Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 5
cimma burinta xata tarwatsa fuskar hamida taga yanda yan biyu dinta xasu sota suso rayuwa da ita. Haka kuwa akayi bayan kwana biyu ta shirya aje gidan da siyayyarta taje inda umma kamar da gaske hr qasa ta tsugunna ta bata haquri akan abinda ta masu akwanakin baya saboda darajar yan biyu dinta yasa umma ta haqura hrta amince da hamida xata bita amma hr a qasan xuciyarta bata so hakan ba tayine dan yan biyu hr suka xo gidan momy na cike da mamakin ganin gidansu hamida ginin xamani duk qauyen ingawa bamai gini kamar nasu abin yabata matuqar mamaki ta kuma san aikin yan biyu dinta ne, ta girgixa kanta kawai cike da takaici tana tuqin motar. 28 Tym din da suka iso gidan yan biyu na falo lokaci daya suka tashi tsaye ganin hamida da momy momy na murmushi tace ga hamida nadawo da ita xata cigaba da kula daku kamar da hussien ya rungumeta yana dariya farinciki fal axuciyarsa yace momy kin kyauta mungode sosai itama murmushin yaqe kawai take tana kallon hassan amma ga mamakinta fuskarsa a daure take sai faman lasarjajjayen labbansa yake yana wani dauke kansa hamida hr lokacin bata tantance a wane yanayi take cikiba batta farinciki da dawowarta gidan kawai tabi umarni mahaifiyartane [5:43PM, 11/19/2015] pherty: momy ta shige dakinta ta barsu nan shima hassan yabi bayanta tana shiga dakin yana shiga rufe qofar dakin ne ya sanyata juyowa tana kallonsa cike da mamaki yana sanye da dark space fuskarsa a daure hannayesa acikin aljihunsa kwarjini yayi mata sosai dole yan mata su rude akansu hr yau bata taba ganin muninsu ba ta gyara tsayuwarta fuskarta a daure tace wane salo ne ka bijiro da shi hassan, hrta kai ka shigo min daki ba sallama yace noooooo momy keep dat aside inaso kigayamin dalilinki na dauko hamida kixo da ita tace bayan kula daku ba wani dalili da xaisa nadawo da ita ya xare madubin idanunsa ya kafe ta da manyan idanunsa yace ba gsky bane momy, i knw u hate her nasan ba saboda mu kika dawo da itaba kinada wata manufa akanta 29 ta nunasa da yatsa cike da mamaki tace ni hassan kake qaryatawa, ni xaka tasa gaba saboda mace am.......ya dora hannunsa a bakinta yace kiyi shiru momy xokiji, yajata suka xauna bakin gado yana riqe da hannuwanta yace momy karki cutarda hamida, tana son tagwayenki tana kula dasu shiyasa tafiki sanin sirrinsu akan keda kike mahaifiyarsu, hamida nada ilimi tana samu akan hanya kawai boko ne dabata qarasaba daxaki taimaka da kinsata momy, pls momy karki cutar da ita Allah ya hana na tabbata a yanayin danaga hamida bada son ranta ta biyoki ba kamar an mata dolene shiyasa hr na xargeki, hamida na neman halal dinta shiyasa hrtaamince ta biyoki kuma tayi gsky domin annabi s.a.w yace DALABU HALALU WA JIBBU ALA KULLI MUSLIM( neman halal dole ne akan kowane musulmi) sannan ma momy ki duba dabi'un hamida kigayamin aibunta da bakyason mu aureta kigayamana wani abu cikin halayenta dabashi da kyau wanda Allah ya haramta [6:33PM, 11/19/2015] pherty: tayi shiru kawai tana naxari cos babu ita kanta tasani hamida bata da aibu, hamida yarinyace amma tana da kyau hali kuma ta sami tarbiya duk da tataso cikin maraici da quncin talauci amma duk da haka baisa ta canxa daga kyawawan dabi'ubtaba hassan yacigaba da fadin momy muna sonta kibarmu mu aureta ba inda Allah ya hana auren talaka ki janye wannan aqidar