Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na wannan gida. Kada ka damu suna nan lafiya kuma tabbas suna cikin aminci." Hankalin Aymanul Faris ya kwanta ya bi bayan hadimin suka fice. ****** A can birnin Damashkar kuwa, sarki Ayubul Zairiy ne zaune bisa karagar mulkinsa ya murtuke fuska tamkar bai taba dariya ba. Wata mace ce wacce ke daure da ankwa durƙushe akan mumbari na fadar, kanta a sunkuye yake kai da gani kasan hukunci take jira. Wannan mace tana tsananin kama da Aymanul Faris, kai inda ace yana wannan wuri to da tabbas ya gane waye ce, domin kuwa ba wata bace illa mahaifiyarsa. Ko ya ya aka yi sarki Ayubul Zairiy ya samu nasarar kamo mahaifiyar Aymanul Faris? "Na yankewa wannar matar hukuncin kisa, yanzu take za'a fille kanta. Bata yi laifin komai ba amma jinin sarki Samudul Ansari ce, kowa yasan haɗarin masu irin wannan jini. Masana suna ganin cewa indai za'a dinga barin jinin Samudul Ansari a doron kasa to kuwa tabbas masifu da bala'i baza su daina saukowa ba. Saboda haka zamu kasheta yanzu don tsarkake birninmu." Inji sarki Ayubul Zairiy. Wani ƙaton mutum ya fito yazo ya tsaya bayan wannan mata, riƙe da wata zabgegiyar adda ƙirar birnin Sin. Sarki Ayubul Zairiy ya ɗaga hannunsa sama da nufin yana sauƙe hannun, hauni zai sare kan wannan mata. "A yi mata afuwa mai martaba?" Inji wata kyakkyawar yarinya dake zaune a bayan sarkin. Ayubul Zairiy ya cewa hauni ya tsaya. Sannan ya juyo ya dubi yarinyar, ya ce, "Haba 'yata. Shin kuwa kinsan su waye waɗannan mutane? Su ne fa sanadiyar mutuwar kakanki Yurbaru da ɗan uwansa Asasinu. Kin kuwa san darajar baba Yurbar? Balle kuwa ta dan uwansa Asasinu?" Idanun yarinyar suka ciko da kwalla ta ce, "Ni dai abba. Kada a kashe wannan mata amma a kaita kurkuku. Bana son ganin jinin mata na ta zuba a ƙasa, idan za'a ɗauki fansa a dauka akan mazaje. Ba'a kan mata masu rauni ba, ko kaɗan basu da laifi. Kashe mata rauni ne a gurin jaruman kwarai." Sarki na jin haka jikinsa yayi sanƴi yasa aka dauki wannan mata aka nufi gidan kurkuku da ita, "Kinyi sa'a." Inji sarkin. Wannan yarinya ita ake kira da suna gimbiya *Jaanu* ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance. Tana da dara-daran idanu da dogon gashi mayalwaci, gashin gimbiya Jaanu na da ban al'ajabi domin kuwa ba baƙi bane. Jajawur ne amma ba har can ba, irin wanda Turawa. Fatar jikinta fara ce mai haske da sheki. Ba ta da baiwa ta jarumta ko kaɗan, a ganinta zubar da jini ba shi da wani amfani a duniya. Shiyasa indai tana wuri to fa sarki bai isa ya yanke hukuncin kisa ba. Saboda son zaman lafiyanta da sassaucin da take nemawa jama'a a wajen sarki, yasa jama'ar birnin Damashkar ke tsananin ƙaunarta. Tun gimbiya Jaanu tana 'yar shekaru goma 'ya'yan manyan sarakunan duniya suka sakata a gaba, kowanne ɗan sarki ba shi da burin da yafi ya aureta, saboda tsananin kyawunta. Hakan ne yasa sarakuna da kansu suka dinga zuwa wajen sarki Ayubul Zairiy domin yiwa 'ya'yansu kamu amma gimbiya Jaanu ta ƙi amincewa da ko ɗaya daga cikinsu. Gaba sauran 'ya'yan sarakunan sun