Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 5
shigewarta dakinta, kusan kwana biyu batasa su a ido ba duk ynda xatayi tagansu basa bari duk fushi suke da ita aganinsu bata sonsu tunda bata son abinda suke so shiyasa suka qauracemata , a wata safiya tana xaune a falo cike da damuwa suka shigo kowane fuskarsa ba walwala, suna sanye da shadda milk, banbancin dinkinsu kalar xaren da aka masu aiki dashi, sunyi matuqar kyau ga gashin kansu ya kwanta sosai, mans pride dinsu sai sheqi yake, ta tsura masu ido tana kallonsu, basu taba mata kyau irin na yau ba, yara kamar aljannu, sai ta daure fuskarta ta dauke kanta daga kallonsu, hussien yafara gaidata kafin hassan, amma ba wanda ta amsa, lokaci daya suka kalli juna suka tabe bakinsu suna yatsina fuskarsu(dama hassan bai iya boye damuwarsa ba komai direct yakeyinsa) yace momy mun shirya xamuje ingawa inda hamida munaso cikinmu ta xabi wanda take so,sai kibamu address dinta, sai taji mgnr banbarakwai wai qarfin hali hr kusan faduwa tayi wai yau hassan ke mata mgnr xaije qauye kuma neman wata talakka, ta dubesu da kyau suna tsaye suna kallonta ko kadan hamida bata tako qafar yan tagwayen maxan taba sunfi qarfinta nesa ba kusa ba kuma ta kowanne fanni, ynxu su a hakan xasuje ta xabi daya daga cikinsu chab, hassan ya katseta momy we ar waiting kinyi shiru ko baxaki bamu bane, ta gyada kanta batare da tayi magana ba ta tashi tabar masu falon, suka fito ransu a bace amma sun qudira a ransu xasuje , suna tsaye suna shawara uncle dinsu ya shigo suka gaidashi, yace yan biyu kyautar Allah ina xakuje haka , hussien yace xamuje ingawa duba hamida ba lfy, yace hamida ba lfy ankaita gidansu ne, yace eh, uncle ko kanada address dintane, yace eh xn tuna lokacin da mukaje daukota nida mahaifiyarku(sai yabasu address) [8:06PM, 11/8/2015] Pherty: Yace idan kukaje kun kyauta kuwa, suka soma murmushi, yace kunyi kyau TAGWAYEN MAXA, yakamata insami wannan kwalliyar saboda tarihi, hassan ya ciro wayarsa yana fadin uncle karka damu tunda ka taimakamana muma xamu baka pic dinmu [8:08PM, 11/8/2015] Pherty: 18 Hassan ya gyara space dinsa hade da daga wayar sama, hussien ya matso kadan kusa dashi hannunsa akan space dinsa hassan ya dauki pic din,kuma yayi kyau sosai suka tura masa a wayarsa ya shiga gidan yana murmushi sukuma suka shiga motarsu hussien yajasu. Lokacin da suka iso ingawa sun dan sha wahala kafin su sami gidansu, suna tsaye bakin garkar gidansu sun harde hannuwansu a qirjinsu idanunsu boye a space suna jiran fitowarta dan sun aika yaro ya kirata, ita kuma acikin gida hankalinta a tashe yake dan batada wani saurayi a unguwar daxai xo nemanta, ummanta tace kije kigani mana kin tabayi yaron ko waye, ta girgixa kanta alamar a,ah ,ta sanya hijab dinta ta fita, lokacin data fito idanunta na sauka akansu sai da tayi tuntube saboda firgita da wani kwarjini da suka mata lokaci daya duka su uku xuciyarsu na buga, tana tsaye tana kallon TAGWAYEN MAXA daya bayan daya ta kasa qarasawa suma suna tsaye sun xubamata narkakkun idanunsu masu rikitarwa wadanda nasata dabircewa Hausa novel 28 November 2015 at 17:34 · fertym [4:35pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: [5:06PM, 11/30/2015] pherty: 19 TAGWAYEN MAXA Na fertymerh xarah cikin nutsuwa ta taka inda suke tsaye amma ta kasa furta kalma ko daya daga