Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
barci. Ba tare da ɓata lokaci ba, suka firfito suka wanke idanunsu sannan suka zo suka fara ɗibar gara. Bayan kowa ya ci ya ƙoshi, sai maigida Barban ya dubi Aymanul Faris da jaruma Riya ya ce, "Saura rabin sa'a kacal, mahaifiyarka ta iso cikin wannan daji don haka kuzo muje mu tari Marganu domin yin musanƴa." Yana gama faɗin haka ya tashi ya fice daga cikin kogon, Aymanul Faris, jaruma Riya da gimbiya Jaanu suka take masa baya. Gimbiya Jaanu tana tafiya tana kallon Aymanul Faris zuciyarta nata kukan rabuwa da shi, tabbas a daren jiya ya burgeta matuƙa kuma ta ji daɗin sumbatar da ta yi masa. Haka dai suka ci gaba da tafiya har suka iso wani ƙaton fili, mai yawan dogayen bishiyoyi. A saman bishiyoyin ne suka yi arba da waɗansu dakarun aljanu kimanin su dubu uku, kowannensu ya ɗame kyauro bisa baka yana shirin harbi. Aljani Ranganu ya bayyana a gabansu ya ce, "Duk wanda a cikinku yayi wani yunƙuri na yaƙar yarima Marganu take waɗannan dakaru zasu harbe shi, ya mutu don haka ku kiyaye." Yana gama faɗin haka ya ɓace ɓat. *** Lokacin da yarima Marganu ya shigo cikin dajin Marsas sai yaji wani irin kasala ya rufe shi, baisan meyasa ba amma sam yaji bashi da wani kuzari kuma yaji tamkar an cire masa dukkan ƙarfin damtsensa. Suna ƙara dannawa cikin dajin yana jin wani irin abu a ransa mai kama da karayar zuciya da kuma rashin ƙwarin gwiwa. Suna shafe tafiyar rabin sa'a kacal suka iso wani wuri mai yawan dogayen itatuwa, yarima Marganu yayi arba da dakarun aljanu bisa waɗannan bishiyoyi sun saita tsakiyar filin da kwari da baka. Kafun su yarima Marganu su shiga cikin wannan filin, wani ƙaton aljani ya bayyana a gabansu. Aljani ne dogo mai manƴan fuka-fuki guda biyu a gadon bayansa, inda a ce maigida Barban na wannan da tuni zai gane wannan aljani domin shi ne mai gidansa a harkar sata. "Ni ne aljani Ranganu, nazo gareka ya kai wannan ɗan sarki domin nayi maka kashedi akan kada ka kuskura kace zaka yaƙi su Aymanul Faris domin kana yin hakan, waɗannan dakaru nawa zasu harbeka!" Inji aljani Ranganu yana kallon Hajriya dake kwance a gefen Marganu idanuwanta a rufe. Yarima Marganu ya ƙarewa aljani Ranganu kallo ya ce, "Meyasa tun da na shigo cikin wannan daji, nake jin sauyin yanayi a jikina? Fatan dai ba yaudarata kuke so kuyi ba domin ku haɗamu ni da gimbiya kuyi garkuwa da mu?" Aljani Ranganu ya ɓata rai ya ce, "Kai yaro! Shin kana tunanin akwai abinda zamu buƙata a wajen iyayenka ne? Idan taƙamarku dukiya ce, to nan gidanta kazo! Idan mulki ne kuma ni ɗinnan da kake kallo ƙasashen aljanu bakwai ne a ƙarƙashin ikona. Ka shiga taitayinka!!" Aljani Ranganu na gama faɗin haka ya ɓace ɓat. Aljani Gulzab ya waiwayo da kansa ya dubi yarima Marganu ya ce, "Ya kai wannan ɗan sarki, meyasa baka da tsoro ne? Meyasa kake yiwa manƴa maganganu marasa daɗi? Shin kuwa ka san waye ne aljani Ranganul Husubul Ansari?" Yarima Marganu ya fusata ya ce, "Koma waye shi bai dame ni ba, yi maza ka ƙarasa da mu izuwa tsakiyar wancan wurin..." Ya nunawa aljani Gulzab cikin wannan dogayen