hakura amma akwai wani guda ɗaya wanda ya ƙi hakura. Wannan ɗan sarki ana kiransa da suna *Marganu*. Yarima Marganu ɗan wani hamshaƙin sarki ne dake birnin Hirtoliya wai shi Ratanam. Marganu ya birkice akan auren Jaanu, ya ɗagawa sarki Ratanam hankali har ya rasa ya zaiyi. Sau bakwai yarima Marganu yana yunƙurin kashe kansa akan an hana shi auren gimbiya Jaanu amma sai sarki Ratanam ya kwantar masa da hankali yace komai daren daɗewa zai aura masa ita. Idan aka samu wanda ya kawo labarin gimbiya Jaanu birnin Hirtoliya, kyautar da ake masa har sai ya riƙe baki saboda tsananin mamaki. A taƙaice dai yarima Marganu ya kamu da mahaukacin son gimbiya Jaanu, amma a ɓangarenta kam, a duk cikin 'ya'yan waɗannan sarakuna babu wanda ta tsana kamar Marganu saboda ya kasance azzalumi, mara tausayi. Bayan an kai mahaifiyar Aymanul Faris kurkuku sai sarki Ayubul Zairiy ya sallami kowa dake fadar, sannan ya tura hadimi yaje ya kirawo masa boka Ruguzan. Gimbiya Jaanu tayi sallama da sarki sannan ta tashi ta koma cikin gidan sarautar, tafiyar ta keda wuya boka Ruguzan ya bayyana. Bayan sun gama gaisawa da sarki sai ya fiddo tarkacen kayan tsafinsa ya fara bincike. Sarki Ayubul Zairiy ya kwashe duk abinda ya faru a yayin wannan gumurzu ya zayyanewa boka Ruguzan. "Tabbas cetonsu aka yi." Inji boka Ruguzan. "To amma waye? Na gama bincike na na gagara gano ko waye ne. Duk yadda akayi wani kasurgumin bokan ne daga wata kasa dabam yake taimakonsu." Sarki Ayubul Zairiy ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Nifa jarumtakar waɗannan yara guda biyu tafi daukar hankalina. Tabbas wadannan yara idan suka girma akwai aiki don sai sun gallabi dukkan abokan gabarsu." Boka Ruguzan ya sake kallon madubin tsafinsa ya ce, "Sunan yarinyar Riya 'yar wani sadauki ne da ake kira Jarata. Wannan sadauki jinin sarkin yaki Makau ne na birnin Shaha- Deher." "Ya kai wannan sarki, ka san kuwa da ace ka kashe wannan mata da ba karamin kuskure kayi ba. Saboda me? Ita ce makaminmu a yanzu. Duk inda Aymanul Faris da jaruma Riya suke baza su daina shirye-shiryen daukar fansar abinda muka yi musu ba, amma idan suka tabbatar da cewa wannan mata tana hannunmu to tabbas zasu ji tsoron mu. Shiyasa nake jin dadin zaman 'yarka a fada domin kuwa ta fika lissafi." Sarki Ayubul Zairiy yayi shuru sannan yayi murmushi ya ce hakane. **** A wancan boyayyiyar fada kuwa, kashe gari tun da sassafe jarumi Ayman ya farka. Kuyangi suka kawo masa abincin kalaci ya ci sannan yayi wanka aka rako shi fada, da zuwansa fada ya zauna akan kujerar da ya zauna jiya. Yana jiran fitowar shugaban ɓarayin duniya. Sai da Ayman ya gaji da jira har ransa ya fara baci, sannan saurayin ya fito. "Kayi hakuri na ajiye ka anan kana jira, ko?" Inji saurayin. Ayman ya haɗe gira bai ce komai ba. Saurayin ya kama hannun Aymanul Faris suka bar cikin fadar suka nufi wani ɓangare dabam na gidan sarautar. Kai tsaye suka je cikin wani katon ɗaki wanda girmansa ya kai na wata unguwa guda, babu komai a cikin wannan ɗaki face waɗansu manya-manyan rijiyoyi, rufaffu. Waɗansu