garesu, hussien ya xare madubin idanuwansa yana kallonta yace hamida gidanku haka aka koya maki tarban baqi ne, sai tayi far da idonta cike da jin kunya ta dan sunkuya tana gaidasu, hussien kawai ya amsa hassan na tsaye ya sarqe hannuwansa yana kallonta sai yau ya taba tsayawa ya kalleta da kyau, abinda ya fahimta daga gareta batada tsayi sosai haka kuma ita ba fara bace ba baqa bace chocolate colour ce (kala mai tsada) tafisu manyan idanuwa da gashin ido, hancinta dogone siriri bakamar nasu ba yafi nata tsayi, ya kai dubansa ga qafafunta(duk idanunsa a boye cikin glass yake mata wannan kallon) ta gefen ido take kallonsa gaba ki daya ya tafi da hankalinta hrtakeji aranta inama hassan xai xama nata hr tsawon rayuwarta da babu maccen da takaita sa,ar miji a duniya(aikam naga xarah dange ma ta kyasa) cikin siririyar muryarta dana sarqe tace ko xaku shiga gidane umma na ciki, hassan ya yatsina fuskarsa bayan yacire madubin idanunsa yana kallon gidan, ginin laka ne, ya girgixa kansa noooooo baxamu shiga ba, sai idan ita xata fito, hamida ta saki baki tana kallonsa tace ita umman tawa, ya gyada kansa yace ba gunta mukaxo ba inda kike mukaxo ki xabi daya daga cikin, chab iya bacin rai ranta ya baci ita mahaifiyar tata datake gani a duniya batada kamarta, kowane irin so take wa mutum baxata lamunci a wulaqanta mata mahaifiya ba, karo na farko da ta soma yi masa wani kallo mai cike da mamaki [6:58PM, 11/10/2015] Pherty: Tace bana son ko dayan ku kuma baxan xaba, hussien ya matso gareta yace hrdani hermyderh kimin adalci mana menayi maki, ta yatsina fuska tana kallon hassan daya matso shima kyam idanunsa akanta baisan meyasa baya gajiya da kallontaba, idan ma kyau ne ai baxata fishi kyau ba amma yarasa meyasa yake son kallonta, tace saboda halayyarku bana son ko daya, baxan auri maxinaci ko mashayin giya ba,(lokaci daya hassan da hussien suka kalli juna) tacigaba da fadin 20 ina maku nasiha bama kudai ba daduk masu aikata wani xunubi daya haramta kuji tsoron Allah ku sani shi yafi cancanta da aji tsoronsa fiye da kowa da komai, kuyi roqo da abinda ma,aiki ya umurceku dashi ku hanu akan abinda ya haneku da shi idan muka xamo haka xamu kasance masu nutsuwa da samun ingantacciyar rayuwa, (Allah ya gafarta mana dukkan xunubinmu saboda albarkar manxon Allah, Amin) [7:04PM, 11/10/2015] Pherty: Hassan da hussien suka tsura mata ido ba qaramin birgesu tayi ba kuma ba komai suke sauraro daga gareta ba illah xaxxaqar muryarta, 21 hermyderh ta tsargu da kallon da suke mata sai ta dan matsa daga baya ta sauke kanta qasa tana fadin lokaci bai qure ba xaku iya gyara rayuwarku xn kuma xabi daya na aura acikinku matuqar xaku tuba saboda manxon Allah s.a.w yacewa Allah s.w.t yace yakai dan adam haqiqa matuqar xaka roqeni kuma ka qaunace ni to xan gafarta maka abinda ke kanka na xunubi, kuma ban damu ba, ya kai dan adam da dai xunubinka xai tabo sama sannan sai ka nemi gafarata to xan gafartamaka, yakai dan adam haqiqa da xaka xo min da xunubi cikin duniyarnan sannan ka hadu dani ba tare da kayi shirka dani ba, tor xn xoma ka da cikinta na gafara. (makarantana kunemi gafara olways Allah xai yafe maku idan baka aikata shirka ba kuce ASTAGAFIRULLAH pls) tayi shiru tana kallonsu,ga mamakinta sai taga hassan ya miqo mata baqar leda shima hussien ya miqa mata tashi yace wannan