Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wannan kofa, kasancewarta ba mai son yawo sosai ba. Ya tuna cewa indai ba tare da gimbiya ba, babu yadda za'ayi su fice ta wannan ƙofa. Nan fa ya tsaya yana tunanin dabarar da zaiyi domin samun nasara a wannan aiki. Har kusan tsahon rabin sa'a sannan wata dabara ta fado masa, take yasa hannunsa a cikin aljihunsa ya fiddo Aymanul Faris wanda ke cikin ƙaramar siffa. Barban ya sake dafa kafadar Aymanul Faris take ya dawo ainihin siffarsa ta da, Barban yasa hannu ya shafi kayan dake jikin Aymanul Faris take suka rikide suka zamo masu tsadar gaske irin na 'ya'yan sarakuna, ya sake saka hannu ya shafi gashin kan Aymanul Faris take gashin ya kara baƙi. Wohoho! Kyawu kyautar Allah! Hakika Aymanul Faris ya kasance kyakkyawa na kwatance kuma ga shi sadauki, jarumi. Babu macen da zatayi arba da Aymanul Faris a wannan shiga da yayi ba tare da ta kamu da tsananin ƙaunarsa ba. "Ya kai Ayman, tabbas idan kana so ka ceci rayuwar mahaifiyarka, dole sai kayi abu guda. Basaja zaka yiwa gimbiya Jaanu ka nuna mata cewa kai ɗan wani gagarumin sarki ne. Ku kazo kai da mahaifinka domin neman aurenta. Ka san dabarar da zaka yi mata ku fita daga cikin gidan sarautar nan ta ƙofar kudu, bayan kun fita ku rankaya cikin daji kuyi ta tafiya. Tabbas zamu riskeku a duk inda kuke." Inji sarkin barayi Barban. Har Aymanul Faris ya buɗi baki zaiyi magana amma sai Barban ya ce, bamu da lokaci fa. Don haka sai yayi shuru kawai ya kunna kai izuwa cikin turakar gimbiya Jaanu yana tafiyar ƙasaita tamkar wani hamshakin sarki. Turakar gimbiya Jaanu ƙatuwar gaske ce, an kashe dukiya mai yawa wajen ginata. Ko'ina a cikin turakar a haskake yake da waɗansu irin fitilu masu haske. Wani ƙanshi na turaren miski ya fara dukan hancin Aymanul Faris. A can nesa kaɗan ya hango gimbiya Jaanu kwance akan wani gado na zinari, tana kallon rufin ɗakin. Tunda Aymanul Faris yazo duniya bai taba ganin kyakkyawar mace kamar gimbiya Jaanu ba, babu abinda yafi ɗaukar hankalinsa kamar jan gashin dake kanta, mai sheƙi da haske kamar mudubi. Saboda tsananin ruɗewa da ɗimauta sai da ya kame kamar gunki yana kallon tsantsar kyawunta. Yana cikin wannan hali ne yaga ta juyo ta kalle shi, koda suka hada idanu sai kirjinta ya buga da karfi. Gimbiya Jaanu ta kalli Aymanul Faris daga sama har ƙasa. Taga kyawun fuskarsa da murɗewar jikinsa ai kuwa take taji ta kamu da tsananin ƙaunarsa. Bata san sa'adda ta sauƙo daga kan wannan gado ba, ta rugo da gudu ta rungume shi. "Ya kai wannan ɗan sarki wane ne kai?" Gimbiya Jaanu ta fada cikin sassanyar murya mai dadi saurare. Saboda tsananin jin daɗin sautin muryarta da kuma yadda ya kamu da tsananin ƙaunarta, sai da Aymanul Faris yaji kamar ya faɗa mata gaskiyar al'amari amma a take zuciyarsa ta daka masa tsawa. Aymanul Faris ya yi gyaran murya ya ce, "Suna na Ayman, mahaifina shi ne sarkin birnin Darul Darjan. Ya ke wannan kyakkyawa kiyi sani cewa tun ina dan ƙaramin yaro na kamu da tsananin kaunarki, fiye da shekaru bakwai ina takurawa