Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
san cewa baza mu iya shiga wancan kurkuku ba saboda tsaronta shiyasa muka yi shiri muka zo gidan sarautar muka saceki, mun tabbatar da cewa indai kina hannunmu, sarki zaiyi duk abinda mukeso. Kiyi hakuri akan abinda Riya tayi miki, kinsan zafin rabuwar ɗa da ubansa." Koda Aymanul Faris yazo nan a jawabinsa sai gimbiya Jaanu ta fashe da kuka saboda tsananin tausayi. "Ya ku waɗannan 'yan uwa, kuyi hakuri bisa rashi da kuka yi na masoyanku da 'yan uwanku. Tabbas mahaifina ya cika azzalumi mara tausayi, amma nayi alkawarin da sannu zan sauya shi matuƙar zai sauyu. Ya kai wannan jarumi hakika nikam na kamu da tsananin kaunarka tun sa'adda nayi arba da kai a cikin turakata. Haƙiƙa kana da kyawawan halaye irin wanda kowacce mace take burin samu. Nagode da kulawar da kake nunawa a gareni." Jaanu ta karasa maganarta tana mai goge hawayen dake zuba a idanunta. Aymanul Faris rike hannayenta biyu yayi cikin tsananin so da kauna ya ce, "Nima ina tsananin kaunarki kamar yadda kike kaunata, amma da akwai matsala." Cikin hanzari gimbiya Jaanu ta dago kai ta kalleshi ta ce, "Matsalar me kuma?" Aymanul Faris ya daga kai ya kalli inda jaruma Riya ke tsaye sannan ya fice daga ɗakin, ba tare da ya bata amsar tambayar da tayi masa ba. **** A can birnin Damashkar dai, al'amura sun dada caɓewa sarki Ayubul Zairiy. A ranar wuni guda yayi cir bai sa komai a bakinsa ba, kuma yadda yaga rana haka yaga dare wato bai rintsa ba. Mutanen birnin Damashkar dai su ma a ɗimauce suke saboda yadda suke tsananin kaunar gimbiya Jaanu saboda adalcinta, ace ta ɓata ai akwai matsala. Sarki Ratanam da ɗansa Marganu kuma a ɗakinsu raba dare suka yi suna hira akan al'amarin suna mamakin hatsabibancin da ya shigo har cikin gidan sarautar kasar Damashkar ya sace 'yar sarki guda ba tare da asirinsa ya tonu ba. "A'a naji ance an sami hatimi mai zanen wasu bakaken rubutu masu kama da na mutanen birnin Sin a inda aka shaƙawa dakarun dake tsaron lafiyar gimbiya banju, na taba kallon zanen wannan hatimi a birnin Sin, shaida ce ta wani gawurtaccen barawo wanda ya talautar da sarki Kim Sam a dare ɗaya." Inji sarki Ratanam, ya bawa ɗansa Marganu amsa akan ko akwai alamar da ɓarawon ya bari. Yarima Marganu ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Lallai ko waye wannan ɓarawo ya cika hatsabibi kuma abin tsoro tunda har zaizo yayi sata kuma ba'a kama shi ba a wurin da yafi ko'ina tsaro a birnin Damashkar. Amma meyasa zai sace gimbiya Jaanu maimakon ya saci dukiya kamar yadda ya saba?" Koda jin haka sai sarki Ratanam ya numfasha ya ce, "Wannan tambaya taka abar dubawa ce. Watakila niyyarsa akan satan dukiya ne amma da yayi arba da kyawun gimbiya Jaanu sai ya canja shawara. Watakila kuma dama shirinsa akan satan gimbiyar ne domin yaje yayi ta amfani da ita, ko kuma aljanun da suke taimaka masa ne suka buƙaci ya kawo musu kyakkyawar 'yar sarki." Yarima Marganu ya cije baki. "Ai kuwa idan ya kuskura ya shafa koda kyakkyawan jan gashin dake kanta ne sai na hukunta