taki pls ta janye hannunta daga nasa tana firgixa kanta ganin haka yasa yayi rau da idanunsa kamar xaiyi kuka pls momy, ina sonta itace mace ta farko dana fara so arayuwata idan kin cutar da hamida koma ki hanamin aurenta am sure nima xn cutu ta janye hannunsa tana fadin xnyi tunani akai ya sumbaceta a goshi yana murmushi yace amma momy ynxu hamida xata rage aiki a gidannan ko tunda kin qaro maaikata sai abarta ta kula da mu kawai nan ma qara tsuke fuskarta tayi ta cire gyalen jikinta da dan kwalli tace shima xnyi tunani akai, dai dai lokacin hussien ya shigo ta dubesu tana bata fuska bana son wata mgn kufita pls kada ku dagulamin lissafi hussien yace dame xamu dagula maki lissafi momy kai tsaye hassan yace wai dan nace kada ta cutar da hamida muna sonta momy ta dora hannunta a goshinta hassan baida sirrin kanshi komai xaiyi direct ne tace dan Allah kufita kuje ku bani wuri hussien ya fara fita hassan na bayansa. 30 Bayan kwana biyu tun xuwanta gidan taga kamar komai ya lafa daga yan tagwayen shan giya da neman mata hrta soma jin dadi sai dai batada gwani aciki tunda kowane da ranarsa da irib soyayyarsa a xuciyarta duk da tafison hassan amma umanta tafison hussien hr ynxu bata tantance waye nata a cikinsu ba a wani dare tayi sati biyu da xuwa gidan ta tashi xatayi nafila kamar ance ta duba window sai ta tsinkayo hussien na bude gate din gidan ahankali da sauri ta sauko ta nufi gate din dai dai lokacin yana riqe da hannun yarinyarsa xasu fita gidan dan gr ya fitar da mota jin motsin saukowar hamida ya tayar da momy daga barci sai ta tashi ta hankade labulen dakinta tana kallonsu hamida ta finciko yarinyar daga hannunsa idanunta jawur ya juyo yana kallonta cike da mamaki xuciyarsa na bugawa yace menene haka hamida tace ashe kai maqaryacine bansaniba ko kasan alamomin munafiki shine wnda idan yayi mgn yayi qarya idan yayi alqawari ya saba idan aka amince masa yayi yaudara, kamin qarya hussien kaine kafaramin alqawarin ka daina duk da hassan baimin ba, ka karya alqawarinka na amincema ka yaudareni sai ta fashe da kuka abinka da dare duk abinda suke mgn momy najinsu kuma tana ganinsu hussien yace ynxu ni munafuki ne kike nufi hamida tayi shiru tana cigaba da kukan da take yarinyar tace wai cwty wannan wacece who x she, meyasa take gayama mgn haka bakaa dauki mataki ba, hamida ta dubeta da jajjayen idanunta tace ke wacece dakike wannan mgnr wayeke menene dalilinki na biyo saurayi hr gidan ubansa a wannan lokacin kina mace, mace mai mutunci yar gidan tarbiya a irin wannan lokacin tana gidan ubanta idan kin gurbata rayuwarki meyasa kikeson lalata tashi rayuwar.......keeey ta dakatar da ita bai lalataniba nixan lalatashi, shine baida tarbiya bani..........gau kakeji ya dauketa da mari sai ga bakinta na jini olryt yau nine bnda tarbiya ko ni xaki dubi idanuna kigayamin haka [7:09PM, 11/19/2015] pherty: now get out frm dis house tun banyi qasa qasa dake ba ta janye hannunta daga kuncinta tana kallonsa ranta abace for now dole ka dakeni ka korani waje saboda ka gama cin moriyar ganga tunda can farko da kake xuwa dani nan gidan ai agabanta muke wucewa meyasa tun lokacin bata hanakaba sai yanxu saboda itama kanason ka gurbanta tata rayuwar kamar yanda kamin ko 31 cikin tsawa yace dan ubanki kigayamin waya fara saninki kafin ni a fankonki na sameki akan barikinki kece ma kika bata