itatuwa. Take aljani Gulzab ya buɗe fuka-fukinsa ya dira a tsakiyar wurin, inda yarima Marganu yayi arba da mutane huɗu a tsaitsaye. Wanda yafi ɗaukar hankalin yarima Marganu a cikin mutane huɗun shine Aymanul Faris, saboda shima saurayi ne mai irin shekarun yarima Marganu amma jikinsa yafi na Marganu murɗewa nesa ba kusa ba. Marganu ya sauƙo daga kan aljani Gulzab sannan ya goya mahaifiyar Aymanul Faris akan kafaɗunsa suka fuskanci juna. Dukda cewa gimbiya Jaanu na tsaye a wannan wuri amma idanun yarima Marganu akan Aymanul Faris tuni ya cika da tsananin mamaki, ashe za'a samu saurayi mai irin shekarunsa wanda ya fishi murɗewa da kafiya? Tambayar da ya yiwa kansa kenan amma bai samu amsarta ba. Kilawud Barban ya tako sawayensa ya taho inda yarima Marganu ke tsaye yana kallonsa, har ya iso inda yake tsaye. Aka yi kallon kallo sannan Barban ya fara jawabi da cewa, "Lale marhaban da zuwan jarumi uban jarumai. Muna so ka ajiye wannan mata bisa wancan dutsen domin mu ga lafiyarta, mu tabbatar da cewa babu wani sihiri da kuka yi mata..." Ya nunawa yarima Marganu wani faffaɗan dutse dake ajiye gefe guda, yarima Marganu ya harare shi sannan yaje ya ɗaura Hajriya bisa wannan dutse. Barban yaje ya tsaya akanta ko daƙiƙu sittin masu kyau bai shafe ba ya dawo, ya tabbatarwa da yarima Marganu tana lafiya. "To ai sai ku bani gimbiya na tafi koh?" Inji yarima Marganu yana hararar Barban. Barban ya yi murmushi yazo daf da yarima Marganu har suna shaƙar numfashin juna sannan ya ce, "Baka san waye ne a tsaye a gabanka ba, shiyasa kake min izgilanci. Shin ba zaka bi umarnin da aka baka bane? Ka kama ni mana idan ka isa? Ni ne Kilawud Barban ɓarawon da ya gallabi duniya da azzaluman cikinta da sata, ga ni tsaye a gabanka idan ka isa ko ɗan yatsa ka ɗaga min!" Koda yarima Marganu yaji furucin Barban sai yaja baya a tsorace, domin bai taɓa tsammanin wannan mutumin shi ne ɓarawon da ya addabi sarakunan duniya da sata ba. Yarima Marganu ya ƙare masa kallo yaga ko kaɗan ba shi da wata sura ta jarumta, jikinsa a sake yake tamkar na mata. Wani murmushin nuna isa ya gilma ta bakin maigida Barban kawai ya juya ya nufi inda su Aymanul Faris ke tsaye. ****RUHIN JARUMTAKA! * Babi na 14: *Aikinmu na Farko* * * Umar Sangaru * Yana zuwa daidai inda suke ya tabbatar musu da cewa, Hajriya tana lafiya. Aymanul Faris ya kama hannun gimbiya Jaanu suka nufi inda yarima Marganu ke tsaye. Babu yadda za'ayi mutum ya kalli gimbiya Jaanu da Aymanul Faris yace babu soyayya a tsakaninsu, saboda irin kwanciyar hankalin dake kan fuskar gimbiya Jaanu tamkar a hannun ɗan uwanta take, shi kuma Aymanul Faris sam babu alamun damuwa a tattare da fuskarsa, tafiya suke a hankali tamkar baza su isa inda yarima Marganu yake ba. Koda suka iso kusa da inda yarima Marganu ke tsaye sai suka yiwa juna bankwana irinta masoyan asali. Gimbiya Jaanu ce ta fara magana, "Ya kai masoyina kayi sani cewa, da zarar na koma gida zan nemi wanda yafi kowa iya sassaƙa a birninmu domin ya sassaƙa min gunkinka, sannan zan sa a rubuta min sunanka a gadon bayana saboda kada kewarka ta illata