Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 5
fadin kuma xaa cigaba da biki baxaa dakatar ba saboda munada tabbacin yaronmu yana raye da ixinin Allah kuma xai tashi, Alhaji jafar da Alhaji ismail sukayi murmushin jin dadi lokaci daya kafin su fita a tare uncle na bi bayansu, umma jikinta a sanyaye takalli kawun hamida tace kada ka manta hussien na bawa hamida dashi nakeson tayi rayuwa, kawu ya gyada kansa kawai suka fita gabaki daya hussien ya juyo yakalli dan uwansa har lokacin baisan abinda ke faruwa ba ya girgixa kansa kawai yana hawaye ya juya ya fice [11:26AM, 12/1/2015] Pherty: Gidajen radio, t.v, jaridu e.t.c aka shiga yadawa da sanarda daurin auren TAGWAYEN MAXA, hassan da hussien, cikin mintunan da basu wuce arba'in ba qatoton harabar gidan Alhaji jafar ya cika da mutane iri iri kala kala tundaga yan uwa, abokan arxiki, qawaye ba wanda bai hallara ba, nan take aka daura auren HUSSIEN DA SALMA, HASSAN DA HERMYDERH, wanda hussien ne ya nemi wannan alfarma , 48 An dade ana kacaniyar daurin auren kafin su qaraso asibitin hr lokacin matan basu san ya daurin auren ya kasance ba illah hankalinsu dake tashe saboda farfadowan hassan yana aman jini, Dr.merah naganin yanayinsa yasa aka shiga dashi emergency da gaggawa, yana tafe da sauri ana cire masa alkyabar jikinsa tunda baxai iya cirewa dakansa ba dole sai ancire masa saboda girman qasaitarsa, gab da xai shiga dakin emergency suka gama sanya masa labcoat dinsa suka bude masa qofar ya shige duk suka tsaya a waje suna jiransa, hankalinsu a tashe sunyi tsaye cirko cirko ko wane xuciyarsa bugawa take kamar xata bullo qirjinsa tafito, da sauri duk suka juya suka bar asibitin suka nufi masallaci, arwallah sukayi suka shiga domin kai buqatarsu da kukansu ga ubangiji talikai, Allah ka biya mana buqatanmu ya rabbi!, awa biyar cur suka dauka kafin su sami numfashinsa ya dawo dai dai Alhmddlh komai ya dai daita sai dai yasami barci, kai tsaye aka nufi aminity dashi qafafuwansa duk daure da bandage, ganin komai ya lafa yasa mai gari ya tarasu duka yayi mgn da tattausan lafaxi tareda bawa kowa haquri akan yanda auren ya kasance dan shima a ganinsa hakan yayi dai dai, umma kamar ta hadiye xuciya taji, wuf ta tashi ta fice daga asibitin ta nufi ingawa, salma kuwa dadi kamar ta mutu dama batada gwani aciki kowanensu tana so, yayinda fargaba tasa hamida a gaba jikinta sai faman rawa yake har wani xaxxabi takeji ganin ummanta batayi maraba da auren ba. 49 Sati biyu jikin hassan ya soma sauqi sai dai har lokacin daga kallo bai furta ko wacce kalma ba hassalima baisan meke faruwa ba illah ya tsani kowa a asibitin ba kamar momynsa da hamida ba wanda yake ganin ta dalilinsu ya tsinci kansa a wannan halin, ganin samuwar sauqinsa yasa Alhaji jafar da Alhaji ismail suka tada mgnr bikin aure , anata shirye shiryen biki anyi biki kala kala ankashe naira, ranar da xaa kai amaren xuwa gidajensu uncle yayiwa hassan bayanin komai sai dai ga mamakinsa hassan bai nuna wata alama tajin dadi ko rashinsa ba illah lumshe idanuwansa da yayi kawai, daren ranar da xaa kaisu ake dinner taro yayi taro a qaton hotel din kaya iri daya amaren suka sa wanda uncle yayi masu kayan biki shikuma Alhaji jafar ya gina masu qatoton gidaje guda biyu komai iri daya ciki da waje hatta kayan dake ciki duk iri dayane sai banbancin kala wanda anan ra'ayinsu ya banbanta, gidajen suna kallon juna basuda tserayya