wayatace bn yrda ki kira wani ko akiraki da wayata ba, tawace nikadai xn kiraki da ita, hassan ma ya yatsina fuskarsa yace nima haka wayata bn yarda ko dan uwana ki kira da itaba kowa ki masa amfani da tasa, tayi xuru tana kallonsu cike da mamaki tace baxan karbi wayarku ba bana so ku kanku bana so idan baxaku gyara halinkuba(tor fa hamida su tagwayen ne bakyaso ga xarah dange na neman daya ruwa a jallo) lokaci daya suka ajiye mata ledar agabanta batare da sun damu da kalamanta ba, ga jamaa an taru yara da manya sai kallonsu suke suna yaba kyawun tagwayen maxa, sun rasa gane wane jinsi ne wadannan yara kamar aljannu, su mamaki ma suke me sukaxo yi inda hamida baqar fata kuma talakka,hassan ya maida space dinsa yana furxarda iska daga bakinsa ya tabe bakinsa hade da daga kafadunsa alamar kota xabeshi ko kada ta xabeshi ko ajikinsa dan baxai bar giyar ba ya juya ya nufi motarsu, hamida ta bisa da ido tana kallonsa bataji dadin ynda ya nuna ba ita tanaso ya shiryu ya daina taji kamar ta kirasa ya dawo dan wlhy tanajin sonsa kamar me, tana kallo ya shiga motar yana jiran hussien, shima kamar yanda hassan yayi haka ya juya ya fice batare da yayi magana ba tana tsaye taga sunja motar da qarfi sun bar wurin batare da sun sake waiwayentaba, kada dai sunyi fushine suka barta nan da nan hankalinta na tashi hawaye na soma xubo mata, ganin kallo ya dawo gareta yasa ta sunkuya ta dauki kayan ta shige cikin gida......, ku biyoni mubi yan biyu kyautar Allah, muji anya TAGWAYEN MAXA xasu bar abinda suke su shiryu saboda hamida? Idan suka gyara halayansu dukansu waye xata xaba? Hausa novel [5:12PM, 11/30/2015] pherty: [11:10AM, 11/12/2015] Pherty: 22 TAGWAYEN MAXA Na fertymerh xarah Tunda ta shigo gidan take kuka sosai, umma ta taso tana tmbyrta lfy, da kyar tayi mata bayanin komai umma tayi shiru tana saurarenta kawai......... momy sai faman xirga xirga take a tsakiyan falo ranta duk a bace ta rasa xaman tun fitarsu hr uncle dinsu yaxo ya fita bai fahimci komai ba tana nan tsaye suka shigo a tare hussien ne ya gaidata hassan kuwa dauke kansa yayi yana kallon dianing, ta bisa da kallo kafin ta maida kallonta ga hussien tace kardai kunje ingawa ne hussien inda waccan banxar hassan ya juyo yana kallonta nooooo momy kidaina kiranta banxa mana surukar kice fa, meyasa kike hakane? ta saki baki tana kallonsa cike da mamaki surukata kace as n how? ban fahimceka ba ya dubi hussien kafin ya soma kiciniyar cire rigar jikinsa yana fadin aurenta xamuyi nida hussien, bakiga munje neman auren bane tor waye ta xaba ne? ya yatsina fuskarsa ya xauna, hussien yace momy hamida bata xabi ko daya acikinmu but am sure ni xata xaba danni naji mgnrta xn daina abinda nakeyi momy tace hr wani abu kukeyine da bataso menene shi bansanshi ba? hassan yayi caraf yace noo ummma kibar wannan sirrin mune mu kadai ba wnda yasan da shi sai ita hamida momy tace hrdani mahaifiyar taku, hr akwai abinda xaku boyemin amma wata can mai aiki tasan sirrinku bndani, ya yatsina fuskarsa ya matso ya kara mata rigarsa a hancinta yace momy kiji yanda qauyen k wani wari duk ya batamin jikina baxan iya cin abinciba sai nayi wanka na cnxa kaya, duka mutanen ingawa "they ar not wise they ar ol villagers",inbanda haka meye nasu na xuwa kallonmu nida hussien,ko bamuyi kyau bane ko akwai wani sabon abu a jikinmune (ya fada yana yarfe hannuwansa cikin yatsina fuska) baqincikiduk ya taru ya cunkushe mata xuciya ta juya ta fice a fusace tare da alqawarin sai taga bayan hamida baxata bar gwarxayen maxajenta su qare rayuwarsu akan yar aikinta ba [11:34AM, 11/12/2015] Pherty: hussien yace gobe xamuje ne,inaso na qara ganinta xn gayamata na daina neman mata hassan ya tsare sa da narkakkun idanuwansa kafin yace impossible hussien baxa muje gobe ba sai nxt tym kuma baxan daina ba saboda mace haba dai macece fa Allah baxan bari ba kuma baxata xabe kaba, ina ga dama sai na canxata u knw inada bula bula yan mata kawai they ar not my choice ne, inason mace mai ilimi, mai iya kula da miji da boye sirrinsa saboda hakanne kawai nakeson hamidan kaima ksan ba ajina bace ko turanci ta iyane? 23 Hussien yaja tsaki tunda ba ajinka bace kabarmin ita mana dama ni takeso bakai ba hassan ya lashi jajjayen labbansa yana kallon hussien yana dan wani naxari kafin yayi murmushin da dimple dinsa na bayyana yace tor shikenan na barma, x not bad kuma ba abin baqin ciki bane, nida kai duk dayane, hussien ya dora yatsansa akan dimple din hassan wurin ya lotsa da hannunsa(yana son dimple din hassan da yawa yakan tsaya yayita kallonsa idan yana mgn yanda wurin k lotsaya ko yana cin abinci, shine kawai banbancinsu dama) yace dan uwana baxai bar abinda yakeso saboda niba, nima baxan barta saboda kaiba allura ce acikin ruwa nidakai xamu gwada sa'a aga wanda xai cirota hassan yayi murmushi kawai ya janye hannunsa daga fuskarsa idan da sabo ya saba da hussien wurin taba masa dimple, ya juya ya fice batare da yayi magana ba. [11:59AM, 11/12/2015] Pherty: * Tun daga lokacinduk bayan sati sai sunje ingawa inda hamida tun tana kaucewa tana masu wulaqanci hr ta fara sakin jiki dasu tana ganin hakan shi xaisa su daina abinda suke idan suka saba da ita, wataran ma hr cikin garin suke xagayawa mutanen garin na biye dasu suna kallon fararen mutane hassan da hussien sun soma jin dadin qauye duk da hassan bai ida sakin jikinsa ba still yana qyanqyamin qauyen kuma baya boye w damashi direct yake komai nasa, ban manta akwai wani lokaci da suka xo hamida ta tursasa masu akan sai sun shiga sun gaida ummanta kai tsaye hussien ya shiga, hassan kuwa tun bakin qofar shiga gidan suka soma rigima dashi akan lallai shi baxai shiga gidnba idan hr sai ya sunkuya, danme xa'ayi qofa qarama ace sai mutum ya sunkuya gidan xai shiga hussien ya juyo yana kallonsa yace control ur mouth, hassan yace idan dole ne sai na shiga ka kira wadannan builders din suxo su qarawa qofar tsayi inshiga saboda ni mai tsayi ne ba gajare bane, hussien ya girgixa kansa kawai cikin mamakin hali irin na hassan ya shige cikin gidan hamida ta kallesa idanunta sunyi rau rau kamar xatayi kuka itadai tana son hassan kome yayi yana burgeta tace ahakan kakesona, ahakan xakaxo neman aurena kana kyamar gidanmu kana gudun gidanmu,tor waye xai baka aurena kana wulaqanta arxikinmu, tafashe da kuka ta juya xata fice xata shige yayi saurin riqo hannunta sai da yaji wani shock karo na farko a rayuwarsa da jikinsa ya soma haduwa dana mace yana cikin hayyacinsa, sai yaji wani iri banbarakwai ya saki hannunta da sauri yana yarfe hannuwansa ita kuma idanu ta tsura masa cike da mamakin lashin hannunsa duk da ita agareta bana farko bane tunda ta saba riqosa ta