ni." Aymanul Faris ya yi murmushi ya ce, "A sauƙa lafiya... Gimbiyata." Duk wannan maganganu da suka yi yarima Marganu yana ji, kuma sun san yana ji ɗin amma basu damu ba, ga dukkan alamu suna yi domin yaji haushi. "Ƙarya ne," Inji yarima Marganu. "Ba ki isa kiyi soyayya da babban maƙiyinmu ba. Tabbas na san kina yin hakan ne domin kawai naji haushi amma ba soyayya kuke ba." Gimbiya Jaanu ta dube shi, cikin wani irin kallo wanda ke nuni da cewa ina ruwanka da abinda nake? Ran yarima Marganu ya ɓaci kawai ya koma kan aljani Gulzab ya zauna. Aymanul Faris yaje gurin wannan faffaɗan dutse ya ɗauki mahaifiyarsa bisa kafaɗarsa, ya juyo ya dubi inda yarima Marganu ke zaune ya ce, "Nagode fa, bisa ɗawainiyar da kayi kafin ka kawo min babata." Yarima Marganu ya harare shi, ya ɗora hannunsa kan kufen takobinsa ya fara shafata amma koda ya ɗaga kansa yaga yadda aljanun nan suka kewaye filin kuma ya tuno da gargaɗin aljani Ranganu sai ya fasa. Gimbiya Jaanu taje ta hau kan aljani Gulzab ta zauna, tana kallon Aymanul Faris tana murmushi. Aymanul Faris ya juya ya nufi inda su Barban ke tsaye ya bar wurin da sauri. Yarima Marganu ya yiwa aljani Gulzab umarnin tashi take kuwa ya buɗe fuka-fukinsa ya tashi ya lulluka cikin gajimare. Aymanul Faris na zuwa inda su Barban ke tsaye, aljani Ranganu ya bayyana ya dube su ya ce, "Zamanku a dajin Marsas ya ƙare, kuyi maza ku tafi izuwa ɓoyayyiyar fadar Barban domin jiƴƴar wannar mara lafiya." Yana gama faɗin haka ya ɓace ɓat. Barban ya shafi damtsen hannunsa waɗannan aljanu guda uku suka bayyana suka ɗaukesu suka tafi izuwa wannan ɓoyayyiyar fadar wadda babu wanda yasan haƙiƙanin inda take. Suna dira a fadar, Barban ya sa kuyangi suka kawo musu abinci da abinsha kala dabam- dabam, take suka ci suka ƙoshi. Har a wannan lokaci idanun Hajriya a rufe suke, kai kace suma tayi amma a zahiri ba haka bane. Barban ya tafa hannayensa sau uku take wata farar aljana ta bayyana tana sanƴe da fararen kaya masu haske ta zube a gabansa. Barban ya ce, ta duba wannan mara lafiyan. Aljanar ta kwantar da Hajriya akan wani gado sannan ta ɗauko kayayyakin aikinta ta fara gwaje-gwaje. Bayan kamar rabin sa'a tana wannan aiki, likitar ta ɗago kai ta dubi su Aymanul Faris ta ce, "Wannan mara lafiya tasha duka sosai a sassan jikinta da ma cikinta, a halin yanzu akwai raunika da yawa a cikin cikinta sakamakon dukan da ta sha, zan baku wani magani wanda za'a ɗinga bata kullum kafin rana ta fito har tsahon wata guda, indai ta gama shanƴe wannan magani akwai tabbacin zata sami cikakkiyar lafiya. Haka kuma wannan rauni da aka yi mata na guntule babbar ɗan yatsanta anyi amfani da baƙin ƙarfe mai kaifi wajen aiwatarwa, shima zan gyara shi yanzu." Tana gama faɗin haka ta fiddo wata ƙwalba mai ɗauke da wani farin ruwa mai sanyi ta baiwa Aymanul Faris ta ce shi za'a na baiwa mara lafiyar kullum kafin rana ta fito, sannan ta fiddo wata farar auduga daga cikin jakar, ta gyara wannan rauni dake kan babbar ɗan yatsan. Tana gama gyara raunin ta fiddo wani irin magani wanda su Aymanul Faris basu taɓa ganin kalarsa ba, ta