mutane har xuwa kallon tagwayen gidajen ake masu matuqar kyau da tsari, Alhaji ismail shi ya dauki nauyin auren tun daga kan sadaki,lefe kayan aure da sauransu duk shi yayo odarsu a waje, taro yayi taro suna xaune su uku sun sanya hussien a tsakiya duk acikinsu salma ce kawai k farinciki yayinda xuciyar hussien a dagule take na rashin dan uwansa a kusa dashi ana hidimar ba hassan, hamida ajima ajima take sharar kwallah musamman idan ta daga kanta ta dubi hussien da tashi amaryar ita kuma banata angon bugu da qarima ance baxai iya tfy ba, ta fashe da wani matsinancin kuka dai dai lokacin taji wurin ya dauki shiru lokaci daya taga hussien ya miqe tsaye tare da salma, sai ta janye hannunta daga fuskarta itama ta miqe ta maida kallonta dai dai inda taga jamaa na kallo, yana tsaye kishingide a mota hannunsa riqe da sanda irinta masu mulki idanunsa boye acikin dark space ya xare madubin fuskarsa ba yabo ba fallasa, hussien ya isa wurinsa da sauri yana dariya ya rungumesa yayinda hamida ta rasa yanda xatayi lokaci daya tasaki kuka da dariyar farinciki. Hausa novel [5:00PM, 12/22/2015] Pherty: [5:09PM, 12/12/2015] Pherty: TAGWAYEN MAXA Na fertymerh xarah A hankali ya dauke dubansa gabhamida yamaida kallonsa ga hussien dake rungume dashi hussien ma kallonsa yakeyi yace hassan meke damun kane meyasa kake bata rai, yau ranar farinciki ce kasami lfy kuma hamida ta xama matarka hassan ya bata fuska yana yatsinata yace ashe dakai xaa hada baki aci amanata hussien ya saki baki cike da mamaki yace ban fahimci inda ka dosa ba [5:27PM, 12/12/2015] Pherty: yace meyasa aka aura min hamida, meyasa aka bani ita bayan ance bnda mutunci bnda tarbiya bata dace dani ba,( hawaye fal a xuciyarsa ya nuna qirjinsa da dan yatsansa)yana fadin ni ake wulaqantawa akan mace, macen ma yar talakawa wadda nafita da komai, ni ake gorantawa tarbiya ake cimin fuska dan kawai nace ina son yar aiki, tor na fasa bana.......huss ien yayi saurin toshe masa baki cike da bacin rai idanunsa sunyi jawur yake kallonsa, tun kafin yayi mgn hassan ya janye hannunsa daga bakinsa a fusace cikin tsawa yace kabarni nayi magana ina ruwanka dani ne? cikin fusata hussien yace na barka kayi magana ka fadi duk abinda kakeso ka fada, ka toxarta aurenka a idon jamaa, ka nunawa duniya cewa dole akama ba raayinka bane..... 51 Hamida dake qarasowa inda suke cak ta tsaya lokacin da kalaman hassan na farko na daki kunnenta, nan da nan farin cikin fuskarta na kau, ta tsaya cike da mamakin kalaman da hassan ke jifarta dasu duk qoqarin data nuna akansa, da irin soyayyar da take masa, da son hussien data danne a xuciyarta saboda qaunar da take masa amma da abinda xai saka mata dashi, ta juya taga jamaa sai kallonsu ake ta sunkuyar da kanta tana share hawayen idanunta cike da takaici ta juya tabar wurin hassan yaja numfashi tare da iska kafin ya furxar yana wani huci cikin takaici yace tor meye damuwarka konayi, meye naka idan na wulaqantar da aurena da kai aka hada baki akaci amanata hussien yace auren hamida shine cin amanarka ofcourse ya bashi amsa idanunsa akansa cikin bacin rai hussien yace control ur temper, yace anqi ayi cikin tsawa yace qarya kakeyi, qaryane kace bakason hamida a ynxu, qaryane kace xaka cutar da yarinyar danakeso tamkar raina na barmaka ita,qaryane kace xaka taxarta hamidata a idon jamaa kuma qaryane kace xaka qaryata soyayyar da kake mata qaryane! qaryane!! qaryane!!!