tawa rayuwar saboda dake kawai nake mu'amala tun muna karatu england kika tursasani kika hanamin kula ko wacce mace sai ke, wannan da kike gani itace ke iya qoqarinta na ganin na dawo kan hanya na daina abinda nake amma ke ba maccen xama bace ke ja'ira ce kuma shaidaniya tir da halinki bilki ta fashe da kuka kawai batare da tayi mgn ba ta juya ta fice daga gidan shima ransa a bace yayi shigewarsa part dinsa hamida ta jinjina kanta kawai wato itace ma ta batasa itace tasashi a wannan hanyar, koda ace ba itace tasashiba ai shi namijine kuma kome yayi adone agaresa amma ita da take mace fa? momy dake can sama tana tsinkayosu tana jinsu ta cika da imani wato abinda suke aikatawa kenan tabbas ta yarda da hamida 100% ta yarda ita kadai xata iya canxawa tan biyu dinta halinsu, xamnta dasu batasan suna wannan abinba kuna hamida bata taba faya mata ba, lallai dole su so hamida suso kasancewa da ita sai taji matuqar tausayin hamida musamman dataga tayi tsaye bata shigo gidan ba, tor shi kuma hassan wane abu ne yake aikatawa? bata qare tunanintaba taga an hangame gate din motar hassan ce ta shigo wannan karon bai sha ba amma ya jibgosu xai shiga da su gida yayi kicibis da ita ya bata fuska hade da jan tsaki yace mekikeyi haka sata nayo ne da xaki wani tare ni haka, tace tor meye banbanci da sata tunda baka aikata abinda kake da raa sai dare ya raba ya dauke kansa yana wani cije labbansa ya raba ta gefenta xai wuce bai ankaraba ta sa hanneyenta ta bige kwalaben dake hannunsa gabaki daya suka xube suka tarwatse... keeeey cikin tsawa ya dago yana kallonta idanunsa jawur baiyi wata wata ba ya dauke ta da mari kafin ya dafebkansa da hannuwansa duka biyu yana safa da marwa a harabar gidan xuciyarsa cike da qunci kamareta da duka yakeji bata damu da marinba duk da taji xafinsa sai cewa tayi idan kullum xaka dakeni kadaina shaye shayen nan na yarda, shut up stupid, banxa kinsan ko nawane nayi asara anan kinsan iyakar kudin dana kashe ne kinsan kudin kwaya daya da kika fasa ta girgixa kanta tace ban san iya kudinsuba amma kagayamin kai kasan iya adadin xunubin dake kanka akan sune yace wannan matsalarkice not mind ina maki mgn akan kudin danayi asara ne? tayi shiru kawai tana sharar kwallah yaja dogon tsaki cike da takaici ya juya xai fice sai ga momy tsaye a gabansa idanunta jawur sai da gabasa na fadi. u [4:37pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [7:48AM, 12/16/2015] Pherty: 31 TAGWAYEN MAXA Na fertymerh xarah Ya dauke kansa daga kallonta yana wani cije fuska kai tsaye batare da tunanin komai ba ta wanke fuskarsa da mari ba hamida ba shi kansa hassan ya tsorata ya xuba mata manyan idanuwansa da suka rine xuwa ja, tace ashe daman haka kuke, ashe abinda kuke aikatawa kenan bayan idona [hayaniyarsu na fito da hussien ] kunci amanata kun yaudari tarbiyata dana maku, hussien yace momy me akayi n......, bai qarasaba shima ta wanke fuskarshi da mari, a harxuqe hassan yace but mum a....... Rufemin baki ta fada cikin tsawa, kai kanada bakin magana ne duk abinda k faruwa duk akan idona, sai yau na yarda hamida alhairice agareni ynxu na fahimci komai akanta duk qoqarin datake akanku bata taba gayamin aibunku ba tabbas ta cancanci ta xamo surukata na janye duk wata aqida tawa akan mai kudi da talaka amma kasani hassan bakai ba hamida baka dace da rayuwartaba xn nemawa hussien auren