shashshafa a duk inda ya kumbura a jikin Hajriya take kuwa duk kumburin ya saɓe. Haka dai wannan likita ta ci gaba da gyagygyara raunikan dake jikin Hajriya har ta tsahon sa'a uku sannan ta kammala, ta juyo ta dubi sarkin ɓarayi Barban ta ce, "Ya shugabana na kammala aikin da ka sakani, yanzu abinda ya rage shi ne kulawa da wannar mara lafiyar har tsahon wata guda." Maigida Barban ya yi murmushi ya ce, "Gaisheka ki, Laziyya. Tabbas kinyi aiki mai kyau." Yana gama faɗin haka aljana Laziyya tayi masa sallama ta ɓace ɓat. Aymanul Faris ya ƙarasa inda mahaifiyarsa ke kwance ya zauna kusa da ita sannan ya ɗora hannunsa akan kafaɗarta yana kallon fuskarta, hawaye ne masu zafi suka zubo daga cikin idanunsa a lokacin da ya tuno da wasiyyar mahaifinsa. "Anƴa na cika wannan aiki kuwa, na kare lafiyar mahaifiyata?" Ya tambayi kansa a cikin ransa. Jaruma Riya tazo ta zauna daf da shi, ta dube shi ta dubi Hajriya sannan ta ce, "Ya kai ɗan uwana, farin cikinka farin cikina ne. Baƙin cikinka nawa ne. Duk abinda zai sameka ina so ya same mu tare. Kayi sani cewa maigida Barban ba ƙaramin taimako yayi mana ba, wajen ganin an ƙwato mahaifiyarka daga kurkuku mafi tsaro a wannan nahiya tamu don haka nakeso ka amince masa a duk irin ayyukan da zaku yi saboda dalilai guda uku. Na farko ya taimaka wajen ganin an ƙwato mahaifiyarka, na biyu ya bata kula irin wacce da wuya mu iya bata, na ƙarshe ya baiwa sauran al'ummarmu maɓoya a birnin Darul Barban dukda cewa banje wannan birni ba amma jikina yana bani mutanenmu suna nan cikin ƙoshin lafiya." Aymanul Faris yaji wata nutsuwa ta lulluɓe shi saboda jin bayanan jaruma Riya, shiyasa take matuƙar burge shi saboda hangen nesanta da iya magana. "Idan muka fara aiki da Barban waye zai kula da babata," inji Aymanul Faris. "Shin kin manta da kalaman aljana Laziyya ne?" Jaruma Riya ta yi murmushi ta ce, "Shiyasa na ce farin cikinka farin cikina ne, baƙin cikinka ma nawa. Ina so ka bar mahaifiyarka a hannuna zan kula da ita tamkar yadda zan kula da mahaifiyata, nayi maka alkawarin wannan." Aymanul Faris ya yi murmushi mai taushi ga jaruma Riya sannan ya fara gode mata. Barban dake tsaye a gefe guda ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Ya kai babban jarumi, zo muje wani ɓangare na wannan gidan sarauta tawa domin na fara maka bayanin aikin da zamuyi na farko." Yana gama faɗin haka ya juya ya fice daga cikin ɗakin Aymanul Faris ya yiwa jaruma Riya bankwana sannan ya bi bayan maigida Barban. Wani ɓangare dabam na gidan sarautar Barban yaja Aymanul Faris inda aka ajiye kujeru guda biyu kacal, sannan waɗansu tafka-tafkan bishiyoyi masu fala-falan ganƴe suka kewaye idan mutum ba shiga wurin yayi ba, ba zaiyi tsammanin akwai inda mutane zasu zauna ba. Ga dukkan alamu dai a wannan wuri maigida Barban ke ganawar sirri da baƙinsa. Aymanul Faris na shigowa wannan wuri yaji wani iko ya buge shi, ya tabbatar da cewa in cutar dashi za'ayi a wannan wuri bai isa ya kare kansa ba saboda tsananin sihirin wajen. Barban ya ja hannunsa suka zauna akan waɗannan kujeru guda biyu. Barban ya zuba shayi a cikin