ki rungumi mijinki ko kin rabu dashi kinxama qaramar baxawara kuma yasha dake koda bai maki komai ba [12:07PM, 12/26/2015] Pherty: ballantana wannan rayuwar duka duka nawace xai mutu ya barki ko keki mutu kibarshi idan mijinki baya yarda dake kin mutu kinje lahira dame xakiyi taqama, duniya makarantace ba gida ba an turomu karatune duk wanda yayi karatu mai kyau xaiga da kyau a lahira dama rayuwar aure xomu xauna xomu saba dole sai ankai xuciya nesa anyi haquri sannan komai xaixo da sauqi 70 Akwai inda annabi ya taba cewa da yar'sa fatima idan bakiyi hankaliba fatima sai wata macce anan gefen madina ta rigaki shiga aljanna fatima ta shirya taje gidan matar nan da nufin taje ayi mata kitso nan kuwa taje ne kawai don taga matar anan fa taga yanda matar take tsananin biyayya ga mijinta saboda da farko dataje tace naxone kimin kitso sai matar tace koma sai nagayawa mijina fatima ta koma da mijin ya dawo ta gayamasa yace haba dai kiyi mata mana diyar shugaban halittace fa. da fatima ta tashi dawowa sai taxo tare da hassan sai matar tace a'a ai ban gayamasa da hassan xakixo ba sai ku koma sai nagayamasa,daya dawo tagayamasa yace ya yarda da nana fatima ta tashi dawowa sai taxo da hussaini amaimakon hassan sai matar tace aini da hassan nagayamasa xakixo bada hussien ba dan haka kikoma sai nagayamasa, da mijin ya dawo ta gayamasa sai yace koda da duk yan gidansu xataxo tor kimata kitso da fadima taxo aka fara kitso sai ga mijin nan ya dawo matar ta turata daki ta rufe labule tace shige kada ki ganar min miji,fatima na kallon yanda matar ke girmama mijinta da tarairayarsa kuma annabi s.a.w bayagayawa fatima cewar matar xata rigata shiga aljanna dan ita fatimar bata biyayya bane aa sai dan ta dada sanin cewa girman miji agun matarsa ba abune mai sauqi ba (kuma ku qara akan ynda kuke masa) bama mace kawai ba hrku maxa annabi yace namiji shine mai tsayuwa akan matarsa shike da iko akanta a wata fadar ma yace ku tausayawa mata kuma ku kyatata masu babu wulaqantacce face mai wulaqanta mata,sannan babu mai girma face wanda ke gimama mata a wata fadar kuma antabayi annabi shin xama tare da iyalinka shi yafi maka ko kuma xama a massalaci? sai yace maxa sa'a guda kacal tare da iyalina shiyafi soyuwa gareni daga ittiqafi a masallaci....... salma ta dakatar da ita tatashi tana fadin ina xuwa saboda koda naxo nan gidanki batare da ixininsa bane idan yadawo yabarni anjima xandawo kafin hamida tayi mgn tuni ta fice sai ta bita da kallo kawai [1:42PM, 12/26/2015] Pherty: [1:37PM, 12/26/2015] Pherty: * 71 Tundaga tym din hussien yaga canji daga salma irin kulawar da take bashi yaxamana ya manta da hamida a xuciyarshi ya dawo ba wadda yakeso kamar matarshi salma Hassan an sami abinda akeso kullum ana maqile da hamida komai hamida ko ina yaje hamida farinciki kwanciyar hankali daukaka ya sauka a TAGWAYEN MAXA bama suka dai ba hr iyayensu kuma suna masu yi masu fatan alheri da addua Allah ya cigaba da kawo masu farinciki a rayuwarsa salma ta fara haihuwa tasami duka mata twins, wata biyu tsakani hamida ta haifo nata twins aka sami wasu TAGWAYEN MAXA ranar biki anga qawaye iri iri bama kamar halamcy