sadaukan aljanu guda bakwai Aymanul Faris ya gani suna gadin waɗannan rijiyoyi, da ganin saurayin sai suka risina. Saurayin ya ce su bude rijiyoyin. Nan take suka cika umarni, suka bubbuɗe waɗannan rijiyoyin, babu komai a cikin rijiyoyin face kayan dukiya kala dabam-dabam babu kalar da babu. Kama daga dinare, zinari, yaƙutu, zubar daji, lu'u-lu'u da waɗansun waɗannan. Tun Aymanul Faris yana kirga yawan rijiyoyin har ya gaji ya daina, amma aƙalla yasan sun kusa dubu. "Har yanzu baka faɗa min sunanka ba?" Inji Aymanul Faris. "SUNANA KILÁWUD BARBÀN amma da BARBÀN ake kirana. Ba don komai nake son nuna maka dukiyata ba, sai domin ka tabbatar da cewa dukiya bata gabana, ɗaukar fansa nake. Wannan ita ce taskata ta farko akwai kalarta guda goma a bangarori dabam-dabam na duniya. "Babu wanda ya san inda maɓoyata take a duk faɗin duniya, fiye da shekaru goma ina sata amma ko sau ɗaya ban taba haduwa da ɓacin rana ba. Ina da yara a kowacce ƙasa dake faɗin duniyar nan, fiye da mutum dubu arba'in ke aiki a karkashina amma babu wanda ya taba kallon fuskata. Hasalima ko alamuna basu taɓa kallo ba, fiye da mutum dubu talatin da biyar suna birnina da na sakawa suna DARUL BARBAN. A wannan birni kowanne ɗan ƙasa yana da albashi, babu mugu babu ɓarawo, mutanen kirki ne kawai. Mafi yawa daga cikinsu marayu ne waɗanda suka rasa iyayensu a lokacin yaƙe-yaƙe. A ƙa'idar sata ta bana yiwa talaka ko attajiri sata, sarakuna kawai. Sarakunan ma azzalumai." Inji Barban. Aymanul Faris bai san sa'adda ya gigice ba sakamakon jin wannan suna. "Dama kaine kasurgumin ɓarawo, Barban?" Barban ya ce, "A duniya da mutum uku kawai na yarda. Na farko mahaifiyata. Na biyu kaine. Na uku kuma ba zan bayyana maka shi ba tukunna. Wannan siffar da kake kallo ba ainihin siffata ba ce, wannan ta bogi ce. Da sannu zaka ga ainihin siffata." Yana gama fadin haka ya sake kama hannun Aymanul Faris suka rankaya izuwa fadar. Duk da cewa mutanen dake ƙauyen Gazwar basa yawo amma sun san labarin barawo Barban sarai, saboda shi ne ɓarawon da ya yiwa sarkin birnin Sin sata wacce ta talauta shi. Aymanul Faris kawai mamaki yake, kuma gani yake tamkar mafarki yake. Suna isowa fada sarkin ɓarayi Barban ya sallami dukkanin hadiman dake fadar, ya rage saura shi da Aymanul Faris kawai. Sarkin ɓarayi Barban ya nuna allon tsafin dake fadar da hannunsa guda take hoton birnin Damashkar ya bayyana inda ake yankewa mahaifiyar Aymanul Faris hukunci. "Idan kana yiwa Allah ka fitar dani daga cikin wannan gidan domin naje na ƙwato mahaifiyata. Na rasa abbana bana son sake rasa mahaifiyata, na roƙe ka." Aymanul Faris ya durƙusa a gaban sarkin ɓarayi Barban. Sarkin ɓarayi ya ce, "Ba zasu kasheta ba domin kuwa gimbiya Jaanu zata hana. Zan tura sauran mutanenka zuwa birnin Darul Barban daga baya zamu yi tunanin ƙwato mahaifiyarka daga hannunsu amma bayan kayi min alƙawari guda daya." Aymanul Faris ya ce, "Fadi abinda kake so na yi maka ko mene na rantse zanyi, ni dai kada su cutar da mahaifiyata." Sarkin barayi Barban ya ce, "Zauna muyi magana, babu