hamida......, shima hassan a harxuqe ya katseta look mum mekike nufi did you hate me for now? Meyasa xakice haka menayi ne? Ko angayamiki ni bana sonta ne, tace a hakan kake sonta kana sonta kake dukanta, oh gosh ya dafe kansa da hannuwansa duka biyu ya juya ya dawo yana fadin nooooo mum ina sonta wlhy akanta na fara so itace na fara shiga damuwa akanta pls karkimin haka, tace duk yanda xakayi sai dai kayi amma baxan aurama hamida kaje kana cutar da itaba hussien yafika sonta akanta naga ya haqura da yarinyarsa hr ya korata waje amma kai saboda wadannan abin hr xaka daketa ka nuna sunfita daraja, 33 Tacigaba da fadin, yanxu ina son hamida saboda son da take maku da kuma son gyara maku halayya da takeyi shiyasa baxan so cutarda rayuwarta kamar yadda na qudira a farko ba tabbas hussien kadai xai iya riqeta amana, ya soma yarfe hannuwansa yana fadin mistake ne mum but i promise baxan sake dukantaba kiyi haquri ina sonta mum pls sai ya fashe da kuka abinda rabon dataga kukansu tun suna yara, hankalinta na tashi bama kamar hussien ba da shima ya riqo hassan din yana kuka, tace dama kabar kukan hassan nariga na yanke hukunci xaka auri salma hussien kuma hamida gobe ma xnje ingawa neman aurenta tare da uncle dinku [7:59PM, 11/20/2015] pherty: Cikin daga murya yace bana sonta nace bana sonta who is she? 34 Ya soma marin kansa da hannun daya mari hamida ita kanta hamida a rude take ta fashe da kuka tana fadin momy pls ki dakatar dashi, xuciyar momy sai tafarfasa take tana jin xafin halin da hassan dinta ke ciki amma ta kasa tsayar dashi badan komai ba dan karyaga karayarta, hamida ta janye kawaicin dake damunta taje ta riqe hannunsa dayake marin kansa, tace me kakeyi haka hassan kadaina pls ya fincike hannunsa fuskarsa har tayi jawur abinka da farin mutum, ya hankade hussien daga jikinsa batare da ya waiwayesu ba yaje ya shiga motarsa ya finciketa da qarfin tsiya ya bar gidan, hankalin momy a tashe tace kabishi hussien kada yaje ya halaka kansa a banxa sai ta fashe da kuka, hussien ya shiga mota ya bishi jikinsa har rawa yake hamida kuwa durqushewa tayi qasa tana kuka kamar ranta, tun fitowarsa gidan yake kuka tuqi yake batare dayasan inda xaijeba hankalinsa yatafi qoluluwar tunanin yanda xai iya xama da wata ba hamida ba ita ya fara so gashi har akanta yana jiyo wasu feelings da bai taba jiba tayama xaa kwaceta daga gareshi aba hussien ya tuba ya daina dukanta baxai qara ba, ya fashe da kuka qeeeeeeeey yayi qoqarin tsaida motarsa dataso ta bigi motar gabansa, yayi qoqarin kwacewa yayin da motarsa ta nufi daji, gab kakeji ta bigi wata qatuwar itaciya, hussien yaja wani birki tsakiyan titi ya saki qara ya nufi motar hassan gashi darene........, Hausa novel [7:51AM, 12/16/2015] Pherty: [10:40AM, 11/27/2015] pherty: 35 TAGWAYEN MAXA Na fertymerh xarah Mutane suka rufawa motar baya yanda hussien yaga hassan yasa numfashinsa ya sarqe ya fadi ragwab sumamme, nan da nan aka kwashe su subiyu aka nufi asibiti da su, tym din da hussien ya farfado gadon hassan ya nufa duk jikinsa jinine ya soma kuka sosai kamar ransa fadi yake hassan kada ka mutu kabarni, munxo duniya atare kabari mukoma atare baxan iya rayuwa bakai ba, kamar yanda muka xo tare muka rayu tare kabari mu mutu tare, idan hamidace wlhy na barma nixan auri saalma pls..., ya fashe da kuka mai tsanani, washe gari dole ya buga