shi, idan ya shiga hannuna. Saboda Jaanu tawa ce ni kadai." Sarki Ratanam ya yi murmushi ya ce, "Da wuya. Mutumin da ya gallabi manyan sarakunan duniya da sata, me zaiyi da ƙaramar yarinƴa kamar Jaanu? Mu jira kawai zuwa wani ɗan lokaci na tabbata zai bayyana bukatarsa." Haka dai sarki Ratanam da ɗansa Marganu suka ci gaba da hira, har barci ya sace su. Kashe gari tun daga ketowar alfijir sarki Ayubul Zairiy ya fita izuwa fadarsa ya zauna akan karagarsa yana mai jiran bayyanar boka Ruguzan domin yaji inda 'yarsa Jaanu take. Sai da gari ya gama wayewa sosai aka kawowa sarki abincin kalaci, amma ko kallon abincin baiyi ba saboda ba shine a gabansa ba. Jim kaɗan kuma sai ga sarki Ratanam tare da ɗansa Marganu sun shigo cikin fadar sanye da kaya masu tsadar gaske, nan take suka zazzauna akan kujerun da suke zama kullum. Bayan sun gama gaisawa da sarki Ayubul Zairiy sai sarki Ratanam ya dube shi ya ce, "Ya kai abokina shin akwai wani labari kuwa akan inda gimbiya take?" Koda jin wannan tambaya sai sarki Ayubul Zairiy ya ce, "A'a ban samu wani labari ba amma ina jiran zuwan shugaban bokayen ƙasata domin na san halin da ake ciki. Yanzu haka shi nake ta jira tun ɗazu amma bai ƙariso ba." Ayubul Zairiy na rufe bakinsa, wani dunkulen haske ya faɗo cikin fadar kamar curin nakiya. A hankali hasken ya dinga tarwatsewa yana zamowa hoda, siffar boka Ruguzan ta dinga bayyana dishi-dishi a cikin wannan hoda. Ba'a jima ba ya gama bayyana tsulum, a wannan lokaci ma baƙaƙen kaya ne a jikinsa. Fuskar boka Ruguzan na dauke da tashin hankali da jimamin abinda ya gani, lamarin da yasa jikin sarki Ayubul Zairiy yayi sanyi kenan. Ya taso da sauri ya zo gaban boka Ruguzan ya kama kafaɗunsa ya ce, "Ya kai wannan boka, shin ka gano inda gimbiya take?" Boka Ruguzan ya dube shi cikin nutsuwa ya ce, "Akwai matsala. Shugaban ɓarayin duniya ne ya sace 'yarka. Ya kai shugabana kayi sani cewa nayi iya bakin ƙoƙarina wajen gano inda wannan ɓarawo ya kai 'yarka amma na gagara ganowa saboda ya fini karfin nesa ba kusa ba. Tabbas rayuwar gimbiya na cikin mugun haɗari, domin a binciken da nayi na gano cewa wannan ɓarawo ya ninka dukkanin attajiran dake wannan birni namu a yawan dukiya sau dubu, wato gawurtaccen attajiri ne da babu kamarsa a duniya. Haka kuma gawurtaccen boka wanda yafi kowa ƙarfin sihiri a duniya tunda gaba ɗaya bokayen duniya sun gagara gano ko waye shi, tsawon shekara da shekaru. Idan kayi la'akari da haka, kaga kenan ba dukiya yake so ba. Ba kuma wani sihiri zaiyi da ita saboda ya cika ya tumbatsa da ƙarfin sihiri. Dole cikin biyu za'a yi ɗaya. Ko dai wannan ɓarawo ya aure wannan 'ya taka ko kuma wata bukata mai karfi zai nema a wajenka wacce ya tabbatar da cewa kaine kaɗai ne zaka iya biya masa ita. Yanzu dole mu jira mu ga meye yunƙurinsa na gaba, idan har yana da wata bukata to tabbas zai aiko da wasiƙa. Idan kuma mu kaga kwanaki uku sun shuɗe bai nememu to tabbas akwai matsala sai dai mu shiga duniya muyi ta nema" Koda boka Ruguzan yazo nan a zancensa sai sarki Ayubul Zairiy