(ya cakumo wuyan rigarsa) stop pretending,now tell me why did u betrayed her? [5:48PM, 12/12/2015] Pherty: hassan yayi qoqarin janye hussien daga cakumar rigarsa da yayi nan kokuwa ta barke tsakaninsu(na shiga uku) mutanen dake gurin sukayo kansu da kyar suka rabasu, uncle ya qaraso wurin cikin tsawa ya dakatar dasu cike da bacin rai yaja hannayensu ya nufi mota dasu kai tsaye gida suka nufa a falo suka taradda momy, yanda tagansu yasata faduwar gaba ta tashi daga inda take xaune tayo kan hassan tana tmbyrsa lfy meya samesa shida baida lfy sai kuma tayi kan hussien tana tmbyrsa, duk suka dauke kansu daga gareta kowanensu fuskarsa ba annuri 52 cikin tsawa uncle yace kunmin tsaye duk ku xauna, lokaci daya suka xauna kamar basu so suna tunxure tunxure yace hjy kigayamin dama yan biyu na kokuwa da juna ne? hankalinta yayi matuqar tashi ta xaro ido cike da tsoro tana kallonsu jikinta hr rawa yake kafin tamaida dubanta ga uncle tace a'ah sau daya ne kuma tun suna yara amma bn sani ba ko sunayi a skul xamansu a cairo, fada sukayi ne? yace kunji kunya sakarku,kun ban mamaki kuma kun nunamin ku cikakkun yan iskane bama kamar kai hassan(ya nunasa da yatsansa) hassan ya tunxure baki yana sunkuyarda kansa yace ka tashi ka dakeni ko kuma nima kayi kokuwa dani tunda kayi da hussien tunda ya gayama gsky,yafi kaxauna kanamin qunquni, kuma wlhy summa tallahi tunda na rantse ko kaso ko kaqi sai ka xauna da hamida kuma a yau xaa kaita gidanka idan kuma kaqi wlhy bani bakai kada ka sake kallona a matsayin qanin mahaifinka, ya juya ya fice daga gidan hassan ya tashi yana daga kafadunsa yace so what, tor sai me tunda kai ba ubana bane me k..........yayi shiru sakamakon marin da momy ta daukeshi dashi, ta cakumosa ranta a bace tace menakeji hassan, mekake fadine, shi uncle din daya xama uba agareka hr kake butulce masa kake gayamasa mgn irin wannan inda yaji mekake tsammanin xai faru [6:06PM, 12/12/2015] Pherty: ya fashe da kuka hade da janyeta daga jikinsa, tor mexai faru,kowa damuwarsa yasani bnda tawa,kowa kansa yakeso bandani,dan kawai nayi accident nasami tangarda a qafana ina dingirsa shine baa sona ynxu komai nayi bnyi dai dai ba har akemin kallon nakasasshe xaa aura min yar aiki, nace banayi ko dolene? saboda tsananin raxana da mamaki jikinta hr rawa yake bakinta a bude ta juya tana kallon hussien daya xuba mashi ido, tana qoqarin gyara xaninta dakeson kwancewa saboda raxana tace hussien meke faruwa me hassan ke nufi, ban fahimcesaba cikin tausasshiyar murya hussien ya bayyana mata komai dake faruwa kamar yayi kuka saboda bacin rai ta juya tana kallon hassan idanunta fal da hawaye tace hassan kodai lasami matsala ne a.kwakwalwa, ko giyar da kake sha ta taba kwakwalwarkane? garau nake momy, hawayen da take maqalewa suka xubo mata tace sakayyar da xaka mana kenan, duk halaccin da akama id....ya katseta kiyi shiru momy hamida munafukace hussien take so bani ba nagani a kwayar idanuwanta duka su biyu suna so suci amanar aure nane hussien ya xaburo xaiyi cikinsa momy ta taresa tace kabar shi hussien kabrshi, ya nunosa da yatsa yana huci yace karda kasake kiran hamidata munafuka, kaine munafuki mayaudari wanda baisan darajar soyayya ba baisan haqqin dan adam ba, idan batason ka sai me? k....momy ta rufe masa baki 53 Tace kayi shiru hussien, hamida ynxu tana da aure matar dan uwankace, bai dace ka danganta wasu kalamai akantaba a