wani kofi ya kurɓa sannan ya fara bayani, "Wannan waje shine wurin ganawa ta sirri da aljani Ranganu. Aikin da zamu yi da kai na farko shi ne zuwa birnin Askandariyya domin sato farin lu'u-lu'u. Kayi sani cewa wannan lu'u-lu'u darajarsa ta kai dinari milyan ɗari bakwai da sittin. Meyasa zamu sato wannan farin lu'u- lu'u? Ka san cewa ni ɓarawo ne amma bana zalunci hasalima ban taɓa yiwa talaka ko attajirin kirki sata ba, satata tana da ƙa'idoji kamar haka: Bana yiwa talakawa sata, idan naje yin sata bana yin kisa, kafin nayi sata sai na gama kasafin abubuwan da zanyi da kuɗin, bana sata a wurin adilan sarakuna, bana shiri da azzalumi, na ƙarshe a duk sa'adda nayi sata sai na bar alamar da aljani Ranganu ya bani domin ita ce shaidata. "Dangane da ƙa'idojin da na faɗa maka yanzu, sarki Darwazu ya karya ɗaya daga cikinsu. Wannan abu da sarki Darwazu ya karya shi ne, ya yiwa wani mutum zalunci ya ƙwace dukiyarsa saboda tsananin baƙin ciki wannan mutumi ya rataye kansa ya mutu, ya bar ƴaƴa guda biyu, mace da namiji. A halin yanzu suna can cikin birnin Askandariyya suna bara saboda yara ne ƙanana. Ba komai sarki Darwazu ya ƙwace a hannun wannan mutumi ba face wata farar lu'u-lu'u mai tsadar gaske wacce na baka labari. "Asalin wannan lu'u-lu'u mallakin wata gagarumar attajira ce a birnin Askandariyya, ana kiranta da suna Zarshiyya. Wannan mace tana da dukiya har na gaban misali, kwatsam watarana tayi arba da wannan mutumi ta ɗauke shi a cikin fataken dake yi mata fatauci. Koda taga kyawawan halayensa, da kuma riƙo da amanarsa sai ta aure shi. Bayan sun haifi yara guda biyu Zarshiyya ta mutu sakamakon cutar ajali, wannan mutumi ya ci gaba da juya dukiyarta. Watarana sarki Darwazu na bincike a madubin tsafinsa sai yayi arba da wannan mutumi, tsafin Darwazu ya tabbatar masa da cewa wannan mutumi ya fishi dukiya saboda wannan dalili ne sarkin ya tura dakaru suka ƙwato farin lu'u-lu'u suka kaiwa sarkin. Wannan farin lu'u-lu'u shi ne kaso saba'in da biyar cikin ɗari na dukiyar Zarshiyya, saboda yadda ake wahalar samun farin lu'u-lu'u. Ba'a jima da yiwa wannan mutumi fashi ba, talauci ya yi masa yawa ga yara guda biyu da matarsa ta bar masa. Dukkanin ma'aikatan dake aiki a gidansu suka watse, ya rasa wanda zai kula da waɗannan yara bisa wannan dalili ne ya kashe kansa don ya huta da baƙin ciki. Aljani Ranganu ne ya bani wannan labari. "Wannan farin lu'u-lu'u da sarki Darwazu ya ƙwace ya ajiye shi a cikin wani dogon gini dake tsakiyar gidan sarautarsa. Gini ne dogo mai samfurin husumiya. Akwai dakaru kimanin mutum dubu goma suna kai-kawo a wannan wuri, baya ga haka wannan farin lu'u-lu'u a cikin wata akwati aka kulleta. Akwati ne na sihiri wanda ko ya ya mutum ya taɓa shi, wata ƙararrawa mai sautin gaske zata fara kaɗawa ta cika birnin gaba ɗaya. Da zarar anji ƙarar wannan ƙararrawa kowa ƙamewa yake a inda yake saboda dakaru su ji daɗin kama ɓarawon dake ƙoƙarin guduwa cikin ruwan sanƴi. Me yasa sarki Darwazu ya baiwa wannan farin lu'u-lu'u gagarumin tsaro haka? Saboda yana so ya sayi wani katafaren gida ne dake birnin