ya sake kwarara uban ihu ya dubi Ruguzan ya ce, "Kana ganin nan da kwanakin ukun zai iya aiko mana da wasiƙa, yana bukatar wani abu?" Ruguzan ya ce, "Ina kyautata zaton haka." Sarki Ayubul Zairiy ya ce, "Allah dai yasa ya aiko ɗin." ***** Dakin a haskake yake da manya-manyan fitilu masu tsananin haske, mutum uku zaune ne a cikin ɗakin bisa kujeru na tagulla. Ɗaya daga cikin mutanen saurayi ne kyakkyawa wanda ba shi da sura ta jarumta amma yana ɗaure da kambun tsafi a damtsen hannunsa na hagu, idan ka san sarkin ɓarayi Barban to shine. Ɗayan kuma yaro ne ɗan kimanin shekaru goma sha tara amma idan kaga murdewar jikinsa sai kayi zaton ya baiwa shekaru ashirin baya saboda tsabar murɗewa da tarin kwanji, idan mutum ya san Aymanul Faris to zai gane cewa shi ne ba wani ba. Na ukun ne wani dogon saurayi mai doguwar fuska wadda take ɗauke da wani ɗan gajeran gemu, idan ka duba bayansa zaka ga fuka-fuki guda biyu masu kauri hakan ne zai tabbatar maka da cewa aljani ne ba mutum ba. Kujerun da Barban da Aymanul Faris suke a haɗe suke suna fuskantar kujerar aljani Ranganu. Muryar Ranganu ta fara bada sauti mai kama da kukan kosasshen jaki, "Na gama rubuta muku wannan wasika, yanzu take nake so kai Barban ka baiwa daya daga cikin aljanunka ya kaiwa boka Ruguzan wannan wasiƙa. Na zana taswirar gimbiya Jaanu a jikin wannan wasika sannan na zana taswirar mahaifiyar Aymanul Faris a jikin wasikar. Idan yana bukatar 'yarsa to dole ne ya dauki Mahaifiyar Aymanul Faris ya kaita dajin Marsas dake karshen birnin Sin, sannan mu kuma mu bashi 'yarsa. Acan zamu karbi Hajriya sannan mu bashi 'yarsa. "Wancan daji na Marsas asalinsa mallakin babana ne, babu yadda za'ayi sihirin tsafinsu yayi tasiri a cikin dajin." Aljani Ranganu na zuwa nan a zancensa ya fiddo wata takarda nannadaddiya wacce aka yiwa ado da ruwan zinari ya baiwa Barban, sannan ya ɓace ɓat! Barban ya shafi kambun dake ɗaure a hannunsa take waɗannan gabza-gabzan aljanu guda uku suka bayyana, suka fadi ƙasa suka ce, "Me kake bukata ya shugabanmu?" Sarkin barayi Barban ya basu wannan wasika ya ce, "Su kaiwa boka Ruguzan dake birnin Damashkar." Aljanun nan suka ce an gama sannan suka ɓace ɓat. Aymanul Faris yazo gaban Barban ya zube ƙasa yana godiya bisa taimakonsa da yayi. Barban ya taso shi tsaye ya ce, "Kwantar da hankalinka babban jarumi, wannan ai yiwa kaine. Ina fatan dai har yanzu baka manta cewa ban fada maka aikin da zaka min ba." Aymanul Faris ya ce, "Wanne aiki kenan?" Barban ya ce, "Zan faɗa maka amma sai bayan hankali ya gama kwanciya wato mun kuɓutar da mahaifiyarka daga hannun su sarki Kuffuru." Yana gama fadin haka ya fice daga dakin. *******RUHIN JARUMTAKA! * Babi na 6: *Sarki Kuffuru* * * Umar Sangaru * Sarki Ayubul Zairiy bai jira lokacin tashi daga fada yayi ba, ya tashi ya shige cikin gidan sarautarsa. Kai tsaye ya wuce cikin turakarsa ya kulle kansa a cikin turakar, sannan ya durƙushe bisa gwiwowinsa ya fashe da kuka. Yana cewa a ransa, "Me na yiwa sarkin ɓarayin duniya har zai sace ƴata? Shin me zai buƙata