ynxu,kabarshi idan kasheta xaiyi yaje ya kasheta amma idan na isa garesa kuma ni mahaifiyarsa ce inaso ya xauna da hamida a matsayin matarsa, sai a lokacin hawaye suka xubowa hussien,wani iri yakejin kansa yau shine yayi fada da dan uwansa hrda kokuwa kuma akan macce,ya girgixa kansa yana cigaba da hawaye yace nadaina momy daga yau, insha Allahu baxan qara mgnr hamida ba baxan qara shiga lamarin hamida da hassan ba koda ya cutar da ita,kuma daga yau duk wani abu da ya danganci hassan na daina shigarsa nafita hanyarsa shima yafita nawa,ya kyaleni baruwansa dani kuma yafita rayuwata kamar yanda xnbar rayuwarsa a duk abinda ya shafi rayuwarsa, ya juya ya fice momy na kiransa amma yayi mata banxa kamar baijiba ya fice da sauri yana kuka [6:44PM, 12/12/2015] Pherty: ta juyo tana kallonsa ranta abace amma shi ko ajikinsa ya qara daure fuskarsa yace momy idan kun sake haduwa dashi kigayamasa nafita rayuwarsa yafita nawa,nima ba ruwanshi dani ko a hanya kada ya sake ya nuna ni dan uwansa ne ko inada alaqa dashi saboda na kwance ta aynxu shima ya juya ya fice TAGWAYEN MAXA sun mata abinda bata tb tsammaniba,taya xata yarda su raba kansu bayan tare aka haifesu suka xo duniya suka rayu tare komai tare sukeyinsa sai ynxu saboda mace xasu raba kansu xasu yanke dangantakar junansu ina baxai taba yiwuwa ba baxata aba yarda ta xuba masu ido ba, jikinta a sanyaye ta nufi bedroom dinta cike da tashin hankali 54 * da dare kamar ynda uncle yace haka kuwa akayi, a qaton gidan cikin jerin tagwayen gidajen aka kai kowacce amarya gidanta, tym dinda alhaji jafar,ismail, da uncle sukayi neman angwayen su masu nasihohi basu samesu ba sai daga baya suka sameau daya daya suka masu badan komai a basuson su haduba sai dn kr suga junansu bayan qawaye sun raka angaye kowane gidansa sun watse, hussien yayi qarfin hali shiga inda salma yayi mata sallama hade da ajiye mata ledar da ya shigo da ita kana ya juya ya fita yabar dakin kai tsaye dakinsa ya nufa, ya fada kan luntsumemen gadonsa yana tuna hamida batashi bace ynxu taxamo ta wani hr yake wulaqantata...yayi saurin kauda tunaninta cos ynxu taxamo matar wani,ya qudundune tamkar wani mace acikin lallausan blanket [6:55PM, 12/12/2015] Pherty: * Gogan kuwa da kwalbar giyarsa ya shiga gidan, yana tafe yana sha, tun bayan watsewar angaye da qawayenta ta sauko tana kallon gidan bata taba ganin gida mai kyau da tsari irinsa ba ta window ta tsinkayo dayan gidan suna facing juna komai iri daya ba banbanci tagwayen gidajen sunyi matuqar birgeta, amma me batajin dadin gidan tunda mai gidan ya nuna tsanar ta a fili bayan a baya ya nuna mata so fiye da tunaninta, ta boye damuwata ko ummanta bata gayamaba tunda dama bata son hassan kuma umman ta gargadeta tunda ta kafe akan hassan lallai idan matsala ta taso tsakaninsu kada ta tunkareta kada taxo mata da wata matsala indai akan aurentane da hassan, tuno wannan kalami na ummanta yasa ta sullale na qasan falon tana kuka kamar ranta tana cikin kukan ne ya shigo yana tangadi, yanayinsa ya tsoratata batayi xaton an koma gidan jiyaba a tunaninta komai ya kau ya daina shaye shaye ashe kallon kitse takewa rogo, daga inda take tsaye yaxo shiga sashensa ya taka mata qafa da takalminsa ta dan saki qara cike da xafin dataji amma bai kulataba yi yayi da dai da duniya kamar babu halittarta ya shige part dinsa ya bugo qofa jikake gau..... Hausa novel [5:04PM, 12/22/2015] Pherty: [9:59PM, 12/14/2015] Pherty: TAGWAYEN MAXA NA Fertymerh xarah Da jan qafa ta isa dakinta, tsakiyar dakin ta xube, kuka take sosai kamar ranta xai fita, washe garin ranar ta kira ummanta kusan sau uku koma fiye da hakan bata daga ba hankalinta yayi matuqar tashi sosai, tafito daga wanka daure da towel taji ana buga gidan da sauri ta xira qaton hijabinta ta fito, bata bude falon ba sai da ta tambaya waye, muryar maigadi taji na magana cikin hanxari ta bude masa qofar tana kallonsa bayan ta gaidashi breakfast ne momy ta bada akawo masu ta karba tana godiya, ya juya ya nufi bangaren hussaini. tana jera kayan kan dianing taji motsin saukowarsa kan step da alama tashinsa daga barci kenan, kayan barcine ajikinsa pyajamus, ta dauke dubanta garesa tana cigaba da aikin da yake isowarsa wurin yasa ta dakatar da abinda take ta gaidasa a raunane bai amsaba bai kuma kalletaba illah yatsina fuska da ya somayi yana kallon dianing waye yayi girkin? momy ta bashi amsa a taqaice yace fyn an gud kana ya xauna ya soma ci batare da ya kulata ba, tsayuwa ta gagareta hakan yasa ta juya a sanyaye ta nufi dakinta cike da mamaki itadai a iya tunaninga batasan tayi masa wani laifiba batasan dalilinsa na tsanarta a ynxu ba alhali ta sadaukar da farin cikin mahaifiyarta saboda shi, tana hawaye ta shige dakinta 56 Wata biyu ba abinda ya cnxa daga xamanta tare da hassan kullum tana xaune cikin kadaici ba, lokaci daya duk ta xame ta xama wata iri sanda take yar aiki ma tafijin dadinsa akan yanxu dan ma salma na xuwa ta debe mata kewa amma ita konan da falo baya barinta xuwa ballantana sashen salma tana mamakinrashin jituwarsa da hussien duk da batasan mafarin fadan ba amma ayanda tasan tagwayen maxa batayi tsammanin akwai abinda xai hadasu ba duk da abin ya shafeta ko taga hussien ta gaidashi baya amsa mata hassalima ko kallonta bayayi sai dai yayi shigewarsa ya barta ummanta kuwa da alama ta mantata duk yanda takirata bata dagawa gashi hassan ya hanata xuwa ko ina gwandama momy na xuwar masu idan tasami lokaci xaman ta da hassan sai dai muce Allah ya gyara cos hali bai cnxa ba yana shan giyarsa, idan ya fita aiki baya dawowa sai 6 idan ya dawo ba ruwansa da ita baya kulata xai qara wanka yayi shirinsa ya fice sai dare wataran ma batasanin dawowarsa, duk ta rame taxama wata iri gwani ban tausayi hrta soma dana sanin xabensa da tayi [10:16PM, 12/14/2015] Pherty: kamar kullum kusan magrib salma ta shigo gidan itama a boye take shigowa hussien ya hanata, tace hamida ga wannan kiyi amfani dashi yana da kau kuma yana gyara jiki cikin rashin fahimta tace menene wannan? tace na matane yana tada shaawa sosai idan yaxo kishiga jikinsa koshi qarfene dole ya kulaki amma kin xauna a gida kamar dutse bakida mamora ke kika kyalesa wlhy, nima hussien ya dauko min wannan rashin mutunci amma sai dana saki jiki na shigesa sosai kinga duk duniyarnan ba macen da yakeso kamar ni dam gaban hamida na soma faduwa tayi rau rau da idanu kamar xatayi kuka tace salma ni ba wannan ne damuwata ba sakin fuskarsa nakeso inaso yadawo da kulawarsa gareni kamar da inaso ya taimakamin wajen bawa ummana haquri, nifa bana cikin dadin rayuwa baga miji ba baga uwata ba salma tasaki ajiyar xuciya cikin tausayawa hamida tace nasani hamida mun xama daya nidake banason na cigaba da ganinki haka, kuma namiki alqawari gobe xnje inda ummanki insoma bata haquri, amma inaso kisani shima hassan yanada