kawosa dakinsa idan ya sha amma yau taji wani daban batare da yayi mgn ba ya sunkuya ya shiga kamar xaiyi kuka gani yake an raina tsayinsa bdan hamida ba baiga wanda ya isa yasashi duqawa ba ya sami hussien da umma xaune a tabarma suna hira kamar sun saba can(baisan umma a tsorace take da hussien ba kyaunsa ya rudata take ganin ba mutum bane dan dai hamida tace mutanene shiyasa ta xauna suna gaisawa amma jikinta hr kyarma yakeyi) ganin hassan ya shigo gidan yasa ta xabura daga xaman takurar da take tajuya tana kallonsu daya bayan daya ita bataga banbancinsuba ko hasken fatarsu dayane komai na fuskarsu hr jikinsu da tsayinsu duk dayane hakan yasata tsorata take tunanin kodai tayi gamo da aljanine yake mata gixo da fuska biyu tunda ga kayan jikinsuma iri daya (wannan karonma hr kallar kayansu iri dayane) sai ta saki ihu ta shige quryar daki a tsorace tana karanta amanar rasulu a bayyane cikin dagawr murya [12:18PM, 11/12/2015] Pherty: hussien yasan ta tsoratane da ganinsu sai ya soma dariya hrda taba hannayensa 24 shikuma hassan sai yatsina fuska yake dama tunda ya shigo gidan yaga yanda yakee ya koma da sauri hamida ta maidoshi, kusan sau uku yana shigowa yana fita hamida na maidoshi da kyar ta samu ya qaraso ciki tor gashi tsohuwar ta qara bashi haushi ta maidashi wani dodo tana ganinsa xata wani shige daki tana addua da kyar hamida taje ta lallaso umma ta fito da ita suka gaisaa tsatsaye da hassan yace noooo hamida am sorry amma i cant live in dis environment, hussien a juya yana kallon gidan baiga wani abin qaxantaba ko ina tsaf tsaf kafin yayi mgn tuni hassan ya juya ya fice yana isowa qofar gidan ya manta da sai ya sunkuya yasa kai ji kake goshinsa ya buga wurin gauuuuuuu ya saki qara hannunsa a goshinsa suka fito suka samesa yana ludda wurin oh gosh, chaiii..... Allah baxan qara shiga wannan gidanba idan bxaa qarama qofar tsayi ba, ya duqa ya fice a harxuqe. Hamida tafito tare da hussien ta rakasu suka dauko kyautarsu da sukaxo da ita takalmine masu kyau komai iri daya banbancin kalace kawai dama haka suke mata kyauta duk abinda xasu bata iri dayane sai dai su banbanta kala, idan sarqace iri dayace sai dai dayan tanada digon baqi wata digon ja ko wata kala, idan atampha ce xane iri daya banda kala, lace, englishi wears e.t.c duk iri daya suke bata kuma lokaci daya, su basu yarda suyi hassadar junansuba basu son cikinsu ace wani yafi wani sunfiso ace dai dai suke, komai xasuyi sai sun shawarci juna . da hakan sukayi sallama suka fice, taje ta samu umma suka soma tattauna xancen * Akwai wni lokaci sun dawo daga xaga garin suna tare su uku suna hira gab da xasu iso gidan hamida taja ta tsaye idanu a waje duk suk dubeta alamar tambaya da hannu ta nuna masu gidansu momy suka gani tsaye tare da wasu gardawan maxa ana rushe masu gida nan da nan hamida na soma hawaye suka qarasa wurin umma na daga gefe tana kuka hamida tabungumeta momy kallo daya tayiwa yan biyu ta dauke dubanta garesu hussien yayi qoqarin hanata [12:32PM, 11/12/2015] Pherty: hasan ya riqosa yace noo bros, cool ur mind, kabar momy tayi abinda takeso ko xata sami rest of mind, mahaifiyar muce idan wannan abin xai sata farin ciki kabarta tayi taji sanyi a ranta hussien yayi shiru lokaci daya suka sa dark space dinsu suka sarqe hannuwansu a qirjinsu hade da jinginawa jikin motarsu suna