a wajena maimakon wannan ƴa tawa?" Da ya rasa wanda zai bashi amsar waɗannan tambayoyi sai ya sake fashewa da sabon kuka. A daidai wannan lokaci ne yaji wata azababbiyar ƴunwa ta rufe shi, wani mugun jiri ya ɗebe shi baisan sa'adda ya faɗi ƙasa ba, ya fara juye-juye kamar wanda zai mutu. Muryarsa na rawa ya ƙwalawa wani hadimi kira, take hadimin ya rugo cikin turakar. Koda yaga halin da sarki ke ciki sai ya ɗimauce, ya ruga zai tallafo shi. Sarki Ayubul Zairiy ya daka masa tsawa ya ce, "Kai Muzaffar je ka kawo min abincin kalaci, amma ƴaƴan itatuwa zaka kawo." Hadimin ya risina sannan ya fice, jim kaɗan ya dawo ɗauke da farantin kayan marmari, ya ajiyewa sarki a gabansa. Da ƙyar sarki Ayubul Zairiy ya miƙe zaune sannan ya fara cin wannan kayan marmari, bai gushe ba yana ci sai da ya ƙoshi taf. Gama cin wannan abinci keda wuya sarki Ayubul Zairiy yaga hadimi Muzaffar ya sake shigowa cikin turakar, ya zube a gaban sarki. "Ya shugabana boka Ruguzan ya dawo ya ce, a kirawo masa kai." Sarki Ayubul Zairiy ya ja dogon numfashi ya ce, "Shin fadar ta watse ne? Ko har yanzu akwai jama'a?" Muzaffar ya ce, "Kwarai har yanzu akwai jama'a birjik a fadar." Sarki ya ce, "Je ka yiwa boka Ruguzan jagora izuwa wannan fada tawa, tare da su sarki Ratanam da ɗansa." Hadimi Muzaffar ya sake risinawa sannan ya fice daga cikin turakar. Jim kaɗan aka sake buɗe wannan ƙofa, boka Ruguzan, sarki Ratanam da ɗansa yarima Marganu suka shigo cikin turakar. Sarki Ayubul Zairiy ya ja su gefe guda inda aka tanadi wadansu kujeru masu yawan gaske suka zazzauna. "Ya kai shugaban bokaye meke tafe da kai?" Sarki Ayubul Zairiy ya tambayi Ruguzan. Maimakon boka Ruguzan ya bashi amsa kawai sai ya sanƴa hannu a cikin aljihun rigarsa ya fiddo wata nannaɗaɗɗiyar takarda, koda sarki Ayubul Zairiy ya yi arba da wannan takarda sai gabansa ya faɗi. Ruguzan ya miƙa masa wannan takarda. Hannun sarki Ayubul Zairiy na karkarwa ya karɓi wannan takarda, ya buɗeta amma sai ya gagara karanta abinda ke ciki. "Ya shugabana ka kwantar da hankalinka, ka karanta abinda ke cikin wannan takarda saboda ita ce kawai mafitar mu." Inji boka Ruguzan tamkar ya san abinda ke cikin takardan. Sarki Ayubul Zairiy ya yi ajiyar zuciya ya kwantar da hankalinsa, ya sake buɗe takardar ya fara karanta ta a fili kamar haka: "Wasiƙa daga shugaban ɓarayi, sarkin talakawa na duniya. Zuwa ga sarkin Damashkar, sarki Ayubul Zairiy. Ya kai wannan sarki da fatan kana lafiya. Ba don komai na aiko maka wannan wasiƙa ba sai domin na shaida maka cewa ƴarka gimbiya Jaanu tana hannuna, ma'ana ni ne wanda ya saceta. Ba don komai na sace wannan ƴa taka ba sai domin kuɓutar da ƴar uwata, mahaifiyar Aymanul Faris daga kurkukun daka tsareta. Idan kana buƙatar ƴarka, to ya zama dole ka aiko mana wannan mata ko kuma ka kawota da kanka izuwa dajin Marsas dake ƙarshen birnin Sin nan da cikar kwanaki talatin, idan ba haka ba kuwa. Zan yanko kan ƴarka na aiko maka da shi. Ƴarka tana cikin ƙoshin lafiya, ka tabbatar da cewa an kawo mana wannan mata a cikin ƙoshin lafiya