ya sanarda momy, aikuwa a rude ta iso asibitin hamida na bayanta ko mayafi babu [10:42AM, 11/27/2015] pherty: 36 Innalillahi wa inna ilaihir rajiun shine abinda momy ke maimaitawa, hamida kuwa a qofar dakin ta xube hannunta dafe a bakinta ta fashe da wani matsinancin kuka, momy tace nooooo hassan, katashi pls idan hamida ce gaka gata, meyasa xaka nemi halaka kanka kan abinda kafi qarfinsa , hamida ta tashi ta qarasa wurin da yake kwance qafafunsa da kansa duk jinine dai dai lokacin dr.merah ya shigo tare da hussien, ya dafe kansa da hannuwansa duka biyu yanaa girgixa kansa cike da tausayawa yace saai an masa x_ray saboda jinin dak) fita a kanssa but actually ya sami matsala a qafafu da kyaarne idan xai sake tfy akansu [10:47AM, 11/27/2015] pherty: Lokaci daya duk suka juyo suka xuba mashi ido cike da tashin hankali, momy tace qaryane dr. Dole hassan dina ya tashi baxai xauna ba qafafu ba, inada kudin daxan fita dashi waje ayi masa magani, ta fashe da kuka ta cakumo rigarsa tana girgixashi cikin wani irin kuka mai tsuma xuciya, 37 da kyar dr.merah ya banbareta daga jikinsa yana fadin hjy a waje nayi karatu kumaa a waje)nake aiki ina xagayowa nigeria kasancewarta mahaifata kuma family dina suna xaune anan idan kuka cire matata da ya'yana, duk abinda xaa iya masa acan insha Allah xn iya kuma xn gwada qoqarina akai (magana yake cikin isa da qasaita da kyar ma suke jiyosa yanayi yana yatsina fuskarsa amma a xuciyarsa kallon hussien yake yana kallon hassan cikin boyayyen dark space dinsa ya rasa gane banbancinsu tagwayen kamar aljannu ko taya suke gane abinsu oho ya tabe bakinsa ya juya ya fice) hussien da momy suka soma kuka kamar ransu, hamida kuwa fita tayi ta nufi office din dr.merah ta samesa kishingide yana juyi kan kujerar da yake xaune, sallama tayi a qasan xuciyarsa ya amsa batare da ya kalletaba, da hannu ya nuna mata wuri ta xauna, tace 38 Dr. Da gaske hassaan baxai sake tfy ba, ya gyada kansa yana kallonta qaramar yarinyace ko meye damuwarta akansa,ta soma share hawayen fuskarta , yace ko meye damuwarki akansu by main looking bakiyi kama dasu ba nasan ba qanwarsu bace ke, kanta a qasa tace ni mai aikin gidansu ce amma ta dalilina ya sami wannan matsala, ya xuba mata idanuwansa cike da mamaki bayan ya xare madubin idanunsa, (cikin lokaci qanqani ta bashi lbrin komai batare da shayin saba saboda tasan Dr.Aiman merah taji labarinsa ga ummanta da momy, taji lbrin mulkinsa da qasaita) nan take yaji yana tausayin yarinyar itace mace ta uku daya soma tausayi a rayuwarsa bayan matarsa Affiya, sai Dr.fulani da ita [10:51AM, 11/27/2015] pherty: Yace hermyderh kada kidamu baxamu iya yimasa abinda Allah bai nufaa ba, kiyi masa addua -kiroqi Allah bashi lfy namu shine mu taimaka masa, 39 But i promise u insha Allah xai sami lfy yayi tfy da qafafunsa kada ki damu hamida,murmushi tayi tana kallonsa tana mamakin girman mulkinsa da qasaita tana mamakin yanda yake furta magana da kyar kamar bayaso, duk mgnr dake fitowa bakinsa idanunsa akan laptop bawai kallonta yake ba, idan bata manta lbrn yarima aiman ba data qaryata sarautarsa da qasaitarsa(duba mulki ko sarauta)ta tashi tafice tana fadin nagode Dr. Ta juya ta fice da sauri yabita da kallo kafin ya girgixa kansa ya maida kallonsa ga laptop , tana fita office din asibitin tabari ta nufi ingawa cikin tashin hankali ta sanarwa