kallonsu sai da momy tasa akayiwa gidan kaca kaca aka rushe komai sannan ta shiga motarta mutanenta na bayanta suka bar garin ingawa hussien yaciro wayarsa ya matsa daga gefe shima hassan haka yayi suna tsaye suna kallon yndasu hamida ke kuka hr ma'aikatan da suka kira suka iso kusan kashi biyu kowa ya kira nasane hussien yace tor duk su hada hannu suyi aikin tare shi yayi masu bayanin yanda yakesonbgidan kafin ya juya yana kallon umma yace umma kuje maqota ku xauna hrna wasu kwanaki kafin agama ginin umma ta shiga wani gida tana hawaye hassan sai kallon hamida yake tana sharar kwalla, abin nan dayaji ranar daya riqa hannuta shi yakeson ya qaraji idan ya riqa hannunta , bai tabajin irin wannan abinba shiyasa yakeso ya qara taba hannu yaji ko xaiji, sai ya juya yana kallon hussien da hankalinsa na gun aikin da ake, ya nufi inda hermyderh k tsaye yana wani yatsina fuskarsa. Hausa novel [5:15PM, 11/30/2015] pherty: [3:40PM, 11/14/2015] pherty: 25 TAGWAYEN MAXA Na fertymerh xarah Yana isowa dab da ita sai kuma yaja ya tsaya yana jin nauyin tabata abinda bai saba yiba, ta share hawayen ta tana kallonsa sai ya dauke kansa yana kallon wani gun, still shaidan na qara tunxurasa ya tabata ko xaiji wannan abin dayaji dayake komai direct yakeyinsa sai kawai ya riqo hannunta itama tabisa da kallon mamaki mtsew yaja dogon tsaki yana fadin banji komai ba fa, ya saketa yana yatsina fuska bata gane meyake nufi ba illah kallon mamaki datake masa a xuciyarsa yace kodan wancan karon nina bata mata raine tunda yanxu momy ce tasata kuka,kenan idan momy ta tabata xataji wannan shock din tor shi ynxu mema xai mata ya bata mata rai yatabata ko xaiji hussien ya qaraso yana fadin nagaji muje gida, hamida kishiga gidan da umma ta shiga hr gobe idan mun dawo, a sanyaye ta gyada kanta tana kallonsu suka shiga motarsu suka fice [4:54PM, 11/14/2015] pherty: tym din da suka iso gidan kamar momy na jiransu ne ta soma balbale su da masifa, fada take ba kakkautawa abinda basu taba ganiba sai suka harde hannuwansu suna daga tsaye suna kallonta hr tagama hussien yace kiyi haquri momy mundaina tunda bakyaso, baxamu sake xuwa guntaba kuma munjaye mgnr mu ta neman auren hamida amma momy Annabi mohd s.a.w yace wanda bai jinqan mutane Allah baxai yi jiqansaba mussaman talakawa hassan ya janye hannuwansa yana kallonta yace kin mantane momy Annabi mohd s.a.w yace wanda ya tausayawa mutum koda dabbobi ne Allah xaiji qansa a ranar tsayuwa, c'mon momy bnga abin fada anan ba bnga dalilinki na son wargaxa rayuwarsu ba idan mune bakyaso da hamida shikenan mun barta , ya juya ya fice hussien ma yabi bayansa. Bayan kwana biyu momy na xaune da xuqa xuqan yan mata ya'yan abokantane su ta xabawa yan tagwayenta ko wacce ba laifi tana da irin nata kyau kuma sunaji da kudi yan biyu suka shigo falon suna tafe suna dariya kamar basuda wata matsala a xuciyarsu gabaki daya yan matan sai da suka rude basuyi tsammanin kyawunsu da kwarjininsu xai rudasu haka ba sai kowacce ta sallamawa xuciyarta basu kulasuba suna tafe suna hira abinsu gab da xasu shige sashensu momy ta kirasu ganin ko kallonta basuyiba cak suka tsaya suna saurarenta batare da sun juyo ba tace kuxo nan nace ba mgn nake maku ba, suka dubi juna suna yatsina fuskarsu kana suka tabe bakinsu suka juyo suka dawo tsakiyan falo sunyi tsaye sun xuba