haqqi akanki kamar yanda kike da nasa, dama xaman aure haka ya gada dole sai ana samun haka, idan shi ya hau kesai ki sauko hamida ta sunkuyarda kanta kawai salma ta cigaba da fadin, inaso ki kwaci yancinki da kanki hamida, kisha wannan maganin wlhy baxan maki abinda xai cutar dake ba, kiyi wanka ki feshe jikinki da taurare mai sanyin qamshi kije dakinsa kijirasa.... hamida ta xaro idanuwa tana kallonta tace so kike nayi kwanan asibiti yau salma tayi shiru kawaikafin tace baki yarda dani ba kenan baki yarda da abinda nake gaya maki ba kenan kinason ki dore a hakan bakida wani amfani a gidan dake da babu duk daya a gunshi, kina xaune watarana xakiji yayimaki kishiya nan da nan hamida na soma hawaye batada wani xabi illa ta amshi maganin tasha 57 sun jima nan xaune salma nabata shawarwari game da xamantakewar aure, kiran sallar.magrib ya tadasu salma ta nufi sashenta da sauri kada hussien yaxo bai sametaba, itama hamida ta haura sama duk jikinta ya fara sanyi idanunta sai lumshewa suke [10:27PM, 12/14/2015] Pherty: A daddafe ta qarasa sallah, wani irin yanayi takejin kanta, abu takeji tun daga tsakar kanta hr tafin qafafuwanta, tunda take bata taba tsintar kanta a irin wannan yanayiba, shaawa ta tasomata sosai, ta kwanta sai faman juye juye take kafin ta fashe da kuka da tasan haka maganin yake da bata sha ba, ita a tunaninta na gyara ne kamar yanda salma ta fada mata, ta sauko daga saman gado, kitchen ta nufa ruwa kawai takesha ba adadi, ba sauqi abin hakan yasa ta fito harabar gidansu dai dai lokacin mota ta kunno kai harabar gidan, yana fitowa ta nufesa, idanunta a juye sunyi jawur ta qanqameshi tana kuka tana roqonsa ya taimaketa hankalinsa inyayi dubu ya tashi ya soma kiciniyar kwaceta daga jikinsa cikin tsawa yace keee hermyderh me kike hakane kinada hankali kuwa, hussien ne ba hassan ba ki bude idanunki kwata kwata bata cikin hayyacinta bata fahimci komai daga maganarsa ba illah qara fashewa da kuka datayi tana qoqarin shiga jikinsa dai dai lokacin motar hassan na shigo gidan nan hankalin hussien na tashi musamman lokacin dayaga hassan ya fito daga motarsa, ya soma kiciniyar rabata da jikinsa amma sai qara manne masa take a harxuqe cikin bacin rai ya kai mata wani gigitaccen marin da ya janyo hankalin hassan garesu qara tasaki sosai sai ga salma ta fito a guje, ragwaf ta fadi wurin a sume bakinta na fitar da jini,lokaci daya hassan da salma sukayo kanta a rude..... Hausa novel 22 December 2015 at 17:22 · [4:39pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: Edit · Delete Fertymerh Usman > fertymerh xarah novels [1:50PM, 12/26/2015] Pherty: 58 : TAGWAYEN MAXA Na fertymerh xarah Hussien yaji uwa ya dora hannu aka ya saki ihu ya shiga tashin hankali hr xufa ke karyo masa mussaman lokacin da hassan ya dauki hamida cak ya nufi motarsa da ita, salma na biye dashi hankalinta a tashe sai hawaye take wani kallo da hassan yayi mata yasanya ta dakatawa da nufin shiga motarsa tana kallo ya figi motar a xuciye saura qiris ya kwasheta yabar gidan salma ta qarasa gun hussien ta cakumo wuyan rigarsa tace kagayamin mekayiwa hamida meyasa ka daketa? ya janyeta daga jikinsa kwata kwata baya cikin hankalin kansa halin da hamida take ciki yake kallo duk wani tsumi nata ya taso masa sabon feelings yakeji game da ita ayau da jikinsu na hadu cikin mutuwar jiki ya bude motarsa ya shiga itama salma da sauri ta shige...... [9:05PM, 