idan ba haka ba kuwa, ka san sauran... Za mu kasance masu jiran zuwanku a dajin Marsas ranar ashirin da tara ga watan Nuwamba. Idan kana so ka ceci ƴarka, sai ka kawo wannan mata a wannan rana. Kahuta." Lokacin da sarki Ayubul Zairiy yazo nan a karatun wasiƙar sai hankalinsa yayi mummunan tashi, idanuwansa suka kaɗa suka yi jawur. Kamar yadda sarki Ayubul Zairiy ya tsinci kansa a cikin wannan hali haka shima sarki Ratanam ya kasance, al'amarin da yayi matuƙar baiwa Marganu mamaki kenan. Ya dube su ya ce, "Ya ku shuwagabanina me yake damunku ne, naga duk kun sauya? Shin wannan fursuna da za'a sake tana da haɗari ne, wanda zai sa ku ji tsoron sakinta? Ai ni a gani na rayuwar gimbiya Jaanu tafi ta wannan fursuna muhimmanci a gare mu!" Sarki Ayubul Zairiy ya ɗago kai ya dubi yarima Marganu ya ce, "Wannar fursuna da muka tsare, ba ni ne wanda ya kamota ba. Mai gidanmu ne nida mahaifinka. Kayi sani cewa wannan kurkuku wanda aka tsare wannan fursuna, ƙasashe huɗu ne keda mallakinta. Mai gidanmu ya horemu sosai akan kada mu kuskura mu yarda a kuɓutar da wannan fursuna, saboda haka har sojojin haya ya kawo daga ƙasar Hindu wanda zasu ƙarawa wannan kurkuku tsaro. Kayi sani cewa duk zaluncinmu da rashin imaninmu, ba mu kama farcen mai gidanmu ba. Haka ma sadaukantaka da jarumta ko rabinsa bamu yi ba. Ni kaina bansan dalilin da yasa mai gidanmu ya kamo wannan mata ba, amma dai ya ce mu tsareta kamar yadda zamu tsare lafiyarmu. Tabbas idan mai gidanmu yaji wannan labari na sace ƴata da abinda ɓarawon ya buƙata ba lallai bane ya amince, mu yi masaƴa da ɓarayin ba. Tabbas rayuwar ƴata guda ɗaya jal a duniya, tana cikin mugun haɗari." Sarki Ayubul Zairiy na zuwa nan a zancensa ƙwalla ta cika masa idanu. "Wai shin waye ne wannan mai gidan naku?" Yarima Marganu ya tambaya cikin ƙarfin zuciya, tamkar shi kaɗai zai iya yaƙar wannan mai gida nasu. Sarki Ratanam ya dubi yarima Marganu ya ce, "Kai yaro! Da sanin wannan mai gida namu gwara kullum a yi ta gana maka azaba kala dubu har ka mutu. Da sanin mai gidanmu gwara ace baka wanzu a wannan duniya ba. Ina tabbatar maka da cewa SARKI KUFFURU ɗan FARHAMA mai mulkin Kufa shi ne wannan mai gida namu. Idan ban manta ba mun taɓa zuwa birnin Kufa da kai, tun kana ɗan shekara goma. Kaga kyawun birnin da kuma yadda aka tsara shi, duk kyawun birninmu baiyi rabin birnin Kufa ba. Sarki Kuffuru baya son wargi ko kuma magana ta rainin hankali yanzun sai yasa takobinsa ya sare mutum ko shi waye, don haka lallai samun wanda zai je wa sarki Kuffuru da buƙatar nan zaiyi wahala saboda yadda ake tsananin tsoronsa. Mu kanmu da muka kasance abokansa tun na yarinta baya raga mana." Koda sarki Ratanam yazo nan a jawabinsa sai sarki Ayubul Zairiy ya tari numfashinsa ya ce, "Ai babu abinda zai hanani zuwa gare shi face bana numfashi a doron ƙasa. Kai yanzun nan ma nakeson tafiya gurin wannan sarki, Ruguzan kirawo mini hadiminka na aljani ya kaini." Boka Ruguzan yayi ajiyar numfashi sannan ya ce, "Ya shugabana. Zuwa wurin sarki Kuffuru ba shine damuwar ba, damuwar