abbana akan yazo ya nema min aurenki amma sai ya dinga bani hakuri yana cewa na jira sai zuwa nan da wani lokaci ƙanƙani. Yanzu haka abbana yana can fada tare da abbanki suna tattaunawa, kuma mahaifin naki ne ma yayi min izini nazo ganki domin ya yi miki bazata. Ya ya kika ce shin kin amince dani?" Gimbiya Jaanu tayi murmushi mai taushi ga Aymanul Faris wanda ya rikirkita shi ta ce, "Tun ganin da nayi maka na farko na tabbatar da cewa na samu wanda na daɗe ina jiran zuwansa. Ina son namiji kyakkyawa, kuma sadauki. Tabbas kana da waɗannan abubuwa da nake buƙata don haka na amince, kaine wanda zan aura. Yi maza kazo muje wurin abbana domin na shaida masa na samu wanda zan aura." Aymanul Faris ya ce, "A'a mahaifina da abbanki suna tattaunawa mai muhimmanci shiyasa ma suka turoni nan wajenki, sai dai in kin amince mu ɗan zagaya cikin wannan gida naki na sha kallo." Gimbiya Jaanu tayi murmushi ta ce to muje mana. Nan take gimbiya Jaanu ta shige gaba Aymanul Faris na biye da ita suka fara kewaya cikin wannan gida nata, wanda aka cika shi da shuke-shuken furanni da 'ya'yan marmari. Tuni soyayya mai karfi ta ƙullu tsakanin masoyan biyu a haduwar farko. Duk abinda Aymanul Faris yake yi burge gimbiya Jaanu yake, yanayin yadda yake magana da kuma tsantsar nutsuwa da kamalar dake tattare dashi. Shi kuma babu abinda yake burge shi kamar tsananin kyawunta da kuma halayyarta mai kyau, idan ya tuna cewa ita ce ta ceci rayuwar mahaifiyarsa sai yaji sonta ya ƙara kwarara a zuciyarsa. Kwatsam! Sai Aymanul Faris ya yi arba da wani kyakkyawan tsuntsu wanda babu kalarsa a duk cikin tsuntsayen dake lambun, take yaji ya ƙawatu da wannan tsuntsu. Don haka sai ya ruga yabi tsuntsun da gudu, tsuntsun ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi sama ya hau kan bishiya. Aymanul Faris yaje gindin bishiyar shi da gimbiya Jaanu suna jifan tsuntsun amma sai ya sake tashi ya hau kan wata bishiyar. Haka dai suka yi ta guje-guje da tsuntsun har ya iso ƙofar nan dake kudu wacce za'a bi a fice daga gidan sarautar gaba ɗaya. Tsuntsun ya daka tsalle ya haye kan toluwar dake ginin fadar, kafun su Aymanul Faris su ankara ya tashi sama ya fice daga gidan sarautar. Gimbiya Jaanu ta dubi Aymanul Faris cikin tsananin so da ƙauna ta ce, "Kash! Ya riga ya gudu yanzu dole sai dai mu hakura mu nemi wani!" Aymanul Faris ya dubeta ya fara bayani a cikin murya mai nuna tsantsar ƙauna ya ce, "Ya ke masoyiyata kiyi sani cewa, wannan tsuntsu da kike kallo sau ɗaya na taɓa kallon irinsa a yankin ƙasarmu. Sai da na sha wahala sosai na kamashi, na saka shi a cikin keji. Da zamu taho ɗinnan na same shi a keji ya mutu haƙiƙa nayi baƙin ciki sosai, saboda haka lallai ba zan bari yanzu wannan ya kubce min ba. Dole na fita daga cikin gidan sarautar nan nayi ta binsa har na samu nasarar kama shi." Koda gimbiya Jaanu taji wannan jawabi sai ta ɗimauce taji kaunar Aymanul Faris ta sake lulluɓe zuciyarta saboda ra'ayinsu yazo ɗaya. Gimbiya Jaanu tana son ganin kyawawan tsuntsaye suna shawaƙi shiyasa ma aka kawo