ummanta abinda ke faruwa taje taxo da kawunta akan xasuje asibitin, harda maigari taaje ta roqa akan yabiyota asibity abinka da babban mutum saai yaje da mutanensa ciki hrda liman, abin yayi matuqar daurewaa umma da kawunta kai saai dai basu tankataba har suka shigo mota suka xo asibitin, har lokacin bai farfadoba sai dai sun sami iyayen salma ma sunxo salma sai kuka take sosai, hamida da mutanenta yabawa kowa mamaki kamar mutuwa akayi, kai tsaye ta nufi inda hassan ke kwance ta riqo hannunsa tana kuka, 40 tace ina son hassan xn iya xama dashi a kowane hali koda yaxama nakasasshe bnsoshi dan wata dukiyarsa ko kyawunsaba sai dan yana hassan akwai wata kissa inda wani mutum yaxo inda manxon Allah yace ya manxon Allah shiryardani xuwa ga wani aiki wanda innayi shi Allah xai soni mutane kuma xasu soni, sai Annabi yace guji duniya [10:52AM, 11/27/2015] pherty: Allah ya soka kuma ka guji abindake hannun mutane,mutanen xasu soka, shiyasa naxo da wakilina kawuna ga mai gari da limaminsa, inaso a dauramin aure da hassan, dam xuciyar hussien na buga gabaki daya dakin aka xuba mata ido bama kamar hussien da salma dana tsinci kansu cikin wani tashin hankali ba......... Hausa novels [7:56AM, 12/16/2015] Pherty: [4:47PM, 11/30/2015] pherty: 41 TAGWAYEN MAXA, Na fertymerh xarah Duk dakin akayi shiru aka xuba mata ido cike da mamaki, ganin haka yasa ta qara fashewa da kuka ta girgixa kanta ta qarasa gurin momy dake tsaye ta riqo qafafuwanta tana wani irin kuka mai narkar da xuciyar mai sauraro nan da nan jikin momy nayi sanyi, umma ta dubeta cike da mamaki tace hamida har ynxu ban gane inda kika dosa ba inaji kin daukomune dan mudaba marar lfy ko? Hamida ta dago manyan idanuwanta dana rine xuwa ja tana kallon mahaifiyarta tace harda auren hassan umma, yana sona yana son halaka kansa saboda ni dan Allah ku tausayamasa, nan da nan ran umma na baci ta murtuqe fuska cike da takaici ta fisgota daga tsugunne datake itama hamida ta tsorata da ganin yanayin da umman nata take ciki [4:54PM, 11/30/2015] pherty: Mekike fada ne hamida qara maimaitawa inji inajin kunnuwana basuji da kyau bane, hamida ta tsorata ta xare idanuwanta tana kallonta tana girgixa kanta cike da tsoro, 42 umman ta sake saura qiris ta fadi ta juya ga kawun hamida tace bn amince da wannan auren ba ban yarda hamida ta auri mutanen da basu da kirki basu da tausayiba, lokaci daya xuciyar momy da hussien ta buga duk suka dubeta a raxane, umma tacigaba da fadin hamida ya'ta ce jinina ce ban yarda ta auri ko daya daga cikinsuba saboda mahaifiyarsu batada mutunci tunda har ta iya toxartamu ta wulaqantamu saboda Allah bai bamu ba, hakama ya'yanta..........hussien ya katseta da hanxarinsa, yace umma kimin adalci kinfi kowa sanin yanda nakeson hamida, wlhy ina sonta dalilinta nadaina aikata duk wani abu marar kyau, sannan mahaifiyarmu bai kamata ki jefeta da wannan kalamaiba idan kikayi la'akari da irin halaccin datayi maki a rayuwa bawai gori nake maki ba, 43 mai gari yayi gyaran murya kafin yace Asmau(umma) ba iko xn maki ba abinda na fahimta anan duk su biyu suna sonta kibarta ta auri wancan da baida lfy ina ganin hakan shine dai dai, umma ta girgixa kanta cikin tashin hankali tace bana son hamida ta auri hassan nafi yimata sha'awar hussien shine yafi sanin darajarta shi nakeson ta aura, wasu xafaffun hawaye suka xubowa hamida