ita ce dazuzzuka da tsaunukan da za'a ratsa kafin a je dajin Marsas. Kuyi sani cewa wannan daji na Marsas yana da nisa sosai daga birnin Sin, kafun mutum yaje wannan daji sai ya ratsa ta cikin waɗansu muggan dazuzzuka guda biyu haka kuma sai ya bi ta kan wani makeken tsauni. Daji na farko ana kiransa da suna Djinn, babu komai a wannan daji face ayarin waɗansu fararen aljanu masu zuƙan jinin bil'adama, fiye da shekaru goma sha bakwai baya aka ƙauracewa wucewa ta cikin wannan daji saboda duk wanda ya shiga cikin dajin, ba ya fitowa a raye. Komai hatsabibancin mutum da ƙarfin sihirin tsafinsa da zarar yayi arba da waɗannan fararen aljanu ta sa ta ƙare. Ba kowa bane ya ajiye waɗannan aljanu domin su yi gadi ba, sai sarkin sadaukai Samudul Ansari, sai mun samu lokaci zanyi muku bayanin waye ne sarki Samudul Ansari. "Daji na biyu kuma wanda ke kan hanƴar zuwa dajin Marsas shi ne dajin Shiwazu, babu komai a wannan daji sai tafka-tafkan koguna da koramu masu ɗauke da muggan kadoji da manƴan kifaye wadanda suke iya kifar da jirgin ruwa komai girmansa. Wani abun al'ajabi dangane da waɗannan dazuzzuka guda biyu shi ne abu mai fuka-fuki bai isa ya ƙetare ta samansu ba, walau tsuntsu ko aljani. Duk gangancin da ya kai aljani waɗannan dazuzzuka guda biyu to tasa ta ƙare sai dai uwarsa ta haifi wani, saboda ƙonewa zaiyi ƙurmus ya zama toka. "Idan mutum ya ƙetare waɗannan dazuzzuka guda biyu zaiyi kiciɓis da wani katon tsauni wanda ya tare hanya, babu yadda za'ayi mutum ya wuce ba tare da hau wannan tsauni ba. Matsalar ita ce a saman wannan tsauni gari ne guda na waɗansu muggan arnan daji, manya-manya kamar mutanen farko haka zaka gansu. Waɗannan arnan daji sun kware matuka wajen iya ɗana muggan tarkuna, su ɗinga kama mutane suna yankawa gunkinsu. Ya shugabana wannan shi ne taƙaitaccen bayani akan haɗarin dake kan hanƴar zuwa dajin Marsas, haƙiƙa wannan ɓarawo ba shi da niyyar bayar da wannan ƴa taka. Saboda ya san da wuya a iya tsallake masifun dake cikin waɗannn dazuzzuka da wannan tsauni. Dangane da batun neman buƙata a wajen sarki Kuffuru ni nasan abinda za'a faɗa masa ya yadda a sake wannan fursuna amma ba zan faɗa muku a nan ba, sai kun yanke shawarar wanda zaije gare shi. Shi wannan shi kaɗai zan faɗawa." Lokacin da boka Ruguzan yazo nan a jawabinsa sai hankalin Ayubul Zairiy da na sarki Ratanam yayi mummunan tashi, saboda sun gama tsorata da batun waɗannan dazuzzuka guda biyu da kuma tsaunin nan na arnan daji. A ɓangaren yarima Marganu murmushi kawai yake, saboda a ganinsa ya samu babbar dama wacce zai sadaukar da rayuwarsa ya ceto rayuwar gimbiya Jaanu wataƙila ta kamu da tsananin sonsa itama. Sarki Ayubul Zairiy da sarki Ratanam na tsaye cikin jimami kawai sai suka ga yarima Marganu ya durkusa bisa gwiwowinsa ya ce, "Ya ku shuwagabanina, alfarma ɗaya nake nema a wajenku. Dukkaninku kunsan cewa na kamu da tsananin son gimbiya Jaanu, so ba na wasa ba. Saboda haka nake son ku amince min, na sallama rayuwata naje birnin Kufa wajen sarki Kuffuru na nemi izinin ɗaukar