abinda zai samu babarka matukar Jaanu tana raye a birnin Damashkar." A sannan ne hankalin Aymanul Faris ya fara kwanciya. "Meye burinka a rayuwa? Me kake so ka cimma?" Inji Barban. Aymanul Faris ya yi shuru ya faɗa kogin tunani mai zurfi har tsahon dakiku dari da tamanin. Sannan ya numfasa. "Burina shi ne naga an daina zalunci a ban kasa. A daina zubar da jini. Burina na biyu shi ne cika wasiyyar da abbana ya bar min, ta kare lafiyar mahaifiyata da kuma ɗaukar fansa akan manyan sarakuna guda uku wato sarki Ayubul Zairiy da sarki Ratanam da sarki Kuffuru. Ban san meye suka yiwa abbana ba amma dole ne na sare kan kowanne daga cikinsu." Inji Aymanul Faris cikin kololuwar yadda. Shi kansa bai san meyasa ba amma yaji ya yarda da Barban tamkar wani ɗan uwansa. "Burinmu iri daya ne da kai" inji Barban. "Abubuwan harinmu duk ɗaya ne, wadannan sarakuna guda uku. Bari nayi maka taƙaitaccen tarihi akan kowanne daga cikinsu da abinda yasa zan dauki fansa akansu. Kafun nayi maka tarihin wadannan sarakuna bari na fara baka tarihin rayuwata da birninmu." Sarkin barayi Barban ya gyara murya shikuma Aymanul Faris sai ya gyara zama, bisa mamaki sai Aymanul Faris yaga sarkin barayi Barban ya tashi yaje bakin ƙofa ya budeta. Jaruma Riya ta shigo cikin fadar. "Ni na tura a taho da ita saboda tana da muhimmanci sosai a ayyukanmu, kuma tana da riƙon amana." Inji Barban a lokacin da suka zo suka zauna kusa da Aymanul Faris. Bayan Aymanul Faris sun gama gaisawa da jaruma Riya sai sarkin ɓarayi Barban ya fara bayani. "Kimanin shekaru tamanin da biyar baya, a arewa-maso-yammacin duniya anyi wani ƙaton birni mai suna Shàha. Wannan birni da girma yake domin ya tara tarin al'umma da manƴan attajirai. Birnin ya kunshi ƙabilu kala dabam-dabam har guda goma, ƙabilar da tafi kowacce fice a kasar ana kiranta banu Kuyuru. Dama tun asali ma su ne suka kafa birnin Shàha, don haka gaba ɗaya muƙaman iko suna hannun mutanen wannan ƙabila ta banu Kuyuru. "Sarkin da ke mulkin wannan birni a wancan ya kasance sadauki kuma jarumi ana kiransa da suna Al-Khamis. Sarki Al-Khamis na da 'ya'ya guda biyu sadaukai, Deher da Meher. Uwarsu daya ubansu daya. "Ƙabilar da ke bin bayan banu Kuyuru a wancan zamani wata kabila ce da ake kira banu Huturu. Sun kasance masu tsananin kishi da zalunci suna ganin kamar an zaluncesu ne tunda babu nasu a cikin majalisar kasar, saboda haka suka fara yiwa sarki Al-Khamis maƙirci domin su samu su kawar da shi su haye karagarsa. Lokacin da sarki Al-Khamis ya fara tsufa sai farin ciki ya lullube 'yan ƙabilar babu Huturu da ƙabilar Jenher, suna ganin kawai idan sarki ya mutu zasu karɓi mulki. "Kwatsam! Kuma sai 'ya'yan sarki Al-Khamis suka taso wato Deher da Meher, suka zamo zakwakuran mayaƙa, zaratan sadaukai da ba'a taba kamar su ba a birnin Shàha. Komai zasuyi kansu a haɗe suke yi, basa zalunci. Lokacin da sarki Al-Khamis ya kamu da cutar ajali wacce ta hana shi fitowa fada, sai 'ya'yan sa suka fara zuwa suna zartar da hukunci. Da yake birnin Shàha katoto ne sai aka raba 'ya'yan sarkin