Kisra. Idan baka manta ba wannan gida shi ne wanda na ce maka sarki Kim Sam na birnin Sin yake burin saya a baya kafun na tarwatsa shi. Yanzu sai ka kasa kunnuwa da kyau kuma ka bani hankalinka ɗari bisa ɗari domin ka ji yadda zamuyi wannan sata, ba tare da wannan akwati ta tona mana asiri ba. "Ta ya ya zamu shiga birnin Askandariyya? Ta ya ya zamu shiga gidan sarautar sarki Darwazu kai tsaye? Ta ya ya zamu isa inda wannan doguwar husumiya take? Ta ya ya zamu shiga cikin husumiyar ba tare da dakaru sun kama mu ko kuma sun hallaka mu ba? Ta ya ya zamu saci farin lu'u-lu'u ba tare da akwatin sihiri ta tona mana asiri ba? Idan muka sami amsar waɗannan tambayoyi tamkar mun sami nasara a wannan sata ne." Maigida Barban ya saisaita maƙwagoronsa ya sake kurɓar wannan shayi, yana kallon Aymanul Faris wanda ke cike da tsananin mamaki. "Kamar yadda bayanai suka zo mini daga bakin mai girma Ranganu, birnin Askandariyya na da ƙofofin shiga guda biyu kacal, ɗaya a kudu ɗayar kuma a arewa. A bakin kowacce daga cikin waɗannan ƙofofi akwai dakarun tsaro aƙalla dubu ashirin, babu mai shiga birnin Askandariyya face waɗannan dakaru sun caje shi kuma sunyi masa tambayoyi akan inda ya fito. Shiga birnin ba zai bamu matsala ba saboda babu wanda ya sanmu balle ya san abinda ke cikin ranmu. Za muyi shiga irinta malami da kuma ɗalibinsa masu neman karatu a addinin Darayyish, wani addini ne da mutanen birnin Askandariyya ke bautawa ruwa. Tabbas idan aka ganmu da wannan shiga za'a barmu mu wuce. Kaga mun gama da matsala ta farko wato shiga birnin Askandariyya. "Gidan sarautar sarki Darwazu tana da muggan tsaro, mai girma Ranganu ya ce min, ba mutane ne ke tsaron lafiyar sarki Darwazu ba waɗansu irin halittu ne masu siffa biyu, rabin jikinsu na zaki rabi kuma na mutum. Daga cibiyarsu yayi ƙasa shi ne na zakin, daga sama kuma jikin mutum. Waɗannan halittu Ranganu ya ce suna da tsananin ƙarfin damtse har na Allah ya isa. Zaka iya cewa mu da ba sarki Darwazu zamu kaiwa hari ba meye zai haɗamu faɗa da waɗannan halittu? Hakane, akwai irin waɗannan halittu guda bakwai dake cikin wannan husumiya suna kewaya farin lu'u-lu'u babu dare babu rana, kullum a cikin aiki suke. Matsalar waɗannan halittu shi ne ƙarfin sihirin tsafi baya tasiri akansu sai tsagwaron jarumtaka da iya yaƙi. Ba zamu fuskanci matsalar komai ba a shiga cikin gidan sarautar amma ko ya ya muka yi gangancin zuwa inda wannan husumiya take zamu ga fushin dakarun gidan sarautar. "Kaga kenan da zarar mun shiga gidan sarautar zamu san hanƴar da zamu bi mu shiga cikin wannan doguwar husumiya, inda matsalar take muna shiga zamu yi arba da waɗannan dakaru masu siffa biyu. "Wannan akwati ta sihiri asalinta boka Balwaz ne ya ƙirƙireta, amfaninta kawai shine tona asirin ɓarawo idan yazo satan abinda ke cikinta. Ya kai babban jarumi kayi sani cewa waɗannan dakaru masu siffa biyu da na baka labari, wannan akwati bata aiki akansu. Bansan meyasa ba amma haka mai girma Ranganu ya faɗa min, don haka ta kowanne hali sai mun kashe waɗannan dakaru guda bakwai dake cikin husumiyar mu wanke wannan akwati