12/19/2015] Pherty: * kusan minti talatin kafin ta farfado lokacin momy ma ta iso tace sannu hamida, hamida ta lumshe idanuwanta tana tunano abinda yafaru salma taci amanarta ta cuci rayuwarta datasan qudirin salma kenan akanta da bata amince da itaba, gashi abinda ta janyo mata(hawaye suka xubo mata) meya sameki hamida,kukan me kike?acewar momy salma taxo ta riqa hannunta tace laifinane amma kiyafemin hamida bnyi dan cutardake ba hassan ya qaraso fuskarsa a murtuqe yake kallonta yace laifinkine, kigayamin mekika mata mekikayiwa matata wato baki kuka hada da axxalumin mijinki dan acutar da matata ko? ta girgixa kanta tana hawaye hussien na tsaye bai tankaba amma ransa yayi matuqar baci momy tace salma mekika mata ne? ta soma sheshshekar kuka tana inda inda, hamida ta tashi xaune ta xare drip din da aka samata bata damu da jinin dake xuba a hannunta ba ta sauko menene haka ina kuma xakije? cikin kuka tace gidanmu xnje inda ummana,inason ummana inajin saboda tana fushi danine na rasa jin dadin aure, naxabi hassan akan ummana amma ya yaudareni sai ta fashe da kuka hassan yace nooooo hamida ba yaudararki nakeyiba c'mon momy kice tadaina wannan kukan banaso ina fushi da itane saboda hussien 58 Amma hamida kigayamin gsky meye tsakaninki da hussien meyasa naganki yau ajikinsa? ba hamida ba gabaki dayansu tmbyr ta girgixasu, baki bude idanunta na xubar da kwallah take kallonsa hussien yace sharrin da xakamin kenan, bayan qiyayyar dakakemin hrta kai kamin sharri da matarka hassan ya yatsina fuska hade da daga masa hannu yace bada kai nake magana ba matata nake tambaya kamin shiru? ya juya yana kallonta yce hamida kigayamin gsky meyasa naganki yau ajikinsa me...... momy ta katsesa a harxuqe tace yimin shiru banxa, mekake nufi kada kace kana xargin dan uwankane da matarka, na shiga uku ni Asma'u sai ta fashe da kuka stop crying momy,ba qaxafi bane nagansu da idanuna i knw hamida baxata ci amanata ba saboda nasan halinta, shikuma halinsane neman mata..... hussien ya soma hawaye xike da qunan rai ya kasa gasgasta cewa dan uwansa ne hassan yau k hantararsa, duk fadan da suke da hassan haquri yake yana jure rashinsa amma baxai iya rayuwa bashiba yariga yaxamo wani bangare na jikinsa amma gashi hassan ya tsanesa saboda mace yakasa yardarwa xuciyarsa ya rufe fuskarsa da tafin hannuwansa duka biyu ya xube yana kuka, kuka mai tsuma jiki hr cikin xuciya hassan kejiyo kukan amma saboda bacin rai yasa yaqi nunawa cikin wani irin yanayi salma ta riqo hassan tace ba laifinsu bane laifinane kada ka xargi dan uwanka da matarka wlhy hussien baisan komai ba [9:20PM, 12/19/2015] Pherty: da qarfi ya finciketa yace angayamaki kowama dan iskane kamar mijinki da xaki taba jikina idan bakisan aure ba ni nasan darajjarsa kuma kije duk wanda yaci amanata nabarshi da Allah ya juya ya fice yana sharar kwallah jiki a sabule cikin rashin dadi hamida taja qafafunta danayi mata nauyi tafita daga asibitin duk basu ankaraba tana fitowa ta nufi motar ingawa.... 