mata su da yawa. Nan take ta cewa Aymanul Faris ai sai dai su fita tare domin itama tana son ganin kalar wannan tsuntsu wanda tunda take bata taba ganin kalarsa ba. Aymanul Faris yayi murmushi mai taushi. Zuciyarsa tayi fari domin yana ganin ya samu nasarar kuɓutar da mahaifiyarsa Hajriya. Kai tsaye suka je bakin ƙofar fita daga gidan sarautar. Aymanul Faris yayi arba da waɗansu irin gabza-gabzan dakaru masu kama da dakarun nan masu tsaron kurkuku, kowanne na riƙe da zabgegiyar takobi. Koda suka ga gimbiya tare da yarima sai suka risina suka kwashi gaisuwa. Babban cikinsu wani ɓarkeken kato ya fara magana da wata irin murya mai kama da tsawa ya ce, "Ya ke shugabarmu ina kuma zakije a tsakiyar ranan nan?" Jaanu ta ce, "Zamu je cikin gari ne tare da wannan yarima wanda zai zamo mijina na gobe domin yaga gari." Barkeken katon ya yi murmushi ya ce, "A dawo lafiya sarauniya. Ammafa ki sani baza mu bari ku tafi biyu jal ba, dole ne na haɗaku da waɗanda zasu baku tsaro." Gimbiya Jaanu ta ce, ba laifi. Take ɓarkeken ƙaton ya zabo waɗansu zakwakuran dakaru guda ashirin ya ce su raka gimbiya kuma su tabbatar sun dawo da ita gida. Zuciyar Aymanul Faris kawai bugawa take domin ya tabbatar da cewa indai aka tafi da dakaru, shirinsu na sace gimbiya zai iya wargajewa. Nan take aka kawo dawakai guda biyu ingarmu, gimbiya Jaanu ta hau ɗaya Aymanul Faris ya hau ɗaya. Waɗannan gabza-gabzan dakarun suka kewaye su sannan aka buɗe kofa suka rankaya suka fice daga cikin gidan sarautar. Kamar tsafi suna fitowa sai suka yi arba da wannan tsuntsu nata shawaƙi a harabar gidan sarautar yana ganin sun fito ya fara gudu a sama amma gudun nasa baya sauri. Gimbiya Jaanu ta umarci waɗannan dakaru dasu bi wannan tsuntsu duk inda yayi, saboda shi ne dalilin fitowarsu. Tuni Aymanul Faris ya gano wannan tsuntsu kuma ya tabbatar da cewa ba asalin tsuntsu bane, Barban ya rikiɗa izuwa wannan siffa. Sannu-a-hankali dai wannan tsuntsu yayi ta gudu a sararin samaniya dakarun gimbiya na ta jifansa da raga don su kama shi amma sun kasa, kafun su ankara sun fara barin cikin gari sun fara shiga jeji. A haka dai har suka fara nisa ba tare da sun kamo wannan tsuntsu ba, shi kuma tsuntsun bai bace musu ba. Yayin da suka shigo cikin wani wuri mai yawan dogayen bishiyu sai suka nemi wannan tsuntsu sama da ƙasa suka rasa, ɗaya daga cikin dakarun ya dubi gimbiya ya ce, "Ya shugabata wannan tsuntsu fa ya mana, kuma ga shi munyi nisa da cikin gari ina ganin mu koma kawai. Daga baya zamu dawo nan mu bincika ina yayi, saboda muna tsoron kada wani abu ya taba lafiyarku keda wannan ɗan sarki." Gimbiya Jaanu tayi murmushi ta dubi Aymanul Faris ta ce, "To masoyina, ka ji abinda suka ce shin ka amince?" Kafun Aymanul Faris ya buɗi baki ya ce wani abu, sai suka ga wannan tsuntsu ya ɓullo daga saman wata bishiya da gudun gaske ya nufo inda suke. Kafun dakaru su fiddo ragarsu tuni tsuntsun nan ya tarwatse ya zamo hodar banju, ya bi iska. Take kowa dake wurin ya shaƙi wannan hoda ta banju daga kan Aymanul Faris har zuwa