bawai batason hussien bane tana sonsa amma xuciyarta tafi rinjaye akan hassan din, ahankali taja qafafuwanta daga dakin ta fita tana fitowa ta tsinkayo Dr.merah na fitowa theater yana tafe yana xare handgloves cikin isa da qasaita ga fadawa birjik a asibitin, guards dinsa suna biye dashi a baya, yana tafe yana yatsina fuska ma'aikatan asibiti sai xubewa suke suna gaisuwa nurses da likitoci sai dai ba wanda ya kula ballantana ya amsa, cak suka ga ya tsaya harabar asibitin suna ganin haka fadawan da guards suka san akwai matsala tabbas akwai abinda ya fadi daga hannunsa daman hakane duk abinda ya fadi hannunsa baxai taba magana ko ya nunaba sai dai ya tsaya masu more masa baya suje su duba , haka kuwa akayi da yawa suka juya suga ko menene ya fadi suna isa cikin asibitin suka sami turban dinsa ne har wata nurse ta dauka xata kawo masa da sauri suka karba suka fito , hamida na tsaye na kallon sarauta wannan tor dame yake taqama MULKI KO SARAUTA? tana kallo aka bude masa mota ya jima tsaye kafin acire masa labcoat din jikinsa aka musanya masa da alkyabba suka nada masa turban dinsa kana ya shiga motar sukajata ahankali kamar masu tfy a hanya, kusan motoci biyar suka morama motarsa baya suka fice, ta sauke ajiyar xuciya ta tuna cikin lbr da aka bata akwai wani lokaci da sarki merah ya sauka daga sarautarsa aka nada Aiman, saboda tsabar sarauta da ji da kai a daren ranar yana tare da mai dakinsa Affiya xasuje [4:59PM, 11/30/2015] pherty: Lambu, kunama ta cijesa a dan yatsan qafansa, amma saboda qarfin mulkinsa bai fada ba ko raxana ko wata alama da xai nuna illah tsayuwa da yayi cak a xaton fadawan ya yarda wani abinne sai suka shiga dube dube anan suka ci karo da qatuwar kunama dai dai inda yake tsaye nan take suka kasheta hankalinsu a tashe suka juya suna kallonsa yana tsaye inbanda xufa ba abinda yake, 44 iya rudewa affiya ta rude ta rungumosa tana tambayarsa inda kunamar ta cijesa amma yaqi ya fada hassalima dauke dubansa yayi daga garesu, fadawan cikin rudani suka xube qasa suna roqansa ya fadamasu amma fafur yaqi tankawa saboda gani yake idan ya nuna rakinsa tabbas girmansa dana sarautarsa ya fadi, Affiya nan take ta fashe masa da kuka ganin kunama ce fa ta cijesa ta juya xatabar lambun sai ya riqo hannunta yasa dayan hannunsa ya xare space din idanun sa da idanu yayi masu alama da yatsantsa...... Cabdi wani mulkin,sarauta da qasaita sai kun duba littafin MULKI KO SARAUTA?shima littafin fertymerh xarah ne. kukan salma ya dawo da hamida daga xurfin tunanin da take, sai a lokacin ta tuna halin da take ciki tadawo da kallonta ga salma idanunta sunyi rau rau ta koma cikin asibitin gab da xata shiga dakin taji muryar momy cikin kuka tana fadin abar hamida ta auri hassan, hussien xai iya haqura da hamida amma batasan ya rayuwar hassan dinta xata kasance ba idan ba hamida, umma tace nafison hussien akan hassan, nafi ganin girmansa mutuncinsa tarbiyarsa sosai akan hassan saboda haka na xabawa yarinyata hussien ta aura, ta juya a raunane tana kallon limamin idanunta taf da hawaye tace ga wakilin hamida shine kawunta tunda baa sanarda yan uwan hussien ba inaso mai gari ya xamo wakilinsa a daura auren hermyderh da hussein yanxu ba sai anjima ba tunda TAGWAYEN MAXA baxasu auri hamida dukkansuba dole dayane xai xamo mijinta kuma hussien, nan take hamida na xube da gwiwoyinta qasa