mata idanu tace kun shigo ba sallama baku gaidani ba ballantana kusan da yan'matan dana xaba maku ku aura abinku da manemin mata yaji ankira mata sai ya juya yana kallonsu da sauri hussien kenan hassan kuwa tabe bakinsa yayi shi bai kallesu ba kuma shi bai dauke dubansa ga momy ba hussien ya maida kallonsa gareta yace momy wadannan fa ta soma murmushi tana fadin ka xabi daya hassan ya xabi daya nxt mnth sai ayi aurenku ya cije jajjayen labbansa yace ni bana son ko daya(sai da yan matan suka tsorata)ba wacce tayimin ban saniba kodai hassan, ya fada yana kallonsa hassan ya qara tsuke fuskarsa shi ajin nasa ma ya hana ya kallesu gani yake girmansa ya fadi ya tsaya kallon mata ya dafe goshinsa da hannunsa gosh" momy kamata xaki nemawa macce kenan tallata kike ta harxuqa tace kada ku maidani wata shashasha mana kagayamin aibun wadannan yan mata daxakace ba wadda tayima, kai kuma kake gayamin mgnr banxa alhali baka dubesu ba ransa ya qara baci ya juya yana girgixa kansa yana yarfe hannayensa yace baxan kalli ko dayaba kuma banason ko daya hussien ya tabe bakinsa yana qara qare masu kallo kamar xai taya dayar bawai da aure ba sai kuma ya fasa ya juya yabi bayan hassan iya jin kunya momy taji kunya.musamman da yan matan suka soma roqonta akan ta lallashesu sudai tunda suka gansu sunji suna so(yar baqa ma tayi naci ta barsu) momy tace karsu damu nan da lokaci qanqani su dubesu gidansu yan matan mai suna maryam da salma suka tashi cike da murna suka fita, momy ta tashi a harxuqe ta nufi sashensu amma tana murqa qofar falon tajita qarqame alamar sunsa key tayi bugun qofar su bude sunajinta sukamata banxa hrtagama fadanta ta hayewarta sama. 26 kwanaki kadan hr an kammala ginin gidan ba laifi duk ingawa bamai irin ginin gidansu hamida sai gashi mutane sun soma bibiyarsu ba kamar da da ake hantararsuba ranar da suka shiga gidan an kammala komai ansa kujeru da duk wani abu na qayata gidan a ranar kuma yan biyu sukaje batare da sanin momy ba wannan karon ba gardama hassan ya shiga gidan tunda an masa qofa dai dai tsayinsa mai hali baya barin halin ranar da sukaxo ranar aka bude gidan su hamida suka tare gadai gida sabone ko ina tsaftsaf tayis sai sheqi yake ga qamshi natashi a falon umman amma hassan sai yatsina fuska yake yn kakkama rigarsa karta dauki datti [5:30PM, 11/14/2015] pherty: sai wani kyankyami yake nunawa hamida na lura dashi ta rasa gane murdadden raayi irin na hassan yayi tsaye bakin falo umma dasu hussien nadaga ciki umma sai godiya take tana sharar hawaye dan bata taba tsamani ko mafarkin irin wannan gidan xai xama nataba hussien yace ba komai umma Allah xaki godewa shine yayi maki ba muba ta juya tana kallon hassan a dan xaman da tayi dashi ta soma gane halinsa shidai daban ne ta lura sai wani shan qamshi yake yana qarawa, a dabi'unsa take banbanceshi da hussien bayaga haka baxata iya banbantasu ba tace hassan baxaka xauna bane yayi rau da idanunsa yana kallon hamida taxo ta riqa hannunsa da niyar taje ta xaunar dashi, gogan kuwa sai yaji irin abinda yakeso yarrrrrr tsikar jikinsa hr tashi take kasala ta saukar masa hr kusa da umma ta xaunar dashi duk jikinsa amace ya tafi duniyar tunani wannan riqonsa kawai tayi yakejin wannan abin tor idan ta rungumesa fa mexaiji chab sai ya soma murmushi wanda yaja suke kallonsa cike da mamaki dawowar