waɗannan dakaru babu wanda bai bingire ƙasa ya kama barcin dole ba. Kwatsam! Sai ga bayyanar sarkin ɓarayi Barban tare da jaruma Riya bisa wani shirgegen aljani, dukkaninsu sun rufe fuskarsu da rawani iya idanuwansu ake kallo. Barban ya yiwa aljanin nan umarni ya dauki gimbiya Jaanu da Aymanul Faris sannan ya buɗe fuka- fukinsa ya tashi sama cikin gajimare ya ɓace ɓat! Suka bar sauran dakarun gimbiya kwakkwance rashe-rashe suna barci sakamakon shakar hodar banju. *****Ruhim Jarumtaka!!! * Babi na 5: *Gimbiya ta ɓata* * Acan fadar sarki Ayubul Zairiy kuwa, lokacin da sa'a guda ta shuɗe sai sarki Ratanam ya dubi sarki Ayubul Zairiy cikin tsananin damuwa ya ce, "Ya kai abokina, wai shin mene ne ya tsayar dasu gimbiya ne har yanzu basu ƙaraso ba?" Ayubul Zairiy ya yi murmushi ya ce, "Ai daga wannan fada zuwa turakar gimbiyata, tafiya ce ta kusan sa'a guda kuma ka san cewa dole ne gimbiya ta tsaya yin kwalliya. Kuyi haƙuri zuwa lokaci kaɗan zata fito!" Yana gama wannan batu kawai suka ci gaba da hirar duniya. Yarima Marganu na zaune zuciyarsa sai dukan uku-uku take, yana tunanin wacce amsa gimbiya Jaanu zata bayar. Shin zata amince da bukatarsa ko kuma dai wannan karon ma zata ƙi shi? Marganu ya ayyana a ransa idan gimbiya Jaanu ta amince da buƙatarsa sai yayi kyautar dukiya irin wacce bai taba yi ba a rayuwarsa, kuma sai yasa shugaban mawaƙan duniya ya rubuta masa waƙoƙin soyayya waɗanda zai dinga rera mata kullum babu dare ba rana. Idan kuma ta ƙi shi to tabbas bai ga amfanin rayuwarsa a duniya ba, zai kashe kansa ya huta. Yarima Marganu na cikin sake-sake a ransa har wata sa'a guda ta sake shuɗewa babu gimbiya babu labarinta, al'amarin da ya sosa ran sarki Ayubul Zairiy kenan saboda baya so ko kaɗan yaji kunƴa a wurin sarki Ratanam. Don haka sai ya kira shugaban dakarun dake tsaron lafiyarsa ya umarce shi da yaje ya dubo abinda ke faruwa, badakaren ya risina sannan ya wuce kai izuwa yankin gimbiya Jaanu. Kwatsam! Ba zato sai sarki Ayubul Zairiy yaji zuciyarsa ta buga da karfi, tsikar jikinsa ta mimmike. A duk lokacin da yaji irin wannan yanayi, to tabbas wani mummunan abu na shirin faruwa. Har ya miƙe zai shiga yankin gimbiya da kansa, kawai sai ga badakaren da ya aika ya dawo. Fuskar badakaren cike da jimami da damuwa. Bayan ya risina a gaban sarki Ayubul Zairiy sai ya ce, "Ya shugabana. Gimbiya Jaanu fa bata cikin wannan gida nata gaba ɗaya. Barde Shanjalu ya tabbatar min da cewa sun fita rangadi tare da yariman da ka turo ya ganta domin ta nuna masa gari........." Kafin wannan badakare ya ƙarasa abinda yake faɗa tuni sarki Ayubul Zairiy ya daka masa tsawa wacce tasa hantar cikinsa ta kaɗa. "Wanne yarima ne kuma na tura yankin gimbiya? Shin ba ga yariman da yazo kallonta ba? Wai shin kuwa ka samu Luwaisa a cikin turakar gimbiya?" Badakaren ya zube kasa yana tuba, ya ce, "Ka gafarceni ya shugabana." Sarki Ayubul Zairiy yasa kafa ya doki kirjin badakaren sannan ya zare takobinsa ya ruga izuwa cikin yankin gimbiya Jaanu, sarki Ratanam da yarima Marganu na