wannan fursuna. Daga nan na wuce kai tsaye izuwa dajin Marsas don amso abar begena, madubin zuciyata gimbiya Jaanu. Kuyi sani cewa a wannan karon idan gimbiya Jaanu bata amince da buƙata ta ba, zan kashe kaina kamar yadda mazajen jiya suka kashe kansu domin banga amfanin rayuwata a duniya ba. Ina haɗaku da girman ababen dogaronku kuyi min izini, ni kuma na rantse da ƙaunar da nake yiwa gimbiya sai naje har dajin Marsas na dawo da ita." Koda jin haka sai sarki Ratanam ya sake gigicewa ya dakawa yarima tsawa ya ce, "Baka da hankali ne?! Ka san waye Kuffuru kuwa? Idan barci kake ka farka, idan wasa kake ka daina. Na rantse da karagar mulkina, babu wani sadauki a wannan nahiya tamu da yayi rabin ƙarfin damtsen sarki Kuffuru. Sarki Kuffuru azzalumi ne na gaban kwatance, baisan wani abu wai shi tausayi ba. Masu hasashe da kiyasi sun tabbatar da cewa a duk shekara ana yankewa mutane dubu ɗari da arba'in hukuncin kisa a birnin sarki Kuffuru. Zaluncin Kuffuru bai tsaya iya kan talakawa ba, hatta sarakuna ƴan uwansa zaluntarsu yake. Ya ya kake tsammanin zai amince da buƙatarka ta kuɓutar da wannan mata? To in baka sani ba ka sani, wannan mata da ya tsare a kurkuku tana daga cikin tsatson sarki Deher ɗan sarki Al-Khamis da ya shuɗe. Sai mun samu zama zan baka tarihin yadda aka yi Deher ya tarwatsa zuri'ar kakannin sarki Kuffuru har mahaifiyasa tayi gudun hijira ta haifeshi a birnin Kufa, da ya girma yayi hankali ya kashe sarkin garin sannan ya haye karagarsa. Ya kai ɗana kada soyayya ta ruɗeka kazo kayi dana sani daga baya, ka bari kawai mubi abin a hankali har a samu a ƙwato gimbiya." "Idan ka amince masa zaiyi wannan tafiya nikuma nayi alƙawarin zan sanar dashi wani sirri wanda indai ya faɗawa sarki Kuffuru zai amince da buƙatarsa. Sannan zan ba shi taimako sosai wajen ganin ya ƙetare waɗannan manyan dazuzzuka guda biyu masu mugun haɗari." Inji boka Ruguzan cikin tsantsar nutsuwa da yarda abinda yake cewa. "Ka tuna ya kai wannan sarki, wannan ɗa shi kaɗai gareka. Kana ƙaunarsa kamar yadda kake ƙaunar mahaifiyarsa da ta mutu. Ka tuna cewa sau bakwai yana yunƙurin hallaka kansa akan wannan gimbiya tamu wato Jaanu, na san baka so ka rasa wannan ɗa naka. Wannan babbar dama ce ya samu da zai nunawa gimbiya yana ƙaunarta fiye da yadda yake ƙaunar rayuwarsa, tabbas wannan zai kashe mata jiki ta kamu da tsananin ƙaunarsa itama. Ya ya kake tsammanin yarima Marganu zai kasance idan aka ce yau an ɗaura masa aure da gimbiya Jaanu?" Koda boka Ruguzan yazo nan a zancensa sai jikin sarki Ratanam yayi sanyi ya faɗa kogin tunani mai zurfi. Daga can sai hawaye ya soma tsiyayowa daga cikin idanunsa ya fara kuka. Marganu ya riƙo hannayensa biyu ya ce, "Abba? Lafiya kake kuka?" Sarki Ratanam ya ce, "Ya kai ɗana na tuno tsohon tarihin matata ce, gimbiya Sharlisa. Ka sani cewa muna tsakiyar soyayya da ita, mahaifinta sarki yace ba zai aura min ita ba face naje birnin Duma na saro kan sarkinsu na kawo masa a matsayin sadaki. Sarkin Duma a wancan zamani wani gawurtaccen tsohon sadauki ne kuma shine