59 Lokacin da ta iso ingawa kusan qarfe goma na dare ta shiga gidan kamar daga sama umma ta ganta nan da nan ta daure fuskarta tayi shigewarta cikin daki hamida batayi qasa da gwiwa ba ta bita hr dakin ta tsugunnan daga can gefe idanunta fal da hawaye tace umma ya gida shiru ba amsa umma na sameki lfy nan ma shiru a sanyaye tace umma dan Allah kiyi haquri ki yafemin laifin me kikamin dakike neman gafarata, ta qara matsowa gareta tace kiyi haquri umma kiyafemin nagane fushin kine ya janyomin halinda nake ciki dan Allah kiyafemin kidaina fushi dani kona samu sassauci a xuciyata umman tace a yau kika tuna dani ynxu kikasan dani saboda kin auri hassan kin sami abinda kikeso mai kyau da kudi sai ynxu xaki tuna dani cikin kuka tace Allah umma kina raina kece xabina banida kowa a duniyarnan face ke, dake na soma rayuwata koda natashi ke nasani taya kike tunanin xn manta dake kiyi haquri umma dan Allah fuska a daure umman tace hamida tashi kibarmin gida kitashi nace banason kalamanki ta fashe da kuka mai tsanani tana roqonta amma fafur taqi sassautamata akan sai tabar mata gida ta koma can ga hassan din data xaba umma hassan baya raina ynxu yafice min daga xuciya ki tsaya ki saurari kukana ba wanda xai tausayamin a duniyar nan face ke, ba wanda xai sharemin hawaye kamar k da kike mahaifiyata dan Allah kiyi haquri ki saurareni nace hamida ki fita tun banyi mugun kalami akanki ba...... a sanyaye hamida ta miqe tana kallonta tana hawaye ta fito daga dakin qofar gidan ta nufa ta xauna ta hade kanta da gwiwa biyu tana kuka mi tsanani kamar ranta, hassan shine sanadiyar batawarta da ummanta tunda bata sonshi, hussien shine sanadin tarwatse mata jin dadin aurenta tabbas tayi dana sanin kasancewa da tagwayen maxa, sun mata abinda baxata taba mantawaba, bata taba kuka kamar irin wanda tayi a dalilin tagwayen maxa ba kowane ya cutar da rayuwarta tabbas tagwayen maxa sun mata illah a rayuwarta ta qara shigewa jikin cinyoyinta tana kuka sosai kamar ranta........ sick ur prayer needed. Hausa novel [1:53PM, 12/26/2015] Pherty: [4:08PM, 12/22/2015] Pherty: TAGWAYEN MAXA Na fertymerh xarah Tunani umma tayi mai xurfi na ganin rashin dacewarta akan abinda tayiwa yar ta koba komai hamida kadai takeda a duniya kuma tabbas fushinta xai janyo rashin kwanciyar hankalin hamida gashi batasan dalilin xuwanta ba a wannan daren sannan ta korata idan hr hassan korata yayi tor ina xataje a wannan daren da wannan tunanin umma ta tashi ta fito a hanxarce sai tasami hamida rakube taxo ta tsugunna a gefenta hade da dafata hamida ta dago da sauri tana kallonta idanunta sharkaf da hawaye umman ta kasa furta komai illah riqo hannunta datayi suka shiga cikin gida. * Bayan fitar momy daga asibitin a harxuqe itama sai salma ta janyo hannun hussien suka fito a harabar asibiti suka sami hassan ya hada kansa da motarsa da alama ya jima wurin salma na jan hussien yana gocewa suka iso wurin da qarfi ya fincike hannunsa daga gareta ya nunata da yatsa dai dai lokacin hassan ya dago kansa jin motsi a kusa dashi idanunsa jawur saboda bacin rai salma ta juyo da kallonta ga hassan dan Allah kayi haquri ka saurareni wlhy badaniya ko dan neman fitina nayi ba, bai tankataba ya maida kansa jikin motarsa, ganin haka yasa salma ta gayamasa gskyr komai, ba hassan ba ko hussien sai dayayi matuqar mamaki tana kuka ta durqusa qasa tana roqonsu akan su shirya kodan kwanciyar hankalin mahaifiyarsu duk tagwayen suka dauke kansu sama lokaci daya suka juyawa juna baya. 61 Kamar daga sama suka jiyo muryar momy na fadin maganata ta qarshe daku idan hr baxaku sasanta kanku ba kudawo yanda kuke kamar da babu ni babu ku xn yafe ku nafitar daku daga cikin xuciyata koda kuwa sonku shine ajalina [4:37PM, 12/22/2015] Pherty: Hassan ya soma hawaye yana fadin amma momy ni.......

Chapter 4 of 5