da baa gayyataba, amma su sady, miss aysher, xarah dange, matar saif, ammi lurv, kdeey, baby aysher da kausar,unique da hssina, mamu da namcy, sally,m.boy, mahasin da nusee da duk wanda ban fada ba yayi haquri ban manta dashi ba yana raina hrdama masoyan tagwayen maxa da duka members dina gabaki daya duk a hangosu HAUSA NOVELS 1,2&3 NISA'UL JANNAH 2 MATA MASU DUNIYA TASKAR MARUBUTA MATAN KWARAI UNIQUE NOVELS duk ban barku baya ba da duk wani grups ma Na sadaukar da wannan littafin ga Ammi Bari'ah marubuciyar AMARYAR PHERTY da PHERTY 72 Shin addini yayi gsky da yace ba lallai bane ka sami duk abinda kakeso ba arayuwa ka xauna lfy kamar yanda ta faru da SERLYMERH (makauniya)...... Yaushe ne soyayya takeyin tasiri a xuciya ta wanxu batare da sanin juna ba wanda daga humayd hr afra baxasu iya fassarata ba a littafin AFRA HUMAYD..... Soyayya ba lallai ta faru a sanda akaso faruwarta ba ita wata irin abace daba ruwanta da lokaci matsayi da dangoginsu abuce wadda k faruwa a duk sanda taso ta gudanar da tunani ta sarrafa gngar jiki kamar yanda tayiwa ZARAH da Dr.Saifullahi Bakori Ta taso cikin tarairaya gaa da shagwaba a gidan arxiki mulki da bunqasa , babu abinda tasani sai taqama isa da wulaqanta dan adam haduwarta da Bilal ya sauya mata raayi inda duk isarta mulkinta dataqamarta suka xube a qasa IHSAN Haduwar kan hanyace ta xamo haduwar xuciyar Abdulsalam da Falmata ,aminci, tausayi, soyayya, ha'inci da xalunci sune suayi gingimemen gini a rayuwar ALMAJIRA Abin tambaya acikin rayuwar JIDDAH meyasa kowacce bata auri wanda takeso ba amma ta samo soyyaya a gidan aurenta mami da jidda Soyayya ko sadaukarwa wanene yafi rinjaye a rayuwar AFNAN tsakanin Adnan da Affan Pherty tace xata iya fassara ta ta soyayya da defination mai yawa a LABARINA wanda neither Dr.fulani Gafai nor Marhoom experience it. Dariya take sosai ba kakkautawa kafin ta tsaida dariyar tana kallonsa tace ka ceto ni daga cikin wani hali dana shiga duk da cewa kaine sanadin haukata kuma kaika dai nakeso nake kishi baxan iya kwatanta ganinka da wata macce ba.... Humayd Danbatta yayi murmushi hade da rungumota yace ba wadda nakeso nake qauna a duniyarnan kamar ke bakida kishiya ke kadai kin isheni rayuwa kuma bake ba hauka har abada ina sonki HERLYMERTU Menene sirrin pherty, miss aysher da serdy daya janyo suka xamo taurari masu haske da walqiya a xukatan xaratan maxajensu koda yake sun auresune bisa tubali na soyayya SADTEEYASH TAGWAYEN MAXA ne,kamanni daya amma mabambanta a halayya da dabi'a duk da kasanvewarsu gida daya amma they ol acting according to their experience,xamansu da Hamida ta sauya tunaninsu daga marar kyau xuwa mai kyau.... Daga inda pherty take xaune ta maido hankalinta ga jinin sarauta inda taji yana roqon Affiya kiyi haquri na tuba kece rayuwata qasaita ta a waje take baa gida, idan a gidane affiya keda qasaita ita keda ragamar komai nawa. ta juyo tana kallonsa da murmushi tace hrda MULKI KO SARAUTA? ya gyada kai yana murmushi ALHAMDULILLAH Qarshen littafin TAGWAYEN MAXA Much luv to.masoyan littafaina da duka members dina na pherty Novels An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 5 of 5