take masa baya da gudu. Da shigowar su yankin sai suka ji komai yayi tsit tamkar babu mai rai a wurin. Lamarin da ya ƙara fusata sarki Ayubul Zairiy kenan, ya shiga kwalawa dakarun dake tsaron yankin kira. Duk badakaren da ya fito sai sarki Ayubul Zairiy ya tambaye shi ina gimbiya?, idan ya gagara bada amsa take sarkin yake saka takobinsa ya fille mai kai. Kafun a jima ya kashe dakaru goma, sarki Ratanam ya ce, "Haba abokina ka daina kashe dakarunka mana, shin kuwa ka san asara kake?" Sarki Ayubul Zairiy yayi murmushin mugunta ya ce, "Ai ba su da amfani tunda sun gagara kare abinda darajarsa yafi zinari miliyan dubu a wajena." Kawai suka ci gaba da tafiya har suka iso turakar gimbiya. Suka kunna kai cikin turakar amma basu ga kowa ba. Ayubul Zairiy ya takarkare ya kurma uban ihu wanda ya cika gidan sarautar gaba daya da amsa kuwwa, nan take kowa ya shiga taitayinsa saboda ansan ran sarki ya baci. Ayubul Zairiy na gama wannan ihu nasa wani irin jiri ya ɗebe shi, ya tafi kasa luu a sume. Sarki Ratanam da ɗansa yarima Marganu suka ruga kan sarki Ayubul Zairiy suka shiga yi masa fifita amma bai farfado ba. Don haka sai suka ɗauke shi suka nufi inda turakarsa take domin likitansa yazo yai masa magani. Tuni cikin barde Shanjalu ya ɗuri ruwa, jikinsa ya fara kyarma tamkar ace kyat ya sume. Saboda duk abinda ya faru dangane da sace gimbiya laifinsa ne, ko ya zaiyi sai ya fuskanci hukunci mai tsanani watakila ma sarki yasa a sare shi. Lokacin da sarki Ratanam da ɗansa Marganu suka iso bakin ƙofar turakar sarki Ayubul Zairiy sai suka yi arba da boka Ruguzan tsaye fuskarsa a murtuƙe, suna zuwa ya karbi Ayubul Zairiy sannan ya shimfide shi akan gadon kwanciyarsa. Shi dai Ratanam bai ce da Ruguzan komai ba, shima Ruguzan baiyi masa magana ba. Bayan boka Ruguzan ya kwantar da sarki akan wannan gado kawai sai yayi tsafi, ruwa ya zubo daga cikin 'yan yatsunsa ya wanke fuskar sarki. Sarki Ayubul Zairiy ya farka a firgice yana mai kwalawa gimbiya Jaanu, koda ya buɗe idanunsa yayi arba da boka Ruguzan da sarki Ratanam a cikin turakarsa sai ransa ya sake btaci, ya dakawa boka Ruguzan tsawa ya ce, "Ya kai wannan boka shin ina ka shiga ne lokacin da gimbiya ta ɓata? Shin kuwa ka san halin da zan tsinci kaina idan aka ce ta ɓata?" Boka Ruguzan ya ce, "Kwantar da hankalinka ya shugabana. Tabbas 'yarka tana nan cikin koshin lafiya kuma da yaddar abin dogaranmu zanyi bincike na gano inda take a cikin abinda bai wuce sa'a ashirin da hudu ba. A yanzu zanje na shiga halwar tsafi ta tsahon sa'a bakwai ba zan dawo gareka ba, sai gobe warhaka domin jin amsar inda gimbiya take." Boka Ruguzan na gama fadin haka yayi girgiza ya bace bat! Kai hatta sarki Ayubul Zairiy bai kai yarima Marganu dimaucewa ba da yaji gimbiya Jaanu ta bata, tun daga lokacin kirjinsa bugawa yake, zuciyarsa tana dukan uku-uku. Marganu ya kudurce a ransa lallai idan wani ne ya sace gimbiya tofa kowane ne shi sai ya kashe shi koyaya ya taba lafiyar gimbiya. Wannan shi ne abinda ya faru a birnin Damashkar bayan su