babban abokin gabar mahaifin Sharlisa, saboda tsananin ƙaunar da nake yiwa Sharlisa yasa na sayar da raina naje birnin Duma, muka gwabza yaƙi da sarkinsu na kashe shi da ƙyar na saro kansa, na kawowa sarki sannan aka ɗaura min aure da Sharlisa. Sai da nayi jiƴƴa ta tsahon shekaru bakwai sakamakon mugun artabun da nayi da sarkin Duma. Tabbas nayi babban rashi na masoyiyata Sharlisa. Saboda haka na amince ka sayar da rayuwarka domin cikar burinka." Hawaye ya kwacewa sarki Ratanam daƙyar su Ayubul Zairiy suka bashi baki sannan ya daina kukan. Marganu ya dubi Ayubul Zairiy cikin girmamawa ya ce, "Ya kai sirikina, na hutassheka. Zan je har dajin Marsas sannan na dawo maka da ƴarka, abu ɗaya da nake buƙata daga wajenka shi ne. Ina son idan muka dawo a ɗaura min da ita, ko tana so ko bata so. Saboda hakan shi ne zai dauwamar da zumunci tsakanin birninmu da naku. Ka sani cewa duk abinda nasa a gabana sai nayi nasara, ina son wannan ƴa taka fiye da yadda kake tsammani. Da ace na rasa gimbiya Jaanu kwara ace anyi gunduwa-gunduwa da sassan jikina don hakan zai fiye min alheri. Shin ka ɗauki alkawari, idan na dawo tare da gimbiya zaka ɗaura mana aure, ko tana so ko bata so?" Sarki Ayubul Zairiy ya harari yarima Marganu ya ce, "Baka da hankali ne? Ya ya kake tsammanin zan so abinda ƴata bata sonsa? Idan kana tunanin don kuɓutar da ƴata ce zaisa nayi mata auren dole to ka sake tunani. Kai nima fa zan iya zuwa dajin Marsas ɗinnan kawai dai don ina kunƴar abokina Ratanam ne shiyasa zan barka kaje. Tsahon shekarun nan kasan nikam babu wanda nakeso ƴata ta aure, idan ba kai ba. Ita ce bata sonka. Shawarar da zan baka ita ce kayi amfani da wannan dama, ka shawo kanta ta amince da kai. Kaga kenan kuna dawowa sai mu sha shagali." Yarima Marganu ya bushe da dariya ya ce, "Da yaddar mai girma Nurutu za'a yi hakan!" Ba tare da ɓata wani lokaci ba, yarima Marganu yayi bankwana da mahaifinsa yana kuka don basu taɓa rabuwa ba na tsahon wuni guda. Boka Ruguzan ya dafa kansa suka ɓace ɓat, daga cikin turakar suka bar sarki Ayubul Zairiy da sarki Ratanam. "Wai shin wannan yaro naka sadauki ne?" Ayubul Zairiy ya tambayi Ratanam cikin raha. Sarki Ratanam ya riƙe baki ya ce, "Ka taɓa ganin an samu ɗan ƙabilar Jenher rago?" Ayubul Zairiy ya ce, na sani?! Ratanam ya ƙara da cewa, "Ɗana fitaccen sadauki ne, kuma jarumin jarumai. Shi ne ya saro min kan ɗan fashi Bajaru na dajin Kajhar dake ƙasata." ***** Yarima Marganu na bude idanunsa ya tsinci kansa a tsakiyar wata fada madaidaiciya, wacce aka yiwa da ado da fatun manƴan dabbobin daji da ƙoƙon kawunansu. Kallo ɗaya zaka yiwa fadar ka tabbatar da cewa, fadar mashahurin boka ne. Shi dai Marganu a zaune ya tsinci kansa bisa wata lumtsetsiyar kujera. Boka Ruguzan ya hango zaune akan wata karaga mai siffar kan zaki wanda ya wangame baki. Boka Ruguzan ya ce, "Ya kai babban jarumi kuma yarima. Dangane da bayanan da suka zo mini na sirri daga aljanu, sun shaida min cewa jarumi Aymanul Faris ɗan Hasanul Jalwar da jaruma Riya ƴar sadauki

Chapter 6 of 41