biyu, Deher ya tsaya a bangaren arewa. Meher kuma aka tura shi yankin kudu. "Nan take al'amuran mulki suka ci gaba da gudana kamar sarki yana nan, mutane suna tsananin jin dadin mulkin Deher da Meher saboda sun gado mahaifinsu a fagen adalci. "Bayan wata bakwai, sarki Al-Khamis ya mutu. Aka binne shi sannan aka dawo rikici akan waye zai gaji sarki? Bayan zubar da jini da yaƙe-yaƙe majalisar ta amince a raba birnin Shàha gida biyu - birnin Shàha-Deher da birnin Shàha-Meher. Kowa ya amince da wannan tsari har da su kansu ƙabilar banu Huturu da Jenher kuwa. "Ashe wadannan ƙabilu a fuska ne kawai suka nuna sun amince amma a baɗini haushi suke ji, saboda an kashe musu mayaka da yawa sakamakon yakin da aka gwabza. Shugaban ƙabilar banu Huturu ya tara dukkanin manƴan kabilar a gidansa domin suyi shawara akan yadda zasu ga bayan 'ya'yan sarki. Da farko ɗakin yayi tsit, amma daga baya sai wani dattijon mutum mai yawan dogon gemu ya ce, "Idan muna son muga bayan waɗannan 'ya'yan sarki, tofa lallai sai dai mu ɓullo da salon yaudara tunda karfin soja an nuna mana an fimu." Kowa ya nutsu yana sauraron jawabin dattijon. "Dattijon ya ci gaba da cewa, "Mazajen duniya da suka yi zamani suka shuɗe, suna da rauni. Wannan rauni shi ne soyayya. Misali kamar sadauki Hantaru mai saiful lujara soyayya ce taga bayansa. Kamar haka ne, indai muna son kashe waɗannan 'ya'yan sarkin zamu saka su faɗa soyayya da 'ya'yanmu mu kuma sai muyi amfani da wannan dama mu gama da su." Dattijon yaja dogon gemunsa yana kallon sauran mutanen dake ɗakin yana sauraron ko akwai mai wata shawara. "Macen da tafi kowacce kyau a kabilar banu Huturu, ita ce Samra 'yar sadauki Jamnas. Dole ne Jamnas ya amince mana mu aurawa sarki Deher wannan 'ya tasa don cika burinmu." Sadauki Jamnas ya gyada kai alamun amincewa. "Akan kabilata zan iya sadaukar da komai." Inji shi. Dattijon ya yi murmushi, ya ci gaba. "Ruhin Huturu ya albarkaceka. Wacce take bin bayan Samra a fagen kyau kuwa ba wata bace illa gimbiya Amra 'yar shugaba Fahalu na kabilar Jenher. Gobe zamu shirya kowacce daga cikin 'ya'yan nan namu mu turawa kowanne sarki, mu ce idan bai aureta toh har abada baza mu taɓa mara masa baya ba." "Gaba daya mutanen dake dakin suka kyada kai alamun amincewa sannnan suka jinjinawa wannan dattijo bisa shawarar da ya kawo. Kashe gari aka tura waɗannan 'yan mata guda biyu gurin kowanne sarki, tare da wasika da sa hannun kowacce ƙabila. "Koda Meher yayi arba da Amra sai ya ɗimauce saboda tsananin kyawunta, take ya amince da bukatar ta. Aka daura musu aure a take a fadar, ba tare an gayyaci kowa ba. "A bangaren sarki Deher kuwa, cewa yayi sam wannan ba abu ne mai yiwuwa ba, saboda ya yiwa mahaifiyarsa alkawari; 'yar kabilar banu Kuyuru kawai zai aura. Saboda haka ya baiwa Samra haƙuri, ya hada ta da dukiya mai yawa ta koma inda ta fito. "Koda su sadauki Jamnas suka ga ɗaya ya amince dayan kuma bai amince ba sai suka sake zama. Dattijon nan ya yi murmushi ya ce, "Hakanmu ya cimma ruwa." Wani daga manyan ƙabilar Jenher ya dube shi ya ce, "Haba