Aymanul Faris sun sami nasarar shiga gidan sarautar kasar kuma sun sace gimbiya. ***** Kogon dutse ne ƙaton gaske wanda aka kawata cikinsa da kayan alatu kala dabam- dabam, babu yadda za'ayi mutum ya tsinci kansa a cikin wannan kogo yayi tsammanin a cikin dutse yake saboda yadda aka kawata shi. Kai kace turakar wani hamshakin sarki ne. Hatta ƙasar cikin kogon ba turbaya bace, dabon yakutu ne shi mutum zai ɗinga takawa. Sarkin ɓarayi Barban ne tare dasu Aymanul Faris da jaruma Riya zaune akan waɗansu kujeru da suka kewaye wani ƙaton teburi, wanda aka cika da kayan abinci. Dukkansu sai cin abincin suke cikin tsananin farin ciki, bisa nasarar da suka samu a gagarumin aikin da suka yi. A gefe guda kuma gimbiya Jaanu ce zaune ita kaɗai akan wata kujera, an daure hannayenta ta baya a jikin kujerar, haka kuma an rufe mata idanu da wani baƙin kyalle. In banda mutsu-mutsu babu abinda take yi, kai da gani ka san a takure take sakamakon wannan daurin da aka yi mata. Aymanul Faris cin abincin kawai yake amma gaba ɗaya hankalinsa na kanta, don ji yake tamkar shi aka daure haka. "Ya kamata mu kwance mata wannan ɗauri domin ta ci abinci." Inji Aymanul Faris cikin murya mai nuna kulawa da tsantsar soyayya ga Jaanu. Wannan batu da Aymanul Faris yayi ba karamin ɗugunzuma hankalin jaruma Riya yayi ba, domin ta fara fuskantar akwai soyayya mai ƙarfi tsakaninsa da Jaanu tun sa'adda aka ɗaureta yake satar kallonta. Jaruma Riya ta jima da kamuwa da tsananin son Aymanul Faris amma bata sanar dashi ba, saboda ganin halin da suke ciki, tana faf da bayyana masa sirrin zuciyarta sarki Ayubul Zairiy ya tashe su daga tsibirin. Saboda haka ta kudurce a ranta, sai hankalinsu ya kwanta zata bayyana masa amma da taga alamun ƙaunar gimbiya Jaanu tattare da Aymanul Faris sai hankalinta ya tashi. "Meyasa zaka tausayawa 'yar babban abokin gabarmu? Shin kuwa ka manta cewa mahaifinta ne ya kashe mana al'ummarmu har ma ya kashe maka abbanka!" Jaruma Riya ta tambayi Aymanul Faris cikin murya mai nuna ƙiyayya ga ƙabilar banu Huturu. Duk wannan tattaunawa da ake gimbiya Jaanu tana ji. Tuni ta cika da tsananin mamakin jin muryar Aymanul Faris a cikin waɗanda suka yi garkuwa da ita, amma dukda haka ko kaɗan son sa bai ragu a cikin zuciyarta ba. Koda taji yadda yake nema mata 'yanci sai taji ya ƙara burgeta, ta tabbatar da cewa lallai da gaske yake ƙaunarta. Idan da gaske yake kaunata meyasa za'a haɗa kai dashi a kawoni wannan wuri da bansan ma a ina nake ba? Amsar da ta gagara baiwa kanta kenan. "Haba kawata! Kin kuwa san me kike cewa. Tabbas in ba don wannan kyakkyawar gimbiya ba, da tuni yanzu na zamo cikakken maraya wanda ba shi da uwa kuma ba shi uba. Fansar da zamu ɗauka akan mahaifinta ne kawai, amma ita kam babu abinda ya shafeta. Na rantse da ƙaunar da nake yiwa mahaifiyata ko kwarzane ba zamuyi mata ba, har mu mayar da ita gurin abbanta mu karbo mahaifiyata." Inji Aymanul Faris cikin kololuwar yadda da abinda yake cewa. Jaruma Riya dai shuru kawai tayi ta ci gaba da cin abincinta saboda ta gama