da jininsu indai mukai haka, ko mun taɓa akwatin ba zata haifar da ƙara ba. "Waɗannan su ne amsoshin waɗannan tambayoyi da na zayyane maka ɗazu. Yanzu sai ka sake saurarawa da kyau domin ka ji amfanina da amfaninka a cikin wannan aiki. "Amfanina a cikin wannan tafiya shi ne zanyi amfani da hikimata wajen amsa tambayoyin da masu gadi zasu yi akan addinin Darayyish, sannan zanyi amfani da hikimata wajen gano hanƴar da zamu bi mu shiga cikin wannan husumiya, sannan zanyi amfani da hikimata wajen ɓoye farin lu'u-lu'u ba tare da an kalleshi a hannunmu ba. Kai kuma amfaninka a wannan tafiya shi ne zaka yi amfani da dukkanin ƙarfin damtsenka yaƙar waɗannan halittu guda bakwai, idan baka manta ba sihirin tsafi baya tasiri akansu. Zaka yi amfani da ƙarfin damtsenka wajen shigar damu cikin wannan husumiya domin ina tunanin ta sama zamu shigo. Zaka yi amfani da ƙarfin damtsenka wajen kare lafiyarka da tawa da kuma abinda zamu sato wato farin lu'u-lu'u. Wannan shi ne taƙaitaccen bayani akan aikin da zamuyi na farko. Shin kana da tambaya ko kuma neman ƙarin bayani?" Aymanul Faris ya yi shuru gami da shiga kogin tunani, yana ta jinjina maganganun maigida Barban a cikin ransa yana tunanin ta ina ya kamata yayi tambaya. "Yaushe zamu je wannan birni na Askandariyya domin wannan gagarumar sata? Ka ce waɗannan dakaru masu siffa biyu ƙarfin sihiri baya tasiri akansu, shin sara da suka zaiyi tasiri akansu kuwa? Idan muka je yin wannan sata za'a ga fuskokinmu ko kuma rufe su zamuyi? Sannan ina so kayi min ƙarin bayani akan sarki Darwazu da zaluncinsa. Waɗannan su ne tambayoyina ya shugabana." Inji Aymanul Faris. Maigida Barban ya gyara zama sannan ya sake kurɓar shayi ya ce, "Yau talatin ga watan Nuwamba. Ranar sha-tara ga watan Disamba zamu je wannan gagarumin aiki. Bani da tabbacin cewa sara da suka yana tasiri akan waɗannan dakaru amma kafin nu tafi zan tambayi mai girma Ranganu. Ban taɓa zuwa nayi sata fuskata a buɗe ba, yana daga cikin ƙa'idar sana'ar sata, koda ba'a san ɓarawo ba yana da kyau ya rufe fuskarsa saboda tsaro. Don haka fuskokinmu a rufe zamuje muyi wannan sata, akwai wata hula da aka dinka a birnin Shuzzus wacce aljani Ranganu ya bani, da irinta zamuyi amfani. "Sarki Darwazu ɓarkeken ƙato ne, sadauki ne kuma jarumi. Asalinsa ɗan ƙabilar Dajjan ne, bayani akan zaluncinsa ba zai wassafu ba face abubuwan da idanu suka gani kawai. Amma kayi sani cewa sarki Darwazu ya taɓa ƙwaƙule idanun yara goma a cikin kogon tsafinsa domin aiwatar da wani sihiri, Darwazu ya taɓa fyaɗe mace mai juna biyu ya fiddo ɗan-tayin dake cikin cikinta yayi tsafi dashi. Ka sani cewa waɗannan dakaru masu siffa biyu dake tsaron lafiyar Darwazu asalinsu waɗansu mayun aljanu ne dake rayuwa akan wani tsauni, basu da abinci da ya wuce naman bil'adama, ruwan shansu kuma shi ne jini. Sarki Darwazu yasan da haka amma ya amince, kullum ci da shan waɗannan dakaru yana wuyan sarki Darwazu. Sun fi shekaru goma suna tsaron lafiyar wannan sarki, kayi kintacen adadin naman da suka ci da kuma jinin da suka zuƙa?" Koda Aymanul Faris yaji wannan batu sai ya cika