tunaninsa ya dubi inda yake xaune kusa da umma a hankali ya matsa daga kusa gareta tace hassan me xn kawo mane yace ba komai umma nagode tace a'ah kyautar Allah kagayamin koma menene xn baka shi inaso ne kasaki jikinka dani kamar hussien yace tor tunda kin matsamin kibani hamida ni ita nakeso tayi shiru tana naxari idan aurene tafi sha'awar hamida ta auri hussien yafishi faraa da son mutane baya kyankyami ko wulaqanta mutum kamar hassan shiyasa hrta yankewa xuciyarta hukuncin hussien tabawa hamida ko bayan ranta shikuma hussien sai yabkwashe da dariya yace wannan ce matsalar ka hassan hassan ya harxuqa ya tashi olryt shiyasa naga umman tamin shiru tunda baxaku bani ba shikenan kafin suyi mgn tuni ya fice hamida ta tashi tabiyosa hr harabar gidan tace hassan meyasa kakemin hakanan ya juya yana kallonta tor menayi daman nasan keda ummanki baku sona hussien kukeso tor meye abin damuwa tunda jininane shi kije nabar masa ke tace meyasa kake wannan mgnr me nayi nida ummana yace ai tunda nace ina sonki kema ai bakice kina sona ba hussien kike so ta girgixa kanta tana hawaye ba haka bane kayarda dani ina sonka hassan yace tor shi hussien fa kina nufin bakyasonsa? tayi xurr da ido tana kallonsa tace shima ina sonsa yayi murmushi alamar yaji dadi daxu kin riqani naji dadi ynxu kuma ina son ki rungumeni ingani mexanji(tor fa ikon Allah) a tsorace take kallonsa idanunta waje tace in rungume kafa kace.... ya gyada kansa yana murmushin da dimple dinsa ya bayyana abinda ke qara burgeta dashi kenan shifa har a xuciyarsa he mean it bai iya boye abinda k xuciyarsa ba shiyasa yakeyin komai direct ta girgixa kanta baxai yiwuba kadaina wannan tunanin yace nooooo hamida karkice haka pls bana neman abu na rasa just for you to hug me inaso naji wani abune pls wannan karon jikinta har rawa yake uwa uba gashi ya tsareta da narkakkun idanuwansa yana kallonta....... Hausa novel [4:37pm, 10/6/2016] Fatyma Zahra Too Nv: 27 TAGWAYEN MAXA Na fertymerh xarah Ta soma ja da baya tana girgixa kanta tace ai ni ba yar idka bace..... ya tabe bakinsa hade da daga kafadunsa yace tor shikenan tunda baxaki bani ba itama tabe bakinta tayi dai dai lokacin hussien ya fito yana kallonsu fuskarsa dauke da murmushi yace hamida kishiga gida umma na jiranki itama tana murmushi take kallonsa tace tor shikenan, ta juya xafa fice sai hassan ya kirata keeeey.....xo nan, ta juyo tana kallonsa cike da mamaki kamar baisan sunanta ba ya qaraso inda take tsaye yavriqo qaramin yatsanta ya sanya mata xobe, hussien na ganin haka shima ya tuna danashi yaxo ya riqo hannunta da hassan k riqe ya sanya mata xoben a yatsan da hassan ya samata sai ta saki baki tana kallonsu taya xobe biyu xai xauna a yatsa daya hussien yace kada kiciremin xobe kibarshi inda nasa maki hassan ya furxar da iska daga bakinsa yace nima kada ki canxashi daga yanda nasa maki shi.......lokaci daya suka juya suka shiga motarsu suka fice tabi yatsun hannunta da kallo xobe biyu a yatsa daya wannan ai haukace [5:16PM, 11/19/2015] pherty: * Momy sai faman kaiwa da kawowa take a tsakiyan falonta tasani ba wata hanya daxata iya raba yan biyu dinta da wannan yar iskar yarinyar idan har bata halaka ta ba, mafita daya ce taje ta basu haquri akan abinda ta masu kana ta roqi alfarmar hamida ta dawo aiki gidan tana ganin ta haka xata

Chapter 2 of 5