baba Amjas. Kamar ya ya?" Dattijon da aka kira baba Amjas ya ce, "Zamu yi amfani da dutse daya mu jefo tsuntsaye biyu. Amra zata canjawa Meher ra'ayi akan ya juyawa ɗan uwansa baya kuma ya yaƙe shi, hakan zai janyo 'ya'yan sarkin suyi ta yakar juna har suyi mutuwar ragas." Kowa a dakin ya bushe da dariya. "Lokacin da sarki Deher ya samu labarin cewa ɗan uwansa Meher ya auri Amra 'yar kabilar Jenher sai hankalinsa ya dugunzuma domin ya tabbatar da makiricin da ake ƙulla musu. Saboda haka ya rubuta wasiƙa da kansa kuma ya buga hatiminsa ya aikawa ɗan uwansa. "Wani abin mamaki shi ne Allah ya jarrabi Meher da tsananin kaunar Amra tun sa'adda ya aureta tayi amfani da surƙulle ta tsafe shi. Ya dawo tamkar bawanta duk abinda take so shi yake yi, ko kara ta ajiye bai isa ya tsallaka ba. Manzon sarki Deher ya isa birnin Shàha-Meher lafiya to amma koda aka karanta wasiƙar da ya kawo take Amra tasa sarki yasa aka sare kan manzon sannan aka maidawa sarki Deher raddi mai zafi. "Ran sarki Deher yayi mugun ɓaci ya ce, yanzu ɗan uwana ne zai min haka. Na rantse da sadaukantakar babanmu sai na sato wannan mata tasa na sare kanta kamar yadda suka yiwa manzona Razzan. "A sirrance sarki Deher ya tura a nemo masa ɓarawon da yafi kowa iya sata a duniya." Sarkin barayi Barban ya yi murmushi sa'adda yazo nan a labarinsa, sannan ya ci gaba. "Asalin sunana shi ne Aswàd. Ina rayuwa a wani ɗan ƙaramin ƙauye dake tsakanin birnin Shàha-Deher da birnin Shàha-Meher ana ce masa Shahil. Babana ya kasance mashayin giya, mutumin banza, mai son holewa da bin mata sosai. Mahaifiyata ta kasance abar wulanƙatarwa da muzantawa a gare shi, a gaban idanunta yake shigowa da karuwansa har ɗakinsu na aure suyi ta fasikancinsu. "Saboda ka sa jurar ganin wannan abu yasa mahaifiyata ta ɗaukeni muka bar masa gidan, muka koma kwana a rumfar kasuwa. Da safe sai muyi tabi rumfa-rumfa muna bara domin samun abinda zamu ci, wataran a ji tausayinmu a bamu wataran kuma a hanamu. Wani abin takaici shi ne mahaifina yasan halin da muke ci amma bai taɓa kula mu ba, kullum cikin sharholiyarsa yake. "Watarana sai mahaifiyata ta kamu cuta mai tsanani. Hankalina yayi mugun tashi na ɗauketa na kaita gurin wani mutumi mai magani. Koda ya gwadata sai ya dubeni ya ce, "Cutar òlsa ne ya kamata sakamakon yadda take yawan zama da yunwa. Abun har yayi yawa dole sai an kashe mata makudan kudade kafun ta samu lafiya." Na durkusa na cewa mai maganin dan Allah ya yi mata aikin, ko nawa ne zan kawo. "Kudin ba kaɗan bane saurayi. Dinare dubu arba'in fa. A ina zaka same su?" Na ce shi dai yayi mata aikin da yamma zan kawo masa. Don gudun kada yace bazai yi ba, na ruga da gudu na shiga kasuwa. Ina shiga kasuwa na nemi gindin wata bishiya na zauna, ina ta nazari akan ina zan sami dinare dubu arba'in? "Ina cikin wannan hali na hango mahaifina tare da wata zabgegiyar budurwa sun nufi gidanmu, cikin hanzari na bi bayansu. Mahaifina na daure da wata lalita a kunkuminsa wacce ya ajiye kudinsa a ciki, sai da na bari sun shiga cikin cunkuson jama'a na zaro wata