da tsananin mamakin rashin imanin sarki Darwazu. Ya dubi maigida Barban ya ce, "Tabbas a duniyar nan akwai abubuwan shaiɗanci da zalunci da yawa. Wani abun idan mutum yaji sai yaji kamar ya kashe kansa saboda takaici, mutum da hankalinsa da tunaninsa zai fyaɗe mace mai ciki ya ɗauki ɗan cikinta yayi me da shi? Tabbas dolene mu hukunta wannan sarki." Maigida Barban ya yi murmushi ya ce, "Wannan kaɗan kenan, zakaji sauran sarakuna guda tara da suke cikin littafin harinmu. Su ma zakaji tsantsar rashin imaninsu." Aymanul Faris ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Kuma a duk cikin waɗannan ayyuka guda tara, nima ina da amfani?" Barban ya ce, "Kwarai ma kuwa. Kayi sani cewa wahalar da zaka sha a waɗannan ayyuka namu zasu zamo tamkar horo wajen ratsa dajin Djinn domin riskar ruhin kakanka." Aymanul Faris ya ce, "Yaushe zamu kaiwa dattijo Samazan ziyara domin jin hikayar SAMUDUL ANSARI?" Barban ya ce, "Sai bayan munyi aiki na biyar, zamu je wajen wannan dattijo. Saboda idan muka yi aiki na biyar zamu huta sosai wajen shekaru biyar kafin mu ci gaba." Aymanul Faris ya cika da tsananin mamaki. "Kana nufin zamu shafe fiye da shekaru goma a wajenka?" Barban ya ce, "Kwarai ma kuwa. Shin akwai abinda baka jin daɗinsa anan ne?" Aymanul Faris ya kaɗa kai alamun a'a. Maigida Barban ya dubi Aymanul Faris ya ce, "Ya kai babban jarumi, ina so nayi maka waɗansu tambayoyi? Mene ne a tsakaninka da gimbiya Jaanu? Waɗanne maganganu kuka tattauna lokacin da Marganu yazo ɗaukarta? Shin kana ƙaunar jaruma Riya a cikin ranka?" Koda Aymanul Faris yaji waɗannan tambayoyi sai idanunsa suka zazzaro ya dubi Barban cikin tsananin mamaki, kamar yana mamakin meyasa Barban zaiyi masa waɗannan tambayoyi. "Gimbiya Jaanu? Masoyiyata ce, tana ƙaunata nima kuma ina ƙaunarta. Ba zan ɓoye maka komai ba, saboda kallon ubangida nake ma. Tabbas ina ƙaunar Jaanu fiye da yadda kake tsammani, amma gani nake kamar soyayyar tamu ba zata yiwu ba. Tun da ta bar wannan wuri namu bansan a ina zan sake kallonta ba. Mahaifiyanta ba zai taɓa aminta dani na zama sirikinsa ba, kuma idan na fille kansa gimbiya Jaanu ba zata manta dani ba, saboda baƙin cikin da zan ƙunsa mata. Waye zai ƙaunaci mutumin da ya kashe masa mahaifi? "Maganganun da muka tattauna, bankwana ce kawai irinta masoya, bayan wannan bamu tattauna komai ba. Jaruma Riya? Ƴar uwata ce kuma abokiyata. Idan nace maka bana ƙaunar Riya kasan ƙarya nake, ina sonta sosai amma bata kai matsayin gimbiya Jaanu a cikin zuciyata ba." Inji Aymanul Faris. Maigida Barban ya cika da tsananin mamakin kalaman Aymanul Faris, "Waya ce baza ka iya auran gimbiya Jaanu ba? Soyayya ƙarya ce aka ce ma? Tabbas zaka iya auranta amma bayan ka jure wahala da wulaƙanci." Aymanul Faris ya yi murmushi. "Wahala kuma? Kamar wanne kenan?" Barban ya ce, "Ba zaka taɓa samun nasarar kashe sarki Ayubul Zairiy, sarki Ratanam da sarki Kuffuru ba face ka mallaki ruhin jarumta. A farkon haɗuwarmu sa'adda na baka tarihin rayuwata da rayuwar birnin Shaha naso na baka tarihin waɗannan sarakuna guda uku kamar yadda na

Chapter 12 of 41