tana rusa kuka mai tsananin gaske. Hausa novel 16 December 2015 at 08:05 · fertymer [4:39pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [4:57PM, 12/22/2015] Pherty: 45 TAGWAYEN MAXA Na ferty xarah A raunane hussien ya matsa yana kallon hassan da har lokacin bai farfadoba, yana tausayin dan uwansa yana son dan uwansa kuma komai xai iya akan dan uwansa, tabbas yafison rayuwar dan uwansa akan hamida, mace baxata taba xama sillar rabuwar xumuncinsuba, yau gashi duk kudinsu kyawunsu da ajinsu suna neman rasa abu a duniya, komai na hassan nashine, kuma komai nashi na hassan ne tor idan hakane dan me baxai iya barwa dan uwansa jininsa abinda yake soba, ya rumtse idanunsa yanason hamida tamkar ransa kuma yaxama wajibi yabarwa hassan shikuma ya karbi salma a matsayin matarsa, ya girgixa kansa yana hawaye ya kalli umma yana share hawayen fuskarsa sai kuma ya juya yana kallon liman kafin yajashi gefe sukayi wata magana batare da kowa yajiyosuba kana hussien ya dubesu yace xaije ya dauko uncle dinsu dole shi xai xama wakilinsa saboda shine ubansu a yanxu, ya juya ya fice yana fitowa yaci karo da hamida tsugunne a gefe kallo daya yayi mata ya dauke dubansa gareta tana ganinsa ta taso da sauri ta taryesa, ya murtuqe fuskarsa, hakan yasa jikinta yayi sanyi ta langabar da kanta tana hawaye, tace nasan tunaninka xai baka cewa bana sonka wlhy ina sonka hussien, tausayin hassan da kasancewarsa dan u.... Ya katseta ta hanyar daga mata hannu yace qaryane hamida qarya kike kice kina sona, maganarki ba gsky bace duk hasashe ce ba tun yau nake ganin soyayyar hassan atare dake ba idanuna na kanki hamida, kada kidamu hassan din da kikeso xaki samesa sannan duk wata kulawa da damuwa da kika nuna akaina nagode ya juya ya fice ransa a bace tabisa da kallo cike da tashin hankali da rashin fahimtarta da baiyiba, 46 kusan minti talatin da fitarsa sai gashi tare da iyayensa maxa kusan uku sun shigo asibitin kai tsaye aka nufi dakin da hassan k kwance, sun raxana da halin da suka sami hassan dan basuda lbr hr sun juya xasu rufe momy da fada ganin suna raye Dan' yayansu yana neman rasa rayuwarsa basuda labari yasa momy tayi saurin katsesu muryarta a sarqe tana kuka ta koro masu bayanin komai [11:18AM, 12/1/2015] Pherty: Nan da nan iyayen maxa suka juyo da kallonsu ga umma suka dubi hassan matsayinsa kudinsa kyawunsa da ajinsa amma ace shine ya koma hakan saboda mace macen ma yar talakawa to menene amfaninsu a duniya idan baxasu iya samawa TAGWAYEN MAXA abinda suke so ba, amma abin tambaya da mamaki anan yanda duka xaratan maxan suka kafe akan mace daya kuma kowane daga cikinsu na buqatarta duk da basuga yarinyar ba, sannan basajin ta ummanta saboda sunada kudin da xasu nuna mata FIN QARFI akan yarta(chabdi) hussien ya katse tunaninsu xuciyarsa a raunane yace a daura auren amma duka iyayen mata su fita daga dakin, 47 uncle ya katsesa yace wane irin daurin aure ne wannan hussien sai kace bakuda gata a duniya, wane irin aurene xaa daura a asibiti kamar wasu marar galihu, bamu yarda da wannan daurin aurenba, tabbas kamar yanda duniya tasan da mahaifinku kafin ya rasu tasan da xaman kyawawan maxa kamarku dole sai kowa yasani kuma ya shaida auren TAGWAYEN MAXA a doron qasar nan, bamai gari ba hatta liman da kawu sai da jikinsu na dauki rawa wato abin na manya ne, uncle ya cigaba da

Chapter 3 of 5