ƴar karamar wuƙa na yanke lalitar na gudu. Na nemi wata bishiya na sake zama na irga abinda ke cikin lalitar na samu dinare dubu tamanin. Saboda tsananin farin ciki bansan sa'adda na bushe da dariya ba. Na koma wurin mai magani na biya shi kuɗin aikinsa dubu arba'in. Naga yana yi min wani kallo-kallo kamar bai yadda dani. "Abokin babana ne attajiri Zairan ya bani kuɗin" na fadawa mai maganin. Bayan kwana goma ya sallame mu, dama kafun mahaifiyata ta fito tuni na saya mana ƙaton gida da sauran kudin da na sato a lalitar babana. "Mahaifina ya yi juyin duniyan Allah ya rasa a ina kudinsa suka ɓata, sai da ya kusa haukacewa saboda tsabar son kudin da yake. Dubu tamanin ba wani abu bane a wajensa amma dukda haka sai da ya rude. Koda yaji labarin mun sayi gida sai ya tabbatar da cewa lallai ni ne na saci kuɗinsa, da farko ƙarata ya kai gurin sarki. Sarki ya kore shi. "Ban san hawa ba, ban san sauƙa ba watarana na dawo daga cikin kasuwa nazo na sami mahaifiyata kwance a cikin jini tana numfarfashi. An caka wata wuƙa mai tsananin kaifi a cikinta ta dube ni ta ce, "Kada ka zamo talaka! Har ka mutu a rayuwarka ka ci gaba da neman kudi kawai ta kowanne hali......." Nan take numfashinta ya ɗauke, jikinta ya sandare. Ta mutu akan hannayena. Nayi kuka har na gaji bayan an binneta. "Daga wannan lokaci na gallabi mahaifina da sata don na tabbatar shi ne ya kasheta. Babu irin tarkon da mahaifina bai kafa min ba amma na haye, daga karshe guduwa yayi ya shiga duniya ya barni a wannan ƙauye. Sai dai kafun ya tafi ya bawa wani abokinsa labarin baiwata akan sata. "Daga lokacin da mahaifina yayi hijira na daina sata, na dawo ina neman abinci da ƙarfina. Babban abinda yake bani matsala shi ne ko kaɗan bani da jarumta, aikin karfi yana wahalar dani sosai. Nan fa yunwa ta fara kamani saboda ragontaka ta wanda ubangiji ya ɗaura min, na rasa ina zan saka kaina domin na ciyar da kaina. Idan ina neman taimako korata ake." "Kwatsam! Watarana sai naji labarin sarki Deher yana neman ɓarawon da zai sato masa gimbiya Amra akan kudi dinare milyan guda. Koda naji wannan labari sai farin ciki ya lullube ni, na dauko rigata guda ɗaya na saka na nufi fada. "Fada ce kasaitacciya a wannan fada babu kowa daga sarki sai masu tsaronsa. Ina shigowa sarki Deher ya bini da kallo kawai har nazo na kwashi gaisuwa a gabansa, sarki ya sallami duk na cikin fadar suka fice. "Dama kai nake jira domin ka sato min Amra, na san kai kaɗai ne zaka iya wannan aiki a duk faɗin duniya." Inji sarki Deher. Idanuna suka zazzaro na cika da tsananin mamaki yadda akayi wannan sarki ya gane ni. "Sarkin ya ci gaba da cewa, "A halin yanzu ɗan uwana ya samu labarin ina son sace matarsa, ya karfafa tsaron birnin Shàha-Meher. Dole sai kayi da gaske, a nan ne hikimarka zata yi aiki." Bayan sarki ya gama min jawabi akan birnin Shaha-Meher sai nayi masa sallama na tafi. Ko sanda ban dauka a matsayin makami ba balle ayi tunanin wani abu daga ni sai rigata da wandona. "Daga birnin Shàha-Deher zuwa birnin Shàha-Meher tafiya ce ta sa'a biyar kacal, saboda