tabbatar da abinda take tsammani, wato soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin Aymanul Faris da gimbiya Jaanu. Gimbiya Jaanu kam, kanta kullewa yayi saboda jin kalaman Aymanul Faris. Ta faɗa kogin tunani tana kokarin tuno wace ce fursunan da Aymanul Faris yake magana akai, wacce ta sa akayi garkuwa da ita. Wani iko na Allah ta gama tunanin duniyan nan ta gagara tuno mahaifiyar Aymanul Faris. Har yanzu Barban cin abincinsa yake ba tare da yace dasu komai ba, bayan ya ƙoshi kuma ya wanke hannunsa. Sai ya mike tsaye tsam, ya ɗauki kwanon abinci guda yaje ya ajiye a gaban gimbiya Jaanu, sannan ya zagayo ta baya ya kwance mata daurin hannayen da akayi mata, ya sake kwance bakin kyallen da aka rufe mata idanu dashi. Sannan ya fice daga ɗakin. Idanun gimbiya Jaanu suka fara buɗewa dishi-dishi kafun daga bisani suka wartsake, ta tsinci kanta a tsakiyar wani katon falo mai tsananin kyau. Al'amarin da yayi matuƙar bata mamaki kenan domin bata yi tsammanin hakan ba. Tana dago kai ta hada idanu da Aymanul Faris wanda ya taso daga inda yake zaune ya taho gareta, yana murmushi. Bata san sa'adda ta maida masa martanin murmushin ba. "Ki ci abincin mana, ko kina son nazo na baki da kaina?" Inji Aymanul Faris. Gimbiya Jaanu tayi murmushi sannan ta buɗe kwanon abincin ta fara ci. Har Aymanul Faris ya yunƙura zai ƙarasa wurin sai yaji muryar Barban na kwala masa kira daga cikin wani ɗaki dabam dake cikin wannan kogo, don haka murmushi kawai ya sake yiwa gimbiya Jaanu sannan ya fice ya nufi wannan ɗaki. Kamar jaruma Riya jira take Aymanul Faris ya fita daga ɗakin, yana fita ta yiwo kan gimbiya Jaanu tana murmushin mugunta. Ta jawo wata kujera ta ajiye a gaban gimbiya Jaanu ta zauna suka fuskanci juna. "Mene abinda tsakaninki da dan uwana Ayman?" Wannan ita ce tambayar da Riya ta yiwa gimbiya Jaanu. Ko kallonta Jaanu bata yi ba, ta ci gaba da cin abincinta. Al'amarin da ya fusata Riya kenan ta kamo jan gashin dake kan Jaanu ta jawota kasa ta ce, "Ke ba tambayarki nake ba?" Gimbiya Jaanu ta dago fuskarta a fusace ta dakawa Riya harara ta ce, "Ban sani ba!" Kafin ta ankara sai taji saukar mari akan kuncinta na dama. Ai kuwa take jini ya fara zubowa daga hancin gimbiya Jaanu. Lamarin da yasa tayi ƙara kenan. Aymanul Faris ya dawo ɗakin a guje don ganin abinda ke faruwa, koda yaga jini a hancin gimbiya Jaanu sai ransa ya ɓaci. "Wai ke Riya me yake damunki ne? Meyasa zaki yiwa 'yar gagarumin sarki kamar wannar irin wannan wulakancin?" Jaruma Riya ta juyo tayi masa kallo mai cike da ma'ana ta ce, "Ya ya kake tsammanin zan ragawa mutanen da su ne suka yi sanadiyar mutuwar abbana, mutumin da nafi kowa ƙauna a duniya. Haba Ayman, kada soyayya ta rufe maka idanu mana. Ya kamata ka dawo taitayinka kasan aikin dake gabanmu." Koda Aymanul Faris yaji wannan batu na jaruma Riya sai jikinsa ya yi sanyi. Ya kama hannun jaruma Riya ya ja ta gefe inda gimbiya Jaanu baza taji abinda suke tattaunawa ba, ya ce, "Ya ke 'yar uwata kiyi sani cewa, wannan yarinya bata da laifi domin