haka da yammaci na isa kofar birnin wacce aka yi ta zallar mulmulallen karfe mai kaurin gaske. Tun daga dazuzzuka da ƙauyukan dana ratso lissafi kawai nake tayaya zan iya wucewa da gimbiya idan na satota? "Kofar birnin Shàha-Meher a kulle take, a saman kofar an rubuta 'ba'a shiga wannan birni sai zuwa wani kayadadden lokaci.' Dukda cewa na karanta waɗannan rubutu amma sai naje bakin kofar na kwankwasa. Wata mitsitsiyar taga ta buɗe aka harare ni, "Kai mara kunya, ba kaga abinda aka rubuta a saman kofar nan bane?" Na ce na gani. Aka ce me ya kawoka? Na ce, "Ni dan aike daga ƙabilar Bulaizu." Mai gadin ya ce, "Maƙaryacin banza a yankin kasashen nan namu babu ƙabilar Bulaizu." Bisa mamaki sai mai gadin nan yaji shuru, ya daka tsawa yaji ban amsa ba. Kawai sai naga ya turo ƙofa zai bude don ya leƙo yaga ina nayi. Nikuma ɓuya nayi a saman dutse dake bakin ƙofar, mai gadin na fitowa ya shaki wani abu mai kama da banju ya bingire ƙasa ya kama bacci, ba wani bane ya watso masa banju ba sai ni ɗinnan. Na toshe hancina da tsumma don kada nima banjun yayi aiki akaina, na sauƙo daga kan dutsen naja wannan sadauki cikin jeji na cire kayan jikinsa na saka. Sannan kai tsaye naje na shiga cikin birnin, sa'ar da nayi ita ce a dai-dai lokacin rana ta fadi ba'a shaida masu gadin sosai. "Dakyar na samu na mayar da wannan kofa na rufeta don tsananin nauyi, dare nayi aka sallamemu daga wurin aiki wadansu dakaru dabam suka zo suka karɓa mana. Na shiga kasuwar garin na sayi bakaken kaya na ajiye, na kuma sayi farare. A wannan dare banyi wani yunƙuri na shiga gidan sarautar sarki ba, amma a anguwar da 'yan kabilar Jenher suka fi yawa na kwana, na yi ta yi musu tambayoyi akan Amra. "Washe gari kasuwar garin ke ci, don haka tun da safe na tafi kasuwa sanƴe da fararen tufafi, na tara jama'a ina ta nuna musu siddabaru da rufa ido. Gimbiya Amra tana matukar son ganin irin wannan wasa, kamar yadda na samu bayani daga baƙin mutanen garin. Koda jama'a suka ga abubuwan al'ajabin da nake a kasuwa sun fara yawa sai aka fara yaɗa labarina a cikin gari, wannan ya faɗawa wancan wancan ya faɗawa wannan. Har sai da naga waɗansu kuyangin gidan sarautar sunzo sannan na fara wani wasa. "Takobi nake sakawa na fille kan wani saurayi sannan daga baya na dauki kan na sake ɗaura masa, bisa mamaki sai aga kan saurayin ya sake jonewa kamar ba'a sare shi ba. Na sake dubawa inda waɗannan kuyangi suke tsaye naga sai shewa suke, suna ta mamaki. Kawai sai na saka baƙaƙen kayan nan dana saya, na fara zane-zane akan kasa. Dokin wasa na zana amma bisa mamaki sai aka ga dokin itace ya ratso ya fito. "Wannan saurayi wanda muke wasan nan dashi, ya haye kan dokin. Take dokin ya tashi sama yana ta lilo akan iska yana kewaya jama'a, 'yan kallo. "Kai ammafa wannan saurayin ya iya wasan tsafi. Inda ace sarauniya zata ganshi na rantse da sai taji dadi." Inji daya daga cikin kuyangin nan. Kawai sai naga sun rankaya sun nufi unguwar da gidan sarauta yake. Saurayin nan ya ci gaba da lilo akan iska kafun ya sakko. "Haka dai muka

Chapter 3 of 41