kuwa ita kanta bata san waye ne ainihin mahaifinta ba. Kin kuwa san ba don komai muka satota ba sai domin kuɓutar da mahaifiyata bai kamata ace mun yi mata wulakanci ba. Idan baki manta ba ita ce wacce ta ceci rayuwar mahaifiyata, a lokacin da sarki Ayubul Zairiy ke kokarin sawa a fille mata kai. Tabbas wannan abu da tayi, yasa ta burgeni matuƙa. Yanzu haka muna tattaunawa da maigida Barban ne akan yadda zamu aikawa mahaifinta wasiƙar cewa 'yarsa tana hannunmu kuma baza mu bayar da ita ba sai ya kawo mana mahaifiyata, saboda haka na roƙeki don darajar mahaifinki kada ki sake yi mata komai." Koda Aymanul Faris nan a zancensa sai ya juya ya nufi inda gimbiya Jaanu ke durkushe bisa gwiwowinta har yanzu jini nata zuba daga hancinta. A gigice ya ruga izuwa inda take, yasa wani farin kyalle ya toshe hancin nata don tsayar da jinin. Sannan ya dauki wani katon kofi cike da ruwan sanyi ya fara zuba mata akan gashin kanta. Gashin kan gimbiya Jaanu ba baki bane sidik, jan gashi ne amma mai haske. Irin wanda turawan kasashen yamma ne kawai keda kalarsa. Ruwa na soma jika gashin ya soma sheƙi da haske, yana ƙara kyau. Ai kuwa take habon nan ya tsaya. A sannan ne ta dawo cikin hayyacinta, koda taga Aymanul Faris tsaye a gabanta sai dube shi idanunta a cikin nasa ta ce, "Ya kai kyakkyawan saurayi, shin kuwa wane ne kai? Meyasa ka yaudare ni har ka kawoni nan, 'yan uwanka suna ta cimin mutunci? Ashe ba kaine wanda muka ƙulla soyayya jiya-jiyan nan ba?" Koda jin wadannan tambayoyi sai Aymanul Faris ya kama kafadun gimbiya Jaanu a lokacin da shima idanunsa ke cikin nata ya ce, "Ya ke wannar 'yar sarki kiyi sani cewa ni ne Aymanul Faris ɗan shugaba Hasanul Jalwar na ƙabilar banu Kuyuru. Wata guda baya da ta shuɗe muna zaman lafiya ni da mutanena akan tsibirin Gazwar mahaifinki ya aiko mana da wasiƙa, ya ce, mu tashi mu bar masa yankin ƙasarsa ko kuma ya yaƙemu. Mahaifina da sauran dattijan ƙabilarmu suka yanke shawarar muyi hijira daga wannan tsibiri mu koma yankin ƙasar Kisra domin mu ci gaba da noma da kiwon da muka saba. Bayan dukkanin al'ummarmu sun hau kan jiragen ruwa sai muka miƙa muka kama hanya a cikin teku, ba mu jima da fara wannan tafiya muka yi kibicis da gungun dakaru su ma bisa jiragen ruwa waɗanda basu da adadi. Daga bisani kuma muka ga mahaifinki ya ratso ta cikin waɗannan dakaru sannan ya basu umarnin su afka mana da yaƙi, bayan fafata mugun azababben yaƙi. Mahaifinki ya kashe min mahaifina, dakarunsa kuma suka kashewa jaruma Riya mahaifinta. Bansan yadda aka yi ba amma ana gama wannan yaƙi na nemi mahaifiyata sama da ƙasa na rasa, sai bayan mun samu nutsuwa mai gida Barban ya nuna min ita a madubin tsafi a lokacin da abbanki ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar fille kai. Amma bisa mamaki kika ceci rayuwarta kika roƙi mahaifinki akaita kurkuku maimakon a kasheta. "Tabbas ba yaudararki nayi ba, duk abinda kika ga nayi miki a cikin gidanki, nayi ne kawai domin na samu amincewarki mu fice daga cikin gidan sarautar ku. Mun

Chapter 5 of 41